Showing 3001 words to 6000 words out of 59199 words

Chapter 2 - FAHIMAH Book 1 Hausa Novels by Takori kabara .pdf

ya nuna ba karamin mutum ba ne, ilmi da hatimin nasara
sun wadace shi. Sannan ga wani irin sassanyan kyau da ya rasa gane daga kabilar da ya
dauko shi. Above all Allah ya yi ma Uwais wani irin kwarjini, ilhama da cikar zati da ya wuce ya
nemi alfarma wurin mutum a kasa yi mass.
Amsar da ya so bayarwa sai ta canza kanta ba tare da ya ankara ba, domin da farko so ya yi ya

ce su tashi su tafi, ba yanzu zai yi wa yarsa aure ba.

Wane ne Babanka? Kai dan wace kabila ne? Gama na ga ba Bahaushe bane
Uwais ya muskuta sannan ya kara dukar da kansa in ka ganshi a wannan lokacin kamar bawan
da ke neman taimako. Ji yake zai jure komai, zai iya komai in dai Alhaji Dikko zai ba shi auren
Amrah a karshe.
"Sunanan Babana Grand Khadi Abdulkarim Shagari, ya jima da rasuwa, na girma a hannun
mahaifiya ta, Babana basakkwace ne, mahaifiyata basudaniya ce.
Alhaji Dikko ya gyada kai, sannan ya kara jifansa da tambaya.
Mene ne matakin karatunka? Kuma mece ce sanaarka?
Uwais ya zuki numfashi, a ransa ya ce, wannan wane irin mutum ne?
Ina da kwalin digiri na biyu, sannan ni banker ne da Guaranteed Trust.
Alhaji Umar Dikko ya gyada kai cikin gamsuwa, sannan ya ce, Kana da masaniyar cewar Amrah
karatun likita ta ke yi a matakin farko? Za ka iya jiranta ta kammala tsawon shekaru shidda?
Uwais ya hadiyi yawu da kyar shi fa jiran ne ba zai iya ba, burinsa ya bude ido ya ga ya mallaki
Amrah, don haka bai yi kasa a gwiwa ba.
Daddy, ku yi min alfarma, na yi alkawarin barin Amrah ta yi ta karatunta a dakina har sai ta ce
ya ishe ta.
Ya kara dukar da kansa cike da zullumi da fargabar amsar da zai samu daga Alhaji Umsr Dikko.

Bai san dalilin da ya sa farad daya yaron ya shiga ransa ba. Kamalarsa ce ko kamewarsa? Ba
zai iya cewa ba, ga wasu exceptional qualities da ya gani a tare da shi. Shi kansa Jabir a yadda
ya san mahaifin su bai zaci tambayoyin Daddyn nasu za su tsaya a nan ba. Sosai Alh. Umar ya
dubi Uwais kafin ya ce,
Na ba ka izni ka nemi auren yata. Idan ta amince da kai dari bisa dari zan iya ba ka aurenta a
bisa alkawarin da ka yi min na cewa za ka barta ta ci gaba da karatu a gidanka.
Besides ni kuma zan yi nawa kyakkyawan binciken a kanka da iyayenka, idan na samu wani
mummunan hali a tare da kai zan dakatar da kai. My daughter is innocent ka yi taka tsaftacciyar
muamala da ita a cikin neman aurenta.
Farin ciki ya sa bakin Uwais ya kasa rufuwa, kansa a kasa ya yi godiya tare da alkawarta wa
Daddyn insha Allahu zai kiyaye abin da ya fada masa, kuma da yardar Allah ba zai samu wata
mummunar shaida a kansa ko iyayensa ba.

Suka fito shi da Jabir, inda Jabir din ya ja shi suka shiga cikin gidan wajen amaryar Babansu
Aunty Nana. Suka gaisa tana da kirki sosai. Jabir ya gabatar mata da Uwais matsayin
abokinsa, kuma manemin auren Amrah, wanda Daddy ya san da zamansa a yanzu. Aunty
Nana ta yi mamaki sosai, don ta san Daddyn ya ce ba zai aurar da Amrah ba sai ta kammala
MBBS. Ta karbi Uwais hannu bibbiyu, ta yaba da komai nasa cikin ranta. In Amrah ta same shi,
to hakika ta yi dace da miji na nuna wa saa.
Suka taho gidan Jabir inda Uwais ya sauke shi, Jabir ya yi masa tayin shiga gidan ko zai so yin
magana da Amrah. Uwais ya yi murmushi ya ce da shi,

Not now, Im not in contentment, tunda na samu licence dina.

Zuwan Uwais na farko wajen Amrah a wani daren asabar ne, ana tsula ruwan sama, ruwan har
ya fara jika shi, a lokacin da ya yi parking ya fito daga mota, ya bi ta garage zuwa falon Jabir
inda nan ne ba shi da shamaki, kuma sun yi waya da Jabir ya ce yana gida ita ma Amran tana
nan. Amma ya ce masa ya zo da wuri don Amrah in ta fara karatun darenta ba ta so a katse ta.
Kuma wannan ne karo na farko da za su ga juna officially, ta sanshi a fuska amma a matsayin
abokin Yayanta.
Yana zaune a falon Jabir yana mai duba agogon hannunsa. Jabir ya ce da shi ya jirata tana
zuwa, sannan ya gaya wa Murjanatu Amrah na da bako a falo, kuma da sanin Daddy ya zo
ganinta.

Bako daga Daddy?
Amrah ta tambayi Aunty Murjanatu cikin mamaki. Murja ta ce, Haka dai ya ce, kuma ki yi sauri
yana jiranki.
Ko kadan Murjanatu ba ta yi mamaki da zuwan Uwais yau wajen Amrah ba, don ta dade da sa
wa a ranta in ka ga kare na sunsunar takalmi dauka zai yi.

Amrah ta yi sallama a falon da siririyar muryarta mai kidima nutsuwar Uwais. Mikewa tsaye ya yi
ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba. Har sai da Amrah ta shigo suka tsaya suna
kallon-kallo ta hasken farin kwan lantarkin da ke falon. Zuciyarsu na bugu iri guda a lokaci guda,
yayin da Amrah ta ji tamkar an sauke mata wani nannauyan dutse daga kirjinta.
Uwaisun da ta ke kwana da shi tana tashi da shi Uwaisun da ya yi wa zuciyarta babakere ya
hana ta sukuni da jin dadin rayuwar ko ta ya ya, yau ga shi a gabanta officially ya kawo kansa
matsayin manemin auren ta..Me zata ce? Ko me zata yi? Banda tazbihi ga Ubangiji?
Ita ta fara dauke idonta daga cikin na Uwais amma ta yi-ta yi ta furta kalmar ina wuni? Ko sannu
da zuwa ta kasa. Zama ta yi a kujera mafi kusa da ita, ta jingina kanta a makarin kujerar don
hana kafafun ta kayar da ita daga wadannan kaifafan sexy eyes din na Uwais, tana sauke
numfashi a hankalitamkar Uwais ya karanci abinda ke ranta, sai bai wahalar da kansa wajen
gabatar da kan sa ba. Kai tsaye ya tafi straight to the point .
Amrah am I welcome as a husband?
Uwais ya fada daga karshe, yana mai durkusawa a gabanta a kan gwiwoyinsa.... wani abu abu
da bai taba tunanin zai iya yi a kan diya mace ba.
Murmushin da Amrah ta yi, da fuskarta da ta rufe da tafukan hannunta kadai a matsayin ta na
bafullatana tamkar amsa ce ga UwaisUwais Shagari, Uwais Abdulkarim Shagari.... and that is
the beginning mafari, tushe, sila, na dukkan abubuwan da suka biyo baya......Sannan silar data
zamo hanyar auren UWAIS da FAHIMAH...... ****



Ya dauki lokaci mai tsayi yana zuwa zance wajen Amrah, sun fahimci juna sun yarda da juna,

soyayya ta yi kaka-gida, hutun nata da ma na watanni uku ne, har ga shi gobe za ta koma
Abuja inda daga can za ta zarce makarantarsu ta Limkwokwing, Malaysia.
Yau da ya zo sallama ce za su yi, in ka gansu very emotional kamar masu shirin barin duniya
don damuwa, Amrah ta shiga ran Uwais yadda ba'a zato haka Uwais ya samu matsayi mai
girma a zuciyar Amrah, ta yadda suke jin rabuwar tasu ta yau har cikin bargonsu.
Ba don kada in yi wa Daddy laifi ba ya ce zan hana ki karatu, da na kawo miki ziyara a
Malaysia.
Amrah ta zaro ido ta ce, Kada ma ka fara 'Habib - Qalby', Daddy bai hada karatu na da komai,
za mu kasance a waya koyaushe insha Allah. Abinda zan sake dawowa bayan watanni hudu
kuma a nan Kano zan sake yin hutuna?.
Ke kike ganin watanni hudu kwana hudu Amrah, i see them like eternity. To Amrah ta ya ya zan
amince ni ina nan goho ina jira, wani a can ba zai min shigar sojan badakkare ba?. Ya fada
sounding emotionally worried. Amrah ta yi murmushi, ta ce, Tunda Daddy ya amsa maka, to ka
kwantar da hankalinka ya tsumma a randa, domin Daddy ba ya magana biyu. Sannan ni wa zan
kula? Karatun da ke gabana kadai ya ishe ni, ka yarda da ni Habib-Qalby...(sunan da ta rada
masa) a Hausance yana nufin 'masoyin zuciya ta'..
Ya ce, Na yarda da ke Amrah, in na ce yarda ina nufin yarda ta har abada cikin aminci. Ki yi
karatu mai yawa with me in mind and our next coming babies.
Amrah ta kai tafukanta ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Ba ta ga lokacin da Uwais ya taso daga
kujerarsa ba, sai tsinkayarsa ta yi tsaye a gabanta, hannayensa duka biyu zube cikin aljihu, ya
ce,
Amrah kin amince min kafin ki dawo in tura magabatana wajen Daddy su kara rokonsa a
gabatar da neman aurenmu?
Na yi alkawarin za ki cigaba da karatunki ko da kina Malaysia ni ina nan Kano. And I promised
you eternal love Amrah, jiran ne ba zan iya ba.
Amrah ta kai hannu ta rufe fuskarta, kyakkyawan murmushin da ke kan fuskarta kadai amsa ce
ga Uwais, na ta amince ya tura neman auren ta. Don haka da karfin gwiwarsa ya koma gida duk
da yana cikin alhinin rashin Amrah da zai yi a kwanakin. Ta riga ta zama wani bangare na
ruhinsa cikin dan lokaci kalilan.
Ya shigo gida misalin karfe goma na dare. Tuni Ammi ta dade da kwanciya. Har ya shiga
bangarensa. Ya yi wanka ya canza kaya zuwa Pajamas farare sol ya ankara da yana jin yunwa,
yunwa sosai da ke bukatar tallafi, ya san yanzu Talatu ta jima da komawa Baskwata, Ammi
kuma ta kwanta, don haka ya yanke shawarar zuwa kitchen ya nema wa kansa dan abin da zai
iya ci ko ya yi barci cikin nutsuwa.

Ta juya baya tana fasa kwai a cikin tangaran, ita ma yunwar daren ce ta taso ta, kawai sai ta jiyo
takun mutum a bayanta, ta juyo da sauri duk da kamshin turarensa ya riga ya gaya mata ko
waye. Ya sunkuya ya bude firji ba tare da ya lura da tsayuwarta ba, Fahima ba ta kara mallakar
kanta ba daga lokacin sabida rudewa da bugun zuciya wanda ke faruwa da ita a duk sanda ta
ga Uwais.
Kwan hannunta ya subuce ya fashe a kan kafarta, daidai lokacin da ya dago da gorar ruwa a
hannunsa sai idonsa cikin na Fahimah. Wani haushi ya kama shi da karfi ya ce,

What are you doing here? You Goddam Black, mai idanu irin na kyanwa! Ganinki cikin dare sai
ya firgita mutum get out from here.
Ya fada da tsawa.
Jikin Fahimah na mugun rawa ta juya ta bar kicin din, ko kamin ta kai dakinta hawaye ya jika
fuskarta. Ta tsani tsawa, ta tsani kyara da hantara. Amma inda sabo ya kamata a ce ta saba da
su daga bakin Yaya Uwais, don tun tana karama duk wata haduwa da za su yi in dai ba'a gaban
Ammi ba ne to irin haka ce ta ke kasancewa. You goddam black
Ta saba da wannan kalmar. Shin laifi ne in mace ta kasance baka? Shin kyawun halitta shi ne
yake sa wa a so mutum? Ko kuwa dai akwai wani dalili da ya sa Uwais ya tsane ta bayan
wannan da rashin asalin ta? Za ta so wani makusancin sa ya samo mata wannan amsar daga
Yayanta Uwais. Amma ta san ba za ta taba samun wannan alfarmar ba, ta sanin wani abu da ya
danganci wannan kwayan mutum guda daya mafi soyuwa a zuciyarta, sannan mafi munana
mata.
Yunwar da ya shiga kicin din da ita sai ya ji ta dauke sabida bacin ran ganin Fahima. Tsaki ya yi
ya ajiye gorar ruwan ya koma daki. Ya yi nafilfilin da yake yi kafin ya kwanta sannan ya dauko
waya ya kira Amrah don jin muryarta ne kadai zai sa ya yi barci lafiya.
Sun dade suna hira, planning iri-iri na irin yadda za su gudanar da rayuwar aurensu. Hatta
yayan da za su haifa sai da suka kayyade. Sannan suka koma musun da wa suke so yayan su
yi kama, shi kuma ya dage da ita yake so su yi kama itama ta dage da shi take so, a haka suka
shiririce suka bata lokaci. Hirar da ta kai su har sha biyun dare, sai da Amrah ta soma hamma
sannan suka yi sallama.
Da wani irin nishadi Uwais ya yi barci don in yana gaban Amrah ko yana jin sassanyar muryarta
manta kansa yake yi, duk wannan miskilancin da izzar nemansu yake ya rasa in dai yana
tareda Amrah, in ka ji shi yana zubo hira da kalaman soyayya ka kuma sanshi a tsumammen
Uwais dinsa manajan GT ba za ka taba yarda cewa shi ne ba.
Fahimah a wannan dare ba ta runtsa ba. Ba bacin ran abin da ya yi mata ke damunta ba, aa
soyayya ce ta ke nukurkusarta, soyayyah yar usli mara algus daga indallahi wadda ba za ta iya
tantance daga lokacin da ta samu muhalli a zuciyarta ba. Abin da ta sani kawai shi ne, ta taso
cikin son Yaya Uwais ba tare da ta san hakikanin mene ne maanar feelings dinta a kansa ba.
Sai yanzu a hankali da hankali ya soma game jikinta, ta fahimci zuciyarta is infactuated sosai a
kan Yaya Uwais, son da ta tabbatar ba zai taba amfana ta da komai ba.
Don haka a wannan dare Fahimah ta yanke shawarar fara adduar Allah ya cire mata Uwais
daga zuciyarta ko ta samu sa'idah. Ya munana shi a zuciyarta kamar yadda ta ke mummuna a
tashi zuciyar.

Har aka yi kiran assalatu ba ta yi barci ba, tana kai wa Sarki Allah kukanta a kan Uwais. Amma
ko da ta kwanta barci bayan ta sallaci asubahi, mafarkin da ta yi ya firgitata...
9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: *****
Washegari da ta gama shirinta tsaf na tafiya makaranta ta cimma Ammi a dakinta tana karatun
littafin Bulugul Maram da ta ke yi duk safiya. Ta tsugunna a gabanta ta gaishe ta sannan ta yi
shiru tana wasa da yatsun hannunta. Ammin ta lura akwai magana a bakinta, ta rufe littafin ta

ce,
Ya aka yi autar Ammi? Kina son wani abu ne?
A hankali Fahimah ta motsa dan bakinta kamar mai tsoron abin da za ta fada. A karshe ta daure
ta ce,
Ammi don Allah kada ki ce Yaya Uwais ya dauko ni a makaranta, don yau ma muna da practical
na food and nutrition. Ammi zan dawo da kaina tunda gobe Surajo (direbanta) zai dawo. Ammi
yar ki ta girma, ki bar ta ta dinga yin komai da kanta. Ta karasa da murmushi.
Murmushi mai sauti Hajiya Safiyyah ta yi, alkunyar yarinyar na sa wa ta kara shiga ranta. Ta
tabbata Uwais rashin kirkinsa ya yi mata jiya, sannan ya hora ta da ynwa, amma ba za ta fada
mata kai tsaye ba sabida kawaici irin nata. Ta kai hannu ta shafa kan Fahimah affectionately..
I will not send him to pick you again, na lura da yadda ya azabtar da ke da yunwa jiya, amma
kansa ya yi wa. Ungo kudin mota ki hawo adaidaita ki dawo gida.
Ta karbi kudin da hannu biyu ta yiwa Ammi godiya ta wuce.

Ammi, sai na dawo!.

Ammi ta ce, Rehlah Saeedah (wato a dawo lafiya).

Bayan wucewar yarinyar Hajiya Safiyyah ta lumshe ido ta jingina bayanta da bango tana tunani.
Anya mafarkin ta zai zama gaskiya? Anya Uwais zai cika mata burinta? Idan kuma ta tursasa
shi anya tirsasawar za ta haifar da Da mai ido? A kafiya da miskilanci gami da izza irin nasa da
ta dade da sani? To in ba shi din ba wa zai auri Fahimah ya rike mata ita da amana? "Babu!"
Amsar ta kutso da karfi cikin kwanyar ta.
Ko ta samu masoyi ya ji ko wace ce ita guduwa zai yi, in kuma ya karbe ta a haka tofa babu
daraja da martaba. Uwaisun dai da ta haifa shi kadai ne guarantee dinta a kan Fahima, amma
baro-baro ya nuna gara kowa da shi in dai a kan ya so Fahimah ne. son ma irin wanda ita ta ke
mafarkin ya yi mata, wanda ya kasa karbarta a kanwa ta jini, ta ya ya zai yarda ya karbe ta a
matsayin MATARSA?

Shekaru goma sha biyar a baya suka soma gilma mata tamkar a majigi.

*****

TUSHEN LABARIN!
Bayan haihuwarta ta biyu ne jini ya tsinke mata, washegarin haihuwar yar ta koma ga
mahaliccinta. Ita kuma ta samu matsalar da dole aka cire mata mahaifa bakidaya. Shi kadai
gare ta, shi kadai Allah ya bar mata, UWAIS kenan.
Mahaifinsa Justice Abdulkarim Shagari tsohon alkali ne dan asalin jihar Sokoto, wanda ya taka
har matsayin Grand Khadi a lokacin rayuwarsa. Dan asalin Sokoto ne amma a Kano ya rayu
sanadin aikin sa da ya samu a Kano, ya yi kuma aure da Safeeyah tun yana dalibin digiri na
biyu a kasar ta Sudan inda ya yi dukkan karatunsa. Sun zauna a can shekaru biyar, sannan ya taho da ita kasarsa ta haihuwa, Nigeria, ya samu

aiki da (Shariah Court of Appeal), ya sanya ta a jamiar Bayero, inda ta yi nata karatun a fannin
tsimi da tanadi. Allah ya azurta su da Da guda daya, ko ace daya tamkar da goma, shi ne
Uwais, wajen haihuwarta ta biyu ne waccan matsalar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login