Showing 42001 words to 45000 words out of 108975 words
ya matso kusada ita ganin taki daina kukan cikin muryan lallashi da
murya dake nuna asalin so da tsantsan so yace “I know! and it’s okay I am here for you okay”
gyadamai kai tayi tana sauke ijiyan zuciya, hannunshi yakai yakamo hannunta ahankali yadaura
hannun nata kan kirjinshi yana kallon idanunta yace “can you feel yanda zuciyana ke bugawa
sabida yasan kina cikin damuwa?” Gyadamai kai tayi ahankali murya chan kasa yace “I came to
your house tun ranan ban sake samin kwanciyan hankali ba because I know my Pickle is not
fine, I lost sleep, I lost peace, bana iya komi sabida ke, kinason zuciyata tabuga because of you
ne”? Girgizamai kai tayi ahankali tanajin maganganunshi har a bargon kashinta, murya chan
kasa yace “I lost my Mom when I was 25yrs, I know what u are going through Khairy, but if
anything yasameki bazan iya rayuwa ba I will die, I love you alot, Ummulkhair I Love You” wani
sanyi taji ya ziyarci zuciyanta each magana dayake gayamata zuciyanshi datakejin bugunshi
nakara tantance mata cewa gaskiya yake fadi, ahankali yace “when I lost my mum I was
depressed but as time goes on nazo ma fahimci this is not abinda mamana keso, she wants me
happy, tanaso na cigaba da rayuwana, tanaso nai fulfilling dreams dina and above all she wants
me happy and praying for her, Pickle abinda kikeyi yanzu is that abinda Mama kiso”? Girgizamai
kai dasauri tayi alamun aa ahankali yace “to mesa kike hakan”? Lips dinta na rawa kuka na
neman kufce mata tace “because banajin magana and nasa Mama fushi dayawa, halama saisa
taki fadamin she had blood cancer” tafashe da kuka tana kallonshi girgiza mata kai yayi yace
“Mama taki gayamiki she’s ill ne because you are her youngest daughter Khairy u can’t handle
it, and Mama wants wats best for you, that’s is the reason, trust me pickle you are not stubborn,
ke y’a ce dakowani parent will wish to have, I know Mama is so proud of you, ta haifi selfless
and fearless yarinya that can stand for her self a ko’ina, karki kara tunanin Mama is angry with u
iyaye basa iya fushi da yaransu, and Wanan kukan dakike da rashin cin abinci shizaisa Mama
tai fushi dake, cus instead of kinata addu’a kina using time din to cry and not eating zai baki
wani sabon ciwo u want to be sick” girgizamai kai tayi dasauri ahankali yakai hannunshi yakama
dayan hannunta yace “promise me daga yau kin chanza, u will stop all this, take care of yayyinki
and your Dad, do you have any idea yanda sukeji ga rashin Mama gaki” sake girgizamai kai tayi
yace “promise me you will change daga yau, u will always pray for Mama, study well and pass
exam dazaku fara next week, did u promise” gyadamai kai tayi ahankali tace “Uhm I promise”
murmushi yayi he feels kaman yarungumeta yasata ajikinshi and just stay like that forever”
ahankali yace “smile for me i finds it healing is my therapy, smile” dan murmushi kadan tayi ita
kanta tamanta the last time datai murmushi.
To jama’a anan nakawo karshen free pages zan barku da tambayan nan ALIYU NE KO ZAYN
NE???
Dan samin amsoshin nan kucigaba da bina awanan Littafin mai suna ALKAWARIN ZUCIYA!
Dan son cigaba da karanta Wanan littafin zaka iya turo 1k ta 3107021073 aisha Muhammad
first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding
naki a group din danake posting.
Dan girman Allah badan niba kubiya ku shiga group ku karanta. Support me
You can chat me up directly by clicking on this link
wa.me/+2347012181461
Thank you
M Shakur
3️⃣1️⃣
WARAKA TEMPLE
wa.me/+2347042419516
Waraka temple gidan maganin kowacce irin cuta da izinin Allah
Karin niima da dadi
Karin dandanonki da duminki
Matsewarki ki dawo yar Sha shida
Gyaran nono
Sa megida sambatu
Sa kyauta
Maganin Sanyi
Da sauran magungunan damuwar da ke addabar mata zaku samu a waraka temple ku
tuntubemu a no waya ko Instagram.
Murmushi yamata sanan yamika hannunshi yadauki jakanta wayanta yaciro yakunna yace “this
phone should always be on” gyadamai kai tayi ahankali tana kallonshi Ya Aliyu is
just….bamatasan taya zatai describing nashi ba, he’s just everything datake so, he’s so cool,
calm, religious, selfless, caring, loving and above all very handsome. “will you marry me?”
Kaman daga sama taji yajefo mata tambayan dan tayi nisa a tunanin shi while looking at him,
ware manyan idanunta tayi da sun soma washewa, ijiye wayan nata yayi akan cinyanshi
dayagama saita mata dan komi na ciki ya hargitse sanan yadaura mata mayun idanunshi akan
nata, ahankali yace “zaki taimaki Aliyu Hydar ki aureshi yazama mijinki?” Batasan mesaba but
wani kalan bala’in kunya ne taji ya lullubeta dasauri takai hannayenta duka biyun tarufe
fuskanta dashi tana murmushi sosai kaman ba Khairy ba, dan murmushi yayi ganin yanda
tambayan shi yabata kunya, matso da fuskanshi saitin fuskanta data rufe da hannayen ta yayi
kaman mai whispering yace “I want to go and seeaBaba fa” girgizamai kai tayi tareda makemai
kafada batare data bude fuskanta ba hakan yasa yace “what”? Awani irin shagwabe kaman Yar
baby one year tace “ni karkaje wajen Baba yanzu” dasauri yana kallon long yatsun hannunta
masu bala’in kyau da fararen kumbunanta kal kal yace “sai yaushe” ahankali kaman bataso
tafadi maganan tace “sai nagama second semester exam dina nagama school” dan shiru yayi
kaman mai calculating dan yamai nisa, dan yatsine fuska yayi yace “to but will you marry Aliyu”?
Shiru tayi kaman bazatai bashi amsaba yana kallonta sai chan yaga ta gyadamai kai wani irin
murmushi yayi ya dunkule hannu yadaki iska yace “yessssss!” Juyamai baya tayi akunyace
tana daukan jakanta ahankali tace “mutafi inada class by 2” dan murmushi yayi ganin kunyanshi
takeji dan tace zata aureshi, yace “ok” tashi tayi ahankali tafice daga wajen murmushi yasakeyi
ya kwashe dadduman dasauran abubuwa yafito, discarding nasu yayi sanan yazo yasameta
tsaye jikin motan tana kallon wasu tsintsaye dake wasa jikin bishiyan wajen, ga gidajensu birjik
a wajen da alamu kiwonsu ake awajen, abayanta ya tsaya yana kallon tsuntsayen shima murya
chan kasa yace “u like them”? Gyadamai kai tayi da sauri batare data cire idanunta daga kansu
ba, wani mutum dakaman shine mai gadin wajen yakira da hannu ko kadan bamata lura ba dan
hankalinta nakan tsuntsayen datake kallo, kawai gani tayi mutum yafito dawani basket cage na
gidan tsuntsu yazo wajen bishiyan cikin sauki taga yakamo guda biyu yana kokarin sawa ciki,
dasauri tace “Ya Aliyu meyake yi wanchan mutumin”? Ahankali yana tsaye kusada ita yace “I
don’t know let’s see” saka tsuntsayen yayi a basket din sanan yataho dasu gabansu da sauri
yamikama Aliyu yace “officer gashinan macen da namijin ne kaman yanda kace” hannu yasa ya
karba sanan ya ijiye akan motan Khairy tabishi da kallo, hannu yatura a aljihu yaciro wallet kudi
dayawa yaciro yamikama guy din godiya yamai sanan yawuce, hakan yasa yamaida wallet din
aljihunshi kafin ahankali yadauki cage din yajuyo yana kallon Khairy dake kallonshi yamika mata
yace “take” wani cute smile tasaki sanan tasa hannu takarba tana kallonsu tana murmushi
sanan tadago kanta takalli Aliyun dake kallonta tace “they are so cute, they’re so tiny and
adorable” matsowa kusada ita yayi yana kallonsu shima acikin cage din sanan ahankali yace
“mace da namiji ne, this is Aliyu Hydar” yanuna mata namijin, sanan yanuna mata macen da
yatsa yace “and that’s the lady, Miss Ummulkhair” wani kalan murmushi tayi she’s so happy
bata taba zatan dan tace tanaso zai sayamata ba harma guda biyu, fuskanta yakalla yanda take
murmushi tana kallonsu, ahankali yace “are you happy Pickle”? Juyoda fuskanta tayi takalleshi,
gyadamai kai tayi ahankali tace “I am very happy” “mutafi to”? Gyadamai kai tayi da sauri tace
“a ina zan ijiye idan zan shiga class”? kofar motan yabude mata shiga tayi dan shiru yayi kaman
mai tunani sanan yace “I will keep them for you harki gama class, how does that sound”
“perfect” tafadi tana girgiza case din dake jikinta dan suyi attempting flying wani dadi taji tace
“yayyyy they’re flying, Ya Aliyu kalli” kallonsu yayi yana mamakin yanda abin kesata murna,
maida kofan yayi yarufe yanajin wani kalan sanyi aranshi, duk wani damuwa da kunci dayakeji
yatafi ganin yanda take murmushi looking happy.
Shigowa motan yayi yatada yaja motan kusan every minute and second saiya juyo ya kalleta
yanda take wasa da tsuntsayen sosai, yana bala’in son Khairy shi kanshi baisan adadin son
dayake mata ba, ahaka har sukakai school dinta around 15min after 1 na rana, parking yayi
hakan yasa takalleshi daidai shima ya kalleta, dan sunnar dakanta tayi akunyace yace “2 zaku
shiga class ko?” Gyadamai kai tayi, what time zaki gama lectures yau, ahankali tace “5” dan
ajiyan zuciya yasauke yace “yanzu jeki salla a mosque kafin ku shiga class, I will come back
later nakawo miki birds dinki kitafi dasu gida, what do u want me to get for u when coming
back?” Girgizamai kai tayi tace “babu komi” jakanta tadauka sanan tadan saci kallonshi ganin
kallonta yake kaman yauya fara ganinta yasa tajuya da sauri tareda bude kofan tafita tafara
tafiya dan murmushi yayi yakafeta da ido yana kirga step dinta waiting for something, kaman taji
kiran da zuciyanshi kemata juyowa tayi dudda motan is tinted but samin kanta tayi damai
waving hannu dan tasan yana kallonta sanan tajuya da sauri tawuce feeling so happy da shi
can not even deny, bata taba sanin she can feel this happy ba bayan rasuwan Mama gashi
she’s feeling it.”
Kaman yanda yace tayi hakan tayi masallacin su tawuce tai salla abinta sanan tazauna ganin 2
batai ba, jin tunanin Mama yazomata rai yasa tadaga hannu sama tamata addu’a sosai ta shafa
sanan tafito ganin 2 saura, class dinsu tawuce su kansu Amal mamaki sukayi ganin tazo
kujeran dasuke tazauna harma tana karban note dinsu tana dubawa kafin lecturer yashigo wani
kalan dadi duk sukaji, shigowa lecturer yayi yafara musu lectures and Alhamdulillah tana gane
komi. Wuraren 3 suna zaune a ajin taji wayanta na vibrating hannu tasa ajakanta taciro ganin
message ne daga Aliyu Hydar yasa dasauri tabude.
“Are u moody or teary? Concentrate on lectures okay, by the way this birds dinan naki are
naughty, sai kuka sukemin sun tsaneni obviously sunsan I am not their owner”
Bakaramin dariya tayiba dataga text dinshi reply nashi tayi.
“I am happy thanks to Ya Aliyu Hydar, tell my birds not to cry, Mommy takusa gama lectures
bye”
Saida tai sending message din sanan tafarabin messages din dayake turamata tun bayan
rasuwan Mama tana karantawa one after the other tana murmushi, Amal dake kusada ita ta
mintsileta tace “Khairy wai waye Wanan new boyfriend din naki” tai maganan tana leken abinda
take dawaya dasauri tarufe wayan tamaida jaka tareda murguda mata baki ta maida hankalinta
kan lectures din da akeyi.
3️⃣2️⃣
Five daidai suka gama lectures, fitowa tayi suka jero tareda su Amal, kafin su wuce itakuma tai
parking space data hango Aliyu tsaye jikin motanshi wanan karan ba kayan yan sanda ne
ajikinshi ba, Jean da shirt yasaka, wani black jean dawata dark blue shirt dasukamai bala’in
kyau suka haska shi, hannun rigan yakama murdadden muscles nashi sosai, rigan ma kaman
yamai kadan sabida yanda yakama kirjinshi fum fum ya kara bayyano da cikan kirjinshi,
sajenshi ya kwanta yay lub lub hakama gashin fulanin kanshi sai kyalli yake, lips dinshi yayi so
sooo pink kaman ya shafa man baki pink waya nakan kunneshi yana magana, gani tayi kaman
ma kayan yan sandan nan ragemai kyau sukeyi yanda jean da rigan nan suka karbeshi zaka
dauka wani American celebrity ne ko wani hip hop rapper hakanan, gashi da tsayi, ko kadan bai
lurada itaba jidayayi ajikinshi ana kallonshi yasa yajuyo da kanshi, da sauri tadauke kanta
kaman bashi take kallo ba, dan murmushi yayi sanan yacigaba da wayan dayake harta karaso
inda yake, zare wayan yayi daga kunenshi yana kallonta, dan lunshe idanu tayi sabida wani irin
classic kamshi dayakeyi ahankali tabude su, murya chan kasa tace “ina yini” dan murmushi yayi
jin yanda tagaidashi bai amsa ba yabude gaban motan yaciro tsuntsayenta dakuma wani paper
bag da popsicles ke ciki duka yasamata a hannu, kallon paper bag din tayi ganin sunanshi yasa
takalleshi ahankali tace “thank u” murmushi yamata yamaida kofan motan yarufe sanan yace
“direban ki yazo?” Gyadamai kai tayi hakan yasa ya karbe cage din yace “muje nakai miki”
jerawa sukayi gabaki daya duka tsawonta a shoulder shi ta tsaya, har wajen motan yakaita
gaidashi Adamu yayi ya amsa sanan yabude bayan motan ya ijiye case din sanan yakalleta
yanda take tsaye gefenshi yace “get in” shiga tayi ahankali tazauna sanan yamaida kofan
yarufe yamata waving hannunshi, murmushi tayi itama tai waving nashi back sanan Adamu yaja
motan suka wuce, komawa motanshi yayi tashiga ciki yazauna kafin yaja motan shima
hankalinshi ya na bala’in kwantawa.
Gidan Baffa suka wuce, parking Adamu yayi tafito rikeda case nata na tsuntsayen dakuma
jakan popsicles dinta tai side din Mom, da sallama tashiga ganin Mom azaune tana koyama
Zara’u homework yasa tai wajensu tace “Mom nayi tsuntsu” wani ihu Zara’u tayi tana murna
tace “Ya Khairy kibani daya” makemata kafada Khairy tayi tace “zandai aramiki amman bani
baki” ihu tayi cikeda murna Khairy tai murmushi wani kalan dadi Mom taji ganinta haka dayasa
tama manta ta tambayeta waya bata, cikeda farinciki tace “Ya school din?” Ahankali tace “lpy
lau Mom” Popsicles din taciro tabama Zara’u daya tace “ina Batool Zara’u” tana bacci, mikama
Mom daya tayi, Mom tace “waaa rabani da kayan zakin nan naku Khairy” dariya tayi takai
sauran fridge tarike daya tanasha dayan kuma na Batool tai sama Mom tabita da kallo cikeda
mamaki dakuma farin ciki at the same time.
Duka ta dakama Batool dake bacci dasauri tabude ido tana turo baki ganin Khairy ne yasa tama
manta dakomi ta rungume ta turata Khairy tayi tace “dalla gashi” dagudu ta karba suka shiga
sha tare Batool namata hira, saida ta shanye sanan ta tashi tashiga bayi wanka tayi tafito daure
da alwalan magrib salla tayi sanan itada Batool suka tafi dakin Mom. Adakin Mom Baffa yazo yagansu dukansu sun taru suna koyama Zara’u homework, wani kalan
dadi da Baffa yaji zaka dauka kyauta akamai fitowa Mom tayi tasameshi a falon sama wani
kalan rungume Mom yayi ahankali yace “thank you for taking Khairy like your own wife” dan
hararan Baffa tayi kafin ahankali tace “d’a nakowa ne, karka kara godemin Khairy y’ata ce, Ya
Alhaji ya yarda yabika neman Auren kuwa”? Gyadamata kai yayi ahankali yace “amman da
kyar, yanzu dai anyi magana nan da sati daya za’a daura auren, for now zan rike Khairy anan
duk randa taji tanason zuwa gidan su she can go amman dai tana nan koya kika gani”
gyadamai kai tayi tace “hakan yafi, kaga at least nan ga Batool ga Zara’u suna sata surutu,
kaga takoma chan ita kadai ba kanne sai Yayyi kuma fita aiki suke abinsu” Gyadamata kai Baffa
yayi cikeda gamsuwa da maganan ta yace “bari naje na kwanta nagaji” ahankali tace “mu
kwana lpy” kashema ta idanu yayi yace “ashirya min da kyau gobe ina nan” dan dariya tayi
tawuce ciki batare daya tankashi ba tunda yan tsokanan nashi ne suka tashi”.
Har wuraren 11 nadare takasa bacci tuni Batool tai bacci amman ita sai juye juye take tarike
wayanta gam a hannunta babu abinda kemata dadi muryanshi kawai takeso taji ko zuciyanta
zai mata dadi, tana haka wuraren 11:30 wayanta yahau vibrating, har wani dan gajeren ijiyan
zuciya tasauke sanan tadauki wayan takai kunnenta dawata kalan murya da ita kanta batasan
tanadashi ba tace “Ya Aliyu ina yini” wani dan kalan murmushi yayi da saida taji sautin
murmushin tawaya dataji yasa hankalinta yawani kwanta, ahankali yace “how you?” Murya chan
ciki ashagwabe tace “fine” dan shiru yayi sai chan yace “I am sorry nan kirada wuri ba, ina
tareda Abba ne, most time around 11 yake barina, sorry for keeping waiting” gyadamai kai tayi
ahankali tana turo baki. “Kinci abinci”? “Eh” ta amsashi kadan, “me kikaci” ahankali tace “tuwon
shinkafa Mom tayi da miyan taushe” dan murmushi yayi yace “iyye kinci sosai” girgizamai kai
tayi tace “oh’oh banci ba” murya chan kasa yace “why Pickle” ahankali tace “miyan was peprish,
banson yaji yanasa cikina yay ciwo” cikeda kulawa yace “ohh no sorry about that mekika zo
kikaci yanzu” dan murmushi tayi da saida yaji sautin murmushin tace “popsicles dina nakarasa
shanye wa” dan zaro idanu yayi yace “duka kika shanye” dasauri ta girgizakai tace “naba Batool
da Zara’u, nabawa Mom itama taki karba wai batacin zaki” ahankali yace “who is Batool and
Zara’u” anatse tace “yaran Mom ne, Batool ne babba shes 22, itama tana 400level a baze sai
Zara’u tana primary one, sai Ammi itakuma ta haifi su Ya Zayn shine Babba, sai Ya Hafiz, sai
twin Ya Hassan da Hussain” ahankali yace “Uhm Masha Allah” dan shiru yayi hakan yasa
ahankali tace “kaci abinci”? Dan shiru yayi saikuma yay murmushi dan ya bala’in jin dadin
tambayan yace “yes, I just had tea yanzun nan tareda Abba, dazu da yamma naci tuwo awajen
Gwaggo” wani dan murmushi tayi tace “Gwaggo, u have a grandmom”? Yanda tai tambayan he
could feel excitement a voice nata that just tell him batada grandma nata are late.
Ahankali yace “Gwaggo is my grandma ta haifi yara goma amman Abba kadai ya rayu, she’s
Fulani daga adamawa, she’s very old though sai masifa da kaima Abba gulma….” Dan dariya
kadan dayaji tayi yasa yaji wani dadi hakan yasa tacigaba, yace “she’s very old bata iya tafiya
dakanta yakai 10steps haka saida wheelchair nata, but dudda haka garin kaima Abba gulma
ranan taje tafadi yanzu ko 5 step bata iyayi dakanta” wanan karan dariya tayi sosai bata taba
sani Aliyu ya iya nada labari