Showing 12001 words to 13942 words out of 13942 words
Dama
can ba sa'an auren yarsa bane shima don yaga kamar auren zai hanata yawo ne.
Alh Sulaiman yana mamakin yadda duk lokacin da yaje baya samun Hanan kullum sai ace
masa bata nan, gashi Umma duk ta kwallafa rai. Shi kanshi yana son ya kara ganin
kyakkyawar fuskar Hanan din. Yarinyar akwai class. Yana dawowa daga office ya
shirya ya tafi gidansu da yamma. kila don saboda zuwan dare yake shiyasa baya
samunta. Yau tararta zaiyi kafin ta fita. Yana tuki Dijengala ta fado masa a rai.
Shi kadai yayi murmushi Allah Yasa itama na sameta...a ransa har ya gama shawarar
idan yau auri hanan zai ce ta taho da kanwar tata.
Yau ma can baya ta ajiye motarsa. Sabuwar benz ce da masu kudi ke yayi ya shigo
lokon a kafa. Farin yadi ne a jikinsa mai bula bula. Wandon da shafi amma babu a
rigar, ana ganin farar vest din dake ciki. Takalminsa da hula duk ruwan toka ne.
Yayi kyau sai kamshi ke tashi duk inda ya wuce. Bai ankara ba yazo daidai kwatar
kofar gidan Mal Yakubu yaji an kwala ihu sai ruwan kwata ya gani ya fallatso masa
ko ta ina a jikin kayansa harda gefen fuskarsa. Ransa ya gama baci sosai saboda shi
mutum ne mai matukar kyankyami. Dijengala ya gani kafarta daya a cikin kwatar babu
ko mayafi a jikinta tana kuka. Ganinsa a tsaye yasa kukan ya karu ta soma bashi
hakuri da karfi. Don Allah kayi hakuri ban sani ba. Inna ce ta biyoni da bulalar
doki. Kafin yayi magana wata dattijuwa ta fito daga gidan da ke kusa dana su Dije.
Daga murya tayi yadda Digen zata ji...me ya faru Digengala? Ta sake wani sabon
kukan sannan ta fita daga kwatar ta karasa wurin matar. Gwaggo, Inna ce tace yau
bazanci abinci ba sai na debo ruwa bokiti goma. Kuma fa na debo shida amma yunwa
nake ji. Tace na sa baba yaki siyo ruwa saboda sun hanani na wanka jiya daya fita.
Gwaggo taja hannunta kiyi hakuri kinji yar albarka shigo kici abinci kiyi wankan.
Ta kalli Sulaiman wanda ya zuba musu ido. Alhaji shigo kaima kuma kayi hakuri.
Ya kalli tsohuwar ba damuwa? Haba yaro ni da 'ya'yana biyar ne a gidan nan babu
mace ko daya sai matar babban. Kazo ka dan gyara jikinka. Suna shiga daga bakin
kofa ya tsaya aka bashi buta ya dauraye kafarsa yana ta dage hanci. Kadan ya rage
burinsa ya koma gida kawai. Yana ta kallon yadda Dije ke cin abinci da sauri da
sauri. Yace don Allah ina da tambaya gwaggo. Ina jinka ta amsa. Wai ita yarinyar
nan wace ce ita? Kamar jira take ta bashi labarin duk abinda ta sani game da
Dijengala da wahalar da Sabuwa da uwale ke bata. Sosai ya tausaya mata bata da wata
damuwa sai ya cikinta. Yayi godiya zai fita Gwaggo tana yiwa Dije waka. Dijengala
ta maigari, ba auren talaka ba. Yana bakin kofa suka ji ance sai auren musaki ba,
kurma irinta.
Inna Uwale ce ta hau kan wata katuwar bambu ta ruwa da aka kifa daga gidanta.
Sabuwa ta riketa ta tsaya don kar ta fada ta leko ta katangar da ta hada gidanta
dana gwaggo. Sulaiman har dan tsorata yayi sai kuma ya tsaya yana jin tijara irinta
Uwale. Dije tuni ta tashi daya kan kwanon tuwon ta koma bayan gwaggo ta buya. Zaki
shigo gidan ki same ni ne 'yar banzar yarinya, waye bawanki da zai debo ruwan.
Gwaggo tace Ke dai Uwale kinji kunya wallahi...idan zaki shekara kina nunawa
yarinyar nan tsana bazaki taba canjawa kanki suna a matsayin kakarta ba. Kuma
wallahi idan kika sake min leqe da wannan shanyayyar kafar taki sai na tsire miki
idanu. Cikin fushi tace ni kike fadawa haka...wallahi zan hadaki da hukuma su shiga
tsakaninmu. Makotaka ai ba hauka bane duk kin samin ido inji uwale. Gwaggo tace
anji kunya dai ace danki ma hakuri yake da halinki, duk kin bata masa gida da
tashin hankali. Kin rabashi da matarsa da yake so kin hada shi da wannan makirar.
Shewa uwale tayi kamar ba tsohuwa ba. Ai na isa ne.
Sabuwa ce taji cizon cinnaka a kafa ta saki Uwale ji kake timmm ta fado tana ihu.
Gwaggo tace Allah Ya kara kadan ma kika gani.
Shi dai Sulaiman tunda yaji maganganun wanda basu san ma yana kofar soron ba sai
tausayin Dijengala mai cin tuwo ya kam[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰24
Yana isa gida Ammar ya tare shi a bakin kofa...hmmm daddy wari. Umma dake zaune
tana yanke farce tace daga ina haka. Itama ta kama hanci kai me ya sami kayanka.
Ina zuwa umma bari na gyara jikina.
Bayan yayi wanka doguwar riga yasa ya sauko kasa. Yana zama ya fara yiwa Umma hirar
dijengala. Yadda yake bayanin cike da nishadi kamar ba shi aka watsawa kwata ba.
Umma tace wai ni Sulaiman kanwar kake so ne ko yayar? Murmushi yayi Umma yar nake
so mana. Ita wannan Dijen zanso ki ganta. To ai yadda kake fada kamar babar hanan
din ke takura mata. Ba don yar ka fara nema ba ai da sai ince ka nemi Dijen don
naga tafi burgeka. Ahh haba umma kurma ce fa. Ta rike baki to sai me Sulaiman?
Kurma ba mutum bace? Ni nafi son irin auren nan da zai kasance taimako ga wani.
Tun da Umma tayi masa magana sai kawai hankalinsa ya rabu biyu. Tabbas sau biyu
yana tarar da rigima da Dije akan ruwan wanka. Kana ganinta kuma sam babu gyara.
Yasan a kalla zata kai shekaru ashirin. Da wannan tunanin ya jira litinin tazo. A
office ya sake yiwa modibbo tambayoyi akan Hanan. Wannan karon gaskiya ya gaya masa
game da halayyarta. Kuma a yadda babansu ya fada min jiya wai kakar ta zata kaima
aikin gini kake yi shiyasa suke son a bawa wani. Mal Yakubu har kunyar ka yake ji
saboda yadda take ficewa daga gidan kafin kazo. Hmm wato sun dauka talaka ne shi
yake fada a ransa. To idan ba damuwa modibbo ka sanar dashi zanzo gidansa zuwa
karshen sati akwai maganar da zamuyi. Modibbo fata ya rinka yi Alh Sulaiman ya nemi
auren Dije.
Alh Sani ya kalli dansa Ashir..yanzu da gaske ka fasa auren sakina? Ashir me kake
son mayar dani ne. Haj Lami tace kaga duk wancan auren kai kake zaba masa kila
shiyasa baya karko wannan karon don Allah kada kayi masa dole. Ai dama da saninki
yake wannan wulakancin. Yanzu meye aibun Sakina? Haj tace bazawara ce fa. Ga
budurwa ya samu son kowa. Har hotonta nagani. Alh Sani yace shi ma ai bazawarin
ne...bazan tilasta masa aurenta ba kada ya bata mana zumunci amma wallahi Ashir
idan ka kara sakin mace zan maka ba dadi. Shashasha wanda bai san mutumcin kansa
ba. Shi dai Ashir ko tak bai ce ba ya tashi ya tafi gidansa. Me zaiyi da wata
Sakina ana zaune kalau. Yadda son Hanan ke ci masa zuciya baya fatan a wuce wata
daya bata zama matarsa ba.
Yau Alh Sulaiman da abokinsa ya tafi gidan Mal Yakubu bayan sun yanke shawara shi
da Ummansa. Umar yace yanzu Sulaiman har lokon nan ka zo neman aure? Wannan yarinya
ta ciri tuta. Yayi dariya sai ma ka ganta mutumina. Ai na iya zabe.
Goruba take ci a kofar gidan Gwaggo ita da kawarta. Kawar ce ta fara hango su
Sulaiman tace ke Dijengala kinga wasu yan gayu can. Dije na ganin Sulaiman ta gane
shi. Al'Quran shine mutumin dana watsawa kwata. Tashi mu gudu dan sanda ya dauko
min. Na shiga uku.
Da gudunta ta tafi zata shiga gida ta kira babanta ya basu hakuri don taga kamar
kayan jikin abokinsa na yan sanda ne. Bakaken kaya ne shirt da wando ne. A kokarin
gudun ne dan katakon daya raba kwatar gidansu ya rufta da ita ta sake yi masa
kwalliya da kwata. Rasa bakin magana yayi don takaici yana tunanin fasa abinda ya
kawo shi. Ita kuwa Dijengala ta gama tsurewa don tsoro ta bare baki tana kuka,
muryarta a sama.
Batul Mamman💖
[8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰26
Gwaggo ta dauko tabaryarta tayo hanyar soro. Tana ganinsu tace au Alhaji
kaine...kaji shirmen Dijengala ko. Wallahi duk na zata da gaske take. Kallon
jikinsa tayi...ba dai yau ma kwatar kuka fada ba? Murmushi yayi yace bata kula bane
ta fada ciki.
Daga ciki suka jiyo Dije tana cewa ba dai sun tafi da Gwaggo ba. Na shiga uku me
zan fadawa 'ya'yanta. Shigowarsu ta gani ta saki baki na tuba don Allah ku yi
hakuri kaga ni bana ma ji sosai kaina bazai yi kudi ba. Gwaggo tace rufa min baki
sarkin surutu.dauko musu ruwa a buta. Kema ki je ki gyara jikinki.
Bayan sun kammala gwaggo tace kai kuma kullum kuka hadu da Dije sai tayi maka wanka
da kwata. Ba komai Gwaggo dama mahaifinta nake son gani. Bari naje nayi masa magana
da kaina to, kasan halin yarinyar nan ina iya turata taki dawowa.
A wulakance su Uwale suka gaisa da gwaggo tace wurin Mal nazo. Sabuwa tace bacci
yake yi. Mal yakubu ya fito suka gaisa. Tace dama kayi bako ne shine babu dan aike
nazo yi masa sallama da kai. Uwale tace haka dai aka iya gulma da sa ido. Gwaggo
bata kula ba suka fito waje...mal yakubu bakon yana gidana fa. Yace sunansa Alh
Sulaiman. Mal yace subhanallah wallahi har kunyarsa nake ji. Ya sanar da ita yadda
suka akan maganar Hanan. Gwaggo tace to Allah Ya kyauta muje sai kayi musu bayani.
Umar ne ya gabatarwa mal Yakubu bukatarsu game da Dijengala. Sulaiman yace baba
kada kaga kamar ina maka yawo da hankali. Naga kamar Hanan din tana da wani ne
shiyasa. Tamkar an mishi albishir da kujerar makka yace da gaske kake Alhaji? Kai
zaka auri Dijengala. Sulaiman yace in har ka amince. Na fara sanar da kai ne don
neman izini kafin na turo maka iyayena. Farincikinsa baya misaltuwa yayi godiya
sosai. Umar ya bashi dubu ashirin yace baba ga wannan mungode.
Suna tafiya Mal ya dauki kudin ya bawa gwaggo ajiya dama ya saba shawara da ita.
Yace yanzu zan sami nutsuwar amsawa wanda yazo neman auren hanan. Dama saboda na
riga na amsa tun farko ne. Gwaggo tace ai gara tayi auren saboda Uwale kara bata ta
take yi. Haka suka yi ta yan shawarwarinsu sanan ya kira Dije ta fito daga daki
suka koma gida.
Ashir ya dage sai shirye shirye yake. Anyiwa gidansa sabon fenti an gyara ko ina.
Dama ya kusa gama hada lefen Sakina saboda haka abinda ya rage ba yawa. Ya dai
kashe kudi sosai don duk abinda Hanan tace ta zauna. A dan lokacin da suka hadu ya
siya mata sabuwar waya ga kudi daya ke kashe mata.
Mal Yakubu ya sanar da uwale zaije gida ya sanar da kawunsa da nata yan uwan za'a
zo neman auren Hanan dana Dije. Uwale da Sabuwa sam basu damu ba da jin Dije ta
sami miji tunda Mal Yakubu yace wannan abokin ginin nasa ne zai aureta. Shima yana
sane yaki fada don gudun kada su toshewa yar tasa hanyar arziki. Ita uwale harda
cewa kyan da dama ya gaji ubansa, tunda ita mace ce gara ta auri mai aiki irin na
ubanta.
Tunaninsa bai wuce ina ma Munari tana nan. Ina ma zata ga auren yarsu. Babu ranar
da baya tuna su ita da Sadi. Amma gashi Inna uwale ta gargade shi ko sau daya yabi
hanyar gidan su munari bata yafe masa ba.
Haka yaje kauyensu ya sanar da yan uwansa zancen auren ya dawo a ranar.
Batul Mamman💖
Copied By
VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.
AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching
this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.
We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction,
non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors
We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with
thier permission.
AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake É—auke da littattafan hausa, dalilin
bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.
Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin,
soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu
a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.