Showing 6001 words to 9000 words out of 13942 words

Chapter 3 - FARAR HAIHUWA Part1 by Batul Mamman

19 May 2026

30

dake. Ta sunkuyar da
kanta kasa nasan wanda ya mutu baya dawowa amma inda hali a saka mata Ramlah.
Murmushinsa ya fadada dama haka naso ina dai tsoron yi miki fami ne. Allah Ya raya
mana ita. Tace amin. Uwale dake bakin kofar dakin ita da Zulai wanda dama gulma
suka zo ji ta shigo tana matsar kwalla. Yanzu dan nan ko kara bazaka min ba kasa
sunana sai zabin matarka. Inna ke fa kika ce ba kya so tun a haihuwar marigayiya.
Akan Hanan ma kika sake cewa bakya so kika zaba mata wanan sunan. Ta dan fito da
ido ni dan nan? Abin harda sharri? To ba damuwa ka saka mata sunan da kake so. Tana
juyawa zata fita Munari tace haba Inna kiyi hakuri sunanki za'a saka mata. Ba haka
inna uwale taso ba, so tayi Munari ta ce bata son sunan sai ta hadasu fada da
Yakubu. Tsaki tayi ta fice Zulai na rufa mata baya. Duk da abin baiyiwa munari
dadi ba sai ta nuna wa Mal Yakubu jindadinta sosai.

Ranar suna aka radawa yarinya suna Khadija. wata yar uwar baban Mal yakubu ce tazo
ta karbi jaririyar wanzami yazo za'a cire mata beli. Uwale ta gama lura da yadda
munari ke matukar kaunar jaririyarta sai ta fita wurin wanzamin tare da waziriyarta
zulai. Basu dade da fita ba aka jiyo sautin kukan Khadija da katuwar murya kamar
zata shide. Mata an sami abinyi suka yo soro da gudu. Tani ce kan gaba tana zuwa ta
tarar uwale ta kwaye gefen fuskarta wanzan yana kallon kalangunta ya fara zanawa
jaririya a gefen fuskarta na dama. Fizgota Tani tayi ta koma cikin gidan da sauri.
Munari ta karbeta zata bata nono amma taki karba sai wani irin kuka take. Har dakin
Uwale ta biyosu. Amma Tani baki da ta ido. Yanzu nace ayiwa yarinya kalangu zanen
fulani irin nawa shine zaki dauketa. Munari tana hawaye tace yanzu Inna duk gidan
nan wa aka taba yiwa zane a fuska shine zaki ce ayi mata. Au kema rashin kunyar
zaki min? Bani ita a karasa mun barshi a zaune. Munari tasa zani ta goya yarta tana
ta kuka. Wallahi Inna idan kinga anyi wa yarinyar nan zane a fuskarta to mutuwa
nayi. Ya kike so nayi da raina ne? Matsalar yau daban ta gobe daban. Allah bari Mal
ya dawo idan mutuwar aurena ce tazo sai dai na tafi da yata. Zanen nan fa Allah Ya
tsinewa maiyi da wanda akeyiwa. Kuka wiwi Uwale tasa ita a dole anyi mata rashin
kunya. Nufinki Allah Ya tsine min ko? To yau zanga wanda dan nan zai zaba cikin mu
biyu.

Daga gefe wasu mata suka ce gidan uwale duk taron suna sai anyi dirama. Ai munari
ta kyautawa kanta yau.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:09 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰11



Wasa wasa har magariba ta gabato ana ta mayar da zance a gidan Mal Yakubu. Shi dai
tun a kofar gida da labari ya riske shi komawa yayi ya kira wan babansa Baba Hadi.

A tsakar gidan ya tarar dasu gaba daya da sauran mata 'yan jin kwakwaf. Baba Hadi
na shigowa yace duk su fice su bar gidan. Sum sum suka rinka fita daya bayan daya.
Ba dai haka aka so ba don sun so jin yadda zata kaya aji dadin ba da labari. Suna
fita Inna Uwale cikin kuka take labarta masa abinda ya faru. Baba Hadi yace ba
matsala ke Munari bani yar . Ba musu ta mika masa jaririyar bayanta. Yace to Yakubu
karbo yayarta ya nuna Hanan dake hannun Sabuwa. Bari na sa Yau ya kira wanzamin duk
sai ayi musu. Shima Sadi idan suka zo gari sai a karbo shi a yi masa. Uwale ta
wurgo kafa cikin sauri bangane ba Yaya Hadi wai harda Hannan za'ayi wa? Eh ya amsa
a takaice. Dukkansu ba jikokinki bane? Tayi tsuru tsuru da ido...anya ayi harda
ita? Sabuwa ta ce Al-Quran ba za ayi mata ba. Mal bani 'yata. Baba hadi yace au ita
wannan da baki isa da uwarta ba shine zaki ce kada ayi mata, amma ita munari ko
kadan baki damu da lamarinta ba? To wallahi ki fita idona Uwale. Akan yadda kike
takurawa matar yaron nan zan nuna miki ni ba marigayi bane. Shine yake jure halinki
na tsiya. Kai ta sunkuyar kasa bata ce uffan ba. Ya mikawa munari yarta. Ki kara
hakuri kinji Maimunatu. Allah Ya raya muku yaranku. Tana ta godiya ya fita Mal ya
raka shi.

Tun daga lokacin uwale ta kara kunnawa Munari karan tsana. Duk lokacin da Mal
Yakubu ya fita sai wulakanci kala kala. A can birni kuwa Yaya Salihu yasa Sadi a
makaranta tare da yaransa. Lokacin da Ummita ta shiga wata na ashirin da haihuwa
Munari tayi shirin yayeta. Wata rana tana kwasar tuwo Ummita tana ta zillo a
bayanta. Tace haba mamana so kike na kona hannu ne? Uwale wadda tuni zulai ta bata
shawarar yadda zata kori munari daga gidanta ta daga waje ni kuwa munari kin fiye
kinibibi yaushe ta zama mamanki. Na zata sunan uwarki Baraatu. Munari tayi murmushi
Inna ai kema uwata ce. To indai haka ne daga yau tunda dai nike da iko da kowa a
gidan nan yarinyar nan zaa rinka kiranta Dijengala. Ni na tsani suna Ummita dinnan.
Gara dai a kirata dijengala a gargajiyance. Munari tace to ba komai inna ai yadda
kike so haka zaayi. Ba haka inna uwale taso ji don fada tazo takala. Sabuwa ta fito
daga dakinta tace inna kinji da yadda ta amsa miki kuwa? Ai gatse tayi miki. Allah
Ya kyauta uwar miji ace bata isa da surukarta ba. Ni kina ji ai sanda ta sawa tawa
yar suna. Wannan ma idan na haife ita zata sa suna.

Munari dai bata kula ba don tasan neman rigimar tasu ne ya tashi. Da Uwale taga
haka zama tayi a wurin sai da mal yakubu taji sallamarsa tasa kuka. Karya da
gaskiya ta rinka hada masa Sabuwa na mara mata baya. Ganin ko kadan bai yarda ba
tace kai na gaji so nake indai ba tare na haife ku ba ka saketa ta koma gidan
ubanta. Munari ta soma hawaye tana bata hakuri. Ta tabe baki kyayi kya gama. Yau
abincinki ya kare a gidan nan. Idan baka saketa ba yanzu a gabana ba wallahi sai na
tsine maka albarka. Haba inna ya kike so nayi ne? Babu abinda kike nema da bana
miki. Don Allah kiyi hakuri. Itama kukan tasa masa idan baka saketa ba Allah Yakubu
zan maka mugun baki. Naki jinin bakar matar nan. Ka saketa yanzu.

Munari tace mal idan kana son gamawa da duniya lafiya kabi umarnin Inna. Yana kuka
tanayi yace na sakeki saki daya. Wani kukan ne ya zo mata da karfi ta shiga daki
dauko mayafi. Inna don ta kara kuntata mata tace kwanto goyon ai ba dashi kika zo
ba. Dama yar ta isa yaye. Munari ta kalli mal yakubu yace Inna don Allah. .hannu ta
daga Allah Ya tsi....da sauri munari ta kwanto yar da take matukar so ta bashi ta
fita daga gidan cikin kuka.



Batul Mamman💖
[8/22, 3:10 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰13



Da gudu ta karasa don yau akan wannan yar Mal yakubu yana iya karairaya ta. Tana
dagota wani irin tari ta rinka yi har uwale ta jiyo su ta fito. To 'yar nema zaki
fara sanaar tarin ne....kai lafiya sabuwa me ya faru? Wallahi Inna bansani ba. A
cikin robar wanka na ganta. Na shiga uku na yau a gidan nan. Ba kuka zakiyi ba
dauko gyalenki mu kaita kemis. Kila ruwa ta shaqa. Su 'ya'yan munari kamar kifaye
kowa ya tashi mutuwa sai ya tsumbula ruwa.

Basu tarar da mai kemis ba dole suka wuce asibiti. A nan Mal Yakubu ya hadu dasu
bayan dan aiken su inna ya riske shi. Likita yace gaskiya Mal akwai ganganci a tare
daku. Yarinyar nan ba karamin kamu sanyi yayi mata ba tun kafin yau. Sannan idan ta
tashi za'a sake yi mata wasu gwaje gwajen amma gaskiya a yadda na fahimta
kunnuwanta sun tabu. Da kyar zata ji kamar da. Shi kam mal yakubu sarkin hawaye har
ya fara. Sabuwa taci fada don ma inna ta tsaya mata ne. Karshe yace idan ta sake
bari wani abu ya sami yarsa sakinta zaiyi ya hadata da hukuma.

Labarin abinda ya sami Dijengala ya sami su Inno. Hanawa sukayi a sanar da munari
son kada tace zata taho tunda ta fara karatu a wata makarantar addini. Inna Ladi da
ce taje gidan ta bukaci a basu ita tunda basa sonta. Bayan doguwar muhawara tace su
jira shammaci daga kotu. Wannan kalami nata na karshe ne yasa Zulai ta bawa Uwale
shawarar suje wurin wani malami a dauke musu hankali daga kan Dije. Anya ayi haka
Zulai? Nifa gaskiya bana son inyi shirka. Haba Uwale malami ne fa ba boka ba. Ai
irin malaman nan ba bokaye bane, suna da ilimin islama gashi idan kika je zaki ga
littattafai da carbi kala kala. Sannan idan kika bari aka shiga kotu daurin shekaru
zasu yi miki duk da tsufanki da yar kafarki. Tuni Uwale ta tsorata .A haka ta ja
raayin Uwale suka je wurin malamin. Bukatarsu biyu ce. Mal Yakubu yaso Sabuwa ya
hakura da abinda ya faru sannan Munari da 'yan uwanta a dauke musu hankali daga kan
Dije da zancen zuwa kotun nan. Ya kasance munari ta manta ma da yar tata gaba daya.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:11 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰12



Cikin kuka ta shiga gidansu da sallama. Inna Ladi ta ajiye butar hannunta ta taro
ta. Me ya faru Munari? Ta shafa bayanta taji ba goyo. Ina 'yar? Ba dai ta mutu ba.
Munari ta kasa magana sai kuka. Inno tace wai ba magana ake miki ba. Inna ya
sakeni, inna uwale tace idan bai sakeni ba zata tsine masa. Innalillahi wa inna
ilaihi raji'un. Ita kuwa Uwale tana son gamawa da duniya lafiya? Ina ruwanta da
zaman ku inji Inna Ladi. Inno dama bata saka baki a lamarin gidan yarta saboda kara
amma yau bakinciki ya isheta. An sako mata 'ya da magaribar fari. Tace ina goyon.
Munari ta sake fashewa da kuka tace ba dashi nazo ba. Inno tace Alhandulillahi in
anyi duniya don Manzon Allah SAW kin bar gidan Yakubu har abada. Saurin dago kai
tayi haba Inno wallahi ba da son ranshi bane. Na dai fada miki...munari ba fa
sadakarki aka bani ba. Haihuwarki nayi kamar kowanne da. Kyautace Allah Ya bani to
nayi hakurin da zanyi Allah Ya yanke miki wahala. Inna Ladi tace hakane amma kada
muyi saurin yanke hukunci.

Sallama suka ji daga waje. Inna Ladi ta amsa don ta gane mai muryar tare da yi masa
izinin shigowa. Yana shiga gidan ya zube a kasa yana basu hakuri. Inno tace ai ni
so nake ka cike mata sakin gabadaya. Inno kiyi hakuri don girman Allah. Zan kama
mata gida sai na mayar da ita can. Kaga tun ina ganin mutumci da kimarka ka bar
gidan nan kafin ayi abun kunya. Yadda Uwale ta karbi Ummita to zan aikawa Yayansu
ya dawo maka da danka. A'a inno na bar masa ki dena maganar nan don Allah. Ya kalli
Inna ladi ki bata hakuri, ko kula shi bata yi ba taja hannun munari tana tirjewa
cikin dakinta. Haka ya gaji da zama ya koma gida.

Washegari kafin azahar Inna Ladi ta aika Tani tazo da mai binta Shafa suka raka
Munari birni gidan Salihu bisa umarnin iyayensu.

Haka Dijengala inji kakarta uwale ta tashi cikin kuncin rayuwa da wahala.
Mahaifinta ne kadai gatanta. Tana da shekara biyu Sabuwa ta kara haihuwa. Dama ba
wata kulawa Digengala ke samu ba hatta wanka sai babanta ya matsa ake yi mata.
Watarana ya fita da sassafe Sabuwa ta kai ruwa bandaki a katuwar roba ta kira Hanan
da Dijengala tayi musu wanka. Tana gamawa yarta tace muje in shafa miki mai
tukunna. Dije wadda aka yiwa tsirara sai rawar dari take saboda sanyi tace Mama
nima wanka. Wani mari Sabuwa ta gaura mata ta dauki yarta suka fita. Dije tana kuka
ta taka sabulu ta zame ta fada cikin robar ruwan. Sai da sabuwa ta gama shirya
Hanan bayan kusan minti goma ta dawo ta tarar da Dijengala ta kusa shidewa a robar
ruwa.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:11 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰14




BAYAN SHEKARA 17

Cikin daga murya irin na wadanda basa ji sosai tace Inna ina kwana? Uwale ta sha
kunu matsa can ni kada ki tofe ni da yawo kinzo kina min ihu a ka. Dijengala tace
naam? Alamun bata ji abinda kakarta ta fada ba. Tsaki Uwale tayi tare da daga hannu
lafiya nace. Murmushi tayi wanda yake kara mata kyau tace au banji ba ne. Dama ai
ba jin kike ba. Ta sake daga hannu tashi ki bani wuri. To..to..to ta mike ta koma
dakin su ita da Hanan da kanwarsu Zaliha.

Wata yaloluwar katifa ta nufa ta kwanta. A hankali idanunta suka ciko da hawaye.
Ita meyasa bata da Umma? Ina dangin ummanta suke? Hawayen ne suka gangaro sai tari
ya sarke ta. Zaliha ce ta ganta bayan ta dawo daga makaranta. Yaya Dije sannu ta
dafe mata kirji. don idan ta fara tarin numfashinta har neman daukewa yake. Rashin
kudi sosai yasa Babanta ke yawo da ita gidan masu maganin gargajiya, wasu suce
sanyi wasu suce asma. Zaliha ta dago kan dije ta bata ruwa bayan tarin ya lafa. Ta
daga murya Yaya Dije kuka kika yi ko? Tayi saurin girgiza kai tari ne Zaliha. Allah
Yasa da gaske kike, bari naje na dauko mana abinci nasan yunwa kike ji ma.

Haka dokar Sabuwa ta koma abincin Hanan daban, Zaliha da Dije tare ake hada musu.
Tunda Dije ta gama secondary school wadda ba wani abin kirki ta iya ba saboda
rashin kunne kullum sai ta jira Zaliha ta dawo zasu ci. A cewar sabuwa kada dije ta
cinye abincin. Babansu bai taba sanin wannan dokar ba don har yanzu yana so da kula
da lamuran yarsa. Shekararsu goma sha biyar da baro kauyensu suka koma birni da
zama. Takurawar iyayen Munari kan sai an basu Dije yasa Uwale sayar da filayenta
harda gidansu ta matsa masa sai sun tashi indai ba so yake ya kulleta a gidan yari
ba. Tayi mamakin yadda aikin malam bai kama su ba sai dai kuma bata kara jin
duriyar Munari ba tunda tasa Yakubu ya saketa. Aikin gini da noma yake yi a haka
yake ciyar da iyalinsa yake saka su a makarantar gwamnati. Tun tafiyarsu wadda basu
yiwa kowa sallama ba iyayen Munari suka sanar da ita duk abinda ya faru. Tayi kuka
sosai saboda tana matukar son 'yarta kuma ta kara tsanar Yakubu akan guduwa da yayi
da ita. Allah Yasa ma Sadi yana wurinta.

Hanan ta fara karatu a polytechnique ta garin kano tana ji da kyau da gayu. Duk
gidansu babu wanda take so kamar kakarta Uwale saboda yadda take shagwabata tana
kuranta kyaunta. Duk yar yaudarar samarin da take da izinin kakarta take yi. Tana
kwance kan gadon uwale tana chatting Mal Yakubu ya shigo dakin. Wani wuntsulowa
tayi da sauri zat gudu. Hannunta ya rike ya dawo da ita dakin munafuka ina zuwa. Ya
zaka kirata munafuka dan nan ka kiyayeni fa akan Hannan wallahi. Inna kina bata
yarinyar fa. Kalli wayar hannunta abinda take saurin boyewa kenan kada na gani.
Uwale tayi murmushi zancen banza ai kudin dashi na na bata ta siya dashi. Hanan
tace Allah Baba ita ta bani.bari saurin rantsuwa ni tsakanina daku shawara ce. Iya
abinda zanyi miki nayi na tarbiya. Allah Ya shirya.
Ficewa yayi rai a bace ya tafi dakin yaran wurin Dije da Zaliha. Baba sannu da
zuwa...yauwa Zulaihatu. Taba min yayarki nasan bata ji shigowata ba. Tsinkin
tsintsiya Zaliha ta sawa Dijengala a kafa ta mike a firgice. Wayyo Allah...muryarta
duk ta cika gidan. Tana ganin babanta ta matsa kusa dashi. Baba kaga Zaliha
ko...zan zane ta fa. Guje guje suka rinka yi a tsakar gidan yana dariya. Yaran nan
biyu kadai ne suke wanke masa bacin ransa da damuwa. Sune kuma Uwale bata so don
abin mamaki duk farin Sabuwa haka ta haifo Zaliha baka har tafi Dije duhu. Shiyasa
uwale bata shiga sabgarsu kamar babu su a gida.




Batul Mamman💖
[8/22, 3:12 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰15




Ranka ya dade ga takardun filayen guda uku aka samu a wuri daya. Alh Sulaiman
Hassan ya kalli sakatarensa Modibbo nagode dan fillo. Zanyi magana da managers din
sauran kamfanin sai muyi finalising project din. Modibbo yace hakan yayi ranka ya
dade amma akwai sako daga wurin Hajiya fa. Murmushi yayi alamun yasan sakon Hajiyar
yace nasan cewa tayi ka tabbatar yau na tashi da wuri ko? Shima Modibbo murmushin
yayi ni dai umarni nake bi kuma lokaci ya riga yayi. Wai ni waye ke biyanka ne ni
ko ita? Ai Alhaji da kai da kaya duk mallakar wuya ne. To naji ya fada tare da
mikewa.

A hankali yake tuki don yau drebansa bai zo ba matarsa ta haihu. Karatun Al-Quran
yake ji kira'ar Sheik Khaleel Husary yana bi cikin nutsuwa har ya isa gidansa a
unguwar bompai ta cikin garin kano.

A falo ya tarar da ita ta gama hade rai alamun tana fushi dashi. Mata ne biyu zaune
tare da ita. ko da ya gaisheta da kyar ta amsa masa shima yasan yayi laifi bai
matsa mata ba yayi hanyar bene tace cikin fushi Sulaiman ina zaka je kuma? Umma zan
canja kaya ne na dawo. To kayi sauri yaran kawata ne suka zo gaisheni shine nace su
jira kazo ku gaisa. To kawai yace a ransa kuwa harda dariya...umma kenan ta zama
matchmaker karfi da yaji ita a dole sai yayi aure a wannan shekarar. Shima kullum
yana adduar samun ta gari yasan kuma Allah mai jin rokon bayinSa ne.

Wanka yayi yasa kananan kaya ya sauko. Yana zama Umma ta mike to bari na duba
abinda ake dafawa. Yasan so take ta basu wuri ya ce to kawai. Tana tashi dayar
wadda take ta yi masa kirikiri da ido tace Yayanmu ni sunana Ainau wannan kuma
kanwata ce Bilkisu. Ko kallonsu baiyi ba don basu yi kama da masu kunya ba ya zaro
kudi a aljihunsa ya mika musu ga kudin mota nice meeting you. Sai anjima muje nasa
dreban Umma ya kaiku gida. Ainau ta bata rai ai Hajiya tace mu jira zaka kaimu da
kanka idan ka dawo saboda kaga gidan. Ashe ma doluwa ce yarinyar ya fada a ransa.
Kinga naji ciwo a hannun bari a kaiku. Bani number dinki zan kiraki musamman.
Kanwar tace nifa? Itama karbar tata yayi yana so suyi su fita kafin Umma ta dawo.
Sai da yaga fitar motar daga gate din gidan ya dawo ya zauna. Muryar ummansa yaji
tace Sulaiman ina su Ainaun suke. Ai sun tafi wai sauri suke yi...amma yaron nan
baka da kirki. Wai so kake na mutu banga jika na ba shekarunka talatin da shida
fa...jin ta fara shakar hanci yasan kukan blackmail ne ya tashi. Kiyi hakuri Ummana
na sami mata ina jira mu gama daidaitawa ne. Ta washe baki hakoran makkanta suka
bayyana. Da gaske Sulaiman? Da gaske Umma..to ai da kayi magana da wuri bazan kira
yaran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login