Showing 90001 words to 93000 words out of 147042 words
suka zo da Hamma Jibo amma shi kaɗai ya zo bai zo da su Nauwara ba, jirgi ya biyo ma. Suma dai duk haƙuri da nasihan suka yi ta Ummu Salma ganin yadda duk ta faɗe ta rame ba ta mgana. Daman a wannan lokacin kowa haƙuri yake ba ta, domin babu wani abu da za a yi mata.
Zuwan su Hamma Jibo aka yi maganar kwaso kaya. Mami da Ummin ikki ne suka je gidan tun da key ɗin gidan da man su Baɗɗo sun taho da shi kaf aka haɗa kayan ta waje ɗaya babban mota mai budaɗɗen baya ta zo ta kwashe zuwa gida a ɗakin kusa da na Ammah mai ciki da falo aka saka kayan aka rufe, kayan abincin da Hamma Jibo ya siya mata jibgi haka aka kwaso su sai dai aka kai su store ɗin Baffa.
key ɗin kuma suka ba ma maigadi sallahu in megidan ya zo ya bashi ko masu duba gidan tun da suna zuwa duk sati kayan Habibu ko ɗaya ba su samu a gidan ba tun washegarin ranar da ya yi sakin kafin ya tafi sai da ya kwashe duk abu da yasan na shi ne daman iya kayan sawa ne da takalma sai takardunsa duk ya kwashe su.
Ranar da aka kwaso kayan kwana Ummu ta yi tana kuka. Ba kuma wanda ya hana ta Mami ta ce a ƙyaleta ta yi kukanta ko za ta samu suƙuni kar baƙincikin ya ƙume mata a zuciya ta samu matsala. Tunani take yi shike nan komai ya ƙare tunda gashi an kwaso kayan ta, shike nan ta rasa komai ba ta da wani abu kuma da ya yi mata saura. Cikin dake jikinta ne kawai ya rage mata shi kaɗai ne abin da ya rage ta ƙarisa a halin yanzu.
Habib ya cuce ta, Habib ya gama da rayuwanta.
Habib ya yi ma duniyarta kaca-kaca, Habib ya yi sanadiyar da labarinta ya shiga bakin mutane ya mayar da ita bazawara ya sanya kanta a cikin mata masu taɓo a zukatan su, ya jijjiga duniyanta sannan ya bar ta da abin tunawa har na tsawon rayuwarta na har abada.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t
*14*
Sai da Mami ta shafe sati ɗaya a garin Jimeta kafin ta koma Kaduna. Kuma zaman ta ya yi amfani tunda Ummu na jin maganarta sannan tana sauraranta, zamanta a gidan kafin ta tafi ya taimaka ƙwarai wajen sake dangana a zuciyar Ummu Salma, tana cin abinci tana kuma samun hutu sannan koke-koken da take yi ya ɗan ragu sai dai abin da ba'a rasa ba.
Mami ta so Baffa ya amince ta tafi da Ummu Salma Kaduna wajenta ta zauna na wani lokaci saboda yanzu garin Adamawa gabaɗaya ya yi mata ƙunci in ta yi nesa za ta fi samun sukuni da jin daɗi lokacin Hamma Jibo na nan shi bai koma ba ya yi na'am da shawaran Mami har Ammah ma ta ce gwara ta ɗauketa su tafi na ɗan lokaci har zuwa komai ya lafa, shi kan shi Baffa ya fahimce su amma sai ya yi tunani a matsayin shi na Babba, bai ba ta Ummu ta tafi da ita da farko ba amma ba wai ya hana ta ba ne.
"Fatima Auta fa ƴ'arki ce, ni ko Amman ku ba mu isa mu hana ki tafiya da ita ba. Sai dai ya kamata mu yi abin hankali, ke fa matar aure ce kina da miji da kike zaune a ƙarkashin ikon sa, bai kamata ba tare da sanin shi ko izinin shi ba kawai ya ga kin zo da yarinya ba. Ya kamata ki yi shawara da shi in ya amince ki zo ga Auta nan halak malak Fatima ba wanda ya isa ya yi miki iko da ita."
Abin da Baffa ya faɗa mata kenan ana gobe za ta koma da ta same shi da maganar son tafiya da Ummu Salma gidanta dake Kaduna.
"Baffa ka fa san Abban Islam ba shi da wata damuwa. Mun yi ma magana da shi a waya shi ya ma kawo wannan shawaran na cewa ko zan taho da ita ne ta ɗan samu natsuwa? Shi fa ko har abada za ta zauna damu ba shi da wata damuwa."
Mami ta amsa ma Baffa cikin magiyan ya amince ta tafi da Ummu amma ya hana ta, ba da niyyar ba ta da hurumi ba sai da niyyar ta bi komai a hankali da cewa ta koma su tattauna da mijinta in ya amince daga baya sai ta zo ta tafi da Ummu sun ba ta ita har abada.
Dole Mami ta amince amma ba haka taso ba, ita ma ta ce ba domin wajen aiki ba, da sai ta yi wata a garin Jimeta amma saboda aiki ya sa ta yi shirin komawa. Kafin tafiyarta haka ta zaunar da Ummu ta sanar da ita za ta koma Kaduna amma ba daɗewa za ta dawo ta tafi da ita can ta zauna tare da ita.
"Mami me ya sa ba yanzu ba?
Ummu ta faɗa cikin raunin murya har ta fara hawaye. Za ta fi son Mami ta tafi da ita, domin garin nan da mutanen cikin ta sun gama fita da zuciyarta, wani ƙunci take ji da duhu daga cikin zuciyarta watakila da za ta yi nesa da gida da garin gabaɗaya za ta fara mantawa da kaddaranta har ta manta da Habib daga zuciyarta gabaɗaya.
"Ni ma haka na so, to amma kin san halin Baffa ya matsa sai na koma gida na yi magana da Abban Islam."
Ummu tana ta kuka har da shessheƙa, Mami ta yi ta lallashinta da ban baki, ba ta so Mami ta tafi tana son zama da ita domin ita ce kawai ta fahimci halin data ke ciki, ita ce kaɗai ta san irin raɗaɗi da zafin da kaddaran take da shi, ita ce kuma ta san irin yanayin da ake shiga in ka rasa dukkan wata dama ko mafitar daka ke tunanin ka kama ko ka dafe tuntuni amma sai daga baya ba ka shirya ba, ba zato ba tsammani komai ya kubce daga hannun ka.
"Ki yi haƙuri Daughter in sha Allahu zan dawo na tafi dake. I promise you in sha Allahu."
Da haka ta samu ta lallasheta ta daina kuka. Sannan ta bi ta da kalamai masu sanyaya zuciya da alkawarin ko bayan ta tafi ba za ta cigaba da damuwa ko kuka ba, sannan ta riƙa cin abinci saboda lafiyanta da inganta abin da ke cikinta kuma ta yi mata alƙawarin duk za ta ji maganarta. Sannan ta umarce ta da duk abin da take so kar ta yi ma Baffa ko Ammah magana ta kirata ta sanar da ita, ita kuma ta yi mata alƙawarin komai take so in dai bai fi karfinta ba za ta yi mata.
Ranar Jumma'a da misalin ƙarfe goma na safe jirgin da Mami ta shiga ya ɗaga zuwa Kaduna. Abdullahi ne ma ya tuƙa ta zuwa filin jirgin, bayan tafiyarta Ummu ta yi ta kuka ba wanda ya hana ta kowa ya san akwai shaƙuwa mai tsanani tsakaninta da Mami, balle itama Mamin lokacin da za su yi sallama har tana sharan ƙwalla kamar kar ta tafi haka take ji.
Bayan tafiyar Mami kamar Ummu ta saduda sai kuma ta koma gidan jiya, ita kenan sai kwanciya tana kuka ba ta cin abinci sai Ammah ta shigo ta yi magana ta tsakura kaɗan, ko Baffa in ya tsaya mata ko kuma ta ji zuwan Hamma Abdulrrahman, ga ta da juna biyu amma ba ta taɓa cewa yau ga abin da take sha'awa ba ko Ammah ta tambayeta ba ta magana sai ta ce komai aka ba ta za ta ci, ita a ganinta ba ta da wani sauran zaɓi kuma a rayuwarta tunda Habib ya sake ta kamar tara sa dukkan wata damarta ne.
Koda Baɗɗo ta koma gida saboda makaranta tana yawan leƙewa duba Ummu Salma, wata rana ma in ta yi dare nan take kwana da safe ta wuce makarantan daga nan haka ma Ummin ikki koda yaushe tana kan hanyar zuwa domin duba Ummu, kuma in dai ta zo sai ta zaunar da ita tana yi mata nasihan haƙuri da ɗaukan kaddara zuwa lokacin tuni Ummu Salma ta yarda da kaddaran Habib ya sake ta amma ta kasa gasgasta kaddaran cewa ya rabu da ita har abada, gani take yi zai zo gare ta ko da take gida zai dawo gare ta, ta kasa ba ma zuciyarta hakuri da fahimtar cewa Habib ya yi mata nisa har lokacin ba ta sare ba, saboda tana son shi duk abubuwan nan da suka faru ba ta jin haushin shi sai ma soyayarsa dake sake kassara tunaninta kuma ko yanzu ya dawo gare ta, za ta iya yin komai domin itama ta koma gare shi. Habib kaɗai ta sani shi ne fa Duniyarta ya za a yi ta fara yin wata sabuwar rayuwar da ba shi a cikin ta. Gaskiyan da Ummu Salma ta kasa karɓa kenan gani take yi ba ta da wani sauran jin daɗi kuma tunda dai ba tare da Habib, ta lamkaya jin daɗin ta da samun komai na duniya a lokacin da take Matar Habib ba a yanzu da ta ƙare ba ta da komai ba.
Tafiyar Mami da kwana goma sai ga Shamsiya afufujan tana kuka wiwi tana faɗin ita ba ta san abin da ke faruwa ba kenan ta yi tafiya zuwa Taraba gidan Sister ɗin ta, tun a can take faman kiran wayar Ummu a kashe kuma ba ta ganin ta a chart hankalinta ya tashi shi ne fa ta kira Baɗɗo ita ke faɗa mata wannan mugun labarin mara daɗi.
"Bestie Habib ya sake ni."
Ummu ta faɗa hawaye suna kece mata.
"Ya sake ni Bestie."
Ta sake faɗa tana mai kwantar da kanta saman cinyar Shamsiya dake zaune a saman gadon ɗakin da Ummu Salma take.
"Na yi komai domin na tsira da aurena amma na kasa Bestie. Na kasa na faɗi.."
Take faɗa tana wani irin gunjin kuka Shamsiya na ɗan bubbuga bayanta alamun lallashi take faɗin" Sai da na ce ki bi umarninsa Bestie amma kika yi taurin kai, da a ce kin zubar da cikin da yanzu kina gidan mijin ki, da yanzu ba ki zauna kina kukan nadama da dana sani ba."
Take faɗa tana sharan kwalla itama, amma ba ta fasa faɗa ma Ummu ita ce ke da laifi ba, ita ba ta ganin laifin Habib a wannan maganar.
"Bestie su fa iyayenmu tunanin su da namu ba ɗaya ba ne. Ban so ki kawo maganar gida ba, da kawai kin bi umarninsa kin zubar da cikin da yau duk ba a yi haka ba. Da kina can gidan mijin ki ba wanda ya san abin da ya faru."
"Besite ko na zubar da cikin nan ko ban zubar ba Habib ya gama samun duk abin da yake so a wajena. Ba zai ɗaga mini kafa ba sai ya sake ni, da man kawai cikin ya zo a gabar da ya fake da dalilin shi ne, amma ba ya so na ya ma faɗa mini da bakin shi."
Ummu ta faɗa tana cigaba da kukanta.
"Ni fa ban yarda Habib ba ya son ki ba Bestie kawai kin ɓata masa rai ne da kuma shigowar su Baffa cikin maganar, amma ke kanki kin san cewa Habib na son ki Bestie."
Shuru kawai Ummu ta yi mata, ba za ta gane ba ne, amma tunda har ita ta furta mata cewa Habib ba ya sonta to ai ya kamata ta yarda da ita. Itama da fari ba ta gasgasta ba amma daga baya da abubuwa suka yi ta faruwa dole ta aminta ta kuma gasgasta cewa Habib ba ya sonta , sannan saboda jikinta ya aureta kuma tun da ya gama biyan bukatar shi ai ba ta da wani amfani a wajen shi kamar yadda ta faɗa.
"Shima ya yi kuskure me ya sa ya yi saki uku? Ai da ya yi ɗaya ne in iyaye suka shiga ciki sai a gyara lamarin. Ni fa har kiran shi na yi ta yi bai amsa kirana ba daga karshe ma kamar ya rufe ni ne kwata-kwata bana samun shi."
Ta faɗa tana kallon Ummu Salma wacce ta miƙe daga kwancen da take, tana kallon Shamsiya da mamakin maganganun ta.
Ta buɗe baki za ta yi magana kenan Shamsiya ta katse ta.
"Ban ji dadin faruwan wannan lamarin ba Bestie. Na yi miki kaico domin da wahala ki samu kamar Habib. Ba ma tamtama ba za ki taɓa samun kamar sa ba har Abada Ummu Salma."
"Za ta samu, za ta samu wanda ya fi shi komai da komai in sha Allahu."
Suka ji magana a bayansu, suna juyawa gabaɗayansu suka ga Ammah ta shigo da kulan abinci ba da niyyar laɓe ba ne, amma ta daɗe tsaye a kofar ɗakin tana jin irin maganganun da Shamsiyan ke faɗi.
"Ammah."
Shamsiyan ta faɗa lokaci ɗaya tana saukowa daga saman gadon. Kulan abincin hannun Ammah ta amsa tana faɗin" Sannu da aiki Ammah."
Ta sakar mata lokaci ɗaya tana cewa" Yauwa."
Sai kuma ta kalli Shamsiya da take sauke kulan a saman side drower ɗin gadon tana mai ɗagowa, Ummu Salma ta kalla ita kuma tana ta kuka har da sauti.
"Shamsiya."
Ammah ta kira sunanta sai ta ɗago tana amswa cikin ladabi.
"Don Allah ki daina tuna ma Auta da wani Habibu. Ba shi da wata amfani yanzu a sabuwar rayuwarta. A matsayin ki na ƙawarta ki lallasheta ne ba wai ki zaunar da ita kina nuna mata kamar ta ci baya ba. Habibu da man bai cancanta da zamowa abokin rayuwar Auta ba, kaddara ce ta aura mata shi kuma yanzu ta raba su. Ina mai baki tabbacin shi ne ya yi asara shi ne kuma har abada ba zai taɓa samun madadin ta ba, amma a gare ta za ta samu ire-iren su masu tarin yawan da sai ta zaɓa ma, kuma ni na faɗa miki Ummu Salma za ta sake yin farinciki fiye da irin farincikin da ta yi a farkon rayuwarta da Habibu."
Ammah ta gama faɗa tana mai kallon Shamsiya, ta ma ɗan kausasa maganganunta, amma har cewar da ta yi da Ummu Salma ta bi umarninsa ta zubar da ciki duk ta ji, kamar a mganganunta ita ba laifin Habibu take gani ba, laifin Ummu ne ita da su iyayenta. Ai ko ba ta san Ummu bai kamata ta faɗi haka ba, ballanta Ummun ce silan da ya sa ta ma san Habibun gabaɗaya.
"Haka ne, in sha Alkahu Ammah ba zan sake tayar mata da maganarsa ba."
Shamsiya ta faɗa kanta na ƙasa cikin jin nauyin Ammah.
"Yauwa na gode da kika fahimce ni, ga abinci nan bari na kawo muku farantai da ruwa."
Tana gama faɗin haka ta juya har za ta fita sai kuma ta sake juyowa tana kallon Shamsiya. Duk da suke ƙawance da Autar ta ba ta taɓa jin ba ta natsu da ita ba sai yau, haka kurum yau sai ta ji maganganunta sun bambamta da yanayinta.
"Maganar zubar da ciki kuma."
Sai ta dakata tana kallon Shamsiya da ta yi tsuru tsuru.
Ummu ma ta daina kuka tana kallon Ammah ta san halin ta ba ta ɗaukan wani reni ko sakarci ko waye kuwa sai ta faɗa masa gaskiya ita kanta ta ji maganganun Bestie yau sun ɗan yi tsauri amma ba ta ga laifinta ba yanayi ne da tsarin gidan da ta taso kowa abin da ya ga dama yake yi babu takura.
"Na jinjina ma Auta da ta yi wannan jarumtar. Har yau mu iyayenta ba ma cikin nadaman dawo mana gida da ta yi da ciki a jikinta. Tunda dai cikin kowa ya san uban shi to ai an gama magana. Da Ummu Salma ta tashi a ranar lahira cikin waɗanda Allah zai tuhuma da kashe rai gwara ta mutu wajen haihuwa a tashe ta a matsayin shahidiya."
Ammah na gama faɗin haka ta fice daga ɗakin ta bar Shamsiya da ajiyar zuciya.
"Kamar Ammah ba ta fahimce ni ba Bestie"
Ta faɗa lokaci ɗaya tana zama a gefen gadon tana kuma kallon Ummu Salma.
"Ki yi hakuri. Watakila ba ta fahimci maganarki ba ne"
Ummu ta faɗa cikin wani irin amon mai sauti mai cike da rauni.
Sai Shamsiya ta yi mirmishi kafin ta ce" Ba damuwa. Na san anan gaba za ta fahimci in da maganganuna suka dosa."
Ta faɗa tana sake kallon Ummu cikin mirmishin da ya kasa ɓacewa a saman fuskarta
Sai ga Ammah ta dawo ɗakin ɗauke da filet da cokula guda biyu sai ruwan gora guda biyu ta kawo ta ajiye tana faɗin Shamsiya ta sauko ta zuba musu.
"Sannan ki matsa ma ƙawar ta ki ta ci abinci."
"To Ammah."
Ta faɗa cikin ladabi, kuma ta yi abin da ta saka ta,ta matsa ma Ummu ta ci abinci taliya da miyar jajjage ne. Ummu ta ji daɗin taliyan nan saboda miyan na ta ƙamshin kayan kamshi ta kuma soyu sosai, ga cikin ta ya cika amma bakin ta bai daina son ci ba sai ta koma tana lasan miyan saboda ta yi mata daɗi a bakin ta.
"Bestie ki bar lasan miyan nan kar ki yi amai ko cikin ki ya lalace fa."
Shamsiya ta faɗa tana kallon Ummu Salma na ta lasan miya
"Bar ni na sha, na ji daɗinta ne sosai "
Jin haka yasa sai ta ƙyale ta, sai da ta shanye duka miyan da ta rage kuma Allah ya taimake ta, ba ta yi amai ba.
Shamsiya na gidan har yamma sai gabda kiran mangariba ta tafi lokacin Baffa ya dawo tun safe daman suka fita da Abdullahi har ɗaki Ummu ta kai Shamsiya ta duƙa ta gaishe shi.
"Lafiya lau Shamsiya, ya kwana biyu ya makaranta?
Ta amsa da lafiya lau mahaifinta ya tambaya Dr. Nura babban ma'aikaci ne a minitary of Education na Jahar Adamawa.
"Ashe kuma abin da ya faru da ƙawata kenan?
"Wallahi Kuwa Shamsiya "
Baffa ya ba ta amsa.
"Allah ya kyauta na gaba. Allah ya saka mata."
Baffa ya amsa da Amin yana faɗin" Ya za a yi da lamarin da Ubangiji ya hukunta kenan. Zai wuce in sha Allahu."
Da za ta tafi ya yi ta mata addu'an Allah ya kawo mata miji na gari mai albarka nagartattace. Domin duk wanda ya san Ummu Salma a dangi ya san