Showing 12001 words to 15000 words out of 40972 words
Chapter 5 - ZUMA DA MADACI Romantic Hausa Novels by Maman Teddy .pdf
masarautar Sarki Mai lafiya don
taga magamin Rayuwan nata ko tasamu yau tayi Baccin dadi.
*___________________________*
Kaman daga sama naji muryan Oumma na tana furta kiran Sunana Suhaimart" tashi kije dakin
ki ki kwanta kinji. ta fadi tana dan girgixa ni. a Hankali na bude darararan idanu na hadi da
Sauke su akan nata. Cike da muryan mai Barci na furta Oumma Har kin tashi". Murmushi
Oumma tayi sannnan taban Amsa da Ehhh Suhaimart na tashi, tashi kije ki kwanta Allah yayi
maki Albarka kinji. Ameen na bata amsa sannnan nafara shurin mikewa daga Kwancen da
nake. Cike da muryan Wanda sukayi shaye² sukayi tatul naji Muryan Zaid yana cemun Kehhh
Suhaimart ina kudin dan Uban ki. Shiru nayi don bani da amsan bashi. aiko ganin Haka yasa
shi nufo ni da niyan dukana. Oumma na ne tayi saurin tashi daga zaune ta dauko Mucciyan
gyefen ta ta nufo shi dashi,ganin haka yasa shi fucewa daga dakin yyn da Oumma na ke bin shi
da zagi dacewa ya kiyayeni. shiko Zaid duk Rashun jin shi baya son yaga bacin ran Oumma
shiyasa ya fice daga gidan. Niko Zama nayi ina mai Rafka uban tagumi har Oumma na ta shigo
dakin nata. Suhaimart maza ki kwanta ni yanxu xan je gidan Tani na ranto mana Bashin abun
da xamu ci,kan karshen wata a buyaki Albashin Aikatau dinki sai mu biya". Tom" Oumma na ki
dawo lafiya". Allah yasa sai na dawo. Ammie tace hadi da ficewa. Ina a zaune fitan Ammie ba
wuya sai ga Ya Zaid ya shigo gidan. Keni ne xakisa Oumma tazaga aiko yau sai naci ubanki a
gidannnan..... Wani wawan Mari ya kaimun,wanda sai da yasani na kifah sai jini da yafara
xubomun ta hanci da baki. Duka na yake yana karawa,nan na hau ihu ina mai Rokon shi kan ya
Hakuri nan da gobe xan samo masa,amma ko saurarona baya yi,sai uban duma na da yakeyi
kaman sa'ar sa. A haka ya Haujah mun Hannu har wajen soron gidan mu.
*******************************
Yanxu Huday ya zanyi ni bansan ma ta yaya zan sanar mata da soyayya ta a gareta ba.Dariya
Huday yy yana mai kallon yanda gabaki daya Khaleed soyayya ta gama sauya sa lokaci guda".
Hmm tom yanxun bari mu gani? Huday ne yace yana mai tunano mawa aminin nashi mafuta.
Year yanxun dai Ka kirawo Mhiss Caterine kace kana son bama wannan Maaikaciyar Aiki ne".
Kallon Sa Khaleed yy kan daga bisani yace ohk. Wata ma'aikaciya ce taxo wucewa mai irin
kayan Suhaimart, gaishe su tayi wanda nan Khaleed yace Tayo masa kirar Shugaban tasu. cike
da girmamawa ta juya dai² Oummu Sulaym na shigo wa don ta karke aikin Suhaimart da ta tafi
ta bari. Barka da Gida Yallabai". Kallon ta sukayi kawai sai suka kware da Dariya. wanda ya
sanya ta tsayawa tayi shiru tana kallon sa dama suna dariya haka? tom meye Abun dariya a
tare da itah. Huday ne cike da muskilanci yace mata Halan mu mata ne daxaki ce mana Barkan
mu da gida"? Tom ai yanxu xamu fice Madam. Ita dai kasa basu amsa tayi sai tace masa toh
kayi Hakuri kuskuren Harshe ne. Ohk Khaleed ne ya bata amsa a dakile. mai kikaxoyi nan?.
Ehhh yallabai dama dama² uhmmm naxo na karke aikin Suhaimart ne". Kallon ta Huday yy
sannan yace ita ina Take mai aikin? Umm bata jin dadi ne shine yasa ta koma gida". Ai dajin
Suhaimart babu lafiya tuni Khaleed ya mike daga kwancen da yake,cikin Sauri ya furta mai
yasame ta"? Ba wani ciwo ne ba sosai. uhmmm ina ne gidan su sai muje muga lafiyan ta,ko
aikin da tayi mun ne yasa ta ciwon. Bude Baki Oummu Sulaym tayi sai kuma tace tom Ranka ya
dade a cikin Zaria take". Mikewa Huday yy yana furta a gsky ya kamata mu duba ta Khaleed.
yanxu je ki dakko komai naki muna jiran ki a Moto ki same mu,don ke Zaki kai mu". Tom
angama ranka yadade ta fadi tana Rawar jiki ta juya. Dariya Huday yy yana cema Khaleed see
dis girl like a jorker. kara kwashewa da dariya sukayi suna mai kwasan keys din su don su nufi
Parcking space............
Labarin ZUMA DA MAD'ACI ta kudi ce zaki turo #200 VIP, idan SPC #300,NORMAL #100 duka
ta wannnan number 08081202932/09137392680.
*Maman teddy*
https://www.facebook.com/100186388252056/posts/100188104918551/
*Typing...✍*
*ZUMA DA MAD'ACI*
_*(True love never end...)*_
Na
*Maman teddy*
*Episode 9 - 10*
*_____________________________*
*ALHERI WRITERS ASSO.️*
*A.W.A*
```Kungiya daya tamkar da dubu,kungiya masu aiki da nazari da ilimi,Alheri sai d'an Alheri```
*______________________________*
مسب* الله رلا نمح رلا *ميخ
Haka suka tattara kayan su suna mai nufan Farfajiyan gidan suna mai jiran isowan Oummu
Sulym. Itako Oummu Sulym tunda ta nufi Sasan su ta Ma'aikatan gidan sam ranta yaki
natsuwa,tabbas tanaji a jikin ta kaman da wani dai abun ne kasa". Haka ta tattara kayan ta a
jakanta sannan ta nufo filin Harabar gidan da ya kayatu da Abubuwan more Rayuwa komai na
filin abun burgewa ne da ban sha'awa... Nufo su tayi a tafiyan ta na halin ko in kula,don baxaka
ce Oumu sulaym wai budurwa ce ba. Ba Ruwan ta ita tafiyan ta kawai take babu Ruwan ta da
komai. Binta da Kallo duka sukayi sannan da isowan ta Huday yy murmushi gami da fitowa
yana kokarin bude mata Murfin moton. Murmushi tayi masa tana mai furta masa Ranka ya dade
Ae na iya budewa,koba haka bane tafadi tana kokarin bude murfin moton wai ala dole xata
nuna masa. Dariya yayi yajah ya tsaya yana kallon ta har ta bude sannan ta Waigo tana furta
Ranka ya dade kagani?. Nan yayi mata tumb da babban yatsa alaman da kyau. sannan ta
shige tana dariya. Yana mai Rufo mata murfin moton.
Shiko Sir Khaleed gaba daya sun fara bashi haushi,shi dai har ga Allah ya kosa yaga hurril
aynin shi. A haka cike da zalama yajah moton yana furta Ibeg muje Huday i'm eager. Dariya yy
yana furta Okay Rumio,ka kosa kaga Juliet ko,don't worry ai mun kusa isa kaganta.
Haka dai yayi Dariya da jin maganan Da Huday ya fad'a masa,nan ya furta masa waye wani
Rumio da Juliet,aeni a Son ta nafi Layla majnun....
Dariya duka suka saka.yyn da Oummu Sulaym ta baxa kunni don ta nadi gulma ta sanar ma
Aminiyar nata Suhaimart. Amma sai dai kash ita sam tagaxa gane inda zancen su ya dosa ba.
Ita dai kawai abun da take ta nanatawa shine Layla majnun gasky dole ne ta tambayi Suhaimart
wannan maganan wai Layla Majnoon don ta fahimci inda suka nufa.
A haka dai ta cigaba da nuna masu Hanya tana kwatanta masu inda zasu shiga ahaka har suka
isah cikin Zaria city.
"Duka na yakeyi kaman Zai Karni don kiyayya,yyn da tun ina gani har na soma ganin
duhuwa,saukar marin da Oumma na ta wanka ma Zaid yasa ni xubewa yyn da sama² na kejin
hayaniyar Muryan Oumma na tana Zube masa Bala'i da hargoguwa tana mai Zubar da Hawaye
da kirar Suna na". Suhaimah" Suhaima na bude idon ki ki kalleni".
Girgixa ni take amma ko numfashi bana iya fitarwa don bana numfashi. Hawaye ne yafara bin
kuncin Oumma na,dagowa tayi tana kallon Zaid da ya tsaya ya rasa duk wani abun yi,don shi
sam baya a hayyacin sa yy mun wannan duka,tun da a bige yake. Ficewan shi yayi yana
maganganu kasa² yyn da Oumma na tayi saurin fita daga soron namu tana taro me Napep
daga bakin Hanya. nan ta ciccibe ni sannan me Napep yajah muka nufi Asibitin A.B.U hospital.
Wanda da isan mu nan cikin Gaggawa Nurses suka amshe mu hadi da nufan Emergency room
dani.
Itako Ommu Sulym a haka suka dinga kurdawa har xuwa Unguwan namu wanda da shiganka
basai anfada maka ba kasan unguwan talakawan tilis ne,amma ko a unguwan gidan mu yafi na
kowa talauci don Abun ma yy muni matuka. Shikuwa Da Sir Khaleed tun isan su Unguwan yake
tunanin dama da akwai Unguwa masu fama da Talauci irin haka?" A gsky shi sam bai san da
hakan ba,indai ma kam hakan talaucin take tom bai taba ganin talauci ba a rayuwan shi.
"Dako A kozo dai² gidan mu ne Oummu Sulym tayi saurin cewa Sir Khaleed mun zo fah".
Tsayawa yy hadi da yin parking din moton nashi,sannan yace mata Bismillah". A hankali ta bude
side din ta gami da fitowa daga moton tana mai nufo gidan namu".
" Suko Khaleed da Huday shiru sukayi babu mai iya furta kanzil", Musamman Khaleed da a
zuciyan shi yake furta Sorry Hayatee na". Nan da yan lokaci kadan baxan barki ki zauna a cikin
wannan Talauci ba". Zaman Nageria ma baxa muyi ta ba inshaallh". Abun da Khaleed bai sani
ba shine ba a zuciyan shi yake mgnan ba a sarari ne". Huday ne yy murmushi cike da Tausayin
Aminin nashi,duba da yanda ya fada soyayya ga Wannan yarinya,soyayya makauniyya wanda
sarai yasan Khaleed bai taba fadawa duniyar irin wannan Son da yakeyi ba. gashi yasan irin
soyayya r Khaleed don inyafara baijiin bari sam. Shiru yy yana Aiyana Allah yasa Yarinyan nan
ta Kaunace shi kar ta Wahalar da Abokin nashi,don a halin yanxu Khaleed ya rasa wannan
yarinya bb shakka komai na iya faruwa dashi".
Tabo shi Huday yayi yana mai furta masa A'a Khaleed ka natsu don Allah. Inshaallh Suhamart
Matar kace zata kasance ma yanda kake buri,kuma inshaallh zaka sanyata cikin Farin ciki
kaman yanda kake mafarkin gani".
Murmushi Khaleed yayi cike da jin kaunar Aminin nashi yace Na gode Huday da Addu'ar ka
gare ni". Kafin Huday yace masa Wani abu ne sukaji Muryan Oummu Sulym tana cewa Sir
Khaleed wlh mun zo arashin sa'a don gidan ma a rufe take basa nan dukan su". Saurin kallon ta
yy don lokaci guda idon shi ya sauya Kala daga Fari zuwa jahhh..." Nan take Zuciyan shi tafara
kisima masa kodai Ciwon nata ne yy worst?. Muryan Huday yaji yana bata amsa da Ohk
Badamuwa, Amma bakya tunanin Ciwon nata ne yy tsanani???. A'a ranka yadade inshaallh
komai zai zo da sauki".
Ohk Allah yasa,shiga mikai ki gida".
da jin haka Oummu Sulym tayi dariya hadi da cewa" A'aa Ku tafi ai nan unguwan mu ce,yanxu
zai kai gida inshaallh ". Okay tom shikenan mun gode". Bakomai ranka yadade". Haka dai suka
tafi suka bar Sulaym tsaye don ita kanta tana mmmkin inda Suhamart ta tafi da wannan
Yammaci haka". haka dai ta tsaya tagama kusifa abubuwa kan daga bisani ta fara tattaki zuwa
layin su".
Niko tunda nasamu kulawar kwararrun likitoci tuni na dawo hayyaci na,yyn da Suka yimun
Alurar Bacci Hadi da saka mun drip. Oummu na kam taso daga hankalin ta,babu abun da take
tunani sai Kalmar Ga Amana ta nan". Safa take da marwa har Wata nurse da doctor suka fito.
Cikin Hanxari tasha gaban shi tana mai furta Doctor ya jikin yarinyan nawa?. Kallon ta Doctor n
yy cike da tausayi don ko ba'a fada masa ba yasan suna cikin talaucin Rayuwa. Ki kwantar da
hankalin Mama inshaallh ba abun da zai sameta,kinga yanxu ma tayi Bacci". Hamdalah Umma
na ta hauyi hadi da yima Doctor n Godiya,sannan ta juya hadi da nufo Dakin da aka kwantar
dani tana mai tsaye bakin window don ance ba'a bukatan kowa a ciki. Haka Oumma na ta dinga
kallona ta jikin tagan,yyn da Wasu Zafafan Hawaye ki bin fuskan ta,bakin ta kam harda ma
Zuciyan ta Addu'a kawai take mun.
A haka fiye da Awanni sannan ta nufi farfajiyar Asibitin don tayo Alwala taga batar da sallah don
a lokacin har an soma kirar Ishaa'i.
Niko sam ban farkaba sai Wuraren 8:30pm. Mikewa nayi cike da cije labbana don wani irin
tsami danaji jikina yy gaba ki daya. Addu'a nakeyi wanda dai² idona na sauka kan file dina da
aka ajiyemun gyefen Gadona saman drower".
A hankali na kai Hannu na hadi da dauko File din na bude ina mai duba rubutun dake kan farar
takardan. Wanda duk da ban da wani ilimin zamani,makaranta ma na gomnati nayi,wanda a SS
2 Ummma na ta dakatar dani saboda rashi da ya ishemu akan na soma zuwa aikatau.
Duk da Hakan ina da dan ilimi na na boko dai². Karanta takardan na somayi nan take gaba na
yayanke yafadi don kirgina sai da Naji bugawan ta. Cigaba da karanta takardan nayi yyn da
hawaye kebin kuncina. Wanda sam banji shigiwan Doctor Zainab ba sai muryan ta da naji tana
kirar Sunana" Suhamart " Suhamart ar you okay?". kina ganina da kyau ko??.
Goge kwallah nayi ina mai kakalo murmushin da yake a jini na ne nace mata ehh Doctor ".
Yauwa mashaallh. Nan ta zauna kusa dani tana mai fuskantoni hadi da saka hannun ta ta amshi
file din" Shiru kusan minti 5 babu wanda yace komai,kowa da abun da yake kisimawa a zuciyan
shi.
Suhamart... " kaman daga sama Naji muryan Doctor tana kirar sunana" Kallon ta nayi akaro na
biyu na kuma ce mata Na'ammm...!!!"
Suhamart kiyi hakuri komai da kk gani akan file din ki kisashi a mixanin Kaddaran ki". Komai
Allah keyi,kisani ana doraki akan magani zaki warke,kuma koda an vata maki rai kidaina
Damuwa plz, idan kina sawa a ranki to tabas xaki ringa xubar da jini ta hanya daban², kaman
Ha6o da sauran su: Don haka kisani Suhamart zaki warke inshaallh ". wani irin mun murmushi nayi mata mai dauke da fassarori da dama, kana nace da ita Doctor
kina ganin zan warke? wannan Ciwon fah ba karami bane,kuma sannan koda zan warke Doctor
ina zan samu wa'annan zunzurutun Kudi???.
Nan Hawaye ya cigaba da mun Ambaliyya akan fuska ta. Wani irin tausayi na ne yagama kama
likitan a hankali ta kai Hannun ta tana mai dafo kafada ta da cewa" Kiyi Hakuri Suhamart kije ki
cigaba da huddan ki da mutane,bb abun da Zai kuma samun ki,kuma ciwon baxai taso maki ba
sai bayan nan da kaman watanni Uku. Kuma nasan kafin nan kinsamu kudin Maganin. Ga
wa'annan magungunan su zaki ringa amfani dasu kan wannan lokaci ". Ta idda maganan tana
nuna mun wasu magunguna,nusawa nayi ina mai amsan maganin sannan na kalleta ina mai
cemata" Doctor don Allah ina so ne kimun wani alkawari daya ina zaki iyah". Cike da bata
kwarin kwiwa irin na likita da majinyaci tace mun fadi maganan ki Suhamart.
Nisawa nayi kana daga bisani na ce da ita" Doctor don Allah so nake ki rufe wannan sirrin wani
ciwo na,kar ki sanar ma kowa dagani sai mahalliccin ki,saboda sam bana son Hankalin Oumma
na ya tashi,wlh itama ba lfy ne da ita ba". Na fadi cike da matsanancin damuwa". Girgixa kai
Doctor tayi kan daga bisani tace nayi maki Suhamart, amma don Allah duk bayan wata 1 kiringa
xuwa ina dubaki naga lfyn ki kinji"?
Daga mata kai nayi ina dan murmushi na jin dadi. Haka ina A zaune tayo kirar nurse don ta dan
gyarani hadi da mun bed making. Doctor Zainab ne ta ciremun Drip din Hannuna don ya
kare,nan wannan nurse ta fara aikin ta.
Niko jirgawa kadan nayi duk inda na muskuta ta gyra har ta gama aikin ta. Dai² Oumma na na
shigowa gaisawa suka yi da Doctor sannan Dr. Zainab ta fice daga dakin tana mai kara sanar
mawa Oumma na da Na sauki sosai kilan mu amsa sallama a daren nan .
Cike da jiin dadi Oumma na ta matso gareni tana furta Sannu Suhamart!!! ya karfin jikin
naki???.
Murmushi nayi mata sannan na furta Oumma na naji sauki sosai, don A yanxu Oumma nafi
dama jin karfin jikina. duba ki gani !!!... na fadi ina washe mata fararen hakora na". Dariya Oum
Rabi tasa cike dajin dadin ganina ta hau cewa" Kai mashaallh" Alhmdllh.
Nufo ni tayi tana zama gab dani,sannan ta bude kwankwatstsayan kwanon da ta tahomun da
Tuwo miyar yauki a cikin ta". Kallona tayi hadi da furta Suhamart maza kici abincin nan Ko
kyakara jin karfi jikin ki. Murmushi nayi ina daukan ruwa na wanke hannu na a wani Bowl
sannan nasaka hannu na da zamman fara cin Tuwon". Wani magana ne yafara dawo mun a shekarun baya da suka wuce!!!.
Ga Dumamen ki nan ki ci". Tom Oumma Zaid ina spoon?. Hhhhhhh Zaid ne ya kwashemin da
dariya,yyn da Oumma ta galla mun Harara da cewa kehhh bana son shashanci,idan kinsaba
komai naki na dabi'un nasara,tom nan mu koyi muke da addinin musulunci maza kisaka Hannu
kici da yatsun ki kar ki fusata ni". Ya Hakuri Oumma na bata amsa yyn da nake tsoma hannu na cikin kwanon abin cin.
Murmushi nayi gami da kallon Oumma na da tayimun kurr da ido,a sanyaye na fara kai loman
tuwon baki na.
Sai da na kammala sannan na ajiye kwanon tuwon ina Mai Hamdalah ga Allah,sannan na kalli
Oumma na ina mai Furta Oumma na I luv u".
Murmushi tayi mun tana mai kallona da cewa" ohh ni Rabiatu!!" Suhamart ni sam nafada
making bana jin wannan yaran naki fah".
Okay tom Oumma ya kamata mu amshi sallama don banason kwanan Asibitin nan,suce a
biyasu Kudi n gado kuma.