Showing 123001 words to 126000 words out of 147042 words

Chapter 42 - FARGAR JAJI Ƙarfin Boye By Janafty

Janafty   

31 Aug 2026

535

rana. Da man da yunwa ta dawo jikinta har rawa yake yi in ta na jin yunwa yanzu.
Sai da ta ci sannan ta ɗan kwanta saboda a gajiye take daga nan barci ya ɗauke ta.
Sai wajen biyu saura na rana ta iya tashi ta yi salla.
Haka kurum ta ke jin kasala jikinta ba daɗi zuciyanta tana ta tsinkewa sai ta ɗauko Qur'ani ta yi karatu, sannan ta ɗan samu salama Baffa ba ya nan sai Yamma ya dawo. Daga ita sai Ammah a gida kuma ba hira suke yi ba, kowa na ɗakin shi.

Misalin shidda na yammah tana cikin ɗaki ta ji maganar Hamma Abdullahi sai bayan ya bar gidan ne ta fito ta ga Ammah baki har kunne.

"Ammah Me ya faru ne?  Kamar muryan Hamma Abdullahi na ji yanzu?

Ta tambaya tana kallon Ammah.

"Baba ne ya zo yana faɗa mini Yayanki Lamido ya kira shi, da cewa ya je filin jirgi ya ɗauke shi yanzu nan."
Ummu ta yi shuru ba ta yi magana ba.

"Zuwa ba sanarwa, ai da ya yi magana da ko gidan na shi an je an ɗan share"

Ammah ta faɗa tana miƙewa.
"Amma dai nace Baba ya yi ma matarsa mgana ya ɗan kaita ta je ta ɗan gyara gidan kafin ya iso "
Ummu ta ɗan yi yaƙe ba ta yi magana ba.
Ammah ta kasa zaune ta kasa tsaye tana tunanin abin da za ta dafa masa.

"Ummu ko na yi masa tuwo ne? Kin san yana so"
"Kai kuma yamma ta yi gaskiya."
Ita kaɗai take ta maganganunta
Ummu Salma na jin ta ba ta ce mata komai ba shigowar Baffa ne ya katseta sai ta juya tana faɗa masa halin da ake ciki.

"Ba laifi ga Ummu nan ta ɗan yi masa abinci nan da take yi mana na yan gayu."
Ya faɗa yana kallonta, mamakin Baffa ya hana ta magana wannan ne zai ci abincinta.
Ta ma san Ammah za ta ce aa ga mamakinta sai Ammah ta juya tana ce mata ta ɗan sama masa wani abun.

"Za ki iya ko?
Ba ta da magana in ta ce ma ba za ta iya ba Ammah ce za ta ɗaga hankalinta.

"Zan iya Ammah."
Ta faɗa a fili amma a zuciyanta sai ƙunƙuni take yi tana faɗin sai kawai mutum ya zo ba sanarwa da man halin shi ne ya yi ta abu gaban kansa.

Haka nan ta shiga kitchen chinese rice ta ce za ta yi, Allah ya sa akwai cefanen kayan lambu shekaran jiya Hamma Abdulrahaman ya kawo, amma sai da ta dafa ganyen zoɓo sauran nata ne ma da aka dawo da shi ta fito da shi tana yi musu zoɓo lokaci bayan lokaçi. Girkin kaɗan ta yi tunda suna da sauran taliya da miyan da Ammah ta dafa shi da rana, gogan ne ba zai ci ba tunda shi na musamman ne.

Bayan mangariba ta gama aikinta tunda gas ne Ammah na da gas na tsaye mai uku da electric da shi ake amfani, shi ya sa aikin ya yi mata sauri zobon ta zuba a wani jug na tangaran ta saka a firiza, abincin kuma ta zuba a ƙololin Ammah sabbi ne ma a kwalin su da ta je bikin Autan Umma Salamatu ne ta zo da su ko Baffa ba a taɓa sanya masa abinci a ciki ba amma yau Ammah ta ce ta ɗauko a zuba ma Lamiɗo a ciki.

Ta gama komai ta jera saman faranti sauran kuma ta zuba ma Baffa a ranta tana faɗin ai nima sai ubana ya ci tunda Ammah ba ta kanshi take yi ba.

Har ta koma ɗaki ta yi alwala ta yi sallan Mangariba shuru ba Hamma Abdullahi ba ɗan Ammah, sai da Ammah ne da kanta ta leƙo tana ce mata ta kira mata Baba a waya ta ji ko lafiya ba su kariso ba ita wayarta kamar ba kati ta dai ki shiga.

Hakanan ta ɗau wayarta ta kira shi sai ga shi ta shiga ta ba ma Ammah suka yi magana.
Ashe Hamma Lamidon bayan an ɗauko shi daga filin jirgi gidan shi ya ce a wuce da shi zai yi wanka. Sannan ya ce ma Hamma Abdullshi ya koma gida in ya gama abin da yake yi zai tuƙo kansa zuwa gida.
Haka Ammah ta ke faɗa mata ita da Baffa da bai daɗe da dawowa daga masallaci ba.

Abincinsa Ummu ta kai masa ɗaki sai ya wuce can Ammah kuma ta bi bayan shi.
Ita kuma sai ta koma cikin ɗakinta da tsinin cikin ta a gaba wayarta na hannunta kamar an ce ta buɗe data sai ta ja sama ta kunna ba wasu saƙonni ne masu yawa take samu ba tunda sabuwar lamba ce ba kowa ya santa da lambar ba.

Sai dai saƙonnin da ta gani a group ɗin makarantar su ne ya ɗan ja hankalinta, kuma ta ga har tagging ɗinta an yi sai ta shiga.
Sai ta ga ana ta fatan alheri da Allah ya ba da zaman lafiya.

"Ga wacce za ta dinga amsa addu'o'in ku nan."

Madina ta faɗa bayan ta yi tagging ɗinta akan an ce ana ta fatan alheri amarya ta yi shuru ba ta amsa ba.
abin ya sake ɗaure mata kai ganin Shamsiya ake tagging ana mata fatan alheri kasa wasu hotuna ne guda uku jikinta har rawa yake yi wajen dannawa ta buɗe hotunan domin ta ji suna ta cewa Allah ya sanya alheri ya kuma kai mu lokacin
Zuciyanta ya ba ta cewa auren Shamsiya ya zo ba ta faɗa mata ba.

Sai dai me katin biki ne ya fara buɗewa da farko.
Ba ta ko tsaya duba sunan angon ba ta fara duba date ɗin bikin jibi ne ɗaurin auren. Mamaki ya sake kamata da al'ajabi kenan da gaske ne Shamsiya ta ja baya da ita sannan da gaske ne zargin da take yi a kanta cewa tunda yanzu ta zama bazawara ba ta bukatar ta.

Tana ta hawaye ita kaɗai tana zaune da waya a hannunta.
Jikinta ya fara karkawa ne lokacin da hoton ƙasa suka buɗe. Sai ta ga kamar ko idanuwanta ke yi mata gizo ba gaskiya ba ne. Har sake murza idanuwanta ta yi ta sake ƙura ma wayar idanuwanta cikin fitan hayyaci.

Zuciyanta ne ya tsaya da bugu na lokaci ɗaya.
Me take gani haka?
Shamsiya ce da Habib cikin shigar alfarma a cikin hotunan nan guda biyu.
Ɗaya ya kwanto ta bayanta ya haɗe hannayensu a saman cikinta. Dayan kuma tana zaune a kan kujera shi kuma ya tsaya a bayanta suna masu kallon juna suna mirmishi cikin yanayin da amarya da ango kan yi a lokacin yin hotunan pre-weeding pic, tamtama take yi kamar ba Habib ta gani a jikin hoton ba sai dai kuma ina shi ne domin ba za ta taɓa mantawa da kamaninsa ba har abada.
Habib ne mijin da Shamsiya za ta aura?

"Kai gaskiya sun dace."
Ta ga saƙon wata Hamdiya"

Kar dai a ce Shamsiya Habib za ta aura tunanin da take yi kenan zuciyanta na sake tsinkewa.
Ko ba ta san Habib ba ne? Ko ba ta san Habib shi ne mijin da ta aura ba? To ai in mijinta ne a da a yanzu ba mijinta ba ne sun rabu. Ba kuma za ta ce Habib bai san Shamsiya ƙawarta ba ce, ba kuma za ta ce Shamsiya ba ta san Habib ba.

Dukkansu sun san juna, kuma shi ne za su yi aure! Da man shi ne mijin da ta samu lokaci kaɗan? Ko da man shi ne dalilin da ya sa ta ja baya da ita. Ta sani ta san Habib ne za ta aura ta sani kuwa.
Zuciyan Ummu ya daina aiki kwata-kwata kanta na sarawa ta ma rasa tunanin da za ta yi, wayar na hannunta addu'oin fatan alheri ke ta shigowa ga Shamsiya da mijinta Habib, tun tana tunanin mafarki take yi har ta gasgata a zahiri ne yake faruwa. Ta kashe wayarta yafi sau uku tana sake kunnawa amma still in ta sake shiga hotunan take gani hoton Habib da Shamsiya a cikin yanayin farinciki.

Ta kasa zama ta kai gauro ta kai mari a cikin ɗakinta. Tana jin har abin da ke cikinta yana juyawa tsabar halin datake ciki.

"A'a Bestie ba za ta auri Habib ba."

"Ba za ta aure shi ba."

Take faɗa tana kallon hotunan lokaci ɗaya tana faman girgiza kai. An ce kuka ma Rahama ne ta kasa kuka amma a kasan zuciyanta take jin wani irin zafi zafin da ba ta taɓa jin irin shi ba har ya ninka irin zafin da ta ji lokacin da Habib ya sake ta. Ta kasa gasgata gaskiyan abin da ta gani, in har auren ne da gaske to watakila Shamsiya ba ta san Habib ba ko shi ne bai gane Shamsiya kawarta ba ce, ga shi dai zuciyanta na cigaba da hasko mata hotunan su a lokutan da Shamsiya da Habib suka sha haɗuwa tun kafin aurenta da shi har ma bayan auren amma wani shashi na zuciyanta faɗa mata yake kila dai kuskuren fahimta ne ba abin da idanuwanta ke ganin mata ba ne.

Saboda ma ta samu tabbacin abin da ta gani sai ta sake duba katin bikin ga sunan Habib Idris Mai imani nan raɗau a jikin katin tare da na Shamsiya.

"Aa No.."

"Ba gsskiya ba ne."

Ta faɗa kamar mahaukaciya. Ba ta yarda ba zuciyanta ba ta aminta da abin da ta gani ba tana bukatar wani ya yi mata karin bayani
Jikinta da hannunta na rawa ta lalubo lambar Shamsiya ta kira ta amma kira sama da sau goma ba ta ɗaga kiran ta ba, in wayar na ringing tafiya yake yi da bugun numfashin Ummu Salma tsabar tashin hankalin data ke ciki.

Ganin da ta yi tana ɓata lokaci a daran nan a wannan lokacin take son karin bayani take kuma son sanin gaskiyan komai tun kafin zullumi da fargaba su saka zuciyanta bugawa. Wani dogon hijabin da take salla ta raruma ta saka a saman bakar doguwar rigar jikinta.
Har ta fito falo sai ta tuna ba ta ɗauki kudi ba sai ta koma da gudu ta yayo mu ƙaramar jakarta dake saman madubin dakin, tunda ta dawo daga asibiti ta ajiyeta a wajen wayarta na hannunta ta fito, takalmin Ammah dake kofar ɗaki wani na roba na zirga-zirgan tsakar gida ta zura ta fice daga gidan ba tare da tunanin komai ba, tana jiyo hiran Ammah da Baffa a turakansa amma ko waiwayowa ba ta yi ba, a lokacin hankalinta ya bar  gangan jikinta. So kawai take yi ta buɗe idanuwanta a cikin na Shamsiya ta nuna mata hotunan da ta gani ta ji shin abin da ta gani gaskiya ne ko ƙarya ne?

Ba ta ko ganin gabanta kafin ta isa titi ba ta san adadin sau nawa ta ci tuntuɓe ba, amma ba ta damu ba Kekenapep ta tsayar ta shiga ta ce ya kai ta barraks road suna tafe amma ji take yi kamar ta yi tsuntsuwa ba ta taɓa ganin nisan gidan su Shamsiya ba sai a ranar suna isa tun daga kofar gidan ta san ana sha'ani domin get ɗin gidan ma yana buɗe ne ga motoci nan birjit a haraban gidan wasu har waje, ba ta damu da kowa ba, ita dai ta san ta fiddo kuɗi da ba ta san ko nawa ba ne ta mika mai nepep ɗin daga nan sai kawai ta tsinci kanta a falon gidan su Shamsiya akwai mata ga sunan da yawa amma idanuwanta ba su tsaya tantance fuskokinsu ba. Waige-waige kawai take yi ba wacce idanuwanta ke son gani irin Shamsiya.

"Wa nake gani kamar Ummu Salma."

Ta ji an faɗa daga bayanta tana juyowa sai ta ci karo da Anty marikiyar Shamsiya.
Mirmishin dole ta yi mata wanda ya tsaya iya saman fuskarta.

"Ni ce ina yini Anty"

Ummu ta faɗa tana sauke numfashi.

"Lafiya lau sannu Ummu Salma."

Ta faɗa tana kallonta daga sama har ƙasa.

"Ai na yi ta cewa Shamsiya za ta rako ni gidanku na yi ma Umman ki jajen abin da ya faru ban samu dama ba."
Ummu ta sunkyar da kai, amma tana ta kalle kalle domin hango ta in da za ta ga Shamsiya.

"Allah ya kyauta na gaba. Allah ya zaɓa mafi alheri."
Ko amsata Ummu ba ta yi ba domin ba ta ita take yi ba.

"Kin samun kin rarafo kenan? Da man da na ga ban ganki ba Shamsiya ta ce ai kin yi nauyi."

Da gaske kenan Shamsiya za ta yi aure, amma dai da tabbacin Habib za ta aura ne ba ta sani ba kuma shi ta zo ta sani daga bakin ita Shamsiyar.

"Shiga ciki tana cikin ɗakinta ba ta ma daɗe da dawowa daga wajen gyaran kai ba"
Ko kafin Anty ta gama magana Ummu ta wuce ta zuwa cikin ɗakin Shamsiyar da dama ta san ɗakin.

Kofar ma tana buɗe suna ta hayaniya ta san ta shiga cikin ɗakin kuma ta ga harda yayyen Shamsiyar a ciki amma wacce idanuwanta ke son gani ta nema sai ko suka haɗa ido tana zaune gefen gado ta buɗe kanta yan'uwanta na duba gyaran kan da aka yi mata.

"Kai Ummu kin rarrafo kin zo?

Badawiyya yayar Shamsiya ta faɗa bayan duk hankula ya dawo kanta.
Ita dai kawai tana yaƙe ne amma hankalinta da natsuwarta na kan Shamsiya.

Wato ta ce ba za ta samu zuwa ba ne saboda ta yi nauyi to ai ba ta yi ƙarya ba tabbas ta yi nauyi tunda ga nauyi nan a gabanta tana fama da shi.

"Bestie sannu da zuwa."

Shamsiya ta fada bayan ta taso zuwa gare ta har tana riƙo hannunta.
Ta kuma ja ta har gefen gado ta zaunar da ita, ita kuma kamar gaula ta zauna.
Suna ta yi mata sannu ta kasa amsawa kawai Shamsiya take kallo ko a jikinta sai jikinta ya bata wata kila ba gaskiya ba ne Shamsiya za ta yi aure amma ba Habib ne mijin da za ta aura ba.

"To mu je ko mu bar Bestie ta gana da Bestien ta."

Badawiyyya ta faɗa tana tattara sauran yan matan dake ɗakin, wasu ta san su yan'uwan su Shamsiya ne wasu kuma ba ta ma tsaya iya gane su ba. Tunda in dai na kusa da Shamsiya ne ta san su kamar yadda itama ta san duk wani da ya shafe ta. Kamar yadda Shamsiya take zuwa gidansu itama haka take zuwa nan gidan wajen Shamsiya tun ma kafin ta yi aure.

Dukkansu suka fita sannan suka rufe ƙofar, suna fita Shamsiya ta kalle ta, tunda daman ita Ummu tunda ta shigo take kallon ta.
Mirmishi ta yi mata irin mai ƙayatarwa nan kafin ta ce" Tunda na ganki na san cewa zuwa yanzu kin ji komai ko kin ga komai."

Ta faɗa tana mai yi ma Ummu wani kallo.
Cikin wani yanayi Ummu ta ce" Na ji mana, na ji za ki yi aure amma ba ki faɗa mini jibi ne bikin ki ba."
Ta faɗa kafin ta ɗan ja fasali.

"In ba ki so na zo bikin ki Bestie ba sai kin ɓoye mini ba nima a wannan halin ba zan zo ba ballatana har na na ɓata miki bikin ki."
Ta faɗa cikin rawan murya, tunani kawai take yi ba gaskiya ba ne , ko dai ita ce ba ta gani daidai ba ko kuma an samu wani kuskuren.

Shamsiya ta sake kallonta kafin ta kwashe da dariya.
Ummu ta yi jagale tana kallonta ganin tana yi mata dariya

"Wai akan me kike magana?
Ta faɗa lokaci ɗaya tana mikewa..
"Kin ce ma su Anty na yi nauyi shi ya sa ba zan samu zuwa bikin ki ba, alhalin ni ba ki faɗa mini ranar bikin ba."
Shamsiya ta sake kwashewa da dariya tana nuna Ummu kafin ta ce" Wai da man ba abin da nake tunani ya kawo ki ba?

"Me kike nufi?

Ummu Salma ta tambaya cikin shan jikin jikinta.

"Ba ki san abin da na ke magana akai ba?
Ko dai kin sani kin zo ki tabbatarwa ne kina yi mini alaye"
Ta faɗa tana mai kallonta cikin kurullah.
"Me me kenan?
Ummu Salma ta tambaya har bakinta na harɗewa.
Shamsiya ta dauko wayarta a gaban madubi ta yi danne danne ta miƙa ma Ummu wacce ta yi tsai tana kallonta.

"Karɓi ki duba."

Hannunta na rawa ta karɓa. Tana dubawa, sai gata ta sake ƙamewa a zaune.
Ba sabo ba ne a idanuwanta hotunan nan ne dai da ta gani ɗazu ta kasa gasgatawa.

"Ki yi ta yin gaba, hotuna ne ne ni da mijina in sha Allahu"
Hannun Ummu na rawa zuciyanta na bugawa, haka ta rika wucewa tana kallon hotuna kala kala sama da kala goma ba ta ko gama gani ba ta ɗago idanuwanta cikin wani yanayi tana kallon Shamsiya.

"Da ma. Da ma da gaske ne?

Ta faɗa cikin rawan baki da na zuciya.

"To da kin ɗauka karya ne?
Shamsiya ta faɗa tana ɗan dariya.

"Habib ne fa! Ko ba ki gane shi ba ne?

"Habib ne, na gane shi Sweety ba."

Shamsiya ta katseta cikin ba ta tabbaci.
Ummu ta kasa magana bakinta na rawa, tare da jikinta Shamsiya kuma ta ɗaure fuska tana kallon Ummu kallon kasƙanci.
"Ga shaida nan na nuna miki. Jibi uwar haka ina gidan Habib a matsayin matarsa in sha Allahu."
Ta sake faɗa tana sakin wani mirmishi.

"Habib fa! Habib miji."

"Kul ɗinki. Kar ki sake kiran shi da mijin ki domin Habib ba na ki ba ne nawa ne. Ummu Salma."
Ta faɗa tana taso mata a fusace
Kafafun Ummu har gara suka yi saboda jin abin da ba ta taɓa tsammani ba.

"Ban karya ta cewa ke kika fara sanin Habib kafin ni ba, amma zan baki tabbacin ni na baki aron shi har kika aure shi kika kuma yi zaman aure da shi."
Ta dawo gaban Ummu Salma ta tsaya sannan ta nuna cikin jikinta da yatsunta guda ɗaya.

"Ni ce har na baki damar da kike da wannan cikin a jikin ki. In da na so da baki aure Habib ba, in da na so da yau ba ki rigani ɗaukan cikin shi ba"

Ummu ji take yi kamar mafarki amma da ta runtse ido sai ta sake ganin ta a gidan su Shamsiya kuma ga ta a gabanta tana faɗa mata wasu maganganu waɗanda ta kasa yarda da su.

"Ke Habib ya fara gani yana so, ranar da kika nuna mishi a matsayin saurayin ki na ji dama ace shi ɗin nawa ne, bani na fara kai kaina ga Habib ba shi ya kawo kansa gare ni da cewa sai da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login