Showing 42001 words to 45000 words out of 147042 words
shi kuma ba ta son wani abu ya samu auran ta.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t
*07*
Washegari.
Ummu-Salma ta ƙulla ƙawance da kuka. Ta kwana yi ta yini yi, jiya ma kwana ta yi kuka shi ya sa ta tashi idanuwanta sun kumbura sun yi luhu-luhu, fuskarta ta yi jajir abin ka ga farar fata.
Ba ta fito daga cikin ɗakin ta ba sai da ta ji fitan Habib daga gidan sannan ta fito domin tsoron haɗuwa da shi take yi. Ba ta iya tsinana komai ba, ga ciwon kai ga jikinta duk ba daɗi ruwan zafi ta dafa ta sha ruwan lipton saboda za ta sha magani sai da ta sha mgani ta ɗan ji ya kwanta mata sannan ta shiga ta yi wanka tana cikin shiryawa ne Hamma Sadam ya kira wayarta. Tana ɗauka ta ji yana faɗin.
"Ke wai kin mutu ne? Ko an yi miki magana a WhatsApp ba kya dubawa. Sai yau na sake duba ki na ga kin kwana biyu ba ki hau ba."
Mirmishi Ummu ta yi kafin ta ce" Zan mutu ba ka sani ba ne Hamma?
Ta ƙarishe faɗa cikin sanyin murya.
"To na sani,"
Ya faɗa cikin ƴar dariya. Dariyan Ummu ta taya shi kafin ta ce" Ba ni da lafiya ne fa Hamma."
"Oh haka ne kwanaki mun yi waya da Amma ta ce ba ki jin daɗi, shi ne har yanzu?
"E."
"Me ke damun ki?
"Zazzaɓi ne Hamma."
Ta faɗa cikin kasalan da ta ji ya sake rufe ta bayan ta yi wanka.
"Sannu. Allah ya ƙara lafiya."
Ta amsa da Amin. Shi kuma ya tambaye ta ko ta je asibiti.
"E mun je"
"Allah ya ƙara afuwa sannu."
Ta amsa masa da yauwa. Habib ya tambaya ta ce ya fita aiki.
"Allah ya ba mu sa'a."
Daga nan ba daɗewa suka yi sallama da juna kowa ya kashe wayarsa.
Ɗan wayar nan da suka yi da Hamma Sadam ya ɗan rage mata damuwa. Shi fa ɗan'uwa daɗi ne da shi.
Ballatana Hamma Sadam irin mutanan ne masu amfani da social media sosai, duk gidan su ba kamar sa, komai na shi kowa ya sani, shi ne instagram shi ne Twitter, shi ne Facebook kullum ba shi da aiki sai posting ɗin hotunan shi komai yake yi sai duniya ta sani. Shi ya sa duk wani labarin da ke faruwa Hamma Sadam na da labarin shi da har hoton Baffa da Amma yana kafewa a Facebook Hamma Abdulrrahaman ne ya yi masa faɗan akan ya daina posting ɗin hotunan su Baffa in zai saka na shi ya saka amma ban da na Ammah da Baffa shi ya sa ya daina amma na shi kam bai daina ba, a ko wani hali ya ke ciki kafin ya yi mgana posting ɗin shi ya bayyana halin da ya ke ciki. Kuma shi ba ma'abocin kiran waya ba ne amma za ku yini kuna chart bai damu ba. Shi ya sa ai Hamma Sadam kodayaushe yana online ne.
Sai da ta ɗan kwanta domin sai ta ji amai yana ta so mata, sannan kasala duk ya rufe ta sai wajen goma da wani abu ta iya rarrafawa ta fita. Doguwar riga ta saka na wata Atamfa sai ta yi amfani da bakin mayafi, ƙaramar jakarta ta ɗauko in da ATM ɗin ta na Banki yake tun da ba kuɗi a hannunta sai ta cire, sai da ta biya ta wani shago ta cire 5k sannan ta samu mai Kekenapep ta yi drop zuwa gida.
Bai sauke ta ko'ina ba sai ƙofar gidan su dake tsakiyar anguwan Zone 3. Ta sauka ta biya shi kuɗin shi sannan ta fara takawa ta tunkari baƙin get ɗin gidan na su, a baya ba baki ba ne da Hamma Lamiɗo ya sa aka gyara gidan ne a lokacin aka sauya get ɗin gabaɗaya. Ba ta tsaya ma ƙwanƙwasawa ba ta tura ta shiga sanin da ta yi get ɗin a buɗe yake, tuni Ammah ta ce a riƙa barin shi a buɗe saboda ba za ta iya wahalan kai da kawo tsakanin get da cikin gida ba shi ya sa a buɗe yake sai dai za a tura shi amma ba za a rufe ba tun da ba maigadi, tun tuni da man gidan Baffa ba mai gadi ballatana yanzu da rayuwa ta gangara.
In ka shiga gidan haraba za ka fara gani, daga yamma kuma akwai wani flat ɗakunan mazan gidan ne falo ne da ɗakuna huɗu kuma kowanne da banɗaki a ciki. Hamma Sadam ke zaune a ciki yanzu amma in su Hamma Mustapha suka zo su kan sauka a wajen ko baƙi daga Mubi dangin Ammah ko Baffa. Daga nan sai bangaren kudu akwai ɗan korido da za ka bi zuwa cikin gida wanda ke ɗauke da tsakar gida daga gefe kuma kitchen ne Babba sai yamma kuma ɗakin Baffa sai daga gabas kuma Ɗakin Ammah ne mai ɗauke da falo da ɗakuna huɗu a ciki. Sai gefen can kuma falo ne sai ɗaki ɗaya a ciki da banɗaki. Ɗakin da Mami ta yi rayuwarta kafin ta yi aure sannan anan Ammah kan sauki baƙin da za su fi sati kafin su tafi. Ɗakin a gyare ya ke, tsab kamar yadda bangaren Ammah ya ke shima kamar ɗakin wata Budurwa. Kusan duk shekara Hamma Lamiɗo sai ya sauya mata tsarin falo, Amma ta yi ta faɗa tana cewa ya bari ita ya gama biyan ta tunda ya kai ta Hajji sannan ya kai ta Umra amma ba ya ji ba ta ma sani sai dai ta ga Hamma Kabiru ya zo yana zuwa to kamar shi ne ya zo tun da duk wani abu da Hamma Lamiɗo zai yi ma Amma na suprising ɗin ta, to da Hamma Kabiru zai fara tattauna maganar sannan Hamma Abdullahi ya gabatar.
Tsakar gidan duk shimfiɗe yake da interlock. Tsakar gidan tas Amma ta share shi Ummu na ta sallama da ƙaramar muryanta ta ji shuru ta dai ta san Baffa baya nan tunda ba ta ga motar da ya ke hawa a haraba ba, ɗayan ta gani Benz ce tana lulluɓe da tamfol ya jima ma bai yi amfani da ita ba.
Jikinta ba karfi shi ya sa ta kasa ɗaga murya ƙarisowa ta yi kofar falon Ammah ta ɗaga labulen tana leƙen cikin ɗakin.
"Ammah."
Ta faɗa a hankali tana zagaya idanuwanta a cikin ɗakin amma shuru kamar ba kowa ashe ba ta sani ba Ammah na dakin Baffa.
Amma ta fito daga ɗakin Baffa ita kuma Ummu Salma ta juyo sai suka yi ido huɗu.
Mamaki ya kama Amma cikin mamakin a muryanta ta ce.
" Ke kuma daga ina kamar an jeho ki?
Ta faɗa tana nazarinta. Kafin ta wuce ta zuwa cikin falon ta.
Ummu ta ja kafafunta sannan ta cire takalmin kafanta ta bi bayan Ammah zuwa cikin falon.
Kan kujera mai zaman mutum biyu ta zauna tana mai mikar da kafarta ji ta ke yi kamar ta kwanta saboda wata gajiya da ta ke jin tana sauka a cikin gangar jikinta.
Amma ciki ta shiga ba daɗewa sai ga shi ta fito ganin Ummu zaune a yanayin da ba ta gane mata ba yasa ta nemi kujerun gefen ta lokaci ɗaya tana faɗin" Ke lafiyan ki kuwa?
Ta faɗa tana sake kallon Ummu da ke yamutsa fuska duk da ta san halinta amma yanayin ta ya nuna ba lafiya tun ballanta ganin ta rame ta sake yin fari.
"Ina mgana kin yi mini shuru?
Ammah ta sake tambaya cikin fusata da sauri Ummu ta ce" Ina kwana Ammah "
Ta furta cikin harshen fillanci Amma ta amsa da sauri tana cigaba da faɗin" Ko jikin ne har yanzu?
Sai kawai ta gyaɗa mata kai lokaci ɗaya tana bin shawaran zuciyanta ta kwanta a saman kujeren da ta ke zaune.
"Sannu. Me ke damun ki hala?
"Ammah zazzabi ne?
Ta ba ta amsa, ita kuma sai ta sake kallonta abin da ta gani kamar ciki ne laulayi ne ke wahalar da Ummu, amma tunda ba ta faɗa mata ba sai ba ta nuna mata ta gane ba.
"Kun je to asibiti?
Wannan karon ma kai ta gyaɗa mata ba ta yi mgana ba,sabo da ba ta so Ammah ta fahimci wani abu ta san halin ta yanzu nan za ta rikita lamarin ya zama ba yadda take so ba gwara Baffa shi yana da sauƙin kai da fahimta.
"Allah ya sauwaƙe, ya wajen shi Habibun!? Kuna nan lafiya dai ko?
Amma ta tambaya lokaci ɗaya tana mikewa.
"Lafiya lau."
Ummu ta amsa cikin sanyin murya sai da Ammah ta kalleta na wani lokaci kafin ta girgiza kai, jikin Ummu duk ya yi sanyi kamar ba ita ba amma ba ta kawo aran ta ba sai ta ce wataƙila laulayi ne mai zafi shi ya sa duk ta sauya.
"Baffa fa? Ba ya nan ne?
Ta tambaya lokacin da Ammah ke shirin ficewa daga falon.
"Yanzu nan ba daɗewa ya fita zuwa cikin Yola."
"Yaushe zai dawo? Ba zai daɗe ba ko?
Ummu ta tambaya a marairai ce, Amma ta fasa fita ta juyo tana kallon ta.
"Tare da Abdullahi suka fita watakila ba za su daɗe ba."
Sai ta jinjina kai lokaci ɗaya tana mai lumshe ido.
"Ummu Salma."
Ta ji Ammah ta kira sunanta da sauri ta buɗe ido tana kallon ta duk da tana kiran ta da haka lokaci bayan lokaci amma na yau cikin wani irin amo ne da ya sa ta natsuwa.
"Me ke faruwa ne?
Haka Ammah ta tambaya lokaci ɗaya tana tsare ta da idanuwanta, da sauri ta dukar da kallon ta ga Amma kafin ta ce" Ba komai Amma."
"Kuma kike tambayan Baffa?
"Kawai fa ina son ganin shi ne"
Ummu ta faɗa cikin yar shagwaɓa har tana ɗan turo bakin ta gaba.
Amma ta yi ƙaramin tsaki ta fice tana faɗin" In kin gan shi sai ki haɗiye shi "
Har sai da ta saka Ummu dariya Ammah shagali, tana nan kwance tana mirmishi lokaci ɗaya da tunanin yadda za ta fara taran Baffa da mgana tana tufka tana warwara ba ta san lokacin da barci ya kwashe ta ba, ita dai ƙamshin wani abu ne ya tashe ta, tana tashi sai ta ga Ammah ce ta dama kunu da ya ji kayan kamshi shi ya sa ƙamshin ya cika falon ta.
"Amma zan sha kunun."
Ummu ta faɗa lokaci ɗaya tana tashi zaune, ɗankwalin ta ya fita kanta kitso ne duk ya tsufa har ya fara zarewa da kansa. Ba ta da wata natsuwa ballanta ta iya tsefewa ta sauya wani.
"Ga shi nan ki diɓa, da ma Abdulrrahaman ne ya ce na dama masa yana nan zuwa "
Sai da ƙirjin Ummu ya amsa a cikin zuciyarta ta ce Allah ya sa lokacin da zai zo ta gama mgana da Baffa domin masifaffe ne in ya ji wannan mganar zai iya ɓata komai a lokaci ɗaya ba tare da ya damu ba. Tana kallo Ammah ta diɓa masa a cikin ƙaramin fulas sannan ta bar mata sauran a ƙaramin botikin da ta dama kunun da cewa in ta tashi za ta sha sai ta samu kofi ta diɓa daga nan Amma ta fice daga falon zuwa Kitchen.
Tana son kunun ya biya mata rai, duk da tana tsoron amai haka nan ta tashi ta fita ta ɗauki kofi saman frizan Amma ta zuba kunun ta koma ta zauna tana sha, har wani lumshe idanuwana take yi saboda da daɗi, da man in dai Ammah ta yi girki ko da dama abu daɗi ne da shi ballatana garin kunun ta na daka ne, yana jin kayan ƙamshi in ta dama ma shi ya yi ta tashin ƙamshi.
Kamar abun arziƙi ta shanye kofin da ta ɗiba daga farko har ta kara wani ma, sai dai tun kafin ta yi rabin shi zuciyarta ya fara tashi kafin ta yi wani yunƙuri amai ya taso mata ai da gudu ta faɗa ɗakin Ammah ta shiga toilet ɗin ta, ta fara kelaya amai gabaɗaya abin da ta ci sai da ta amayar da shi, tana cikin yiin aman ne Ammah ta shigo ɗakin har sai da ta leƙo ta.
"Sannu."
Ta ce mata sannan kumavta shiga ta kama ta bayan ta ɗauraye bakin ta, sai ta ce ta fita bari ta wanke wajen, kan gadon Ammah, Ummu ta faɗa tana ma yar da numfashi tas Ammah ta wanke tiolet ɗin sannan ta fito tana kallon Ummu da ke kwance kamar ruwa ba ta sake yin mgana ba ta kaɗa kai ta fice daga ɗakin. Ita kuma Ummu aman da ta yi duk ya sake sakar mata da jiki, kasalan da ta ke ji daga farko ya sake zuwa ya rufe ta da take jin ta kasa tashi sai kawai ta sake naɗewa a kan gadon Ammah ta jawo filo ta rumgume ta lumshe ido tana sauke numfashi sama-sama.
Daga nan sai barci ashe ta daɗe tana barci ba ta sani ba. Sai bayan azahar ta farka. A lokacin ta iya tashi sai dai ta ji yanayin jikin na ta ya ɗan saki tiolet ta shiga ta sake ɗauro alwala ta yi salla ta idar kenan tana kan darduma Amma ta shigo.
"Kin tashi?
"E Amma sannu da aiki "
"Yauwa, ga Baffan can ya dawo "
Amma ta faɗa lokaci ɗaya tana kallon Ummu.
"Ki ci abinci tukunna shima abincin yake ci."
Sai ta gyaɗa mata kai ba tare da ta yi mgana ba.
"Bari na yi wanka."
Haka Amma ta faɗa, lokaci ɗaya kuma tana tura kofar tiolet ɗin ta shiga. Shuru Ummu ta yi kafin ta yi saurin mikewa gwara ta je ta samu Baffa da maganar kafin Ammah ta fito daga wanka. Tana fita falo sanye da hijabin Ammah ta iske ta zuɓo mata abinci a kula da ruwa tana dubawa sai ta ga Dambun shinkafa ne da zogale. Allah sarki Ammah ta ɗauka har yanzu tana son dambun shinkafa da zogale ba ta san yanzu duk wani abu da take so a baya yanzu ya fita ran ta ba, amma ƙamshin gyaɗan da ke tashi a dambun ya sa miyan ta ya tsinke ba ta ci ba sai ta rufe da niyyar sai sun gama mgana da Baffa tukunna. Ta gode ma Allah da Hamma Abdullahi bai biyo ta gidan ba, ba ta son kowa ya san mganar nan sai Baffa ta fi amin ta da tunanin shi akan na kowa.
Sallama ta yi a ɗakin Baffa ba ta shiga ba sai da ya amsa mata.
Yana zaune a ƙasa a saman darduma yana cin dambun da Amma ta yi, gefe ɗaya da kunu da ruwa a saman wani faranti
Tana shigowa ya ɗago yana kallonta nan da nan ya faɗaɗa mirmishin sa.
"Autan Baffa"
Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai cire hannun shi a filet ɗin Dambun.
Itama cikin fara'a da farinciki ta zauna a gaban shi lokaci ɗaya tana faɗin.
"Baffa."
Ta faɗa cikin yar shagwaɓa, Baffa na dariya ya ce" Na dawo Amman ki ta ce kin zo kina tambaya na "
"To Baffa na yi kewarka ne. Ba ni da lafiya daga kai har Ammah ba wanda ya zo ya duba ni"
Da man ƙiris take jira sai hawaye, shi kuma ya shiga aikin lallashin ta da cewa suna shirin zuwa ne sai ga shi ta zo amma in ta koma zai matsa ma Ammah ta shirya su je su duba ta.
"Da gaske Baffa?
Ta faɗa tana kallon shi, shi dai ya je ɗakin ta sau ɗaya ɓarin da ta yi amma Ammah ba ta taɓa zuwa ba, shi ya sa take mamaki da ya ce mata za su zo.
"In sha Allahu."
Ya faɗa yana dariya, in ban da rigiman Ummu me zai kai su gidan ta, amma saboda ya san halin ta ya sa ya lallaɓata da za su zo, abincin ya ce ta zo su ci sai ta ce nata na ɗakin Amma, shima kaɗan ya ƙara ya ce ya ƙoshi. Ummu ta ɗauko masa wata roba ta zuba masa ruwa ya wanke hannunsa sannan ta kwashe kwanukan da ya yi amfani da su ta mayar kitchen ita saurin ta kafin Ammah ta fito ta sanar ma da Baffa abin da ke faruwa shi ya sa tana dawowa ta sake tankwashe kafafu a gaban shi tana kallon shi, yana kurɓan kunun sa lokaci ɗaya yana nazarin Ummu.
Tambayanta jikinta ya yi ta ce da sauƙi.
"Ya wajen shi Habibun? Fatan yana nan lafiya ko?
Habibin da ya ambata kamar ya yi mata fami ne, sai ta fara marairaicewa kafin Baffa ya sake mgana Ummu ta kece masa da kuka cikin tashin hankali ya ajiye kofin hannun shi yana kallon Ummu.
"Kuka Ummu? Me ke faruwa ne? Wani abu ne ya samu Habibun?
Ya faɗa duka a jere, kai ta girgiza masa kafin ta kira sunan shi.
"Baffa."
"Naam Ummu Salma."
Kukan ta ya ki tsayawa hawayenta suna zuba tana saka gefen hijabin jikinta tana gogewa.
"Me ke faruwa ne?
Baffa ya sake tambayan ta cikin kyakyawan lafazi.
"Baffa."
Kafin ya amsa ta cigaba da faɗin" Da ma, da ma ina da ciki ne."
Sai kawai Baffa ya washe baki yana faɗin" Ma sha Allah. Wannan ai abun murna ne ba na kuka ba Autan Baffa."
Kallon sa ta yi kafin ta ce" Baffa Habib ya ce ba ya son cikin fa"
Baffa ya zuru yana kallonta cikin mamaki kafin ya ce" Ban gane ba ya son cikin ba kamar ya ya?
Ummu-Salma ta sake fashe masa da kuka ƙasa-ƙasa ta kasa mgana.
"Kukan kuma dai Auta! In ba ki bar kukan nan ba ta ya ya za ki yi mini bayanin da zan fahimce ki?
Ya faɗa cikin damuwa saboda tunaninsa ya tsaya a dalilin kukan Ummu saboda mijinta Habib ne kuma ya shafi cikin jikin ta.
"Baffa kai kaɗai ne za ka iya taimako na. Shi ya sa na zo wajen ka."
Kai ya gyaɗa mata kafin ya ce" In sha Allahu Auta sai dai abin da ya gagare ni, sai na bar ma Allah ya yi na shi ikon."
"Baffa ina son Habib."
"Na sani."
Baffa ya ba ta amsa a ɗokance domin ya ƙosa ya ji dalilin Habibu na cewa ba ya son ciki.
"Ba na so na rasa shi, ko na rasa aurena."
"In sha Allahu alheri ne zai biyo baya Ummu-Salma.".
Ya kira sunanta, suna mai darajan da ba ya iya kira saboda sunan mahaifiyar shi ce sai dai ya ce Ummu ko Autan Amma ko Autan Baffa amma tun da ta ji ya kira sunan ta tasan wasa kuma ya ƙare.
"In ba ki yi mini bayanin abin da ke faruwa ba, ai ba zan iya taimaka miki ba Auta"
Tana