Showing 36001 words to 39000 words out of 147746 words

Chapter 13 - RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

in je mata barka tayi min lahani, ko"

kuma ta ™ulla min sharrin da zan shiga bakin duniya. Wannan shi ne dalilin da yasa kai tsaye na ce mishi

"bazan je ba."""

"Tsawon mintuna biyu Baffa ya kasa magana, babu abinda yake sai jujjuya maganganun Zulaikha a"

"zuciyarshi. A karo na biyu ya sake sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan yayi mata umarnin komawa cikin gida."

"Bayan sallar isha'i ya shiga Sangaren Innaye da nufin yi mata sai da safe, tunda ranar ba girkinta bane."

"Daga yadda idanuwanta suka zurma ciki lokaci yasa matsanancin tausayinta ya ™ara lulluSe shi, bai shiga cikin falonta da niyyar zama ba, amma lura da halin da take ciki yasa shi zama kan kujera nesa da ita kaWan yana yi mata nasiha kan muhimmancin yarda da ™addara mai kyau da mare kyau a matsayinta na"

cikakkiyar musulma.

"""Shi ma ya fasa auren Auta ta ko?"""

Ta katse shi da tambayar da raunin murya.

"""Eh toh! Bazan ce eh ba bazan ce A'a ba. Domin har zuwa yanzu ban samu wata gamsasshiyar amsa"

"daga gare shi ba kamar yadda ya ce zai min aike. Kawai dai mu cigaba da addu'a."""

"""Uhmmm! Allah ya jisshe mu alkhairi."""

Abinda ta iya cewa kenan ta sunkuyar da kanta ™asa. Har Baffa ya fice daga falon bata iya sake ce mishi

komai ba.

"A wannan dare, idan Baffa ya ce ya yi cikakken barci na awa Waya yayi ™arya. Duk yadda yake ganin"

kamar abin bazai dame shi ba inaa... Mama Laminde da take da girki tun tana mishi nasiha da tausasan kalamai har dai ta gaji ta zuba ma sarautar Allah idanu. A ™arshe ma juya baya tayi ta kwanta ta ™yale shi yana ta tufka da warwara.

"Babban damuwarsa Waya ne, idan Mudan ya ce ya fasa auren Zulai a waWannan kwanakin wa za'a samu"

"kuma yayi ™undubalan fitowa ya ce zai aure ta? Ya sani duk maganganun da Zulai ta faWa masa akan Yaha gaskiya ne, domin Rahina tana faWa masa, amma duk su biyun basu Wauki hargagin Yahan da"

muhimmanci bane domin a ganinsu surutu ne kawai irinna mace me mahaukacin kishi.

Sannan shi da kanshi sai yau ya ™ara yarda da halin Mudan da ake ta faWa mishi na rashin ha™uri da

"rashin iya magana. Amma duk waWannan abubuwan bai Wauke su da muhimmanci ba, babban burinsu shi da Rahina shi ne su aurar da Zulai."

Domin anyi ittifaki a yanzu dai duk faWin ™auyen Fa™o babu yarinya budurwa da take da shekarun Zulai.

Sa'anninta duk suna Wakin mazajensu da ΄a΄ayensu.

Tun da daWewa da ace shi mutum ne mai yarda da camfi da tuni ya daWe da fantsama gurin masu

"magunguna yana nema ma Zulai taimako. Domin da yawan mutane na ganin Aljani ne ya aure ta. Wasu kuma na ganin nauyin jini take da shi, dole sai an nemi taimako sannan za ta sami mashin-shini."

Maganar ta saka ma kanta girman kai don ta yi boko ko kuma don Hafizu yana da gida a Habuja ne yasa

take Waga ma samarin ™auyen kai bai taSa ji ba sai yau a bakin Mudan.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a karo na barkatai. Ya Wauki ΄ar ™aramar wayarsa mai tocila da take

"ajiye kusa da shi ya danna ta kawo haske ya duba lokaci, ™arfe uku da minti ashirin da bakwai na tsakiyar"

dare.

"Hasken tocilar wayar ya kunna, sannan ya mi™e tsaye ya buWe ™ofa hannunsa ri™e da buta ya fita can"

tsakar gidan ya Wauro alwala. Ya sani duk wani tunani da sa™e-sa™e baza su samar mishi da mafita ba. Don haka ya ™arasa daren yana mi™a kukanshi ga mai kowa mai komai mahaliccin sammai da ™assai da abinda ke cikinta.

Washe gari ko da ya tashi zuciyarsa babu damuwa kamar na jiya. Da asubah bayan idar da sallah ya tare

"΄an'uwansa sha™i™ai guda uku da suke uba Waya ya faWa musu duk halin da ake ciki, sun nuna alhini sosai."

Sannan suka daWe suna tausarsa da daWaWan kalamai. A ™arshe suka Suge da addu'ar Allah ya kaWe fitina

yasa su ji alkhairi.

"Ko da ya shiga gida, ya le™a matansa gaba Waya yadda suka tashi turakarsa ya shiga ya kwanta. Yana"

tasbihi da hailala daga kwance nannauyan barci yayi awon gaba da shi.

"˜arfe goma da rabi na safe Innaye ta shiga Wakinsa ta tashe shi. Idanunta sun kaWa sunyi jaa, da™i™u"

talatin ya Sata yana kallonta kafin a hankali ya ce

"""Me yake faruwa Rahina?"""

"""Mudan ne ya aiko a bashi kayan auren Zulai da ya kawo. Wai ya fasa aurent..."""

"""Ubangiji Allah yasa hakan shi yafi alkhairi. Allah ya haWa ta da wanda ya fi shi alkhairi nesa ba kusa"

"ba."""

Ya katse ta da faWin haka tun kafin ta ™arasa faWa masa abinda ke faruwa. A fuskarsa babu wata

shahararriyar damuwa.

"DaSas! Ta zube a gefen katifar da yake kwance ta fara matsar ™wallah, domin Allah ya sani ba haka ta so"

ba. Da tausasan kalamai yayi ta rarrashinta har ya samu tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.

"Daga can bakin ™ofa sai ga sallamar Mama Laminde da Baba Laraba. Shi ya amsa sallamar, Innaye kam ta"

kasa magana. Fuskokinsu a dame suka shiga cikin Wakin suna ™ara jajanta ma Baffa wannan abin ba™in

cikin da ya same su.

"""Babu komai ai. Wani baya taSa auren matar wani. In Allah ya yarda ko da shi ko ba da shi ba ranar"

"Waurin auren Zulai bazai canja daga yadda aka tsayar da shi ba. Ku kwashe kayansu ku kai musu."""

Da yake duk kayan da Mudan ya kai gidan hatta ihsani da yake mata na saurayi da budurwa ba amfani da

"su take yi ba, Innaye take dam™a ma ita kuma sai ta kai Wakin Baffa ta adana. Don haka cikin ™an™anin"

"lokaci aka gama fitar ma da matan da ya aiko kayayyakinshi gaba Waya, hatta sadakinshi sai da Baffa ya ba Mama Laminde ta kai musu."

"Kasancewar kayan Waki da na kicin da komai Hafizu ne ya Wauki nauyin yin su, shi yasa ko sisi ba'a taSa a"

"cikin kuWin na gani ina so, kuWin gaisuwa da kuWin sadaki da ya biya ba."

"Kamar wutar daji, zuwa ™arfe biyu labarin fasa auren Zulai da Mudan yayi har ya zaga ™auyen Fa™o."

³a΄an Innaye da sauran ΄an'uwansu da suke uba Waya haka suka cika gidan suna jajanta ma junansu wannan abin ba™in ciki. Amma ko da iyayensu mata suka sanar da su abinda Baffa ya ce za'a Waura auren ko ba da Mudan ba sai kuma suka yi tsuru-tsuru.

Tsoronsu Allah tsoronsu a aura ma Zulai tsoho ko kuma nakasasshe wanda baiyi mata ba ta ™i yi masa

biyayya saboda rashin ha™urinta. A sako ta kuma da ™ananun shekaru ta zama ™aramar bazawara a gari a

cigaba da mata tofin Allah ya tsine.

"""Innaye? Amma kina ga aurar da Zulai ga wanda bata sani ba hanya ce mai Sullewa? Kar fa fushi yasa"

"mu aikata aikin da za muzo muna da na sani..."""

"""Yayansu ke dai kiyi addu'a. Babu abinda zai faru sai alheri in Allah ya yarda."""

Innaye ta katse Yaya Balira da take maganar fuskarta cike da damuwa.

"Kafin Balira ta sake cewa komai wayar Innaye da ke cikin hular kanta ya hau tsuwwa. Wayar ta ciro, ko"

"da ta duba sai taga alamar mota, alamar da Zulai ta saka mata a lambar Hafizu."

Bata Sata lokaci ba ta Wauka don daman ta kira shi a Wazu domin ta faWa mishi halin da ake ciki bai Wauka

ba.

"""Assalamu alaikum! Hafizu..."""

"""Innaye barka da yamma. Ki taya ni murna Innaye, Bintu ta haifi Wa namiji yanzunnan, ni ma na zama"

"Baba Innaye."""

Da karaWin farin ciki da zumuWi sosai a muryarsa yake jero maganganun.

"Kamar yana gaban Innaye, haka fuskarta lokaci Waya ya ™ayatu da farin ciki mara misaltuwa."

"""Alhamdulillahi Hafizu Alhamdulillah! Barka da arziki. Allah ya raya mana yasa cikon musulunci ne?"

"Yaushe ta haihu?"""

Ta sake tambayarsa ta ma manta ya faWa mata yanzu Bintun ta haihu.

Da fara'a shi ma a muryarsa ya sake amsa mata yanzu aka yi haihuwar.

"""Šazu da za mu taho asibiti lokacin da take na™uda ruWewa da tashin hankali yasa na manta da wayar a"

"gida. Sai da ta haihu na sami nutsuwar komawa gida na Wauki wayata, yanzu wanka zanyi sai in koma asibitin."""

"""Ma sha Allah! Allah ya raya mana. Hafizu na ya ™ara girma, ya zama Baba."""

Dariya ya kwashe da shi zuciyarsa cike da farin ciki.

"Kafin ya katse wayar, kaf yayyinsa da suke cikin Wakin sai da suka yi masa barka da arziki yana amsawa da"

matsanancin fara'a sannan suka yi sallama.

Wannan haihuwa da Bintu tayi shi ya dakushe kaifin damuwar da suke ciki na batun fasa auren Zulaikha.

Hatta ita Zulan da tun zuwa karSan kayan auren take cikin uwar Waki du™un™une akan gado tana kuka

babu abinda ke fito da ita

sai Wauro alwala sai da ta daure zuciyarta ta fito falo cikin yayyenta suna murnar ™aruwar da Wan'uwansu

ya samu.

Fitar zancen haihuwar cikin gida da ma™wafta yasa Wakin Innaye ya sake Winkewa da mata ana yi mata

barka da arzikin samun jika. Sai da aka yi sallar Isha'i sannan Baffa ya fatattaki ΄a΄an masu aure suka

wuce gidajen mazajensu.

"""Haba Hafizu, raWin sunan jaririn ne har sai na taka ™afafuna zuwa Habuja? Ai ina ga wannan duk abu ne"

"mai sau™i. Ba sai na je ba..."""

"""A'a Baffa!"""

Ya katse shi da sauri.

"""Kar ka ce baza ka zo ba don girman Allah! Ka ga fa tunda aka yi haihuwar nan iyaye da ΄an'uwan Bintu"

"ke ta safa da marwa a gidannan, sai ni ne daga Sangarena babu wani sha™i™i nawa da zai zo takanas-ta- kano barka?"""

"""Kamar ya ba wanda zai zo daga Sangarenka? Ca nake jiyan nan ka gama faWa min irin hidimar da Alh"

"Lurwanu da Iyalinsa suke yi tunda aka yi haihuwar?"""

Baffa ya faWa yana murmushi.

"""Baffa hidima da Wawainiyar gidan Abba Lurwanu daban zuwan da za kayi daban. Wallahi ko shi sai da"

ya tambayeni amma dai za ka zo ganin abokin na ka ko? Babban abin alfahari gare ni shi ne kai da kanka

"ka taka ™afafunka zuwa muhallina ka sa albarka, kaga jariri, sannan ka raWa mishi suna da bakinka. Saboda Allah Baffa ni kenan don ina birni sai kuma ace mahaifana baza su dinga zuwa gida na ba? Ka ga fa Innaye ta ce baza ta sami zuwa ba, gara ma ita ta taSa zuwa ta ga inda nake. Amma kai tunda na fara aiki shekara bakwai kenan sau Waya ka taSa zuwa Abuja, dalilin zuwan ma Waurin aure na ne. Don Allah"

"kayi ha™uri Baffa, duka tafiyar fa ta yini Waya ne za kuje ku dawo. Don Allah Baffa, don girman Allah."""

"Ya ™arasa maganar da magiya sosai a muryarsa, kamar zai fasa kuka."

"Tunanin gaskiyar da ke cikin maganganun Hafizu da yasa shi amincewa zuwan, amma Allah ya sani ba"

"wai don zuciyarsa tana son doguwar tafiya ba. A ganinsa, tunda shi Hafizu yana yawan zuwa ™auyen, kuma ya Wauki duk nauyin bu™atunsu dai dai gwargwado, ba ma su kaWai ba, hatta ΄an'uwa da jama'ar gari suna WanWana daga alkhairan Hafizu. Me yake bu™ata kuma bayan wannan? menene zai saka shi da"

girmansa yayi ta jelar zuwa gidan yaro?

"Tunda dai acan Habujan akwai Alhaji Lurwani, Baban Ibrahim abokin Hafizu, ya Wauki Hafizun Wa kamar"

"yadda ya Wauki Wan shi Ibrahim, kuma ba don sun haWa dangantaka ta jini ba, sai don kawai sun yi karatu tare da Wan shi Ibrahim."

"A ta™aice ma, hatta aikin da shi Hafizun yake yi shi ya nema mishi tare da Wan shi Ibrahim. Duk wasu"

"al'amura na Hafiz tsaye yake akai kamar Wan shi na cikinshi, hatta hidimar auren Hafiz acan gidan Alhaji"

"Lurwanu aka gudanar da komai. A ganinsa, da waWannan dalilan me zai sa shi da ake yiwa kara ya dinga nuna rashin ta ido?"

Amma tunda a wannan karon Hafiz ya nace za su shirya shi da ΄an'uwansa uku da Liman da yake

"Amininsa suje su dawo. Tunda dai tafiyar ta rana Waya ce, in yaso daga can ma sa biya gidan Alhaji Lurwanu su ™ara yi masa godiya kan Wawainiyar da suke yi shi da iyalansa akan Hafizu ba tare da gajiyawa ba."

"""Shi kenan! Zan zo. Amma ba ni kaWai ba. Da su Babanka Abubakar za mu zo da Malam Ahmad Liman."

"Yaushe ne ranar tafiyar?"""

Da murna sosai a muryarsa yake jera ma Baffa kalaman godiya saboda tsananin jin daWin amincewa

zuwa gidanshi da yayi. Har sai da Baffa ya dakatar da shi da cewa godiyar ta isa haka.

"""Wallahi na ji daWi sosai Baffa. Yanzu dai ka ga ™arfe sha biyun rana. Zuwa ™arfe biyu Mal Musa zai"

"kamo hanyar zuwa, na san dai duk yadda ake ciki in Allah ya yarda magrib a Fa™o za tayi mishi, idan ya"

"kwana. Gobe da asubah sai ku shirya da wuri ku kamo hanya, yadda za ku iso da wuri, idan za ku tafi sai in yanka muku tikitin jirgi zuwa Kaduna, daga can sai kuyi shatar mota zuwa gida."""

"""To babu damuwa. Allah ya kawo shi lafiya."""

*****

"Kamar yadda Hafiz ya tsara, washe gari ™arfe goma sha Waya na safe a gidan Hafiz tayi ma su Baffa. Sun"

"isa yana gurin aiki, baiyi niyyar tafiya aiki a ranar ba. Amma kiran gaggawa da aka yi mishi a Ofis yasa shi"

"fita babu shiri, da misalin ™arfe goma saura kwata."

"Da yake tun kafin ya fita ya jaddada ma Bintu su Baffa suna nan zuwa barka. A gabanshi, da murna sosai"

ta karSi maganar har tana cewa

"""Lallai abokin na Baffa ya zo da farin jini, daman bai taSa zuwa gidannan ba. Allah ya kawo su lafiya."""

"""˜warai kuwa. Ameen ya Allah."""

Ya amsa yana dariya. A gaggauce ya sake mata sallama da cewar bari ya je ya dawo kafin su Baffa su iso.

Yana fita daga Wakin taja wani dogon tsaki ta raka bayanshi da harara. Ranta a Sace ta fice daga Wakinshi

"zuwa na ta, ta kalli Raudha da take zaune gefen gado tana ri™e da Baby ta fara faWa mata abinda ke shirin faruwa, bayan ta gama faWa mata ta ™ara da cewa"

"""Na san shegen iyayin My dear ne yasa shi cewa su zo ganin Baby. Ai kam na rantse da Allah ba"

"ba™auyen da ya isa yazo gidana ya damu™a min baby da hannuwansu da suka saba damu™a kayan cuta. Don haka idan suka iso, Raudha ki naWe baby da showel da kyau sannan ki saka shi a abin Waukar can nasa mai kama da gado, ki kulle net Win kija zip ki rufe, sannan ki Waure belt Win yadda baza su taSa iya buWewa ba. Kin san ™auyawa ne sosai, na san basu taSa ganin irin abin saka jaririn nan ba balle su iya"

"amfani da shi."""

Ta mayar da idanunta kan ™anwarta Mashkura da take tare da ita tunda aka yi haihuwar ta cigaba da

cewa

"""Mashku idan kin kai musu Babyn ki matsa su ganshi daga cikin gadon ba sai sun taSa min Wa ba. Atoh!"

"Ni kaWai nasan wahalar da na sha gurin haihuwarsa don haka kwanaki biyar da zuwansa duniya bazanyi sakacin da za'a goga masa cuta ba."""

"""Kina da gaskiyarki Madam! Ban ga laifinki ba. Malam bahaushe ma cewa yayi taya Allah kiwo ya fi"

Allah na nan. Balle ™auyawan nan da tsubbace-tsubbace na tsiya yanzu haka sun ™ullo wani abun da za

"su shafa ma yaron a matsayin tsarin jiki. Gara su kalle shi daga nesa kallon kura."""

Raudha ta faWa da salon ingiza mai kantu ruwa.

"Ita dai Mashkura bata ce komai ba, amma fuskarta kawai za'a kalla a ga yanayin rashin jin daWi. Kamar"

"dai bata ji daWin maganganun Yayan nata da na ™awarta ba. Amma dai bata ce komai ba, domin a"

"ganinta gidan Bintu ne, iyayen mijinta ne, kuma Wanta ne. Tana ikon tsara duk abinda take so kan iyalanta."

Bayyanannen kamannin da ke tsakanin Baffa da Hafiz yasa tun kafin Mal Musa ya faWa ma ma'aikatan

"gidan wanene Baffa a gurin Oga su da kansu suka fahimci haka. Da girmamawa sosai suka dinga zubewa har ™asa suna gaida su Baffa, bayan musayar gaisuwa a tsakaninsu Mal Musa yayi musu jagora suka shiga cikin falon gidan da™yar, domin da sun dage su a shimfiWa musu tabarma su zauna a harabar gidan"

ba sai sun shiga ba.

"Sai da Mal Musa ya kira Hafiz ya faWa masa halin da ake ciki, shi kuma ya kira Baffa yai ta masa magiya"

sannan suka amince da shigarsu cikin falon gidan.

"""Mahaifin Oga ne da ΄an'uwansa. Ki kawo musu abin sha da abubuwan taSawa sannan ki shiga ciki ki"

"faWa ma Hajiya isowarsu."""

Mal Musa ya faWi haka ga Rabi.

Cikin ™an™anin lokaci Rabi ta cika gabansu da lemu kala daban-daban da ruwan gora. Ta haWo musu da

snacks saboda a lokacin bata gama abinci ba.

"Jikinta na rawa, ta haura sama zuwa Wakin Bintu don ta faWa mata zuwansu Baffa."

"""Rawar jikin miye kike yi kamar wasu ba™i ne na musamman suka zo?"""

Bintu ta daka ma Rabi tsawa da tambayar haka bayan ta saurari abinda ke tafe da ita.

"Sakalau Rabi tayi da baki tana kallonta, sai kuma ta ce"

"""Ba komai Hajiya. Bari in koma kicin, sai kin fito."""

Jikinta a sanyaye ta fice daga Wakin. Da kunnenta taji sadda Bintun ta raka ta da dogon tsaki. Zuciyarta

cike da mamakin halayen Bintu na ™in iyaye da dangin mijinta don kawai sun kasance ™auyawa.

Saboda Allah ta ina aka taSa haka? Kina son Wansu amma ba kya son iyayen da sukai sanadin zuwansa

duniya?

"""Allah ya kyauta."""

Ta faWa a fili sannan ta ™arasa sauka ™asa ta wuce kicin. Bayan ta faWa ma su Baffa ga Bintu nan zuwa.

"Kafin Bintu ta sauko Mashkura ta fara turowa da Wan jariri, an naWe shi a Wan ™aramin abin Waukansa mai"

kama da godo kamar yadda Bintu ta tsara.

Da fara'a a fuskar Mashku ta gaishe su sannan ta matsa kusa sosai tana nuna musu fuskar babyn kamar

yadda Bintu ta umarceta.

"""Sannu yarinya, Allah ya raya. Abokin namu tsoron gamuwa da mu yake yi aka naWe shi a cikin gado"

"don kar muyi masa rubdugu?"""

Liman Malam Ahmad ya tambayeta yana dariya.

"Ita ma dariyar tayi, ta kasa cewa komai sai sake ri™e abin Waukar babyn da tayi da kyau."

Baffa kuwa kai tsaye cewa yayi

"""Ki ciro shi daga ciki a Wauke shi, raWa mishi suna za'ayi da addu'o'i."""

"A Wan daburce Mashku ta kalli Baffa bayan ta ji abinda ya faWa, sai taga yayi mata kwarjini sosai baza ta"

iya musa umarninta ba. Da Wan rawar jiki ta aje abin Waukar akan kafet ta fara warware Waurin belt Win da aka ma yaron.

Karaf! Akan idanun Bintu da take saukowa daga can sama.

"""Ke! Keh! Ke Mashkura? Me kike ™o™arin yi haka?"""

Ta tambayeta cikin tsawa da Wan Waga murya tun kafin ta ™arasa sakkowa.

"Bib-biyu ta dinga harhaWa Step Win da Wan gudu-gudu har ta ™arasa sakkowa. Fuskarnan a Waure tamau,"

ko kallonsu Baffa bata yi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login