Showing 39001 words to 42000 words out of 147746 words

Chapter 14 - RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

ta sake daka ma Mashkura tsawar ta daina ™o™arin fito mata da Baby da take ™o™arin yi.

Da mamaki sosai a fuskokin su Baffa duk suke bin Bintu da kallo. Da farko kamar ba wanda zaiyi magana

"a cikinsu, sai kuma Baffa ya ce"

"""Ni ne na ce ta fito mana da shi mu Wauke shi a raWa mishi suna ayi mishi addu'o'i..."""

"""Yi ha™uri Baffa. Umarnin Likita ne ya ce kar a ringa damukarsa da hannuwa mabanbanta saboda"

"jikinsa baiyi k'wari ba bazai yi wahalar d'aukar cututtuka ba..."""

"""Bintu?"""

Hafiz da shigarsa cikin falon kenan ya tsinci maganar da take yi ya kira sunanta da mamaki sosai a

fuskarsa.

"""A hannun iyayen nawa ne zai kwashi cuta?"""

Ya sake tambayarta ranshi a bace.

"""Common dallah fito musu da Baby su d'auka in yaso ya kwashi cutukan duniya ba ma ciwo d'aya ba."""

Da saurin gaske Mashku ta karasa warware belt Win ta fito da shi ta mi™a ma Baffa. Ko fushi yayi ne Allah

"masani. Bai karSi yaron ba, sai Malam Ahmad ne ya mi™a hannu ya karSi Wan da murmushi a fuskarsa,"

duk a ™o™arinsa na shashantar da abinda ya faru.

"""Lallai wannan aboki namu manomi ne. Kai ka ganshi Abubakar har ya fi sadda aka haifi Hafizu girma?"""

Yayi maganar yana dariya idanunshi akan Waya daga cikin ³an'uwan Baffa.

"""A lallai kuwa. Da alamun an samu Sarkin noma. Bana damuna za tayi albarka."""

Baba Abubakar ya faWa shi ma fuskarsa cike da murmushi. Idanunsa akan jaririn yana kallonsa cike da

burgewa.

Bintu da take tsaye cikin matsanancin girgiza da tashin hankali don bata taSa tsammanin bayyanar Hafiz

"a daidai lokacin ba rasa tudun dafawa tayi. Bayan zafafan tambayoyin da Hafiz ya aika mata waWanda sam ba ta da amsarsu, a ™arshe ya Suge da yi ma tilon Wan nasu fatan kwasan miyagun cututtuka tana ganin wani mahaukacin kallo da yake aika mata daga inda yake zaune a ™asa kamar zai cinye ta Wanye."

Ita kuwa Mashkura daman tunda ta samu aka karSi jariri daga hannunta ba wanda yasan sadda ta bar

falon.

"Tsakanin Mal Ahmad da Baba Abubakar, Baba Lukman, Baba Hamisu kuma raha suke tayi a tsakaninsu"

suna karSa-karSa da jaririn suna addu'o'i da yaba girmansa.

"angaren Baffa kuwa babu wanda zai ce ga yanayin da yake ciki, fuskarsa a baibai take. Kuma har"

lokacin bai karSi jaririn ba. Ya ™ura ma guri Waya idanu kamar yana tunanin wani abu.

"Hafiz dai yana zaune a gaban iyayen nasa kan kafet, idanunsa a ™asa kamar zai saka kuka. Idan ya Waga"

kai ya kalli Bintu da take tsaye a gabansu kamar mutum-mutumi ransa a Sace sai kuma ya sunkuyar da kansa.

Ko da ake faWin karin maganar nan ta ruwa na neman ™are ma Wan kada bata taSa fahimtar cikakkiyar

ma'anarta ba sai yanzu da nata ruwan ke neman ™are mata.

Lura da tayi lallai idan bata yi gaggawar gyara wannan shirmen da ta tafka ba kwaSarta na gaf da yin

mugun ruwa yasa ta fashe da ™a™™arfan kuka sannan ta zube a ™asa. Da rarrafe ta ™arasa gaban Baffa ta ri™e gefen Babbar rigarshi ta fara jero mishi kalaman ban ha™uri cikin kuka da ™an™an da kai.

"""Na tuba Baffa na tuba. Don girman Allah kayi ha™uri ka yafe min. Kai mahaifi ne a gare ni idan baka"

yafe min ba ina zan saka kaina? Na rantse da Allah ba da gan-gan na so hana ku Waukar jaririn ba. Likitan yara Dr. Kauthar da ta fita yanzu kafin shigowarku ita ce ta ce lallai a kiyaye yawan Waukarshi saboda

gudun kwasar cutuka domin fatar shi babu ™wari. Don Allah kuyi ha™uri ku yafe min. Baba Abubakar ku

ma don Allah kuyi ha™uri. Malam ku yafe min don Allah bazan sake ba. Don Allah kuyi ha™uri. My dear

"kai ma ka yafe min."""

Irin yadda take rusa kukan tana magiyar su yafe mata ba ™aramin tausayi ta basu ba.

Gaba Wayansu basu wani ja da nisa ba suka ce sun yafe mata. Har suka sa baki Hafiz ya ce babu komai ya

wuce. Bata daina kuka ba har sai da taga Baffa ya karSi jaririn a hannunsa yayi masa addu'o'i.

Sannan ya mi™a ma Malam Ahmad ya sake yi masa huWuba ya raWa masa suna. Kafin ya raWa sunan ko da

"ya tambayi Hafiz ko suna da wani zaSin suna da suke so a raWa ma yaron da sauri ta riga shi cewa, duk"

dai a ™o™arinta na ™ara share laifinta ta ce

"""Malam ka raWa masa sunan Baffa ne don Allah. Daman tun kafin in haihu na ™uduri niyyar in dai namiji"

"ne sunan Baffa za'a sa idan kuma mace ce sunan Innaye za'a saka."""

Da wannan maganar da tayi yasa Malam ya raWa ma yaron suna Aminu (Al'ameen).

Rabi da take kicin tana laSe tana kallo kuma tana jin duk abinda yake faruwa babu abinda take yi sai

dariya.

"""Iya duniya ya fi iya mota."""

Ta faWa a fili tana sakin dariya ™asa-™asa. Da saurin gaske ta koma gurin aikinta ganin Bintu ta taso daga

gaban su Baffa ta nufo kicin Win da sauri.

"Tun safe, ta saka Rabi tayi mata farfesun kaji a zambaWa kayan ™amshi da Wan daddawa su dahu ruguf,"

ko za ta iya ci sosai saboda tunda ta haihu bakinta babu daWi.

Tana shiga cikin kicin Win ko kallon Rabi bata yi ba ta Wauki Waya daga cikin kulolinta masu tsada ta juye

farfesun gaba Waya.

"""Ki Wauko farantai da cokula ki kawo min falo."""

Ta ba Rabi umarni gaf da za ta fice daga cikin kicin Win.

Da kanta ta zuzzuba musu farfesun ta ajiye a gabansu tare da basu ha™urin su ci kafin a ™arasa abinci. Ta

mi™e za ta haura sama a fakaice ta kalli babynta da har lokacin yana hannun Mal Ahmad suna hira da

Hafiz suna ta dariya.

"Kamar ta ce ya kawo shi su ci abinci, amma tsoron kar ta sake Sallo ma kanta ruwa yasa kawai ta wuce"

zuwa sama duk zuciyarta a ™untace.

Lallai da gaske idan ka ji ™i gudu sa gudu ne bai zo ba. A irin wannan tsaka mai wuya da ta shiga cikin

"™an™anin lokaci, bata taSa tsammanin za ta iya samar ma da kanta mafita cikin sau™i haka ba. Sai ga shi tsabar tashin hankali da tsoron abinda zai biyo baya tsakaninta da Hafiz yasa ™wa™walwarta buWewa, ta"

"aikata aikin basira, hikima, wayau da bata taSa tsammanin za ta iya aikatawa ba."

"""Hmmmm!"""

"Ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta huro iska mai zafi daga bakinta, sannan ta buWe ™ofar Wakinta"

"ta shiga da siririyar sallama a bakinta. Duk jikinta a sanyaye, ga idanunta sun canja launi sun kumbura, alamun ta sha kuka."

Kallo Waya Raudha da take kwance akan gadonta tana daddanna waya tayi mata ta mi™e zaune da sauri.

Idanunta warwaje ta ce

"""˜awata lafiya? Me ya samu idanunki?"""

"""Uhmmm! Ke dai bari Raudha. Yau na tsallake rijiya da baya. Sai fatan Allah ya kiyaye na gaba."""

Amsar da ta iya ba ta kenan ta shige banWaki.

*****

"˜wan zabi ™warya uku, kajin hausa manyan zakaru guda goma. Garin kukar miya mai kyau da garin"

busasshiyar kuSewa su ne tsarabar da Baffa ya ri™o ma Hafiz da gidan Alh Lurwanu.

Duk yadda suka so tafiya da wuri sai da suka kai ™arfe Waya da minti goma a gidan Hafiz. Sun ci abinci

"sunyi nak! Sannan Baffa ya Wiba musu tsarabar ™wan zabbi ™warya Waya, kaji guda huWu, kuka da kuSewa dai bai Wiba musu ba, domin bai ga alamun cin tuwo a gidan Hafizu ba."

Baya ga haka ita kanta Innaye da ta bada kuka da kuSewar da sunan iyalan Alh Lurwanu ta bayar.

"""Ita kuma matar Hafizu fa?"""

Ya tambayeta da mamaki a fuskarsa.

Sai da tayi dariya kafin ta amsa da

"""Matar Hafizu ΄ar gayu ce ta bugawa a jarida. Har muka gama zamanmu a gidan ko da kuskure bamu ji"

"ta ambaci tuwo ba."""

"Dariya suka yi duk su biyun kafin ya sake mata sallama, ita kuma tayi mishi addu'ar Allah ya tsare hanya"

sannan suka fice daga gida.

Hafiz da kanshi ya tu™a su a mota zuwa gidan Alh Lurwanu. Ya rabbi! Mal Bahaushe ya ce in da ba ™asa

nan ake gardamar kokawa. Wata irin tarba ta girma kuma ta musamman da basu taSa tsammanin samun irinta ba suka samu a gidan Alh Lurwanu.

Duk da sun daWe da shaida shi Win mutumin kirki ne. Amma a wannan ranar ya ™ara tabbatar musu da

halayen kirki da karamcinsa. Ya kuma ™ara tabbatar musu da fa babu wani banbanci tsakanin talaka da

"mai kuWi, ko kuma banbanci tsakanin mutumin ™auye da na birni."

Irin yadda ya sake a cikinsu suna hira da SaSSaka dariya irinta manya suna caccafkewa a tsakaninsu

wanda bai sani ba sai yayi tsammanin aminai ne na ™ud da ™ud. Tun ana gobe za su zo Hafiz ya sanar da

"shi zuwan su Baffa, don haka ya soke duk wasu shirye-shiryenshi na ranar da za su zo."

"Kamar wasu manyan ba™i da suka taho daga wata ™asa, ™ayatattun girke-girke na musamman yasa aka yi"

musu. Bayan sun ci sun sha ya cika su da abubuwan arziki masu yawan gaske. A dole aka yi asaran tikitin

jirgin ™arfe biyu da Hafiz ya yanka musu aka sake booking Win jirgin ™arfe huWu.

Wani ™arin karamci na musamman da yayi musu shi ne tun kafin su isa Kaduna akwai direba na

"musamman da Alhajin ya tura yake jiran isarsu. Suna isa, ba tare da Sata lokaci ba ya kwashe su da"

kayayyakinsu suka kama hanyar Fa™o a wata luntsumemiyar mota da idanu kaWai zai bayyanawa mai kallonta mai masifar tsada ce.

˜arfe bakwai da rabi na yamma suna ™ofar gidajensu. Wannan tafiya dukkansu ba ™aramin daWinta suka

"ji ba, babu abinda ke fita daga bakunansu sai addu'ar fatan alkhairi ga Alh Lurwanu da duk zuri'arsa."

"Ana sauke kayayyakinsu ba tare da Sata lokaci ba direba ya juya zuwa Kaduna, duk yadda suka so ya"

tsaya ko abinci ya ci ya ce musu a ™oshe yake. Ya tafi suna ta bin shi da addu'ar Allah ya tsare hanya ya

maida shi gida lafiya.

******

"Da mamaki a fuskarta take kallonsa. Da yake har ta fara barci ya tashe ta, sai tayi tsammanin ko"

kunnuwanta ne basu ji da kyau ba.

"""Me ka ce Baban Yasin?"""

Ta tambaye shi don ™ara tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiye mata.

"""Na ce miki Hafizu ya kira ni Wazu da rana, ina cikin Kaduna ya ce in sami mai POS a tura mishi da"

Akawun namba. To a ta™aice dai bayan an tura mishi ba a daWe ba ya saka dubu Wari. Bayan ya tura

"kuWin ya sake kira na ya ce in samu motocin Bus guda biyu duk da tawa uku kenan musha mai, gobe idan Allah ya kaimu mu kwashe ku da sauran masu shirin zuwa suna mu kai ku Abuja..."""

"""Shi Hafizun ne ya faWa maka akwai masu shirin zuwa suna gidansa har mota uku?"""

Ta tambayeshi tana Wan harhaWe giran sama da ™asa. Kafin ya amsa mata ta ™ara da

"""Ai kuwa za ku mayar masa da kuWinsa. Domin ko ni da su Ladidi ba ma wani shirin zuwa suna balle"

"sauran ΄an uwa su ce za su je. Suyi sunansu lafiya, mu dai babu inda za mu je..."""

"""Wani irin zancen banza ne kike yi haka Balira? Matar Wan'uwan na ku sha™i™i namiji Waya tilo ta haihu"

"kuma haihuwar farko ku ce baza ku je suna ba?"""

"""To miye a ciki? Mun yi murna, kuma munyi addu'a Allah ya raya. Zuwa suna Habuja ne dai baza mu je"

"ba."""

Ta faWa da dukkan gaskiyarta.

"Kallonta yayi mamakinsa na ™ara girmama, sai kuma ya tuna tun bayan dawowarsu Abuja da daWewa bai"

™ara ji tayi mishi zancen zuwa gidan Hafizun ba. Lallai akwai wani abu da ya faru a wancan lokacin amma bata faWa mishi ba.

"Guri ya nema ya zauna a kusa da ita, a tausashe ya ce"

"""Me yake faruwa Balira? Ko akwai matsala tsakaninku da matar Hafizu ne?"""

"""Babu matsalar komai."""

Ta faWa da sauri. Domin a ganinta matsalar da ta shafi Wan'uwanta daban! Haka zalika matsalar da

mijinta zai sani daban. A ganinta babban kuskure ne ta kwaye ma Wan'uwanta baya a gaban mijinta. Kowa da muhimmancinsa daban!

"""In dai kuwa babu matsala suna dole sai kun je. Domin kuWin da ya turo har mun ciccika tankin"

"motocinmu da mai. Gobe sai tafiya da misalin ™arfe sha Waya na safe in Allah ya yarda. Bari ma in kira Baffa in faWa masa halin da ake ciki..."""

"""Ko ka faWa masa shi ma bazai goyi bayan zuwanmu suna ba. Kuma zan kira Hafizun yanzu in mishi"

"kaca-kaca tunda ba ya jin magana, tun rannan na faWa mishi baza mu je suna ba amma don neman zance shi ne ya tura muku kuWin mai. To kuwa sai dai yayi asara, ni kam ba ni zuwa ko ina"""

Baban Yasi dai bai saurareta ba ya fice daga Wakin ya barta tana bambamin faWa kamar za ta ari baki.

"A fusace ta Waga filon da kanta yake kai ta Wauko wayarta, ™an™ance idanu tayi ta lalubo lambar Hafiz ta"

danna mishi kira. Second Waya biyu sai ta ja tsaki ranta a Sace. A can Sangaren Hafiz da yake ya san

"yadda suka rabu da ita tun sa'adda ya tambayeta masu zuwa suna yana ganin kiranta ya ki daga wayar, a karshe ma sai ya kashe wayar gaba daya don kar ta cigaba da damunsa."

"[1/4, 7:40 PM] Fareeda Abdallah: Zancen d'aukar shatar motoci da Hafiz yayi ga masu niyyar zuwa suna"

"gidansa yana isa kunnen Baffa ya karbi maganar da hannu bibiyu. Irin yadda ya dinga nuna farin ciki da zumudi, ba karamin mamaki ya ba Innaye ba. Domin tun a daren ya fara kiran mazajen 'ya'yansa mata da suke gidan aure yana nema musu izinin tafiya suna gidan d'an'uwansu a Habuja."

"Ya kira 'yan'uwansa ya sanar da su lallai su fada ma matansu da yayansu da suke gidan aure, duk wacce"

take son zuwa suna gidan Hafizu mota kyauta ne zuwa da dawowa.

"Ya aika gidansu Innaye ya fada ma yan'uwanta. Tun Innaye tana shiru taga iya gudun ruwansa, sadda ta"

ga ya fara aikawa gidan abokan arzikinta yasa ta kasa hakuri har sai da ta ce mishi

"""Anya Malam gayyar mutanen nan da kake yi zuwa gidan Hafizu zai haifar mana da d'a mai idanu kuwa?"

"Matar Hafizu ba irin matan birnin nan bane da suke son mutanen kauye fa..."""

"""Ba don ita za su je ba. Don shi ne, tunda dai shi namu bai guje mu me ya dame mu da halinta na"

"gudun mutanen kauye? Na tabbata Hafizu bazai taba bari matarsa ta wulakanta masa yan'uwa ba."""

Ya katse Innaye tun kafin ta aje numfashin maganarta.

"""To shi kenan! Allah ya kaimu goben Lafiya."""

Ta yi addu'ar jikinta a sanyaye.

"""Ameen."""

*****

Motoci ukun da Hafiz ya dauki shata sai da suka cika tam da yan'uwa da abokan arziki saboda kara irinta

"mutanen kauye. Duk yadda Yaya Balira taso zille ma zuwa sunan sai da Baffa ya tilasta ta tafiya, haka nan ta shirya yan kayayyakinta kala biyu a cikin jaka suka kama hanya, duk zuciyarta a kuntace. Domin Allah"

ya gani sam bata so tafiyar ba. Ita da yan'uwanta da suke daki daya fuskokinsu ba yabo ba fallasa.

Su kuwa sauran yan'uwa da basu san dawan garin ba bakunansu har kunne. Sai murna suke suna

"dararraku, ko wacce tana baje labarin irin nisan tafiyar da ta taba yi a rayuwarta. Dukkansu dai kololuwar"

"tafiyarsu Kaduna ne, hatta yan'uwan Hafiz da suke uba daya basu taba zuwa gidanshi ba tunda yayi aure sai yanzu da za su tafi."

"Karfe biyar na yamma suka isa gidan Hafiz. Da yake ya shirya ma zuwansu sosai, wadataccen abinci yasa"

"aka dafa musu da ya ji nama zuk'u-zuk'u. Katan-katan na lemu masu sanyi aka tare su da shi da ruwan gora, komai dai sun same shi a wadace sai da suka ci suka sha suka bar saura."

Dakunan BQ da suke manyan dakuna kuma a wadace tun kafin su isa yasa an gyara ko ina fes! Daman

"akwai funitures a ciki, duk abinda babu kuma kafin su isa an tanade shi."

Gidan Hafizu bai fara d'aukar harama da nuna alamun gidan da za'ayi suna bane sai da suka isa. Duk da

tazarar da ke tsakanin inda suke da ainahin inda matar gidan da daidaikun yan'uwa da kawayenta ke zaune har nan ake jin hayaniyarsu.

"Bintu ta cika tayi fam kamar za ta fashe. Ita kadai sai huci take yi kamar kububuwa, amma ta kasa furta"

"ko uhmm! saboda Hafiz yana gidan. Kamar wata sakarya, da ya shiga dakinta ko kuma ya kira ta zuwa dakinsa sai tai ta washe mishi baki tana dariya duk don dai kar ya ji a zuciyarsa kamar ba ta maraba da zuwan 'yan'uwansa."

Tun abinda ya faru ranar da su Baffah suka je a tsorace take. Don ma Allah ya taimaketa Hafiz din ba

"mutum bane mai rik'o. A sadda abu ya faru, idan ya nuna bacin ransa cikin kankanin lokaci zai warware ya koma da walwalarsa. Shi yasa take iya yinta wajen kiyaye abinda zai sake janyo mata wani bacin rai da"

ba ta tunanin za ta iya warwareshi cikin sauki.

Abu daya da ya aikata ta ji nutsuwa kadan a ranta shi ne bai bar yan'uwansa sun shiga bangarenta ba.

Umarnin shiryawa yayi mata sannan ya dauki Baby Al'ameen wanda ake yiwa inkiya da Aadil suka je bangaren da aka sauki bakin suka gaisa.

"Tana ji tana gani sukai ta damukar jaririn ranta yana k'una, amma ko a fuska ta gagara nunawa har suka"

"gama gaisawa da tambayar lafiyar su Innaye sannan ta fice ta barsu da d'an'uwansa. Har d'an tsayawa tayi ko za'a ce ga Aadil ta wuce da shi amma ta ji shiru, haka nan ta fice ta barsu da Hafiz tana ta jan kananun tsaki a zuciyarta."

Gudummuwar naira dubu talatin 'yanuwansa suka hada mishi a matsayin gudummuwa. Sadda Aunty

Balira ta kebe shi gefe ta bashi kudin ji yayi kamar zai saka kuka. Zuciyarsa ta kara cika da kaunar 'yan'uwansa.

"""Mun so mu siya ma Babanmu kayayyakin jarirai sai kuma muka ji tsoron siyan abinda bai dace da ku"

"yan birni ba. Shi yasa kawai muka yanke shawarar taho maka da kudin, kayi hakuri. Ka san yanayin garin..."""

"""Haba! Ba komai Wallahi Aunty Balira, na gode. Allah ya bar zumunci. Na ji dad'i sosai Wallahi. Amma"

"yanzu dai ki ajiye min kudin a gurinki, zuwa safe in sha Allah zan karba."""

"Da haka suka rabu, ya karbi jaririn da ke ta barci hankalinshi kwance ya mayar da shi gurin Mamansa. A"

lokacin ana ta kiraye kirayen sallar Magriba a masallaci.

Washe gari da asubah tafiyar aiki mai matukar muhimmanci ta kama Hafiz da wasu daga cikin abokan

"aikinsa. Lagos za su tafi, bai so tafiyar ba ko kaWan, amma da yake kira ne da suka daWe suna jira daga branch Win su da ke Lagos yasa tafiyar ta zama dolen-dole. A gaggauce ya fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login