Showing 27001 words to 30000 words out of 31453 words

Chapter 10 - Mar Atussaliha Book 1 by Hafsat Umar Dangoro

fadamaka Wai ya kashe
matarsa ya dorawa megadin gidansa sharri akan shiya batar da ita Nan ko ba,ason
kasheta yayiba, to dai har yanzu anan ana bincike akai, ance Nan da wata biyu za,a
karasa cigaban labarin domin aji makomar Dan,iskar ,wato zurwaja haini
kenan"murmushin karfin hali Habib ya kakaro tare da hadiye wani mugun yawu agigice
yace" munir dan Allah inakasamo wannan labarin dan Allah kafadamin yanzu"munir ne
ta zubamasa ido Yana kallonsa kamar me nazarin wani abu daga bisani kuma yace,
Habib kanutsu mené zaka samu kanka akan abin da bakai ka aykata ba,bafa kaine
mutumin ba kawai nabaka labari ne,to mené n'a damuwa" dan sosa keya Habib yayi yace
am um dama kawai na tausaya masa ne,tab to amma ko wanene wannan yacika azzalumi
"uhm hakane Allah dai ya tona asirinsa ,munir ya fada, shiru Habib yayi bece komai
ba, munir kuwa ganin Haka yasa yace" Bross banjifa kace ameen ba" am um Ah ay
nafada azuciyata Ameen Allah ya tona ashirin Dan banza,am kaga munir tafiya zanyi
ina da wani ayki n'a ugila"to shirrar kenan gaskiya ni van yarda ba sai da Shira ta
dakko dadi zakace zaka tafi ni dai ka zauna" murmushi kawai Habib yayi ya dau Kee
dinsa ya nufi hanyar fita daga dakin,yanaji munir Yana cewa sai kadawo Allah ya
kiyaye hanya kakula da tuki fa kada kayi accident"becemasa komai ba ya fuce ya
shuga motarsa ya ja ya fuce daga gidan a guje....



______________________________________________________________MEDUGURI_____________
____


Tun da saliha ta bude idonta Babu abin da take gani sai duhu,Hatta hannayenta idan
ta dagasu duhu take gani bata ganinsu,hakanne yasa ta fara addu,a acikin zuciyarta
duk wadda tazo bakinta yi takeyi bata tasayawa,ganin yadda take addu,a Babu abin da
ya sauya daga cikin daki saima karuwa da duhun yake dadayi,hakan yasa saliha ta
soma tunanin ko ta mutune ,wannan duhun da take gani kabarintane a Haka ,
innalillahi wa'inna ilaihirraju,Mena aykata ,kodai azaftar da Habib danayine ,koba
komai mijinane kodai fushin Mala,ikune ke ayki akaine nashiga uku,Allah yasa dai ba
gaskiya bane ba, nashiga uku ni saliha inanake nan,runte idon ta tayi tasake budewa
nan danan abubuwan da suka faru suka shiga da wo mata filla filla,musamman yadda
take kallon Habib ido cikin ido Yana sokamata wuka acikin cikinta ,waiya zubillahi
Habib me nayi maka. Allah sarki baiwar Allah da tarasa abin da zatayi kawai sai ta
fashe da kuka hawaye masu dumi da azaba sun bin kuncinta kamar ruwa, kuka tacigaba
dayi sosai har sai da tayi me isarta sannan tayi shiru da kukan tace"ya allah nasan
duk inda kake Kana kallo Kana ganin yadda bawan ka ya wulakanta ni ya tozarta
rayuwata da ta "yan,uwana ya lalata komai da yazamana shi mallakinane sannan yake
kokarin kasheni "Allah Ina rokonka daka bani tsawan Rai da lafiya domin na ga yadda
zaka ramamin abin da ya aykatamin Allah inarokonka ka bani aron rai domin naga
karshen Habib ya ubangiji kada kadaukemin numfashina harsai Naga yadda karshen
bawannan naka zai kasance, tana Gama fadar hakan tasaki murmushi ,sannan tace"Habib
kenan if Allah see yes no body can see know....



Hasken fitila tagani Yana haskawa acikin dakin ,cikin sauri ta dago domin
ganin wake nufo inda take,tana daga idonta wazata gani,wata kekkewar budurwace
wadda bazata huce shekara 25/27 tana karaso ta Tana sakar mata murmushi,dafarko
saliha sai da ta tsorata da ganinta daga bisani kuma sai ta dake data tuna tana da
Allah ,Nan take tashiga yin addu,a tana furtawa dasauri da sauri ,matar kuwa Dada
tunkaro ta take tana na cigaba da yimata murmushin,sai da ta karaso daf da gadon da
saliha take ta tsaya a daidai kanta tace" ki kwantar da hankalinki sunana, Amina
"ki yar da Dani bazan cutar da ke ba inason ki bani hadin Kai duk abin da nace
kiyishi, kinjini "dasauri saliha ta daga kanta tare da cewa to, a hankula Amina
tasaka hannunta ta kama hannun saliha, suka shiga tafiya har suka karaso bakin
kofar fita, lokacin da saliha ta saka kafarta a bakin kofar jitai kanta Yana juyawa
dasauri da sauri kamar hajijiya,Amina da tafahimci haka tayi sauri tashiga tofa
mata addu,a da wani kullun ruwa dayake hannunta, sannan saliha ta dawo hayyacinta
suka fito, suna fitowa doctor faruq yace"yawa Aminatu agaskiya na jinjina Miki
kinyi kokari ,yanzu zaki iya tafiya kingama aykinki na yau saura gobe Kuma, Amina
ce ta bushe da wata mahaukaciyar dariya sannan tace,ku Kuna da hankali kuwa ,ni
Aminatu zaku ce zaku hada baki dani kucuci baiwar Allah batajiba bata gani ba ,to
muddum Ina Raye sai na ceci wannan yarinyar",tafara tare da Kara damke hannun
saliha.


Daya daga cikin "yan daban gurin ne ya taso a hargitse yayo kan Amina da wata
doguwar wuka a hannunsa yace,ke muzakiyiwa taurin kai" yan zunnan nan zan hullaki
inda ba,a dawowa ,ya daga wukar zai caka mata" yaji anyiwa wukar kekkewan ruko,yaja
yaja yakasa kwacewa ,take ya juyo Dan ganin wanene,Yana juyowa suka hada ido da
saliha wadda idon ta yakada yayi jajur kamar garwashi Nan danan fuskarta ta canza
kala tazama wata iriya idan ka ga saliha wannan lokacin abin sai ya baka tsoro"
afusace", ta ja wukar Nan danan ta fede masa hannu ta wukar sannan tayi wulli dashi
gefe yaje ya daki wata bishiyar tsamiya ,dayan ne yatashi da gudu zai gudu,cikin
zafin nama saliha ta damkoshi tare dacewa " ni zaku kashe akanme "menayi muku!" Ta
shararamasa maruka har hudu wan da yayi sana diyyar murdewar kansa gefe daya" amma
duk da Haka saliha bata barshiba tacegaba da marinshi tana cewa me tayi musu,tana
tsaka da Haka ta hango doctor faruq har yayi nisa ya gudu tun tuni,wayar tashima a
gurin ya wurgar da ita Sabi da tsabar tashin hankalin da yagani, jikin saliha
harrawa take ta kama hanya tanufi inda doctor yayi "sai dai kashe tana daga kafarta
ta fadi a gurin sumammiya ,Nan take Amina ta durkusa tashiga Kiran sunan ta Amma
shiru, da sauri ta dakko wayarta a aljihun wandonta tashiga contact ,ta danna wata
number wadda akayi seven da my best friend ,sannan tashiga Kiran number bugu daya
ya daga,tare da cewa" my best da matsala fa" bakinsa harrawa yake wajen cewa
matsalar me fa,meya faru da,ita ?" Ka kwantar da hankalin ka kawai dai ta tada
aljanune kasan tana da dinki acikinta yanzu ansamu matsala dinkin ya bude kana
kusane ka karaso, pleace my best ka nutsu dan Allah,ka debo Kayan ayki cikin
nutsuwa kada ka manta abu ko daya ,yanzu Zan dauketa na huce da ita gida kasamemu
acan" okay thanks ya fada tare da katse wayar,yashiga debo kayayyakin ayki,daganan
kuma yafito ya shiga mota ya Sona tuki,abin takaicin shine ban gane wanene Shiba
sakamakon lullube fuskarsa da yayi ,Ina dai iya gano launin idanuwansa daga cikin
hiramin daya yafa......



Tom tuki yakeyi sosai be tsaya ba har sai da ya Isa,wani Dan madaidai cin
gida,wan da yake shi kadaine a bangaren sai wasu tsillatsillar gidaje agefansa,
parking yayi a bakin gidan,sannan ya saka hannu ya debo kayan aykin ya rufe kofar
ya shiga cikin gidan da sauri, Yana shiga Kai tsaye wani saki yashega wan da yake
tunanin Yana suna ciki, Yana shiga yasamesu a falo, inda saliha take ya
kalla ,tanakwance saman kujera 3ster idanuwan ta a lumshe,fuskarnan tayi suwet ta
rame,sabi da tsabar ciwon da yake cin ta,gurin da Habib ya caka mata wukar ya kalla
da sauri ya runtse idonsa ya bude tare da karasawa gurin da sauri, ya durkusa a
gabanta tare da zubamata ido hawaye na bin fuskarsa,zuciyarsa cike da tsananin
tausayinsa, Aminace ta saurin dakatar dashi dacewa" mené Haka best, bakuka zaka
zauna yiba ka fara ceto rayuwarta tukuna ,idan yaso saika cigaba da kukan, murmushi
sakar mata yace"Amina nagode sosai Allah ya saka Miki da alkairi, " Amina dole nayi
farinciki kasancewar MAR'ATU na bata mutuba" Amina mekikeso na Baki kifadi duk
abin da kikeso nikuma na amince Zan Baki duk abin da kikeso" murmushi Amina tayi
tace" kafara ceto rayuwarta tukuna,kar katsaya soyayya Kuma soulmate din taka ta
mutu" don wannan yarinyar idan baka sameta ba mutuwa Ina tunanin zakayi, dariya
yayi sosai sannan ya dauki kayan aykin yashiga gyra gurin ciwon, yanayi Amina tana
taimaka masa ,Sabi da shi akwai tausayi da soyayya daker yake aykin,ahaka dai suka
samu suka gama gyramata gurin sannan hankalin best ya kwanta.....
Habib kuwa ... Tsawan awa 3 Yana Kiran number wayar doctor faruq Amma shiru
kakejj anki dagawa ,Nan take hankalinsa yayi mummunnan faduwa ,Nan danan yashiga
tunanin kodai asirinsa ne yake Shirin tonuwa idan ko hakane , shikkenan tashi
takare aduniyar Nan domin yasan Babu me fahimtar sa, shiru yayi acikin motar Yana
sunanin kodai yaje ya samu munir ya karasa masa labarin mutumin Nan, Dan yaga kusan
labarin nasu iri dayane ,Yana tunanin idan yaji makomai wancen mutumin ,shima tashi
zata iya kasancewa haka in yaso sai yayiwa kansa kekkewan shiri, dafe kansa ya
sakeyi tare da tauna lebe ,yadda har sai da kini ya fito sannan Kuma yadaki
sitiyarin motar yace"to ay Kuma yace sai Nan da wata biyu za,a fadi makomar wannan
mutumin kash yafada dakarfi"oh my God ni Habib Naga takaina....


12...


MEDUGURI.....


""Namata allurar bacci Amina" yanzu zantafi inafatan dai zaki kulamin da lafiyar
ta"nasan kina da kokari akan Haka inaso ki Kara" murmushi Amina tayi tace" to king
of the love Insha Allah zankula sosai " ka kwantar da hankalin ka Babu abin da zai
samu saliha insha Allah"

"Yauwa Amina nagode sosai Allah ya bar zumunci "yanzu Zan huce gida sai gobe zan
dawo ki kuka da lokacin yimata allurar bacci domin zuciyar ta tasamu nutsuwa"

"Tom shikkenan INSHA allah ay naji basai kata maimaitamin ba"sai kace bansan
aykina ba ,ko akan ta akafara ciwo"nifa ka isheni"

"Allah ya huci zuciyarki Aminatu "Kinga tafiya ta " yamike tsaye tare da yin
hanyar fita, har yakai bakin kofa Kuma sai ya dawo ya Kara zubawa saliha ido kamar
zai cinyeta Yana faman murmushi"

Itakon amina rike haba tayi tana kallon ikon Allah agaskiya tayar da da irin.
Son da best ya ke nunawa saliha, ta yarda saliha ta mamaye zuciyar best yadda Babu
wata "ya mace da ta Isa tasamu gurbi a zuciyarsa Babu ita.

"Gyran murya tayi tace to sarkin love zaka tafine kokuma nasa maka ita a mota
ka tafi da ita ?" Dan zaro ido Habib yayi yace "a,a tazauna anan"

"To ay Naga zaka cinye 'yar mutane ne,ko dai kafara maita ban Dani ba?"
Dariya Habib yayi yace "keko sai addu,a haryanzu dai halinki bazai canza
ba ,to natafi hankalinki ya kwanta" Yana Gama fadar Haka yajuya yatafi , itako
Amina bayansa tabi da kallo zuciyarta cike da tsananin tausayinsa.


Bayan futar best , Amina ce ta dauki katon bargo ta lullube saliha" sanan
ta Mike ta nufi cikin kicin ta kunna gas sanan ta dora ruwa akan gas, bayan ruwan
yayi zafine ta sauke ruwan ta zuba acikin kula domin karyayi sanyi, bayan ta gama
ta dora wani ruwan acikin karamar buta ta karfe,sanan ta zuba citta ,kanimfari,
n'a,ana,a , da ganyen shayi e.t.c, bayan shayin ya dahune ta sauke a kasa,sannan ta
nufi daki ta Kwan ta "tana kwanciyar ta jiyo rurin wayarta Yana Kara a falo,dasauri
ta Mike ta nufi falon ta dauka,tana dubawa taga Ashe best ne, murmushi tadanyi tace
uhm "romiyo kenan tafada tare da daga wayar ta Kara a kunne ta tace"...

"Hello"
Daga can bangaren aka amsa da "assalamualaikum"

"Ameen wa, alaikumussalam" best ya akayine har kaje gida"

"Eh wlh naje yajikin madam Dina" dasauki best Wai meyasa ka takurawa kanka Haka"

"Uhm bazaki gane bane shiyasa, bikisan yadda nakeji da itaba" dariya tadanyi
tace Niko nasan yadda kakeji da MAR'ATU"

"Adai bar maganar Amina kadan kika Sani "yanzu dai ya jikin nata ta farka" a,a
Nan da zuwa 5na yamma zata iya farkawa " okay zuwa anjima zan kara kiranki"

"Okay babu damuwa mujima da yawa"

Tana katse wayar ta saki wata ajiyar zuciya,tadan furzar da iska daga bakin ta
tace"Allah sarki so" lokacin da Best ya bar kasarmu muka Gama karatu sau ayi wata
uku be kirani ba Amma tun da ruhinsa tazo hannun na shikkenan nashiga siradin
takura, tana Gama maganar ta kwanta akan kujerar ta lumshe ido sai bacci...


"Malan Wai ko kaji batan wannan matar da kaje cire mata aljanu" eh naji
wallahi amma ina tsoron zuwa gidan karda naje ina shiga ta dawo,inason naje nayiwa
Habib jaje Amma Babu dama" haba Malan ay a Haka zaka daure kaje "idan bakaje ba
Habib bazaiji dadi ba" hm shikkenan Zan je amma kafin natafi zan yi ban kwana da ku
bansani ba ko mutuwace ke bina,"dariya ce ta subucewa matar malan batasan lokacin
da ta kwashe da ita ba harda kwanciya a kasa tsabar dariya...



To juneid ne zaune a dakinsa Yana dan daddanna wayarsa" danna wayar yake amma
hankalin sa na can wani gurin tunani kawai yakeyi" Yana tsaka da Haka yaji wayan na
ruri bugu daya ya daga tare da Kara wayar a kunne yace "assalamualaikum"doctor wa,
alaikumussalam sir barka da wannan lokacin" barka dai yakake ya me jiki" lafiya kau
sir daman nakira Kane n'a sanar da Kai wannan yarinyar ta samu lafiya" Dasauri
juneid yace alhamdulillah"yanzu ina take" sir sai dai matsala daya dole saika zo
India Sabi da kullum cikin furgici take da kokarin guduwa" okay Babu damuwa Nan da
two weeks Zan iso yanzu Ina da San wani ayki danake son karasawa da nagama Zan
shigo insha Allah,inason kacigaba da kuka da ita Dan Allah,sannan kadinga kwantar
mata da hankali" okay sir angama,ya katse wayar tare da sakar ajiyar zuciya...



Shiko doctor juyawa yayi inda take a kwance, idanuwan ta lumshe da alama bacci
takeyi" Masha Allah kekkewar budurwace wadda akalla zatayi shekara 24 a duniya
farace doguwa sosai,gashinta ya barbazo kan fuskarta gabadaya ya lullube fuskar,da
alama andanyi dambe da ita kafin asamu ta nutsu tayi bacci, bacci takeyi Amma sai
faman sauke ajiyar zuciya take,kanta kuwa daure take da farin bandeji Wanda ya
karamata kyau da kwarjini,sai Dana Kara kurama fuskarta ido sannan na tabbatar da
cewa idonta ne kawai arufe amma kamar ba bacci takeba sakamakon bakinta danaga ni
Yana motsawa Yana furta karma biyu sune"Abba Zan mutu "Abba zanmutu"Abba Zan
mutu"cikin tausayawa doctor yake bin budurwar da kallo,Yana mamakin yadda akai
yarinya budurwa ",yarshekara 16 akayiwa wannan mummunan tabon da baya taba gogewa
har tsufanka,kumama bayan haka sabo da tsabar rashin Imani irin na mutum,kwakwalwar
tatama baza,a Bari ta zauna kalauba sai da aka nakasata "jibi fa tsawan shekara 8
muna zaune da ita anan asbitin bata iya furta komai sai Abba zanmutu" ankawota tana
shekara 16yanzu gashi tacika shekara 24 bansan Kuma Nan gaba adadin shekarun da
zata dauka a kwanceba, Allah sarki baiwar Allah ...
__tom Amina sai bata tashi daga bacci ba sai karfe 4:30 shima saliha ce ta
tashi tana Kiran sunanta" zumbur ta Mike ta nufi gurinta tana mata sannu"daker take
iya cewa yauwa" murya a sanyaye saliha ta kalli Amina tace" kina da kirki Dan Allah
ki fadamin me wacece?"murmushi Amina tayi tace"ki kwantar da hankalin ki saliha
indai nice karki wani tsorata, ni d'un da kike gani kawar best ce "shinenan
yakirani yace naje n'a taimakeki" best Kuma saliha tashiga maimaita sunan
abakinta ,tashiga duniyar tunanin Ina tataba Jin me sunannan, runtse ido tai ta
bude Amma ta kasa tunano inda tasan me sunan, sai kawai ta Kara kallon Amina tace
please waye best" murmushi kawai Amina tayi tace kinsan shi idan kika Gandhi zaki
ganeshi"yadda Amina take magana saliha ta kuramata ido tana kallonta" Kallonta take
kamar tataba ganin ta Amma Kuma sai ta kasa Tina ainada tasan ta ,hakanne yasa
saliha ta dafa kanta tace oh my God" Amina ce ta kalleta tace"lafiyar ki kuwa"
marda kanta tayi ta kwanta tace "lafiya kalau "oky Bari naje na hadamiki ruwan
wanka ko inyaso sai na kawomiki ko ruwan zafine Kisha domin cikinki ya sarware,Dan
na fuskanci kina kin yunwa...


13...



"Tashi tayi ta je ta hada mata ruwan zafi sannan, tazo ta kamata zuwa
bathroom"bayan ta shigar da ita ne sannan ta fito ta jawo kofar ta koma falo,

Saliha kuwa bayan ta shiga bathroom zama tayi dirshe a kasa ta shiga duniyar tunani
tana cewa azuciyarta "kenan da Habib soyayi ya kasheni" to amma menene nufinsa
akaina da yasa aka sani awannan dakin kuma akamin dinki aciki" kodai soyake ya
azaftar Dani" Kay a,a to idan ba Haka ba meyakeso ya min" shiru ta danyi tana bin
bandakin da kallo kamar meshirin tunano wani abu can Kuma kamar an tsikareta ta
Mike tashiga yin wankan...


*Gudu yake taugawa akan titi kamar wan da zai tashi sama har ya karasa bakin
katafaren get din gidansu, Yana karasawa me gadi ya bude masa geta ya shiga a
guje,ko parking space be karasaba ya ajiye motar ya futo yayi cikin gida a
guje,yana shiga yasamu momy a falo tana zaune tana Shan ruwa, bece mata komai ba ya
huce sama ya shiga dakinsa ya kwanta tare da Jan bargo me kwauri,ya rufa "momy kam
bayansa tabi domin taji lafiya, tana shiga dakin tasameshi akwance a rufe, gefan
gadon ta zauna sannan ta ce "abee lafiya kuwa kashigo a hargitse meyasameka" ta yi
tambayar cikin damuwa, Habib kuwa jikinsa hauwani rawa yake tsabar sanyi da kaduwa
yashiga cewa "momy ki rufeni Dan Allah momy sanyi nakeji "what sanyi "bangane na
rufekaba me kake nufi, wannan bargon da ka lulluba fa "momy wallahi sanyi nakeji
dan Allah ki rufemun jikina,ni bargonnan babu abin da ya tare mun" momy bansan me
yasaba jinake kamar wani abu zai faru Dani "jinake kamar ana caccakar jikina kiyi
min addu,a Ina tunanin mutuwa zanyi" momy kam tun da tadau abin na Habib wasa
yanzukuma ta fara ganin kamar da gaske bashi da lafiya" kallonsa ta karayi tace
"habibu kodai rashin matar ka da kayine ya sa kashiga wannan yanayin eh "uhm momy
bazaki gane ba inason nayi bacci ki kwanta a kusa Dani momy"zaro ido mom tayi tare
da cewa akusa dakai fa kace na kwanta akan me ,baka da hankali Kato da Kai zakace
na kwanta a kusa dakai" please mom wallahi indai nikadaine zanta gani Ana
tsoratanine momy tsoro nakeji "mummunnan mafarki zanyi idan na kwanta Nika,dai" au
Dan kana mafarki shine zakace na kwana dakai Sabi da agarin mahaukata ake, Ina
laifin kace na taimaka maka zuwa dakin yayanka Junaidu ka kwana dashi" a,a momy
wallahi yaya juneid bazai rarrasheni ba tsokana ta kawai zai tayi " yayi maganar
kamar zaiyi kuka, Tom shikkenan Zan kwanta Amma afalo sai na dinga kula dakai" tana
Gama fadar Haka ta Mike tanufi hanyar fita,

Shiko Habib wata kwalla ya goge daga idonsa Yana jin Babu dadi azuciyarsa zuwa
yanzu yafara tausaya wa kansa da iyayenka,jibi yadda mahaifiyarsu take tausayinsa
kawai sabi da farinciki sa zatazo ta kwana anan,idan ban da mahaifiya Wace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login