Showing 21001 words to 24000 words out of 37626 words

Chapter 8 - HALIN GIRMA By hafsat rano

29 May 2026

73

dadi kafin gobe naje na ganta, dan yanzu ina da"

"license, na matsu na ganmu tare, muna yawo a garin nan cikin mota my hands in to her's, ga cool music na tashi Malam, wow love in the air."""

""" Toh Mr Romeo, Allah ya kaimu dai zamuyi kallo, yadda kake son ta Allah yasa tana maka ko rabin sa"

"ne."""

""" I don't care, as long as munyi aure, zan koya mata yadda zata so ni."""

""" We shall see."""

"***Ruwan zafi ne a katon bawo, Khalil na zaune a gaban ruwan hajiyar su na danna masa bayansa, gaba"

"daya jikin sa ciwo yake kafarsa kamar zata cire yake ji, babu irin tambayar da batayi masa akan me ya same shi ba amma yaki fad'a mata, haka Mama ta bugu tana fad'an tafiyar Khalil din hajiyar ta fad'a mata a yadda ya dawo, kuma yaki cewa komai. Yana jin su har suka gama ya tashi ya koma dakin sa ya kwanta yana tariyo abinda ya faru cikin tausayin kansa. Shi ya jawo yana takama da shegen bakin sa ya je ya kaishi ya baro, dama an fad'a mutum ya kiyayi harshen sa, akwai hadisi guda da akayi magana akan harshe da kiyayar sa, yaga izina a kansa, gashi bashi da damar fadawa wani abinda ya faru domin yasan shi za'a yi wa dariya, ko da muhammadu a iya soja ya tsaya matsayin da yake kai ya isa ya taka shi son ransa ba kuma wanda ya isa yace dan me? Balle ganowar da yayi waye Muhammad din, anan ya gane bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane, shi din ma ganganci ne da kuruciya. Eh toh kuruciya mana tunda dai yasan a girme Muhammad din zai girma shi dole ya fishi hankali da komai. Abu daya ne zai hana shi walwala, yadda zai yi da tarin soyayyar ta, gashi yayi masa kashedin ko a hanya babu shi babu ita, ya kuma tabbatar idan har ya kuskura yayi wani abu, za'a iya neman shi ma baki daya a rasa, dan masu"

"kudin nan yasan ba wani abu bane a wajen su su batar da mutum bat, har abada a daina jin labarin sa."

Tagumi ya rafka yana jin kamar yayi ta kurma ihu ko yaji sassaucin radadin da zuciyar sa ke masa. Allah

sarki Khalil

08184017082

"GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYANKU"

"09134848107[1/9, 8:38 AM] +234 803 765 3189: Halin Girma"

10

"*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*"

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos.

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

"***Be ji sallamar ta ba, sai ganin ta yayi kawai a dakin bayan a zahiri tayi sallamar amma saboda baki"

daya hankalin sa na ga tunani shiyasa be ji ba sam.

"""Ya Khalil wai a kawo maka abinci..."""

Ai kafin ta karasa ya daka mata uwar tsawa

"""Uban abincin, dallah Malama karki dame ni."""

"""Toh... Me yayi zafi? Hajiya ce ta aiko ni ai."""

"""Fitar min daga daki!"" Yace yana tasowa, da gudu ta juya tana dariya, sai da ta ga ta fice sannan ta daga"

murya tace

"""Bani na kar zomon ba..."""

"Ransa ne ya sake baci, ya bigi kofa yana komawa ya fad'a saman katifar sa yana jin kamar yayi ta cizon"

kansa.

A falo ta samu Hajiya ta zauna tana haki

"""Allah ya taimake ni na kusa cin duka, daga tambaya kawai ya hayayyako min Hajiya."""

"""Toh wai ko dai Khalil tsokana yayo ne aka tattaka shi, kinsan fa Khalil ba dai tsokana da cika baki ba."""

"""Alamu dai sun nuna Hajiya, fad'a ya takalo da yafi karfin sa wallahi, gashi nan yaki fad'an abinda ya"

"faru."""

"""Toh Allah ya kyauta "" Hajiyan tace tana tashi ta fita zuwa dakin nasa."

"***Tana tsaye a bayan kitchen dinsu, wanki ta gama tana ta sauri saboda kwana biyu bata maida hankali"

"zuwa islamiyya saboda abubuwan da suka sako kai, tana wankin tana tunanin maganar da sukayi da Abba da ta zama tamkar bitar karatu haka take yin sa, takun tafiya taji, ta juyo sai taga Abban a tsaye yana duban ta, da sauri ta dan russuna,"

"""Abba sannu da zuwa."""

"""Wanki ake ne?"""

"""Na'am.?"" Tace tana zaro ido sanin cewa ba da sanin sa take wankin ba, musamman ya samu almajiri"

"yake wanke musu kaya ita da Zeenat da Marwan yake biyan shi ta hannun Mama, duk da yasan dole zasuyi wanki irin kayan ciki da abubuwan da ba za'a iya bawa me wanki ba, amma kuma tarin kayan da ya gani a wajen da ya gane na Marwan ne sai wasu na Maman ya saka ransa mummunan baci, har a jiya"

sai da Maman ta karbi kudin wanki a wajen sa da zumar yau me wankin zaizo karbar kudin sa ya kuma

"bata babu musu. Yanayin sanyin garin zai yi wuya wajen wanki musamman da tun da dadewa yasan fatar Iman din bata son wahala idan tayi wanki hannun ta kanyi ja sosai, shi kuma Allah ya hore masa son yaya Kuma gasu ba wai yawa ne dasu ba shiyasa duk wani aikin wahala baya son siyi duk da ba wai kwata kwata ba zasuyi komai ba, amma kamar wanki yana ganin be kamata shima a saka shi a cikin aikin mata ba, mata na wahala da aikin gida kula da yara da girki wankin aka dauke musu zasu samu sassauci."

Matsowa yayi ya sake leka kayan kafin ya girgiza kansa ya juya bayan yace

"""Ki bar wankin nan kizo ki wuce ciki."""

Sakalo tayi a tsaye tsoro na kamata

"""Bakya ji ne?"" Ya daka mata tsawa, da sauri ta bi bayansa har cikin gidan, dakin su taga ya wuce ya"

kwankwasa sannan ya tsaya

"""Waye?"" Zeenat tace tana daga kwance cikin rufa, a yadda tayi maganar zaka gane knocking din ya"

"takura ta, sake kwankwasa wa yayi sannan ya tura kofar da sallama, be shiga ba, ya tsaya a kofar yana karewa dakin kallo, gadon zuwa katifar dake shinfid'e a kasa da ta tabbatar masa da ta Iman din ce. Tuna lokacin da ya bada kudin gadajen nasu yace a siyawa kowa nasa amma sai Mama tace daya ya ishesu me dan girma saboda hakan zai sake shakuwa tsakanin su,da wannan yayi amfani a ganin sa hakan ne ya kuma dauki hakan a matsayin soyayyar da Maman ke wa yar tasa. A yadda yake jin zuciyar sa a lokacin"

"zai iya yin komai, sai kawai ya fice daga gidan gaba daya ba tare da ya koma daki ba."

"Tsoro ne ya kama Iman musamman da bata san me zata ce wa Maman ba akan wankin, shiryawa tayi"

"cike da fargaba ta tafi makarantar tana fatan koma menene ya taso ya zama daidia kafin ta dawo dan a rayuwar ta, ta tsani tashin hankali ko kad'an."

"Rabi da kwata bata gane kan karatun ba, haka dai ta taho gidan tana ta zulumi, tana shigowa ta ganshi"

a tsaye ya harde hannayen sa a gadon bayan sa yana kallon kofar shigowar. Shigar jikin sa ta bi da kallo

"zuwa gyaran da yayiwa fuskar sa, murmushin da ta gani kwance a fuskar tasa, ya saka ta samun nutsuwa har ta karaso wajen da yake a tsaye."

"""Ashe kina kusa da shigowa, naji a jikina."""

Murmushi tayi kafin tace

"""Sannu da zuwa."""

"""Yawwa, ya hanya?"""

"""Alhamdulillah wallahi.*"

""" Akwai wanda ya kalleki da kina tahowa? Idan akwai fad'a min naje na same shi."""

"Sosai ya bata dariya,"

""" Kai... Babu kowa fa, ya gida yasu Mama?"""

""" Mama? Ammi muke ce mata, tana nan lafiya tace ma na gaishe ki, na gaida wacce ta kwace mata"

"yaronta kafin tazo haka tace."""

Rufe fuskar ta tayi tayi yar dariya

""" Allah sarki, ina amsawa nagode."""

""" Itama ta gode, tace ta matsu ta ganki."""

"""Watarana zata ganni in Sha Allah."""

"""In Sha Allah, very soon."""

"""Abba Babba yace idan kazo ka shiga ciki."""

""" Da gaske? Kice na zama dan gatan Abba."""

Dariya tayi

""" Naga alama kam, Abba ya yarda da kai sosai."""

""" Allah sarki, ai yana da kirki sosai."""

""" Sosai."" Tace"

""" Bari na bud'e maka, chan ne seat room din sa."""

""" Owk."" Yace ya harde a jikin ginin yana kallonta, har ta bud'e ta dawo sannan ya bita a baya yana"

admiring steps dinta zuwa ciki.

"A kofar dake farkon kofar ya zauna ita kuma ta shiga ciki, yana zama Aliyu ya shigo da ruwa a tray, ya"

"ajiye ya gaishe shi sannan ya fita, ruwan ya dauka ya sha sosai sannan ya kalle ta, gefe take kallo tana wasa da jikin kujerar da take kai."

""" Zahraah, tafiya ce ta kamani, ba zan iya wucewa ban sanar miki ba, ba wani dadewa zan ba in sha Allah,"

"inaso kafin lokacin da zan dawo mu sake fahimtar juna sosai, idan na dawo sai a shigo da magana me karfi, bana so a ja lokacin."""

""" Allah ya kiyaye ya tsare, ya dawo da kai lafiya."""

""" Amin ya Allah, Amin Amin Zahraah Nagode"""

"Shiru ne ya dan shiga tsakani, shi yana kallon ta yana sake ganin ainihin kyawun ta, ita kuma ta tafi"

"tunanin Allah yasa ya dawo din kar taji shiru idan ya tafi, har zuciyar ta bata son tafiyar tasa, amma kuma ya zatayi? Ba zata hanashi ba ai."

"""Ina wannan yayan naki da muka hadu ranar nan? Har ya korar min ke?"""

""" Uncle Khalil?"" Tayi dariya"

""" Auw sunan shi kenan."""

""" Eh kanin Mama ne, a nan gidan ya taso kafin ya koma gida."""

Gid'a kansa yayi kamar be sani ba

""" Shiyasa ya nuna min iko kenan."""

""" Uhum."" Tace kawai bata ce komai ba."

"""Yana ina kuwa?"""

"""Kamar dai ya koma, naji dai mama na fad'an ya tafi be sanar ba."""

"""Ai be isa ya sanar."""

"""Na'am?"" Tace tana kallon sa"

"""Sorry ba komai."" Ya maze kamar be ce komai ba, be san maganar zata fito ba shima."

""" Bari na gudu, kar nayi rana."""

Mikewa tayi

""" Daga nan zaka wuce?"""

""" Eh gaskiya, idan na koma gida na koma baya."""

""" Ok ina zuwa."""

"Ta fita ya tashi ya dan zagaye falon yana observing komai na ciki, yana tsaye jikin wani frame ta shigo"

dauke da leda ta mika masa tana dan russunawa

""" Gashi ka kaiwa Ammi, ina gaishe ta."""

"Rik'e ledar yayi yana kallon ta, tayi saurin dauke kanta k'asa ta sakar masa ledar gabanta na faduwa."

""" I love you."""

"Ya samu kansa da whispering cikin muryar da tayi masifar shigewa ciki, wani irin feeling taji, sarai ta jishi"

"sai tayi kamar bata ji ba, ta ja baya sosai tana diriricewa, shi kansa wani iri yake ji, be taba tunanin haka daga gareta ba, da tasan yadda Ammi take a wajen sa, da kuma yadda sakon nan yayi nasarar kara masa son ta ninkin ba ninkin, da tun ranar da ya fara zuwa tayi, kasa matsawa daga in da yake yayi, sai"

murmushi yake shi kadai.

"""Nagode sosai, Ammi ta gode."""

"""Ba komai."" Tace tana jin nauyi da kunyar yadda yayi"

"""Zan tafi, ki kula da kanki kinji? Karki yarda wani ya bata miki rai, kin fi karfin haka, ke din ta daban ce, ta"

"musamman ce."""

"""In Sha Allah."" Tace tana jin dadi , a kalla idan tana tare dashi tana jin cewa itama tana da yanci, sannan"

takai matsayin a so ta.

"Ta cikin idon sa yake ta kokarin aika mata da sakon sa, sakon da yake so ya tafi ya bar mata, irin me"

"zafin nan da zatayi wuyar dauke shi daga tunanin ta, sau daya ya samu nasarar aika mata da sakon, ya kuma je a yadda yake so, sai ya marairaice mata fuska yana jijjiga kansa."

"""Allah ya kiyaye Allah ya kaimu lafiya."" Tace da sauri ta bud'e kofar kuusa da ita ta fice ta bar shi a ciki,"

"dariya sosai ya saka, ya sake rik'e ledar hannun sa gam gam, ya fice yana jin sa tamkar yana yawo a cikin gajimare."

"A kafa yake tafiya rik'e da ledar, iska na kada shi, sam baya jin komai baya ganin kowa sai tsadadden"

"murmushin sa, shi kadai yasan yadda yake ji a lokacin, shi ya saka shi tafiya kawai ba tare da ya neme su"

"ba. A chan bayan layin da suka saba haduwa suna tsaye tana masa mitar kwana biyu be zo ba, hakuri yake bata akan wata tafiya ce ta taso masa Muhammad din yazo wucewa"

"""Kaga saurayin Iman."""

"Tace da sauri tana nuna masa shi. Wani kallo Bashir yayi masa daga nesan kafin yayi saurin juya bayan sa,"

"yayi saurin bud'e motar ya shiga ciki, yayi kamar yana neman wani abu a ciki"

"""Baby me kake nema? Fito ku gaisa da Malam mana."""

"Kin fitowa yayi ya cigaba da bud'e dashboard yana rufewa,"

"""Assalamu alaikum."" Moh yayi musu sallama yana karewa motar kallo."

"A wani yanayi Bashir ya fito bayan nacin da Zeenat din tayi masa, ya diririce ganin Moh din"

"""Sannu ko?"" Moh yace masa yana mika masa hannu"

"""Sunana Muhammad, kaifa?"""

"Yace masa, a sakale Bashir ya miko nasan hannun kamar me tsoro cikin rada rada yace"

"""Bashir."""

"""Yayi Bashir, sai anjima."" Ya wuce ba tare da yace komai ba. Dariya Zeenat ta saka"

"""Shi wannan din kika ce shine zai auri Iman?"" Yace da sauri"

""" In Sha Allah, baka ga sun dace ba? Ko baka ga yanayin su daya bane?"""

""" A haka yake tun zuwan sa gidan kuma?"

"""Babe me ta faru?"""

"""Noo noo babu komai."""

"""Naga duk ka damu ne, me ya faru?"""

""" Ah babu komai, kawai na ganshi haka haka ne."""

"""Dan ma baka ganshi sanda ya fara zuwa bane, tab!"" Ta sake kwanshewa da dariya"

"""Abun mamaki."" Ya furta ba tare da ya sani ba."

"""Abun mamakin gaske , mutum kamar wani mahau."""

"""Keee."" Yace mata yana zaro ido, sai kuma ya waske da sauri"

"""Bari naje, ya kamata mama tayi tayi ya shawo kan Abba ina so na turo manya."""

"""Ka turo kawai, ka bar komai a hannu na, bbu me min auren dole, wanda nake so zan aura babu me"

"hanawa."""

"""Toh shikenan."""

"Sallama sukayi ya tafi itama kuma ta koma gida, tana shiga ta tarar da Abba a compound, ya tasa ta a"

gaba ransa a bace.

"***Wani kallo da Maman tayi wa Iman lokacin da ta shigo ya saka ta shan jinin jikin ta, ta wuce bayan ta"

"gaishe ta bata amsa ba, ta ajiye jakar ta sannan ta fito ta shiga kitchen ta sha ruwa ta dora ruwan abinci sannan ta fito falon, tana tsaye ya hade ran ta sosai, ta tsaida ita"

"""Uban waye ya baki izinin ajiye min wankin da na sakaki? Ka tafi?"""

"""Ubanta ne!"" Abba da suka shigo tare da Zeenat yace, da sauri Mama ta juyo sukayi ido biyu dashi"

"***Ba karamin matse kaina nayi ba saboda na cika alkawari, kuyi hakuri babu yawa"

"[1/10, 8:03 PM] +234 803 765 3189: Halin Girma"

11

"*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*"

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos.

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

_*Mierah's dukkan_*

_*Mierah s dukkan_*

_*Mierah s dukkan_*

_(Palace of exotic scent and more) _

"_MD: is ur plug! Muna siyarda kaya kala2 kamar jaka da takalmi kamfanin lamis,Dior,vellabela da dkny"

"da sneakers 'yan yyi dominku da yaranku,Muna order kaya dga kasashe daban-daban,Muna siyarda da"

"kayan decors,plated gold,da turaruka kala-kala Hadi dna tasa (oil perfume) dga kamfanin naseem hr"

"suratti,Muna da room fresh da turarukan wuta Dan gangaria. Muna adashe na yargata(kaya) Dana kudi ku tuntube mu awannan nmbr kamar haka wa.me/07039773001 Muna turawa ko Ina afadin Nigeria da"

wasu kasashen ketare ngd_

***

"A wani yanayi Maman ta dago, gabanta ya fadi ganin Abba a tsaye a kofar Zeenat na rakube a gefe"

kamar munafuka

"""Dr, Sannu da zuwa."""

"""Kinsan daga ina yarinyar nan take?"""

Ya nuna Zeenat yana jin kamar ya rufe ta da duka.

"""Aiken ta ne nan baya gidan Amarya me koko."" Tace bayan tasan ba hakan bane. Kwafa yayi cikin kada"

Kai yace

"""Yaron da nace babu ita babu shi take zuwa suna haduwa a bayan layi, na fad'a miki na kuma bana son"

"yaron domin ba yaron kirki bane, amma a bayan kunnenku."""

"""Idan har ta dage ba zata ji magana ta ba, zata dinga fita suna haduwa a wani wajen ba da izini na ba ko"

"na yan uwana, zan sallama masa sai tace ya turo,amma..."""

Ya nuna ta da yatsa

"""Idan har wani abu ya je ya dawo, kar ku kuka da kowa, ta kuka da kanku!"""

"Shiru Maman tayi taki cewa komai, haka Zeenat din da ya zaci zata bashi hakuri sai yaji tayi shiru"

""" Kin amince da Bashir din, kin yarda zaki aure shi?"""

"Daga kanta tayi da sauri babu kunya ba tsoron Allah, wani irin faduwa gaban Abban yayi, yaji tamkar zai"

"fadi saboda wani jiri da ya nemi zubar dashi, be zaci haka daga gareta ba, sam ba tarbiyyar da yayi wa yaransa bace, sake maimaitawa yayi cikin danne abinda yake ji yace"

""" Kinji kin gani, kin Amince?"""

""" Dr ka bar maganar nan idan muka shiga ciki sai mu..."" Dakatar da ita yayi da hannu, ya dakawa Zeenat"

din tsawa

""" Ki bani amsa!"""

""" Eh Abba."" Tace tana nokewa idon ta fes tamkar an soye gyada"

""" Shikenan, shikenan."" Ya maimaita"

""" Kice dashi ya turo magabatansa, suzo wajen Yaya."""

Sai ya juya wajen Iman da tayi kamar ta bud'e kasa ta shige saboda kunyar abinda Zeenat din tayi yace

""" Kema ki ce masa ya turo dan ba zan bata lokaci ba."""

"Daga kanta tayi da sauri, ya wuce su yana jin wani irin tashin hankalin abinda Zeenat din tayi, tabbas"

"laifin Hajara ne, ita ce bata tankwarata ba, bata nuna mata daidai da akasin haka ba, abinda ma ya lura"

"Itace take son abin, ba zai yarda wani abu ya faru ba a dalilin hana ta auren Bashir din, dan yaran yanzu"

"zasu iya komai akan soyayya, shiyasa kawai ya yanke shawarar aura mata shi din idan har ta kafe, da azo ana wallahi tallahi."

"Abban na barin wajen itama Iman tayi saurin ficewa dan tasan sarai Mama zata huce akanta, tana juyo"

"fad'an da take wa Zeenat din sama-sama, ta kara sauri ta zagaya ta baya ta shiga ta kitchen ta wuce dakin su kawai."

"Tsawon kwanakin Abba bashi da walwala sam, ita kanta Mama ta kasa gane kansa, da ya shigo zai"

"wuce dakin sa kawai sai kuma gobe, a da tayi tunanin fushin ba zai nisa ba, sai taga abin yana neman zarcewa, takanas ta same shi da maganar da ban hakuri amma sai ya share ta yama yi ficewar sa ya barta, haushin hakan ya sakata share shi itama ta san dole zai gama fushin sa ya dawo ko da Anyi auren yaji su kalou zai ajiye komai ya dawo, tasan ta fishi gaskiya shiyasa taki goyon bayan sa, dan tasan"

zugashi akayi dan an ga Zeenat din zata huta.

"***Bayan tafiyar Muhammad basu yi magana da ita ba, sau biyu tana kiran number sa bata samun sa,"

"hakan ya saka ta damu sosai, gashi tasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login