Showing 96001 words to 99000 words out of 108975 words

Chapter 33 - ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE M SHAKUR .pdf

M Shakur   

14 Nov 2025

1320

suka fito atare, ido da ido sukayi da Aliyu
Zayn yawani irin dauke kai batare daya basu second look ba yawuce, shikuma Manaf yay
murmushi yabama Aliyu hannu suka gaisa cikin mutuci Khairy tarikemai hannu tana mai
shagwaba kan baikawo nata Aisha ba yabisu suka koma falon, Baba na falo zaune da Anty
Mariya da Baffa suna ganin su Aliyu aka shiga gaisawa while mai gadi na shigo da abubuwan
dasuka kawo.

Sunyi hira agidan kaman nothing has ever happened sai wuraren 11 Baba yashiga kwalama
Khairy da Anty Mariya tajata sukaje sama tana hadamata wasu hadaddun kayan mata kan suzo
sutafi dare yayi.
Saida Anty Mariya tagama hadamata sanan tazaunar da ita abakin gado anatse tace “Khairy
nasan niba mahaifiyar ki bace amman yanzu nine ke matsayin mahaifiya a rayuwanki, kinriga
kinyi aure yanzu iya zama da miji da dabarun ki na mata sune zasu zaunar dake, kinga maza all
of them are thesame, Ummulkhairy biyayya shine abu na farko dazaisa ki siye mijinki
completely, kinga Aliyu mijinki yarone mai natsuwa ma gaske, ga kunya gashinan very very
calm kinga maza irinsu dinan dako abokanai basuda shi matayensu sune komi nasu, dole zaki
daura damnaran zama dashi, kinga shiru shirun nan masu sanyi sanyi sunfi kowani namiji
jaraba da yawan bukata, Khairy dole zaki daure ki biyamai kinaganin Aliyu ke kadaice mace
dakuma namijin rayuwanshi, u are his mom his everything kika iya tafiya dashi za’adauka kin
magance shi ne sabida yanda kome kikace shizaiyi, ki rike sirrin mijinki komene ne bayaso ki
kiyayi abin, kinga maza masu suna Aliyu akwai zuciya barin ma wanan nakin dani naga
zuciyanshi da idanuna ranan da yazo ya saceki” dan murmushi kadan Khairy tayi tunawa da
ranan, Anty Mariya tace “kidage da shan magungunan nan naki kinji karkiyi wasu dasu, sanan
karkice kesaikun tare menene menene yakiraki shimfidan shi ki amsa kinajina” Gyadamata kai
tayi jin Baba yasake kwalamata kira yasa Anty Mariya ta tashi tace “muje kinga Babban ki chan
yana kiranki” tai maganan tana bude kofan suka fice, falo suka sauka babu kowa a falon hakan
yasa sukai waje, dukansu na tsakar gida harda Zayn dataga Baba namai magana tareda Aliyun
dabata san na meye ba, ganinta yasa Baba yajuyo ya kalleta yace “tahonan ku tafi Khairy dare
yayi” gyadama Baba kai tayi takaraso tanaso ta gaida Ya Zayn but sanin halin mijinta yasa ko
inda yake bata kalla ba agaban kowa Aliyu yakama hannunta sanan yakalli su Baba da Baffa
yace “goodnight Baba saida safen ku” saida safe duk suka musu sanan Baffa yace “muje kaga
Zayn, saida safe Amini” suma suka wuce motansu Zayn yaRshiga mazaunin direba yajasu suka
fice daga gidan.

7️⃣2️⃣

Suna kaiwa gida bude musu gate akayi suka shiga ciki parking yayi wajen parking sanan
yakashe motan batare daya budeba yakalleta kaman yanda tajuyo takalleshi yace “leki ijiye
kayayyakin nan kima Gwaggo sallama kizo wajena ki kwana” makemai kafada tayi ahankali
tace “ni kunya nakeji” dan murmushi yayi yace “ashe ko ni zan biyoki let’s go” murmushi tayi
suka bude mota suka fito, tai hanyar flat din Gwaggo dagudu Aliyu ya tsaya yasaki baki yana
kallonta saikuma yadan saki murmushi kafin yamaida kofan motan yarufe yawuce side din
Mami, sallama yayi yashiga falon, daga Dad sai Mami ne afalon tana zaune kusada Dad
shikuma Dad yana some paper work ganinshi yasa yature kome yakeyi ya kalli Aliyun, dan
murmushi Aliyu yayi yace “Dad ina yini, Mami ina yini” yagaidata batare dayama kalletaba
murmushi tayi ta amsa tace “ai mun zaci dagachan ka gudu da amaryan kane wanan dahar
shadaya baku dawoba” Dad da tunda yashigo yake kallonshi babu wanda yakaishi
understanding Aliyu a duniya yace “Yaya akayi Gadanga?” Kallon Dad Aliyu yayi yanaso yamai
maganan yana jin nauyi kuma yama kasa Dad Ya tsareshi da idanu yace “talk what is it”?
Ahankali yadan saukan da kanshi kasa murya chan kasa yace “Dad bazamu iya maida tarewan
this week ba dole sai in 3weeks time” dan murmushi Dad yayi na manya ba Aliyun dayake cewa
ya tsaneta bane wanan ba hmmm lallai yaran zamani tunda harshi dakanshi yay magana haka
gwara ya maida tarewan this week kafin ayi abin kunya agidan nan, maida kanshi yayi kan
rubuce rubucen dayake yace “okay Allah yakaimu wanan satin zaku tare zan waya da Babanta
tashi kaje” dasauri yatashi yanajin wani dadi da kunya at the same time haryakai kofa zai bude
Dad yace “one more thing Aliyu” dasauri yajuyo kanshi akasa, ahankali Dad yace “you are not
allowed ka shiga side din Gwaggo dagayau, dagayau karka kara ganin Ummulkhairy sai
ankaimaka ita gidanka, inhar kabi kan dokan nan dana shimfida maka to baza’a tare wanan
satin ba kanajina” gyadamai kai Aliyu yayi ahankali dudda baiso hakan ba amman he’s willing
yay hakan yau Saura kwana hudu asabar din, wucewa tayi yafita dasauri Mami tace “yaza’ayi
ka yarda Alhaji bayan kasan ba’a gama shirye shirye ba” anatse Dad yace “akwati ne kawai
baki gama hadawa ba kuma kece kebata lokaci, gobe duk wani kaya da ake bukata na akwatin
nan ni dakaina zansa akawo, wata na hudu kenan ake da bikin nan basu tare ba, tunda shi
harya cire kunya yace yanaso atare abarshi yatare Aliyu ba yaro bane ina fata kin fahimta”
gyadamai kai Mami tayi ahankali tadade tanama kanwarta Hajo kwadayin Aliyu sabida yanda
mijinta keson Aliyu, babu wanda yasan assets nashi dakomi nashi passwords pins nakomi
nashi sai Aliyu, ga Aliyun banda company da gidaje da mahaifinshi yabashi shi kanshi Aliyun
nada businesses da dama dake yielding mai bala’in money, wani kalan bakinciki taji aranta
dayasa ta tashi kawai tama wuce sama.

Saida sukakai gida zai bude kofa yafice Baffa yarike hannunshi hakan yasa dasauri yakalli
Baffa, murmushi Baffa yamai yace “sit Zayn” komawa ahankali Zayn yayi yazauna yana
murmushi, ahankali Baffa yace “abokinka Mamu yabani labarin Aisha da kai achan kasan wajen
dakukai karatu Zayn” Baffa yakirashi ahankali yace “Naam Abba” ahankali Baffa yace “kagadai
bani na zabamaka Aisha bako amman duk wanda yayi abu domin iyayenshi baya tabewa, hakki
nane nai guiding naku and put all my children a right tract, naga amincin dayake tsakanin
mahaifiyarka da mahaifiyar Aisha, duka duka bikinku saura sati daya Zayn, inhar kai imani da
kaddara sanan kama iyayenka biyayya trust me reward dinka is with Allah, Son ka manta da

Ummulkhairy Khairy aranka, Allah yariga yakaddara cewa ita Matan Aliyu ne, yaron nan abin
tausayi ne shima Zayn baida mahaifiya kaman Khairy gakuma mugun ciwon zuciya, kakosan
yanzu haka akwai yan abubuwa na likitanci dake supporting heart dinshi acikin zuciyanshi”
kallon Baffa Zayn yayi shiru, gyadamai kai Baffa yayi yace “yes Zayn, nasan ka nasan koda
bakasan Aliyu ba ayanda yake neman mutuwa kan Khairy zaka iya barinmai kai musulmi ne
kuma zaka iya soma dan uwanka abinda kake soma kanka, Zayn I love you kaine d’ana nafari I
don’t want you to waste your life, Zayn kaso Aisha for me, for ni mahaifinka, for mahaifiyarka, for
sake na ita Aishan dake sonka Allah will reward you for that kaji yaro na” ahankali ya gyadama
Baffa kai yanajin duk wani nauyi da zuciyanshi yamai natafiya, hannu Baffa yakai yakama
kuncinshi sanan ahankali ya matso ya manna mai peck akumatu da goshi ahankali yace “Allah
yamaka albarka Zayn” ahankali yace “Ameen Abba” murya chan kasa Baffa yace “start planning
your wedding kome kakeso tell me kaji” gyadamai kai yayi ahankali sanan Baffa yawuce yafita
daga motan zuwa flat dinshi.

Ijiyan zuciya Zayn yasauke he hates Aisha sosai but for the first time yau kalaman Abba yasa
yaji he’s ready to give her a second chance, kowa arayuwan nan deserves second chance, idan
yana cewa yar iskace ita shima ai hakan ne, Yar iska da dan iska kowa deserves a chance inhar
yayi tuba na gaskiya, tunda aka samusu rana kusan kullum Aisha kuka take tana rokonshi ya
yafemata, kullum test messages ta rantse takara rantsewa cewa sex din dasukai da Kb sau
dayane kuma shima was a mistake ranan sunyi drunk yasa tasha shisha, sex din datayi kuma
dashi was all out of love tadauka ayanayinshi that’s the only thing dazaisa ya sota he’s really to
let go off everything yama iyayenshi anything, babu amfanin d’a dabazai iya sacrificing
happiness nashi for iyayenshi ba, he was a bad boy before but sanadin Khairy kasheta da aka
kusayi yasa ya shiru idanunshi suka bude yaga gaskiya, ya tsani shisha, kwadayin mace wanan
da kyar yakema bacci saisa kullum yake azumi yana istigifari bazai kara zinaba shida mace sai
halaliyanshi, ijiyan zuciya ya fuzar sanan ahankali yasa hannunshi yaciro wayanshi daga aljihu
number Aisha yaciro ahankali yashiga yimata text.
“Aysha I’ve accepted you, but I need to ask for your forgiveness, nasaki kuka, bakin ciki, i
judged you call you all sort of names bayan ni I am even far far worst than u are, ance iskanci
awajen namiji ado ne but is all a lie, wutan jahannama guda ce for mace da namiji, kiyafeni let’s
ask Allah for forgiveness, build a new life and forget our past, this is to new beginning, I can’t
wait to make you mine Ayshatu”
Turamata text din yayi tareda sakin murmushi dan yasan she will be delighted taga messege
dinan sanan ahankali yabude mota yafito yana kulle motan yawuce ciki.

“Iskanci bin mata, shaye shaye bashine farin ciki da wayewan rayuwa ba, shidama ance sabon
Allah nada dadi, Allah nada so many ways na kama mutane, I hope all of us mun gyara kanmu
ta hanyar daina sabon Allah damukeyi azahirance dakuma aboye, Allah ya shiryemu gabaki
daya, Allah ya yafemana kura kurRanmu Ameen”.

7️⃣3️⃣

Gagarumin biki ake shiryawa agidaje uku, gidansu Aliyu gidansu Baffa da gidan su Aysha.

Baba yama Khairy lafiyayyen kayan daki da aka kai babban gidan Aliyu an jeramata komi,
akwatinan da Aliyu dakuma Dad da Gwaggo sukama Khairy kusan 40 dan set daban daban
designers, fir daga Dad har Gwaggo sun hanashi ganin Khairy da akema lafiyayyen gyara sai
yanzu Khairy takeji aure take tasa Batool tamata inviting all her friends ranan Friday da
Saturday ne za’ayi biki asabar da night akaita gyara akema Amarya na ban mamaki.

Ranan Friday wajen kamu aka bari Aliyu yaganta bayan yabiya kudi dayaga Khairy saida yadan
kusan zarewa akahau nai dariya Dan rudewa yayi su Meena sai dariya suke dan tunda Aliyu
yakirata yanunamai shiya yafema Khairy komi yawuce between them kuma yanaso tabata
hakuri sudawo kaman sisters taje tabama Khairy hakuri da ita da Batool sune manyan kawayen
amarya akai shagali har dare ko kadan ba’a bari Aliyu yakebe da Khairy ba Aiko yacika yay fam
yace zata ganene sai dariya take.

Yau babban ranane wajen both Aliyu da Khairy wato babu abinda yakai soyayya dadi sunma
kosa dare yayi tabar gidan nan ta tafi gidanta wajen Aliyun ta dan tayi kewan shi sosai kwana
nawa bata ganshi ba.

Karfe 8 nadare aka tafi da Ummulkhairy gidan mijinta gidan Aliyu Hydar.
Karfe 8 nadare aka kai Ayshu gidan mijinta Zayn.

VIP kunason amarcin this two angwaye konasu KhairRy kadai???

7️⃣4️⃣

Dagaske Aliyu one single friend bayida shi saidai yaran aiki, hakan yasa Dad yadaukeshi amota
sai uban kunya yakeji har zuwa Babban gidanshi, cikin gidan Dad yashiga gidan yahadu bana
wasaba kaman wani gidan gwamna, kallonshi Dad yayi yace “Oya get down and go kasayi baki

kasan yanda zakayi da kawayen amarya sutafi nidai saida safe” awani irin kunyace yace
“Daddd plssss” hararanshi Dad yayi yana murmushi yace “don’t Dady me, Allah baku zaman lpy
gud night son” ahankali yabude motan yasauka yabude baya ya kwashi manya manyan ledojin
dasuke nan aciki sanan yamaida kofan yarufe Dad yaja mota abinshi yawuce yay tafiyan shi.

Okay Gidan yabida kallo sanan ahankali yafara tafiya zuwa gaban flat din ahankali yabude
kofan ya shiga gidan wani haddaden kamshi yake banawasa ba, furnitures na ciki zaka dauka
villa kaje, ganin babu kowa a falo yasan suna sama yasa yawuce wani hadadden daki dakenan
kasa yabude kofan yashiga dakin shima yahadu yasha furnitures ga kanshi da dakin keyi ijiye
komi yayi awajen sanan ya kwanta kan gado wayanshi yaciro yay dialing number ta amman
harya gama ringing bata dauka ba hakan yasa yamata text.

“Suwaye tareda ke”?
Ko 1min text din baidauka ba tamai reply.
“Gwaggo, da Meena, da Batool da Amal, Ya Aliyu wai kwana zasuyi please kazo na ganka yau
kwana nawa I didn’t see you”
Wani kalan murmushi yayi yana tunanin yanda zaiyi dawanan jarababbiyan kakan nashi, tashi
kawai yayi yawuce sama Gwaggo yagani zaune falon sama dawani katon ghana masgo guda
daya tana lissafin wani daki zata dauka adakunan dake saman tana ganin Aliyu tace “yauwa
Gadanga zo bani dakina da kanka kagani naje najera wayan nan kayan a sip, gobe direba zai
karasa kwasomin kayayyakina na jera adakin nawa” wani kallo Aliyu yamata daidai Meena tafito
daga dakin da Khairy keciki ganin Ya Aliyu da Gwaggo yasa ta gimtse dariyan datakeji tazo
wajen da sauri tace “Ya Aliyu Gwaggo tahada kayanta tass wai gidanka zata dawo dazama
bazata iya rabuwa dakai ko Khairy ba” wani kallo Aliyu yama Gwaggo da itama kallonshi yake
yace “wlh bazaki zaunamin agida ba ki koma chan gidan danki kicigaba da zama” nuna kanta
Gwaggo tayi tace “ni zakama rashin mutunci” hararanta yayi yace “eh” cikeda masifa ta tafa
hannu tace “yo idan ka isa Aliyu zoka korani daga gidan nan” wuceta yayi yay dakin dayasan
Khairy keciki yabude dakin, Khairy na zaune kan gado an rufemata kai da lafaya ga Batool da
Amal duk akan gado suna mata hira, ganin Aliyu yasa duk suka gaidashi, dan murmushi yayi
yasa hannu a aljihu yaciro bandir na yan dubu guda biyar ya ijiyemusu akan gado yace “ka
kudin siyan baki ina zuwa bari na ari Mrs Aliyu” yay maganan yana kama hannunta dayasha
lafiyayyen lalle, ahankali tabiyoshi ta sauka kanta alullube yawuce suka fito daga dakin ganin
yafito da Khairy yasa Gwaggo ta mike tsaye tace “ina zaka kaita kasayi kudin bakin bakin ne”
ganin acike Gwaggo take dashi yasa ahankali yace “magana zamuyi da ita afalo Gwaggo, kuma
ai nasaya ko Meena” dasauri Meena ta gyadama Gwaggo kai tace “ga kudin chan adakin”
dasauri Gwaggo tace “muje ingani” tai hanyar dakin, dawani irin sauri Aliyu yaja hannunta suka
sauka kasa zuwa dakin maida kofan yayi yarufe yasaka key yakai hannunshi ahankali Ya yaye
gyalenta murya chan kasa yace “Assalamu Alaykum” wani irin murmushi Ummulkhairy tayi tai
wani tsalle ta rungumeshi, wani irin fito da ita daga jikinshi yayi kawai Ya dauketa sama yana
murmushi sosai yace “I miss this girl, me kikamin ne”? Sauketa yayi dawani irin sauri tazauna
kan jikinshi tana kallon fuskanshi yanda yamata kyau ahankali tadaura hannunta kan kirjinta

dayan hannunta kan kirjinshi tace “wani sirri ne da only this 2 zasu iya ganewa” hannunta
yakama ahankali yamma hannun kiss yana kallonta kaman baitaba ganinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login