Showing 15001 words to 18000 words out of 39902 words
yarnan Allah ya tsari gatarina
da saran shuka nikam Saratu ban haifi karuwa yar oya ogaba sakarya kawai asararriya wacce
ta rako Mata duniya wannan uwar data haifeki ma tayi asara......"
"Mommyyyy!" Ya Kira sunanta da qarfi tare da kallon Habeey da take durqushe jikinta na tsuma,
tabbas badon darajar Taheer da Kuma shekarun Mom ba dasai ta yagata saboda aduniya ta
yarda da kowacce wahala da cin mutunci amma banda taba mata martabar iyaye, musamman
Addanta. Miqewa tayi tana girgiza kanta tana hada kayanta a Jakarta tana kuka, itakuma Mom bata daina
zaginta ba tana kwashe Mata yar ragowar albarka data rage Mata a jikinta.
Doguwar rigarta ta dauka tasa ta dauki jakar hannunta ta raba zata wucce ya cafkota ya hadata
da jikinsa yace.
“Mom kada ki soma yin wannan gangancin babu inda Habeey zataje in kuwa kin matsa to nima
zan barmiki gdan sai ku zauna a ciki ni na kama hotel nida matat...." Sake buge bakinsa tayi
tace “idan ka qara cewa wannan munafukar yarinyar matarka wlh sainayi maka baki ka lalace
Koda yake dama ai ka lalace din tunda har ka fasa gardin mace ajiyeta ma kake a gdanka, to
bari kaji ma Taheer yau qafata qafarka in kaga nabar qasar nan to tare muka tafi dakai tunda
abin naka iskanci ne aure ma zanyi maka dan ubanka"
Fincikewa Habeey tayi daga jikinsa ta dauki hanyar fita da gudu shima yabita yana kiranta itama
Hajiya binsa tayi ta riqo rigarsa yasan halin Habeey sarai zuciyace da ita kamar masifa bata
daukar wulaqanci in ba nasa ba shiyasa hankalinsa ya tashi.
Baisan sanda ya durqushe ya cafki qafarta ba yace “Don girman Allah ki tsaya Habeey kada ki
tafi a wannan daren bakisan inda zaki ba..." Cikin kuka ta warce qafarta tace “Indai kanasona
kuma kanaso nima nasoka to kayiwa mahaifanka biyayya don Allah Taheer dama nice kai...."
Tana fadin haka kukan da ta hadiye ya qwace mata tace “kai dan gatane mahaifiyarka tanada
iko akanka ba kamar tawa ba" Kama hannunsa tayi tace “don Allah kada ka bata kunya kaji ta
isa dakai ne shiyasa take qoqarin saitaka a hanya, Taheer kada ka damu dani ka damu da
kanka kawai ni tawa qaddarar kenan" Miqewa tayi ta fice da gudu daga gdan shima ya fincike daga ruqon da Mom tayi masa yabita
amma harta tsare mota ta hau.
Bin gurin yayi da kallo tare da zamewa ya zauna a qasa ya buga hannunsa akansa ya kalli
Mom da ta qaraso yace “shikenan ranki yayi fari kin koreta Mom batada kowa fah a garin nan
buri nake na aureta Mom kema fah kin haifa kuma wlh Habeey batada matsala har tafi yayanki
tarbiyya kawai qaddararmu ce hakan..." Tsaki Mom tayi tace “ai nima tafini tarbiyya shiyasa ta baro iyayenta ta taho take karuwanci a
qasar daba tataba shashasha soko bandama tsabar iskanci ubanme zakaci a jikin wannan
yarinyar mazan titi sun gama debe albarkar jikinta, zaka tashi mu shiga ciki kosai naci
qaniyarka"
Miqewa yayi suka koma ciki ya zube a kujera Mom nata sababinta shikam baimasan tanayi ba
wayar Habeey kawai yake Kira amma taqi dagawa takaici yasashi jifa da wayar yace “yanzu ya
kikeso nayi kin bata Mata rai nima kinjamin ko wayats taqi dagawa don Allah kibarni naje
naganta" Ko kallon tsiya bai samu ba balle na arziqi saima miqewa da tayi ta zare key din parlourn ta
shige wani dakin a cikin dakunan tayi wanka ta dawo ta tayar da sallah, Bushirah ce ta dubesa
tace “amma Ya Taheer meye yasa bazaka auri Habeeba ba kalamanta sun kashemin jiki sai naji
inason sanin wacece ita, don Allah ka bani lbrnta koda wani taimako da zan iyayi Mata wannan
rayuwar bata dace da kyakkyawar mace kamarta ba"
Iska ya furzar ya miqe yace “ni kaina bansan komai game da Habeey ba kawai dai nasan nine
na fara lalata Mata rayuwa amma bazan iya cewa dake ga abinda ya kawota Dubai ba nasan
dai sometimes zanji tana kuka tana cewa Pappa ka cucemu Allah ya saka mana, Amma bansan
waye Pappa ba bansan me yayi Mata ba"
____________Tana fita cikin saa ta samu taxi ta hau har sukace unguwar tasu kuka takeyi ga
wani mahaukacin sanyi da takeji, hakanan dai cikin dauriya ta fito ta shiga cikin gdan Aysher na
ganinta ta miqe da sauri tace.
“Habeey kece a daren nan?" Kada Mata kai kawai tayi ta bude dakinta ta fada saman katifarta
taja bargo ta qudundune jikinta tana kukanta me taba zuciya.
Juyawa Aysher tayi ta fice saboda inda sabo ta saba da kukan Habeey me taba zuciya gashi
bajin rarrashi takeyi ba balle tace zata rarrasheta.
Haka tayita makyarkyata har tasamu bacci ya dauketa, sai asuba ta farka ta samu jikinta ya dan
ware ta shiga tayi wanka tayi sallah ta koma ta kwanta har yanzu qirjinta ciwo yakeyi.
Tananan kwance ta kasa ko tashi taji an bude qofar dakinta an shigo ta bude idonta a hankali ta
saukeshi akansa gabanta na faduwa shikam Taheer wanne irin mutum ne da asubar nan har ya
samu ta fito?
Zama yayi kilusa da ita ya kamo hannunta yace “kinsha maganinki kuwa?" Daga masa kai tayi
ya fitar da huci yace “bazan barki anan ba inada wani gdan Dad dina dake hannuna ki tashi
muje na kaiki can kafin Mom ta tafi"
Kada masa kai tayi ta sake Jan bargo ta rufa ya yaye yace “banaso halinki na gardama Habeey
inayi ne don mutuncinki zama a irin gurin nan bai dace da nutsattsiyar mace ba komai zai iya
faruwa"
Daga masa hannu tayi tace “nikam nace banaso ko dolene" kada Mata kai yayi yace “eh dolene
kibi umarnin mijinki kuwa Habeey Koda bakyaso, ki tashi muje yau zan wucce 9ja idan komai ya
lafa zan dawo gareki Ina fatan faruwar abubuwa da yawa kafin lkcn"
Juyawa tayi tace “Allah ya tsare hanya" daga haka bata qara cewa dashi komai ba har ya gaji
dayi mata mgn ya dagota yace “kinyimin alqawarin duk tsanani duk wahala bazaki juyamin baya
ba, meye yasa tun kan aje ko Ina kikeson ki fara butulcemin Habeey Mom mahaifiyata ce amma
batada ikon canza abinda ya riga ya ginu a zuciyata inasonki a duk yanda kike kuma zan tsaya
tsayin daka wajen kare qimarki a ko inane a duniya"
Itadai batace masa komai ba saida taji yana shafa bayanta a hankali tasan sarai inda zancen
zaije wannan dalilin yasata miqewa ta fada bathroom ta kulle.
Bugun duniya taqi budewa magiyar duniya taqi ta bude har saida yaji Mom ta fara kiransa ya
daga yace “inazuwa Mom" kashe wayar yayi ya dauki biro da takarda yayi wani dan short note
ya ajiye Mata tare da check na kudi masu yawa ya fice.
Saida ya nemi magajiyar gdan yayi Mata ihsani tare da roqonta ta kula masa da Habeey kada
take barinta zuwa ko Ina har zuwa lkcn da zai dawo, sannan ya tafi zuciyarsa babu dadi yana
tuqi yana hawaye tare da jin haushin Mom dinsa yasan itace duk taja masa wannan matsalar da
yake ciki.
*UMMUH HAIRAN CE...✍️*
[7/23, 9:22 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI*✈️
*PAID BOOK*
*HAƘƘIN MALLAKAR*
*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*(UMMUH HAIRAN)*
*_21/7/2020_*
_Kamar yanda duk Wanda yaga status dina na yau ya sani cewa, littafin *DUBAI* ya koma na
kudi da sabon farashi VIP 1k 30 people's kawai nakeso single 300_
_Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin_
_Account number_
_0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_
_GTB_
_Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp_
_09013718241_
_Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number_
_09013718241_
*LAST FREE PAGE*
*Episode 12*
Yana Isa gdan Mom ta rufeshi da fada tana sababin ya saci jiki daka zuwa masallaci ya tafi
gurin karuwa, zubewa yayi a gabanta ya kasa boye abinda yakeji a zuciyarsa, tsoro ya kama
Mom ganin yanda dan nata yake kuka kashirban yana girgiza kai yace.
“Mom wlh idan kikaja na rasa Habeey kema Zaki rasani don na tabbatar mutuwa kawai zanyi
Mom yarinyar nan tafi kowa buqatata a rayuwarta batada kowa a garin nan saini idan kika
matsa na tafi nabarta bansan halinda rayuwata da tata zata kasance ba..."
Wata tsawa data daka masa tasashi hadiye guntuwar mgnrsa tace “ashe kuwa zaka mutu don
wlh nama rantse maka idan kaga ka auri yarinyar nan to ka qaddara babu numfashin Hajiya
Saratu ne kai ko bana raye ka auri yarinyar nan bazan taba yafe mak..."
Rufe mata baki Bushirah tayi tace “don Allah kada ki rantse Mom matar mutum kabarinsa
bakisan abinda Allah yake nufi da hakan ba idan kika cika matsawa komai zai iya faruwa haba
Mom kifa tsaya ki duba na tsanaki cikin lamarin nan tunda kike da Ya Taheer banajin ya taba
cemiki yanason wata mace sai akan Habibatullah..." Angajeta tayi ta fada jikin Taheer daya dafe kansa ysnajin kamar zai tarwatse tace “kajini da yan
iskan yara to kuyimin nasiha tunda kunfini sanin abinda ya dace" fuuuuuu ta shige daki ta dauko
mayafinta da Jakarta tace “kayi sauri yau qafata qafarka kaida Dubai kuwa zaka dade dan
ubanka shashasha shi ko tsoron ciwukan zamanin nan bayayi"
Saida taje bakin qofar ta juyo tagsnshi a zaune inda tabarshi ta juyo a fusace ta daukeshi da
mari sannan ya dawo hayyacinsa ya miqe ya shiga dakinsa ya hado kayansa har ya juya zai fita
ya koma ya bude inda kayanta suke ya zauki rigar baccin data kwana da ita kwananta na
qarshe a gidan ya rungume a jikinsa yana shinshinawa. Saida yaji Mom na qwala masa Kira sannan ya fito a gajiye rungume da rigar a jikinsa ya shiga
motar driven yaja suka nausa airport, da sukazo hanyar unguwar su Habeey har leqowa yakeyi
wai ko zaiganta amma Bai ganta ba, ya furzar da iska tare da gyara zamansa ya dora rigar a
qirjinsa yanajin kamar Habeey ya rungume.
___________Biyar jirginsu ya sauka kasancewar lahadi ce governor waziri dakansa yaje dauko
iyalansa tun daga fitowar Taheer a jirgi yaga yanda yake layi yasan ba qalau ba har ya iso
gareshi ya fada jikinsa ya rungumeshi yace “Dad don Allah kada ka bari Mom ta rabani da
Habibatullah itace rayuwata Dad bantaba son wata ya mace ba sai akanta, kaji Dad don Allah
wlh Itama bason wannan qazamar rayuwar takeyi ba kawai dan babu yanda zatayi ne Dad har
yanzu Habeey tsoron maza takeyi saboda bata sababa..."
Rufe masa baki yayi yace “could down My Son kayi addu'a kawai ita mace allurar ruwa ce me
rabo ke dauka balle irin wadannan matan, Son banayi maka sha'awar auren karuwa nafison ka
auri kamilar mace manzon Allah yace mu zabawa yayayenmu uwa ta gari wacce zasuyi
alfahari da ita"
Share qwallarsa yayi yace “itama ta garice nine na fara batata nine ma bana gari ba saboda son
zuciya da kwadayi yasa na wulaqanta mata rayuwa Dad nifa koma ya take inasonta kawai ka
nemamin aurenta"
Jikin Dad yayi sanyi sosai amma zuciyarsa bata amince da ya nemawa Dan nasa auren
Habeey ba musamman da suka shiga mota Mom tarinqa famfashi tana fada masa qarya da
gaskiya, shima ya hau ya zauna tare da cigaba da lalllashin dannasa.
Ganin bashida alamun cinmma nasara yasashi sharesu yaci gaba ta qulla me yuwuwa a
zuciyarsa, Abu na farko dole ne duk yanda zaiyi yayi ya kasance tare da Habeey Koda aure ko
babu aure saboda barinta gidan magajiya Adama matsalace babba itadin ster of women's ce
duk namijin da ya kalleta sai yaso dandana daga gareta shikuma abinda baya fata kenan yafiso
ya kasance shi kadai ne yake mu'amala da ita.
Da wannan tunanin suka shiga government house din motar tayi parking a wata qatuwar rumfar
aje motoci Taheer ya riga kowa bude motar ya fice a fusace yanaji Dad na kiransa ya daga
masa hannu batare daya juya ba yace “me zakacemin Dad bayan wannan matar" ya nuna Mom
yace “ta zigeka har sharri ma tayiwa Babena saboda kawai batasonta to nidai babu ruwana ko
ku auramin ita ta zama matata ko kada ku auramin ita bazan fasa hutawa da ita ba saboda
babu macen da take certified dina kamarta kunga kenan sai ku shirya daukar jikoki course
bazan qara yi Mata amfani da maganin hana daukar ciki ba gara mu samu zuri'a mum...."
Wani mugun mari Alh Wazir ya dauke dannasa mafi soyuwa a ransa dashi yace “ashe bakada
hankali dan ubanka Taheer, ni zaka kunyata ka tozarta a idon duniya? Ok na gane inda ka dosa
kaje Taheer kaje kayi abinda kaga dama aurene kaida yarinyar nan har abada dan ubanka idan
mune muka haifeka zamu gani idan kuma Kaine ka haifemu nan ma zamu gani sakarai kawai
da baisan ciwon kansa ba"
Marin ya bashi mamaki kuma ya shigeshi tunda yake da iyayensa musamman Dad baitaba
daga hannu ya dakeshi ba sai akan Habeey hakama Mom, “Habeey! Habeey!! Habeey!!!"
Baisan sanda bakinsa ke furta wannan kalmar ba sai jiyayi Mom tace “ba Habeey ba inma
habibu ne saidai zuciyarka ta tarwatse amma bazaka kawo mana baragurbi cikin ahlinmu ba"
Dagowa yayi ya kallesu kawai yayi wani murmushi dashi kadai yasan me yake nufi ya juya da
sauri ya shige part dinsa ya datso qofar da qarfi Mom da Dad suka kalli juna cikin dan firgici
Kubrah ta tabe baki tare da nufar nasu bangaren ita kuwa Bushirah kawai hawaye take zubarwa
as Imaging tana jin da ace itace a halin da Habeey take ciki haka itama iyayenta zasuyi mata
kenan?"
Saurin kada kai tayi tare da nufar bangaren nasu da sauri tana kuka, nan fah Dad yabita da
kallo yace “au ita kuma wannan fah?"
Tabe baki Mom tayi tace “yar abi yarima asha kida ce ita kasan duk abinda wancan shashashan
yakeso itama shi takeso dazu har wani wa'azi takeyimin fa" shidai Dad baice komai ba ya nufi
part dinsa Mom ma ta nufi nata.
___________Cikin satin da Taheer ya tafi Habeey tasha wahala sosai don Saida ta sake
kwanciya a asibiti gashi Pappa ya matsa mata ta turo masa da kudi, hakanan a batada lfyr ta
samu ta tura masa kudin da Taheer ya bata kusan million of nairas tace ya siya mata gida anan
Gombe. Aikuwa rufeta yayi da fada wai me zatayi da wani gda a Gombe har yana cewa shifa baya fatan
ta sake dawowa Gombe tayi zamanta a Dubai kawai tana turo masa kudi yanashan giya yana
caca.
Lkcn da aka sallameta daga asibitin suka koma gidan nan ma ba wani sauqi ta samu ba har
yanzu tanajin ciwon ciki da bayan dake damunta saidai ba kamar na kwanakin baya ba.
Wayarta da ta dade da mutuwa saboda Kira ta dauka ta jorner a charge ta kunna tana duba
Miss calls din sunfi dari biyu, kusan dari da hamsin duk na Taheer ne hakanan tayi murmushi
saboda itama zuciyarta tana azabtuwa da rashinsa zuwa yanzu ta fara sabawa da halinsa duk
da yanada gundura idan kana tare dashi amma yanada shiga rai. Bangaren saqonni ta shiga nan ma duk shine ta sauke ajiyar zuciya tare da rafsa tagumi
maganganun Mom sunayi mata yawo a kwanyarta, tana shirin tashi wani Kiran ya shigo takai
hannunta ta dauka wayar tana dubawa taga shine taja huci tare da kwanciya ta danna pick ta
kara a kunnenta tare dayin sallama cikin siririyar muryarta me sanya masa kasala.
Ajiyar zuciya ya jera tafi guda bakwai sannan yace “inata kiranki baki dagawa hankalina ya tashi
na dauka fushi kikayi dani sai daga baya Aysher take cemin ashe jikinki ne yaqi dadi har takaiki
ga sake kwanciya a asibiti, sannu ya jikin naki?"
Numfashi ta sauke tace “naji sauqi sosai sai ciwon ciki da baya da yaqi barina" da sauri yace
“wht? Amma shine kuka dawo gida?" Iska ta fesar tace “to zamuyita zama a asibiti ne Taheer,
inasa ran shima zai tafi" qwafa yayi yace “ok Allah yasa ya kk ya kewata ko bakiyi?" Shiru tayi
masa, yace “kice wani abu mana hearty koda kince bakyayi bazanji haushinki ba kamar yanda
bazanyi mamaki ba saboda nasani baki sona nine kadai na jarabtu nake azabtuwa da
soyayyarki take neman aikani lahira"
Dariya yabata sosai tayi dariya shima yana tayata yace “tunda nake bantabajin dariyarki haka
ba sai yau saboda kinji qaunarki zata kasheni ko?" Ajiyar zuciya tayi tace “me zakayi da karuwa
mara gata mara mafadi Taheer?"
Wani murmushinsa yayi me ciwo yace “so baya duba wannan Habeey huda zuciya yake ya
shigeta faraddai cireshi ko sai an hada gayya nidai koma ya kike inasonki kuma ko duniya zata
taru akaina bazan taba daina sonki ba ki riqe wannan aranki"
Bai bata damar mgn ba yace Mata Dad ya turani Malaysia zan kula masa da wani company
nasa na watanni shidda nayi mgn da Fu'ad zaizo ya karbi passport dinki da sauran
documentation naki zaiyi miki Visa Zaki sameni acan, don Allah kada ki batamin lkc na fada
masa kada Visarki ta wucce sati saboda wlh a mugun matse nake dake na gaji da zama ni
kadai Habeey aure nakeso nayi"
Tabe baki tayi tace “aa nikam Taheer bazanje ba gsky inajin tsoro...." “me kikejin tsoro?" Ya fada
tare da dirowa daga gadon da yake yace “kina tsoron kada na siyar dake ne, ko kina tsoron
kada na kasheki ne? To koma meye kike tsoro dolene kiyi biyayya kibi mijinki zuwa inda yake
domin cetoshi daga halaka wlh idan bakizo