Showing 423001 words to 423255 words out of 423255 words
duk motsin ku, da duk abun da take yi, muna samun labari ta ɓangaren Jamil.
Dan haka sai ka zaɓi ɗaya, fito na fito da masu ƙasa, ko kuma ka rasa rayuwarka da na matarka, dan ka san ba abu ne mai wahala ba. Sai dai fa ka yi haƙuri, domin kuwa rayuwar matarka ta salwanta kamar ko wani karabutin ɗan ƙasa, duk da kasancewar ka mai kaki, kuma jinin babbar masarauta, ire-iren yaranmu ne kisan su baya tafiya a banza. Kuma duk wani abu da zai faru Jamil ba zai taɓa furta sunana ko na ɗa na ba. Dan haka gara ka watsar da duk wani yinƙurinka, ka tattala abun da yayi saura a rayuwarka, kan mu gama ɗiaɗaita ku" ya katse wayar.
Duk da hatsaniyar da ta kaure a falon, yanayin da takawa ya shigo, ya sanya kowa yin shiru, wani irin gumi yake yi, jikinsa yana tsuma, kuma aka rasa mai tambayarsa meyafaru, kowa ya zuba masa ido.
Ruma ce ta miƙe tsaye, ta ce "Papa lafiya kuwa?"
Gabanta ya ƙarasa, jiki a matuƙar sanyaye ya zube a kan gwiwoyinsa ya furta "Na gaza, dama kin gaya mini, na gaza rumaisa ba laifina bane, na yi iya yina, abun ya fi ƙarfin yadda nake tunani, na barwa Allah, tun da a cikin gidanmu ma aka kware mini baya, ba ni da saurin ƙwarin gwiwa. Da izzar da tawa da sarautar tawa da komai na zube su a kan gwiwoyina, na gode rumaisa, na gode. Ke alkhairi ce ga rayuwata da ahalina, wataƙila ba dan ke ba,