Showing 72001 words to 75000 words out of 147042 words

Chapter 25 - FARGAR JAJI Ƙarfin Boye By Janafty

Janafty   

31 Aug 2026

533

ba, mace ce mai ji da kanta da sarauta, ita ɗin babanta ya yi sarki kakanta ma Sarki ne sannan mijinta ma Sarki ne kuma ɗan ta ma zai yi sarauta, shi ya sa ba ta ƙaumar talaka ko mara arziƙi tana harkokinta da masu asali ne da sarauta a labarin da ya ji ma tana nema ma ɗan ta auren ɗiyar wazirin Daura ne a lokacin.

Ba yadda Baffa bai yi da kar a yi auren ba amma ba wanda ya saurare shi, dangin Gwaggo suna ganin wata dama suka samu guda tak a kaf zuru'an su, suma su Baffa Hamza haka suke gani musamman shi da yake Babba mulki da kwaɗayi sun rufe masa idanuwa ganin irin dukiyar da Sarki yasa aka aiko wasu amintatttunsa da shi a matsayin Sadakin Fatima har da gwala-gwalai, Umma(Asma'u) a lokacin itama ta goyo bayan Baffa amma Baffa Hamza bai saurare ta ba, yana ji yana gani aka ɗaura ma Fatima aure da Hakimin Daura daddare domin sirrinta auren. Auren da aka ɗaura a garin Mubi sannan anan aka saka Fatima a lalle tana kuka tunda ko sau ɗaya bata taɓa sanin mijin ba, ta dai san Hakimin Daura a saman doki kansa da rawani idanuwansa kawai ta taɓa gani tunda suna zuwa kallon hawan salla lokacin shagulgulan salla a lokacin mace ba ta ikon cewa ba ta son wanda aka bata ko ba ta so dole za ta yi hakuri ta zauna kowa faɗa mata yake yi ta yi dace a dangin su kaf daga asalin tushen su ba wacce ta taɓa samu sa'ar da ta samu, Baffa ne kaɗai bai yi farinciki ba Ammah daga baya ta saduda ta riƙa lallashin Baffa da ya yi hakuri ya yi ma ƙanwarsa addu'an samun dacewa.  Da za a tafi da Fatima Daura a wani kebantttacen gidan Maimartaba da ba wanda ya san da shi za a ajiye Fatima cikin sirri, Baffa ya yi magana da ƙanwarsa ya yi mata nasihan ta yi ma mijinta biyayya amma shi dai a ƙasan zuciyarsa yana ta jin tsoro, tsoron faruwan abin da yake gudu kuma daga ƙarshe sai da ya faru ɗin

  Tun Baffa na tunanin nan da wata ɗaya zai ji wani abu game da Fatima har dai aka kwarari wattani bai ji komai ba sannan tana yi masa saƙo da cewa tana nan lafiya lau. Sai hankalin shi ya kwanta ya ɗan samu natsuwa bai sake jin ya natsu ya samu kwanciyar hankali ba sai da Fatima ta zo ganin su a Yola tare da wani dogari amintattacen Hakimin Daura ya kawo ta Fatima ta yi kyau ta yi kiba har da wayar nan ta zamani a hannunta Handset sannan ta tabbatar ma da su Amma da Baffa cewa mijinta na son ta Sarki ma na zuwa dubata amma dai ba ta zuwa  ko'ina itama ba mai zuwa wajenta daga ita sai wata amintattaciyar Baiwa mai suna Zulai tare ma suka zo sai dogarai guda biyu masu gadin ta da direba, irin kayan alfarman da ta zo da su kawai ya isa ya ba su tabbacin abin da ta faɗa gaskiya ne sannan ta zo ma da Baffa da kuɗi da suturu shi da Ammah da yara ta ce daga Hakimin Daura. Baffa dai ba abin duniya ba ne a gaban shi, shi dai fatan shi da burin shi Fatima ta samu farincikin da zai dauwama. Bayan zuwan Fatima sun sake dawowa tare da Hakimin Daura mijinta sun zo yi musu sallama zai tafi wani cos na wattani biyar kasar waje kuma tare da Fatima zai tafi, Hakimin Daura har ƙasa ya duka ya gaishe da Baffa ya kuma ba shi tabbacin har iya numfashinsa na ƙarshe zai kare Fatima. A lokacin da suka bar kasar Fatima ta bar Ammah da cikin Kabiru ne itama acan ƙasar da suka je ta samu ciki kuma suna garin ba su dawo ba maganar auren Hakimin Daura ya tabbata da Ɗiyar Wazirin mai ci a lokacin dalilin haka ya sa Fulanin Daura ta tsara bikin da yana dawowa za a ɗaura aure a yi shagulgula.

Auren da ya zagaya duniya, amma Baffa bai damu ba tunda Fatima ta tabbatar masa tana lafiya babu abin da auren nan ya rage ta ko shafe ta. Ita tunda auren sirri ne yanzu ne duniya ta shaida Hakimin Daura ya yi aure suka kuma tare a wani katon bangare a cikin masarauta. Fatima ta zo taron sunan Kabiru da tsohon cikin ta in da suka haɗu da dangi daga Mubi,  kowa ya ga Fatima sai ya rike baki ta yi wata kiba sannan duk in ta taka kunyanga na biye da ita riƙe da jakarta ta zama abar sha'awa a wajen dangi, tana ma Yolan ne ta samu labarin Maimartaba Sarki Muhammad Shitu ba lafiya an fita da shi ƙasar waje domin nema masa lafiya kuma tare da mijinta aka tafi, dalilin da ya turo direba ya ɗauke ta ya ma yar da ita Daura ta koma da kwana uku Allah ya yi ma Maimartaba rasuwa, mutuwar da ta saka ma suna da mutuwa mai tonon asiri, domin sanadiyar mutuwar maimartaba sirrin auran ta ya bayyana a masarautar Daura. Ranar da Hakimin Daura ya zo hankali tashe yana sanar da ita mahaifiyarsa Fulanin Daura ta saka ana bibiyansa ta gano komai saboda haka ta shirya zai saka a zo a ɗauke ta zuwa can Mubi har zuwa komai ya lafa ya fita ya barta cikin tashin hankalin da ya jawo mata gajeruwar naguda.
Daga ita sai Zulai ta haifi kyakyawan ɗanta namiji mai kama da uban shi, tana ma nishin haihuwan Fulanin Daura ta dira gidan a daran tare da Mijinta Hakimin Daura.

Fatima na kwance a cikin jinin Haihuwa Fulanin Daura ta umarci ɗanta da ya sake ta a cewarta zama da Fatima zai iya yi masa cikas da hawa karagan mulki ita kuma nan duniya ba abin da take muradi da fata kamar ta gan shi ya gaji mahaifinsa Fatima na kuka yana kuma yana roƙon ta amma Fulani ta ce ya zaɓa ko daraja da ƙimar masarautan Daura, Ko auren Fatima
Ba shi da yadda zai yi anan take ya yi ma Fatima saki ɗaya sannan ko ɗan da aka haifa masa Fulanin Daura ba ta bashi damar ɗaukan gudun jininsa ba a daran ta saka aka ɗauki Fatima a mota ita da abin da ta haifa, a cikin jinin haihuwa ita kanta da tsamin naguda da jinin haihuwa a jikinta ta kamo hanyar Yola a daran ba ta je ga gidan mariƙanta ba , sannan ba ta je mubi ba Sai ta je ga Baffa da Ammah ƙarfe uku na dare Fatima ta isa ita da Zulai da wani dogari Baffa sai da ya yi hawayen tausayin Fatima. Suna kuma kawo ta ba su tsaya ba suka juya daga Umarnin Fulanin Daura bayan an basu kuɗaɗe da gwala'gwalai da cewa kar Fatima da abin da ta haifa su sake dawowa Daura har abada. Sannan su Madibbo ma sai da Fulani ta saka a ka sauya musu gari suka koma cikin garin kurfi a cewar ta, ba ta son duk wani da ya danganci Fatima ya zauna a garin Daura ba ta fatan nan gaba labarin Fatima ya fito har ya yi ma ɗanta cikas ɗin zamowar Sarki. Waɗanda ma suka sani a lokacin duk ta rufe bakin su, ta haramta musu ambaton labarin.

Tabbas burinta ya cika, Hakimin Daura Muhammad Nasiru ya gaji mahaifinsa ya hau ƙaragan mulkin Daura bayan matarsa Gimbiya Shahida ya sake auran mata uku ya cike kofa a halin yanzu mata huɗu gare shi, ita kuma Fatima tana wajen Baffa tana rayuwa cikin kunci da baƙin ciki, dalilin Fatima domin ta samu kwanciyar hankali ya so da a ce shi mai kuɗi ne da zai yi nesa da garin Yola na har abada saboda Fatima ta samu kwanciyar hankali amma duk da haka sai da suka bar Yola suka koma cikin Jimeta da zama, kuma dawowar Fatima gida bai sa ya je Mubi ya faɗa musu abin da ya faru ba daga can ne Midibbo ya sanar da su ga abin da ya faru Baffa Hamza ya dawo yana wallahi tallahi, duk dai bayan an gama jajantawa ba wanda ya sake bi ta kan Fatima ballanta halin data ke ciki.

Fatima ba ta mgana sai kuka sai damuwa ba ta cin abinci sai Baffa ya zaunar da ita yana ba ta baki da lallashi da nasiha kamar ta ji amma da ya bar wajen sai ta koma gidan Jiya. Muhammad Lamiɗo  da Baffa ya yi ma shaƙika da huɗuba wajen ma bashi Nono ma sai Baffan ya tsaya mata ba domin Ammah ba sai dai Lamiɗo ya mutu ba mai kula da shi, itace ta haɗa shi da Kabiru a lokacin mutane da dama suna tunanin ko y'an biyu ta haifa tunda tsakanin su bai fi kwana arba'in ba. Ammah ta sha wahala sosai ga Fatima ita kanta kula da ita ake yi Aminiyarta Aisha ce auren ta ya mutu a can Mubi kuma ana ta magana sai Amma ta yi ma Baffa mgana ya ce ta taho ta zauna da su na wani lokaci, ko domin ta riƙa taimaka ma Amma da kula da su Lamido ga Fatima.

Ta zauna da su na tsawon shekara ɗaya a wajen su Ammah ta samu miji ta yi auren ta da Babansu Baɗɗo Malam Sani, mutumin Jada ne shima kasuwancin siyar da hatsi ne ya kawo sa Jimeta ba jimawa suka yi aure anan kuma cikin Jimeta suke zaune Amma ta fi kowa murna Aminiyarta ta dawo kusa da ita. Haihuwan ta na fari mace ta haifa mai suna iklima shi ne dalilin da ya sa ake kiran ta da Ummin ikki.
Fatima ta sha gwargwarmaya kafin ta dawo daidai. Daga lokacin ta tsani duk wani abu da ya shafi sarauta, ta tsani har garin Daura gabaɗaya. A daddafe ta yaye Lamiɗo ta sakar ma Ammah ita kuma da taimakon Baffa ta koma makaranta a zaman ta a gidan Baffa har deperession sai da ya kamata Allah ne ya taimake ta tana da sauran kwana a gaba, zuciya da takaicin abin da aka yi mata ya sa ta ji tana so ta tashi daga Fatima yar ƙauyen Mubi zuwa Fatima mai ilimi wacce za ta nemi ilimi domin gobenta ta yi kyau.

Daga SS1 ta fara karatu sannan tana zuwa lesson haka saboda taimakon kanta tunda daga sama ta faro karatun kamar ba za ta iya ba domin ta sha wahala kafin ta fara ganewa ko za ta sare sai ta ba ma kanta ƙwarin gwiwa ta cigaba. Ta zana jarabawa kuma ta ci sai ga ta da taimakon Baffa ta samu gurbi a Federal Collage of Education Yola Jimeta. Saboda ma ta yi karatun a cikin makaranta take zama sai bayan wata ɗaya take zuwa ganin su Baffa Lamiɗo ko tun da ta yaye shi ta sakar ma Ammah ta ce ta bar mata shi halak makal a matsayin ɗan ta. Shikenan ta koma kamar ba ita ta haife shi ba shi ma yadda ba ta ta kansa shima Ammah ya sani a matsayin uwa tun yana ƙarami. Fatima ta mayar da hankalinta a kan karatunta da taimakon Baffa.
Bayan ta gama NCE ba ta zauna ba ta nemi gurbi a jami'ar Maddibo Adama University, tun a lokacin tana Federal University of Tecnology.

Shima saboda nisa a garin Girai jami'ar take can take zama a hostel sai ta samu hutu take zuwa gida kuma tana karantar Biology ne. Fatima ta saka kanta da cewa za ta iya ta yi dakiya ta yi naci kuma Allah ya taimaketa ta cika burin ta.

****

SHEKARU TALATIN DA SUKA SHUƊE A BAYA.

Bayan shuɗewar wasu shekaru Talatin a baya Rayuwa ta daidaita. Tunda Baffa harkokinsa sun buɗe ya yi arziƙi da kasuwancin sa na siyan tsoffin ƙarafa yana siyarwa sannan shekaru goma a baya ya fara haɗawa da siyar da motoci tun haɗuwarsa da Alhaji Isa Ɗan marke bazamanfare mai siyar da motoci wanda ke da kamfani a garin Kaduna sun daɗe suna kasuwanci kuma dalilin shi Baffa ya samu alheri masu yawan gaske. Baffa ya gina katon gida a anguwan Zone 3 in da iyalansa ke zaune har yanzu.

Shima Alhaji Isa Ɗanmarke a dalilin Baffa ya samu matar aure. Ya auri Fatima tana da shekaru talatin da biyar mai kwalin karatun Degree da masters a lokacin. Matarsa ta rasu kuma ba su taɓa haihuwa ba yana ganin Fatima a gidan Baffa ya ce ya yi mata Baffan kuma ya bashi domin a lokacin shi ke da alhakin aurar da Fatima da duk itama tana da haƙƙi tun da ita bazawara ce. Fatima ta auri Alhaji Isa ta kuma tare a gidan shi dake Kaduna. Suna kuma yin auran ta ɗora karatun ta na PHD a jami'ar Amadu Bello dake Zaria wato ABU ZARIA.
Tana cikin kuma karatun ne ta samu ciki ta haifi yarta mace Islam(Fatima) bayan ita sai da ta gama karatu da shekaru biyar sannan ta haifi Faruk(Umar). Tun bayan barowan ta Daura ba ta sake komawa ba amma su mutanen Dauran sun neme ta daga baya saboda Lamiɗo.

Baffa kuma ya tara zuru'a sai son barka. Hamma Jibo ne babba wanda ya yi karatu har matakin Master mazaunin Abuja da iyalansa shekarunsa na haihuwa 40.
Sunan matarsa Nauwara da yaran su huɗu, Saudat, Jamila(Amma) sai yan biyu Hassan da Hussaini sai Isma'il.
Sai Hamma Mustapha shima ya yi karatun boko har matakin Degree yana garin Gombe tare da iyalansa yana aiki da hukumar ruwa(Water resourses) shekarunsa na haihuwa 38.
Sunan matarsa Aisha(Momi) ya'yansu uku Fatima(Mahma) Zainab sai Hadi(Baffa).
Sai Hamma Kabiru shima ya yi degree a kan medical lap, yana aiki da asibitin Federal hospital Jalingo. Shi kuma shi da Lamiɗo suna cikin shekaru na 35 ne.
Sunan matarsa Safinatu yaran su biyu, Muhammad da Yusra, kuma a can Jalingon yake zaune da iyalansa.
Sai Hamma Abdulrrahman lauya ne mai zaman kansa yana zaune  a garin Jimeta shekarunsa 33. Matarsa Ummu Sulaim da ya'yan shi biyu duka mata. Mariya da Jamila(Mimi) sai Hamma Abdullahi tare suke kasuwanci da Baffa shima ya yi karatun Boko ya karanta harkan kasuwanci shekarunsa 31 babu nisan haihuwa tsakanin a duka yaran Amma.
shima yana zaune da matarsa Suwaiba da ɗansa ɗaya Umar(Maddibo) sai Hamma Abdulrahim shi kuma yana can ƙasar singphore yana karatun likitan ci, ɗan kimanin shekaru 29.
Wanda Hamma Lamiɗo ya ɗauki nauyin karatun na shi.

Sai Hamma Saddam wanda ke karatun mass com a jami'ar ATBU BAUCHI yana aji uku, tsakanin Saddam da Auta Ummu wata ashirin ne.
Shi yana cikin shekaru na 27 ne. Sai Auta Ummu Salma wacce iyakar ta sakandiri ta tsaya aka yi mata aure.

Zuwa lokacin rayuwa duk ta yi kyau, a can Mubi ma Baffa Hamza ya rasu haka ma Umma(Asma'u) a gidan su Baffa yanzu Baffa Umaru ne Babba duka kuma a gidan su ke zaune da ƴa'ƴansu da iyalansu, su dai ba su bar Mubi ba suna nan a cikin ta amma dai Baffa da iyalan shi suna zuwa Mubi akai akai in an yi wani abu Amma ma tana da zuru'a a can tun da su Umma Balki sun tara iyalai masu yawa a can Mubi ɗin. A nan kuma ita da Ummin ikki ne suka tara iyalai, sai son barka Ummin ikki ta aurar da matan ta huɗu, iklima, Saratu, mai sunan Amma Jamila, sai Binta sannan kaltume da Baɗɗo(Aisha) su ne yanzu a gabanta ita Allah bai ba ta namiji ba amma Mallam Sani ya kara aure amaryan ta haifa masa maza uku. Amintansu da Ammah sai ma abin da ya yi gaba sai dai duk amintan dake tsakanin Ammah da Ummin ikki Baffa da Mallam Sani ba sa Aminta sosai amma suna da kyakyawan alaqa da juna sai dai ba kamar Aminta da shakuwa irin na matan su ba

Abin da Mami(Fatima) ba ta sani ba shi ne tun Lamiɗo na ƙarami Mahaifin shi Maimartaba Sarkin Daura Alhaji Dr Muhammad Nasiru na tura kudaɗe duk wata domin hidimarsa a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba sannan duk in da Baffa suke yana sakawa ana bibiyan su
Da shawaran ƙanwarsa mai bi masa Hajiya Zaliha(Magajiyar Sanda Mata) kuma ita ke auran Madakin masarautan Zazzau, tun faruwan lamarin ita ce kawai ta nuna rashin kyautawar Fulanin kan abin da aka yi ma Fatima. Amma sauran duk sun goyo bayan Fulani a wancan lokacin. Ita ce ta bashi shawaran ya nemi in da Fatima take domin gudan jinin dake tsakanin su, ya sani Fulani ba yadda za ta yi domin Ubangiji mai haɗawa ya riga ya haɗa danganta a tsakanin shi da Fatima ta sanadiyar Lamiɗo.

Tunda ga haihuwar Lamiɗo har girman shi da komai da komai Marmartaba yana da labarin komai sannan shi ya saka a ka samo masa lambar asusun bakin Baffa yana tura masa kuɗi, a saƙon da ya taɓa tura masa na farko ne ya yi bayanin kan shi sannan ya roƙi Baffa da cewa kar ya ce ba zai karɓi kuɗin ba, har abada ba zai taba karɓan Lamido daga hannun su ba, shi ko Baffa daman ko bai roƙe sa ba, ina shi ina ma yar ma da sarki kuɗi kuma ko ya ce zai karɓi Lamiɗo ai ba shi da ta cewa ba zai iya ja da masu mulki ba, shi ya daɗe da yafe komai da man sanadin Fatima ne, yanzu kuma Fatima ta samu komai na rayuwa kuma yawancin mutanen da suka yi ruwa da tsaki a kan auran ba sa raye. Hatta mariƙan Fatima na Daura sun rasu da daɗewa amma dai har yau akwai wasu daga cikin ahalin Gwaggo a garin Daura Baffa dai kan tura musu saƙo amma shima ba zuwa yake yi kamar yadda Fatima ta tsani garin haka shima ya ji ya fita kan shi gabaɗaya.

Mami ba ta san Maimartaba ke ɗauke da nauyin Lamido ba sai da ya tafi ƙasar Malesia karatu a lokacin Baffa ya sanar da ita komai saboda ta san ba shi da kuɗin da zai kai Lamiɗo waje domin ya yi karatu kuma kaf cikin yaran ba a kai kowa ba sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login