Showing 36001 words to 37626 words out of 37626 words

Chapter 13 - HALIN GIRMA By hafsat rano

29 May 2026

74

ciki, Mama na"

"zaune an sha lullubi da kayan alfarma suka shigo, ta bisu da kallo ta kasan Ido, mata ne hamshakai"

"wanda suka amsa sunan su mata, hutu da jin dadi ya kama jikin kowacce kai ba sai an fad'a maka ba. Rawar jiki jamaar Mama suka fara su a lallai an zo wajen su, dangin su Abba na gefe sun zama yan kallo, akwatunan aka dinga shigowa dasu Mama ta hadiye wani yawu me karfi, cikin al'ajabin uban kayan da ake ta shigo dasu, gaba daya ma sai ta bata lissafi suka dinga yi mata gizo, kamar ta tashi ta hau bubbudasu taji, wani farin ciki na ziyartar ta. Duk gaishe gaishen da ake tsakani bata wani fahimta saboda yadda ta tafi tunanin kalar hutu da gatan da Zeenat zata shiga, gashi alamu sun nuna dangin"

"mijin nata masu karamci ne, basu da nuna kyama ko wulakanci ko kadan."

"""Baki ne daga gidan sarki, mun kawo lefen dan mu, jikan Maimartaba sarki, sannan d'a ga sarkin"

"Adamawa Alhaji Ahmad Santuraki,Ina mahaifiyar amaryar tamu take?"""

"Mama tayi firgigit sanda taji wata cikin matan na tambaya, murmushi ta yi tana sake kama kanta ita a"

"dole akwai surkutar nan. Aunty Faty ce ta tashi tsam, ta isa gaban Maman ta mika mata akwatin hannun ta, dake dauke da hoton Moh da Iman da ita kanta Iman din idan ta gani zatayi mamakin yadda ya same shi, hoton yayi masifar kyau zaka rantse tare suka dauka, yana sanye cikin shigar babbar riga da rawani, yayi wani murmushi da zaka kalla ka sake kalla. Wani irin shock Mama taji lokacin da ta karbi akwatin a"

hannun ta hoton da yake jiki ya shiga cikin idon ta ya aikawa da kwakwalwarta sako a take.

"""Wannan itace kyauta ta farko ga yar mu Fatima, akwai sauran kyaututukan da bazasu kirgu ba, amma"

"dai ita wannan din ita ce zamu iya cewa ja gaba ga sauran."""

Kamar mutum mutumi haka Mama ta dinga kallon matar da take mata wani yare da sam kwakwalwarta

ta gaza dauka balle ta fassara mata abinda matar take cewa.

"""Wadannan kayan kad'an ne daga cikin abubuwan da muka tanadawar Fatima, in sha Allah ba zata taba"

dana sanin amincewa da dan mu Muhammad ba.

""" Dan sarki jikan sarki kuma sarkin gobe idan me dukka ya kaimu."""

"Wata mata tace daga gefe, duk suka amsa da in sha Allah."

"Guda aka saka a wajen, gudar da Mama taji kamar an saka allura ne ana chacchaka mata a tsakiyar"

"kanta, kokarin sakin box din hannun nata take, wata kanwar su Abba da take lura da ita tuntuni ta taso da sauri ta karbe tana ma yan uwan Maman kallon banza."

"""Masha ALLAH, lallai mun ga Halin Girma da karamci na wannan babban gida, mun kuma tabbatar da yar"

"mu ta shiga hannu na gari"""

"Ta fad'a bayan ta koma wajen zaman ta, ta kuma mikawa wata babba a dangin box din. Murmushi"

"matan sukayi dukka, sannan aunty Faty tace"

""" Sai a bude kayan ko?"""

"Da karfin guiwar su dangin Abba suka tashi, aka fara bud'e box din farkon nan, kowa ya shiga mamaki,"

"mukullaye ne wajen guda uku na mota, sai mukullin gida da takardun su, sai kuma wani babban set of gold masu girman gaske. Wata irin guda da tafi ta dazu aka sake saki, jira ya soma dibar Mama, ta kasa gane komai sai hajijiya da take ji kamar zata kayar da ita daga zaunen da take, me yake faruwa? Me yake"

shirin faruwa.

"Daya bayan daya aka dinga bud'e kayan, tun mutane na irgawa har kowa ma ya gaji aka zuba ido ana"

"kallon tarin dukiya, dukiya me sunan dukiya, dangin Abba da Mama ta dinga dagawa kai sai suka zama kamar sune kawai a wajen, farin ciki suke dama kowa yaji haushin abinda Maman tayi a dan tsakanin gabatowar bikin, sai kuma yadda ta dinga yada habaici a ranar da za'a kawo kayan wanda suka tabbatar dasu take shiyasa suka ji haushin ta sosai, amma yanzu da haka ta faru sai suka hau murna suka dinga"

yin abu da gayya dan su kara haukata Maman.

"Tashi sukayi bayan an gama ganin kayan, aka damka duk wasu abubuwan da suke da muhimmanci"

"sosai kamar golds da takardun gida da keys a hannun kannen su Abba sannan suka yi musu sallama, abubuwn da aka shirya da sunan Zeenat suka je suka dauko aka saka musu a mota, basu ma so karba ba"

amma yadda suka dinga insisting yasaka suka karba dan kar suga kamar sun raina musu ne.

"Suna gama fita daga gidan masu kawo kayan Zeenat ta shigowa, mata ne kwantsam masu mugun yawa,"

"masu goyo ne, gasu nan harda wanda suka ciko bus suka zo. Ana kokarin daga Mama a maida ta cikin daki sanarwar zuwan su ya katse su, a sanyaye suka dawo suka zauna, suka shigo bayan an matsar da"

kayan Iman an tura wasu dakin Abba da dakin Maman.

"Da kallon bakin ciki Mama take bin su, kamar ta tashi ta hau bugun su haka taji, yaran da suka zo dasu"

"suka dinga ihu na goyen sai da aka sakko su, na hannu kuwa suka hau wasa a falon. Gaisawa akayi suka gabatar da kansu, kafin ma su dire sunan Zeenat din Mama ta ja numfashi da take jin kamar zai fice daga"

jikin ta.

"""Kuyi hakuri asthma ce da ita nema take Kuma ta tashi tun dazu, tashi Yaya mu shiga ciki ki huta."""

"Aunty Maimuna kanwar Maman tayi saurin rufawa ta janye Maman dan ta hango matsala babba, kamar"

"ma kokawa take da numfashiin ta. Suna shiga dakin ta kurma ihu, ihun da kowa ya ji shi, da tayi sauri ta saka hannu ta rufe mata baki"

"""Haba Yaya Hajara, ai sai aji kunya, dan Allah kiyi hakuri."""

"""Kutmar uban hakuri, kike ce min nayi hakuri? Bayan kinga abinda ya faru? Kinga yadda Ibrahim ya"

"munafurce ni da yan uwansa? Bayan duk halaccin da nayi musu ? Amma kike cewa nayi hakuri, ke kinsan me nake ji? Innalillah, wayyo Allah na."""

""" Ni dai kiyi hakuri, ko ma menene ki bari a gama taron nan, kinga mutane zasu tafi dake a baki."""

""" Taro? Ke kina ganin za'a cigaba da taron nan?"""

""" Toh me za'a yi Yaya?"""

""" Ba zai yiwu ba, wallahi sai dai a fasa auren, amma ba zan bari bakin ciki ya kashe ni ba a banza."" Sai ta"

"sake fashewa da kuka, kuka irin wiwi din nan da kana gani zaka tabbatar da ba karamin kuka mutum yake ba. Duk yadda Aunty Maimuna taso ta bata baki tayi hakuri ta kasa, sai kawai ta fito ta rufo mata kofar ta dawo wajen bakin, lokacin har an soma bud'e kayan, akwatu na guda hudu sai kit daya, da kayan ta masu kyau daidai da tsarin akwatunan, amma ganin da mutane sukayi wa kayan Iman ya saka zasu ga na Zeenat din kamar bola, a daddage kowa ya kalla, suka dauko dubu ashirin suka ce gashi nan ta kai"

dinki ba'a samu an dinka ba saboda kurewa lokaci. Daga haka sukayi musu sallama aka je dakin Mama a

"dauko ragowar kayan da suka rage ta ce idan an basu ko ruwa ba'a za'a basu ba, da k'yar Aunty"

Maimuna ta bata hakuri aka saka musu ruwa da lemo a bayan mota suka tafi.

Daya bayan daya yan uwan Abba suka zo suka kwashe kayan iman suka maida su bangaren Gaji a

cewar su kar bakin ciki da kishi ya saka Mama ta saka wuta ta kona su.

"Hauka hauka Maman ta soma da suka shigo, kowa yayi mata banza suka dinga dariya suna yada mata"

"da magana, suka kwashe komai suka yi tafiyar su. Jiki a sanyaye kawayen Mama suka dinga sulalewa suna guduwa kowa burin sa ya isa gida ya bada labarin abinda ya faru."

"Zeenat na wajen saloon suna ta waya da Bashir kiran Maman yake ta shigowa tana kin dagawa, da dai"

"taga kiran ya ishe ta sai tace ya bari ta daga wayar Maman, katse nasa kiran tayi ta daga na Maman."

"""Kina gidan uban wa wai?"""

"""Mama kinsan fa ina saloon."""

"""Toh ki bar komai kike ki taho gida, kizo yanzu ki same ni."""

"""Mama ban gama ba, kuma kinga zamu je mu siyo head din da zan saka da dinner da Bashir daga nan..."""

"""Bashir din yaci abu ta kaza uban sa, na rantse da Allah kika bari man da awa guda baki dawo gida ba, sai"

"kinga yadda zan miki"" tana kaiwa nan ta katse kiran, saroro Zeenat din tayi rik'e da wayar cike da mamakin Maman."

"""Me ya faru kuma?"" Ta Tambayi kanta cike da mamaki."

"Safa da Marwa Mama ta dinga yi a daki tana jiran Zeenat, ko sama da kasa zata hade ba zata yarda ayi"

"auren nan ba, tasan idan ita kanta Zeenat din tazo taga abinda ya faru zata ce ta fasa ne, shege matsiyaci dama munafurtar su yayi kenan."

""" Yaya Hajara da kin zauna kin nutsu, tashin hankali ba zai gyara komai ba."""

""" Ba zaki gane halin da nake ciki ba, ba zaki gane ba, ina cikin tashin hankali, bayan kunyar da nake ciki."""

"Ta fad'a tana cigaba da zagayen, idanun ta ya kada yayi jajur taci kuka ta godewa Allah. Jugum sukayi"

"kowa da abinda yake rayawa a ransa. A haka Zeenat ta shigo ta same su, Mama tayi kanta da sauri ta fizgo hannun ta da sauri."

""" Kika ce min talaka ne, kayan jikin sa ma a yayyage, daga gani bashi da komai."""

"""Waye? Wai Mama menene ya faru?"""

""" Ubanki, bake ce kika ce min wanda yazo neman auren Iman talaka bane?"""

""" Eh Mama, dan baki ganshi ba."""

Dundu Mama ta kai mata ta goce cikin bacin rai tace

""" Toh dan ubanki dan sarki ne."""

""" Sarki!!!"" Zeenat ta fad'a da karfi tana zaro ido"

*_ZAFAFA BIYAR 2022 _*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_1aHALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*

D aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*

09134848107

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login