Showing 6001 words to 9000 words out of 10655 words
Chapter 3 - MATAR HEDIMASTA by Aisha Abdullahi Sani
naki baza ki bini da wannan haukar ba."
Da gudu taje ta wanke tana"cab yanzu haka kishi yake yi na yi kyau kar a kalle mai ni ,yoo da yaki fita dani ai gwanda inje in goge ,ysn kishi yake ya ga kyakkyawar mata."
Saboda ta riga ya gama caba fuskar raguwa dai hodar tayi amman da sauran fari farin.
Ta koma tana washe baki, "Mijin na goge."
Bai ce komai ba ya tashi.
Ita ma ta bi bayan shi.
Suna shiga motan sai ga kiran Dady ya na cemai su biyo ta gida kafin su wuce zai bashi sako.
Suna zuwa gidan Salma ta shige a guje ta rugume Inna.
Inna ta ce, "ke wai har kin gama amarcin ne ya haka?"
Sallamar Saheer ce ta katse su
Da yake duka Momy har Dadyn ma suna falon.
Dady ya ce, "e zasu je makaranta ne zata fara zuwa Inna kinga ba dadi abarta a gidan ita kadai."
Inna ta ce , "Ah eeh kuma kam hakane ya yi kyau."
Bayan duk sun gama gaisawa Dady ya bawa Saheer Files din da yace ma shi yazo ya karba.
Zai tashi kenan Salma ta ce, "Yawwa Inna ba kin ce gado daya zamuna kwana ba?"
Inna ta ce, "kwarai kuwa yo mene ne auren in ba kwana gado daya ba?"
Salma ta ce , "aradun Allah cewa ya yi wai shi bazai kwana dani ba har da tureni a kasa kuma wai ko jikinshi kar in kara tabawa."
Kuka Inna ta fashe da shi, "Oh Allah oh duniya yanzu Sahaaru abun da za ka mun kenan? Ka ce baza ku kwana gado daya ba? Sahaaru in baka kwana da matar ka ba dawa zaka kwana?bakin ciki kake mun da ganin yaran salame kafin in bar duniya? Sahaaru anya kana so ka ga Annabi kuwa? Wato da so kake ka ci bulus ka ci bati siddin anki an rufa ma asiri shine bari mu ka tona mana" Ta kara fashewa da kuka.
Dafe kai Dady ya yi,ya kalli Saheer ya ce, "Ka bawa Inna hakuri kuma daga yau kar ka kara cewa ba za kwana da matarka ba kar in kara jin abu makamancin wannan."
Saheer ya ce, "kiyi hakuri Inna in sha Allah hakan bazai kara faruwa ba."
Share hawayen ta yi ta ce, "to too Allah yasa, ku tashi ku tafi."
★★Suna zuwa school din ta fara washe baki tana, "mijin nan ne makarantar da zaka sani?"
Wani gigitaccen kallo ya bita da shi da yasata yin shirun dole.
Office dinsa ya wuce da ita kai tsaye sannan ya kira wata teacher ya ce mata ta je ta mata interview kafin a bata class.
Rike mata hannu tayi suka fita suka shiga wani office din.
Ta mika mata takarda da biro ta ce, "Oya write ur name."
Kallonta salma ta yi da mamaki tana, "namai? Namai kuma?"
Teacher din ta yi murmushi ta ce, "Sorry rubuta mun sunanki."
S din ta fara rubutawa tana kallon gabas kafin ta rubuta a na kallon yamma l din kuwa tun daga kasa har sama aka rubuta anan ta tsaya.
Ta washe baki tana, "gashi nan malama."
Teacher Hafsat ta ce, "mene ne sunan naki?"
Salma ta kara washe baki kafin ta ce, "Salamatu amman Inna na ce mun salame amman yan garin nan gidan yan uwanmu ce mun suke salma."
Teacher Hafsat ta jinjina kai kafin ta ce, "to zaki iya rubuta mun Abcd yanzu?"
Salma ta girgiza kai, "cab aradun Allah ban iyawa duka na dai iya rerawa da waka duk."
Bayan Teacher ta gama yi mata tare suka koma office din Saheer ta ce, "Sir gaskiya akwai matsala bata iya abubuwa ba da dama infact ma zan iya cewa tana bukatar sabin darusa ne indai ana son karatunta ya tashi da sauri."
Saheer ya ce , "ok Teacher Hafsat amman me kike ganin ya dace a mata a yanzu?"
Teacher Hafsat ta ce, "ehto ina ganin akaita primary four amman kuma a bawa iyayenta shawarar ana mata lesson a gida domin zamanta a primary 1 to 3 zai iya durkusar da ita maimakon so da ake ta tashi tunda duk yarana kananu sosai, in akace sa'a kuma ta maida hankali ina ganin za a iya samun abun da ake so."
Saheer ya ce, "Ok to ki kaita class din yanzu sai kije ki duba ko za asamu uniform daidai nata da duk wasu materials ki hada ki kawo mun nan."
"Ok sir." Ta amsa kafin su suka fice.
Salma na shiga class kallon kallo take da yan ajin kusa da wani namiji da girman jikinsu ya kusan zuwa daya ta zauna.
Ya daga mata hannu.
Ta washe masa baki tana, "sunana salame kai fa."
Ya ce , "Habib."
Dariya ta yi ta ce, "Habibu."
Kwanciya tayi akan desk ta fara barci har sai da lokacin break ya yi Habib ya tabata.
Tana fita ta yi office din Saheer.
Cike yake da mutane ya yi baƙi ko a jikinta ta bankada ta shige tana, "Mijin an fita tara,ka bani kudin tara......
Free pages na daf da karewa In sha Allah
Saura two pages
500 ne kacal
8103080717
Aisha Abdullahi Sani
Opay
Or
1453215759
Aisha Abdullahi Sani
Access Bank
Evidence of payment to
08103080717
Luvs u all
[6/30, 10:38 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*
PAGE-7
Saheer ya kau da kai kamar bai ji me take fada ba.
Ya ci gaba da yi musu bayani.
Karasawa gabansa ta yi ta ce, "Mijin na ce ma an fito tara ka bani kudi inje in siya abu nima in ci."
Ganin hankalin kowa agun ya koma kanta yasa shi yin gyaran murya ya ce, "Sorry guys she's our new student and she comes from villege,so she may not be familiar with our way of behavior."
Yana karasa maganar ya duba aljihunsa daga 500 sai 1000 , 500 din ya mika mata domin damuwarshi kawai ta fice daga office din ne a halin yanzu.
Aiko yana mika mata ta fisge da sauri ,ta juya zata tafi Coke din ta gani gaban bakin ta koma ta kallesu sai da suka hada ido kafin ta dauka ta zura aguje.
Sai da taje bakin kofar zata fita kafin ta juyo ta kallesu ta yi gwalo kafin ta ce, "in kana da karfi kazo ka kwata."
Ta arce a dari.
Dariya suka fara ban da Saheer da ya kulla.
Ya yi gyaran murya ya ci gaba da maganarsa.
Ita kuwa tana fita school shop din ta nufa inda ta ga yara na siyan abubuwa.
Tana zuwa ta mika kudin tana abani, "fanke."
Tsayawa kallon ta matar tayi domin ita bata fahimci me take fadi ba.
Da salma ta ga haka ta ja robar fanken ta ce, "ki bani wannan fanken guda uku."
Sai a lokacin ta gane ta zuba mata uku a leda sannan ta bata canjin dari biyu dake dari dari ne.
Salma na karba ta baje school compound .
Gabadaya ta wage jiki kamar an aje kayan dauda.
Ta sa bakinta ta bude coke din, ta fara cin fanken tana hadawa da coke din hankalinta kwance tana waƙa.
Sauran student din sai binta da kallo suke tamkar tv.
Wata ta zo wucewa tana kallonta.
Bakinta cike fal ta fara galla mata harara tana, "ke dilla ya da kallo? Na ci tuwon gidankune ban wanke kwano ba? To mijina ne ya bani kudin tara na siya ehee kwadayayya kawai." Ta kara galla mata harara.
Tsayawa yarinyar tayi tana mata kallon tara saura kwata ta ce, "villege girl."
Salma bata fahimta ba ta ci gaba da zakan coke da fankenta.
Sauran kawayen yarinyar ne suka hadu su biyar suna kallonta suna dariya suna fadin villege girl.
Daya a cikinsu ta ce, "She's not getting it, she only speaks hausa, so let's switch langauges."
Suka fara fadin, " 'Yar Kauye kawai , katuwar banza ji beta ta wani baje tana shan coke."
Salma na jin jawabansu ta tashi ta ajiye coke din da sauran fanken gefe ta cire karamin dankwalin dake kanta ta daura a ƙugunta ta ce, "ni kuke cewa yar kauye? Ni kuke cewa wawiya?"
Nunata da hannu suka yi suna dariya, "e din wawiya yar kauye ka....
Kafin su karasa rufe baki Salma tayi kansu gabadaya dukansu take ta ko ina ba ji ba gani gasu su biyar ita daya amman ta gagare su.
Da gudu sauran yaran dake gefe suka kira displine master din school din.
Aiko dakyar ya kwacesu a hannun salma.
Daga mai fasasshen baki sai masu kumburarren goshi duk ya yi ƙulu rudu rudu domin dukansu take ta ko ina harda wacce ta ciza kumatu.
Sai numfarfashi take tana fadin, "ba ku kun iya raini ba? Iye ku kun iya raini? Ance muku ni sa'ar kuce? Mijine dani e mijine dani."
Sai da displine master din ya zabga mata bulala kafin ta yi shiru tana cuno baki tana sosa baya.
Kamar bakin ya mutu sai kuma ta ci gaba da sambatu, "gaba kwa kuma waya ce muku ni ana kawo mun wargi wallahi zan balballa yarane gida saba in ba tara, ni ba sa'ar wasanku bace ko a kauye ma ni ba saar yara bace bare nan."
Kallonta displine master din ya yi ya ce, "After all this nonsense you've done, you should be ashamed to speak further. You ought to be more reflective,Oyaa get on your knees."
Kura masa ido ta yi tana kallonsa, kafin ta ce , "ni kuma? ni na yi me? Su fa suka rainani ni ban kulasu ba cin kayan dadina nake kawai suka fara tsokanata."
Dafe kai ya yi, ya ce, "ki durkusa akan gwiwarki yanzu nan zaki dauki hukunci."
Salma ta zare ido , "cab hukunci? Hukunco aradun Allah ba mai dukana kuma naki dukawa kan gwiwar."
Kara zabga mata dorinar hannunsa ya yi da ta saki wani sauti sai da ya karade School din.
Jin hayaniya tayi yawa yasa Saheer saurin fitowa.
Salma ya gani tsaye tana rike da baya tana bambami ga sauran student mata biyar jina jina sun bugu wata har bakinta ya kumbura mai kumatu ma ya yi combis haka ma goshi sai kyalle yake na azaba.
Yana zuwa Salma da gudu ta koma bayan shi ta tsaya tana rike shi, "mijin wallahi su suka raina ni yaran can kuma ka ce musu ni matar aure ce,kuma kai ne mi......
Kafin ta karasa ya mata wata irin gigitacciyar tsawar da sai da ta razana.
Ya ce.....
Saura page daya free pages su kare maza hanzarta ki fara biyan naki domin har yanzu ba a fara asalin wasan ba😻 shagali na gaba.
500 ne kacal
8103080717
Aisha Abdullahi Sani
Opay
Or
1453215759
Aisha Abdullahi Sani
Access Bank
Evidence of payment to
08103080717
[7/1, 8:43 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*
PAGE-8
"Ki mun shiru kar in kara jin bakinki anan gurin."
Salma ta cuna baki tana un uni kasa-kasa.
Saheer ya ce, "Oya ka daukesu aje ayi ma wajen da suka ji ciwo dressing in an gama kuma su zo office su sameni."
Salma dai tanata magana kasa-kasa , "aradun Allah yara suka ƙara rainani sai na ci musu mutunci marasa karfin banza da wofi kawai."
Jan hannunta Saheer ya yi ya shiga da ita office dinsa sai da ya rufe kofar kafin ya rike bakinta da hannu, "kin ga wallahi in kika kara cemun wani mijin ko miji a cikin makarantar nan sai na yanke miki baki sai na farfasa miki shi ya yi caɓa-caɓa."
Kokarin fara bude baki ta cijeshi tayi ya yi saurin sake mata bakin.
Murgudawa ta yi kafin ta ce, "to karya na yi? Ai ba karya na yi ba kai mijina ne ko kaƙi ko kaso ehee kai mijina ne mijin Saheeru mijin Salma e."
Ta fada tana juya jiki.
Ganin ya ciro wata dorina yana fadin , "au ba za ki daina din ba kenan ko?"
Da gudu ta bude kofar office din ta fice tana, "ai ba karya nake fada ba bare ace ba kyau indaina."
Ta wuce class abunta.
Tsaki Saheer ya yi ya koma ya zauna.
Lokacin tashi kuwa na yi da gudu ta koma office din tana fadin, "an tashi,ka zo mu tafi gida mi...."
Kallon da ya bita da shi ne yasata yin shirun dole ta tsaya tana murmurguda baki tana wurgi da hannu.
Keyn motarshi ya dauka yana, "daga yau ba tare zamuna zuwa ba da kafafunki zakina zuwa school dinnan kuma kar ma ki kara nuna kin sanni."
Taɓe baki ta yi , "unm oho ohon maka dai."
Ta bi bayanshi ta shige motar ta zauna.
Da sauri ya janye motar ya bar School din domin bai son kowa ya fahimci tare suke.
Aiko suna zuwa gidan ta baje a falo zata yi kuka, "yunwa nake ji ni wallahi,yunwa nake ji."
Ji ya yi kamar bai san me take fadi ba ya wuce cikin daki ya shiga toilet.
Ta bi bayanshi tana zuwa ta bankada toilet din ya tuɓe wando kenan zaiyi fitsari.
Idonta idon jikinsa.
Wata kara ta sake tana rufe baki da hannu.
"Na shiga uku na mutu na lalace kai kuma naka abun macijine zabgege ashe." Sambatu ta fara barkate kuma tana tsaye ta kura masa ido taki tafiya.
Cikin fushi ya tura kofar sai da ya buga mata goshi.
Ta rike goshin tana tsaye agun, "mugu kawai mai maciji aradun Allah sai na rama ji zaka fasa mun goshi."
Gaban mirror taje tana kallon goshinta.
Kwafa ta yi ta ce, "kyakkyawa dani yana son ya cuceni ya bata mun fuska,zan yi maganinka ysn."
Man shafawa ta dauka taje daidai tais din dake bakin toilet din inda yana fitowa zai fara takawa a hankali ta shafa man.
Sai da ta tabbatar ta shafa yadda mutum na takawa santsi zai ja shi ya fadi kafin simi simi ta fice a dakin ta tsaya a bakin kofar tana leƙe.
Aiko yana fitowa da santsi ya ja shi ya yi wata irin sulewa sai ga kanshi a gefen gado ya bugu daram.
Har cikin ranshi yaji wata irin azaba na ratsa shi yana sa hannunshi a goshi ya ji kamar an daura masa wani tulu.
Salma mai zata yi ban da dariya harda rike ciki.
Musamman da ya tashi ta ga goshin shi ya kumbura har tana birgima a kasa.
"Wayyo ni da fatanya sunan wani abu, ji kai har wani sheƙi yake kamar naman akuya wayyo cikina,maganin mutum ai kenan in dai mutum ya ce shi mugu ne zai ga mugunta."
Saheer bai kulata ba har sai da ya kalli kanshi a madubi.
Lokaci gudu yanayin kamaninsa har ya canja goshi ya kumbura sintim.
Yana kallonta ta kara shekewa da dariya.
Binta ya yi a guje ita ma ta fara gudu......
*Da dai na so in tsaya da free pages 8 Dinnan amman yanzu saura 2 pages zamu kai page 10 In sha Allah a hanzarta a gama payment masoyan asali nice matar Hedimastan ga fa ko kun daina kaunata ne ban sani ba? Inga ruwan alert mussaman Xh Narrative Nest members*😻😂
MATAR HEDIMASTA
500 ne kacal
8103080717
Aisha Abdullahi Sani
Opay
Or
1453215759
Aisha Abdullahi Sani
Access Bank
Evidence of payment to
08103080717
[7/2, 12:57 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*
PAGE-9
Haka suka dunga zagaye gidan daga ciki har waje, ko a jikinta ganin tana kokarin mai da shi karamin mahaukaci karfi da ya ya kyaleta yana numfarfashi ya koma daki.
Kwanciya ya yi akan gado ban da haki babu abun da yake yi,ga azaban da goshin sa ke yi masa, ga shi kuma sai ƙulu yake karawa kamar wanda ake sawa yeast.
Ya rasa meke masa dadi,kwanciyar ma ya gagara,ya kwanta ya kifa kai, ya tashi ya juya yana kallon sama,ya koma gefe shi kadai dai yasan abun da yake ji ya rasa ina zai sa kanshi ya ji dadi.
A karshe wani barcin azaba ne ya dibesa ba tare da ya ankare ba.
Ita kuwa Salma kitchen ta shiga dake ta iya kunna gas caraf ta kunna
Tana, "mutum na jin yunwa baza a bashi abinci ba,dadinta ma ai nima na iya girkin yi zan inci in koshi abuna."
Ruwa ta fara zubawa a tukunyar sannan ta dibo shinkafa ta ko aunawa batai ba ta zuba.
Sauran man gyadan da ya dafa indomie da shi ta kwashe ta zuba a ciki.
Sauran magin indomie dinma ta dauka tana, "bara muji wannaan kuma mene ne." Ta zuba a hannunta kafin ta lashe a baki, dariya ta fara tana, "aradun Allah dandanon girki ne, ji kamar madara madara." Ta juyeshi kaf a cikin shinkafar ta dauki ludayi ta juya,ta juya shi sosai kafin ta rufe ta fita falo tana, "umm kafin abincin ya yi bara inyi kallona ma."
Bai fi minti daya ba taje ta kara dubawa ta diba ruwan ta dandana , "umm da saura gaskiya amman shinkafar nan zata yi dadi sosai."
Ta kara rufewa kafin ta koma falon ta ci gaba da kallo.
Tana cikin kallo barci ya sace ta.
Abinci tun yana yi a hankali har ruwa ya tsotse ya fara konewa.
Har hayaki da ƙauri ya fara karade kitchen din da falon tana ta sharban barcinta ko a jikinta.
Saheer na barci kamar ance ya farka ya fara jiyo wani irin hayaƙi.
Da sauri ya tashi aiko yana zuwa har kitchen din ma ya gama karadewa da hayaki ya cika fal.
Da sauri ya kashe gas din yana toshe hanci ban da tari babu abun da yake saboda ya riga ya shaƙi hayakin, Salma har lokacin bata san meke wakana ba barcinta take harda gwarti.
Sai da ya daidaici daidai duwawunta ya maka mata duka, a zubure ta farka ta zata fara masifa kuma da ta kalleshi ta kalli goshinsa bata san lokacin da ta fashe da wata irin makirar dariyar mugunta ba.
Ƙara kula ya yi ya ce, "wai ke duk bayan mintuna shashancin naki karuwa yake? Ki daura abinci ki zo nan ki wage baki kina barci? Da yanzu kin ja mana gobara fa."
Sai a lokacin ta tuna da da abincinta.
"Innalillahi wayyo abincina." Ta fada tana wucewa ta gefensa ba tare da ta kula shi ba.
Tana zuwa ta sa hannu ta jefar da murfin tukunyar saboda zafi sannan tasa zaninta ta sauke tukunyar gabadaya ya kone yyi baki sai dan kadan a tsakiyan tukunyar da bazai wuce cokali goma ba.
Bajewa ta yi a kasa kitchen din ta ja tukunyar gabanta tana kuka tana ci, "Ban da mugunta ace abar abincin mutum ya kone baza ana duba masa ba, wannan ai mugunta ne da son zuciya kuma aradun Allah sai na ci sai dai bakin ciki ya kashe mutum."
Don takaici kasa kulata Saheer ya yi kawai ya zauna a falon ya yi tagumi.
Shima wata azababbiyar yunwa ya fara ji gashi bazai iya shiga kitchen din ya yi girki ba.
Tashi ya yi kawai ya fice masallaci ya fara zuwa ya yi sallah sannan ya wuce 3D Resturent ya ci abinci har ya fito kuma