Showing 42001 words to 45000 words out of 59199 words
Chapter 15 - FAHIMAH Book 1 Hausa Novels by Takori kabara .pdf
da a yi
'a rashin uwa' da itaâ? gara kowa ya mutu da urges ya huta. Ta dauka zai biyo ta, shi ne dalilin da yasa ta rufe kofar da mukulli ta kuma bar shi a jiki don ma
kada ya dauko safayar na Ammi ya cigaba da damunta, amma har dare ya tsala ba ta kara jin
motsin shi ba.
Sau uku tana lekawa ta taga ta tabbatar yana nan bai fita ko'ina ba, ta hanyar ganin motar sa,
sai ta yi ajiyar zuciya ta koma ta kwanta
Amma kuma barci ya gagara zuwa ga Fahimah a wannan daren, tunanin a wane hali Uwais
yake? Ya hana barcin zuwa ya kuma hana ta zaman lafiya.
A daddafe garin Allh ya waye da ita, barcin da ta yi yau kwata-kwata bai yi na awanni biyu ba.
Da ta tashi duk sammakon ta ba ta ga motarsa ba, tabbacin ya fice ofis ba tare da ya nemi karin
kumallo daga gare ta ba.
Don haka ita ma ta yi shirin shiga makaranta don bada excuse na zuwa Sudan kwana biyu ko
uku ga abikan karatunta don su yi mata attendences, amma duk jikinta a sanyaye yake. Tana
dai karfafa kanta da cewa hukuncin da ta zartar shi ne daidai, kada ta bari soyayya a inda ba ta
da gurbi ta kassara rayuwarta. Ya jira matar SO ta dawo. Su dora daga inda suka tsaya.
*****
Ta yi wanka ta shiga kicin domin nema musu abin da za su ci. Duk da ba ta da tabbas ko zai ci
din? Tunda fushi yake, fushin da ta ke kira na karfin hali wai barawo da sallama. Kai da ba ka
son mace, ka fada ka kara, a idonta da bayan idonta, don me ka ke son auratayya ta kasance a
tsakanin ku? Haka kawai ita ma a barta stranded din idan matar so ta dawo babu gaira babu dalili? A hakan
ma yaya ta kare da sabbin darussan da ya koyar da ita duk da bata san kan dawar garin ba? Ba
ta taba ganin mutum mai son kansa a duniya irin Uwais ba. To ita ma tana son kanta, kuma za
ta yi wa rayuwarta gatan da bata da shi in reality, sai ranar da ya furta mata hakikanin kalmar so
daga zuciya da ruhi, da kuma fatar bakinsa. Ya janye mummunan sunan da yake kiranta da shi
na gorin halitta "Goddam Black".
Yamma lis Uwais ya shigo gidan, a matukar gajiye ya ke ga yunwa da ya dawo da ita, rabon shi
da sanya wani abu a bakin shi tun wani dan hot coffee da ya sha da safe a ofis da bai fi rabin
kofin mug ba, inda akwai abin da Uwais ba ya yi wa fulako ko zuciya to abinci ne, ko dazu da
safe duk da fushin da yake da Fahimah kafin ya fita sai da ya duba ya ga ba ta ajiye komai ba
shi ne ya fita, amma shi zai yi fushi da komai ban da cikinsa, sabida yawan excercise din da
yake yi yana saka shi saurin jin yunwa.
Yana shigowa dining ya nufa. Luckly ta ajiye lafiyayyar sakwara (pounded-yam) da miyan Ugu
wadda ta ji naman rago zuqu-zuqu. A gefe ga jug na lemon carrots da ta hada da fresh abarba,
ta zuba kananun kankara a cikin sa.
"Ko da wannan mijin fahimah ya tsira ya tsira". Uwais ya ce a zuciyarsa, yana mai jan kujerar da
ya saba zama akai a dining din. Ammi ta yi mata kyakkyawan raino mai matukar ban sha'awa,
tarbiyya ingantacciya da kuma tsayuwa a kan raâayi guda. Ya fahimce ta tun jiya, ya fahimci
manufarta as the same time ya kuma yaba da jarumtakar ta.
Amma har gobe yana faman cigaba da lalubawa a fadar zuciyarsa bai ji tsayayyen muhalli ga
Fahimah ba, balle yayi mata karya wadda ba halin sa ba. Amrah ta bi ta cike kowanne gurbi ita
dai barta da son bokonta.
Ta karaso wajen yana cikin cin abincin, sanye da riga da wando na Pakistan ruwan zuma, ta
kame kakkarfan gashin kanta a tsakiyar kanta wanda bai da tsayi sai cika da kuma karfi na
hausawan usli. Ta lulluba mayafin kayan a kanta. Idanunsu suka hadu, duk sai ta ji kunya ta
kamata. Data tuna rashin arzikin data yi masa jiya. Uwais kallonta kawai yake har ta karaso, ya aje cokalin hannunsa. Ta yi wani fresh da ita,
dark-skinned din sai sparkling ta ke yi. Ashe dai a can baya kallon tsoro yake mata, bakin ma,
kyau ne, ga wanda ya yi dacen sa.
âKi dau abinda za ki dauka, gobe za mu wuce wajen Ammi, sai ki je ki ba ta bayani cewa kin
ki yarda auren ya dore yadda ta ke so, kuma ba daga gare ni ba daga gare ki.
Na yi rantsuwa da Ubangiji idan baki sauya ra'ayin ki ba har muka dawo, mata ta uku zan aura
muna dawowa daga Sudanâ?.
Yana fadin haka ya ture plate din gabansa ya mike. Murmushi ya kwace wa Fahimah, beautiful
serene smiles, ko mene ne damuwarta don Uwais ya kara aure? Ai kishi na matar so ne, ita ke
da damuwa. Ita matar shige ina ruwanta? Ammi kuma in ya ga zai iya tarar ta ya fada mata
wannan babbar maganar ai sai ya je ya gaya matan. Kaya kala biyar ta kara dauka, sai na barci da na amfani, wadanda suka dawo da su daga
Lagos ta zuba su a kayan wankin ta, tana shirin kwanciya sai ga Uwais ya shigo.
Ta yi maza ta maida rigar da ta ke niyyar cirewa ta canza da sleepy, ya yi kamar bai ga abin da
ta yin ba, ya zauna daga tebir din jikin madubi.
Pajamas ne a jikinshi farare âyan gidan Marks & Spencer. Bakin gashinsa sai sheki yake cikin
hasken farin kwan lantarkin da ya haskake dakin.
Ya ce, âSorry, Iâm not here for what you are thinking right now. Na zo ne mu fahimci juna
kafin zuwan matata ta uku. Ina son sanin me ye a ranki game da ni Uwais, da har ki ka yarda
aka kulla irin wannan auren tsakanin mu ba ki yi kowanne irin protest ba alhalin ba kya
sonaâ?.
Fahimah ta lumshe idanunta, wai ita yau Uwais ke wa gorin ba ta son sa! Ina ma ana ciro
zuciya a nuna, ta tabbata da Uwais ya yarda duk duniya babu macen da ke sonsa kamarta.
Ba ta tanka masa ba ta dauki kayan da ta ke son canjawa ta yi toilet, ta sanya sannan ta fito
duk Uwais na kallon ta. Ya rasa abin da ke damunsa a wannan dan tsukin a kan Fahimah da
har ya biyo ta dakin ta again duk da wulakancin da ta yi masa jiya, wanda babu 'ya macen da ta
taba yi masa. Alal hakika ji ya yi kawai yana son ganin ta kafin ya kwanta, ya tsokane ta ko
âyar kokawar ce ya lakato su yi, it will keep him company tonight.
âFah- himah, ina magana shi ne ki ka yi banza da ni ko?â?
Ya fada cikin rauni, da muryar da Fahimah ta yi tantamar anya ta Uwais ce? Zama ta yi a bakin
gado tana kallonsa da idanun mamaki dafe da goshin ta, kafin ta yi wani kasalallen murmushi.
âYaya Uwais ban gane tambayar taka ba ne, protest kamar yaya?â?
âIrin ki dan nuna wa Ammi rashin amincewar ki da auren, tunda kin san ba son ki nake ba,
kema kuma na fahimci ba sona kike ba da baki yimin abinda kika yi jiya ba, amma sai ki ka yi
shiru, aka kwaci sadaki daga mijin wata ta karfi da yaji aka baki, kuma an ce ki yi aikin sadakin
kin kiâ?...â?. Ya fada yana kallonta kai tsaye cikin idanunta da narkakkun kwayan idanunsa. Wani kallo ne
mai nuna tsananin bukatuwar miji zuwa ga matarsa.... wanda Fahimah ba ta san maâanar sa
ba.
9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Daga lokacin da ya taso zuwa lokacin da ya iso gare ta, Fahimah
ba ta farga ba. Ta dai tsinci kanta ne a tsaye nannade cikin hannayen Uwais. And he began to
kiss her, first softly, sannan gently, kafin ya maida shi a urunce (abruptly), kafin kuma ya dakata
yana kallonta kasa-kasa. âKarya ki ke Fah-himah, kina sona, kina son Yayanki Uwais ba tun yau ba, bakin ki bai fada
ba amma zuciya da gangar jikin sun gama confessing, na tabbata son ne kuma ya sa ki ka
amince da aurena babu protest.
A bisa hakan ,nake rokon ki da ki yi hakuri da ni, mu yi amfani da son da ke dankare cikin
zuciyar ki mu gina kyakkyawar muâamala ta aure. Ki manta da cewa wai bana miki so irin na
soyayyah. Babu abin da lokaci ba ya canzawa Fah-himah. Ki bar ni in tabbatar da sunnar da ke
tsakanin mu, na yi miki alkawarin ba za ki yi da na sanin ba ni rayuwar ki ba. Ban yi miki alkawarin SO ba, amma na yi miki alkawarin ADALCIâ?.
Wani haushi ya zo ya tokare Fahimah a kahon zucci, duk da kasalar Uwais da maganganun sa
ya saukar mata, amma bacin ran kalamansa na karshe ya sa ta angije shi. Ta juya masa baya
tana hawaye.
âYaya Uwais ka fita min a daki, pls, tunda ni da bakina ban furta maka kalmar so ba, don
Allah ka daina furtan kiyayya. Babu adalcin da nake bukata daga gare ka duk ka hada ka baiwa
matar so. Ina bukatar sarari wallahi, kasa daki na ya min kadan, kana sa min ciwon zuciyaâ?.
Uwais ya zuba hannayen shi duka biyu cikin aljihu yana kallonta da murmushi a siririyar fatar
bakinsa.
âThen why are you jeolous? Da matar so da wadda za a karo?â?
Da sauri ta juyo, ba ta san ya karaso bayanta ba don haka kanta ya bigi kirjinsa. Ta sake ja da
baya ta ce, âKishi kamar ya ya fa? Ban gane ba? Na ce kar ka yi aure, ko na ce kar ka koma
wajen matar ka?â?
âBut you called her MATAR SOâ? in ba kishi ki ke ba don me za ki kira ta da wannan
sunan?â?
Fahimah ta gama lura tsab yau Ya Uwais neman magana ya ke ji, ya zo ne musamman don ya
yi ta takalar ta, tayi ta hargagi yana murmushin jin dadi, ta fahimci in za su kwana suna yi ba zai
gaji ba. Sai kawai ta yi tattaki da baya-da baya ta shige toilet da sauri ta murza key ta barshi a
wurin. Uwais ya karaso kofar toilet din ya ce, âNi ki ka kulle wa kofa Fah-himah? Ai ba sai kin kulle ba na gaya miki tun shigowa ta Iâm
not here for what you are thinking. Na zo ne mu fahimci juna, kuma alhmdulillah na gama
fahimtar duk abin da nake son fahimta a kan ki.
Ya rage naki ki baiwa zuciyar ki salama da abin da ta ke so, ko ki yi ta zaman jiran tsammanin
warabbuka (sai ranar da aka so ki kamar matar so). Ci ba daya ba kuwa, ai koshi bai taba zama
dayaâ?.
Fahimah ba ta tanka sa ba, ta san ta shaka masa. A yadda ta ganshin nan da bata tsere ba
abinda zai biyo baya Allah kadai ya sani. Ta ganshi ya koma kamar ranar su ta farko a Lagos.
Rabar da period ne kadai ya ceceta. Tsoronta daya ne kada ya fita neman matan kan titin
kamar yadda yake ikirari, don haka ta yi ta leke ta tagar bandakin ta tabbatar motarsa tana nan
bai fita ba. Ta yi ajiyar zuciya ta fito ta rufe dakin ta ciki, sannan ta yi alwallah ta kwanta.
Ta kasa barci, sai tunanin maganganun Uwais dalla-dalla. A zahiri ta gane cewa; their
relationship is taking another direction. Ta tuno yadda Uwais yake kissing nata a Ikko da dazu
babu kyama, a hakan ma don tana zamewa ta ki sakar masa jiki. It was all sudden changes a
tare da shi wadanda bata taba tsammanin za su faru da shi ba cikin dan kankanin lokaci irin
haka. Sai dai ta lura shi a karan kansa bai san da wadannan tarin sauyukan a tare da shi ba.
Da ma an ce mahakurci mawadaci, kuma mai hakuri shi ya kan dafa dutse har ya sha romon
sa. Idan tafiyar su ta ci gaba a haka, ba ta san iya ina za ta kai su ba, amma dai ko ina ne
destination din zai zamanto mai maâana ne.
Me ya kamata ta yi maimakon kwanciya? Ai kawai ta tashi ta gode wa Sarki Allah. Jallah Wa
Azza. Wanda cikin mulkinSa da buwayarSa ne yake ta karkato mata da zuciyar Uwais, batare
da shi din ya san hakan ce ke faruwa da shi ba. All of a sudden, da ma dai Ammi ta fada,
âUwais bai iya rayuwa ba tare da mace ba", kuma ga zahiri tana ta gani.
****
Uwais da Fahimah, washegari a cikin jirgin SUDAN AIRWAYS, wannan karon bai kai ta
economy class ba, ya barta a first class seats kusa da shi duk da cewa ya ki sakar mata fuska
sabida abinda ta kara yi masa daren jiya. Tun da suka taho yake kumburi, ga wani bakin dark
spaces ya maka wa kwayar idonsa, wanda ya boye halin da kwayar idanunsa ke ciki. Ko abincin da aka ba su a jirgi bai taba ba, duk a cikin fushi ne, fushi yake sadidan da Fahimah,
ita kuwa ko a jikinta. Ta ci abincinta ta yi nak! Aka zo aka kwashe kayan, ta soma jin barci, sai ta
jingina da kujerar sa barci ya dauke ta.
Ba ta san ya ya aka yi ba, ta farka ne ta ganta kan kafadun Uwais tana barci. Ko ita ta sulmiyo
zuwa jikinsa, ko shi ya gyara mata kwanciyar ba ta sani ba. Da asubahi suka sauka a Khartoum
babban birnin kasar Sudan kuma garin su Ammi, Mahdi babban dan Baffa Shuraim shi ya zo ya
tafi da su zuwa can main house din su Ammi, inda a can ne ake zaman makoki.
Ammi baki ya ki rufo, da ganin yadda Fahimah ta yi mulmul cikin 'yan kwanaki kalilan. Wannan
ya tabbatar mata suna cikin kwanciyar hankali fiye da tunaninta. Duk da an yi adduâar bakwai
an watse dangin Ammi na nan ba su koma ba, nan ta yi ta gabatar da Fahimah matsayin âyar
ta da ta rike tun tana karama kuma matar Uwais. Wasu sun yaba, masu racism din ciki ba su
yaba ba, kin san balarabe da kabilanci. Matar Mahdi sai da ta yi gulmar Ammi a bayan idonta ta
ce da mijinta Mahdi cikin harshen larabci,
âDuk matan Sudan Ammi Safeeyyah ta rasa wadda za ta aura wa Uwais sai mara asali mara
hasken fata?â?
Mahdi ya harareta yace "to ina ruwan ki? Ita ta ga tayi dai-dai da danta, ko ke kika haifa mata
shi?"
Da yawa kuma tarin nutsuwar Fahimah da rashin rawar kanta, uwa uba kwarjinin da Ubangiji ya
yi mata shi ya burge su zuciyar su ta kaunace ta.
Da daddare Uwais ya shigo yi wa Ammi sallama zai tafi masaukin shi ya kwanta, Mahdi na
jiransa a waje cikin motarsa zai sauke shi. Sannan ya wuce nasa gidan. Fahimah na gefen
Ammi tana cin abincin dare sanda Uwais ya shigo. Kallo daya ta yi masa ta dauke kai, shi ma
ya yi kamar bai ganta ba, amma gani ta yi har duhu ya dan yi sabida gajiyar da ke tare da shi. âAmmi fi-amanallah zan je na kwantaâ?.
Ammi ta ce, âAllah ya huta gajiya, a ina ku ka sauke shi Mahdi?â?
Mahdi ya ce, âNan gidan saukar bakin Abbu na gyara masa daki, amma shi ya ce ya fi son
Fundaq (hotel)â?.
Ammi ta dubi Fahimah da ta kasa ci gaba da cin abincin ta ce, âSai ki tashi ku tafi, ni ba zan
kwana gado daya da ke ba, hauri ki ke yi da wadannan dogayen kafafun naki in kina barciâ?.
Fahimah ta zaro ido tana kallon Ammi. Uwais bai ce komai ba ya juya ya fita, yanzu sai ta
tsallake kowa da ke cikin gidan nan ta bi Uwais zuwa masauki? Ta bude baki za ta yi magana,
Ammi ta jefa mata mayafin ta ce,
âDo as I saidâ?.
Tana kunkuni hadi da turo baki gaba ta mike, âDuk mutanen gidan nan Ammi?â?
Ammi ta ce, âSu ba a dakin mazan su suke ba? Bari mu koma gida da ni ki ke zancen,
wallahi tarewa za ki yi ko kuma ya dawo da matarsa, ba zan dauki rainin hankali ba, ku zo ku sa
ni a tsakiya ina dalili ni ba tsohuwar banza ba?â?
Tuni Fahimah ta kai kofa, ga uban horn da Uwais ke antayo mata don ya tsani jira a rayuwarsa.
Suna kan hanya shi da Mahdi da ke tukin mota suna gaba, ita kadai tana gidan baya. Uwais ya
yi kwafa sannan ya yi magana da hausar da ya san Mahdi bai ji.
âDa ma kin dage kin ki biyo ni, aâa ke komai sai ki yi shiru ke ga sarkin biyayya wa Ammi,
in kin biyo ni amfanin me kike amfana min? To ni zama da ni DEAL ne kin sani, gara ma ki rufa
wa kanki asiri ki bi Mahdi ku komaâ?.
Fahimah ba ta tanka shi ba. Daidai lokacin da Mahdi ya shigar da mota hotel din, shi ya je ya yi
musu komai, sannan suka haura dakinsu ta elavator.
Suna shiga dakin wanka ta shiga ta fara yi sabida tunda suka iso ba ta yi ba, jikinta har
danko-danko yake mata, sanda ta fito Uwais na kishingide cikin kujera ya