Showing 9001 words to 10655 words out of 10655 words

Chapter 4 - MATAR HEDIMASTA by Aisha Abdullahi Sani

sai ya koma ya yi takeaway ya sa a mota.
Bai koma gidan ba har sai da dare ya yi.
Yana komawa yaga gidan da dakin kaca-kaca har wani hamamin wari ne yake tashi.
Ita kuwa tana zaune gaban tv tana kallo tana ta sheƙa dariya ko a jikinta.
Har ya shigo bata sani ba sai da ya kashe tv kafin ta juya tana , " wani dan iskan ne ya kashe mun kallona." Tana rufe baki suna hada ido.


Ya ce , "Dan iska ko? Inaga dai duk ranar da na fasa miki bakin nan naki zaki setu ki rage rashin kunyar nan da fitsara kuma maza ki tashi ki gyara gidan nan tas domin ni ba dan aikin ki bane."


Bin falon da kallo ta fara yi kafin ta kalleshi, "ina za a gyara me ye ya faru a gidan?"
Saheer ya ce, "kin makance ne? Na ce ko kin makance ne ko kazantar taki ce ta shahara?"


"Yoo shahara na nawa kuma? Ai ni sunana ma a kauye shahararriya salame." Salma ta fada tana murguda masa baki.


Kasa hakuri ya yi ya cire belt dinsa zai maka mata cikin Muryar sauri ta ce, "zan yi wallahi zan gyara."
Ya nuna mata kitchen da hannu.
To maza muje ki fara da nan sai kin wanke komai kuma kinyi moping.
A kanta ya tsaya da belt din a hannunsa ya na yi mata direction yadda zata yi tana yi tana kuka.
Domin ba saba aiki tayi ba ta wanke ya ce bai wanku ba ta sake wankewa a haka har ta gama wanke wanken.
Mopping din kuwa da rarrafe ta karasa tana yi tana zufa.
Tana gama gyara kitchen din ya ce su dawo falo ma ta gyara, nan ma haka ya tsaya sai da ta gyara shi tsaf.
Don dole bakinta ya mutu ta kasa magana bare motsawa a inda ta zauna.
Ganin dare ya yi takeaway din da ya tawo da shi ya bata.
Aiko tana karba ta fara ci hannu baka hannu kwarya.
Tana gama ci ta baje agun sai barci.
Saukar ruwa taji a fuskarta Saheer na fadin ta tashi taje tayi sallah.
Tsaki tayi tana kokarin komawa.
Ganin ya dauko belt ai tuni ta tashi aranta tana, "aradun Allah duk abun da ka mun yau sai na rama ai kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha."


Sai da yyi sallar isha kafin ya dawo gidan ya kunna TV tana zaune a gefe yana zama ita ma taje kusa da shi ta zauna.
Tsawa ya dakata mata yana, "wani irin iskanci ne wannan? Dallah nemi wajenki ki zauna."
Bata kula shi ba kuwa ta zauna a gefe tana kallonshi.
Can anjima ta kalleshi sai sun hada ido sai tayi kwafa sai ta kawar da kai haka ta dinga yi har sai da ya kashe tvn yaje ya kwanta ita kam tana zaune.
Lakashi tayi sai da ta tabbatar ya yi barci sannan ta jura farar jallabiyarsa a jikinta ta shafa farar hodo a fuskarta ta bude kanta gashinta kamar hamtar yan iska a tsattsaye.
Wutar dakin ta kashe sai na falon kadam kadan dake haska dakin.
Ta shiga dakin tana Wata irin ƙatuwar muryar tana kiran sunan shi, "SAHEERUUUUUU SAHEEERUUUU SAHEERRUU."
Kamar a mafarki Saheer yaji yana kiran shi aiko yana bude ido me zai gani.....


*Gobe zamu gama free pages In sha Allah*
500 ne kacal
8103080717
Aisha Abdullahi Sani
Opay
Or
1453215759
Aisha Abdullahi Sani
Access Bank


Evidence of payment to
08103080717
[7/3, 9:53 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*


©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*


PAGE-10
*Last Free Page*

Fararen kayan kawai yake ganin alama ana motsi kuma ana kiran sunan shi.
"Innalillahi wa inna illaihir ra'ji'un,na shiga uku,na shiga uku." Ya fada yana ƙankame jikinsa yana janyewa zuwa karshen gadon.
Ya gama tsorata.
Ita kuwa Salma ƙara binshi take tana kiran sunan shi tana, "kar ka ƙara taɓa mana diyarmu salame kar ka kuskura ka kara dukanta ko yi mata kallon banza."
Yana jin wannan maganar ya gane Salma ce.
Cikin ɓacin rai ya tashi ya kunna wutar dakin idonta a rufe Bata san har ya tashi ba ci gaba da zaro zance take tana, "in ka kuskura ka kara taɓa mana diyarmu sai mun halakakaaa." Saukar marin da taji ne ya sata saurin bude ido.
Saheer ya ce, "in ke baki hallaka ni ba ni na hallaka ki ai wawiya kawai."
Da harara ta bi shi tana, "Oho dai Allah saka min mugu kawai mai kan agwagi." Ta karasa maganar tana ficewa da sauri.
Tsaki ya yi ya ce, "idiot." ya koma ya kwanta abun shi.


Sai da ta kara tabbatar da cewa ya koma barci kafin a hankali ta shige ta kwanta.
Ta kwanta barci yaki zuwa ga baki ya saba da kwadayi.
Haka ta tashi ta koma kitchen tana dube dube ta ci karo da gwangwan madarar gari.
Washe baki tayi ta dauka ta dauki cokali ta je ta hau gadon ta Fara nakar madara kamar tuwo.
Bakinta da fuskarta baja baja madara ta ko ina hatta zanin gadon ma duk ta fara batawa.
Sautin yadda take shan madarar ne ya tada Saheer kamar mai jan ganda har wani gwaranci take.
Yana tashi ta boye madarar a bayanta tana sude baki.
Idanun nan kuwa sunyi kifi kifi na rashin gaskiya. ya ce, "me kike sha cikin daren nan?"
"Umm umm ba komai." Ta fada tana kara boyewa .
Kallon fuskarta ya yi da bakinta tana sudewa ya ce, "bani abun da kike sha."
Salma ta ce, "ba komai fa ni ba wani abun da nake sha."
"Na ce ki bani." Ya fada cikin tsawa.
Da sauri ta mika masa gwangwanin madarar.
Ya yi tsaki ya fita ya mayar ciki ne amman har ta kusa shanyewa saura kadan.


Yana komawa dakin ya ce, "ke wai wace iri ce Don Allah? Hankali ne baki da ko yaya? Shin wannan ba madarar shan tea bane? Ko ke karamar yarinya ce?"
Yana maganarsa ta juya masa baya abunta tana , "oho to waya sani ma."


Saheer ya ce, "kar kimin shiru a wajen nan, kuma daga yau na kafa miki doka kullum kina tashi da sasafe kina gyara gidan nan kina dafawa kanki abun da zaki ci domin ni ba bawanki bane in ko hakan yaki samuwa zaki sha mamaki." Ya fada yana kwanciya.
Kananun magana ta dunga yi ciki ciki har barci ya kwasheta ita ma.
Wani irin kwanciya sukai gabadaya ta cinye gadon duk ta bararraje shiko ya tukura gefe guda gashi yana tsoron ba abun ya sauka kan gadon ba ta fadawa Inna ya shiga uku.


Da asuba ya tasheta tana sallah ya sa ta fara gyaran gidan kamar yadda ya fada tana yi tana mita domin ita barci take ji.
Yana gama shirinsa ya ajiye mata 200 kudin Break ya yi tafiyarsa.
Binsa Salma ta yi tana, "Mijin mijin ba za ka jirani ba? Ban gama shiryawa ba fa."
Wani mummunan kallo ya bita da shi ya ce, "kar ki tawo da kafafunki." Ya shige motarsa ya fice.


"Mugu kawai mai kama da kashin awaki." Ta fada tana komawa ciki.


Haka ta kwaba indomie ta dafa kamar an wanke kan mahaukaciya ta zauna ta naki abunta.
Ta kwashe sauran madaran da ya kwace a gunta tasa a leda tasa cikin jaka.
Uniform din tasa duk ya matse mata jiki ko ina ta motsa yana rawa .
Irin guntuyen rigunan nan ne iya gwiwa da karamin hijabi.
Hijabin nata kuwa ko kirjinta bai gama rufewa ba ga nonuwa a baje ba breziya duk inda tayi sai sun bi sun motsa.
Rataya jakarta ta yi ta fice ita ma ta kama hanyar school din.


Tana cikin tafiya ta tsaya bude jakar ta dauko kullin madararta tana tafiya tana sha.
Ta ga wancen ta tsokana ta ga wannan ta tsokana har ta kai School din.
Ta shige tun daga mai gadi har sauran student Binta ake da kallo.
Zata shiga class ke nan
Ta hango Saheer ya fito a office dinsa da kumburarren goshi ya kara tsini.
Wage baki tayi tana dariya da karfi ta ce, "Mai ƙulu a goshi."
Gabadaya student da sauran teacher din da ke wajen sai da suka juya suna kallonshi.
Tana nuna shi tana dariya.
Kunya kamar Saheer zai nutse haka ya koma office ba don ya so ba.
Habib ne ya jata yana, "Ke Salma Headmaster ne fa ki daina."
Ta ce "Shegemasta sunan shi?"
Habib ya ce, "aa Headmaster shugaban makarantar nan."
Tsaki ta yi, "yoo ina ruwana da wani Shegemasta gashi nan garin muguntarsa ai ya sha kulu." Suka shige class tare tana dariya.


Bayan Kwana Uku.
Kwance take a gado daga ita sai zani zanin ma ya fice babu komai a jikinta a dole tana jin zafi tayi daurin kirji ta kwanta barci shi kuma Saheer ya fita bai dawo gidan ba.
Shigowar sa kenan da nufin zai shiga toilet ya yi wanka,har ya wuceta kawai ya dawo ya tsaya akanta wajen minti biyar yana ta sake sake a zuciyarsa can kuma kawai ya tsinci kanshi da fara cire kayan jikinsa ya haye kan gadon.
Damkar da ya mata ne ya sata saurin farkawa tana kokarin kauce masa.
Ina ya riga ya gama tafiya ihu ta fara ta tana "wayyo ni wayyo Allah inna ta aura mun mugu wayyo ni wayyo zai kasheni, shikenan zai kashe ni, mugu ne azzalumi mai fuskar agwagi, dan iskane maciji yake samun cikin jikina, mugu zai kasheni." Ta fada tana gantsara masa cizo.
Tamkar zugashi take bai barta har sai da ya tabbatar da abun da yake bukata ya tabbatu.
Washegari bata tashi ba har ya tafi School sai wajen karfe takwas da rabi ta tashi.
Tana ganin agogo ta fara salati tana, "mugun cen, mugun cen ne ya ja mun." Ta tashi da sauri tayi wanka ta ci abinci duk da cewa bata jin dadin jikinta amman ta gammace taje school dinnan da ta zauna agidan.
Haka ta fara nakan hanya tana yi tana hutawa.
Tana zuwa kuwa shine a class dinsu.
Ta shiga zata zauna ya ce, "wait yanzu ake zuwa school? Kin san karfe nawa ne yanzu?"


Salma ta ce, "kai ka manta abun da ya faru jiyane da.....
Kafin ta karasa ya yi saurin....


*To Ma Sha Allah wannan shine last free page duk wacce take son ci gaba zata biya domin ta shiga grp ta karanta, indai kun gama payment kan lokaci In sha Allah Monday zan ci gaba da posting😻🤍.*


500 ne kacal
8103080717
Aisha Abdullahi Sani
Opay
Or
1453215759
Aisha Abdullahi Sani
Access Bank


Evidence of payment to
08103080717

2
3
4

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login