Showing 6001 words to 9000 words out of 52880 words
fita Wai akwai jariri agidan Nan maganganu suka fara yawo hankalin baffa yafara tashi musamman da zancen yafara yaduwa Wai 'dan na Anano ne tunda dai ba Wanda zai haihu a gidan.
Zaune suke a tsakar gida yau duk sunyi jugum jugum bamai magana Sai Inna daketa aikin Kai kawon girkin dare datakeyi Anano kuwa tana zaune tana yiwa Inna wanke wanke jiki a sanyaye sbd tun Daren jiya taji hirar Inna dake bawa baffa shawarar akai yaron gidan Mai gari ace tsintarsa akayi.
Cikin sanyin murya baffa yace,
Idan muka kaisa mukace tsintarsa mukayi kenan mun bada damar daza'a yarda da zargin da ake Mana sbd zaaga meya Hana tun farko mukaisa Saida aka ganomu,
Kawai dai na yanke shawarar aikasa can binni gidan marayu kamar yanda Yusuf yace tun farko.
Da wannan tunanin ta kwana ta tashi sosai taji hankalinta yatashi sbd tausayinsa dakuma qaunarsa dake maqale aranta.
#vote
#comment
#share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_
*16*
Ahankali baffa ya 'dago ya kalli yanda take aikin cikin sanyin jiki duk saiyaji qaunar yarsa da tausayinta Dana yaron ya qara shigarsa ya bu'de baki ahankali yace,
Zo Nan Anano.
'dauraye hannayenta tayi ta taso ahankali ta zauna kusadashi ya kalleta dakyau yace,
Anano bazamu bar yaron nanba a gidan Nan sbd mumaganganun dake yawo zasu Bata Miki suna su Bata Mana zuria shiyasa na yanke shawarar Yusuf da Usman zasu kaisa binni gidan marayu.....
Kaka tasake ahankali batareda yakai qarshen zancen nasaba.
Shiru yayi Yana sauraron kukan nata ganin batada niyar dainawa yasa ya dafa kanta yakira sunanta.
Bata 'dagoba saidai tadan tsagaida da kukan.
Cikin tsananin qaunarta dake rinjayarsa kowane lokaci yace,
Anano wlh da inada wani zabin bayan wannan da bazan rabaki da 'dannan ba sbd koba komai mun taimakesa Kuma bamusan baiwar da Allah 6oye cikin alamarinba saidai vanida wani zabin kodan gudun lalacewar sunanki.
Cikin kuka ahankali tace,
Baffa Dan Allah karka biyewa maganar mutane ka fasa abinda kayi niyya na taimakawa marayan Allah dabaisan kansaba.
A qule Yusuf yace,
Ke dallah ki rufe Mana shegen bakinki badan shegen iyayinki da rawar kanki ba da duk haka Bata faruba,
Wannan yaron yagama barin gidannan Dan wlh bazai zaunaba.
Cikin takaici Aliyu ya kar6e zancen da cewa,
Wama yasani ko shegene uwar tasa ta Haifa.
Katsesu baffa yayi da cewa,
Koma dai meyene shi yaron bayada laifi tako Ina Kuma kamar yanda Anano tace munyi niyar taimakawa sabida Allah Kuma zamuyi.
Tunda suka fara magana Inna ko inda suke Bata kallaba sai lokacin takallesa cikeda mamakinsa tace,
To yanxu abinda takeson shi kake nufin za'ayi kome?
Eh'''yafada Kai tsaye tareda kallon jafar da tuni jaririn ke hannunsa Yana 'dan jijjigasa sbd dagashi Sai Anano ke saukarsa a gidan Sai Inna idan zatai Masa wanka Amma ko baffa Sam bai ta6a daukarsaba iyakaci dai Yana tausayinsa shima sbd ananonsa nasonsane kawai.
Cikin sakewar fuska yace,
Jafar meye shawararka akan hakan?
Kallon yaron yayi yakuma kalli Anano datai zuru cikin hawaye Sai yaji tausanta da 'dan yakalli baffa yace,
Baffa shawarata 'dayace
Komai zakayi kayisane domin Allah badan waniba kokuma badan abinda wani zai fa'daba..
Murmushin qarfin hali baffa yasaki cikin jinjina Kai yace,
Usman da jafar ku shirya zuwa jibi zamukai Anano gurin gwaggwonta tareda yaron zuwa wani lokaci idan komai ya lafa saita dawo.
Ajiyar zuciya Inna ta sauke duk dai bahaka tasoba tasone su yarda qwallon mangwaro su huta da quda Amma ko ahakan da sauki sbd itadai dama damuwarta zaman yaron ne agidan bataso ga ananon da shegen taurin Kan tsiya sbd samun daurin gindi daga baffan.
Yusuf da aliyu kuwa miqewa sukai suka ficewarsu sbd takaicin hukuncin da baffan yanke na barin yaron.
Anano kuwa jikinta ne yayi sanyi ta matsa ta riqo hannun baffan ta kallesa hawaye na gangaro Mata tace,
Baffa Allah zai saka maka da mafificin abinda kayi Koda a bayan ranka ne.
Shafa kanta yayi yace,
Allah yabiyani ta hanyar kawo farin ciki da haske Mai dorewa a rayuwarki ananona.
Jafar ne ya katse yanayin nasu na shaukin uba da 'ya ta hanyar cewa,
Yaron haryanxu bashida suna..
Fuskar Anano baffa ya kalla yace,
Anano za6ar Masa suna.
Sunkuyar dakai tayi cikin fargaba tace,
Abdulshakur..
Su Inna sunaji suna gani baffa yasa jafar ya Kama rago 'daya ya yanke aka ra'dawa yaron suna abinma Sai ya daina Basu takaici sbd ganin yanxu Kam su baffa kawai wahalar ta fasha sukam sun cire hannunsu musamman aliyu daya tsani Koda ganin yaron.
Kafin jibi ranar tafiyar tayi gata da kulawa sosai baffa da jafar suka shiga nuna Mata harma da Usman yanxu da ananon ke basa tausayin ganin Allah ya 'dauki son abinda batada alaqa dashi yasa Mata kamar jininta saiyake ganin hakan da wani 6oyayyan sirri daga Allah.
Ranar dazasu tafi sosai tayi kuka kamar ta tafi kenan musamman dataga Inna na farin ciki da tafiyar tasu Dan har Allah Allah take su wuce.
Basu shiga motar mandeba sbd gudun tsegumi Kai tsaye doguwar tafiya sukai da qafa har bakin babban titi kafin suka shiga motar shiga yola.
Tunda suka iso taji hankalinta yafara tashi Dan hakanan takejin fa'duwar gaba.
Direct wata qaramar unguwar talakawa suka nufa cikin adaidaita jafar dayasan gidan Yana nunawa Mai napep 'din inda zaibi.
Har bakin kwanar layin gidan aka ajesu Nan baffa ya biyasa suka gangara suka shige lungun.
Ba wata tafiya sukaiba suka iso gidan jafar ne agaba Yana kwada sallama suna shiga Dan qaramin tsakar gidan asiya matar qanin mijin gwaggon daya rasu ta fito 'dakinta tana Sanya hijab tana ganin jafar ta washe baki tana musu sannu da zuwa tareda 'dauko musu tabarma tana cewa,
Gashi kuwa gwaggon batanan tanacan gidan datake aiki rasuwa akai musu matar gidance ta rasu gurin haihuwa.
Allah sarki Allah yaji qanta....cewar jafar dake qoqarin juyawa waje yafadawa baffa da Usman gwaggon batanan.
Kallon hijabin anano asiya tayi ganin Sai muqu muqu take batason asan meyene aciki tace,
Ananon gwaggo bazaki zaunaba.
Qoqarin zaman take jafar yasake shigowa Yana kallon asiya yace,
To Wai zamu samu Wanda yasan can gidan da gwaggon take Sai akaimu?
Eh Bari nakira Bello yananan waje saiya kaiku yasan gidan.
Qofar gidan ta nufa saidata gaisadasu baffa kafin ta kirawo bellon a gidan maqwaftansu inda suke kallon qwallo 'dakin abokinsu.
Sallama sukai Mata suka nufi titi Bello Kam Yana tare Mai adaidaita kwatancen gidan yayi Masa Dan shikam baiso ya rasa kallon qwallonsa Dan yau wasar na zafi sosai.
Yana fara kwatancen Mai adaidaita yace ya gane sbd gidan ba wani a boye yakeba idan kaje anguwar danma masu adaidaita da mashin Sam basa shiga layin Dan mugayen soldiers din dakecin uwarsu na gadin gidan.
Nesa ka'dan da gidan ya tsaya ya nuna musu gidan da hannu suka biyasa ya juya suka nufi gidan kowannensu gabansa na 'dan tsinkewa sbd ganin gidan da akace nanne ga sojoji dasuke hangowa tun daga nesa.
Wangale qaton gate din sukaga anyi wasu jibga jibgan motoci suka fito aguje kamar zasu tashi sama ta qarshen ita ta tsaya sauran sojojin dake qofar gidan suka fa'da ciki aka figa da qarfi harsaida su baffa suka daka wani mugun tsalle suka ra6e gabansu na qarasa tsinkewa Dan Anano tuni taji ta tsinke tana adduar Allah yasa ba anan gwaggon zata zauna da itaba sbd Allah yagani arayuwarta ba abinda ta tsana take tsoro irin soldier.
Baffa ma Kam wani irin mugun yawu ya ha'diye na tsoro da tausayin ananon Dan shima Kam Yana tsoron kaki( kunsan Fulani da tsoron soja😂😜 just kidding)
Usman damashi tuntuni atsure yake tunda suka iso yaga mutane sunyi Masa yawa Dan harwani jiri jiri yake gani Dan baita6a fitowa birni duk cikinsu jafar ne kawai Mai zuwa shima sbd visiting din ananon ne idan tana makaranta.
A darare suka Isa bakin gate din kusan atare suka 'dan sauke ajiyar zuciya ganin ba soja ko 'daya days saura.
Cikin Yar fargaba jafar ya qwanqwasa qaramar qofar qatoton gate din dayake jabiru na kusa Yana hamdalar samun yancin aikinsa oga saheeb Yakoma da gayyar sojojinsa.
Bu'de qofar yayi Yana ganinsu ya fito tareda jawo qofar Yana kallonsu a 'dage sbd daka gansu kaga fulanin qauye futuk ananon cema ta'dan banbanta ka'dan acikinsu.
Ganin irin kallon dayake musune yasa jafar jiki amace yace,
Dan Allah gwaggo hinde muke nema.
Sake kallonsu yayi dakyau kafin yace,
Wa za'a cemata sunxo?
Kacemata baffa salisu ne yayanta daga qauye tareda Anano.
Juyawa yayi yashige tareda maqala sakata ya nufi babban part 'din oga saheeb.
Zagayawa yayi ta qofar baya inda 'dan qaramin boys quarter din part dinsa Wanda ke 'daukeda Palo 'daya da room daya Sai toilet.
Ta qofar kicin din part dinsa zaka it's fadawa direct palon gwaggon Wanda anyi hakan ne Dan aikinta basaita zagayo ta qofar paloba Kuma nafeesa ce tasa akai Mata hakan sbd tsananin qaunarta da gwaggon hakama shima saheeb sosai Allah yasa Masa qaunar gwaggon da ganin girmanta.
Qwanqwasa qofar palon zaiyi saigata ta fito zataje can 6angarensu mum asee.
Da mamaki take kallonsa tace,
Mal jabiru lafiya naganka nan....
Baqi kikayi sunce baffa salisu da anono ne koma meye sunan na manta....
Da sauri ta nufi gate din cikin farin ciki dakuma fargabar Allah yasa lafiya wannan zuwa haka.
Shigo dasu tayi har cikin boys quarter palonta inda baffa daqyar ya zauna takawo musu ruwa suka gaggaisa baffa yace,
Dagacan muke gidanki aka kawo mu Nan.
To hamma salisu Allah dai yasa lafiya.
Anano ya nuna Mata ta waigo Sai alokacin ta lurada 'da ahannunta.
Zaro idanuwa tayi tana sake kallawa danta gasgata idanuwanta tace,
Na boni ni hindatu menene wannan ahannunki Anano.
Ba yanda kike tunani bane Nan dai yayi Mata bayanin komai ya 'dora dacewa,
Nakawota da kainane danta zauna agurinki idan komai ya lafa saita dawo.
Badan zuciyarta tagama aminta da zancen 'dan bana Anano bane jiki amace tace,
To shikenan zanyi magana da Mai gidan idan ya amince saimu zauna anan idan bai aminceba zamu koma gida Dan dama jiya da'akai kwana bakwai da rasuwar Mai 'dakinsa naso tafiya yace nayi zamana anan harsai yace na tafi.
Ba yanda bataiba dasu su tsaya suci abinci sukaqi musamman Usman da yake a firgice kamar ace qyat ya ruga da gudu.
Har titi suka rakasu suka tafi Anano da baffanta kamar karsu rabu musamman dayaga tana kuka ahankali.
Tundaga gida dama gwaggo ta kar6e 'dan tagoyasa shiyasa Koda suka juyo ananon ke tafiya ahankali tana share hawaye jitake kamar karta koma gidan.
Suna shigowa direct part din mum asee suka nufa Dan Inna ta gabatarda ananon daidai zasu shiga Kamal shikuma yafito cikin sauri zai fita saiji yai yayi karo da mutum ba zato.
Please ku ringa saurarawa kuga menene zai faru kafin ku ringa magana akan abinda yadace da Wanda bai daceba afterall karku manta novel ne is not reality so Dole wasu abubuwan zasu banbanta da reality so please take note#no bad comments ko Kuma judgen abinda bakusan qarshensa ba Dan bakusan me writer ta shirya rubutawa agaba ba...
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_
*17*
Ja baya yayi da sauri cikin 'dan 6ata fuska Yana qare musu kallo.
A 'dan ladafce gwaggo tace,
Yi hakuri kamalu Bata lura dakai bane baquwace duk a takure take shiyasa.
Kallon ananon yayi tundaga sama har qasa Nan take idanuwansa suka kyallo Masa kyanta da dirinta dazai fita matuqar tasamu kyakkyawar rayuwa musamman dogon hancinta daya qarawa fulani face 'dinta kyau da tsari.
Wani gajeran murmushin gefen baki yasaki tareda 'dan sakin fuska ya maido kallonsa kan gwaggon yace,
Baquwar waye cikin gidan?
Washe baki gwaggo tayi tace,
Eh wlh 'yatace 'yar gurin yayana da muke uwa 'daya uba 'daya tazo guri nane Zan kaita ta gaida hajiya babba.
Wucewa yayi da sauri sbd Kiran daya shigo wayarsa Yana cewa,
Ki shiga idan nadawo xan gaisa da ita.
Murmushi gwaggo tayi sbd Sam kamalu yafi yayansa saheeb sakewa dason mu'amala da mutane Kuma gidan kaf yafisu rashin qyamar mutane Ammafa kaf yafisu rashin imani da tausayi Dan komai na uwarsa mum asee bai baroba.
Itadai Wani yawu Anano ta ha'diye daqyar tareda saurin sauke kanta qasa sbd wani kallo daya jefeta dashi daya mugun fa'dar Mata da gaba.
Da sallama suka shiga palon Nan Anano taga kyau da tsari tareda uwar dukiya na aka narka a palon ta sake sauke kanta qasa sbd itadai zuwa lokacin jitake Sam Zama a hannun gwaggon yafita ranta sbd yanda takejin fa'duwar gaba da wani irin tsoro irin yanda ta riqa ji lokacinda qaddarar samun abdulshakur zata sameta,.
Kicin gwaggo ta nufa gurin asabe suka gaisa tace,
Ga 'yata na kawo ta gaida hajiya
Anano matso gaida asabe itama aiki takeyi anan 'din.
Cikin sanyin murya tace,
Ina wuni.
Lafiya qlau ya Kika baro mutan gida?
Lafiya qlau'''"tace atakaice.
Saukowar mum asee ne daga sama yasa gwaggo fitowa ananon na biyeda ita kamar jela suka zauna qasan kafet gwaggo na sake gaisawa da mum asee 'din itama Anano murya na rawa ta gaidata Sai alokacin mum asee ta lura da ita ta tsaida kallonta akanta tsawon mintina ka'dan kafin ta 'dauke Kai zuwa kallon tv tace,
Gwaggo hinde wacece wannan Kuma?
Hajiya 'yatace tazo daga qauye sbd wata Yar matsala data samu acan shine nakeson koza'a Kira abdulshakur a sanar Masa zankoma gida.
Qaramin tsaki mum asee taja batareda tasake juyowa gurinsuba tace,
Basai ankirasaba sbd ba da'dewa zaiyi yadawoba kuje idan yadawo kinyi magana dashi koba komai Ina neman sabuwar Mai aikin dazata riqa kularmin da tsaftar Nan sbd asabe ayuka sun fara Mata yawa batamin yanda nakeso.
Hawayen takaici ne suka taru a idanun anano Jin Wai zatai aikatau agidan.
Gwaggo ma jiki asanyaye tace,
To shikenan hajiya Bari muje ta'dan huta taci abinci zuwa gobe tafara aikin.
Bata kallosuba bare ta amsa taci gaba da abinda takeyi na qoqarin canza tashar DStv.
Jiki ba qwari suka miqe suka koma dakin gwaggo
Daqyar tasa ananon taci abinci tayi sallah tasakeyin wanka gwaggoma tasauke abdulshakur tayi Masa Anano. Tabasa madararsa dasukazo da ita ta fulani.
Washe gari tunda safe mum Asee ta Aiko aka Kira Mata ananon jiki asanyaye ta tafi
A dining ta tarar da ita batareda zaune tareda wata kyakkyawar budurwa black beauty tana waya,
Batareda takalli gefenda ananon take ba tace,
Asabe ki nuna Mata ayyukan dazata Kama Miki dasu Kuma ki tabbatarda kin koya Mata Dan kartamin 6anna dankifi kowa sanin bana 'daukar qaddara.
Tunda asabe tafara nuna Mata ayyukan dazata yi taji hankalinta yayi mummunan tashi Dan ita Koda take qauye Yar gatace Bata Saba da wahalaba Amma data tuno Dan abdulshakur dinta zatai saita fara qoqarin farawa.
Ahankali take aikin cikin nutsuwa sbd gudun banna kotai ba daidaiba.
Tana cikin mopping palon Kamal yashigo yana waya ransa kamar a 6ace ba zato yaji sul6in ruwan data cika gurin mopping din ya jasa saura qiris ya Fadi yakurah data kawo gurin tai saurin taresa tana cewa,
Hey careful.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda juyowa ya qurawa fuskanta da tuni tayi wani iri sbd fargaba murya a sanyaye tace,
Yi hkr bansan ya zanyi bane ruwan ya bushe da wuri.
Danne tsananin 6acin ransa yayi sbd qudirin daya qulla akanta tun jiya daya fara 'dora idanuwansa akanta yasaki murmushi yace,
Ba komai kawai dai ki kiyaye gaba Kuma ki Kira asabe ta qara Miki qarfin AC sbd ya bushe da wuri.
Kallonsa yakurah tayi dakyau cikin mamaki sbd tsaf tasan Kamal Dan iskane na qarshe matuqar baida wata manufa akan wannan yarinyar bazai sakar Mata wannan murmushin ba.
Anano kuwa suna wucewa tabi bayansa da kallo cikin mamakin sanyin halinsa.
Sai guraren azahar tabaro sashen tana shigowa ta fa'da toilet din gwaggo tayi wanka daidai Nan abdulshakur dake kwance a katifa ya tashi daga bacci tayi sauri ta shirya ta dauko madararsa tabasa tasake yi Masa wanka duk da dai ba Sosai ta iyaba.
Wasa ta ringa Mai duk da dai jaririne baisan tanayiba saidai ya bu'de idanu kawai.
Sannu ahankali tafara sabawa da aikin gidan duk da iko da duk wani Shan qamshin mum asee tuni tafara sabawa dashi hakama yakurah Sam ba ruwanta da ita saidai idan zata sakata aiki takira shima tana gamawa take tafiyarta sbd ko kallon arziki Bata Mata.,
Ta 6angaren girki ma itada asabe ne sukeyi yanxu sbd tanason iya ayyuka da dama sbd agida can qauye ko shara batayi bare ta iya wani aiki,
Sunyi sabo da asabe sosai duk da ta girmeta Amma tanajin da'din fira da ita musamman idan tana koya Mata aiki tana Bata labarin kyawawan halayen matar gidan data rasu.
Gwaggo kuwa sosai ta maida hankali gurin taimakawa ananon gurin kulada abdulshakur sbd ganin ba laifi ta saki jiki tana 'dan Jin da'din aikin datakeyi duk da dai tuni abdulshakur din yadara wayo yafara gane itace uwarsa Dan kusan tsawon wata hudu kenan da zuwanta gidan Kuma har lokacin saheeb baidawo ba Yana Lagos ayyuka sun Masa Dan yawa Kuma dama bason dawowar yakeba.
Ta 6angaren Kamal kuwa tuni wani irin sabo yafara shiga tsakaninsu Dan kuwa wata irin kulawa da mutumta yakeyi ga hidimar siyayyar Kaya dayake Mata kusan duk yafita.,
Hakanne yasa ahankali batareda ankareba soyayyarsa Mai tsanani tashige zuciyarta Wanda tuni yagano hakan Dan dama hakan shine burinsa.
Yau bayan tagamo aikin girkin Rana tashigo 'dakinsu ta tube tayo wanka tana cikin saka Kaya Mai gadi yazo ya sanarda gwaggo zuwan jafar da baffa Aida sauri tagama sako kayan tasa hijabi tafito itada kanta taje gate tashigo dasu jikinta har rawa yake sbd tsananin farin cikin ganin baffanta da hammanta jafar.
Baffa kasa rufe baki yayi sbd tsananin farin cikin ganin yanda ananonsa ta canxa hankalinta ya kwanta ga abdulshakur shima yayi wani irin girma gashi farine sosai shima Wanda hakan zaisa kace 'dantane.
Sunci abinci sunyi fira sosai kafin suka miqe suka fita sukayo sallar la'asar a masallacin gidan suka fara Shirin komawa gida.
Har titi Anano ta rakasu jafar na riqeda abdulshakur Yana Masa wasa Sai dariya yakeyi kamar dama can yasansa.
A gabansu motar Kamal ta tsaya ya sauke glass Yana kallonta tasaki murmushi tareda yin qasa dakai tace,
Su baffanane sukazo.
Saurin fitowa yayi ya gaida baffa harda 'yar rusunawa kafin ya miqawa jafar hannu suka gaisa Sai alokacin idanuwansa suka sauka kan abdulshakur dake hannun jafar yaji gabansa yayi mummunan fa'duwa sbd hakanan saiyaga kamar idanuwansa na nuna Masa kamar yaron da kusan mutum uku na farko kamar nafeesat sbd Dan qaramin bakinsa da fa'din fuskarsa,
Saiyaga kamar Kuma saheeb sbd dogon hancinsa da manyan idanuwansa masu maiqo aciki Sai kuma Anano da kalar fatarsu take iri daya har yellow yellon.
Fa'duwa gabanta ya'dan yi sbd ganin yanda yake kallon abdulshakur Dan haryau ba Wanda yasan da akwai 'da agidan.
Cikin sakewar fuska yace,
Muje na sauke ku Tasha Mana.
Aa baffa yace Yana tsayarda Mai adaidaita dayaxo wucewa.
Shiga sukayi jafar ya miqo Mata Abdul suka wuce.
Kallon kallo suka shigayi tsakaninta dashi ya daure yace,
Yaron waye....
Sunkuyar dakai tayi cikin sanyin murya tace,
Dashi nazo.
Wat"""yafada Yana kallon yaron yace,
Yaron nanfa na hannunki nake magana..
'daga Masa Kai tayi tace,
Eh dashi nazo