Showing 60001 words to 63000 words out of 108975 words
kafa ahankali
yashigo dakin batare dayakai wajen gadon ba yay folding hannunshi akirji yana kallon kwayan
idanunta da ita kadai zata iya fassara maganganun dake cikinsu asanyaye yace “lay ur back”
gyadamai kai tayi kaman Yar baby shi, sanan takoma ahankali ta kwanta back, murya chan
kasa yace “Ya jiki”? Ahankali kaman ba itane kemagana da dan kyau ba dazun nan tawani
narke kaman wacce ke shirin fashewa da kuka yace “fine” kasa daurewa yayi zuciyanshi namai
zafi da ciwo sosai, ahankali yace “meke miki ciwo”? Daga Anty Mariya har Zayn kallonta sukayi,
gently takai hannunta tanunamai gefen cikinta, boyayen ijiyan zuciya yasauke sanan yajuya
yace “lemme call Dr for you” yawuce zai fita, saida yakai daidai kofa tasake kiranshi amugun
hankali. “Ya Aliyu” chak ya tsaya still, kafin chan batare dayajuyo ba yace “I will get the Dr for
you, sai anjima Anty” dasauri Anty Mariya tace “sai anjima Aliyu an gode” kallon Khairy yayi
nakusan 1min dayaga takife kanta a filo sanan yatashi shima yakalli Anty Mariya yace “bari naje
anjima zan dawo” murmushi tayi tace “tom Zayn angode” sanan yawuce yafita, Anty Mariya da
takaranci komi that just happen in this room tasauke ijiyan zuciya ahankali tana kallon Khairy
datai kaman tana bacci taji anbude kofa Dr yashigo.
Aliyu na gab da tada motanshi yaji anyi knocking glass din motar, juyowa ahankali yakalli wajen
ganin Zayn ne tsaye yasa ahankali ya danna botur yasaukar da glass din motar yana kallon
Zayn din da idanunshi dasuka dan chanza launi, folding hannu Zayn yayi akirji dan idan baiyi
hakaba ayanda kirjinshi yaji yana tafarfasa da mugun kishi zai iya dambe da wanan dan
sandan, cikin wani yanayi na rashin mutunci yace “what’s between kai da kanwata”?Wani kallo
Aliyu yamai ido da ido kaman yazaro bindigarshi ya bindige Zayn yakeji, akufule yace “go and
ask ur sister” wani irin kallo Zayn yamai ganin kome yake takama dashi shima haka Aliyu yake
takama dashi yasa awulakance yace “stay away from this hospital and stay away from my
sister, I don’t want you handling case din barayin nan zanzo nasa abama wani dan sandan, duk
randa nakara ganinka anyway near my sister law zai rabamu” wani matsiyacin kallo Aliyu yamai
kafin yadau bakin glasses dinshi yasa a idanunshi yakalli Zayn din awulakance yace “I am the
law! So do your worse” yana maganan yadaga glass din motanshi sama yawani ja motar da
mahaukacin gudu yafita dashi daga asibitin yanaji kaman zai mutu da bakin kishi.
Kwana uku Khairy takara a hospital aka sallameta gidansu tace zata Anty Mariya kaman an
mata kyauta, fir Batool tace itama gidan Baba zata koma babu wanda yahanata suka koma
wajen nan tabama Khairy labarin all abinda yafaru har jinin da Aliyu yabata sanan tace taji Baffa
yace ankama duka barayin sun saida motan Zayn din amman an samo motan itama, sanan
Zayn suka dinga bi tun ranan farko daya fara zuwa Variety suka ganshi suke binshi dan sunga
big boy ne.
Wuraren 11 nadare tai dialing number Aliyu harya katse bai daukaba saigashi yakirata dawani
irin sauri tadauka ahankali yace “Pickle” murya chan kasa tace “Ya Aliyu ina yini” ijiyan zuciya
yasauke yace “ancemin an sallameki yau ko hope u are good” shiru tadanyi kafin ahankali tace
“Ya akayi kasan an sallameni” murya chan kasa yace “I come everyday to check on you dudda
bana shigowa dakin” wani kalan murmushi tayi tanason Aliyu over ko Allah ma yasani, murya
chan kasa taji yakira sunanta. “Ummulkhair!” Dan faduwa gabanta yayi dan wani irin faduwa
gabanta yaje most time idan yakira sunanta haka, murya chan kasa tace “na’am” dan shiru yayi
nakusan good 1min, sanan ahankali yace “is there anything between you and dan uwanki Zayn
da I don’t know about” dan zaro idanu tayi dan bama tagane kan tambayan ba hakan yasa
takasa ma magana, ahankali yasake maimaita tambayan. “Akwai soyayya tsakanin ke da Zayn
ne?” Wani irin zaro idanu tayi adan rude tace “ni? Nooo a’a wlh, why will you ask me such
question”? Dan shiru yayi sai chan taji yasauke ijiyan zuciya yace “abar maganan tunda kince
no I believe you” tsoro taji yadan shigeta ahankali tace “Ya Aliyu are u fine” ijiyan zuciya yadan
sauke sanan da kyar yace “I am now!” Yasake yin shiru saikuma chan yace “remember I told
you I am a very very jealous person, banda yan uwanki danasan kun fito ciki daya su Manaf I
can’t stand inga any man on this earth yana baki any affection look, Khairyyyy I love you don’t
you get that, I am crazy and obsess dake” dan murmushi tayi sai yanzu tama gane maganan
dayake yadauka ita da Ya Zayn soyayya suke saisa duk yay wani iri Ya Aliyu nada mugun kishi
kam, dan murmushi tayi tace “Ya Aliyu kai kadai nakeso aduk duniyan nan, nima I am obsess
with you, saisa nama zuciyana alkawari kai nata ne, THE PROMISE OF MY HEART is you”
murmushi yadanyi kafin ahankali yace “Khairy inaso naturo iyayena suga Baba” dasauri tace
“Ya Aliyu dan Allah kabari nakarasa school kagafa baifi 2month yaragemin ba nama fara project
ta online nake turama professor na yana dubawa, kaga I want to enjoy my wedding ayi event
kala kala nai rawa kasan na iya rawa” dan murmushi yayi yace “so I heard” dariya tayi tace
“dagaske fa” hira tadinga mai kaman ba ita aka sallamo daga asibiti ba harsaida yasaki
zuciyanshi sosai sanan wuraren 1 yasata tai bacci badan taso ba.
Kusan kullum sai Zayn yazo gidansu batasan mesa ba kofan tambayan da Ya Aliyu yamata ne
hakanan saita fara gujemai, dazaran yazo tagaidashi zata wuce dakinta zatajishi dasu Manaf
suna hira afalo Baba ma yadawo duk suhade sai dare yake barin gidan amman ita bata taba
saukowa, kullum tana zuwa school tadage da project dinta Maheer natayata yi yanzu ma haka
tana chapter 4.
Yau duka duka saura 14 days sufara final exam dinta tadage da karatu sosai, at the same time
Baba da Baffa da abokanen su sukaje nemawa Manaf Auren Aisha, Mu’az kuma Auren
Maimuna sanan washe gari sunday Baba yasa dukansu su shirya dan gidan Baffa zZasu yau
zasuyi family meeting.
4️⃣7️⃣
Ahankali take shiryawa dan ita ko kadan bataso taje gidan Baffan dan bamataso su hadu da
Zayn dataga Kwanan nan wani mugun kallo yake mata kaman zai hadiyeta, Batool da harta
gama shiryawa tace “wai bazakiyi sauri ba kinata abu ahankali kaman bakida kayan ciki”
hararanta tayi tace “dalla chan” bude kofa Anty Mariya data shirya tayi takalli Khairy tace “har
yanzu baki gama ba” gyalen abayan data saka tadauka baki tace “na shirya Anty” sanan
tadauki jakanta Batool ta tashi suka fito zuwa compund ganin Ya Manaf da Mu’az yasa tai wani
murmushi cikeda tsokana tace “angwaye wai kwana nawa aka saka ne” hararanta Baba daya
fito yayi yace “ban fadamusu ba sai munje gidan Baffan su zasuji” dariya tayi tace “wlh Baba
duk sun kosa” hararanta Manaf yayi yashiga motan shi yace “karki sake kizo motana Batool
taho kinji” dasauri Batool tai wajen, Baba yace “manta dasu muje motana kinji” gwalo tamusu
suka wuce tashiga motan Baba, Anty Mariya na gaba ita kadai abaya sanan suka wuce batasan
mesa ba hakanan taji gabanta nafaduwa dum dum dum, daura hannunta tayi kan kirjinta tana
addu’a azuciyanta tana kallon hanya ahaka har sukakai gidan Baffa, Babban falon Baffa sukaje,
tunda tashigo taga Zayn na kallonta kaman zai hadiyeta dawani irin sauri tadauke kanta tagaida
Ammi data amsata ciki ciki sanan tawuce wajen Mom tazauna kusada kafanta Batool ma
tazauna awajen tana gaida Ya Hafiz dake zaune kusada matanshi yana rikeda Babyn su dake
bacci, gasu Hassan a zaune kowa a zaune, Baffa na zaune kusada Baba
Ahankali tadago kanta hada idanu sukayi da Zayn dataga yasakin mata wani cool smile dasauri
tadauke kanta takalli Baffa dake gyaran murya.
Anatse Baffa yabude taron nasu da addu’a sanan yace “jiya munje gidan iyayen yarinyar da
Manaf dakuma Mu’az sukeso su aura, Alhamdulillah komi ya daidaita bamu sanar daku komi
gabe da abin bane sabida akwai abinda mukeso musanar daku wanda dukanku nan babu
wanda yasan maganan dagani sai Baffan ku nan” yanuna Baba saikuma “marigayiya
mahaifiyan ku Manaf” yanuna su Manaf, tsit dakin yayi, gyaran murya Baba yasakeyi yace “an
sakawa Manaf da Mu’az ranan aure kimanin sati hudu wato wata daya kenan” murmushi duk
akayi Hafiz najan bayan rigan Manaf dake murmushi cikeda tsokana yana kabarda hannunshi
sanan anatse Baffa yace “yara nata aure amman asalin Babban yayan gidan nan shiru” dariya
Hafiz yayi Ammi ta ballamai harara, anatse Baffa yace “gawata labari” sanan ahankali yafara
magana yace “shekaru ashirin dasuka wuce abaya, lokacin Zayn yashiga JSS 1, Hafiz na
primary school, su Hassan na Hussaini sune yara alokaci dudda suma primary suke, Maryama
wato mahaifiyan Ummulkhairy ta haifi Ummulkhair” Baffa yadanyi shiru, ajiyan zuciya yasauke
yace “bayan an haifi Khairy Maryam was very very sick, after series na test and investigations
alokacin ne aka fara gano cewa mahaifiyar ki nada blood cancer!” Shiru kakejin dakin kaman
ruwa ya hadiye kowa, ganin Baffa yakasa magana yasa ahankali Baba yace “Maman ki was
very very scared Khairy son da Mama kemiki tun ranan dakika fado duniya ne, bansan mesa ba
kodan agidan marayu ta taso tana matsayin ya mace batasan kowa nata ba tai wahalan
rayuwa, kodan sabida taga kema mace ce batason kiyi wahalan rayuwan datayi gashi ance
tanada cancer bazatai wani rayuwa mai tsawo ba dan lokacin bama agama sanin kan treatment
na blood cancer ba yasa ranan cikin dare ina bacci akan kujera naji Mamanki ta tabani tana
kiran sunana” Baba yadanyi shiru ahankali yace “bude idanu nayi naganta zaune kan gadon
asibitin rikeda ke a hannu” Baba yakarayin shiru yadan fuzar da iska nai dumi, Ahankali yace
“Maman ki was very very sick jikinta yay bala’in zafi tacemin tana ganin one of this days zata
mutu dan haka nakira Baffa nacemai idan zai taho yazo mata dasu Manaf dake gidanshi wajen
Ammi nacemata to ganin hankalinta atashe yake sanan takara kallonki” Baba yay shiru yace
“tana kallon fuskanki tacemin batason Ummulkhairy tasha wahala, sanan duk duniyan nan
banda ni babu wanda ta yarda dashi kaman Baffan ki tasan ko Bana duniya sai inda karfinshi
yakare akan yarana sabida haka tanason ta aurar dake tun yanzu datake da ranta a inda ko
yanzu yanzu tafadi tamutu zata tafi batada damuwa” Baba yakara yin shiru kowa na kallonshi,
handkerchief yaciro daga aljihu yakai kan idanunshi dan ko kadan bai son yay kuka agaban
yaran shi, kafadan shi Baffa ya matse sosai yakalli yaran yace “Baban ki yadauka awanan
daren Maman ki zata rasu, bayan tamai maganan nan tasashi yakirani awaya, kunga acikin
kuryan darenan haka nashiga mota nazo asibitin nan, cikin tsananin zazzabi tana rike dake a
hannunta tace tanaso tabani amanarki sanan tana neman alfarma wajena…..” wani irin faduwa
gaban Khairy dake kallon Baffa chass takeyi dabama tasan na miyeba, ahankali Baffa yace
“Maman ki tace tanaso nahada Ummulkhair da Zayn babban dana wanda Mamanki takeso
sosai sun shaku da mamanki sama da su Hafiz ma, tace tanaso nahada ku aure” Zayn da tunda
aka fara maganan kanshi ke kasa sai alokacin yadago kanshi yakalle Babanshi dake Magana,
Baffa yace “jikin Maman ki yay zafi yay tsanani duk mun zaci zata rasune, Gyadamata kai nayi
na nuna amincewa na, tace mukaita masallaci adaura auren, I remember Baban ki yafita waje
yadauko keken guragu muka daurata akai muka gungura keken har zuwa masallacin dake
asibitin nan dayake nan kaman ba dare ba jama’a duk suna zazzaune some a kwance iri masu
jinyan nanne, da sauransu limamun muka kira mukamai bayanin komi ya matukar tausayama
Maman ki sanan aka gungurota aka shiga da ita masallaci tana rike dake a hannu limam
yadauki microphone aka tada duka mutanen dake bacci” tsinkewa gaban Khairy yahauyi yana
dawowa daidai hakama Batool, Ammi, Zayn dakuma Anty Mariya, kowa na kallon Baffa, murya
chan kasa Baffa yace “all I had was 20k ajikina haka na bayar kudin sadaki dani da mahaifinki
limamin masallacin mahaifiyar ki jama’an dake wajen suka shaida daurin aure tsakanin
Ummulkhair Ahmad Muhammad da Zayn Abdullahi Gabas akan sadaki naira dubu ashirin!”
Khairy jitayi numfashinta zai dauke kunenta yay dummm kaman ta sume ne kaman tafice
hayyacinta ne oho ita kanta bazata iya tantance wani yanayi take ciki ba, daga Baba har Baffa
murmushi sukayi suka kalli juna, Baffa yace “inda ace Baffan nan naku nada yara mata dayawa
zansa yarana maza duka su aurensu sabida inaso muhada zuru’a wanan amincin dake
tsakanin mu na abota takoma na jini, saisa bayan mun daura auren muka yanke shawarana sai
yaranmu sunyi girma sun mallaki hankalin junansu zamu sanar daku, yanzu ma bikin su Manaf
ne sabida munaso muhada bikin su da kuma taron bikin su Zayn ayi atare saisu tare nan da
wata daya lokacin Ummulkhairy itama tagama jarabawa tagama makaranta ko aminina”
gyadamai kai Baba yayi yana wani irin murmushi, Ammi dajitayi komi na duniya ya tsaya mata
chak takalli mijin nata, cikin wani irin masifa tace “Alhaji na dauki cikin Zayn na wata tara, na
tsugunna na haifo dana dakaina batare da wata ko wani yatayani ba ninasan ciwon kan d’ana
nasan wahalan danasha na tarbiyantan dazai ka kama shekaru kusan ashirin kenan kama
d’ana aure baka sanar dani ba wlh wlh wlh kayi kadan!” Ammi tama Baffa magana babu ko
shakkan shi guda akan idanunshi dayasa kowa yakalleta shima Zayn yakalleta uppan Baffa
baice mata ba hakama Baba duk kallonta suke da Mom da Anty Mariya dasauran yaran.
Hannun kujera Ammi tadaka cikeda bala’in dakin na amsa masifanta jikinta na girgiza tacigaba
da magana. “Idan zuri’a kukeso kuhada abotanku yadawo tajini inace nan nan nan ga Batool
nan diyar kace maisa baka hadata da Manaf ko Mu’az ba koma Maheer sai akan d’ana Zayn
dina, kasan plan din danake dashi , buri danaci akan yaron nan nawa dazaka hadashi da yar
gwal dinku? Kasan wace yarinya nakeso Zayn ya aura kasan matsayin Baban ta anan Nigeria
kuwa kaga kyan Aisha? Wlh bazaka maidani karaman mutum a idanun kawata ba” takalli Zayn
cikeda ihu tace “Zayn kalli fuskan mahaifinka kacemai bakason auren nan yanda sukayi suka
hada auren subi haka su warware” shiru Zayn yayi kanshi nakasa shi bazai iyama cewa farin
ciki yake ba ko bakin ciki all he knows is yaji dadin wanan labarin dayajita bagatatan haka
kaman daga sama.
Baki Ammi tabude zata kara magana Baffa yadaga mata hannu cikin fushi, anatse yace “kinsan
maisa duka wanan ihun dakike yi danki tozartani bazai taba bani kunya ba”? Dan murmushi
yayi yace “sabida agaban dan uwana da yarana kike ko zaginane zaki iyayi” Baffa yasake
murmushi yace “auren nan ba marigayiya kadai tai tunanin shi ba har mu nan, duk duniyan nan
babu wanda zai rike Khairy amana kaman dan uwanta kuma Yayanta Zayn! Bata fita daga
family ba zamu riketa amana dan dan uwanta take aure, banda kwanciyan hankali daya wuce
nasan d’ana ke auren Khairy da mahaifiyarta tabani amana, nasanki karki manta na zauna dake
tsawon shekaru danmu na farko shekarun shi 36 so babu wanda zai iya bada labarin halinki
kaman ni, nariga nasan bakison mahaifiyar Khairy hakan zaisa bazaki tabaso auren shi da yarta
ba abu nafarko dayasa naji bazan taba fadamiki ba kenan sai ranan da zan hada yaran nan
nafada musu kisani kema, dan haka kome zakiyi kiyi Zayn mijin Ummulkhair ne nan da wata
daya za’ayi walima ta tare agidanshi, kutashi kutafi” cikin yaran babu wanda ya iya cewa uppan
duk mikewa tsaye sukayi banda Khairy data kasa mikewa tsaye tana kallon Baba idanunta
sunyi jazur Baba shima yana kallonta, hannunta Batool takamo zata dagata tace “tashi muje
Khairy” ahankali Baba yace “barta Batool” tashi yayi ahankali sanan yadauki wata yar jakan
dake kusada shi yabude wani littafi yaciro tana kallon littafin ta tunashi Dairy Mama ne,
karasowa gabanta Baba yayi ahankali sanan ya tsugunna agabanta yana kallonta, ahankali
cikeda so dakuma tsantsar kaunar yarshi yace “Khairy kingan mu nan we are not bad parents
idanma abinda kike tunani kenan, all abinda kikeji azuciyanki yanzu nasani, kina tunani tayaya
aka miki aure tun kina karama baa taba sanar dake ba, auren ma da Yayan ki Zayn, wanda baki
taba kallo da fuskan so ba, wanda bakisan koshi yana sonki ba” dan murmushi yayi yace
“kituna babu aure mai albarka kaman wanda iyayenka suka zaba sanan suka maka banda haka
kiyi tunanin auren nan mahaifiyarki dakikafi komi so aduniyan nan tahada ita tama miki shi
Ummulkhair, and lastly mahaifiyarki tace nabaki Wanan abin ki karanta idan rana irin tayau tazo
gashi” Baba yasamata book din a hannu, wani irin kankame book din tayi gam gam sanan
Batool tadagata bin Batool kawai take suka wuce mota suka shiga suka zauna itama ahankali
Anty Mariya tashigo taxauna tana kallona Khairy da idanunta suka bushe babu hawaye ko digi
bazama ka iya tantance metake going through ba, chan saiga Baba yafito tareda Baffa motansu
yazo yashiga yaja suka tafi sanan Baffa yawuce yakoma ciki biyoshi Ammi tayi tafara surfafa
bala’i amman tak bai cemaHta ba.
4️⃣8️⃣
Koda sukakai gida kasama fitowa daga motan Khairy tayi duk Baba na kallonta da taimakon
Anty Mariya da Batool suka fito da ita sanan suka shiga ciki Anty Mariya tace “tafi da ita dakinku
Batool” wucewa da ita sama Batool tayi sanan tajuyo takalli Baba zatai magana Baba yadaga
mata hannu anatse yace “Zayn shine best husband da Ummulkhairy will ever wish for, please
karkimin wata magana aikin gama yariga yagama beside auren nan mahaifiyanta tamata shi”
shiru Anty Mariya tayi tana kallon Baba saikuma ahankali tace “ok” sanan tajuya tawuce sama
abinta.
Suna shiga daki Batool tazaunar da ita abakin gado sanan tamaida kofansu tarufe tasa key
sanan tazo gaban gadon da gudu tazauna akasa kanta tadaura kan kafan Khairy tace “Khairy
why are you not crying Innalillahi wa innailaihi raji’un,