Showing 3001 words to 6000 words out of 52880 words

Chapter 2 - EZNAH Dan Sirri By EZNAH

EZNAH   

10 Aug 2026

6

Kai Anano tayi cikin tsananin kuka tace,

Bazan iya tafiyaba.

Sake kamata tayi suna miqewa tsaye yasake harbowa still nafeesa yasamu tayi baya zata zube Anano tayi saurin riqo hannunta suka zube tare cikin rashin sa'a Ashe sun kawo kusada wani dogon cliff mai tsananin zurfi nan suka fara gangarawa suka fa'da.

Wani qaton dutsi kanta ya daka tasaki nishin azaba Mai qarfi Amma cikin dauriya ta daddafa ta tashi zaune ko gani sosai batayi ga wani irin juyawa da kanta keyi.

Daqyar ta lalabo nafeesa cikin azaba ta juyo da ita daqyar sbd a kife ta fa'do ko motsawa batayiba.

Jijjigata tayi cikin tsananin tsoro da tashin hankali.

Wani irin mugun Nishi taji nafeesar tayi Wanda yayi matuqar Bata tsoro Sai kawai taji Abu a gabanta.

Baya tayi a tsorace jikinta na makyarkyata zuciyarta na bugawa kamar zata bar jikinta.

Cikin qarfin hali nafeesa da numfashi ke qoqarin barin qirjinta ta kamo hannunta ta saka Mata wani irin zobe tareda damqe hannunta cikin azababbiyar murya da Bata fita tace,

Dan allah mena Haifa?

Cikeda tsoro jiki na kyarma ta matso takai hannu na rawa ta tabo murya na rawa tace,

Namiji.

Wani wahallalen Nishi nafeesa tasaki tareda sake damqe hannun Anano murya a karye tace,

Dan Allah ga amana Nan Allah yabaki sbd zuwanki Nan ya nuna kina cikin wannan qaddarar kema,
Nice na haifesa Amma kece Zaki Zama uwarsa sbd wannan itace qaddararmu.

Cikin tsananin kuka da tsoro murya a shaqe Anano tace,

Dan Allah ki daina magana kina bani tsoro..

Wasu hawaye ne suka gangaro gefen idon nafeesar murya na karyewa tace,

Nabaki shi halak malak matuqar Zaki iya riqesa sbd koya koma gidan mahaifinsa kashesa za'ayi kamar yanda aka kasheni hakama za'a kashe mahaifinsa...

Sunan mahaifinsa ABDUL SHAKUR Amma ana kiransa da SAHEEB AB..... Bata qarasaba jini ya 6alle Mata daga mahaifarta Ba qaqqautawa,

Kuka Anano tasaki Mai qarfi lokacinda taga numfashinta ya fita Koda Bata San komai akan mutuwaba ta tababbatarda mutuwace tayi Amma qwaqwalwarta takasa yarda da hakan jiki na rawa tafara
Jijjigata  da qarfi cikin kuka Mai tsanani tace,

Meyasa Zaki mutu kibarmin 'danki alhalin bansan ya zanyi dashiba,
Meyasa qaddara ta raboni da abokanaina na taho na tararda wannan mummunar qaddarar.

Kuka takeyi sosai jikinta ba inda baya rawa.

Cikin sanyin jiki takai hannunta dake matuqar rawa ta 'dauki yaron Sai kawai ta fashe da wani sabon kukan sbd tsananin tausayin kanta da nasa daya shigeta Dan ko kuka baiyiba bare wani motsi sbd azabar dayasha kafin a haifesa tasan Kuma ba lallaine Suma su samu tsira da ransuba daga hannun Yan daban.

Hijabinta ta zare tareda na'desa aciki ta kaisa qirjinta ta rungume ahankali Nan take taji tsananin qaunarsa na shiga jininta.

Cikin kuka tace,

Bansan dalilin dayasa Allah yakawoka rayuwata ba,
Wannan qaddaratace kaman yanda mahaifiyarka ta fa'da,
Na rungumi wannan qaddarar da hannu biyu nayi alqawarin riqeka tamkar Dan dazan Haifa,
Nayi alqawarin Zama jajirtacciyar uwar da bazan Bari Akira da gurbataccen sunaba matuqar ina Raye Kuma nayi alqawarin jure komai zai biyo.,,

Kukantane yafara qara sauti tayi saurin cusa Kai cikin qafafuwanta sbd  Kar sujiyo sautin kukan..



#vote
#comment
#and share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_



*13*
Kuka take sosai har jikinta na kakkarwa sbd rashin sanin takamaimai abinyi Dan kuwa batamasan ya zatayi ta fuskanci gagarumin mur'daden alamarin dake gabanta ba,

Miqewa tayi daqyar rungume da jaririn Sai alokacin taji jibiyarsa da ba'a yankeba tasaka hannunta dake rawa ta lalubo wani 'dan dutsi Mai tsini ta rintse ido ta yanke zuciyarta na tsinkewa sbd batasan taqamaimai adadin da ake yankewaba.

Gyarasa tayi ta sake shigardashi jikinta ta qanqame tafara laluban hanyar barin gurin cikin tsananin kuka tana waiwayen gawar nafeesa.

Duk inda tasamu ca6a qafarta takeyi cikin tashin hankali da fargaba take ko waiwaye batayi harsaida taga tayi Nisa da gurin ta 'dan waiwayo hawayen cikin idanuwanta suka gangaro ta Rintse idanu cikin wani irin nauyin zuciya kafin tajuya tafacigaba da tafiya Dan lokacin gab ake da fara Kiran sallar asuba.

Tsayawa yayi tareda zubawa gawar Ido cikin tsananin takaici da baqin cikin mutuwar Tata batareda sunsamu yanda sukeso ba gashi dukkanin alamu sun nuna abinda ta Haifa Yana Raye sbd baya gurin antafi dashi.

Mitssw yaja qaramin tsaki zuciyarsa na tafasa jiyake kamar ya rufe gawar da duka.,

Cikin takaici yakalli Wanda ke kusadashi yace,

Ji9 Kira mum asee.

Waya ya fiddo cikin wandonsa ya dannawa numbernta Kira duk da tsakiyar darene saigashi ta 'daga Dan ko gigin gifta fuskarta bacci baiyiba bare idanuwanta dake butse qyam da tsananin baqin ciki da 6acin Rai.

Cikin nuna zallar takaicinsa yace,

Matar saheeb ta sheqa lahira....

Wani qaton Abu Mai kamada dutse ya danne maqoshinta tace,

Cikin jikinta fa?

Kallon gawar dake gabansa yayi yana yamutsa fuska yace,

Ta haifesa ba Rai sbd tun Yana ciki na harbesa.

Sai alokacin taji abinda ya tokare numfashinta ya fa'da ta 'dan saki murya tace,

Good job bullet yanxu ku dauko gawar ku jefar qofar gidan Nan saiku gudu gawar abinda ta Haifa kuwa kusamu jeji ku wullar da shege.

Bullet na kashe wayar ya kalli yaransa yace,

Matuqar mum asee tasanda mun Bari abinda aka Haifa ya tsira to zamu samu matsala Dan itake biyanmu yanda mukeso a aiki Dan haka har abada karwanda yasan abinda ta Haifa na Raye.

Wucewa gaba yayi tareda cewa su biyosa da gawar.

Gudun tashin hankali suka dinga shararawa har suka shigo cikin gari direct anguwar suka nufa daidai gate suka tsaya tareda aje gawar qofar gidan suka koma mota ji9 daya Sanya niqaf da dogon hijab ya qwanqwasa qaton gate din gidan maigadi dake zaune ya rafka uban tagumin tsoro da fargabar haduwarta da saheeb akan 6atan matarsa ya zaburo da sauri ya bu'de gate din cikin fargaba

Saura qiris yayi tuntu6e da gawar yayi saurin ja baya ya zube jiki na rawa daidai Nan ji9 ya shige mota da gudu sukabar gurin.

Hannu biyu Mai gadi ya 'dora akai Yana salatin daba Kai qarshensa yakeba da qarfi ba inda baya rawa ajikinsa....

Miqewa yayi ya kwasa cikin gida aguje bai tsaya komaiba yahau bubbuga musu qofa hankali atashe.

Abba dake qowarin fitowa sallar asuba yayi saurin qarasowa ya bu'de qofar cikin fargaba
Yana ganin jabiru Maigadi ya fito arikice Yana cewa,

Jabiru lafiya ku......

Gate ya nuna cikin tsananin tashin hankali yace,

Matar oga saheeb ce gatacan awaje wata Mata takawota ta gudu....

Ai abban bai jira sauran bayaninba ya nufi gate din daidai Nan Kamal ya fito da sauri Yana tambayar abba abinda ke faruwa cikin damuwa.

Murmushin gefen baki mum asee dake tsaye bakin windon bedroom dinta dake sama tasaki tareda cewa,

Not bad bullet.,,,
Sbd dabararsu ba laifi tayi Dan yanxu bamai ta6a tunanin maza sukayi aikin za aita bincikene akan mace ce takasheta.

Hmmmnn and I will make sure nikuma Naga na qara lalata tunaninsa  gurin binciken mitswww stupid bastard..

Juyawa tayi tabar bakin windon tareda fadawa toilet ta fiddo spray na pepper tafara fesawa cikin idanuwanta duk da tsananin azabar datakeji kamar zata shide Amma taurin Rai da qarfin baqar zuciyarta ya hanata dainawa
Cikin qanqanin lokaci idanuwanta sukai wani irin mugun kumbura sukai jajir Banda tsiyayar hawayen azaba ba abinda suke daqyar ta it's alwala ta fito hartayi sallah tagama idanuwanta Basu daina tsiyayar hawayenba.

Kodata idar jiki a sanyaye ta sauko Palo cikin hijab din anan ta tararda Abba da Kamal a tsattsaye sun saka gawar agaba jiki duk a mace ga jabiru gefe Sai sambatu yake sbd nafeesat mutuniyarsace sosai.

Gwaggo Hindu Mai Taya nafeesar Zama tuni ta zube qasa Banda kuka ba abinda takeyi hakama fadime da Deborah masu aiki Suma hawayen suke Dan kuwa suna tsananin qaunarta Dan itace kawai Mai mutumta mutane agidan.

Baya mum asee tayi cikin tsananin tashin hankali tareda sakin saririn kuka tana Kiran sunayen Allah yakurah data fito bedroom dinta tayi saurin tareda cikin damuwa itama.

Waya Abba yafitar tareda barin palon yafara Kiran uwayenta ya sanar musu kafin yakira saheeb Amma Sam wayarsa Bata shiga nandai yakira duk yanuwa da jamaarsa yasanar musu da rasuwar.



Qarfe Tara da rabi na safe suna airport ten jirginsu zai tashi jin sauran thirty minutes din yake kamar basa tafiya.

Wayarsa dake kashe tun jiya ya fiddo tareda kunnawa kamar jira ake saiga Kiran Kamal yashigo wayar
Kallo 'daya yayiwa screen din ya mayar da wayar sbd badashi yake buqatar wayaba yanxu.

Yana kallo Saida Kamal yayi Masa Kira bakwai kafin ya daina kiran,
Nemo number Abba yayi ya Kira Sai yajisa line busy sai kawai ya sake kashe wayar tareda miqewa riqeda black smiones leather jacket dinsa da iPad da wayarsa dakuma passport dinsa tareda ticket zayyan na gefensa shima Amma waya tunda sukazo yake waya Sai time din ya kashe Yana saka wayar a aljihu tareda gyara zaman jacket dinsa Mai zanen sojoji.


Tunda suka shiga jirgi ya kwantarda kansa tareda rufe idanuwansa Dan he's having this feeling something is not right.

Zayyan datun a airport Abba yakira yasanardashi jikinsa yake a sanyaye sosai rasuwar ta daki zuciyarsa Dan kuwa yasan tabbas amininsa yayi rashi babba Dan har abada bayasa ran zai Kuma samun maisonsa kamar nafeesat Dan kuwa ta soshi ta qaunaceshi ayanda yake da rayuwarsa da Babu farin ciki ko ka'dan.

Yayita yunqurin sanardashi saiya fasa sbd baimasan ta inda zai fara sanar Masa rasuwarba musamman yanda suka fara ganin haske yafara shigowa duhun rayuwarsa ta sanadin nafeesat da cikinta Amma gashi lokaci 'daya Allah ya karbi baiwarsa.


Koda jirginsu ya sauka suka fito mota biyu ce tazo 'daukarsu 'dayar sojoji ne acike Sai 'dayar driver ne kawai Kuma shima soldier ne dukkaninsu cikin uniform dinsu suke suna ganinsa suka saurin sunkuyar da kawunansu cikin girmamawa sukace,

Wellcome sir.

Da Kai ya amsa musu tareda shigewa mota Nan take suka bar airport din a guje Dan dama yanada wuya kaga soldiers ba gudu sukeba.


Jabiru dake zaune bakin gate daga waje tareda wasu daga cikin masu gadin kusa dasu dasuka zo gaisuwa Yana hango wutar motocinsu duk da da Rana ne Amma yasan motocin soldiers din oga saheeb kullum akoda Rana a kunne suke ya miqe da sauri yayi ciki ya bu'de gate 'din gabansa na tsananta fa'duwa.


Lumshe fararen manyan oily eyes dinsa yayi lokacinda yaga harabar gidan da mutane duk da ma tuni wasu suka tafi
Wani sabon nauyi yaji ya qaru a zuciyarsa Akan Wanda yakedashi ya fito ya nufi gurinsu Abba dake jiran qarasowarsa yayi qasa dakai lokacinda wasu Yan uwan nafeesat maza ke Masa gaisuwa.

Shiru yayi batareda ya 'dagoba har Saida Abba ya dafasa cikin tsananin tausayawa yace,

Allah yaji qanta ya kawo maka sassauci Abdul.

Har magriba ta gabato Yana zaune kusada Abba kansa a sunkuye still
Ba Wanda baiyi mamaki da jinjinawa jarumta da qarfin hali irin nasaba Dan ko magana bayayi duk Wanda yai Masa gaisuwa Kai kawai yake 'dagawa idanuwansa sun rine Sai jijiyoyin kansa dasuka firfito ahaka har akai magriba kafin yashiga cikin gida inda ya tararda mum asee ba lafiya sosai Nan dai Dole yasa Kamal Kiran Dr sbd antabbatar Masa da ko ruwa taqi Sha tunda akai rasuwar Nan take tsananin qaunarta da tausayinta yaqara shigarsa Dan kuwa dan yasan soyayyarta garesa cikin jininta take.






Ana fitowa sallar asuba tafara hango qauyensu maimakon taji sassauci a zuciyarta saitaji hankalinta ya qara tashi gabanta ya tsananta fa'duwa ta tsaya cak tareda 'dago fuskar jaririn ta kalla hawayen idonta ya gangaro ya sauka har kan fuskarsa ta maidasa jikinta ta rungume ta nufi cikin garin zuwa lokacin gari yafara haske daqyar takai kanta qofar gidansu sbd yanda qafafuwanta sukai Mata nauyi suna hardewa ta tsaya bakin qofar gidan zuciyarta na bugawa da tsanani cikin fargaba da tashin hankali ta cira qafarta daqyar tasa cikin gidan.



Vote
Comment
And share

*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_



*15*
Jiki na rawa su Usman suka kwantarda baffa Kan tabarma suka hau you Masa firfita ahankali yafara rage jijjjigar numfashinta ya 'dan farawa rage zaburewar dayayi ya lumshe idanuwansa yayi shiru Yana karanto sunayen Allah a zuciyarsa Dan yasamu nutsuwarsa ta daidaita ya fuskanci Anano Dan haryanxu shi bai yarda da wannan shegen 'dan Mai kukan kwa'di ita ta haifesaba.

Usman ne ya miqe yashiga daki ya qwace Anano daga dukan da aliyu ke Mata cikin tsananin bacin Rai yace,

Wai Kai aliyu meyasa baka auna komai kayisa cikin mizanin hankalin cikakken 'dan Adam ne?

Kana tunanin dukan dakake Mata zaisa ta fa'di gskia ne ko kuwa?
Mitssw''''yaja 'dan qaramin tsaki tareda riqo hannun Anano ya miqar da ita Amma Sam ko tashi Bata iyayi ya miqa hannu zai kar6i yaron tayi saurin 'dago kumburariyar fuskarta ta kallesa saitaga fuskarsa a ha'de ba alamun wasa saita miqa masashi jikinta na rawa gabanta na fa'duwa.

Kwantarda yaron yayi yariqota ta fito tana tafiya daqyar ya kalli jafar da duk yayi zuru zuru yace ya debo Mata ruwa a bokiti tayi wanka.

Ta gefen Inna ta wuce tana kallon yanda innar ke keta faman goge hawaye ta maida kallonta gurin baffa yanayin data gashi acikine yasa hankalinta tashi ta juya 'daki  duk suka bita da kallo

Jaririn ta 'dauko jiki a tsananin sanyaye ta nufi gurinda baffa yake Yusuf yayi saurin daka Mata tsawa Rai a6ace.

Qin tsayawa tayi saidata Kai gaban baffa ta durqusa hawaye nabin fuskarta murya na rawa tace,

Baffa don Allah karka Bari zargi yasa ka cutatar da kanka,
Wallahi wallahi wallahi baffa ban ta6a aikata Zina ba,
Ban ta6a ra6ar ko wani Mai akatawaba,
Wannan jaririn nawa kamar yanda Wadda ta haifesa tabanishi kuma nafada muku da farko Amma wlh baffa bani na haifesa ba.....

Wani mugun kallo aliyu da Yusuf harma da Inna ke binta dashi sbd Jin abinda take fa'da Wai an Bata kyautar jariri.

Baffa kuwa jajayen idanuwansa ya bu'de ahankali ya kafeta dasu cikin rawar murya kamar zaiyi kuka yace,

Anano Abu 'daya nakeson nasani akan jaririn Nan Wanda shika'dai ne damuwata Kuma daga kin fadamin gskia wlh zuciyata Zata iya 'daukar koma meye sauran bayanin
Anano jaririn Nan na waye?

Sabbin hawaye ne suka gangaro Mata ta share murya a dake tace,

taimakon uwarsa nayi lokacinda take naqudarsa Kuma tana haihuwarsa ta rasu.

Tsit sukayi jafar kuwa hambadala yasaki a bayyane aliyu da Yusuf suka bisa da mugun kallo cikin takaici dansu Basu yardaba.

Baffa kuwa tsareta yayi da Ido tsawon lokaci kafin yace,

Anano gskia Kika fa'damin?

Kai ta 'dago ahankali tace eh hawaye na sake gangaro Mata.

Yusuf da Usman ya kalla yace,

Suje inda tafada subi hanyar adubo gawar azoda ita.

Kanta ya maido kallonsa Nan take yaji zuciyarsa ta yarda da ita 'dari bisa 'dari ya riqo hannunta cikin nutsuwa yace,

Anano na yarda dake tako wanne 6angare Kuma natabbatarda bazaki aikata Koda makamancin hakanba Dan haka kiyi qoqarin ganin konan gaba baki rusa yardataba.

Kai ta 'daga ahankali gabanta na fa'duwar wane hukunci baffan zai yanke akan yaron.

Inna ya kalla Koda Bata fa'daba fuskarta ta nuna tashin hankalinta ya 'dan ragu saidai itama kamarsu Yusuf hankalinta bai kwantaba sosai da zancen ananon.

Cikin nutsuwa yace,

Ki tashi ki 'dora ruwa Anano tayi wanka.

Badan tasoba ta miqe ta nufi madafarsu tafara ha'da itace.

Anano kuwa har ruwan yayi zafi tana durqushe agurin Saida jafar ya cika Mata bokiti ya sirka yakai Mata qofar bayi takuna ta miqe jiki a sanyaye ta shiga 'daki ta tube ta fito sum sum tashige bayin.

Duk da tana cikin tashin hankali da damuwar makomar jaririn sosai taji da'din wankan Dan Nan take taji ta'dan warware ajikinta.

Tana gama wankan kafin takai ga fitowa yaron yatashi Nan take ya kara'de gidan da kuka cikin sauri ta janyo zaninta ta 'daura ta fito
Turus tayi jikinta na saki sbd ganin ba Wanda ya motsa cikinsu kamar basusan da acikin gidan ake kukanba.

Sanyi qalau jikinta yayi Dan kuwa taga tabbas ko barinsa ya zauna gidan baffa yayi bamai qaunarsa.

'dakin tashige bayan ta aje bokitin hannunta ta zauna kusada yaron Nan itama tafara nata hawayen Dan kuwa tasan daga ita harshi suna tsaka.

Saidataji kukan harya fara sanyashi laushi takai hannu ahankali ta 'dauke tareda qura Masa Ido Dan Sai alokacin tafara kallon fuskarsa.

Farine sosai Kuma da gani ba lallaine yayi baqi ba duk da dai bazata iya cewa ga fuskar mahaifiyarsa ba sbd komai yafarune cikin duhu..

Numfashi ta sauke ahankali cikin zuciyarta tace,

Allah yasa su hamma su gano gawarta asuturta kodan jaririn.

Sallama aka fara kwadowa a qofar gidan baffa ya kalli qofar da sauri zuciyarsa na 'dan tsinkewa ya miqe daqyar tareda tattaro 'yar nutsuwa ya nufi qofar aliyu nabin bayansa.

Murmushin qarfin hali yasaki lokacin dayaga Mal Garba maqwafcinsa yace,

Aa Mal Garba Kaine da safennan.

Cikin 'yar damuwa yace,

Nine Mal salisu an gari lafiya?

Lafiya qlau Mal Garba ya iyalin?

Alhamdulillah nace ko anji want bayani akan Anano kuwa?

Washe baki baffa yayi cikin qarfin hali yace,

Eh kaga shaf na manta na sanar maka tun a Daren jiyan tadawo Wai Ashe ita da qafa ta qaraso daga can rugar nuhu shiyasa ta iso dare sosai.

Masha Allah Abu yayi kyau dama dai nace ne nazo naji halinda ake ciki Kan 6atan nata Allah ya tsare gaba.

Amin Amin Mal Garba nagode.

Bayan tafiyarsa baffa ya Jima tsaye Yana tunani kafin suka juya suka koma cikin gidan Kai tsaye inna ya kalla yace,

Ki kimtsa yaron ki goyesa duk tsanani Kar kibari agane da akwaisa acikin gidannan.

To tace badan ranta yasoba saidan Bata qetare umarninsa ta miqe ta sake 'dora wasu ruwan.

Cikin qanqanin lokaci Inna tayi Masa wanka ta gasashi sosai ta 'debi sabuwar madarar shanu tabasa yasa sosai Nan take yayi luf bacci Mai da'di ya daukesa takuwa goyesa bayanta tasaka hijab bazaka taba cewa akwai 'da a bayanta ba.

Sai alokacin Anano ta'danji sanyi aranta take Kuma mamakin yanda takejin yaron har tsakiyar ranta.

Kamar jira ake Inna ta goyesa Nan take jama'a suka fara zaryar zuwa barka da dawowarta dakuma ganinta da'akayi.

Su ubaidah sunxo Nan suka hauta da fadan tafiyarta datayi Bata tsaya musu ba.

Itadai murmushin yaqe kawai take musu
Koda suka tambayi kumburin fuskarta da Jan idonta cemusu tayi batai bacciba ahanya qunama ta cijeta.

Sosai suka tausaya Mata duk da sun fahimci kaman Bata cikin walwala hakanan suka qarashi firarsu suka tafi.

Su Yusuf kuwa duk iya bincikensu Basu ga wata gawaba haka suka dawo suka sanarwasu baffa qarshe dai aka tattara zancen aka aje Sai bayan kwana biyu tukuna a yanke shawarar abinyi.

Tunda tadawo kusan komai ya canxa Mata ba kamar da ba da kowa gidan keji da ita kamar su lasheta Amma yanxu kaf yayunta iyakacinsu da ita ta gaidasu idansunga dama su amsa idan basuga damaba su qyaleta baffa da jafar ne kawai ke kulawa da ita Sai Usman idan yaga dama shima,

Inna kuwa kadaran kadahan ga baffa dayasata kulada jaririn Dole badan tasoba.

Sosai hankalin ananon hankalinta yafara 'dan kwantawa sbd ganin anbar zancen saigashi Randa sukai sati 'daya kwatsam zancen yafara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login