Showing 30001 words to 33000 words out of 59199 words

Chapter 11 - FAHIMAH Book 1 Hausa Novels by Takori kabara .pdf

mu'amalar auratayya
a tsakanin su, ta fahimci Uwais ya daina kin Fahimah, ya daina kyararta. Ya karbi auren ta kan

ba yadda zai yi. Ya kuma fara daina dagawa kansa hankali akan kiyayyar ta.

Shi yasa katin hannunsa ya bude dakin suka shige. Yana rufe kofar ya dube ta a dage, ya ce,
“You Goddam Black, ina wayar ki? Your Mum wants to talk to you in bana nanâ€?.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Yana gama daure mata hannun ya fice ba tareda ya kalle ta ba,
tare da cewa,
“idan kin gama kukan I’m waiting for you outside. Ni ba ni nasa kika yanke ba balle ki kai
karata wajen Mamar ki�.

Ta dauki mintuna biyar kafin ta iya komawa hayyacinta. Abubuwa na ta faruwa cikin ‘yan
dakikannan kamar a mafarki. Kwakwalwarta ta kasa digesting kowanne daga ciki domin Uwais
Shagari ya koma mata tamkar hawainiya.
Bata yi zaton yana da wannan compassion din ko yaya a kanta ba, bata yi zaton zai yi wani
action a dalilin fitar jini daga jikin ta ba. Har ya bita da kalaman kare kansa. Ta fahimci dai guilty
ne ya lullubeshi kawai.
Hijab dinta ta sanya wani zurmeme da shi sannan ta janyo trolley din kayanta ta da Ammi ta
hada mata ta tadda shi a waje. Uwais ya baza shanyayyun lumsassun idanunsa don ganin ina
Fahimah za ta zaba don zama. In ta jera da shi a gidan gaba ya zama raini, haka in ta je baya
ta zauna ya zamanto shi ne direban ta ya zama rashin kunya da tsaurin ido, ace ya zama
direban ‘yar gidan marayu tsintacciyar Ammi? Ga mamakinsa tsayawa ta yi hannayenta
dogare da karfen trolley din tana jiran umarnin sa. Wato ya zaba mata wurin shiga da kan sa.

"Bata da azarbabi"

Ya fada calmly daga cikin motar ba tareda Fahimah ta ji shi ba.
“To ai gara in zama direbanki da ki zauna a muhallin AMRAH, don haka shigo bayaâ€?.
Ta kyabe baki ba tare da ya gane ba. Ta rasa me ya sa ta daina jin shakkar sa yanzu, ta fi
alakanta hakan da maganganun da ya gargasa mata wadanda suka taimaka gaya wajen gaya
mata ta kara martaba kanta a idanun Uwais idan shi bai martaba ta ba, ta daina yarda wata
mace ta fi ta don kalar fata kamar yadda Baba Talatu ta ce. Sai dai kuma ba za ta iya yi masa tsaurin ido ba, don haka ne ta bi umarninsa ta bude booth ta
sanya jakarta, sannan ta zagayo ta bude kofar baya ta shige kamar yadda ya umarta.
Tana kallonsa sai da ya karanto addu’ar barin gida, ya shafa, sannan ya ja motar a nitse. Ya
kure kira’ar Minshawy cikin suratul Nisa’i. Uwais na jin darajojin da Allah ya baiwa mata
da hakkokin su a wurin Ubangiji kasancewar sa masanin tafsiri. Dukkansu zuciyarsu ta nutsu da
sauraron karatun nan, tension din bacin-rai da fargaba da ke cikin zukatansu na tafiyarsu tare
da juna da Ammi ta hada su ba zato ba tsammani ya ragu 50% a dalilin jin ayoyin Ubangiji mai
girma.

Ko da suka iso airport ya nemi inda ya adana motarsa kirar Elantra yadda ko kwana nawa ya yi
zai dawo ya tadda ita a wajen lafiya.
Fahimah dai bin Uwais ta ke inda duk ya jefa kafarsa kamar rakumi da akala, tana fama da
jakarta da ta dan fi karfin ta domin ya ki karba mata tasa kawai yake ja. Ba su bata lokaci ba

suka samu jirgin Bell-View mai tashi zuwa Ikko a yanzun nan.
Uwais don dai ya bakanta wa Fahima sai ya kai ta economy class shi ya zauna a first class
seats. Abin da bai sani ba Fahimah ko a jikin ta, don ba ta san wani bambanci tsakanin
economy da first class ba. Ita hakan ma ya fi mata, domin zama kusa da Uwais ai ba karamin
takura ba ne.
Har suka sauka a Lagos ba ta bawa zuciyarta damar yin wani tunani ba bayan na yadda za ta
zauna da Uwais a muhalli guda. Something inescapable, something terrible�...something
unavoidable, Ammi ta rigada ta hada tafiya kuma ta gudu ta bar ta, haka ta ke kallon wannan
moment din da za ta yi tare da Uwais a wannan dan tsakanin na rayuwarta like eternity
moment. Ammi ta kinkimo mata aikin da ba ta taba shiryawa ba (zama da Uwais a muhali
guda). Jin dadinta daya tsoron Uwais da ta ke kamar na mala’ikan daukar rai ya ragu sosai
daga zuciyar ta. Tana jin kanta ta daidai da daukar kowanne irin challenge daga gare shi, tunda
dai ya bi umarnin mahaifiyarsa bai yaudareta ya baro ta a gida a bayan idanun ta ba.

A nan filin jirgin Fahimah ta fahimci tafiyar tasu ta gamayya ce shi da abokan aikinsa. Sai dai
mutum daya ne Bahaushe, sauran duk kabilu ne. Wasu cikinsu sun taho da matansu, amma
Uwais bai yi introducing Fahimah ga kowannen su ba, su dai sun ganshi tare da mace, kuma da
ya ke sun san ya yi aure ba dadewa sai ba su ce komai ba. Domin sama yake da su a mukami,
matan biyu sun gaisa da ita, Femi da Ronke, amma yadda ta ga Uwais na harararta sai ta kama
kanta bayan gaisuwar ba ta kara kallonsu ko shiga sha'anin su ba.
Da kananan motoci na GT Bank aka zo aka kwashe su zuwa masaukin da aka tanadar musu a
(Cascade- Wellness Resort Hotel). Hotel ne mai kyau sosai a Ikoyi ta jihar Lagos. Ta lifter suka
bi zuwa dakin su, Uwais ya sa key din da aka ba su ya bude.
Fahimah bata san lokacin da ta yi catching numfashinta dinta da karfi ba, da ta fahimci dakin
falle daya ne tal, ma’ana ba ciki da falo bane bedroom ne guda daya. Amma gadon dakin
babba ne sosai yadda sai mutum biyar su kwanta ba tare da daya ya gogi daya ba.
A gefe ga sofa-bed, sai tebirin aiki da study-lamp daga can gefe. Bedside fridge da tv a jikin
bango, sai wardrobe ta kayan sawa, bayan wannan babu wani tarkace a dakin, very neat ga
rabar A/C na fita ko ta ina da kamshin room freshner mai sanyi, kuma komai dake dakin daidai
bukatar kowanne dan Adam ne.
Uwais bai ce wa Fahimah komai ba yana aje trolley dinsa ya yi zaune gefen gado yana latsa
wayarsa. Wayar Ammi ya kira don ya ji saukar ta, amma ba ta shiga ba, sai ya aje wayar ya
fada toilet. Wanka ya fara yi sai alwallah, ya yi brush sannan ya fito daure da towell iya
kugunsa. Har zuwa wannan lokacin Fahimah na nan tsaye inda ya barta tana sakawa tana kwancewa. Ko
da ta daga ido ta dubi Uwais daure da towell saura kadan fitsarin da tuntuni ya cika mata mara
ya balle ya zubo. The extra-ordinarily well-built structure, the physique chest, the muscles and
masculine appearance su suka taru suka kusa nakasta ‘yan kananan idanunta. Fahimah tayi maza ta runtse su gam-gam ba ta kara budewa ba, jikinta na mazari kamar wadda
sanyin kankara ke kadawa.
Sauri ya yi ya zura jallabiya a jikinshi don shi ya manta ma tana dakin. Da bai fito a haka ba,

kada ta raina shi ko ta kalle wa Amrah miji. Gara ya je ya nemi wani dakin ya kai ta, shi ba zai
iya kwana da mace a daki ba Amrah ba.
Ya tada sallah, a ransa yana fadin, idan kafafunta suka tara jini za ta zauna ne. Bayan ya idar,
ya kira kan talfon ya yi odar abincin mutum biyu ba tare da ya tambaye ta wanda ta ke so ba. Ya
san dai abincin gidansu kullum ganye ya fi yawa (vegetables) don haka abin da ya yi order
kenan, sai white rice and stew da farfesu. Ba jimawa aka kawo, lokacin ta gaji da tsayuwar da runtse idon kamar yadda yayi hasashe ta
shiga toilet. A yanayin da ta ke jin jikinta ga gajiya ga takurar period wanka kawai za ta yi ta ji
dadi, don haka ta yi wankan, ta kimtsa kanta, ta yi brush sannan ta maida kayan jikinta ta fito.
Samunshi ta yi yana cin abinci. Looking smart and gentle a duk abin da yake yi. Uwais, ba zai
daina tafiya da ruhinta ba watakila har gaban abada! Komai nasa mai ban kaye ne ga zuciyarta,
ba tun yau ba ta dade tana satar kallon sa in yana cin abinci. Wani irin gaye yake komawa mai
yanga idan yana cin abinci amma ba wai ya san hakan ba shi. Actually bai san me ya sa ba, jin
haushinta da tsanarta da yake sun dan ragu, but bai da wani feeling ko kankani a kanta.
Ya sa wa ransa ta zame masa dole, dole kuwa ya yi hakuri da ita ya sawa rana juriya in yana
son farin cikin Ammi. Ya yarda wholeheartedly Ammi ke son Fahimah wato da dukkan zuciyar
ta, da kyar in son da ta ke matan bai rinjayi wanda ta ke masa ba.
Da zamanta shiru ya ishe shi sai ya ce.

“Abincin ma jira ki ke in ce miki ga shi ko? Ashe kuwa za ki kwana da yunwa, look, ki rage
wadannan mayun idanun naki a kaina kada ki sa in kware�.
Uwais ya fada ganin ta je can karshen dakin ta zauna a dofane tana kallon sa, ba tare da ta bi
ta kan abincin ba.
“Malama, ki yi maza ki ci mu je in kama miki daki, kada matata ta jiyo tsamin jikin nan naki ta
waya�.
Wani murmushi Fahimah ta yi, maimakon maganarsa ta bata haushi, he noticed the murmushin,
sai dai bai san ma’anarsa ba. Bakar magana ya gaya mata wadda kowacce mace ka gaya
wa ranta zai sosu. Burin sa har kullum shi ne bacin ranta, muzantar ta da wulakantar ta. To ta
daina bari wani abu nasa ya bata mata rai don ba zamansa ta ke yi ba. Ba ta ci abincin ba har ta yi shirin kwanciya, a ranta tace ka ci kai kadai ka kara zama katoto
dama gaka nan masha Allah. Duk da irin kartawar da cikinta ke yi, ta gwammace ta barwa
Uwais abincin sa tunda har ya ce tana tsami. Ta ji haushi don haushi amma ko a fuska bata
nuna ba. Uwais kuma bai kara ce mata uffan ba, ya harde bisa gado sai faman kiraye-kirayen waya yake
yana zuba turanci kamar bakon Ba’ireshe. Fahimah ta dauki filo daya ta jefa kan sofa ta rufe
kafafunta da katon hijabinta ta yi kwanciyar ta.
Waya ta karshe da ya amsa ta fahimci da matarsa ne, kuma maganar da yake yi ba cikin dadin
rai yake yin ta ba. With a bitter tune take fita fiercely. Duk da haka a tausashe.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: “Whatever Amrahâ€? whatever makes you to disgrace me ta
hanyar tafiya babu izni na. Ga dan iska ko? Wanda bai isa ba, bai isa da matar sa ba don kawai
yana son ta, tunda ni baki dauke ni a bakin komai ba ki je ki ji da boko, ni ma in ji da loneliness
dina. Ba'a sayen soyayyah da na sayowa kaina wata, sai dai duk abin da ya faru nan gaba kada ki yi

kuka da ni. Ki yi da kan ki. Na fada miki na kara, ban iya rayuwa babu mace tare da ni, this is
my hidden nature, ina na akan baka na na ki dawo B.U.K in kina son auren mu ya dore�.
Da sauri ya kashe wayar da ya tuna akwai mutum a dakin, shaf ya manta da ita, shi mutum ne
mai sirri da ba ya son wani ya ji sirrin aurensa ko yaya yake da shi, balle Fahimah.

Gyaran murya ya yi don ya tabbatar ta yi barci ko ba ta yi barci ba? Ta ji sirrinsa da Amrah?
Abin da bai sani ba ta dade da kaiwa birnin Sin a barcinta tun sanda ya fara maganar. Har tashi
ya yi ya wuce ta gaban sofa din ya tabbatar barci ta ke don ga numfashinta na sauka a hankali.
He felt relieved. Ai in ta ji Amrah ta gudu ta barshi sai ta yi dariya ta kyakayata, ta gane son da
yake mata ya fi nata yawa wanda hakan abun kunya ne a gare shi, kuma a zahiri ya dade da
fahimtar hakan. Ba ya so ya yarda ne da gangan, ya fi alakanta hakan da ra’ayin gidansu,
‘yan boko ne na ga ni kashe ni, wadanda za su iya sadaukar da komai don tsira da
profession din su. Soyayya is their last priority.
Shi kuma ba shi ya sanya wa kansa soyayyar Amrah ba, Allah ne ya sanya masa, idan za ta
zama cutuwa a gare shi kamar haka, yana rokon Allah ya rage masa. Ko ya cire masa
bakidaya
Ya yi nafilfili masu yawa a daren yau kafin ya kwanta. Da asubah yana so ya tada Fahimah
sallah yana kwabar kansa shiga sha’aninta. Kulawa ma ai yabawa ce. Ita da kanta ta tashi ta
shiga toilet ta yi changing sannan ta koma ta sake kwanciya.

Sai wajejen bakwai na safe ta tashi ta ga Uwais ya tsuke cikin Spanish suit bakake wul,
wadanda suka maida shi bature zallah, sai tazar kwantacciyar sumarsa yake yi da kumb yana
mulketa da Arganavita. Aka kawo karin kumallo ya karasa ya karbo ya rufe dakin, ya zauna
yana ci yana tunanin ya aka yi jiya ya manta bai je ya kama wa Fahimah daki ba? Zuciyar sa ta
yi gaggawar ba shi amsa da cewa,
“Amanar Ammiâ€?.

What if wani ya je ya cutar da ita a bakon wuri, me zai ce wa Ammin ta?
Don haka ya cire maganar kama mata daki daga ransa sam-sam, zai ta jure hakurin zama da
ita. Da ganin bakar fuskarta. Har Allah ya iyakance masa wannan kaddara, ya dauki aurenta
matsayin jarabta wadda yake fatan Allah ya ba shi ikon cinyewa, ya sa ya gama da
mahaifiyarsa lafiya. Ammin da yake so fiye da yadda yake son kansa. Yadda Uwais ya dauki aurensa da Fahimah matsayin mafi munin jarrabawa a gare shi, ita
Fahima ta dauki aurenta da Uwais ne as a luck by chance, ko Uwais ba zai so ta ba aurensa
rumfa ne, mafaka ne, kuma waraka daga tsohon ciwo, tsohon mikin da ya dade yana wahal da
ita. Don haka ita ko Uwais ba zai so ta ba, she's now contented and satisfied with everything in
life. Ammi ta yi wa zuciyar ta gata, gatan da ba za ta gushe tana mata addu’a ba, tare da
roka mata gamawa da duniya lafiya har karshen rayuwar ta.

Da ya so ta, da kada ya so ta, yanzu duk uwar su daya uban su daya a wurin ta.

A ‘yan kananan shekarunta ta yarda love never fadesâ€? wato soyayya bata taba kodewa
(son da take wa Uwais na har abada ne) sannan sai ta ga dama ta ke yin kanta. In haka ne

kenan ba ta ga laifin Uwais Shagari da ba ya sonta ba, soyayyar ba ta ga damar yin kanta a
kansa ba. Tasa soyayyar a kan Amrah ta ke, wanda ko kusa ba yin kansa ba ne.
Ita kuma ta kasance mai yawan yi wa dan Adam uzuri a rayuwar ta, kamar yadda Annabi SAW
yayi umarni, don haka komai Uwais zai mata uzuri za ta yi masa, uzuri bayan uzuri sau saba'in,
uzuri albarkacin Ammi, da uzuri albarkacin soyayyah.
Ya ci abincinsa, ya kira Ammi a waya, ya ji yadda ta sauka, sannan ya gaya mata su ma sun
sauka lafiya a jihar Lagos. Ammi farin ciki kamar ta yi ya ya! Ta sa wa Uwais albarka a waya ya
fi cikin carbi, yafi sau shurin masaki. Bai taba jin farin ciki a muryar Ammi irin na yau ba.
He was astonished! Har haka ta ke son sa da Fahimar? Shi kuwa me zai hana shi ya daure ya
ci gaba da faranta wa Ammi, in ya so ita Fahimar ta ci gaba da ganin other side din Uwais ita
kadai, uwarsa ta yi ta sanya masa albarka irin haka???
"He who has the blessings of a mother....never loss in life".
Ammi ta cancanci samun kowanne irin farin-ciki daga gare shi, sabida bata da kowa sai shi,
kuma bata da mai rufawa Fahimah asiri bayan shi, kowa zai auri yarinyar ba zai mata rikon da
zai gamsar da Ammi ba, idan aka yi la'akari da asalinta, amma idan shine yasan in reality zai
rike auren ta koda a ladan noma ce, sannan ko gunduwa - gunduwa zai dinga yi da ita a bayan
idon Ammi, a gabanta ya nuna shi mai kyautatawa ne ga Fahimar, albarka zai yi ta sha
kwando-kwando irin wannan a wurin Ammi.
Murmushi ya yi mai sauti, a lokacin da ya gama wannan tunanin, har yanzu Ammina kan layi,
tana ta zuba masa hirar mutanen Sudan, ya ce,
“Ammi ta ki cin abinci tunda muka zo, kuma bata magana, ko za ki yi mata magana kada
wani abu ya faru a ce laifi na?�

Ammi ta ce, “Ba ni Fahimarâ€?.
Fahimah na jinsu, a ranta ta ce, ta inda ya koma ke nan? Hada ta da Ammi? Ina ruwansa da kin
cin abincin ta? Cikin sa ko nata? Ita bata son munafurci. Ta lura abinda ya koya kenan. Tana
karbar wayar ta yi sallama.
“Kin ki cin abinci Fahimah, a wane dalili?â€?
Idanunta suka cicciko da kwallah, ta ya za ta iya cin abinci yana gasa mata bakaken
maganganun sa masu kona ruhin ta, yana hantara da kyarar ta yadda yake so? Shi cin abinci ai
sai da sukunin zuciya ake yinsa, ita kuma zuciyar ta babu sukuni ko kankani. Something deep
down inside her is disturbed, she is emotionally disturbed.
A kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login