Showing 39001 words to 39902 words out of 39902 words
banason ganinka na tsaneka ya zanyi na cireka cikin
qaddarata tunda na hadu dakai qaddarorina suka qara tsanani Taheer nasan badon shegen
cikin nan nakaba da mahaifiyata bazata qyamaceni hakaba shikenan itama ka dasa Mata
tsanata a kunnena akan idona Addah take cemin ta tsaneni na fice Mata daga gdanta inba
hakabs ta tsinemin Taheer nikam nashiga ukuna waye zai soni waye zaiji tausayina..."
Matsawa yayi sosai numfashinsu na bugun juna yace “duk duniya nafi kowa sonki wlh har
mahaifiyarki nafita sonki habeey bazan taba gudunki a cikin hayyacina ba kiyi hqr nasan nine
silar faruwar komai nima a cikin qaddarata kike"
Shiru yayi na wani dogon lkc kukanta na dukar masa zuciya ya janyota jikinsa ya sanya
hannunsa ya shafa cikinta yace “bakici abinci ba kin barmin baby da yunwa ko?" Numfashi taja
ta miqe ta diro daga gadon yayi murmushi da yawan Mata ciki muni yake sanyasu itakuwa
gwanarsa wani sihirtaccen kyau ta qara, wayarsa ya dauka ya fita ya jima yana waya da Hajiya
Dije kakarsu ta wajen uba bai boye mata komai ba yana kuka ya zayyane mata komai itama
cikin tausayin kanta da jikokinta tace.
“Kowanne bawa baya wucce qaddararsa Taheer ka kawomin ita har zuwa lkcn da zuciyar
mahaifiyarta zatayi sanyi haqiqa yarinyar tana buqatar kulawa idan aka qyaleta ta qara
fantsama duniya bazataji kira ba saboda zata cigaba da daukar bata da wani me tausayinta a
duniya"
Yaji dadi sosai na yarda kakar tasa ta fahimceshi yanzu ne hankalinsa zai kwanta yakuma ji da
rikicin cikin gdansu, abinci ya nema Mata ya dawo ya tararta ta fito a wanka tana tsane jikinta
da towel saida numfashinsa ya dauke saboda wani yanayi daya shiga yayi saurin juyawa ya fice
saboda baison sake sanyata cikin damuwa yanzu nutsuwa tafi buqata. Saida ya daidaici ta gama sannan ya dawo ya tarar da ita a saman sallaya ta idar da sallar
La'asar ta dago sukayi ido hudu yayi mata murmushi yace “kinfi kyau kina murmushi Hurul
ainiy" qasa tayi da kanta ya matsa ya zauna yace “kiyi marnege da wannan Grandny tanacan
tana shirya Miki tuwon alkama miyar danyan kuka nasan baby na zaiso tunda shi babansa
yakeso"
Kallonsa takeyi har ya bude abincin ya debo a cokali yakai bakinsa ya tauna sannan ya matsa
gabanta ya kamo kanta ya dagota ya juye mata a bakinta ta lumshe idonta tana sauke ajiyar
zuciya.
Murmushi yayi ya hada mata tea tanacin abincin tanashan tea din tana kallonsa saida ta qoshi
ya qyaleta ya miqe ya fara hade mata kayanta yana zubawa a akwatinta babban ta matsa
gabansa tace “ina zamu Taheer nayiwa addahta alqawarin bazan qara zina ba a rayuwata don
Allah kada kace zaka mayar dani gdanka ka massheni kamar matarka"
Dagowa yayi ya kalleta yace “nima nayi alqawarin bazan sake tursasaki kiyi abinda bakiso ba a
yanzu nutsuwarki nafi buqata Habeey azare zan kaiki gdan kakata wacce ta haifi babana nasan
Zaki samu rayuwa me dadi anan har zuwa lkcn da Zaki haihu sai muyi aure mu raini babynmu
cikin kulawa da soyayya nasan Granny zata soki saboda ta taba ganin hotonki a wayata ta qare
miki kallo tace kina mata yanayi da wani data sani koda yake tace da yayan Abbanmu Sahabi
kike mata kama"
Zama tayi tana kallonsa har ya dauki kayan ya fita ya sake dawowa ya kamo hannunta yace
muje ko?"
Batayi masa musu ba suka fita ya bude mata suka shiga suka dauki hanya lkc zuwa lkc yana
kallon yanda tayi tagumi hannu biyu tana sharar hawaye, basu isa Azare ba sai bayan isha
sosai yabi wata hanya.
Itadai gabanta sai faduwa yakeyi saboda tunanin me zataje ta tarar acan din, parking yayi a
gaban wani gda babba gaban get din gidan cike da almajirai sunata karbar abinci, yayi horn
masu gadi suka bude masa ya shiga Granny tana tsaye a saman bene ta hangosu yana fito da
kayan itakuma ta koma gefe ta zauna a saman wani dutse tanata sharar hawaye gabanta naci
gaba da faduwa.
Tsugunnawa yayi a gabanta yace “inada tabbacin bazaki taba samun matsala anan ba My
Habeey shiyasa na kawoki ki saki ranki kiyi rayuwa me dadi, kamota taji anyi ana cewa "yo
karma ta saki ran nata mana basai na qwanqwashi kanta ba" dariya yayi itakuma ta kwantar da
kanta a kafadar Granny tanajin gabanta na tsananta faduwa itama Granny faduwa gabanta
yakeyi ta shafa kanta tace “ki kwantar da hankalinki kinji Habibatullah insha Allahu zakiyi farin
ciki zakiji dadin rayuwarki a gaba farko rayuwarki qunci qarshenta walwala da farin ciki
dawwamamme" a haka suka shiga ciki Granny tana cewa“Taheer yanzu babarka ta kirani take
fadamin kana neman bijirewa auren Saudat........"
_Tashin hankali kunji fah wata sabuwa Taheer zaiyi aure, wacece Saudat da zai aura? Meye ya
San gaban Granny da Habeey ya fadi lkcn da sukayi arba da juna? Shin wai Taheer ma zaiyi
biyayya kuwa wa zabin iyayensa? Wannan amsoshin sai a DUBAI PART TWO._
_Wannan shine qarshe part one na wannan lbr wadanda suka ruga sukayi subscribe dani akan
lbrn bandaku masu so nan gaba zaku biya kudinku ta wadannan hanyoyin dake sama_
_Zakujini Shiru na kwana uku Ina cikin wani uzuri ne insha Allahu nan da kwanaki ukun zamu
dora daga inda muka tsaya_
*UMMUH HAIRAN CE...✍️*