Showing 6001 words to 9000 words out of 26471 words

Chapter 3 - Tayi Min Kankanta by Zahra Surbajo

Unknown   

21 Apr 2026

75

iya kuka to ba shakka kukan ze ta rusawa.

A Hankali ya miƙe ya nufi ɗakinshi jiki a sanyaye ya faɗa gado yana nazari,shide
gaskiya tayi mishi ƙanƙanta a aure to in ya aureta yace ya auri wa?shi fyaɗen da
aka mata ba damuwarshi bane kawai de shi yafi son mace ƙatuwa ne.


Muje zuwa


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*11*


Muhammad tsawon sati guda ya kwashe ba inda yake zuwa sabida firgicin da yake
ciki,sosai zancan auransa yasakashi,a damuwa,

Zahra sanda mummy ta sanar mata auranta da muhammad sosai taji daɗi,sabida taga ɗan
uwanta ne,ze rufa mata asiri,dan haka bata da damuwar komai aranta.burinta Allah ya
nuna mata lokacin.dan ita tun haɗa idonta dashi na farko taji ya kwanta aranta.

Sosai walwalarta da jin daɗinta ya ƙaru agidan ba mummy ba har daddy ya fahimci
hakan,wani sanyi yakeji aransa sabida ya mata abinda takeso.

Mummy gyara zahra take da duk wani abu data san baze cutar da lafiyarta ba,,cikin
ƙanƙanin lokaci zahra tayi wani kyau na musamman fatarta ta murje tayi fari har
wani sheƙi take,gashi yanzu ba wata rama ajikinta,sema wata ƙiba data mulka,zahran
inna kenan matashiya ƴar kimanin shekaru goma sha shida.kyakkyawa ajin farko,


Saura kwana biyu ɗaurin aure,muhammad na zaune a lambun gidansu zahra ta ƙaraso
gurin,yana ganinta ya ɗauke kai kamar be ganta ba,murmushi tayi dan tasan baya
sonta,ita ko sonshi take dan haka zatai haƙuri da duk wani halinsa har shima ya
sota,gefenshi taje ta zauna,kamshin da take ne yasashi ɗago kai ya dubeta,sannan ya
maida kansa gefe.

"yaya dama inaso in baka haƙuri ne akan auran dolen da zaay maka"
Ɗagowa yayi ya dubeta rai aɓace yace"au auran dolen ni kaɗai zaayiwa kenan ke banda
ke?"

Murmushi tayi kumatunta suka lotsa tace"banda ni gaskiya,kai de za'a yiwa,ni auran
nagani inaso za'a min,"ta faɗi a kunyace.

Tsayawa yayi,yana ƙare mata kallo,tattaro hankalinshi yayi gaba ɗaya kanta,hannunta
ya kamo ya dibeta a tsanake yace"zahra ni kikeso?"yayi tambayar a tsanake.
Murmushinta me sanyi tayi sannan tace "Tunda naganka,naga kuma irin taimakon daka
ba rayuwata da lafiyata,yaya muhammad naji ina sonka,wallahi da gaske nake har
raina"ta ƙarasa maganar kamar zatai kuka.

Yatsun hannunta yake kallo,sannan ya ɗago ya dubeta yace"zahra to ya zakiyi in kika
fahimci ba matsuguninki a zuciyata?"

"addua zanyi,wataran zaka soni"ta bashi amsa batare da damuwar komai ba.

Murmushin takaici yayi sannan yace"to in kuma ba kya cikin kalar matan da nake so
fa?"

"Zanyi ƙoƙarin maida kaina kalarsu insha Allahu"tabashi amsa.

"to ay ni zahra gaba ɗaya kin min ƙanƙanta a aure,taya zan iya zaman aure dake?"

"wataran zan girma yaya,in zama babba,sede ko kace sauran wanine baka so,inaga
shine kawai dalilin daze hanaka aurena"ta ƙarasa maganar tana kuka,

Runtse ido yayi maganar na masa ciwo a zuciyarsa,a hankali ya dubeta yace"to naji
zahra tashi kije kar mummy ta nemeki,"

Miƙewa tayi a hankali,tabar gurin tana waigenshi.

Shima miƙewa yayi yaja motarsa zuwa Hammad hospital dan ya sanar da amininsa halin
da yake ciki,dan barin kashi a ciki baya maganin yunwa.


Muje zuwa


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*12*



A harabar asibitin yayi parking,sannan ya fito ya taka zuwa office ɗin aminin nasa.

Da sallamarsa ya shiga office ɗin cike da fara'a ya taso suka rungume juna,suna ɗan
dukan juna a baya,sannan suka koma kan doguwar kujera suka zauna.

Muhammad ne ya fara magana cikin yanayin damuwa"Abokina ina cikin damuwa fa,?"

"wacce irin damuwace wannan,?"abokin nasa ya buƙata cike da kulawa.

"jibi daddy ze ɗauramin aure da wata ƴar ƙanwarsa,na rasa inda zan tsoma raina".
A razane ya miƙe tsaye yana ja da baya,take duk wani annurin fuskarsa ya kauce
kamar wanda yacewa gobe ze mutu.

Cikin kakkausar murya yace"HAMMAD kana nufin alƙawarin auren ƴarfillo daka lalatawa
rayuwa yatashi a banza kenan?"

Miƙewa muhamnad yayi ya ƙaraso kusa da abokin nasa ya dafa kafaɗarsa yace"JAMEEL
kafi kowa sanin irin son da nakewa ƴarfillo,wallahi babu macen dana keso a zuciyata
sama da ita,kullum jameel bana iya bacci sabida ita,wallahi akan ƴarfillo zan iya
ɓata ran kowa,sede itama wannan dazan auran akwai abun tausayi game da
itan,kwatankwacin kaddarar data faɗawa ƴarfillo itama hakanne,wallahi zan auri
yarinyar ne,kodan jihadin da zanyi na auranta Allah ya kawomin ƴarfillo na cikin
sauƙi,pls jameel in baka fahimceni ba bame fahimtata"muhammad yayi maganar kamar
zeyi kuka.

Waigowa jameel yayi,ya dubi hammad yace "b haka bane hammad ay kai mijin mace
huɗune,bana de so ne sanadin auran da zakayi ka mance da ƴarfillo shine yasa"

"har abada bazan mance da ita ba jameel,kuma zanci gaba da nemanta har se inda
ƙarfina ya ƙare"Muhammad yafaɗi cike da tabbatarwa.

Jameel kwantar masa da hankali yaci gaba dayi akan auransa da zahra,inda yace ya
daure yayiwa daddy biyayya hakanne zesa in ya kawo ƴarfillo ya amince ya aureta.

Sosai Muhammad ya gamsu da shawarar aminin nasa,duka yakaiwa jameel yace yana
dariya"wato jameel,da ace yadda kanka ke kawo wuta haka zuciyar ka take da nigeria
batayi asarar soja ba,amma wai daga harbi ɗaya a baya,sega resigning letter wallahi
ka bada maza,ay gashi nan ka ƙare a kallewa mata al'aura,da wuri zaka makance"ya
ƙarasa maganar yana dariya.

Duka jameel yakai masa yace"ay duk namijin da baya gudu baya tsawon rai,da asara
gara gidadanci,taya na hango lahirar nasha da ƙyar zan bari a ƙarasa ni,kaima kaga
zaka iya ne shiyasa baka fita ba"

"bazan taɓa barin aykin soja ba Jameel sede in ze shiga tsakanina da ƴarfillo to
tabbas zan fita".

Haka de sukai tayiwa juna barkwanci,basu rabu ba se dare,agajiye muhamnad ya dawo
gida,zuciyarshi fal farinciki kamar yaga ƴarfillonsa.

To bari mu waiwaya baya😄

Kowa ta turo data se in ci gaba😎


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*



*Page 13*
Mikewa tayi ta koma dakin ta, kudi ta dauko tasa hijabi,ta nufi gun megadi,yana
hango ta nufo shi yataso da sauri yadan risina yace "barka da safiya hajiya,me kike
da bukata?"amsawa tayi cikin sakin fuska tace"baba don Allah cefane nakeso
kayomin,a wuse market,"

"To badamuwa ranki ya Dade kawo aje ayo miki"

Lissafa masa komai tayi sannan ta bashi kudin kimanin dubu tamanin,yatafi .

Kulle gidan tayi ta ciki sannan ta koma cikin gida,wanka ta shiga sannan ta shirya
ta dawo falo zaman jiran akawo mata cefanen.

Baa jima sosai ba megadi yashigo mata da sakonta bayan ta bude masa gidan,sosai tai
masa godiya sannan ta kwashe komai takai dakinta.

Dan karamin gas din datasa ya siyo mata ta kunna ta daurayo tukunyar daya siyo mata
tazo ta hada komai ta Dora indomie acikin dakin Nata.
Dan duk abinda zata bukata seda tasa ya siyo mata.

Haka taci gaba da gudanar da rayuwarta a kulle acikin daki,koda wasa batason ganin
Rayhan, shiyasa ta kulle kanta aciki,sabida akwai toilet acikin dakin Nata,

A nashi bangaren Rayhan ko tunda ya fice yabar gidan,kotu yaje ya shigar da karar
doctor Amina sakamakon abinda sukawa matarsa,inda alkali yabada sati biyu su
hallara agabansa.

Lokacin da sakon ya riski doctor Amina,tashin hankalin data shiga,bashida
adadi.Neman Farhan take a waya tun lokacin data ga su Rayhan din amma bata
shiga,wannan shine yakara daga hankalinta.

Ranar shiga kotun da safe Rayhan yaje kofar dakin na safna yace cikin dakewar
murya.
"Ki bude kofa ki fito mu tafi kotu Dan yau alkali yabada mu hallara agabanshi ina
jiranki a mota"yana kaiwa nan yayi fucewarsa abunsa

Safna jin maganar tayi kamar saukar Aradu,yau itace Rayhan yakai kara kotu?wannan
wacce irin masiface.
Tunda ya fada tasan dagaske yakeyi,Dan karya bata daya daga cikin halayensa.

Jiki asanyaye ta janyo hijab tasaka,ta zura takalmi ta fito.bayan ta kulle dakinta.

A motar ta sameshi yana cika yana batsewa,ba me cewa shine Rayhan din ta me yawan
murmushi.

A harabar kotun suka samu doctor Amina ma ta iso ita da maaikatan da suka gudanar
da aykin.

Karasawa gunta Safna tayi suka gaisa,inda doctor Amina tace"Safna kinga kaddara
ko?"
Hawaye ne suka gangaro daga idon Safna masu zafi sannan tace"doctor ina cikin
tashin hankali"

Karasowar Rayhan gurin ne ya katse musu hirar,inda ya dakawa Safna tsawa da cewa
"wuce mutafi".ba musu tabishi abaya suka shiga cikin kotun.

Bayan kowa ya hallara ne me gabatar da kara yatashi ya gabatar da karar da Rayhan
Hashim ya shigar agabanta,yana me kalubalantar doctor Amina,da sauya kwayoyin
halittarsa Dana wani ta sawa matarsa,Wanda hakan ya janyo matarsa ta dauki
ciki,yana me rokon kotu datasa matarsa ta zubar da cikin,kuma yanaso kotu me adalci
da ta bi masa hakkinsa.

Bayan an gabatar da kara ne alkali ya bukaci ganin doctor Amina,jiki asanyaye ta
karasa inda aka tanada domun tsayuwar Wanda ake tuhuma taje ta tsaya.

"Munaso ki gabatar mana da kanki"cewar alkali,

"Sunana Amina Galadima,likita,kuma mamallakiyar Asibitin Galadima special hospital"

"Kinji korafin da aka shigar akanki shin haka akayi koko kina da ja game da
hakan?"alkali yasake jefo mata tambayar.

"Duk abinda aka fadi ranka ya Dade haka ne,sede ba nice da kaina na gudanar da
aykinba, kuma kuskuren suna aka samu ta hanyar kamanceceniyar suna,ina me rokon
kotu datai mana sassauci".ta kwashe komai ta sanar da kotu gamida mika takaddu na
bincike da kuma duk wani Abu daya shafi dashen tun kan ayi har zuwa bayan anyi,

Alkali ya bukaci maaikatan da suka gudanar da aykin dasu gabato gabansa,suma suka
amsa sune suka yi,

Bayan dogon rubutu alkali yafara magana,"Bayan nazari da bincike,wainda ake tuhuma
basu wahalar da sharia ba kotu ta gamsu da duk bayanan kowanne bangare,kuskurene
babba suka aykata,Wanda dole ay musu hukunci,Na farko,kotu ta yankewa doctor Amina
hukuncin biyan Tara ta dubu Dari,bisa laifin daukar maaikatan da suke sakaci da
aykinsu,su kuma wainda suka aykata laifin,kotu na umartar da akaisu gidan gyaran
hali na tsawon wata guda,ko zabin Tara,ta dubu goma goma"kotunce ta hargitse da
surutu,kamin alkali ya tsawatar akai shuru, sannan yaci gaba

"Kotu na kira ga Rayhan da yayi hakuri bisa faruwar wannan Lamari,sabida kotu
bazata sa Safna ta zubar da cikiba, Wanda aykata hakan zunubine,kuma shi wannan Abu
daya faru,shima kuskuren ne babba, duba da tabbaci da aka samu daga bakunan
maaikatan na cewa cikin an sameshi bada kwayoyin halittarka ba,kuma kamin ayi an
tabbatar da bata da ciki,bayan anyi kuma baka kusanceta ba seda aka tabbatar da ta
samu cikin,hakan ya tabbatar da cewa cikin jikinta ba naka bane,Dan haka kotu ta
sallami wannan karar"

Gaba daya kotun ta kaure da hayaniya,Safna kuka take kamar ranta ze fita, wannan
kaddara dame tai kama.

Haka ta mike tabi bayan Rayhan din daya fita afusace,

Sede kamin ta karaso tuni yaja motar sa yabar harabar gurin,Dan shi Sam ba haka
yaso ba,so yayi asa safna ta zubar da cikin, sannan adaure doctor Amina, amma gaba
daya ba hakan akayiba,

Hakanne yasa shi tunanin anya ma kuwa alkalin yasan aykinshi?


Muje zuwa


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*AURE DA HAIHUWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Zahra Surbajo*
*Inna Ibrahim kime alkhairin Allah yakai miki, ina alfahari da haduwa dake
arayuwata.*

*14*


Doctor Amina ce ta karaso inda take ta dafata, da sauri ta waiga taga waye,
Ganinta ne yasa ta rushe da kuka ta fada jikinta tana fadin,"doctor ki taimakeni
banason rasa aurena,Ina son mijina sosai"tayi shuru sakamakon kukan dayaci
karfinta.

Jan ta zuwa mota doctor tayi sabida jamaa sun fara taruwa akansu,da gudu ta fice
daga harabar kotun.

Safna ko se aykin kuka take,har suka iso kofar gidan Rayhan din,bude mata kofa tayi
ta fito,sannan tace"gobe zan dawo in mijinki ya fita Dan musan yadda zaa bullowa da
abun ki kwantar da hankalin ki"

Jiki ba kwari ta tura kofar get din tashiga ita kuma doctor taja motarta ta bar
gurin.

A harabar gidan tasameshi tsaye yana huci,kamar wani maciji,bata bi takanshi ba
tayi hanyar shiga ciki,wata tsawa ya daka mata sai da cikinta yayi juyi ta waigo a
firgice,.

Tsayawa tayi cak a inda take,har ya karaso,cikin fushi yake magana "Safna koda wasa
ban dauka zaki ketare maganata ba,nadauka son da kikemin na gaskene,shiyasa na baki
umarnin zubar da ciki amma kika ki,to ni bazan iya zama dake ina kwasar bakin ciki
ba,Dan haka zan baki zabi wallahi sede ki zaba ni ko cikin jikin ki?"ya wurga mata
tambayar batare da shayin komai ba,

Cikin kuka Safna ta tsuguna agabanshi tafara bashi hakuri"don Allah Rayhan kayi
hakuri, kasan ina sonka, wlh nafi sonka akan cikin jikina,fushin Allah ne kawai
banason na fada,sakamakon zubar da cikin,don Allah ka fahimceni"ta karasa maganar
cikin kuka.

"Zabi na baki malama ni ko cikin jikin ki?"yafadi batare daya tausaya mata ba.

Rokonshi take da duk iyawarta kan yayi hakuri amma fafur ya kafe,ganin bata da
mafitane yasa ta mike tsaye ta share hawayen ta tace asanyaye "na zabi cikin jikina
Rayhan"

Kallon mamaki yay mata sannan yace "to kije na sauwake miki aurena dake kanki,na
sakeki saki daya"ya yi saurin barin gurin sakamakon kukan dakeson kubce masa,yana
son matarsa,yayi iya yinsa Dan yaso abinda ke cikinta amma yakasa,shiyasa ya sake
ta gudun kar zuciya takai shi halaka.

Safna ji tayi duniyar tai mata nauyi,rasa abun yi tayi kawai seta kife agurin tana
kuka,ta jima tana kukan kamin ta rarrashi kanta ta mike,ta shiga cikin
gidan,dakinta ta shiga,ta hada kayanta na sawa se Jakarta ta hannu,

Ta janyo akwatin ta fice,daga falon tana kuka.

Shima dake tsaye ta window yana kallonta kukan yake kamar yabita,sede hakan da yayi
shine masalaha agareshi.
Tana fita, taxi ta dauka drop zuwa jabi park, tana isa motar Daura ta hau,fasinga
daya dama suke jira Dan haka direba yaja motar suka nausa kan titi.


Muje zuwa


Surbajo for life
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*Marasa lafiyanmu Allah kabasu lafiya,masu ciki Allah ka saukesu lafiya,Allah
kazaunar da kowa agidan auranta lafiya,Ameen*

*15*


Da asuba,da kanshi ya tasheta yabata jallabiyarsa tasa tayi rolling da rawaninsa
tayi sallah,sannan ta koma bacci bayan ta cire masa rigar tasa,

Bata farka ba se tara na safe,tuni hammad yayi wankansa ya kimtsa,jin motsin da
yayine yasa yazo ya sameta a zaune ta farka,rigarta take ƙoƙarin sawa amma zafin da
gun ƴunar jiya ke mata yasa ta kasa sawa sabida rigar bata kai jallabiyar daya bata
faɗi ba.

Da sauri ya ƙaraso gurinta,ɗago ido tayi ta kalleshi sannan ta sunkuyar da kai,

Zama yayi kusa da ita har jikinsu na gogar juna,waigowa tayi asanyaye ta kalleshi
shima ita yake kallo,hannu yasa ya zagayota dashi ya kamo rigar yasa mata,sunkuyar
da kai tayi ta runtse ido sabida zafin da taji,a hankali yace"sorry,"gyaɗa kai tayi
sannan ta miƙe,ta fice daga ɗakin,yabi bayanta da kallo,yana haɗiye wani miyau.

Se da ta fice ne kuma kunyar ta faɗo mata,to tacewa mummy agurin wa ta kwana,kasa
ƙarasawa cikin falon tayi ta tsaya tana wasi-wasi.

Hammad ne ya fito zashi gaida iyayen nasa,anan yaci karo da ita tsaye tana
tunani,ƙarasowa yayi inda take,yace"ke lafiyarki ƙalau kuwa,tsayuwar me kikeyi
anan?"
A raunane ta ɗago idonta ta dibeshi tana hawaye tace"kunya nakeji suji na kwana
agurinka"

Murmushi yayi sannan yace "sabida kin kwana da kwarto ko?"

Da sauri ta girgiza kanta tana faɗin "Allah ya tsaremin miji da zama kwarto,ni
mijina ba kwarto bane,aniyarka ta bika"sam ita ta mance ma matsayinsa agunta take
wannan batun.

Be kulata ba hannu yasa yaja hannunta suka nufi falon,itako tirjewa take tana kuka
tana "wallahi bazaa ganmu atare ba,nide kasakeni ka tafi kai kaɗai"a haka suka
shigo falon,inda mutanen gidan ke zaune a dinning suna karyawa,ɓurarin da zahra
kewa Hammad ɗinne ya dawo da hankalinsu kansu,
Shiko Hammad be saketa ba seda suka shigo falon,ay tana ganinta gaban su mummy,da
sauri ta ɓoye abayanshi,duk yadda Hammad ya kauce itama da gudu zata koma
gurin,sosai abun yaba su daddy dariya,a hankali daddy yace "rakata ɗaki mana
muhammad,ka tsaida ita anan"

Murmushi yayi sannan yaja hannunta zuwa ɗakin nasu se ɓoyewa take agefensa.

Seda ya kaita sannan ya dawo gun mahaifan nasa,tsugunawa yayi ya gaishesu sannan
yaja kujera ya zauna,

"Angama shirya komai na gidan da zaku zauna,anjima mummynka zasu kaita gidan,ka
kwantar da hankalinka"daddy ya faɗi yana murmushi.

Sosai kunya ta kama Hammad,ya sosa ƙeya yana murmushi yace"daddy ay ko anan ɗinma
zamu iya zama"

"kuci gaba da mana rashin kunya a cikin gida ko?"daddy ya buƙata.

Shuru Muhammad yayi dan se yanzu yagano ma manufar daddyn.

Haka yayi break fast duk a tsarge,yana gamawa ya miƙe ya bar falon.

Shiryawa yayi ya fice zuwa gun amininsa Jameel,kasancewar yana hutu be koma bakin
aykiba.

Surayya ce tasamu zahra a ɗaki tayi wanka ta kimtsa cikin wata atamfa ja da milk me
golden tayi kyau matuƙa.
Tana shiga ta fara mata tsiya,"kaga amaryar yaya,me bin angonta ɗaki"duka zahra
takai mata tana faɗin"zanko haɗaki dashi,bari muhaɗu"

"ayya yarinya kwantar da hankalinki yau zaa kaiki gidanshi seku dena satar hanya"ta
ƙarasa maganar tana tuntsira dariya,

Zahra de ba baka se kunne,seda su mummy sika bar falon sannan taje tayi breakfast
ɗinta.

Da magriba su mummy da ƙawayenta guda biyu suka kai zahra gidan auranta daya gaji
da haɗuwa,se kuka take wurjanjan ita bazata zauna ba,

Surayya aka baro agurinta azuwan in Hammad yazo yasa direba yakawota gida.

Hammad ko suna can shida jameel yana ƙara kwantar mai da hankali,akan auran nasa da
zahra,tare da bashi tabbacin insha Allahu zasi ga ƴarfillonsa,

Sai da ishai daddy ya kirashi awaya ya shaida masa tun ɗazu ankai masa matarsa
gida.

Jameel ne yasa shi yayi wanka ya kimtsa awata sabuwar shadda ta jameel
ɗin,sannan,suka fito domin yamasa rakiya,kaji da madara suka siya sannan suka
ƙaraso gidan.
Jameel besan me yasa ba amma lokaci zuwa lokaci gabansa na yawan faɗuwa,a haka suka
ƙaraso gidan.

Muje zuwa


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra surbajo*


*banida lafiya ne,kuma ga mara lafiyan danake kulawa da ita,shiyasa abubuwan suka
chushemin,pls asamu a addua,Allah ya bamu lafiya*


*16*



A harabar gidan sukayi parking a gurin da aka tanada domin hakan.
Fitowa sukayi fuskokinsu ba yabo ba fallasa,suka nufi cikin gidan.

Sallama Hammad yayi afalon amma baa ansa ba,hakanne yasa ya fahimci tana ɗaki.

"zauna mana ka tsaya kamar baƙo,bari inje in kirata ku gaisa"Hammad yace yana
ƙoƙarin haurawa benen.

Zama jameel yayi a sanyaye shi ya rasa meke damunsa da yasa yanayinsa ya sauya.

A gefen gado ya sameta zaune,ta lulluɓe fuskarta da jikinta da mayafi,ko baa faɗi
ba kuka takeyi.

Sallamarsa ce tasa ta ɗago dara daran idanuwanta ta dubeshi suna tsiyayar da
hawaye,
Tausayinta ne ya kama Hammad,a hankali ya ƙarasa kusa da ita ya zauna,ya sa hannu
ya dafo kafaɗarta yace a sanyaye.

"kince kina sona ke ba auran dole aka miki ba,to kuma se gashi se kuka kike kamar
wacce aka yanka,ko kin dena son nawa ne?"

murmushi tayi sannan ta girgiza masa kai,
"to tunda ba haka bane share hawayenki kizo muje falo gun babban aminina ku gaisa
tare muke dashi"

Share hawayen tayi sannan ta miƙe shi kuma yayi gaba,da sauri ta ƙarasa jikinshi ta
ruƙo hannunsa ta kwantar da kanta a gefenshi.

Hammad bece komai ba ya buɗe ɗakin sika nufi falon.a hankali.

Jameel tunda suka jero sosai suka burgeshi,yaji dama ace da ƴarfillo yaga aminin
nasa dase yafi jin daɗi.

Kujerar dake kallon ta jameel ɗin suka zauna fuskarta a rufe da mayafi.

"A gaskiya ba abinda zamu cewa Allah sede godiya,daya kawomu lokacin da aminina ya
fita akasuwa"cewar jameel yana murmushi.

Dariya Hammad yayi sannan yace"zakuma mu ƙara godewa Allah in ya nuna mana ranar da
kaima zaka bar kasuwar"gaba ɗaya suka tuntsure da dariya.

Ita de zahra ba dan kar ta gasgata kunnenta ba da se tace tasan muryar nan da
jimawa,amma seta kauda tunanin hakan.


Sosai jameel yay musu faɗa da tunasarwa kan suji tsoron Allah inda aƙarshe
yace"kuma shi aure ibada ne kowacce ibada abar tambaya ce agurin Allah kaji
tsoronsa,kar son da kakewa waccan yarinyar yasa ka cutar da wannan,wallahi Allah
baze barka ba".

A sanyaye Hammad yace"insha Allahu son waccan baze cutar da wannan da komai ba,zan
kula"

Miƙewa jameel yayi yana duba agogo,yace yana kallon zahra data rufe fuska da
mayafi"Amarya me rowar fuska,gashi har zan tafi banga kamannin amaryar ba"

Da sauri hammad ya kamo mayafin nata yana dariya yace"tuba muke ina zaa yima rowar
fuska ay dole ka ganta,"ya ƙarasa buɗe masa mayafin data rufe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login