Showing 1 words to 3000 words out of 40972 words

Chapter 1 - ZUMA DA MADACI Romantic Hausa Novels by Maman Teddy .pdf

*✨ZUMA DA MAD'ACI✨*

Na
*Maman teddy*


*ALHERI WRITERS ASSO.*

*A.W.A*


https://www.facebook.com/100186388252056/posts/100188104918551/

```Kungiya masu aiki da nazaru da ilimi,Alheri sai dan Alheri```

_________________________

*Episode 1&2*


~Happy sallah to muslim Al'ummah,Allah kabamu falalar watan ramadan Ameen summa
Ameen....~



*ABIN ALFAHARI NA*
Gare ku iyaye na,Abin Alfahari na,ina matuk'ar godiya abisa tarbiyan da ku ka bani,Allah yak'ara
nisan kwana Ameeen ya Rabil Alameen.

Wannan littafin sadaukar wane ga duk wani mai kaunar labrn Mmn teddy, wannan yar
k'aramar kuma Babban su,wanda ta saba nishad'antar daku da dadad'an littafan ta,mai sanya
ku nishad'i da faranta ranku don nasan tabbas baxaku manta da littafin ta mai suna. *YAR AIKI*
ba, Ga kuma uwa uba *DIJAMA Y'AR FULANI* Hmmm ummmm ga kuma *BINTOTO* Hmm
wannan shiru xanyi don nasan bakwa buk'atar sharhi dan gane ga wannan book d'in... To a yau
ita ta taho maku da sabuwa mai dauke hankali da kuma sanyaya xukatan ku, wato *ZUMA DA
MAD'ACI* Dajin sunan kunsan da badak'ala, labrn da ya xo maku da sabon salon,don
Alkalamin ba irin tasu bace, ku dai keep following. Don tabbas xuma da Madaci shidin ko a
littafan wannan marubuciya na daban ne❤️.

wannan book kaman yanda kuka sani ta kudi ce labarin,Zaki turo #200 VIP, #300 SPC,#100
NORMAL. Duk ta k'ark'ashin wannan number 08081202932/ 09137392680.

*__________________________*

مسب* الله رلا نمح رلا *مىخ



⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️

Tafe nake ina mai yin wani irin sauri kaman zana tashi sama,ta kalmin k'afa ta ko wato slipers
tuni suka sid'e kasan ya cinye,amma saboda tsantsan rashi da talauci ya hanani siyan wasu.
babu muryan wanda t
nakeji yana mani amo a kunnen na irin na Oum Rabi. K'wallah ne ya fara xubo wa a kan fuska
ta,ina mai tunanin abun da xan tadda a cikin gidan namu. bana ko iyah kallon gaba na,buri na
shine na ganni a k'ofar gida kawai.
Ga kuma tunanin Hajiya Zaituna da ya dame ni,don nasan yau tabbas zan fuskan ci hukunci a
bangaran aiki na dana saba yi mata a cikin gidan ta.
Da wannan tunanin na riski gida, bin gidan namu nayi da kallo, a raina ina cewa" Allah sarki
marayun Allah kenan,ko mu duniya ya xata kasance damu. tsayawa nayi ina mai kare ma gidan
kallo,kaman wannan shine ganina na farko da shi. Wasu bulo suna mai gab da watsowa garun
ya rushe,ga shi ko ina na garun ginin k'asa ne. bin kofar gidan namu nayi da kallo,abun ma
anan tafi lalacewa don k'ofan falangyene,shima ya rabu da jikin shi,amma har ilah yau Ankasa
gyara shi. girgixa kai nayi kurum ina mai sharan gwallah,sannan na kutsa kai ixuwa cikin tsakar
gidan namu. Komai tsaf kaman ba mune muke cikin tsantsan ta lauci ba. Saurin shigewa Daki
na nayi,ina mai godiya ga Allah da yasa Ban had'u da Zaid ba. da6e k'afata take a tur6ayan
dakin da nake kwana,don ko arxikin Siminti babu,can gyefen yar filangyen Katifa ta na nufa hadi
da dauko wani buhun gana must go,da yan kayana ke ciki wanda gaba dayan su basu kai Guda
5. duka kodaddun a tomfofi ne,sai kuma rober atampha guda biyu shima,wanda sam bana son
saka shi saboda kama mani jiki da yakeyi. D'auko wasu fararan kaya nayi masu kama da
uniform ina mai saka shi jikina,sai kuma arsh din hijabin da baifi iya kugu na ba,nasaka ina mai
xura safa kaman wanda xan tafi makaranta. wani farin ta kalmi na saka,gaba daya na fito
kaman yanda Hajiya Zaituna ke bukatan ganin ko wani ma'aikaci na cikin gidan ta.
Kaman daga sama naji muryan Zaid yana bala'in da yasaba yi a kaina.
Oummah wai Suhaimah ta shigo kuwa,ko ko tana can yawon banxan nata. kallon sama da
k'asa Oummah Rabi tayi masa sannan ta ta6a baki tana cewa ina xan sani,nima dan uban ta
jiran ta nake tayimun sukola. ta fadi tana mai cigaba da watso da kayan dattin ta. cike da rawar
jiki nayi saurin fitowa daga d'akin jikina banda rawa babu abun da yake yi. Murya na rawa nace
Oummah Barka da gida".
Cike da masifah ta dago kai tana cewa" au dama kin dawo?. ehhh nace da itah a takaice inah
mai nufan ta da karban kayan dattin hannun ta,ina fadin Oummah bara nayi sauri na wanke
kayan!!!. Shiru Oummah tayi don so da yawa idan tafara mata fitina,yanayin sanyin suhaimat
sai yasa tayi shiru ta tsaya tana mai tunanin Rayuwar ta itah da d'iyar nata Suhaimart. Shiru tayi
kawai sai Muryan Zaid mukaji yana cewa" Kehhh Suhaimart Ina kudin da nace kije ki nemomun
iyeh? ya fadi cike da masifah da kuma muryan Yan Allah ka shirya. Oummah na ne ta kalle shi
cike da masifah tafara cewa" Fita idona na rufe Zaid, Suhaimart ne xata nemo maka kud'in da

xaka sha abun shaye²? ke dama bana ce kar ki fita kije ko inah neman masa kudi ba,koda ko
kasheki zaiyi da duka?. Jikin a ne yahau ky'erma a sanyaye cike da sanyin murya ta nace"
Oummah don Allah kiyi Hak'uri.
Tsaki Zaid yajah hadi da ficewa yana mai banbami bata nemo masa kudi ba. Itako Oummah sai
da ta gama tsitsayamun tsiya sannan ta bar tsakar gidan hadi da nufan soron ta.
Bayan shigewanta ne na tsaya ina rarraba ido,nan take komai tun daga farko ya fara dawo mun
I LOVE YOU SUHAIMART".I LUV U TOO HUDAY,. gigif nayi ina cigaba da aikin da Oummah ta
bani inayi ina tunanin shikenan Huday ya mutu baxai dawo gare ni ba. hawaye ne yafara bin
kuncinta. a haka na kammala wanki na,sannan ko d'aki na ban koma ba,nayi saurin nufan gidan
Hajiya Zaituna.
Tun daga nesa nake bin Tanfatsetsen gidan da gabaki d'ayan sa kewaye yake da Sojoji
kasancewar mai gidan Soja ne Babba,wato Gen. Yak'ub d'an larabawa... cike da sauri na kutsa
kaina ixuwa wajen gate din, Da isana nan Sojojin da securities kowa ya Hau kiran suna na
Suhaimart" Suhaimart..." cike da smilling face dina wanda yasa dimple dina suke k'ara shigewa
ciki sosai,wasu ina bin su da murmushi wasu kuma ina gaisar dasu da ce masu Barkan su da
Rana". Kafin su bani amsa nayi saurin shigewa cikin dank'areren gidan hadi da nufan side din
Doc. Zaituna da yan aiki irina suke acan suna mata hidima,don dama mu anan barayin ta muke
mata aiki. Dai² wani coridour ne a palourn ta daya gaji da kayan alatu da more Rayuwa,komai
ka gan shi a falon kud'ine d ya amsa kudi, komai na falon na zamani da tsantsan wayewa komai
a falon Jah ne da milk. sai tum² da aka jera su a tsakiyan falon yyn dana Hango Doc. Zaituna
zaune ta wani kishingid'a tana aikin isan k'adagin da tasaba,domun Doc. Zaituna irin matan nan
ne masu isah da izzah,gata da iya gadara da arxik'i don a ganun ta a kullum talaka bawan
tane,domun kudi xai mata komai a rayuwa,a ganin ta har mutum xata iyah siya.
Koda na shigo falon a sanyaye cikin takona na a hankali na tako inda Maikatan irina suke a
tsaye,ko wanne sanye cikin shigarta na masu aikin wato farar wando,riga da hijaab Arsh colour
iya kafad'a. yanda kasan mutum bai shigo ba haka Doc. Zaituna ta nuna don daukan ruwar
roban gaban ta tayi tana kora ma makoshin ta. sukuwa sauran ma'aikatan kowa duk'ar da
kansa kasa yayi yana mai tausaya mun,don ansan fitinan da xan sha a yau mai yawa ne,don
karamun laifi kayi xata ce tayi maka dedoction din salaryn naka. Oumu Sulaym ne tahau washe
mun Baki tana mai cewa a hankali Besty Suhaimart dina xonan. tana nuna mun inda take
tsaye....
A hankali na matsa inda oummu sulaym take,ina mai gaisar da Hajiya Zaituna tunda sunan
doctor ce mu kirar ta muke da Hajiya Zaituna, Ya tsina baki tayi kan daga bisani ta cigaba da
bayanin ta batare da ta amsa gaisuwan nawa ba,don ita haka halaiyar ta ga talaka yake,samm
bata son talaka,bb mahalukin da tafi tsana a rayuwar ta irin talaka,don ko fadin sunan talaka ba
tayi,sai dai tace gayyar fitina". Wannan kenan,ban wani damu ba,nasaki mata murmushi don
dama wannan dabi'a tace, Muryan ta naji tana cewa" Okay don haka tun daga yau a fara shirin
tarban d'ana. banason kuringa mun shirme don xan sallami mutum kuje can gidan iyayen ku
kucigaba da cin k'asa,ta fad'i tana tabe baki,sai da ta bata mana kusan 15 muna a tsaye sannan
tace mana,ku wuce ku bani wuri. Mhiss Caterine ne ta hau ce mana kowa ta koma bakin aikin
ta. sum³ duka muka fara nufan bakin aikin mu,wanda Mhiss caterine ta kasance itace shugaban
mu wato yan aikin Haj. Zaituna don aikin mu shine shara goge² cleaning dakuma Cooking.
Nufan side din mu maikata mukayi nida Oummu Sulaym don ana cewa mu wuce taja hannu na

tana nufan wani side da aka bamu mai kama da Resting room. Tun a hanya tafara kallo na tana
mai cewa" ohh ni Sulaym wannan duniya ina xata kai mu ne Besty!?, Ace talaka ya koma yanda
kasan bawa daga aiki,ae wlh wannan Abun da ake mana ko bayin gidan sarki baxa'a masu
haka ba, sai kuma ta dora hannu a fuska tana mai rafka ta gumi,wanda nidai ban da murmushi
babu abun da nakeyi mata. A haka muka shiga side din mu dai² na zauna ne tayi saurin cewa"
Besty wlh har nafara tunanin zuwa mune mi aiki a cikin gidan sarkin Zaria,sarki mai Adalci
kenan,mai mayar da bawa tamkar d'an gida. Jin yanda Sulaym ke xubo xance kaman wanda
tasan sarkin yasani washewa da dariyan da ban shirya ba,don so dayawa ko banjin dry,
Shiyasa kuma a kullum nake kara jin k'aunar Sulaym a xuciya ta. Kallona Sulaym ta tsaya tayi
galala da baki tana yi tana mai bin dimple da Hushirya ta da duk suka bayyana da kallo.
Lumshe segxy eyes din ta tayi tana mai cewa" washh mashaallah gsky besty na Allah yy maki
kyau matuk'a. Riko hannun ta nayi ina cewa" Hmm kedai Sam Sulaym bakya gajiya da surutu
kaman gidan radio. Dariya tayi don Sulaym irin yaran nan ne washa,komai abun Dariya koda
kuwa bata ranta kayi sai dai tayi murmushi. shiyasa halin nasu yaxo d'aya da Suhaimart, ita dai
kawai bata da Hayaniya ne,itako Sulaym ta iya shi.
Dafata nayi ina cewa" Sulaym don Allah ki taso muje mufara aikin mu kinga Hjy. Zaituna yanxun
ta gama fad'a fah.
Ban rufe Baki ba ne Oummu Sulaym tace" Hmm ai wlh munga banu,don bamu fara rayuwar ta
kura ba,yanxun ne xamu fara. Kallon ta nayi ina mai cewa" habawa Oummu Sulaym kowa na
son sassauci ke kuma kirar mana bala'i kekeyi?. tabe baki Sulaym tayi hadi da fara mun mgn
cike da muryan rada saboda gulma,nan ta fara cewa " ke Suhaimart kenafi tausaya mawa.
komai kina yin shi too lazy,a kasalance gashi wannan D'an nata baya da mutunci ko kad'an wlh
sai mun gunmace xama da Uwar sa abisa shi. ga miskilanci issah da wulakanci...Uhnm tom
Sulaym ai sai muyi kokari mu kiyaye duk wani abu da xai sa muja mawa kanmu matsala. Wai
dama tana da yara?. nayi maganar ina mai d'an ya tsina baki na. Oummu Sulaym ne ta bani
amsa da,tab kedama baki sani ba,ba yara ne dayawa take dasu ba,guda d'aya Allah ya bata
shiyasa suke kaunar dan kaman su lashe,kuma wama yace maki yaro ne? tom Saurayi ne
wanda akallah xai kai shekaru talatin xuwa da biyu a duniya. ke samarin nan irin butters masuji
da Gayu da tashen kudi,hmmm Kedai Suhaimart bari,ni ne nake fada maki shi din ajin karashe
ne,wlh Ajin Sir Khaleed yana burgeni. Amma abu daya kebani haushi da shi shine son mata duk
da matan ba irin su mu bane,Yara yayan masu dashi su xaki ga sunyo parcking a haraban
gidannan kullum indai ya dawo, kowa so take tayi mu'amalan banxa dashi,shikuma dan iska
sam baya gajiya,ni ban taba ganin Harijin fitinannan mutum Kaman Sir Khaleed ba. Shiru Nayi
na wucen gadi,tom irin gidan danaxo aiki kenan. Muryan Sulaym ya dawo dani daga duniyar
tunanin da nakeyi. Cigaba tayi da cewa " Kuma kinsan abin Haushun ma? ta fadi tana kallo na.
Girgixa mata kai nayi alamar A'a. wai Hajiya Zaituna cewa ma take yara mata sune sukw bibiyar
mata d'a,su suke neman lalata shi. Haka xatayi ta bala'i tasa ayi ma yara koran kare,don wata
xubin intana gida har sawa take a sakar masu kare,cin mutuncin duniya amma bashi xai hanasu
gobe su dawo ba,kaman kar nuka mtswww.... Sulaym taja tsaki hadi da kama hannu na muka
fara dosan side din wanda naji an kira da Sir Khaleed. Xufah ce ta hau karyomun shikenan na
shiga uku na. Ban san lokacin da nace mawa Oummu Sulaym Yanxu mune xamu ringa kula
dashi har yakoma ko!?. waya fada maki xaya koma? ai yadawo kenan. tunda ya kammala digiri
din shi na biyu ne,a fannin ingineering,sai kuma na farko yy a bangaren Architecture. shiyasa

ma aka fi sanin sa da Arch. Khaleed. mune da sauran Ma'aikatan sa na can companyn sa suke
kirar shi da Sir Khaleed, amma da Architect Khaleed aka fi sanin shi. ai kawai gdyn da xamuyi
ma Allah shine daya,da safe yake tafy Companyn sa baya dawo wa sai After 6pm. sannan
kinga kafinnan tuni mun gudu gida masu yin night duty sun amshe mu. A sanyaye nace kuma wai anan gidan yake shek'e ayan sa ko? wlh sai naji bana son ganin shi
sam. na fadi ina mai bin Sulaym da kallo ina tabe dan mitsulun baki na.
Dariya Sulaym tayi sannan ta cigaba da cemun" tom bakiga tafiyan da muke xukawa bane,ae
side din shi dana iyayen shi dan karan nisa ne dashi,ga shi har da gate din da xai fita tacan
batare da wani ya sani ba,shiyasa tanan karuwan sa da yan matan sa ke shigowa har su gama
Hajiya Zaituna batasan ma anyi ba. sai mu da mike hidimta masa. Tun daga nan ban kuma cewa komai,gabana ban da fadi babu abun da yakeyi. Addu'a nake
tayi har muka shiga side din nashi,da komai nashi yafi na sasan Hajiya Zaituna kaman sama da
kasa,don da shigan mu duka muka rufe ido muna mai shakan wani irin daddadan kamshi,sunan
Baya nan ne amma komai na side din tsaff da shi,abun gunun ban sha'awa sai dai kura da side
din yy kadan,tun a yanayin tsarin wajen xaka fahimci lallae mazaunin Side din gogagge
ne,kuma cikakken Bature ne,don sam bai xauna cikin su a banxa ba.
Daura kyallen da muke dorawa kan Uniform namu duka mukayi sannan muka fara aikin
mu,sosao a lokaci kadan mukaci karfin aikin,Muryan Mhiss Caterine muka jiyo daga bayan mu
tana fadin Suhaimart,Sulaym ku kara cleaning din can coridon okay?. tom muka ce mata muka
juya xamu nufah coridon da tayi mana nuni. sai tsintayar muryan ta mukayi tana cewa"
Suhaimart".Saurin juyowa nayi ina mai amsa kurar nata. Cike da daure fuska da nuna bacin rai
tafara cemun sau nawa nake maki magana kan ki rage wannan xurmemen hijab din. ladern
Hannun ta bude hadi da fiddo da hijab Half sunnah arsh,tana miko mun da cewa" kar nakara
ganin ki da wannan,idan ba haka ba kuma xan sallameki a bakin aikin ki. barina har rawa yake
haka jikina nayi saurin saka Hannu na amsa ina cure na jikina na saka wannan, hadi da mata
godiya,duk da bana son hijab dun sam... Juyawa tayi hadi da barin side din.yyn da Sulaym taso
yin mun wata maganar shirmenta kawai sai na kauda mata da kai don idan ta itane xamu kai
dare a haka.
Haka muka cigaba da aikin mu wanda kan lokaci kadan muka kammala sannan muka bar
sauran ma'aikatan don su cigaba da nasu aikin... A wannan rana a kakkauce na kammala
nawa aikin yayin da wuraren magrib muka baro gidan Hajiya Zaituna. Sam oummu Sulaym bata
barni naje gida ba sai da muka wuce karamar kasuwar cikin garin Zaria, ba wani nisa ne da
gidan Hajiya Zaituna ba. itah Hajiya Zaituna a GRA Zaria take,yyn da Daga nan ne muka wuce
kasuwar monday. Sai da muka isa ne na kwasa takaici don ashe gaba da kudin Oummu Sulaym
Naira 150 ne. kallon ta nayi gami da ce mata" wai Sulaym mai xamu siya a kasuwar nan ne. ko
so kike amana wulakanci abimu da kallon banza. Murmushi Oummu Sulaym tayi kana tace"
waya fada maki aiko da dari biyu da Hamsin din nan sai kinga kayan da xamu siyo. kedai muje
daga ciki kiga irin kasuwannan,ae komai nasu arhana ne dashi,nidai ban kuma ce mata komai
ba,na cigaba da bin bayan ta kaman yanda tace. a wani wuri naganmu cikin irin maguxawan
nan wato katafawa. tsumma naga sun xuba a gaban su suna 20 ². ko yar shugaban kasa
albarka. bin mutumin da yake wannan maganan nayi da kallo,nan naga wata irin
mutsitstsikakken riga wanda shida tsumma babu maraba,amma ya daga yana Ko yar shugaban
k'asa albarka har da karin yanxun akayi odan su daga London. dariya lamarin ya bani,wanda

sai nayi murmushi hadi da cigaba da bin Bayan Oummu Sulaym.
Dai² masu sai da safuna muka tsaya, daga kai tayi tana kallona sai tace inyamuran ta bata safa
fari mai kyau. Bayan ta bata ne tafada mana kudin nan ta mika mata 50 sannan muka kamo
hanyan dawo wa gida. A napep ne Oummu Sulaym tamiko mun Safan tana furta Besty naki ne
fah,naga na kafan ki talalace ne,kuma ba'akusa bamu albashi ba,kar Hajiya Zaituna ta gani
yaxa ma mana na sababi. Bude baki nayi ina fadin besty na bakya gajiya tom ngd. Haba meye
na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login