Showing 342001 words to 345000 words out of 423255 words
idan na taso zan biyo, sai na dawo"
Ammi ta ce "Allah ya tsare".
Abun ya din ga damun Adam, baya son tonawa Jabir asiri, amma sam bai dace da auren Iman ba, salihar yarinya kamar wannan, duk da kashedi da gargaɗin da yayi masa, bai ji ba, bai kuma janye maganar son auren Iman ba.
Ga wanccan batu da rumaisa ta ɗaukko masa a kan Jamil, gaba ɗaya sai abubuwan suka ƙara rikice masa. Sosai yake son saka pressure a kan Jamil, dan har yayi maganar da Bashir ma, sai dai gefe ɗaya yana tunanin anya haka zai yiwu kuwa? Kar ya ɓata zumuncinsu, tayaya Jamil zai saka hannu a ɓatan aisha, bayan babu wanda ya san ma ta zo ƙasar sai shi, kar ya biyewa shirirtar rumaisa ta rufta shi, amma duk da haka akwai ƙamshin gaskiya a maganganunta.
Ƙarfe sha biyu ya kira sidi a waya, ya ce ya je ya ɗauki rumaisa, ya mayar da ita gida.
Ƙarfe biyu ya tashi, daga wurin aiki, ya tafi wurin aikin su Jabir.
Fuskar Jabir babu yabo babu fallasa, suka gaisa.
"Jabir, zuwa na yi na ji dalilin da ya sanya ka je ka samu ammi, ka ce mata kana son iman, baya ka san yadda muka yi da kai?".
"Tambayar da ka zo ka yi mini kenan Adam? Ka watsa komai kana neman ka ɓata zumunci, saboda kana auren wannan ƴar yarinyar, gaba ɗaya kanka ya juye, abun da ta ce kawai shi kake yi babu bincike? Ka je ka cewa Jamil yana da saka hannu a ɓatan matarka, ta yaya ƴar uwassa ce fa, ta yaya zai yi hakan? Ta ce Mummy tana yi maka asiri, magana ta koma kunnenta, ka je ka yi wa ƙannenka wulaƙanci dan su je gidanka duba ka, dan rashin ta ido, a gaban Mummy, yanzu kuma ka zo kana maganganu dan na ce zan auri Iman, kai ka san aurena da iman shine rufin asirinta, kuma ka sani Mummy sun kai ƙararka wurin mai girma wambai, dan yau da safe ya kira Ammi a waya, lallai yana nemanka, kuma zama za ayi na mussaman a kanka da matarka, dan da yiwuwar har gaban mai martaba, ba zai yiwu dan ka yi aure, ka hargitsa mana family ba.
Duk da gaban takawa ya faɗi, amma cikin jarumta ya ce "Jabir, gaban mai martaba ba gaban Ubangiji bane ba, daga nan a kaini duk in da aka ga dama, shi ciki da gaskiya, wuƙa ba ta taɓa huda shi" ya fita ya bar office ɗin.
Yanayin yadda ya zo ya wuceta a falo, ya sanya ta gane, akwai damuwa, har zata basar da shi, sai ta ji ba zata iya ba, ta bi bayansa.
"Papa, yau ba cin abinci, ba magana, iya sanina ban yi wani laifi ba"
Ya ɗan lumshe ido ya ce "Bakomai, ki je bacci zan yi".
"Ba bacci ka ke ji ba, wani abu ne yake damunka", ta yi maganar tana murza zoben hannunsa. A hankali ya buɗe idonsa ya kalleta.
Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Bari na yi maka ta Yaya usy, ya ce gist me masoyiya ya ake ciki, to gist me aboki ya ake ciki?"
Ita duk tsananin situation, ba ka rabata da wasa.
Sai ya samu kansa da gaya mata halin da ake ciki.
Ta kwashe da dariya ta ce "Ohh, ni ƴa su, yaro bai san wuta ba sai ya taka, to kar a fasa kaini wurin mai martaban mana, idan ban warware kowa a gabansa ba me nake, ni fa bana tsoron kowa sai Allah, kuma wallahi duk abun da na faɗa gaskiya na faɗa. Sai in faɗi komai a gaban mai martaban".
Cikin rashin fahimta ya ce "Me zaki faɗa?"
"Ba zan gaya maka ba, daga gaya maka abu a kan Jamil ka je ka gaya masa, dama na san zuciyarka ba zata bari ka danne ba, shiyasa bana gaya maka wasu abubuwan, sai ka ɓata mini aiki, ni bana ƙwaina sai da zakara, ka san wanda ya gaya wa Mummy na ce tana yi maka asiri?"
Ya ce "A'a"
"To baba uwani ce, kuma ina sane na faɗa, dan daga ita sai ammi da iman a wurin na faɗa, baba uwani na kwasar sirrin ammi, ta je ta gaya wa Mummy. Saura kuma ka faɗa so muke mu kama ta red handed, Daddy ya tabbatar mini da ya ganta sau biyu a sashin Mummy cikin dare".
A sukwane ya tashi zaune, yana kallon rumaisa kamar ya ga abun tsoro, ya fara tsorata da lamarin rumaisa, kamar wata mai rauhanai.
Ta tura baki ta ce "Meye kuma? Saura ka gayawa wani, idan ka faɗa ba zan sake gaya maka abu ba, yanzu in anjima mu je gida, ina son in ga Mummy, na tabattar maka da babu wanda zai wani kira ka ya tuhume ka".
"Kin fara bani tsoro ne, don't make things complicated, tayaya za ki ce baba uwani tana cin amanar mu?"
Rumaisa ta ce "Ai ban ce ka yarda ba dama, amma zan tabattar maka da hakan, yanzu dai zo mu ci abinci, mu yi wasan gudu a backyard, in anjima in je wurin Mummy".
Ya ce "Am not in mood, je ki yi wasanki"
"To buɗe mini wayarka na yi game" shiru yayi mata, ya tsunduma kogin tunani.
Ta ɗau wayar, ta kama yatsansa ta buɗe, ta jingina da jikinsa tana dannawa.
Shi muma ya bita da ido, kamar mai kallon abun al'ajabi.
Ta gama danne-danne wayarta, ya ajiye masa ta tafi nata shagali.
Sai dai da ta sauka ƙasa, ta tarar baba uwani bata nan, ta tambayi su Asiya, suka ce mata tun safe ta fita ba ta dawo ba.
Ta tafi backyard, ta samu ball ta yi tayi, kamar ba matar ba sarake ba, ta window takawa yake hangota, yadda take sarrafa ball ɗin a ƙafarta ka san ƙanwar maza ce.
Da la'asar bisa kasada, takawa ya ɗau ruma suka tafi gida, suna tafe yana sake tambayar ta, me za ta cewa Mummy, ita kuma taƙi faɗa masa.
Ko da suka je, ya ce sai dai su shiga tare, ita kuma ta ce idan tare suka shiga, abun ba zai yiwu ba.
A falo ta tarar da ruƙayya tana danna remote.
Rumaisa cikin fara'a ta ce "Mummy tana nan ne?".
Ruƙayya tayi tsaki ta ce "Wace Mummy?".
"Jamila babarku"
"Sunan Mummyn ki ke faɗa haka?"
"Kin ji abun da na ji, ranar da ki ka faɗi sunan Ammi gatsal".
Mummyn ce ta fito tana waya, tana ganin rumaisa ta yi turus.
Ruma ta gaisheta, cike da duniyanci, ta yi murmushi ta ce "Amarya ba kya laifi, yau ke ce a sashina?"
Ruma ta ce "Eh Mummy wurinki na zo".
"To gani"
Ruma ta ce "Sirri zamu yi"
"Ba damuwa Bismillah" suka shiga wani ɗakin na daban.
Ruma ta ce "Mummy, na ji kin kai ƙarar papa ne, shi ne na zo na baki haƙuri, dan Allah ki janye, kar ki saka ayi taron nan, ni nayi laifin ba shi ba".
Mummy ta yi murmushi ta ce "Turo ki aka yi kenan? Gara na kai ƙararku ai, dan ban san laifin da na yi muku ba, kuma taro babu fashi, dole ku je ku wanke ni".
"Mummy, tayaya zan san kina yi wa papa asiri, sharri aka yi mini, baba uwani ce fa ta gaya mini, kina yi wa papa asiri"
A firgice ta ce "Baba uwani kuma?".
"Ita, kuma ba ƙarya take yi ba, tun da na kamata da wannan ɗazu da safe" rumaisa ta yi maganar tana ɗagawa Mummy, wasu layoyi, da wasu irin abu a cikin leda.
"Yanzu ko dai ki janye maganganun ki, ko kuma idan aka je gaban mai martabar, zan gaya masa komai, kuma mu ma muna da CID a sashinki, wadda take kawo mana rahoto. Abun da baku sani ba shi ne, na sanku tun kan na shigo cikinku, ina kuma sake maimaita muku, tunanin maza bakwai ne a cikin kaina, da kuma nawa na takwas.
Mummy ina roƙonki, da ki jingine makaman nan, ki sassautawa mijina haka, wallahi a dalilinsa nima bani da kwanciyar hankali, muraran nake ganin abun da mutane ba sa gani a kansa, dan Allah ki bari ya huta haka.
Ayshercool.
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Mummy ji tayi, tamkar an sanya mata dabaibayin ƙarfe an ɗaure mata ƙafafuwanta, ta kasa motsi, jikinta kuma yayi wani irin mugun sanyi, ta kasa motsa ko ina. Har rumaisa ta gama yi mata maganar, ba ta iya cewa uffan ba, mussaman ganin wannan layoyin a hannun rumaisa, kuma rumaisan ta ɓare fatar tsaf.
A tsakiyar garden ɗin gidan, ta bawa baba uwani ta binne mata, shi ne cigaban aikin da ake yi mata a kan Adam, akwai irin layoyin a gidansu, akwai a gidan da ya zauna da aisha, wannan karon ma an yi ta saka a gidansa, saboda ana son ya din ga shige da fice a kai a kai, a in da layoyin suke.
Kuma wannan laya ta bawa baba uwani jinin mage, da za ta din ga zubawa a ƙasar wurin sa'ai da lokaci.
Da safe rumaisa na ta sauri, ta kammala abun da za ta yi kar ta makara, dan haka ana idar da sallar asuba ta hau ayyukanta, sai dai kanta ya din ga sara mata, ta din ga kamar wani sauti, daga bayan ɗakinta, kawai ta sauka ta zagaya, wanda a nan ta iske baba uwani, ta gama binnewa, ta jira ta bar wurin, ita kuma ta tone ba ta sani ba.
"Ina sake roƙonki Mummy, mu rabu cikin mutunci da kwanciyar hankali, abun da aka yi a baya, Ubangiji Allah ya yafe, amma idan aka cigaba a haka zaku ji babu daɗi, na san ni yarinya ce a kan ku, da ku ke yi mini kallon mara hankali, amma zan iya abun da tunaninku bai taɓa kaiwa kai ba, kamar. Na kama baba uwani, kuma ta yi mini bayanin komai, wanda kafin in dawo daga makaranta ta bar gidanmu, amma kar ki damu, ban gayawa kowa ba, daga ni sai ita muka sani, idan kin so, sirrin zai zauna daga ni sai ke, idan kuma aka matsa mini, ki tambayi takawa yadda nake" ta mayar da ledar cikin hijjabinta, ta fita.
Sai da ta fita sannan Mummy ta ji ta dawo hayyacinta.
Jikin Mummy ya fara tsuma, tana zazzare ido, gaba ɗaya ta kasa tunani ma, neman wuri ta yi ta zauna daɓas a kan gado, wani irin gumi ya din ga tsatstsafo mata, har ta tsakanin cinyoyinta.
"Lallai wannan uwani an yi ƴar........, ni zata tonawa asiri, mutuniyar banza da ta wofi?"
Jiki na rawa ta janyo wayarta, ta kira baba uwani.
Baba uwani ta fara koɗata, ta ce "Ke dalla saurara mini, ashe baki da hankali? Shi ne ki ka bari yarinyar nan ta kama ki, kina binne-binne a gidan?".
"Ni kuma? Ai ba ta kamani ba, wallahi ba ta gani ba"
"Ƙarya ki ke uwani, yanzu ta bar shashina, da ƙullin layoyin a hannunta, ni zaki munafunta? Ashe baki da mutunci? Tun yaushe na baki aikin, ki ka ajiye baki yi ba, har ta gani, kenan ma ke ki ka gaya mata ina yi wa Adam asiri".
Kamar baba uwani ta saka kuka, ya ce "Wallahi, wallahi hajiya ba haka aka yi ba, ina iya ƙoƙarina dan Allah kiyi haƙuri".
Kashe wayar mummy ta yi, tana fifita da hannunta, gaba ɗaya ta gigice.
Ruƙayya ta shigo ɗakin, tana duban Mummy ta ce "Mummy ya aka yi ne, wai me ta ce miki?"
"Bakomai, jeki hutawa zan yi" Ruƙayya ta ɗage kafaɗa ta fice.
Rumaisa ba ta tarar da takawa a in da ta bar shi ba, dan haka ta wuce sashin Ammi.
Ta tarar da shi a zaune a gaban ammi suna hira, sabir sai hawa yake wuyan takawa yana saukowa.
"Ammi sannu da gida"
Ammi ta ce "Yauwwa ƴar auta ta, ina ya baro mini ke ya shigo shikaɗai? Ai ban san tare ku ka zo ba"
Ta zauna ta ja yatsan takawa da ƙarfi ta ce "Tafiya yayi ya barni".
"Ke baki san da zafi bane" ruma ta harare shi ta ce "To waye ya ce ka tafi ka bar ni?" Ta mayar da idonta kan Ammi ta ce "Ammi ina Anty Iman ne?".
Ammi ta ce "Kin san ta sarkin ɗaki, tana can ko tana bacci ko tana karatu".
Rumaisa ta tashi ta nufi ɗakin Iman, Sabir ya biyota, ta tsaya ta ɗauke shi suka tafi tare.
Ammi ta ce "Yaya ake ciki, ai yanzu rigimar ta ta da sauƙi ko? Kuna sabawa a hankali na ga ta rage daru sosai".
Yayi murmushi ya ce "Ba zata sauya hali ba, kawai na koyi zama da ita ne kawai. She's simple at times wasu lokutan kuma ba a gane kanta"
Ammi ta yi dariya ta ce "Tun da ka iya zama da ita ai Alhamdilillah, Allah ya ƙara haɗa kanku"
Ya ce "Amin, sai dai Ammi akwai wani abu".
"To, Allah ya sa ba matsala ba ce"
"Ba matsala ba ce ba, ta ce zata gaya wa mummy abun da zai saka a fasa kirana wurin mai martaba, ban san me ta ce mata ba"
Ammi ta ce "Wai yanzu daga can take?"
Ya ce "Eh".
"Takawa meyasa ka barta? Idan kuma ta je sake hargitsa lamuran fa?".
"Ammi, am testing her thinking capacity, tama Sharp brain fiye da tunani, kuma na fara yadda da abun da ta gaya mini a kan Jamil, idan har tayi nasarar sanya Mummy, ta janye ƙarata data kai wurin su mai girma wambai, duk abubuwan da rumaisa take faɗa gaskiya ne".
Ammi ta numfasa ta ce "Takawa, kaifin basirar yarinyar da tarbiyyarta, su ne suka saka na zaɓa maka ita, ni na san tana da kaifin tunani tun kan ku yi aure, tana da basira. Dan haka a ƙara haƙuri, ka bi komai a hankali, bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu zuwa kafin ka yi tafiyar nan, abun da hali zai yi"
"To shikenan Ammi, in sha Allah".
Ammi ta ce "Amma zan so sanin me za ta gaya wa Jamila, da har zai sanya ta janye abun da ta je ta faɗa".
Takawa ya ce "Nima na so sani taƙi faɗa, kuma mun yi da ita ba zan gayawa kowa ba. Idan na cigaba da matsa mata ba zata faɗa ba".
"To Ubangiji Allah ya iya mana, ya sanya ita ce sanadiyyar warwarewar matsalolin nan"
"Amin Ammi".
Ruma kuwa a kwance a ƙasa ta tarar da iman, a ɗan razane ta ƙarasa ta taɓa jikinta, ta ji yayi ɗumi.
"Anty iman, lafiya ko baki da lafiya ne? Ciwon kan ne ya dawo?x ta jero mata tambayoyin.
Iman ta tashi zaune, tare da yin yaƙe ta ce "Maman sabir, saukar yaushe?"
"Ba wani saukar yaushe, baki da lafiya ne?".
"A'a lafiyata ƙalau, kawai dai kwanciya nayi".
Rumaisa ta zaune sosai ta ce "Ke da papa wasu lokutan halinku ɗaya ma, idan ba rashin lafiya ba, akwai damuwa fuskarki ta nuna, dan Allah anty iman menene, bana son in ga damuwa a fuskarki, gaba ɗaya raina ɓaci yake yi. Ko wani ne yayi miki wani abun? zan iya rama miki".
Cikin dauriya, Iman ta ce "Maman sabir, bana son ɓacin ranki nima, kasancewarki a tare da ni, yana bani ƙwarin gwiwa.
Zan gaya miki menene, amma dan Allah kar ki bari ammi ta sani, kin san bana son damuwarta".
"Anty iman, duk surutun nan nawa, ina ɓoye sirri, gaya mini ko bani da maganin zan tayaki da addu'a".
"Ammi ce ta ce mini, wai uncle J yayi mata maganar yana so na, wai zai je ya sanar da mai girma turaki, a zo a nema masa aurena, naga ammi tana murna, amma....." Sai kuma tayi shiru.
Rumaisa ta ce "Amma ke ba kya son sa ko?"
Iman ta zubawa rumaisa ido.
"To wa ki ke so, dan ni ma bana son wannan jabir ɗin, babarsa ba ta da mutunci, wahalar da ke zata din ga yi"
"Ba na son kowa maman sabir, bana son sake yin Soyayya, na barwa Allah lamarina, amma wallahi bana son jabir".
"Kin tabattar babu wanda ki ke so, tuna dai" ruma ta yi maganar tana basarwa.
Sai da gaban iman ya faɗi, tayi fatan, Allah ya sa ba ganota rumaisa ta yi ba.
"Na tabattar bana son kowa ni yanzu"
"Amma ya san ba kya son sa ya nace, kar ki damu ki yi ta addu'a, wannan masifaffiyar babar ta sa ma, ba bari za ta yi ba. Ko kina son wani a yayyena, amma su talakawa ne?"
Iman kallon rumaisa take yi, tana son gano gaskiya, ko dai ruma ta gano ta ne. Ganin sun gaza haɗa ido, ya sanya ta ce "Kin manta nima talaka ce, ƴar fulanin tashi da aka tsinta a dokar daji, ai mutane masu asali kamar yayyenk......"
"Iman bana son wannan maganar wallahi, raina ɓaci yake idan kina gayawa kanki haka"
"Shikenan na daina".
Ruma ta ce "Da dai yafi, yauwwa da muka je gida ranar, mai sunan baba ya tamabayeni kina ina? Na ce masa kina nan ƙalau"
Murmushi ne ya bayyana a fuskar iman ta ce "Allah sarki yaya umar" ruma murmushi kawai tayi, dan tuni ta harbo jirginsu.
"Kar ki damu anty iman, ba zan gayawa ammi ba kya son sa ba, amma in sha Allah ba za ki aure shi ba, dan nima haushin sa nake ji. Bari na je wurin papa" ta tashi ta koma falo, ta tarar ammi ta tashi.
Ta je ta zauna a kusa da adam, ta yi ƙasa da murya ta ce "Done, na gama aiki, ka zuba ido ka gani".
Adam ya ce "Amma baki gaya mini me ki ka ce mata ba".
"Zan gaya maka, amma sai ta fasa ɗin tukuna"
Ya ce "Shikenan, mu tafi ne, kin gama?"
Ta ce "A'a sai da daddare"
"Aliyu ya kirani, ya ce mini mama ta za ta yo miki aike, wannan yayan naki mara fara'a zai zo"
Ruma ta ce "Da mai sunan baba ka ke ko?"
"To waye mara fara'a idan ba shi ba"
"Hmmm, ai kusan halinku ɗaya, ina kallonku fa ko magana ba kwa yi, kowa yana ji da kansa ko, zan gani dai "
"Ke waye ya ce miki bama ma magana"
Ta kai bakinta kunnensa, ta kare da hannunta ta ce "Ina kallon duk abun da ku ke yi fa, idan ku ga