Showing 30001 words to 33000 words out of 37626 words

Chapter 11 - HALIN GIRMA By hafsat rano

29 May 2026

79

zatayi kokari a"

"dan zaman nan ta koya wa yarta kaunar ta da sabawa da ita da yan uwanta, sannan ta nusar da ita rayuwa da yadda zata kula da auren ta. Sallama sukayi da alkawarin ana gobe zai kawo ta, zai kira ya sanar mata. Godiya tayi masa dan har gobe tana ganin kima da mutuncin sa, mutum ne shi na gari, me"

kirki da son iyalin sa.

"Bayan gama wayar da sukayi ne zuciyar sa ta gwada masa kiran Zeenat ya sake gwada tankwarata, idan"

"Allah ya taimake shi ta hakura sai yafi kowa murna, dan yanzu bashi da babban tashin hankali kamar auren zeenatun da yake da yakinin zai iya zamar mata wani Babban tashin hankali a gaba."

"Kiran nata yayi, tana dagawa yace ta matsa daga wajen kowa zai yi magana da ita, da ido ta kalli Mama"

dake zaune ana maida maganar auren Zeenat din da Hajiya ta fice zuwa tsakar gidan.

"""Abba na fito."""

"""Yawwa zeenatu, magana nake so muyi a matsayi na, na mahaifin ki, kin san dai ba zan taba zabar miki"

"abinda zai cutar dake ba, ba kuma zan ga cigaba a gareki na dakushe ki ba, ina neman alfarma, kiyi hakuri da Bashir ki kawo wani ba shi ba,nayi miki alkawarin tsaya miki kinji?"""

"Gabanta ne ya fadi, a tunanin ta an gama wannan babin, sai gashi Abban ya dawo da shi yana kuma"

kokarin daure ta da jijiyoyin jikinta.

""" Kina jina zeenatu?"" Ya sake fad'a cikin yanayi me wahalar fassarawa"

"Shashekar kuka yaji, ta fashe da kuka cikin muryar kukan tace"

""" Dan Allah Abba kayi hakuri?"""

"""Ai ba laifi kikayi min ba Zeenatu, alfarma kawai nake nema a matsayi na, na mahaifin ki."""

"""Abba dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zan iya hakura da Bashir ba."""

"Kamar saukar aradu haka Abba yaji, ya dafe kansa ya shiga karanto innalillah wa inna ilaihi rajiun, babu"

"babbar jarrabawa irin yayanka suyi rashin sa'ar miji, duk abinda yaje ya dawo dole kana ciki, kamar ka saida akuyar ka ne tazo tana ci maka danga, baya fatan hakan ta faru ga ita, shiyasa tun farko ya hakurkurtar da zuciyar sa be ga laifin ta ba sai na Mama, amma yanzu ya tabbata abinda Zeenat din take"

"so shi Maman take goyan ba, dama mafiya yawan lokuta uwa na tafiya ne da ra'ayin yarta."

"""Shikenan zeenatu, duk abinda yaje ya dawo karki kuka da kowa, ki kuka da kanki."""

"""Abba dan..."" Kafin ta kai karshe ya katse kiran, Jan kafarta tayi ta koma ciki tana jin a ranta tayi abinda"

"ya dace, a kalla ta yi kokarin kare soyayyar ta ko ba komai idan akayi auren Abban zai hakura ya sakko."

"""Lafiya?"" Mama tace tana kallon ta."

"""Ya kukayi da Baban naki? Maganar dai ce ko?"""

"Da kai ta amsa mata da eh, tsaki Maman taja"

"""Shine kike kuka ko me? Ni wai Zeenat asiri Bashir yayi miki ne? Da bakya ganin kowa da komai sai shi?"""

Kanwar Maman Atika ta fad'a cikin bacin rai

""" Ni banga wani abun naci a Bashir din nan ba, tunda mahaifin yarinyar nan baya so toh a hakura mana?"

"Iyaye maza sun fi mu tunani da hangen nesa."""

"""Toh Atika ya za'a yi? Shi ma fa duk zuga ce wallahi, ai da be san da hakan ba sai bayan yaga mijin da yar"

"lelen tasa ta samu, shikenan kuma sai kananan maganganu bansan daga ina ba, amma ina kyautata zaton daga wajen Gaji ne, dan ita kadai ce take sauya musu tunani da raayi dukkan su, ita kuma na"

"tabbata munafurcin Iman ne dan ko yaushe tana wajen ta."""

"""Duk wannan ta tunani ne Yaya Hajara, bamu da tabbas din hakan, kinga dai yadda Dr ya dage ya kamata"

"ace kin bashi dama kinji ta bakin sa akai."""

"""Kyale shi kawai, zai sakko ne."""

"""Me yace miki?"" Ta tambayi Zeenat din tamkar abin be dameta ba."

"""Cewa yayi nayi masa alfarma na hakura da Bashir."""

"""Ehen kinji? Har ya saukar da kansa a matsayin sa na mahaifi yace yana neman alfarma kema Yaya"

"Hajara kinsan da matsala."""

""" Me kika ce masa ke kuma?"" Taki amsa atikar ta tambayi Zeenat din."

""" Hakuri na bashi."" Tace tana rakubewa a gefen Hajiya da tunda aka fara maganar bata saka musu baki"

ba sai lokacin

""" Gaskiya da kun hakura kun bi zabin Ibrahim, a kalla shi namiji ne yafi mu dukka tunani da hangen"

"nesa."""

""" Hajiya toh ya za'a yi? Lokaci ya riga ya wuce bata kula kowa sai shi, yaushe zata fara daga farko kafin"

"ma ta samu saurayin su fuskanci juna a zo maganar aure."""

""" Duk wannan me sauki ne akan ka dauki dan ka, ka kaishi inda zai Sha wahala."""

""" It's better to marry late than to marry wrong."" Atika tace tana girgiza kafarta"

""" Khair in sha Allah, babu abinda zai faru."""

"Maman tace a kasan zuciyar ta tana jin tsoron abinda zai je ya dawo, ita kanta ta fara tsoron yadda"

"Abban ya kafe ta tabbata akwai babban dalili, amma kuma ta Ina Zeenat din zata fara? Hasalima bata da farin jinin samarin duk asalin su Iman suke so sai ita maman tayi amfani da wannan a juya mata kansu zuwa Zeenat din dan ba zata iya gani Iman din tayi aure musamman auren babban gida ita kuma Zeenat"

din na zaune a gida.

"***Da sauri ya karasa part dinsa yana jin kayan na masa nauyi sosai, yau tun safe Bubu ya Aiko masa da"

"kaya sannan ya bukaci ganin sa a kofar part dinsa dan shiga tawagar sa zuwa Fada, haka ya tashi ya shirya ba dan yaso ba ya fita. Tun lokacin sai yanzu ya samu dawowa part din sa, yana shiga ya hau cire kayan yayi wurgi da rawanin yana jin shi sakayau. Allah Allah yake ya samu feedbacks din aikin da ya saka Musaddik sai gashi kuwa ya kirashi adaidai lokacin, dagawa yayi yana rage daga shi sai singlet da"

boxer kasancewar zafi ya fara hurawa kadan kadan ba kamar kwanakin baya da ake sanyi sosai ba.

"""Gani fa ga mutumin ka."" Musaddik yace yana dagawa"

"""Da gaske? Sharp sharp haka? Ok bari na kiraka Video Call."""

"Ya katse sannan ya kira video call, a daidai saitin fuskar Bashir Musaddik ya saka wayar yadda yana"

"dagawa Moh zai fara ganin sa. Yana durkushe tamkar me neman gafara, wata dariya ce ta zowa Moh, yayi murmushi kawai yace"

"""Oga Bashir barka da warhaka."""

"""Dan girman Allah ranka ya dade kayi hakuri, wallahi bansan gidan da kaje Neman aure bane nima naje,"

"wallahi kuskure ne kawai amma kayi hakuri."""

"""Ai ba laifi kayi ba Bash, ni hakan yayi min dadi sosai, kuma ina tayaka murna, kaga ni da kai mun zama"

"yan uwa tunda zamu auri yan uwa."""

"""Tuba nake ranka ya dade!"" Yace yana kasa da kansa"

"""Dago kanka bash, bafa wani laifi kayi ba, aiki nake so na baka, bana son kuskure ko kadan a ciki, idan"

"har kayi min yadda ya dace akwai babban tukuiwaci."""

"""Hakan shi yafi komai sauki a wajena ranka ya dade, fadi ko menene ."""

"""Yaushe za'a je tambyar maka auren?"""

"""Gobe ne ranka ya dade, amma idan kace a fasa na fasa wallahi."""

Girgiza kai yayi

""" Ba za'a fasa ba, Ina so idan sun je su nemi a saka musu wata daya!"""

""" Wata daya!"" Ya zaro ido"

""" Wata biyar nace ko shekara, ban shirya ba wallahi,dan dai bana son na rasata ne."""

""" Ba zaka taba rasata ba, ni zan maka komai na auren tun daga lefe har gidan zama zan baka, ni dai"

"kawai kayi duk abinda nace kayi."""

Dukawa yayi jiki na rawa

""" Nagode nagode Allah ya kara girma, zanyi duk abinda kace, ba zan yi komai ba sai da sanin ka."""

""" Good, yanzu aikin me kake?"""

""" Buga buga kawai, sai kuma aiken Hajjaju idan ya tashi."""

"Dariya sosai Moh yayi, ya hangi tsantsar mutuwar zuciya da son zuciyar a tattare da Bashir din, mikar da"

"yan yatsun sa yayi baya, ya dawo dasu gaba suka bada sauti kafin ya katse dariyar yana zama so serious."

""" Abinda nake so kayi min, zaka ji daga bakin Musaddik, bana son kuskure ko kadan, komai Ina so ya tafi"

"cikin tsari , Ina so gobe ka dauki hanyar Katsina, zan aiko maka da sako ka kaiwa Gimbiya Zeenatu, hakan zai sake goge shakku ko wani tunani akanka."""

""" Nagode ranka ya dade, nagode nagode."""

""" Karka damu, kai dai kayi abinda nace, bana son kuskure ko kadan!"""

""" Da yardar Allah zaka same ni da bin duk umarnin ka. """

Daga masa kai Moh yayi sannan yace

""" Guy!"""

""" Yeah Captain!"" Musaddik yace yana matsawa daga wajen da Bashir din yake"

"""Ka kula dashi sosai dan dan iskan kansa ne, duk da be isa ba, amma dai bana so a samu matsala har"

"zuwa ranar daurin auren, watch him and report anything da be maka ba."""

"""Karka damu, babu ma abinda zai faru. """

""" Yau nayi zaman fad'a, kamar nayi kuka wallahi, wannan yazo ya fadi yayi gaisuwa, wanna yazo ya ce"

"makwafcin sa kaza, wannan suzo maganar aure, wannan ta kawo karar mijinta wannan ya kawo karar matar sa, maganar gado, kai abubuwan da mugun yawa, kamar na gudo nake ji, nasan iya zaman da zan"

"Bubu ba zai raga min ba wallahi, har na fara ramewa. """

""" Haka zaka hakura kayi abinda yake so, iyaye dole a bisu ayi musu yadda suke so. """

""" Haka ne dama, shiyasa na matsu nayi auren nan nima na zama me yancin kaina, kasan aure fa yanci"

"yake siyo ma da martaba ba komai Bubu zai dinga matsa min ba da zarar yaga nima na zama dan gari a harkar. """

""" A harkar me? """

""" Harkar auren mana, ina fita daga novice zai yanta ni, kwana kad'an kaji nima ana Daddy, Daddy! Wayyo"

"I can't wait. """

""" Kaifa yanzu baka da magana sai ta aure ko? Wannan sanyin ne ba komai ba. """

""" Sanyi ai ya wuce kuma, ba zan kara yarda na sake wani sanyin a gauro ba wallahi, haba Malam ai an ji"

"jiki kawai. """

""" Dan air. "" Musaddik yace yana dariya"

""" Yan air dai, Wa ma ya kaika ne? Gwara ni wallahi kowa yasan uztaz. """

""" Nima haka ai. """

""" Fadawa wanda be sani ba toh. """

""" Toh ai idan har Moh uztaz ne toh tabbas ni sai da shehin malami, kai din? Ina dai tausayin yar mutane"

"da zata shigo hannun tuzuru irin ka wallahi. """

""" Naji karka bata min tunani, jeka zan neme ka anjima bacci zan."""

""" Hahaha, shikenan sai na jiki, angon Fatiti. """

""" Musaddik.!!! "" Ya furta da karfi"

""" Sorry sir, angon Fatima. """

""" Zaka shigo hannu ne wallahi, sai na saka an samin kai frog jump. """

""" Idan wannan ne ai na gaji da yi, a chanja wani punishment din dai Captain. """

"Kashe kiran Moh yayi, yasan ya biye Musaddik sai su cinye lokacin suna abu daya, wurgi yayi da wayar"

gefe ya kwanta dan rama baccin da Bubu ya katse masa

Halin Girma

15

_*Zafafa biyar na kuWi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haWaki da ALLAH idan kin

saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saSa mana al™awari ta

hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK *

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK *

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK _*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content

=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1D xoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2F xLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK _*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

" " " " " " " " " "

"Kasa fitowa tayi, tana taraddadin yadda zasu karbe ta, ji tayi an bud'e kofar bangarenta, taji muryoyinsu"

a lokaci daya suna mata sannu da zuwa

"""Yau ga Fatima,sannu da zuwa dota, sannu da zuwa."""

Wata farar mata da a kalla zatayi sa'ar Mama ta fad'a tana riko hannun ta. Da wani irin yanayi take

"kallonsu su dukka, kowannen su kokari yake ya nuna mata kansa, mutum daya dage gefe tsaye ta harde hannayen ta a kirjin ta ta daga kai ta kalla, tun isowar su wajen ita kadai ce bata yi magana ba. Wani irin shock taji ta furta Mommy a tsakanin lips dinta, gyada mata kai matar tayi da sauri ta isa gareta ta rungume ta tana sakin kuka, bata chanja ba ko kad'an daga yadda take a hoton ta da take dashi tun na zamanin yan matantaka, duk da ganin ta da ita a zahiri kadan ne amma ko yaushe zuciyar ta na manne"

da hoton mahaifiyar ta.

"Tafi sukaji an saka daga bayan su, duk Kuma sai suka saka dariya har Iman din da kunya ta kamata ta"

sake shigewa jikin mahaifiyar ta tana jin wani irin son ta da kaunar ta.

"""Muje ciki ko?"" Babban namijin ya fad'a yana nuna musu hanya da hannun sa. Sakin Mom din tayi, matar"

farkon nan ta kama hannun ta zuwa ciki hanyar da ta ga sun fito dazun.

"A falo suka yada zango, kowa a cikin su kokari yake yaga ya nuna mata soyyayyar sa, da kallo kawai"

"take binsu cikin mamakin dalilin da ya saka basa neman ta tsawon lokaci haka duk kuwa da soyayyar ta da ta hanga a tattare da family din. Tana da bukatar amsa saboda tasan yadda kowacce uwa take kulafucin danta musamman ita da aka dauke ta da karancin shekarun ta, tabbas a farko farko ta kan zo ta ganta tare da wani babban namiji duk kuwa da karancin shekaru basa barin ta tuna komai amma"

tabbas ta san anyi haka kuma Abba da kansa ya kara sanar da ita a wani lokaci da ta tambaye shi.

"Kamar an jeho su suka shigo su biyu, suka yo kanta da gudu macen ta rungume ta tana sakin ihu,"

namijin kuma ya durkusa a kusa da su yana dariyar farin ciki

"""Welcome sister!"" Yace bayan macen ta saketa ta zauna tana maida numfashi"

"""Welcome sis!"""

Tayi saurin fad'a itama tana hararar sa

"""Sannun ku."""

"Tace tana murmushi tana mamakin su,"

"""na riga shi ganin ki, na rigashi yi miki magana dan Allah ni kadai zaki so kinji? Dama kullum ina jin"

"haushin bani da big sister sai wannan coconut head din , sai gashi na samu yanzu, I'm so happy wallahi, da k'yar na bari aka gama islamiyya yau wallahi."""

"""Amaani kin cika surutu wallahi, ai sai ki barta ta huta ko?"""

""" Tell her Mamma, wallahi kamar na bugeta yau din nan ta bani haushi."""

""" Kaifa ya sunan ka?"" Ta tambaye shi"

""" Amaan."" Amani tayi charaf ta rigashi fad'a sannan ta dora"

"""Nice hassana, shine husaini, na girme shi so nice babba."""

"Murmushi Iman tayi, so adorable yaran,"

"""Oya ku wuce kowa ya cire uniform dinsa kuzo muyi dinner, nasan Iman ta gama gajiya tana so ta huta"""

Mamma tace tana mikewa

""" Zayd, Ya Mubarak dinner na table."""

""" Ni sai nace gida gaskiya, I'm full."""

"Ya Mubarak yace yana gyara zama sosai. Kama hannun Iman Mamma tayi, suka wuce dining din tare da"

"Zayd yana mata tambayoyi. Mommy na jinsu bata saka baki ba, dama kuma ita haka take da kara sosai, komai nasu Itace akai amma bata taba nuna musu iyaka akan nata, shiyasa suma duk wani abu da ya shafe ta toh sune a gaba gaba, sai ta koma gefe ta zama yar kallo. Bata da hayaniya kamar dai Iman koman ta a nutse takeyi musamman kuma abun da ya hadu da arziki sannan ga ilimi both boko da islamiyya. Kujera taja gefen Iman din da suka bar mata ta zauna daidai lokacin Amaan da Amaani suka dawo kowa ya sauya kayan sa zuwa na zaman gida. Amaani na kokarin fara surutun ta suka hada ido da"

"Mommy, kallon da tayi mata kadai yasa taja bakin ta tayi shiru har suka gama babu wanda yayi magana."

"Falon suka dawo, a lokacin Ya Mubarak da Zayd suka yi musu sallama akan zasu dawo gobe kowa da"

"family dinsa, har bakin mota Mommy ta rakasu ta dawo sai kawai ta wuce dakin ta, ta bar Mamma da yaran suna hira, ta lura da yadda Iman din ke jin kunya da rashin sabo amma kuma tasan wace Mamma ba zata taba barin ta ba har sai ta tabbata ta sake dasu, balle uwa uba iyayen magana su Amaani su"

kadai ma sun isheta.

"Kwanciya Mommy tayi farin cikin zuwan yarta na ratsa ta, wayar ta ta dauka ta kira number Abba,"

"lokacin ya gama cin abinci kenan yana kokarin duba wasu papers dinsa a computer yaga kiran nata, tsaywa yayi da abinda yake yi ya daga."

"""Nagode sosai IB, naga Iman fiye da yadda nayi tunanin ganin ta, hankali na ya kwanta dan na tabbatar"

"da tarbiyyar ta, kayi ma maman tasu godiya dan Allah. """

""" 'yaya amana ce a garemu da dole mu kula dasu da tarbiyyar su, domin dole ne Allah ya tambaye mu a"

"ranar gobe kiyama, banyi komai ba face abinda ya zama wajibi na."""

Ya fad'a yana jin chan kasa zuciyar sa da zata samu labarin abinda ya faru a zaman Iman din da Maman

"daku tabbas za'a iya samun matsala, abu daya ya hanata yin wani katabus akan maganar Iman din, tabbatar mata da yayi akan bata da matsalar komai, kuma tana hannu na gari."

"Sallama sukayi ta runtse idon ta, hasashen irin shirye shiryen bikin da zatayi kawai take, ba zata bari ta"

koma ba har sai tayi mata nata kalar gatan da zata tabbatar da ita din yar gata ce.

"Turo kofar akayi, ta daga kai ta kalli Iman din cikin rakiyar Mamma."

""" Sai ki gudo ki bar mu? Gamu toh mun biyo ki."""

""" Na zata wajen Hajiya kuka yi ai."""

""" Munje chan din ma."""

""" Ok."" Tace tana mikewa zaune."

""" Bari na duba yaran chan, ina ga daga haka zan kwanta, sai da safe Iman."""

Murmushi Iman tayi ta amsa sannan mummy tace

"""Sai da safe Yaya."""

Fita tayi ta ja musu kofa cike da farin cikin kwanan da ya da uwar zasuyi yau.

"""Dawo kusa dani."""

"Dawowa tayi ta zauna daf da Mummy din, ta jawota ta dora kanta a saman cinyar ta, cikin tattausan"

lafazi tace

"""Kin girma sosai Iman, nayi mamakin yadda kika kara chanjawa akan last da Dr. Ya tura min hoton ki,"

"amma kuma naga baki da walwala sosai, ko rashin sabo ne? Ko kuma hakan halitta ne?"""

"Murmushi tayi me sauti, nutsuwa ta saukar mata, taji da gaske she's safe fiye da yadda ta taba ji a"

"rayuwa ta, a hankali ta furta"

"""Babu komai Mummy."""

"""Shikenan, ki kwanta idan kika huta duk maganar da zamuyi sai muyi kinji?"""

Ta shafa kanta tana murmushin. Daga kan ta tayi ta ajiye a saman gadon ta fita daga dakin. Wajen kayan

"ta, ta nufa ta ciro wayar ta, tasan ya mata magana a WhatsApp bata samu sukunin dubawa ba. Misscalls ta gani ta whatspp call sai messages dinsa da ya turo mata. Sakon ta fara dubawa ta,tabi kowanne tayi reply ta bar daya da yake tambayar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login