Showing 66001 words to 69000 words out of 108975 words
she cried yanajin muryanta yasani, shiru
yayi yana sauraron kukan ta kaman yashiga wayan yazo inda take yakeji, almost good 2min
yabarta tai kuka yanda takeso sanan ahankali cikeda iya lallashi yace “I always tell you I am
here for you, why will you be crying haaa? Oya yishiru kinji” gyadamai kai tayi tana kokarin
Hana kanta kukan, murya chan kasa ahankali yace “maiya sameki why are you crying”? Jitayi
wani kukan yazomata tasake saki, cikeda damuwa sosai Aliyu yace “Pickle wai kasheni kikeso
kiyi? U want my life eh? Kinsan yanda kukan ki ketabamin zuciya kuwa? Did you have any idea
wlh idan kikaji ance I slump and die kece” rage sautin kukan tayi ahankali dan tasan ko karya
daya baiyiba, cikeda lallashi yace “tell me menene, nazo gidanku naganki” dasauri ta girgizamai
kai dan tasan wlh zai iya tace “a’a” ahankali yace “to what’s the matter”? Batasan yaya ma
akayiba jitayi tace “cikina ke ciwo” tasake taushe bakinta jin takasa fadamai gaskiya for the first
time yau tama Aliyu karya, shiru yadanyi sanan ahankali yace “sorry, is it MP? All this menstrual
cramps shi?” Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” murya chan kasa yace “sorry, sannu, stop
crying, kinsha magani kona siyo nakawo miki” ahankali tace “nasha” murya chan kasa yace
“then it will stop soon, hey you this MP cramps I command you to leave my Pickle alone or I
arrest you, nayi arresting nashi”? gyadamai kai tayi tana dan murmushi tace “eh” murmushi yayi
jin tadanmai murmushi yace “okay MP u are under arrest for disturbing the peace and harmony
na Miss Khairy, for taking away her smile and bringing her kukan banza back” dan dariya tayi,
hakan yasa yace “yes koba kukan banza bane kikemin ba, idan kika ganni saiki kara wani
narkewa kina kuka just to worry my heart Khairy angayamiki ban sani bane” at this point wlh
tama manta itane mai kuka dariya tafara sosai, ganin haka yasa yace “haka ranan nazo asibiti u
were very fine fa hira ma kike, kina ganina kika kokkobe fuska ashagwabe zaki faramin kuka
sabida kawai ki rudani this girl keko don’t worry eventually zan saki kukan mai dalili” dariya tayi
dan ita bamata gane last maganan ba, ahankali yace “kinci abinci”? Gyadamai kai tayi tace “but
small baran iyaci dayawa ba” murya chan kasa yace “tom anjima idan yalafa sai ki karaci ko”
tom, murya chan kasa yace “if it persist tell Batool tasa towel a warm water tamiki massaging
abdomen it will stop” gyadamai kai tayi ahankali tace “tom” ahankali yace “gobe zaki school”
girgizamai kai tayi tace “no sainaji sauki” Gyadamata kai yayi yace “okay, bari na barki kihuta
idan pain din yadawo call me but don’t cry for me again” murmushi tayi tace “saina maka bye”
dan dariya yayi ahankali yace “I love you Ummukhairi” katse wayan yayi dip, ahankali tajanye
wayan daga kunnenta takasa koda kwakkwaraZn motsi.
5️⃣0️⃣
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️
Ranan ma bacci barawo yasace ta da kyar ta tashi dasafe tai salla, tana zaune da safe ita kadai
akasa taji an bude kofanta hakan yasa takalli kofan Baba ne, shigowa dakin yayi hakan yasa
ahankali tace “Baba ina kwana” zama yayi akasa kusada ita shima ahankali yana kallonta yace
“yauma bazaki school ba” gyadamai kai tayi ahankali tace “bama komi sai ranan exam zanje”
shiru yayi yana kallonta hakan yasa ta saukarda kanta kasa, ahankali yakai hannunshi yatallabo
fuskanta yana kallon kwayan idanunta yace “have you been crying Ummulkhairy”? Dan
murmushi takakalo sanan ta girgiza mai kai, baki Baba yabude zaiyi magana dasauri ta girgiza
mai kai tana hadiye miyau sanan tasa hannunta ta goge hawayen daya zubomata da sauri
sanan takalli Baba murya chan kasa tace “Baba nariga na karanta Littafin Mama na karanta
komi naciki” shiru tadanyi sanan tasauke ijiyan zuciya ahankali, murya chan kasa tace “Baba
babu abinda bazan iyama mahaifiyata aduniyan nan ba she’s my number one dan haka karkaji
komi” tasakeyin shiru tana saukar da ijiyan zuciya ahankali tace “I accept Ya Zayn amatsayin
mijina wanda kuka auramin Baba” tai maganan tana danne hawayen ta, wani irin farin ciki
dataga ya lullube fuskan Baba yasa tasakinmai murmushi ahankali, rungume ta yayi yana mata
addu’a sanan yacirota yace “kome kikeso nasaya miki Ummulkhair kifadamin ko yaushe I will
buy it for you, I know Maman ki is very very happy dake, Allah miki albarka, bari naje nafadima
Anty ki dan ta shirya tafiya Dubai yomiki shopping zaki bita kutafi tare” girgixamai kai tayi tace
“zanyi karatu for final exam Baba” “ohhh hakane nama manta tsabagen farin ciki bari naje”
Baba yay maganan yana fita daga dakin cikeda farinciki datama dade bata ganshi da irinshi ba
tun Mama nada rai, hannu tasa tashare fuskanta ahankali tace “Ya Aliyu I am sorry” ko kadan
batasan tayaya zata fadima Ya Aliyu ba ita batamajin zata iya fadamai ba bama tasan tayaya
zatai avoiding nashi ba tana zaune tana tunanin Batool tashigo dakin ganin idanunta sunyi jajir
yasa Batool tamaida kofan tarufe tazo inda take zaune akasa tazauna tace “Khairy zakije
kisawa kanki wani ciwo ne wai, kin fadama Ya Aliyu”? Girgizamata kai tayi cikin muryan kuka
tace “Batool I don’t know Tayaya zan fadamai, I can’t hurt Ya Aliyu, I can’t hurt him, I don’t even
want to imagine what he will go through Idan yaji wanan zancen, banson wani abu yasameshi”
ta karashe maganan tana goge kwalla duk Batool na kallonta tace “to tayaya zakiyi avoiding
nashi yanzu I am sure sabida shine kika kasa zuwa school, Khairy you need to think of
something” hawaye tadan share sanan takalli Batool tace “na chanza SIM card”? Dasauri
Batool tace “ko kin chanza SIM card ai yasan gidan nan, saidai” tai shiru dasauri Khairy ta
kalleta tace “saidai me”? Ahankali Batool tace “call him up kifadamai zakuyi tafiya kauyen su
Mama garin kuma babu service gobe zaku tafi ba lallai idan yakira yasameki ba saiki kashe
wayanki kawai, karki kara zuwa school din saikun fara exam baduk idan kina exam baya zuwa
school wajen kiba” gyadamata kai Khairy tayi tace “to kingani dazaran an gama exam din karki
kara fita kawai nasan idan aka kaiki gidan Zayn zai chanza miki layin waya shikenan, idan bai
ganki ba daga baya yaji kinyi aure zai hakura” shiru Khairy tayi tana kallon Batool Wanan shine
simplest thing datasan zata iya dan she can never ever hurt Ya Aliyu, hannu Batool tasa akan
fuskanta ta sharemata hawayen tace “kirashi yanzu” ahankali tadauki wayanta tai dialing
number Aliyu, saida wayan ya katse sanan yakirata back, ahankali yace “good morning Miss
Khairy yaya jikin I was about calling you Boss dina yarikeni a office annoying man kawai, cikin
yadena ciwo”? Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” sanan tai shiru dukan cinyanta Batool tayi
hakan yasa dasauri tace “Ya Aliyu zamuyi tafiya yau” dan shiru yadanyi kafin ahankali yace “ina
zakuje”? “Kauyen su Mama zamu” ahankali yace “ina ne kauyen”? Dan shiru tayi tana kallon
Batool data Balla mata harara dan tana jin maganan Aliyun daga inda take, ahankali tace
“uhmmm namanta sunan kauyen, nataba zuwa sau daya da ita secondary school” ahankali
yace “ok yaushe zaku dawo”? Murya chan kasa tace “sai Baba yafada I don’t know” hararanta
Batool tayi hakan yasa tace “Ya Aliyu kauyen babu network” danjim yayi kafin ahankali yace
“Tayaya zan dingajin muryan ki to” hawaye taji yazo mata ahankali tace “nima bansani ba” jin
yanda muryanta yayi zatamai kuka yasa yace “to shine zakiyi kuka? Ki tambayi Baba sunan
kauyen saiki fadamin kafin kutafi duk randa naji nagaji da rashin jin muryanki I will just enter
road and come cus I can’t survive this life banganki ba kuma banji muryanki ba, so don’t cry
okay” ita kanta jikin Batool wani sanyi taji yayi ko itane she can’t hurt a guy kaman Aliyu haka
with pure heart gashinan so cool and calm. Ahankali Khairy tace “okay” murmushi yadan mata
yace “mai kukan banza, lemme get back to office kafin boss dina yay firing nawa in the middle
of minute nadauki excuse nafito, bye I love you Miss Khairy” ya katse wayan da alamu sauri
yake ajiye wayan zatayi taga kiranshi yashigo ahankali tadauka gudu taji yanayi yace “I forgot to
tell you Allah kiyaye hanya, kidauki mosquito cream, insecticide and mosquitoe net kauye akwai
sauro I don’t want them biting you, and go with indomie da some cereal incase bazaki iyacin
abincin kauye ba, and again go with some bottle water karkisha ruwan rafi kinji, take care of
yourself for me kinji Ummulkhair” gyadamaikai tayi ahankali tace “naji Ya Aliyu thank you” dan
murmushi taji yayi sai chan taji ya tsaya dagudun yace “shitt! Pickle my heart kinda feel sad, I
guess I am missing you already, zanyi missing Khairy na very very so so sooo much” murmushi
tayi tace “me too” sanan tace “Ya Aliyu ka koma meeting bye bye” takatse wayan dasauri sanan
tafada jikin Batool tace “Batool na shiga uku ina cikin tsaka mai wuya yaya zanyi da
ALKAWARIN ZUCIYA NA?” Bubbuga bayanta Batool tayi tace “kaddaranki kenan kiyakuri
Khairy” da kyar ta lallashi Khairy, sanan tadauki wayan Khairy tacire SIM card dinta tawuce bayi
amasai ta Kefa SIM card din tai flushing dan that’s the only thing dazata iyama Khairy dan
yasan yanda so yake lokacin dazata kunna wayan nan takira Aliyu bazata sani ba and she
needs to let him go dan tanada mijinta, dawowa dakin tayi kawai ta rungume Khairy suna kuka
sosai.
Wasa wasa 2weeks kenan bataji muryan Aliyu ba, gidansu sai gyare gyare ake na bikin da
za’ayi nata dana yayyinta, Anty Mariya was just like a mother to Khairy dan mai gyara ta dauko
daga Sudan aka bata daki daya tana gyara Khairy in and out, Khairy tarame tun tana kuka da
hawaye yanzu tasoma mara hawaye kawai gatanan ne, yau zasu fara exam duka duka 1 week
zasuyi sugama, shiryawa tayi cikin hijabi har kasa da nikabi duk wani abu datasan Aliyu zai iya
ganinta yaganeta dashi ta chanza sanan tafito tama Anty Mariya sallama, amotan da Baba
yasiyawa Anty Mariya da direbanta tadauka suka tafi bayan ta sanar da mai gadi idan wani
namiji yazo nemanta ace batanan, har gaban department dinsu tasa direban Anty Mariya yayi
parking sanan tawuce tashiga exam hall wanda yake zasuyi 2hrs aciki tana gama paper ta
bama tajira kawayenta ba tafito tana tafiya ahankali kamshin Aliyu taji kaman daga sama
amman tadaure taki dago kanta saima sauri data kara zuwa motan, baya taje zama amman
saitaje gaba tabude ta zauna suka wuce saida suka sanyi nisa sanan tajuyo Aliyu ta hango
tsaye yana sanye da kananun kaya yana kallon exam hall din tasan ya tsaya ne yana jira afara
fitowa kozai ganta jitayi kuka yazo mata nikabin takama afuskanta tana kuka sosai.
Wasa wasa yau Friday yau tagama last paper ta yauma still saida taga Aliyu a school dinsu
yarame sosai yay duhu yau kukan datayi yafi na kullum dan tasan yaune last day dazata ganshi
dagayau bazata kara fita ba ahaka suka tafi.
Parking sukayi a compund dinsu da ake fentin tsakar gidan, ahankali ta sauko nikabin kanta
tacire sanan tawuce flat dinsu, ahankali tabude kofa tashiga Zayn tagani zaune afalon su taci
gayu yay wani irin bala’in kyau tana magana da Anty Mariya ganinta yasa yadago kai ya kalleta
dawani irin sauri ta sauke kanta kasa ahankali tace “ina yini” sanan tawuce dasauri tai stairs.
“Ummulkhairy” yakira sunanta ahankali chak ta tsaya batare data juyoba, tashi Anty Mariya tayi
tace “bari kaga naje na dudduba aikin da akeyi Zayn” tai maganan tawuce ta gefen Khairy tai
sama abinta, ahankali Zayn yace “Khairy” juyowa tayi ahankali kanta nakasa sanan ahankali ta
taho yana binta dawani irin kallo ganin yanda takara kyau fatarta harwani sheki take, zama tayi
akan kujera kanta akasa, dan murmushi Zayn yayi sanan yadauki wani Leda da flowers red
keciki dake gefenshi sanan yataso yazo har gabanta tsugunnawa yayi agabanta sanan ahankali
yadaura hannunshi kan nata wani irin rawa jikinta yafara dasauri takalleshi wani cute smile
yasakin mata sanan ahankali yakama hannun nata yana kallon fuskanta yasamata flowers don
aciki yace “congratulations u are now a graduate wife” wani sarawa taji kanta yayi dawani irin
sauri ta lumshe idanunta sanan tabudesu ahankali takalli flowers din Aliyu kawai taji yafado
aranta, sharrrr hawaye yazubo daga idanunta dasauri Zayn yace “why are you crying”
hannunshi yakai kan fuskanta zai sharemata dasauri ta kauda fuskanta tace “kaina keciwo I
want to sleep thank you” sanan tabi ta gefenshi ta tashi dasauri zata wuce karaf taji yakamo
hannunta, dawani irin sauri tajuyo takalleshi tashi yayi ahankali yana kallonta sanan yazo ta
gabanta Ya tsaya yay folding hannunshi akirji ahankali yace “I love you Ummulkhair! And I
wanna spend the rest of my life with you! I accept you as my wife cus ina bala’in sonki! Allah
yajikan Mama data bani ke, and I will forever be greatful to her data zabeni a matsayin soulmate
na yarta, Ummulkhairy Zayn love you alot” wani irin fizge hannunta tayi dawani irin gudu tai
stairs zuwa dakinta maida kofa tayi tarufe tasa kwado sanan tawani cillar da flowers nashi gefe
jikinta na kyarma sabida kalamanshi Aliyu kawai suka dinga tunamata fadawa gado tayi tana
kuka ahaka bacci yay awon gaba da ita.
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️
5️⃣1️⃣
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️
Yau tun safe yama kasa tashi yakai kanshi bayi yay alwala yay salla sabida mugun zazzabin
dayake, Abba dabaiganshi a masallaci ba daman jiya Gwaggo tacemai baida lpy amman da
Aliyun yazo wajen ya tambayeshi yacemai lafiyanshi kalau yasa yana shigowa gidan daga
masallaci straight side din Aliyun yayi ahankali yabude kofan dakinshi yashiga dakin tsaf babu
kowa a falo bwdroom nashi yayi yana budewa kakarin aman Aliyu yaji abayi, Aliyu tun yana
yaro ciwon shi always comes da amai dawani irin sauri yashiga bayin ganinshi a duke yasa Dad
yace “Subhanallahi Aliyu” ruwa yatare Awani bowl yakawo mai da kyar ta kuskure bakinshi
sanan Dad ya wankemai fuska sanan yadaukeshi yafito dashi yanajin yanda jikinshi yay zafi,
bargo yasa ya lullube shi sanan yajuya zai fita dawani irin sauri Aliyu yakama hannun Dad
ahankali yace “Dady” dasauri Dad yazo gaban gadon zama yayi yace “Aliyu menene” ahankali
yace “Dad last 3weeks dasuka wuce Ummulkhair called me cewa zasu village, and a village
nasu basuda network, Dad I’ve been going to school masu all through last week sabida zasuyi
final exam amman batazo ba, Dad I am so worried did something happen to Khairy?” Shiru Dad
yayi yana kallon Aliyu duk cikin yaranshi babu wanda yadauko zuciya da hali irin nashi kaman
Aliyu, Aliyu bai iyason abu ba, bai kuma iya kin abuba, Aliyu loves da zuciya daya, and he loves
completely without rage space, Aliyu is very cool, baida hayaniya da rigima amman akwai
zuciya na masifa. Ahankali Dad yace “sabida bakaga Khairy bane yasa kake neman kashe
kanka Aliyu? When was the last time kaci abinci” murya araunane yace “I can’t remember Dad”
shiru Baban shi yayi yana kallonshi sanan anatse yace “yanzun nan zan taho maka da magani
da abinci write down address na gidan su Ummulkhairy for me zanje gidansu, I will go and
check her up for you daganan zan nema maka aurenta wajen mahaifinta kafin kaje ka kashe
kanka sabida soyayya” Dad yay maganan cikeda tausayinshi dakuma jin haushin shi duka atare
sanan ya tashi yafice, yana fita daga dakin sukaci karo da Gwaggo datasa Meena ta turata
akeke ganin danta yasa tace “haba nakasa bacci lafiya tun tsakar dare Nike damun ja’irar nan
takawoni naduba takadirin yaron nan dan jikina yabani baida lafiya amman taki wai nabarta tai
bacci yanzu ma saida nahada mata da kuka tafito dani, wlh Abdul bakai dacen yara ba ko
kadan, shikuma ina yake yana cikin ne”? Ganin yanda Maman shi tadamu dan shi kanshi
baisan iyakacin irin son da tsohuwar nan kema Aliyu ba yace “muje Gwaggo baida lpy amman
yanzu zan bashi magani yayi bacci” kirji Gwaggo tafara tace “hala yanata amai dan cutan Aliyu
kenan duk ciwo yay ta uban amai na shiga uku, meke damu shi eh gayamin” shiru Dad yayi
ganin yanda tadamu ihu tamai tace “nace kagayamin Abdul” kallon Meena yayi yace “wuce
kitafi” wucewa ahankali tayi ta tafi tsugunnawa Dad yayi yace “Gwaggo sabida yarinyar nan
dayakeso yake rashin lafiya wai tunda tai tafiya zuwa kauye bai kara samunta awaya ba ko
ganinta” fashewa da kuka Gwaggo tayi tace “to laifin wa inba nakaba, tuntuni nike damunka
muje mu newama yaron nan Ummulkhairy amman kaki wai abari tagama makaranta yanzu idan
wani aka bamawa fa iyye, kaini daki na shirya yau kafata kafanka gidan su Khairiya zamu
billahillazi kuwa” kaita dakinta yayi sanan yawuce yahado magani yabawa Aliyu da shayi
dakanshi sanan yamai allura kafin mene bacci yakamashi fitowa yayi yakoma nashi dakin
shiryawa yayi cikin manyan kaya yana fitowa tsakar gida yaga Gwaggo itama ta shirya cikin
lafiyayen atampan ta jajir dashi da aka mata dinkin bubu kan kekenta tai kyau sosai fesfes da
ita duk wanda yaganta yaga Yar fulani. Girgizakai kawai Dad yayi cikeda takaici yawuce dakin
Aliyu Yar takardan daya rubutamai address yakalla