Showing 1 words to 3000 words out of 26471 words
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*Sadaukarwa ga Ahalin Sharoo Gambo Yako,mazan su da matansu,alherin Allah yakai
muku a duk inda kuke,nayi tawassali ga Annabi Muhammadu (SAW),Allah kai ruƙo da
hannayena dan alfarmar ahalin manzon Allah (SAW)*
_Bissimillahirrahmanir raheem_
_wannan littafin nawa ƙirƙirarsa nayi banyishi dan wani ko wata ba,duk abinda kaga
yayi dede da rayuwarka arashine_
_wannan daban yake da sauran,salonsa na dabanne,akwai abun dariya,zazzafar
soyayya,tausayi,ƙiyayya,da ɗumbin danasani,karku bari abaku labari,kubishi sannu a
hankali dan kwashe darasin dayake tafe dashi_
_surbajon ce de har yanzu,salo da basirar duk nata ne,nice da kaina ba saƙo ba,ga
me_
*Ummu Aymana*
*Surbajo*
*Kano to jiddah*
*Karen bana*
*Sanadin kidnapping*
*Ɗan karuwa*
*Cin Amana Ko Fansa*
*Giɗaɗo ba Shege Bane*
*Allah Gatan Bawa*
*Ƴar Bautar Ƙasa*
*Aure Da Haihuwa*
Da de sauransu.ku kasance da wannan banufiya domin ci gaba da samun nishaɗi.😍
*1*
"Zahra'u ya kamata ki fito haka fa kizo ku wuce,tun ɗazu su hanne ke tsaye suna
jiranki,bana son sakarcin banza fa"cewar wata dattijuya dake zaune kan kujerar
zaman tsakar gida tana ɗaure nono a ledar siga.
Daga can cikin bukkar dake kusa da dattijuwar wacce aka kira da Zahra'u tace "Inna
do Allah Do Annabijjo,ki barni in sa jambakina cikin kwanciyar hankali,ke bakisan
in bakayi kwalliya ba ko kallonka ba'a yi?"
"aykin kawai,yo tun bara kike sa jambakin amma har yanzu ba mashinshini,se asarar
kuɗin siya miki da nike yi"cewar inna daga wajen da take zaune.
Fitowa tayi daga cikin bukkar tana gyara ɗamarar da ta ɗaura a ƙugunta,ko ina a
fuskarta kwallliyace irin ta fulani.
Laɓɓanta shafe cikin jan janbaki,yarinyace da bata wuce shekaru goma sha biyar ba.
"kede Inna kinada matsala,bakin ki be taɓa faɗin alkha'iri,se sharri,ni ɗoramin mu
tafi"ta ƙarasa maganar cikin turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.
Gammo ta ɗora sannan ta ɗora mata kwaryar nonon akanta,ta miƙa mata ledar viva da
aka sa ludaya da ƙorai aciki,ta juya gun su Hanne dake tsaye zaman jiranta tayi
murmushi kumatunta suka lotsa,siririyar hushiryarta ta bayyana atsakanin fararen
haƙoranta masu kyan tsari,tace "na ɓata muku lokaci kuyi haƙuri,mu tafi kar mu sake
ɓata wani lokacin"
Murmushi sukai mata,sannan suka rankaya suka fice bayan sunyiwa inna sallama.
Tafe suke suna hirar su ta yau da kullum,ɗaya daga cikinsu Me suna haule tace"wai
duk ƙawancen nan namu muna aure inba riga ɗaya muke ba se ya ragu ko?"
Dariya Zahra'u tayi sannan tace,"Allah ya kyauta,ni aradu ko birnin sin naje aure
bazan dena ƙawance daku ba,bare ma dukanmu muna ruga ɗaya ba inda zamu"
Hanne ce ta amshe zancen da cewa"ni Auran ma tsoro yake ban,kunga de Ma'u kamar
abun arxiƙi Rabi'u ya Aureta amma ku dubi wulaƙancin da yake mata yanzu"
"shiyasa na shiga makaranta dan bazan yarda namiji yamin wulaƙanci ba,"cewar
Zahra'u tana murmushi.
Da wannan hirar tasu suka ƙarasa fitowa daga cikin dajin falgore inda rugarsu
take,suka miƙo tsawon titin zuwa inda barikin sojojin dake cikin dajin yake,sabida
ankawo sababbin sojojin da ake ba training gurin acike yake da mutane kamar
kasuwa,dan motocima in sun zo gurin da ƙyar suke wucewa sabida yawan sojojin.
Basu jima da zuwa ba kowa kayanta ya ƙare sabida ƙarancin abincin gurin,a hannu a
hannu ake siyan duk wani abun ci na gurin.
gurin me saida burodi suka ƙarasa kowa ta sayi guda ɗaya sannan suka juya cike da
farincikin sun sayi burodin da zasu ci yau agurin alibidin sunan Zina,wata ƙawarsu
data haihu.
Karo suka ci da wani matashi sanye da wandon sojoji,hannunsa riƙe da bindiga,se
riga tshits army green da hular sojoji,ba laifi kyakkyawane,raɓewa sukayi zasu wuce
ta gefenshi yayi sauri yasha gabansu yace yana murmushi,
"don Allah kuyi haƙuri mu baƙi ne anan,kuma abinci mukeso mu ci,isowar mu kenan
daga Abuja,amma mun rasa"
Harara Zahra'u ta galla masa sannan tace"amma dan baƙin hali ay kuna gani muka kawo
tallan nono, in yunwar kukeji me ya hanaki siya?"
Murmushi yayi dan ya fahimci yarinyar akwai tsiwa,cikin taushin murya yace"Bamu
lura bane ƙanwata,ayi haƙuri"
"to yanzu me kukeso muyi muku,tunda mude ba abinci bane bare ku cinyemu"cewar
Zahra'u batare da tsoron komai ba,dan ita ba ƙaramin abu bane ke firgitata.
"in anan kuke don Allah ku taimaka mana, kuɗin cefane zamu baku ku dafo mana
abincin ku kawo mana nida abokina,"
Shuru sukayi sannan hanne tace"gaskiya rigarmu da nisa nide bazan iya zuwa gida in
dawo ba"
"yo inba wahalalle ba waye zeje gida yadawo nan"cewar haule.
"don Allah ku taimaka abokina yanada lalurar gyambom ciki be jure yunwa don Allah
ku taimaka ku yi mana kamin yafara jin yunwa wallahi zamu biyaku ladan yi"cewar
matashin kamar zeyi kuka.
Zahrau tsintar kanta tayi da tausayawa abokin nasa,sabida itama tana da lalurar
gyambom cikin tasan azabar ziwon,dan haka tsintar kanta tayi da cewa
"kawo kuɗin,zan dafo muku,sede muna da nisa zaku iya jira?"
Da sauri matashin ya gyaɗa mata kai,sabida tun ɗazu yake neman wanda ze dafo musun
amma be samu ba,ga abokin nashi shegen taurim kai shiba jure yunwa ba amma ko ze
mutu baze ci abincin siyarwa ba,shiyasa duk yabi ya damu.
Hannu yasa a aljihu ya ɗebo kuɗin dashi kanshi besan adadinsu ba yabata,juya kuɗin
take a hannunta tana mamaki,amma batace komai ba ta ɗauka da yawa suke so, dan haka
ce mishi tayi"zan kawo ma insha Allahu ka tsaya a bakin titi de inda zan ganka da
wuri"
Godiya yay mata sosai sannan yace"mu haɗu kawai anan,zefi sauƙi,sunana Capt Jameel
Ahmad zan jiraki anan"
Bata ce komai ba suka juya suka wuce ita da ƙawayen nata,wanda gaba ɗaya haushinta
sukeji,cikin fushi hanne tace.
"nufinki de bazaki gidan sunan ba ko?shiyasa kika amshi girkin gardawan da baki
sani ba"
Batare da damuwar komai ba aranta tace"dan bakusan ciwon ulcer bane da kuma kun
tausaya kun musu,nide zan musu sabida Allah".tana kaiwa nan tai gaba ta ƙyalesu a
baya.
Muje zuwa.
Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*2*
Gudu-gudu sauri-sauri Zahra'u ke tafiya zuwa gida,dan azahar ta kusa,
Tana shiga gida bukkar innarta ta shiga da sallamarta.
"wai har kun siyar?"cewar inna bayan ta amsa sallamarta,
Murmushi Zahra'u tayi sannan tace"wallahi inna mun siyar,yanzu ma wasu sojoji
ne,suka roƙeni in dafo musu abinci,yunwa sukeji gashi suna da me ulcer
acikinsu,shine na dawo in musu"daga haka ta kwashe komai ta faɗa mata,gami da bata
kuɗin.
Sosai inna ta tausaya musu sannan tace"Allah miki albarka Batulu na, daɗina dake
akwai tausayi, maza zo kije ki cefano abinda yadace ayi sauri ayi musu"
Daga haka miƙewa sukayi suka fito tsakar gida,inna ta bata kuɗin cefanen ta tafi.
Kamin la'asar sun kammala komai,abinci lafiyayye bame cewa daga rugar aka
girkoshi,domin,harda,cincin,dublan,duka masu jimawa basu lalace ba kasancewar can
cikin garin falgoren Zahra'u tazo cefanen,shiyasa tasamu komai.kasancewarta ƴar
makarantar gaba da primary,kuma ɓangaren sciece yasa ta iya komai,sabida food and
nutrition da ake koya musu.
Ga kaji da zabbi da suka soya musu rabi da mangyaɗa,rabi kuma da manja sabida me
ulcer shima yasamu yaci,suyar sosai tayi kyau.a ledoji ta juye sannan ta zuba
abincin a kular abincin baffanta,
A babbar roba ta zuba komai sannan tayi gammo ta ɗauka,inna ta bata canjin dubu
biyar daya rage tace ta mayar musu,amsa tayi sannan ta juya ta nufi barikin.
Kusan mintuna arbain ta kwashe tana tafiya kamin ta iso bakin titin,sannan ta
ƙarasa gurin da sojojin ke tare.
Inda sukayi dashi zasu haɗu nan ta ƙarasa,ga mamakinta yana tsaye agurin yana
jiranta,yana hangota ya taho da sauri ya tarbeta yana murmushi.
Kama mata kayan yayi ta sauke,sannan tace"kuyi haƙuri wallahi gidanmu da nisa ne
shiyasa"
Murmushi yayi yace"Ko kaɗan baki buƙatar bamu haƙuri,mune yakamata muyi
hakan,mungode sosai,Allah saka miki da alkhairi,"
Canjin ta miƙo masa tace "ga canjin ku inna tace in dawo dashi,kuma tace tanawa
abokin naka me ulcer ya jiki dafatan Allah ya bashi lafiya"
Sosai wani jin daɗi ya bayyana a fuskarshi,aranshi ya yaba da tarbiyyarta,cikin
murmushi yace"ki maidawa inna kuɗin kice mungode"
Fafur taƙi amsar kuɗin,duk yadda jameel yayi da ita ƙin amsa tayi dole ya maida
kuɗin aljihunsa,
"gobe in munzo talla zan tafi da kwanukan"tace sanda take ƙoƙarin tsallaka titi
domin ta koma gida.
Sallama sukayi ta tafi,jameel yabi bayanta da kallo yana yaba natsuwarta da
hankalinta.
Duƙawa yayi ya ɗauki,robar abincin ya nufi tantin da suka haɗa na tempol sabida
ruwa da rana,kamin ay musu izinin shiga cikin barikin.
Zaune yake daga ƙarshen tantin,yana latsa wayarshi,hannunshi ɗaya,riƙe da
bindigarsa,
Farine sosai yana da ɗan faɗin fuska kyakkyawa ajin farko,sede ko kaɗan ba fara'a
fuskarsa.
Sanda jameel ya shigo tantin,a yatsine ya ɗago kyawawan idanuwansa ya kalleshi
sannan ya amsa sallamarsa.
Robar abincin ya ajiye akusa da shi sannan ya shiga ciro kayan dake ciki,
Buɗe ledar soyayyun kajin yayi,sosai yayi mamakin ganin harda wanda aka soya da
manja,
Ƙamshin abincin ne,yasa ya ɗago kansa da sauri yana bin ledar da kallo,da sauri ya
matso kusa da jameel,yana faɗin"kunyi waya da mummy ne?"ya tambaya cikin zaƙuwa.
"me ka gani"jameel ya tambaya.
"itace kawai take soyamin kaza da manja sabida ulcer ta,shiyasa nayi zargin kunyi
wayane"
"ko kaɗan,wannan wasu nasamu suka dafo mana,daga cikin garin nan,ka matso kaci
abinci kasan tunda mukazo baka ci abinci ba tun ɗazu hankalina be kwanta ba sabida
baka ci abinci ba"
Tausayin jameel ɗinne yakamashi ganin yadda yadamu dashi fiye da kansa,yasan duk
ƙoƙarinnan yayine domin shi.
Ba musu ya matso yasa hannu ya ɗauki cinyar kazar yasa abakinsa,daɗin daya gauraye
bakinsa sosai yatafi dashi,zagewa yayi yaci abincin sosai dan wannan girkin ma yafi
na mommynsa daɗi.
Bayan sun gama cin abincin,su cincin da dublan din duk acikin jakun kunansu suka
saka,sabida taimakon gaggawa,abincin kuma rufe sauran sukayi,sabida dare.
Se a lokacin suka samu natsuwa,Jameel ne ya dubi abokin nasa yace cike da
kulawa"Gaskiya Hammad yarinyar nan ta iya girki,ba me cewa ita ta girka,ji abinci
don Allah sekace a birni"
Cikin rashin fahimta,Hammad ya kalleshi,yace"dama yarinyace ta dafo abincin?"
"eh yarinya ce dan bata wuce sa'ar su surayya ba,ma'ana bazata wuce 14 to 15 years
ba,nono suke siyarwa na roƙeta ta girko mana"
Sosai abun yaba Hammad mamaki dan shi de in ze iya tunowa ba ya jin ko gas surayya
ta iya kunnawa bare ayi zancen dafa ruwan zafi,to taya yarinya sa'arta za'ace har
tafi mummynsa iya girki,ta ya?
"Dan haka in munyi settling komai zan bita inga gidansu,dan mu dinga zuwa cin
abincin can gidansu mudena sata wahalar kawo mana"jameel ya faɗi yana kallon Hammad
ɗin.
"ba damuwa "Hammad ya faɗi yana nazarin zancen.
"innarta ma tace aymaka sannu gameda ulcer da take damunka "jameel ya faɗi yana
murmushi dan yasan bazasu wanye lafiya ba.
A fusace Hammad ya dubeshi yace"Au kace bara kaje kayi da ciwon dake damuna,amma
wallahi ka cuceni kuma ba inda zani wallahi bazan je gidan nasu ba"ya faɗi sanda ya
miƙe ya fice daga tantin.
Muje zuwa
Surbajo for life
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*don Allah masu cewa asa su agroup ɗinnan kuyi haƙuri ni bana adding,haka kuma bana
tura novel private,iyakacina posting a group,kar ki buƙaci ɗaya daga ciki ban miki
ba kiji haushi,pls*
*3*
Har dare Hammad haushin Jameel yake ji,dan shi a duniya ba abinda ya tsana irin a
faɗawa stranger yana da ciwon ulcer,aganinshi kallon mayunwaci za'a masa.
Haka suka ci abincin se cika yake yana batsewa.
Koda gari ya waye,basu wahala ba cincin sukai ta ci da dublan.
Wajen azahar Hammad yafara jin yunwa,duk yadda yaso ya daure ya kasa dole ya isa ga
Jameel wanda shima tun ɗazu yake kallon hanya yanaso yaga ta ina zata ɓullo.
"ya kamata fa kasamo wasu yaran abasu kuɗin suje su girko mana abinci ni yunwa
nakeji"hammad ya faɗi sanda ya isa ga Jameel.
"karka damu nasan yarinyar jiya zata dawo,tabani tabbacin hakan,mu ɗan jirata
kaɗan"Jameel ya bashi amsa cike da kulawa.
Hammad Juyawa yayi ya nufi cikim tantinsu,Bayan yaba Jameel ɗin wayarshi ya riƙe
masa.kamar jira yana barin gurin Zahrau ta ƙaraso gun Jameel ɗauke da kwaryar
nononta,ɗaya hannun kuma ledar abincin data dafo musu,shinkafa da wake dafadukan
manja taji alayyahu da albasa se ƙamshi take.
Murmushi tayi tace"duk da baku buƙata ba amma na dafo muku wannan,sabida me ulcer
nan"ta faɗi tana miƙa masa ledar da kular abincin take.
Da Sauri ya amsa yace"mungode sosai wallahi,shima yanzu yagama tambayarki,nace baku
zoba tukunna"
Murmushi tayi batace komai ba,Wayar da Hammad ya miƙo masa ya riƙe masa ya ɗaga
yasa camera yace"yakamata muyi hoton tarihi ko ƙanwata?"
Zahra'u murmushi tayi batace komai ba ya fara ɗaukarsu hotuna,tana dariya wani tana
murmushi,har seda yagaji ya dena ɗaukarsu selfie ɗin.
Kwanikan jiya ya bata,dan dama suna ajiye agefenshi,sannan ya ɗauko kuɗi masu yawa
ya bata yace"ki ajiye wannan agurinki ki dinga yo mana girkin,in sun ƙare ki sanar
dani zan ƙara miki,sati uku zamuyi anan mu tafi"
Amsar ƙuɗin tayi tana murmushi,ta juya tabar gurin ta ƙarasa inda suke siyar da
nonon.
Ɗaukar ledar Jameel yayi ya nufi gun Hammad,da hanzari,dan yasamu yaci abincin.
Ganin jameel da abincin sosai ran Hammad yayi masa daɗi,matsowa yayi kusa dashi
yana murmushi duk fushin da yake ya huce,yace"ta zone yarinyar?"
"Kana baro gurin tazo wallahi,yarinyar akwai kirki ga sanin ya kamata,kaga yau tun
kan musa tayi tayo mana"
"naga alamar hakan"Hammad yace sanda ya ciko cokali da abincin ya danna abakinsa.
Lumshe ido yayi yana tauna abincin gashide ba nama akasa ba amma daɗin abincin ya
wuce inda yake tsammani.
Jameel na janshi da hira ko sauraronsa bayayi ya maida hankali kan abincin seda
yaji yacika cikinsa tab sannan ya ajiye cokalin.
Kamar daga sama suka fara jiyo ƙarar harbe harbe da guje gujen mutane ana ihu.
A hankali suka fito daga tantin ga mamakinsu ankashe mutane da dama agurin
musamman ƴan talla da suka zo.
Harbin ne yafara yo ɓangarensu,da gudu suka nufi bayan wani dutse,hankali
atashe,Jameel a firgice ya kalli hammad yace"ƴar filanin nan data dafo mana abinci
tana gurin can,bari inje in taimaka mata kar wani abu yasameta"
Yayi yunƙurin zuwa harbin ya yawaita dole ya tsaya,guri yayi guri domin tankokin
yaƙi aka fito dasu daga cikin barikin aka fara ɓarin wuta tsakanin sojoji da Ƴan
bindigar da suka kawo hari garin,dan tuni sun shiga cikin rigagen sun ƙona komai
sun kashe mutane,shine suka dawo nan bakin titin.
A gigice Jameel yaja hannun Hammad suka ruga da gudu zuwa cikin jejin domin su samu
mafaka,sede ƙarar da jameel ɗin ya kwalla ce tasa Hammad tsayawa ya waiwayo yaga
me ya samu aminin nasa,
Wayyo Allah harbinsa akayi agadon baya,rungumeshi yayi suka faɗi tare,ya tallafoshi
yana ƙarajin kiran sunanshi,"No!!!!!!!! Jameel !!!!!!!! wake up!!!!"!!"yana ihun
jijjigashi,Jameel wanda idonsa ke shirin lumshewa a hankali yace"ka kula da
ƴarfilanin nan Hammad"yana kaiwa nan yafara salati jini na fitowa ta bakinsa.
A gigice yake jijjigashi amma ina jikinshi ya riga ya saki.
Ihu Hammad yake iya ƙarfinsa yana jijjiga aminin nasa,yana kiran sunanshi,amma
shuru,
Harbin da ake yowa ta ɓangarenshine yasa ya miƙe da gudu,Ɗauke da Aminin nasa a
kafaɗa ya ƙara nausawa cikin jejin,zuciyarshi na masa zafi.
Muje zuwa
Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*Hindatou Auwal,wannan shafi sadaukarwane agareki,bisa dogon nazari da kikeyi kamin
kiyi comments akan kowanne post nawa,nagode sosai Allah yabar zumunci*
*4*
Yana tsaka da gudu,yayi tuntuɓe da wani dutse beyi auneba seji yayi sun faɗi,kanshi
ne ya bugu da dutsen amma be damuba ya miƙe sede ga mamakinsa,ko kaɗan baya
gani,hannu yasa ya murje idanunsa sam basa gani duhu ne gaba ɗaya ya mamaye idanun
nasa.
Tashin hankali baa sa maka rana,Hammad dirza idonsa yake iya ƙarfinsa amma ganinsa
be dawo ba,
Faɗuwa yayi agurin yana kuka,yama rasa me zeyi,wannan wacce irin masifa ce,kuka
yake me tsuma zuciya,a hankali ya miƙa hannu yana laluben inda Jameel yake, amma
yakasa jinshi.
Rarrafawa yayi yana ci gaba da lalubawa,Amma be jiyoshi,ba,abinda be sani ba,inda
suka faɗi kusa ne da wani ɗan tabkin ruwa,Jameel cikin ruwan ya faɗa.
A hankali ya miƙe yafara tafiya yana ci gaba da laluben hanya,yama rasa ina zebi
haka yake tafiya,ya faɗi ya miƙe,haka ya nausa cikin jejin yana zubar da hawaye.
Zahra'u ko tunda aka fara harbe harben nan,tasamu ta falla da gudu hanyar
rugarsu,gudu take kamar zata tashi sama,har ta iso,sede ga mamakinta gidan nasu
gaba ɗaya a ƙone yake,ga gawar innarta kwance a harbeta a kai.
Ihu tasaka ta nufi innar tata tana kwalla mata kira amma ina,kifewa tayi akanta
tana kuka me tsuma zuciya.
Kuka take kamar ranta ze fita,tunowa tayi da Jameel dan haka miƙewa tayi da wani
mahaukacin gudu ta koma inda tafito da zummar yazo ya taimaki innarta.
Lokacin data iso titin ne yaƙin ya ƙazanta,dan haka tsallaka titin tayi da gudu ta
nausa cikin jejin domin tasamu mafaka kamim komai ya lafa taje ga jameel ɗin.
Tayi gudu me yawa acikin jejin,ruwan da aka fara yi ne kamar da bakin ƙwarya yasa
ta fara neman mafaka,dan batason dukan ruwan sama,wata tsohuwar bukka ta hanga
acikin jejin dan haka da gudu ta ƙarasa cikin bukkar tana rawar sanyi.
Shigarta ba jimawa shima Hammad ya ƙaraso gurin,jin yataɓa bukkar ne yasa yafara
neman hanyar daze shiga ciki,da saurinshi ya shige shima,ƙofar bukkar yashiga
laluba har yasamu ya ɗauka ya rufe sabida feshin ruwan dake shigowa.gefe ya samu ya
zauna,ga mamakinsa ji yayi ya taɓa mutum a hankali ya ƙara kai hannunsa yana
faɗin"waye anan?"
Zahra'u wacce tunda ya shigo tsoro yagama cinyeta,tace bakinta na rawa "Batulun
inna ce,sun ƙona gidanmu ne kuma sin kashemin inna ta,shine nazo kiran capt Jameel
Ahmad yazo ya taimakamin"ta ƙarasa maganar tana kuka.
Cikin firgici,yace "kece ƴar filanin dake dafo mana abinci?"
Da sauri Zahrau tace "eh nice,kaine abokinsa me ulcer?"
Da sauri shima ya gyaɗa mata kai sannan ya shaida mata Jameel ya rasu,sakamakom
harbin da akai masa.
Sosai take kuka kamar ranta ze fita,daga inda5 yake, yake bata haƙuri gamida
rarrashinta.
Suna cikin bukkar har dare yayi,sosai ake xuba wani sanyi me rikita mutum,zahra'u
se rawar sanyi take sabida zazzabin daya kamata,
Shiko Hammad addua kawai yake ruwan ya tsagaita ya fice daga cikin bukkar sabida
shi irin mazan nanne masu ƙarfin shaawa koya sanyi ya taɓa shi gabanshi miƙewa yake
kamar ze faso masa wando,ga zafin da marainansa suke masa.
Addu'a yakeyi azuciyarsa,Zahra'u wacce zafin zazzaɓi yasata neman inda zataji ɗumi
a hankali ta matso jikin Hammad bakinta na rawa,tace "Soja me ulcer dan Allah ka
lulluɓeni sanyi nakeji"ta faɗi sanda ta kutsa mazaunanta gabanshi ta kwantar da
kanta a kirjinshi.
Wani abu ne ya tasowa Hammad tun daga tafin ƙafarsa zuwa kansa,runtse idonsa yayi
gam yana ambato Allah sanda yaji mazaunan Zahra'u na gugar bananarsa.
Muje zuwa
Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*5*
Ƙara shigewa jikinshi take,sabida sanyin da takeji,a hankali ya miƙa hannu ya
zagayeta,ƙara kwantar da kai tayi ajikinshi tana rawar sanyin.
Duk yadda Hammad yaso ya yaƙi zuciyarshi akan Zahrau ina shaiɗanne ya shiga ƙawata
mishi ita a zuciyarshi..
A hankali yake shafa kanta,sannu a hankali ya zame ɗankwalin dake kanta,gashin
kanta yake wasa dashi,
A zuciyarsa beson abinda yake matan amma shaiɗan yariga dayafi ƙarfinsa,
Ƙoƙarin kwance mata zani yake,se alokacin ta farga ta fara riƙewa,ƙarfi ya gwada
mata ya rabata da zanin yayi fatali da ɗan wandon dake jikinta,
Sanda ya afka mata wata gigitacciyar ƙara ta saki sabida azabar datakeji,cikin kuka
take faɗin"soja me ulcer ba kyau kar kayimin,don Allah ka tausayamin,kayi
haƙuri,soja me ulcer!!!!!!"haka take kuka tana dukan gadon bayansa.
Hammad shima kukan yake,yayi iya yinshi wajen ganin ya kaucewa faruwar hakan amma
ina ciwon da marainansa ke masa da shaiɗan su suka taru sukai galaba akanshi.
Be saurara mata ba seda buƙatarsa ta biya,Ya gangare gefe yana kuka,baiwar Allah
kukan ma gaba ɗaya babushi a idonta ware ido kawai take cikin duhu,
A hankali ya miƙa hannu ya lalubota jikinshi ya janyota ya rungume yana cigaba da
kukan,"Kiyi haƙuri da abinda nayi miki,sharrin zuciyane,kiyafemin nayi alƙawarin
kulawa dake har ƙarshen rayuwata,zan miki gata in zamo katanga agareki,ina matiƙar
ƙaunarki ƴarfillo"kukane yaci ƙarfinsa yayi shuru.
Lamo tayi ajikinshi bata ko motsi se hawaye dake biyo fuskarta,a haka suka kwana
kowa be runtsa ba,shi zazzabi itama haka.
Ratsowar haske cikin bukkar ne yasa Hammad farkawa daga baccin daya saceshi,lokacin
itama zahra'u baccin takeyi.
Kwantar da