Showing 93001 words to 96000 words out of 147746 words

Chapter 32 - RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Mummy Saudah da Hajja a cikin gida Wakin Innaye zubewa kawai

sukai goshinsu a ™asa suna godiya ga Allah. Bayan sun mi™e tsaye kuma Hajja ta karkace kai ta ri™e hanci

ta fara rangaWa wata ™a™™arfan guda kamar yarinyar mace.

Daga bisani kuma ta fara rera wa™a irin tasu ta mutanen da tana ΄an raye-raye. Innaye dai tun tana

"kawaici tana Wan murmushi har ta sake ta fara dariya sosai. Cikin ™an™anin lokaci, Wakin Innaye ya cika da"

"abokan zamanta da yaran gida, matan ma™wafta suna yi mata Allah ya sanya alkhairi."

Mummy Saudah kuwa uwar Wakin Innaye ta shige ta ciro wayarta a cikin jaka ta fara latso lambar

΄an'uwa da abokan arzikinta tana faWa musu za'a Waura auren Baban Imam yanzu da bayan sallar azahar.

"""Haba Hajiya Saudah? Wani irin aure ne haka na bazata babu ko gayyata? Ko sadaka aka bashi?"""

KaWan kenan daga cikin ire-iren tambayoyin da mutanenta suke mata suna mamakin al'amarin.

"""Tsaleliyar yarinya ce Waya tamkar da miliyan. Ba sadakarta aka bashi ba, shi da kanshi ya gano ta ya"

"nace yana so, da yake dai iyayenta dattijan ™warai ne shi yasa daga zuwa tambaya suka ce za'a Waura aure nan da sati biyu sai ayi biki."""

"Amsar da take basu kenan, da matsananciyar murna a muryarta."

"Ko a wannan lokacin, sai da ta sake gwada kiran lambobin Hafiz amma gaba Waya basu shiga ba. Mamaki"

"ne ya kamata, don ya saSa daga cikin Wabi'unsa haka kawai ya kashe waya tun daren jiya har wayewar garin yau ga shi ana neman a sake yini bata same shi ba."

Ko da yake ta wani Sangaren rashin samunsa a wayar ma ya zame musu alkhairi. Domin rashin samun

nasa don ya kwatanta musu hanyar da za su bi don su zo Fa™o su kawo ma Zulai ziyara bayan sati biyu da

"tafiyarta yasa ta nemi Alhaji Lurwanu a waya, tunda ta san irin zumuncin da ke tsakanin Alhajin da iyayen Hafiz Win."

Ita kuma Alhaji Lurwanu ya kasance Amini ne ga marigayi mijinta Babansu Kamal. Da yake ita Win ba

"mace ba ce mai Soye-Soye, kai tsaye ta faWa ma Alhaji Lurwanu halin da ake ciki, da kuma a ta™aice abinda zai kai su ™auyen shi ne gaisuwa da ro™on iri."

"""Ai kuwa Hajiya Saudatu ina ga faWuwa ce tazo daidai da zama. Dama akwai abinda zai kai ni Kaduna"

"gobe, to kuma ina tunanin ™arasawa har can ™auyen in kai ma shi Malam Aminu ziyarar bazata, shi yasa ma ban faWa mishi ba. Don haka ina ga goben kawai sai mu tafi gaba Waya. Amma kuma ba kya ganin ya dace mu tafi da Alhaji Musa? Ko don acan Win su ™ara sanin lallai fa da gaske Kamal yake ™aunar"

"yarinyar."""

Abba Lurwanu ya ™ara mata da wannan shawarar.

Hangen nasarar da za'a ™ara cimmawa idan aka tafi da Alhaji Musan yasa bata Sata lokaci ba wajen saka

"Kamal ya kira shi ya faWa mishi halin da ake ciki. Daga bisani itama ta ™ara kiranshi a waya ta sanar da shi halin da ake ciki, ta kuma ro™i alfarmarsa na idan goben ba shi da muhimmin uzuri ya shirya su tafi tare."

Da yake tsakaninta da dangin mijin nata akwai kyakkyawar fahimta. Duk da yana da uzurin haka ya katse

komai nashi ya shirya aka yi tafiyar da shi.

"Ko da suka iso, irin kyakkyawar tarbar da suka samu daga su Baffa duk da ba'a san da zuwansu yasa ta"

™ara ji a ranta lallai Kamalu yayi sa'ar mata da surukai. Ita ma bata mishi zaSen tumun dare ba.

Duk da mamakin da tayi na jin labarin an taSa Waura aure tsakanin Hafiz da Zulai abin bai Sata ranta ba.

"Musamman da taji cewa duk zaman da Zulai tayi a gidanta a lokacin babu auren, ko kaWan bata ™ullaci"

Hafiz ba balle Zulai.

Abinda ta Wauka ma rabon Wanta Kamal ne ya rantse shi yasa da Hafiz yake neman inda zai aje Zulai na

"Wan lokaci gidanta ne kawai ya faWo mishi arai. Yo menene a ciki don Hafiz ya saki Zulai Wanta Kamal ya aura? Ai daman haka rayuwa take. Sai wani ya aje wani zai Wauka, kuma sai wani ya rasa wani zai samu."

"Ko yanzu da take sake kiranshi a waya ba komai take son yi mishi ba face godiya, sannan kuma ta bashi"

labarin duk irin halin da ake ciki. Kuma tayi mishi al™awarin in Allah ya yarda kafin su bar ™auyen ita da Abba Lurwanu za suyi iya ™o™arinsu wajen daidaita shi da iyayensa da suka lura ba ™aramin fushi sukai da shi ba.

"Sai a wannan lokacin, tunanin kiran Bintu don tambayar halin da Hafiz yake ciki ya faWo mata arai. Ba"

tare da Sata lokaci ba kuwa ta lalubo lambarta ta danna mata kira.

"""Wallahi Mummy ba shi da lafiya ne tun jiya. Kin ganshi nan kwance a gida na Waura mishi drip, barci"

"yake yi."""

Bintu ta faWa ma Mummy bayan gaisuwar da ya shiga tsakaninsu.

"""Subhanallahi! Me yake damunshi haka? Har da ™arin ruwa?"""

Mummy ta tambayeta da damuwa sosai a muryarta.

"""To ga shi nan dai Mummy, ya kwana biyu yana yawo da ciwon a tsaitsaye jiya zuwa yau ne dai ya"

"kwanta. Kuma ya ™i yarda mu tafi asibiti, na Wibi jininshi dai na tura asibiti yanzu ina jiran sakamako ne, amma na san bai wuce typhoid."""

Bintu ta amsa itama da tata kalar damuwar.

"""Allah ya sauwa™e ya bashi lafiya. Yanzu dai ba na Abuja, idan mun dawo da wuri zan le™o gidan, idan"

"kuma munyi dare gobe sunday zan shigo in sha Allah. Idan ya tashi ki gaishe min da shi."""

Da haka suka rabu.

"A can ™ofar gidan Baffah, Abban Imamu ne zaune a cikin ™atuwar jeep Win sa yana waya da abokinsa"

"Isma'il, bakinsa har kunne kamar gonar auduga."

"Tsananin farin cikin da yake ciki yasa tun Wazu ya kasa rufe baki, a yadda yake jin zuciya da ™irjinsa a"

"yanzu, kamar bai shiga cikin ™unci da matsananciyar damuwa a iya tsawon sati biyunnan da Zulai tayi ba"

ta amsa wayarsa kuma ba ta chatting da shi sai lokaci bayan lokaci ba.

"Shi da kanshi tun ranar da ta tafi da ya kira ta a waya ya fahimci tana cikin damuwa, amma duk yadda ya"

"buga ya kaWa ya raya ta ™i faWa masa abinda yake damunta. Idan ya matsa mata da tambaya ma, sai dai ta saka mishi kuka ta katse wayar."

Wannan dalilin yasa a daddafe cikin rashin nutsuwa da kwanciyar hankali yayi sati biyu bai biyo ta ba. In

"banda ya kasance yaro mai tsananin biyayya lallai da tuni ya ™etare umarnin Mummy ya bi bayan Zulai a Soye duk da bai san hanya ba, matambayi ai ba ya Sata."

Da gaskiyar Mal bahaushe da ya ce abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala bazai hango ba.

"Yanzu da ya danni zuciyarsa, ya cigaba da haWiWiyar ™unci da damuwa duk da damuwar Zulai na damunsa."

Sai ga shi jinkirin ya zame mishi gagarumin alkhairin da bai taSa zata ba. Daga zuwa neman aure sai ace a

Waura auren kawai a wuce gurin?

"""Wai da gaske kake yi Dude?"""

Isma'il ya sake tambayarsa daga can Sangaren da murya mai bayyana matsananciyar mamaki.

˜a™™arfan dariya ya kwashe da ita yana Wan dukan sikiyarin mota kamar ba shi ba.

"""Kana mamaki ko Dude? Nima har yanzu mamakin nake yi Wlh. Yanzu fa ana idar da sallar azahar"

"Winnan za'a Waura aurena... Gaskiya... ina cikin alkhairi dumu-dumu... Alhamdulillahi rabbil-Aalamin."""

"""Ma sha Allahu laa™uwwata illah billah! Na taya ka murna Aboki. Allah ya sanya alkhairi. Yanzu dai bari"

"in kira Auwal mu tsara yadda za mu biyo jirgin yamma zuwa Kaduna, wannan gagarumin abin farin cikin bai kamata ace bamu a kusa da kai ba..."""

"""Kar ku damu, ba sai kun zo ba. Mu ma bayan Asr prayer za mu kamo hanyar komawa gida. Ka san"

"yanzu Waura auren kawai za'ayi, bikin sai daga baya. Iyayenta sun nemi in basu sati uku ni kuma gaskiya bazan iya ba, na ma faWa ma Mummy gaskiya bikin kar ya wuce nan da sati biyu. So kaga duk wasu"

"shirye-shirye muna da isassun lokacin da za muyi a Abuja, duk da dai ni bidi'o'innan ba burgeni suke yi ba."

"Bari in je inyi alwala kar in rasa jam'i, za mu yi magana bayan Waura auren."""

"""To Aboki, once again Allah yasa albarka yasa mahaWin arzikinka ce."""

"""Amin ya Allah Dude. Na gode."""

***** *****

"[2/15, 9:35 PM] Fareeda Abdallah: Zulaikha da tun Wazu taja Karima da Imam suka tafi gidan Aunty Balira"

sam ba su da labarin halin da ake ciki. Suna zaune suna hira da dararraku sun tasa lafiyayyiyar gurasar da

"Aunty Balira ta gasa musu a gaba suna ci, kawai sai jin sallamar abokan zaman Innaye tayi wai sun zo tafiya da ita in ji Baffah."

"A tsorace, duk suke kallon su Umma Laraba, ita ta ma kasa cewa komai don tsoro da faWuwar gaba. Sai"

Aunty Balira ce tayi ™arfin halin tambaya bakinta na rawa

"""Umma lafiya kuwa? Me Autar Innayen tayi kuma?"""

"""A'a lafiya ™alau Balira. Bata yi laifin komai ba, abin alkhairi ne ya faru da ita. Auranta aka Waura yanzu"

"da Wan'uwan wannan yarinyar da take zaune kusa da ke. Duk da tarewar ba yanzu ba sai nan da sati biyu, kinga matsayinta na matar aure ai bai kamata ace an barta tana yawace-yawace ba, shi yasa Baffanku ya"

"ce muzo mu tafi da ita."""

Tsananin murna da farin ciki yasa Karima bata san sa'adda ta ture kwanon man ™uli da yake gabanta ba

ta mi™e tsaye ta fara kwaso shoki tana watsa ma Zulaikha. Lokaci Waya tana haWa da wa™ar gwanja ta

"Ahayye sama cibiyar nisa, tsakaninki da yaro sai kallo."

"Aunty Balira babu abinda bakinta ke furtawa sai kalaman godiya ga Allah, da jinjina girman hikima irinta"

"Ubangijin sammai da ™assai, da ya ™addara faruwar komai cikin ™an™anin lokacin da basu taSa tsammani ba."

"Zulaikha kuwa, da farko daskarewa tayi a zaune, bakinta a Wan buWe, ta ™ura ma Umma Laraba idanu"

"don ji take kamar dai kunnuwanta basu ji abinda aka faWa daidai ba. Sai da karaWin Karima ya isheta sannan tayi firgigit, sai kuma matsananciyar kunya, da wani irin matsanancin daWi da farin ciki suka lulluSe sassan jikinta."

Cusa kanta tayi a tsakanin cinyoyinta tana murmushi ™asa-™asa. Ita kaWai take jin ta kamar wacce take

yawo a kan gajimare.

"""Ashe haka ake ji a jiki da zuciya idan aka auri wadda ake so?"""

"Ta tambayi kanta da kanta. Da gaske tana son Abban Imam, irin matsanancin son nan da ita kanta baza"

"ta ce ga iyakarsa ba, domin a wasu lokutan soyayyarta har zillo da tsungulin zuciyarta take yi."

"Kawai dai a matsayinta na mace, wacce aka fi sani da kunya da kawaici, da iya danne abu a zuciya yasa"

take matu™ar ™o™ari wajen yi ma soyayyar tasa waigi a zuciyarta. Amma in da ba don haka ba... Wata-kila da tuni ta ™wace da sambatun sunansa da labarin irin son da take masa duk bayan minti Waya biyu...

A ™arshe dai gurasar da basu samu ™arasa ci ba kenan. Ita ma Aunty Balira mi™ewa tayi ta bi bayansu

"bakinta har kunne bayan ta haWa sauran gurasar a cikin ™aton kwanon samira, ta yayyanka kabeji ta tafi"

da shi da nufin kai ma mahaifiyar Karima da Kakarta Hajja.

"Ko da ta isa gidan Baffa, irin yadda ta ga Mummy da Hajja na tarairayar Zulaikha da ina za'a saka ina aka"

aje da ita cikin matu™ar ™auna da tarairaya yasa ta ™ara ji a ranta lallai fa yanzu ne Autar Innaye ta daje

da miji Waya tamkar da dubu. Irin wannan ™auna da tarairaya haka? Gaba Waya sun babbake komai sun hana kowa kusantar Zulaikha.

"Hajja da ta kasance haifaffiyar ™auye ita ta dinga lissafa irin kayayyakin da take bu™ata a kawo mata,"

"wanda za ta fara yi ma Zulaikha amfani da su wajen gyaran jiki. Cikin ™an™anin lokaci aka haWa mata komai, sai ga Hajja a gaban murhu tayi bake-bake kamar ΄ar gida, Balira, Indo, Rakiya, Ladidi da sauran manyan ΄a΄an Baffa suna kusa da ita tana basu umarnin daka wannan, mi™o wancan, Wauraye wannan,"

"kuma ta ri™e sunayensu ram a bakinta, kamar dai daman can ta san su."

"Cikin awanni biyu da suka biyo baya, Hajja ta haWa lafiyayyen ruwan lalle da yaji magunguna da turaruka"

irin nasu na mutanen da tayi ma Zulaikha wanka da shi. Ana wankan tana zazzaga ma Zulai masifa

saboda yadda take ta no™ewa cikin kunya.

"""Kin san Allah Zulai zan ci ™aniyarki. Kalle ni dakyau! Jikata na Wauke ki ba matar jika ba. Yadda zan bugi"

™irji in shirya Kareema ranar aurenta haka zan shirya ki Zulai. Don haka duk wannan nu™u-nu™un da kike

"yi gara ma ki bari, bai sha min kai ba in saka tsumagiya a cikin banWakinnan in zane ki ciki da bai idan kika ce za ki min taurin kai. Atoh! Ni ba ruwana. Haka nake free falo, kin sanni sarai."""

"Ko bayan gama wankan, haka ta tasa ta gaba da haya™i kala daban-daban. Daga ™arshe aka yi mata"

"wankan turare, a cikin sabbin kayayyakin da suka tafi mata da shi aka zaSi doguwar riga Waya aka ba ta ta saka."

"Bayan dogon naci da ro™o da Abban Imam yai tayi ma Mummy, a ™arshe ya bi ta hannun Anty Balira da"

sabo na surukuta ya shiga tsakaninsu cikin ™an™anin lokaci ya samu damar ganawa da ita a falon Baffa.

"Tunda ta shiga cikin Wakin, ta kasa Waga idanu ta kalle shi, wata matsananciyar kunyarsa ce ta lulluSeta."

"Ko gaisuwa da™yar ta iya buWe baki ta gaishe shi, ™irjinta banda bugawa babu abinda yake yi, har yanzu,"

ganin komai take yi kamar ba da gaske ba.

Shi kuwa babu kunya yayi zaman dirshan a gabanta kan dadduma yana le™en fuskarta. Bakinsa har

"kunne, da farko ya kasa cewa komai bayan gaisuwarta da ya iya amsawa."

"""Beb kin ga ikon Allah ko?"""

"Ya tambayeta bayan ya ga kiran Mummy na shigowa cikin wayarsa, yasan ba kiran komai bane face na"

"tunasar da shi ™urewar da lokaci ya fara yi, ™arfe huWu na yamma har ta gota."

"""Alhamdulillah!"

Alhamdulillah!!

"Alhamdulillah!!! Daga yau, har zuwa ™arshen rayuwata, bazan taSa gajiya da cigaba da godewa"

"Ubangiji da ya nufe ni da samun aurenki a sau™a™e ba Zulaikha. Wallahi ina son ki, irin matsananciyar"

"soyayyar da ni kaina ban san iyakarta ba. Ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya da zuri'a Wayyiba."""

"""Ameen."""

"Ta amsa da™yar, a ciki-ciki."

"""Baffa yace bikin sai nan da sati biyu, amma ni dai ina jin gaskiya bazan iya bari har sai nan da sati biyu"

"ba... zan je in ro™e shi ya bari mu tafi da ke yau kawai..."""

"""A'a don Allah kayi ha™uri."""

"Tayi maganar a shagwaSe, tare da buWe fuskarta da sauri tana kallonshi da dara-daran idanunta."

Da sanyin murya ya ce

"""To bayan ma tunda kika taho ja min aji kike tayi don kin ga ba na kusa da ke, na san yanzu ma idan"

"nayi gangancin tafiya na barki haka za ki cigaba da ja na a ™asa tunda ba wani so na kike yi ba..."""

"""Ayya Ayya mana Abban Imam."""

Ta sake faWa a shagwaSe. Kafin yayi magana ta sake cewa

"""Allah kuwa ba haka bane. Kawai dai tunda nazo ba na cikin nutsuwa ne saboda abubuwan da suka"

"faru. Kayi ha™uri, bazan sake ba, ka ji?"""

"˜uriii yayi mata da idanu yana kallonta, yadda hatta muryarta yake fita da wani irin sanyi da ™amshin da"

"yake Wan bugun fuskarsa. Wani daddaWan shaukin ™auna na ™ara ratsa duk sassan jikinsa. Tun da ya fara ganinta, ya rasa dalilin da yasa, komai tayi burge shi take yi, kuma kyau na musamman take ™arawa a idanunsa ko wane lokaci."

Domin kawai ya ™ara ganin shagwaSa da taSarar da take masa yasa ya ma™ale kafaWa kamar ™aramin

yaro ya cigaba da tsokanarta.

"""Na ™i Win! Ba wani nan. Na san wayau kawai za ki min. Ni dai gara kawai mu tafi yau gaba Waya."""

"""Allah ba wayau zan maka ba. Don Allah ka bar maganar tafiyarmu yau."""

Tayi ™wal™wal da idanunta kafin ta ci gaba da cewa

"""Ka ga fa yanzu an ce an Waura mana aure, idan na ™i bin umarninka ai sai mala'ikun rahama suyi ta"

"tsine min. Haka ne ko? To don Allah ka yi ha™uri, ka ji Abban Imamuna?"""

"Tayi masa far da idanunta, ™asa-™asa ta cigaba da cewa"

"""Kuma maimakon sati biyu ma ina laifin wata biyu? Kamar gobe ne za kaga sati biyun ta zo ta wuce, a"

"cikin sati biyu bazai isa inyi shirye-shiryen komai ba..."""

"""Lallai ma Yarinyar nan. Baki isa ba Wallahi."""

Ya katse ta da sauri yana Wan buWa mata idanu.

"""Sati biyun ma Wallahi don Baffa ya yanke ne, amma Wlh da bazan bari ba ki ™ara sati biyu ba tunda"

"kin zama matata. Ni fa ba na son komai, na faWa ma Baffa tun Wazu amma ya ™i cewa komai. Ke nake so,"

don haka ke Win kawai nake bu™ata. Alfarmar da aka yi min ma wajen mallaka min wannan zu™e™iyar

"yarinyar ba tare da na wahala ba ya ishe ni abin alfahari..."""

"""Yaya? Wai Mummy ta ce anan za mu kwana ne? ˜arfe biyar na yamma ta wuce fa"""

Ya tsinkayi muryar Karima daga can bakin ™ofa tana faWin haka.

"Da sauri Zulaikha ta mi™e tsaye tana zazzare idanu tana kallon ™ofa, a tsorace take sosai kar Karima ta"

shigo taga irin zaman da Abban Imam yayi a gabanta.

"""Je ki ce mata ga ni nan zuwa."""

"Ya amsa yana Wan Sata fuska, kamar Kariman tana gabansa."

"Hannu yasa ya janyo Zulaikha da ta nufi hanyar fita daga Wakin da sauri, da yake janyowar na bazata ne,"

"taga-taga kamar za ta faWi yayi saurin tareta ta faWa jikinsa. Ko kafin tayi wani yun™uri na ™wacewa, yayi"

"mata wata kyakkyawar runguma, kansa ya Wan kwantar a saman ™irjinta yana sauke ajiyar zuciya sauri- sauri."

"Lokaci Waya jikinta ya mutu murus, bata yi wani yun™urin ™wacewa ba don ri™o yayi mata ba na wasa ba."

"Runtse idanu tayi da ™arfi, tana jin yadda ™irjinta ke bugawa sauri-sauri, a tsorace take gaba Waya."

"""Ina son ki. Don Allah ba don ni ba ki kula min da kanki sosai. Kuma ko da yaushe ki zama kusa da"

"wayarki. Kin ji?"""

"Sosai bakinta yayi mata wani irin nauyi, sai da ™yar ta iya Waga masa kai, alamar ta ji."

"Wasu da™i™un ya sake Satawa yana ri™e da ita a jikinsa kafin ya sake ta a hankali, hannunta na dama ya"

"kamo, ya laluba aljihun wandonsa ya Webo kuWaWen ciki gaba Waya ya dam™a mata."

"""Ko da za ki bu™aci wani abu don Allah kar ki tambayi su Baffa. Ki faWa min a waya, zan saka a kawo"

"miki duk abinda kike bu™ata."""

"""Tam!"""

Ta faWa a hankali.

"""Don Allah ka bar kuWinka, babu abinda zan nema. Allah ya mayar da ku gida lafiya."""

"""Amin Maman Imam."""

"Ya amsa da sanyin jiki, bai karSi kuWin ba kamar yadda ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login