Showing 15001 words to 18000 words out of 40972 words
Chapter 6 - ZUMA DA MADACI Romantic Hausa Novels by Maman Teddy .pdf
Kallona Oumma na tayi tana zaro ido waje Suhamart haka ne ko???.
Dariya nasaka hadi da ce mata ehmana Oumma ". Ae ko Suhamart bari ki ga tunda dai kin
warware mu tafi a ayau din kawai. tana fadin hakan ne hadi da ficewa daga dakin don nufan
Doctor.
Niko Bin bayan ta nayi ina mai tunanin furucin Oumma na" Suhamart ni bana jin wannan yaran
nake fah". Murmushi nakuma ina mai kuma tuno Abubuwa da yawa" I luv u murmy".
luv u so much too my Daughter". Suhamart ki zo mu tafi kar muyi latti fah"... Tom my boooooo
ina zuwa minti 2 kacal. natafi haba Hamma na iyayen Zuciya ina katafi waxai kaini School din?.
Basai ki je da kanki ba,ae ke komai naki yi kk kaman wata Babba,amma jibiki Har yanxu baki fi
5 yrs ba... Hohiooooooooo Mummy... Dadddy..." Hamma Huuuuuuuu...
Suhamart ya jikin naki??. saurin juyowa nayi ina furta naji sauki sosai. tom mashaallh yanxu ga
takardan sallama nan,bayan Wata daya kai dawo". tom ngd likita. nan Oumma na ta hau gdy
hadi da fara tattara komutsan mu.
Me napep ta taro yayin da ya shigo har farfajiyan Asibitin sannan mu ka nufi gida.
A wannan dare sam Oumma na taki yarda ko nan da can na jirga,karoko ma A dakin ta na
kwana.
Da Asuba kuwa kan na farka tuni ta fice ta dora ruwan koko sannan bayan ta kammala ta
doramun na wanka.
"Khaleed... Khaleed" .... sai da ta yi maganan ya kai sau uku sannan ya dago kan sa yana
kallon ta,fuskan sa kam dauke da damuwa fal. Kirjin ta ne ya buga,cikin saurin ta kai Hannun
tana safa gyefen fuskan sa da yake kwance kan Resting chair. a sanyeye cike da taushin murya
da tsatsan soyayya ta Uwa da dan ta Mum Zaituna ta shafa shi tana furta My baby meke damun
ka,baka da lfy ne??.
Saurin girgixa mata kai Yy hadi da juyi akan jikin ta sannan cike da muryan shagwaban d
yasaba mata ya fara cewa" Oumma Hayatee na bata da lfy ne". Cikin Saurin tace Ayyah Ita
Iftihal din ce babu lfy ai ban sani ba,kuma daxu muka gama mgn da ita tace xata taho Nageria
nan da Kwana biyu 2. Wani daddaciyar yawu ya hadiye da kyarrrr....murya can kasan makoshi
yace Mummy ba ita ba.
Shiru Hajiya Zaituna tayi kan daga bisani ta tsaya tana observing din yaron nata,lokaci daya ta
fahimta tabbas dan nata he fall deply in love...tom amma da waye??? tambayan da ta dinga
mawa kanta kenan!!!. Hmm nan ta nisa tana mai ce masa Ohk tom wace ce ita ? fada mun my
son" aina take YAR WAYE a Fadin Nageria?. littafin maman teddy wanda bata karanta ba anvar
ta back...
Shiru yy kan daga bisani yace Mummy ita Hayatee na ba yar kowa bace,amma ki natsu a
hankali nan da Kwana 2 xan kawota ki ganta.
Hmm dan murmushi tayi don a tunanin ta shadi fada yake mata". Shafa sumar kansa ta dinga yi
hadi da sakat masa AC wanda a haka da kyar Bacci yy awon gaba dashi.
Niko bayan na kammala wanka nayi sallah ne na sha kokon da Umma na ta ajiyemun hadi da
korawa da magani na. saka kayan Aikatau dina nayi,sannan na fito a daki na ina furta Oumma
sai na dawo".
Suhamart ina zaki tafi kina fama da kanki??.
Oumma naji sauki don Allah kar ki damu.
Shiru Oumma tayi kan daga bisani tace Suhamart don Allah ki kula,idon baxaki iya aikin ba kai
dawo gida kinji? tom Oumma na tafi". A dawo lfy.
Haka na nufi gidan Hajiya Zaituna bayan napep ya saukeni na sallame sa sannnn nayi saurin
shigewa gidan,don ko sasan Hajiya Zaituna baje ba,saboda makaran da nayi.nufan sasan Ogan
nawa nayi direct don nayi saurin Kaddamar da aiki na,a raina ina tunanin hukuncin da zan
fuskanta daga gurun sir Khaleed. don nasan yanxu ni yake jira na hada masa breakfast. Shi yasa nayi saurin nufan barayin sa.
Shiko gaba daya Sir Khaleed yagama cika yy fam,Haushin kowa yakeji,buri n shi kawai yaji
halin da Suhamart din sa ke ciki!!.
Ga kuma yan aikin da suka zo su biyu a makofin ta wai su hidimta masa,gaba dayan su
sungama wulakanta don ko sun gaishe sa baya amsawa,sai daure fuska da yakeyi,ga wani
hararan raini da wulakanci da yake binsu dashi. Gaban sa Laptop ce yake Operating yyn da
yake sanye cikin Farar t.shirt sai boxer iya gwiwa,ko shirib nufan Companyn sa baiyi ba. don shi
yau sam bai son ganin kowa sai Hayatee n sa.
Da sallama dauke a Abaki na na shigo falon,wanda kallon inda nake baiyi ba sai ma tattara
laptop din sa da yy ya nufi resting room din sa. Jiki na ne yy sanyi kalau. a raina ina cewa
shikenan yau naga ta kaina,Allah yasa basun sallame ni bane. musamman yanda naga su Atika
na aiki na. Daga masu Hannu nayi nan cike da iyayi suka dago mun,su adole yau sun amshi
aiki na,kila nima an sallame ni ne.
Sum² nafara aiki na ta hanyar nufan kitchen don dama su goge falon da sharewa suke. Banfi
mintoci 30 ba na kammala masa dan abuncuwa da zai samu yy break. Muryan su Atika naji
suna gulma ta hanyar cewa" kuga Wahala Matan da Ansallemi kan mhisd Caterine ta dakatar
dake kinxo kina wani wahalar banza.
Gaba na ne ya fadi Kwallah ya ciko min ido. duk da haka ban bar aikin ba sai da na kammala
komau sannan na dau yar wayata baby nokia. hadi da nufan Resting room din sa,don na gaishe
sa daganan na Wuce gida tinda Naji ansalle meni.
Kwance na hango shi yyn dora Hannun saman koshi idon shi na kallon POP din wurin. Daga
dan nesa na bude baki ina furta Sir Khaleed bar da Safiya". Banxa yy mun, wanda sai da na
mamaita sannan ya tashi daga kwancen ya zauna hadi da kallona. Kasheni yy da ido wanda
hakan yasani saurin sidda kai ina ambaton Allah,kat yy mun tijara sannan ya koreni,gomma ya
koreni da mutunci na!.
Cikin dakakkiyar murya fuska babu wasa yace mun Zo nan". Kallon shi nayi nayi shiru ina
tunanin wani abu. don nagama tsorata da shi.
Muryan shi na kuma ji cike da maxantaka yace mun tsoro na kikejiiiii???.....
*Labarin Zuma da Mad'aci na Kudi ne,ga mai bukata zaki turo #200 VIP,#300 SPC,#100
NORMAL na MTN duka ta wannan numbern 08081202932/09137392680.*
*Maman teddy*
*Typing...✍*
*ZUMA DA MAD'ACI*
_*(True love never end...)*_
Na
*Maman teddy*
*Episode 11*
*_________________________*
*ALHERI WRITERS ASSO.️*
*A.W.A*
```Kungiya daya tamkar da dubu,kungiya masu aiki da nazari da ilimi,Alheri sai d'an Alheri```
*___________________________*
مسب* الله رلا ميح رلا *ميخ
"Tsoro na ne kike ji?.
Shuru na masa sai da kyar na iya girgixa kai na alamar A'a. Hmm nan ya sakar mun murmushi
hadi da kai Hannun shi yana shafa sajen gyefen fuskan sa yana mai kuma cemun a karo na
biyu (2), Ohk tom na gane zo inason sanar dake wani abune Suhamart". Kirgina ne ya buga
mun,duba da yanda naji ya wani kira sunana!!! A raina ne nace dama Sir Khaleed ya san suna
na? Tom ta yaya???. ko baxa ki xo ba?. ya fadi yana kafe ni da idon sa wanda lokaci daya naji
wani irin kwarjinin sa ya Rufe ni". A hankali na fara ta kowa har Zuwa inda yake a Zaune. Shiko
Murmushi yake ta bina da shi har na karako inda yake. Banyi Aune ba sai jin nayi ya kamo
hannu na yana Zaunar dani gyefen sa.
Cike da tsoro da mamaki na bude ido na ina kallon sa hadi da saurin matsawa nesa dashi".
Kallo na yayi yana mai kara jin wani irin kauna na yana ratsa duk wani sassa da gaba na jinin
jikin shi. Cike da gentle Voice din shi ya fara cemun Sorry Hayatee,banyi hakan dan wata
manufah ba. Kawai dai so nake na fada maki wani Abu!!!.
Hmm tom Inajin ka Sir Khaleed, na fadi ciki da Rawar dari wanda daka ganni kasan a tsorace
nake. Dariya yy gami da cemun Okay Rufe idon ki". Kallon sa nayi cike da mmki sai kuma ganin
ya kashe ni da ido yasani Bin umarnin nasa ta hanyar Rufe ido na". Murmushi yy nan yakai
Hannun sa yana riko nawa hannun wanda ya sani Saurin bude idona wanda ban shirya ba.
Murmushi yymun mai kayatarwa nan yace mun Okay kar ki rufe idon naki,amma plz ki tsaya
yanxu xan rubuta maki wani abu ne.
Shiru nayi ina mai kauda kai na gyefe had'i da mika masa hannnun ina mai Ware taffa na gare
shi. A bangaren Zuciyata kuwa sosai nake mamakin mai Sir Khaleed Zai yi mun haka?. Tom
dama wai yana magana ne haka???. jin saukar Biro a kan tafin Hannu na yasa ni saurin rintse
ido ina Addu'ar Allah yasa yayi sauri yagama abun nan nashi,kan wasu kuma su shigo ayi mun
mummunan Zato...
Koda ya kammala Rubutun ina jin shi ya rike Hannun nawa bai sake ba kusan minti Biyar,kana
ya saki Hannun nawa yana fadin Suhaimart kar ki bude hannun naki sai ba kowa kuma sai kin
samu natsuwa kin kwantar da Hankalin ki waje daya kinji?.
Daga masa kai nayi ina saurin mikewa don duk na kosa na gudu na bar dakin. Sai kuma tuno
da ae ni ce Zanyi Serving nashi yasa ni saurin sidda kai ina furta Sir Khaleed Breakfast dinka
fah ya Kammala.
Murmushi yayi mun Hadi da cewa" Nop kije ki huta kiyi Bacci don nasan baki da lafiya And then
jikin nan ki na son kulawa da hutu,kije side din ku ki kwanta kinji?.
Cike da tsantsan mamaki nake bin sa da ido da kallo wanda sai da yayi mun murmushi yasa ni
saurin daga masa kai hadi da ficewa daga Restingroom din nasa wanda yana yin yanda yake
bina da kallo har tuntube da yatsuna nake yi ina furtawa a zuciya ta,Allah yasa Ba iskancin nasa
bane da'ake bani labari zai dawo kai na". kee Suhaimart ke awa ne da Sir Khaleed zaiyi
yunkurin lalataki?. bayan ga yan mata masu ji da aji yayan hutu yayan masu da shi da kullum
suna aikin sunturi a gidannan shikuma yana aikin Wulakanta su???. Zuciya ta ce tabani amsa
da hakan. A haka dai nake ta tunani tom ya akayi Sir Khaleed ya san nayi Rashin lafiya. A haka
dai na nufi Side din mu ina zancen zuci don a tunani na Mhiss Caterine ta sallameni kaman
yanda naji Wa'ancan suna gulman su,amma abun mmki da shiga na ta nufoni tana tana shafa
gyefen fuska ta da tambaya na ya karfin jikin nawa??? Anan na bata amsa da naji
sauki,Oummu ce ta taso itama tana min sannu,kan mhiss Caterine tace ta kaini Dakin mu na
samu na kwanta na huta,yau baxan yi aiki ba sai zuwa gobe innaji Sauki".
Haka dai Muka shiga daga ciki ni da Oummu Sulaym yyn da nan Oummu ke ta kwadun Sannu
har nagaji da amsawa". Don Oummu Sulaym Sam bata gajiya da surutu haka Allah yayi
ta,dakanta ta kwantar dani hadi da gyeramun fillow ina mai tayar da kai na dashi.
"Ban wani jima ba bacci yy awon gaba dani".
_____________________________
Hutawan ka Lafiya allah yajah da kwanan yarima mai jiran gado,gaban ka da baya Mulki ne jinin
sarauta,Naman giwa ta fi karfin hargogowan yara,yaro maza gaexaya je kanemo
tsaranka,yarima Abdoul daya tilo, hutawan ka lafiya ranka yadede...
Duk wannan kirari da ake sheko mawa Yarima bashi yasa shi daga kai ya dube su ba,sai da ya
kwarari kusan mintoci 10 sannan ya daga masa kai a hankali,wanda inba ka kuresa da ido
ba,tabbas da baxaka fahimci yy wani Reaction ba.
Wani bafade ne ya baxa malilin malin sa yana zaman dirshan gaban yarima duba da ya fahimci
da bayani bakin yarima,Amma mulki da isah ta hana sa bude bakin. Ni dai Labban sa kadai
naga yana motsi sai kuma naga Wannan ba faden ya furta angama ranka ya dade Hutawan ka
lafiya...." yana fadin haka Prince Abdoul manan ya mike yyn da Fadawa nan suka tashi suna
mai mara masa baya.
Shiko wannan bafade da mikewan sa ya nufi Barayin Fulani wanda a hanyansa ta zuwa suka
hadu da Jakadiyya".
Sanar mata da sakon yarima yy akan yana so afara shirye² na tafiyan sa zuwa Zaria a satin nan
da yardan Allah". wanda yana sanar mata ya juya hadi da nufan barayin Yarima".
Itako Jakadiyya baki Uwar magana tuni ta juya hadi da komawa barayin Uwar dakin nata Fulani
don ta sanar mata da Tafiyan Yarima zuwa zaria,wanda su sam basu san mai zai kai shi can din
ba".
Niko Suhaimart ban samu farkawa ba sai can Wuraren 4pm. don lokacin tuni aikin mu ya wuce
sai kuma masu aikin dare sune suka amshe mu".
Waigawa nayi gyefena nan naga babu kowa don haka sai na tashi daga Zaune baki na na
dauke da addu'an tashi daga Bacci".
Kaman wanda aka mintsila na tuno da Rubutun da Sir Khaleed yy mun don haka ban tsaya
wata² ba na bude Hannun tawa ina mai kura dakwa² n idona don ganin mai ya rubuta mun".
Kirjina ne ta buga nan take,kara bude ido na nayi ina mitstsuke su don tunanin ko ba sa nuna
mun dai² ne,Amma still abun da nagani shine dai. Nan take Gumi ya fara karyomun,kwallah ya
ciko mun ido a sarari kam furtawa nake wayyo niiii...wayoooo ni Suhaimart, Sir Khaleed mai
yasa zaka cemun haka???? ko so kake dan Abincin da muke samu sanadin aiki a karkashin ka
shima mu rasa!!! Bakomai ni nasan a kwanannan watan Korana daga aiki yatsaya...Ina
maganan ne hadi da Zubar da kwallah,banji shigowar ta ba sai muryan Oummu Sulaym naji
tana cemun Suhaimart mai naji kina cewa ne? Meye Sir Khaleed din yy maki??? Kuka na rushe
mata dashi ina kwantar da kaina bisa kan kafadan ta ina furta Oummu Sir Khaleed ne,shikenan
zai jah mun sallama,yanxun in ankoreni ina xan je?".
Rungumo ni Oummu Sulaym tayi tana furta haba Suhaimart wlh ajiki na nakejin Babu abun da
zai faru babu wlh,meye wai Sir Khaleed din yy maki ne???.
kasa bata amsa nayi sai dai kawai ware mata taffan Hannu na nayi ina mai kawar da kai gyefe.
Bin Hannun nawa tayi da kallo hadi da Karanta kalmar kamar Haka: I LOVE U SUHAIMART!!!
DO U LOVE ME???.
Wani ihu mai hade da kara Oummu Sulaym tasa hadi da kankane ni tana furta wayyo
Suhaimart dina,yanxu tom mai zaki ce???.
Zaro ido waje nayi ina kallon ta tabbas ban taba yarda da Oummu Sulaym bata aiki da hankalin
ta ba sai yau, tom ita har tana ganin na amince masa? ina badani ba,ai Sir Khaleed sam ba aji
na bane,yafini kaman sama da kasa,ai Babban goro sai magogin karfe,Ana babbakan giwa
wake jiyo kaurin zomo?, Ae komai kwarya ce tabi kwarya!. Duk maganan nan a tunani na a zuciya nakeyi but unporturnetly a sarari neke ta zubo su".
muryan Sulaym na tsinkaya tana cemun" Maganan ki haka ne Suhaimart, tabbas Kwarya tabi
kwarya ne,Amma kuma kar ki mance ita Kwarya ta gari..?
Don haka ni sam ban goyi bayan ki janye kiki yarda da amincewar Soyayyar Sir Khaleed
ba,Amma zan maki Uzzuri akan kija masa aji na martaban ki ta ya mace. ta fadi tana mikewa
wanda da'ala Oummu fushi tayi akan maganata, sai da ta kusa ficewa ne daga dakin na
tsinkayo muryan ta tana cewa" Amma kisani K'awa ta wlh amincewar ki kan soyayyar Sir
Khaleed kaman taimakon sa ne zakiyi,don a halin yanxu Sir Khaleed yana bukatan taimakwan
mutumiyar kirki a rayuwar sa bana banxa ba". Sir Khaleed babu wasa a furucin sa da gaske
yake yana Kaunar ki,kuma so na ki zama uwar yayan sa,kisani ni ba karamar yarinya bace
tuntuni na dade da fahimtan hakan,duk da sunan shi miskili ne amma ya kamata tuni ki fahimci
hakan!!, Don haka ni baxan maki tilas ba,Suhaimart inkin kaunaci Sir Khaleed wlh zaki ga ribar
shi gaba,kuma komai kkyi ina maki Izirin yarinta".
Tana gama fadin haka ta fice daga dakin,yyn da niko da ido nabita da kallo,a sarari na furta,Wlh
sam baxan amince ba,sarai nasan Halin wannan bawan Allah mata nawa yasaka kuka akan
soyayyar shi agaban ido na".
ina sam ba dani ba,wai kina wani Zanga ribar shi,wani riba xanga dai asarah,don in Hajiya
Zaituna tasamu labarin nan ae wlh yanda ta tsani talakan nan sai tasa ankarar da dangin mu
duka...
Mtswww wlh Sir Khaleed kayi hakuri duk da nasan kawai yimun dai kkyi,inma tunanin ka ni yar
iska ce tom ba haka nake ba". haka na dingi maganganu na ni kadai ina mai mikewa don nufan
Bandaki nayo Alwala. Bayan fitowa na ne nayo Sallah dako idarwa na ban tsaya ko juran
Oummu Sulaym ba na biyo hanyar gida,a tunani na ma Sir Khaleed xai iyah sakawa a kamo ni
ta karfin tsiya. A hanya kam da zan fice gate ne na ci karo da Wata Zukekiyar Budurwa wanda
ashe karu ta haura 30 a