Showing 249001 words to 252000 words out of 456363 words
suka kwashe su zuwa asibiti na sha zagi a gun su sai cewa suke ban ki yarinyar ta mutu ba ai don nima banda shi mu zama daya ke nan.
Ni dai ban kula su ba ban kuma je asibitin ba wanan karon na share su gaba daya haka shima bai kara kira na ba tun wanan lokacin nima haka ban kirashi ba.
Kwanan yarinyar biyu aka sallamo su uwar ta dauki gaba dani itama hindatu ba dadi a tsakanin su.
Ina karatuna ina hadawa da business dina ban tsaya bin ta kan su ba ban ma da lokacin fitinan su a raina.
Abinda dai na sani shine idan ya dawo a hake yake dani a ranshi tunda ya riga ya hau bai jin has ko kadan.
Ayi hakkuri da wanan har na danji sauki baida yawa kadan na samu nayi tun jiya nake typing ban iya yi da yawa ba don yanayin jikina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE NA KUDI, , , ,
59
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH KAN CIN AMANA DON ONLINE NOVEL NE KIN SANI, , ,
Wanan yawan gorin da matan daddu suke min ya fara damun rayuwana sosai har na fara tunane a kan shi.
Yau ma bayan mun fito da lectures bani sallah don haka na zauna daga wajen massalaci ina jiran fitowan Zarah ban san yadda akayi na zirfaffa ga tunane ba har ta iso girin tana magana dani amma banji ba.
Dafa ni tayi tana fadin Rahama may kike tunane ne haka har ina magana bakiji ni ba.
Murmushi mai kama da yake nayi mata tare da sauke ajiyan zuciya ina fadin kin fito zarah Allah ya karba.
Tace wai tunanen may kike haka ne Rahama kada fa kijawa kanki wani matsala a rayuwan ki.
Na sake sauke ajiyan zuciya nace Zarah ni na shiga uku yaushe zan fita a cikin fitinan matan nan na daddy ne wai.
Rahama in sun fito min nan sunga Allah ya ketare ni gobe ma wani hanyan ne zasu bullo min dashi.
Will you believe cewa yanzun kuma kokari suke su shiga tsakani na da anty ta hanyar yara duk da nasan cewa anty ba dauka zatayi ba amma kuma yau da gobe bai bar komai ba.
Gashi sai faman gori suke min wai ni hankaka maida dan wani naki a haka zan kare wurin bautan diyan kishiya, dama kuma don shi aka dauko ni gidan.
Kai wanan akwai shegun duniya wallahi so suke by all meas sai sun shiga tsakanin ki da anty Saade.
Ina ruwan su da abinda kikewa yaranta ne sunga sun buga ta ko ina baku rabu ba shine suka biyu maku ta hanyar yara su na zuga ko waccen ku akan dole sai sunga wallen ku a tsakanin ku.
Kinga wallahi ki bar damuwa da maganganun su Rahama kici gaba da duban yaran tunda duk zugin da suke wa uwar bata taba dauka ba.
Haka kema gazawan ki akan su daidai da rana daya wani bada gurbi ne a tsakanin ku.
Ki duba fa yadda yaran sukai mugun shakuwa da ke yadda ko uwar da ta haifesu basu shaku da su haka na ba.
Don haka wallahi Rahama kada ki yarda shedan ya rude ki ki zafe ki kara jan yaran ajiki suji haushi in sun yi fushi su mutu mana mugani munafukan banza da wufi kawai.
Sannan da suke maki gorin haihuwa baki san ranan da Allah ya baki cikin kuma bakin cikin haka zasuyi ki ce na fada maki wataran.
Sai kuma idan kin haihu sabon fitina zai fara tun dai idan Allah fara baki da namiiji a gidan zaki ga sai sun fi haka tsanar ki tunda halin su ne hassada.
Ke akasarin mata irin haukan da suke ke nan sai su manta da cewa Allah ne mai bayarwa a inda yaso don gani suke kamar da namiji yafi diya mace don hahilci ke har fa gidajen tallakawa da basu da komai suna da wanan bakin kishin tsiyan a rayuwan su.
Nisawa nayi nace kai Allah ya kyauta kawai ni wallahi suna ma son rudani yanzu duk gidan ya fice min a rai gaba daya wallahi.
Tace ke shifa kishi dama abinda ya kumsa ke nan kima kishiya tai maki itama shine kishin kawai ba komai ba sai dau na wata yafi na wata zafine kawai, amma kishi duk bata son taga kishiya ta fita da gashi ta ko ina.
Mun dauki lokaci sosai da ita muna hira daga karshe mukai sallama kowa ya kama gaban shi.
Tafe nake sai dai still ina tunanen dan matsalan da muka samu da anty na da safe akan yara, don Nasir yace ba zaici abincin da akka dafa mai ba ya ishe shi shine nace zan dafa mai wani yaje dashi.
Sai taimin abinda bata taba min ba akan yaran dan ta rufe idon ta dani da yaron tai muna tas don har cewa tayi aii wanan hanyan lalata yaro ne na dauko ba yau ba tana lura abinda nake wa yaran bai mata dadi a ranta.
Nasan ba komai yasa yanzu take min hakan ba sai don maganan da ya dan hada ne da hindatu har take fadin wai ta fahince ni ba son yaran nakeyi ba tunda kowa ya sani tarbiyan lalacewa nakewa yaran anty don su girma su lalace shine na fake da wai ni ina kula mata dasu.
Ko da na shigo kamar na shige part dina sai naga rashin dacewan haka koba komai bai kamata na biye mata na manta da halarcin da tai min ba a duniya.
Ina shiga na samu tana waya tana fadin aini yanzu kaina ya kawo wuta wallahi wani abin sam bai dace da yaro ba amma sai ace wai abar yaro yayi shi.
Hade bacin raina nayi nai sallama don kada taci gaba da magana har naji abin da zai kara bata min rai.
Ta dago ta kalleni a lalace ta amsa min nace anty ya gida ta ce lafiya kawai batare da ta tambayeni ya school ba kamar yadda ta saba tambayana a kullun.
Ban zauna ba don waya take saurare na fice zuwa nawa bangaren inda na samu Fatima don Atika ta fara zuwa school yanzu.
Ina ficewa wace suke wayan tace munafukar ce ta dawo naji ana gaida ke, tace itace mana nima ji nake wallahi kamar na fita batun yarinyar nan don shegen wayon tsiya ne da ita.
Gata dai karamar yarinya tashin kauye amma bakin wayo ke ga yarinyar nan in fada maki .
Yanzu fa ki duba dukkan mu babu mai wata sana,a agidan nan amma ita wallahi business takeyi sosai ba kama hannun yaro don bata raina sana,a ko kadan .
Matar tace bakinji ba ni narasa wai ina wayyon ki ya shiga Saade mutum ya dauki yuka ya dabawa cikin shi don wani dalilin naki can na banza.
Ai da kike son haka da ki bari idan zaki mutum sai kibar wasiya cewa idan kin mutu kin yarda ta auri mijin ki, amma in bashi ba yaushe zaki dauko yarinya tsaleliya haka kamar tsada ki aurawa mijin ki ki koma kina kallon taikaici da ranki da lafiyan ki.
Tace bari ke dai Nuriya ni sai yanzu danaga abin madon wuce tunane na abin ya ke ci min tuwo a kwarya.
Gashi in fada maki kamar auren sadaka yallah don ta kwaso yan uwa ta cika gida dasu tana batun cin nawa yan gida su.
Nan dai sukai ta maganan su da matar tana kara sakata hanyar shedan ita kuma tana hawa ta zauna a kai.
Kwana biyu sam ba dadi a gidan tsakani na da Anty don ta canza min fuska sosai bata sake min ko kadan .
Ban yarda na biye mata ba haka na nake daurewa ina mata magana tana basar dani cikin rashin kulawa.
Gajiye ne matake fada min ranan na dawo take cewa wai Rama may ke faruwa ne tsakanin ki da uwar dakin mu ne kwanan nan.
Naga ko abincin da take cewa na aje maki ta daina sai ma ta tambaye ni kada na sake na saka maki wai kowa an bashi abinci ki dafa naku idan kuna so.
Murmurshi kawai nayi nace gajiye ba komai shedan ne da shedanu ke son shiga tsakanin mu amma ni ba zan yarda ba don ni ba butulu bace.
Zata ci gaba nace da ita tabar zancen don anty ta fita bata sallami kowa ba don ta fara fita yanzu.
Saboda gaskiya Alhamdullahi maganin nan da na sayo mata na gargajiya ya matukar karbuwan ta sosai ta daina yawan takura yanzu akan ciwo kamar baya.
Ko yaran nason suzo guna kiri kiri wani lokaci zata hana su zuwa ko ina masu magana sai naga suna kallon idon ta da alama dai an masu wani warning akaina ne.
********* ********* *********
Wanan halin ya kai min ko ina, tun ina mamakin jayewan anty gare ni har nazo na daina mukaci gaba da tafiya a hakana sai dai ban yarda ya kaimu ga yadda wani zai fahince mu ba sai mutum ya kula sosai zai gane akwai matsala a tsakanin mu da ita.
Muna cikin wanan halin daddy ya dawo ya samay mu a hakan da ita a tare muka saba zuwa taron shi sai ga shi wanan karon mun zo daban daban ba a tare yadda muka saba ba din.
Bai kawo komai ba sai da dare bayan ya huta ya kira mu yaji wacce zatai girgi a ranan daga cikin mu.
Tace amma dai kasan ka share kusan wata biyar ba a gida ba don haka sai mu koma fresh daga yau yace to shikenan babu damuwa.
Na riga kowa ficewa a falon don ban tsaya ba tana gama magana ta sai na mike na barsu.
Washegari Ina kwance dakina da safe ya shigo dakin don bamu zuwa school ranan karatu nake ban ji shigowan shi ba sai da ya dan ja min kafa na dago na ganshi sai nai yunkurin mikewa zaune ya dakatar dani ta hanyar mayar dani da hannayen shi yai min rufa dashi tare da kura min idanuwan shi cikin nawa.
Ba zan jure ido hudu dashi haka ba sai na kawar da idanuwa kasan yace see you kin gama fushin da kikeyi ne ko har yanzu.
Nace haba akan may zanyi fushi dakai daddy yace yaushe rabon ki daki bugo min waya in ba fushi kike dani ba ya tambaya.
Daddy bani fushi dakai kaine dai baka fahince ni ba kawai amma ni ban fishi da wanda nake a karkashin shi ai.
Yace ko fa ta anty ki na bugo sai tace min bakya nan ko baki kusa da ita shiyasa na san kin dau fushi dani.
Wani iri naji don daidai da rana daya anty bata taba fada min komai ba akan daddy na cewa a bani wayan shi.
Yace to may ke damun ki haka naga duk kin wani fadawa kin ramay kin yi duhu dake ?
Murmushi na kakaro nace ba komai daddy kila don ka dade baka ganni bane kawai.
Ya mike yana Yana cewa OK ban san ki ba ke nan sai wanan time din ko ?
Nace an dawo lafiya yaya gajiyan hanya yace bazan karba ba jiya may yasa ana magana kika fito kika bar mu a falon.
Nace ba komai naga dai an gama magana ne yasa nabar wuein don ina da test shiyasa ban tsaya ba yace anyway yadda kika ce shi ke nan amma sai naga kamar ke baki missing dina ba dai.
Nace haba daddy baka iya ka gane ai abin siri ne banice dakai ba jiyan da ka gane hakan ai glad yace ya fara tafiya yana fadin zan shiga wurin Alhaji nagan su sai na dawo ke nan.
Ashe tare da anty suka fice bata sallamay mu ba sai da nashigo wurinta gajiye ke fada min ai sun fita da maigidan nace Allah sarki kawai.
Ban zauna ba nakoma part dina dama na dan zagayo tane kawai kada kuma ta fasaara ni da wata manufar ta kishi nake da ita.
Can gidan da sukaje Alhaji yake fada masu ai nakan shigo wani bi idan na tafi makaranta na dan duba su.
Yace wanan yarinyar akwaita da kirki sosai kudai ta hakkuri don ba ai zaben tumun dare ba gaskiya don akwai tarbiya da ita.
Can ma gidan mahaifin anty ya fada masu cewa na kanzo dubashi har cake na kawo mai wani lokaci.
Hakan baiwa anty dadi ba a ranta saida suka fito suna tafiya ta nisa tace kai mutum sai ka barshi inda ka gan shi kawai.
Yace may akayi kuma yanzu kike wanan magana kamar an maki wani abu can ?
Tace daidai da rana daya Rama bata taba fada min cewa tana zuwa wurin Abba ba sai yanzu da suka fadi naji.
Yai murmushi yana tuki yace to yanzu may ye a cikin hakan don ta zo gaida mahaifinki shine wani abin kuma ?
Tace wanan ai munafunci ne besty don may da zatazo bata fada min ba koda ta dawo ta fada min taje din.
Yace haba besty yanzu may ye kuma laifin wanan yarinyar anan don kawai taje gaida tsufin nan akan dalilin wa tayi ba naki ba ko don wa tasan su ba kan ki ba kibar irin wanan maganan please don ba girman ki hane hakan.
In ba tsaban munafunci ba don may zata bata fada min ba anyi magana ga gaskiya zahirinta kuma kace kada a fada aini yanzi na gane mutum kabarshi kawai inda ka ganshi wallahi.
Kakai shi yace shi rana zai kai ka kanaji kana gani yace Rahaman ne kuma munafukar ki yau besty ?
Ai kai bazaka bari a fadi ba tunda kaga abinda ke maka ni sai ma ince wai kodai tun farko kana son Rama ne da gaske wai ?
Mirmushi yayi yace yanzu aiko may ye ma aikin gama ya gama don kaki akeji abin kunyane aji wanan maganan kuma a bakin ki keda kikai ruwa kikai tsaki wurin hada halakata da ita.
Gareka yake abin kunya ni yanzu na fahinci komai ko an daina shana ina barci.
Yace ai naga alama kan tunda sauki ya samu yanzu sai a tsiro wani halin sabo daba a sanki dashi ba.
Sun dawo gida ranta a bace ta fice daga motar shi dai yabi bayanta da kallon mamaki kawai don ta bashi mamaki sosai ta canza a lokaci daya.
Dan tsakanin jiya zuwa yau yaga canji sosai a gare ta wanda bai santa da wanan halin ba a baya.
Sun dan jima da dawowa na shiga part din da fara,a na a fuska nake cewa ashe kin dawo anty yadda tabani amsa sai banji dadin hakan ba don cewa tayi eh mun dawo yaya akayi.
Na daure nace babu komai dama na shigo dazun gajiye tace min bakya nan kin fita tace eh naje gaida Abba nane.
Cikin washe baki nace Allah sarki yana lafiya da mutanen gidan tace lafiya suke ina zama sai naga ta saka wayan ta a handbag din ta dake aje a gefe daya tana fadin ni zan shiga ciku na huta nagaji.
Nan ta wuce ta barni zaune na dan dauki lokaci na mike na bar part din don ko yaran basu nan a lokacin.
Na wuce ina mamakin wanan dabiar da anty ta kirkiro a tsakanin mu wanda ni ainihi ban san takamaimai abinda nayi mata ba yakawo hakan garemu.
Haka dai ake zubawa tsakanina da ita har na karbi girki nai komai a part dina don babu fuska ko kadan a wurin antyna.
Na gyara komai neat a part din nai abinci lafiyayye na fitar da sabon kula don ban dauki na ta ba.
Yana zaune na caba kwalliya na shiga falon na samay shi ya saka jallabiya mai guntun hannun don yanayin zafin da ake ciki a kasan duk da bamu da matsalan haka sosai don akwai AC ko yaushe a gare mu.
Na jera abincin yadda ya dace na dawo inda yake na tsuguna inacewa barka da dawo wa daddy ya kuma gajiyan tafiyan ?
Yai dan murmushi ya dago yace tafiya kan ai sai dai wani kuma wanan kan ai anyi angama shi ko.
Allah ya taimaka nace dashi, tare da gyara zamana ina cewa ga abinci nan na kawo yace sannu da aiki.
Bai jima ba ya sauka ya fara cin abincin a hankali sai ga Zulfa da yar ta ta gaidashi bata tsaya ba kodon ina wurin ne tafice abinta.
Anty ce ta shigo tana saye da dogon riga baka a jinkin ta zan iya cewa tun gaisawan safe da mukayi sai yanzu na saka ta a idona don tana dakin ta bata fito ba.
Gaida shi tayi ya amsa mata da fara, a yake cewa da ita yaran basu dawo bane banga yau sun biyo uwar su ba gaishe ni ?
Tace suna can suna assegment ne kasan ai yaro abinda ka saba mai dashi yake amfani yau bata jin zuwa dasu ne kada su bata mata show killa.
Nace a,a ba haka na bane anty na shiga sukace min