Showing 357001 words to 360000 words out of 456363 words

Chapter 120 - Murucin Kan Dutse By Makawa

Unknown   

24 Apr 2026

106

na wani dan lokaci can ya kara kurba ruwan lemon dake gaban shi bayan ya aje ne yace ko akwai may magana daga cikin ku in babu zan kai Raliya gidanta da zata zauna a nan.
Ba nisa sosai da nan din kusan unguwa daya ne da mu nan din da inda zata zauna ita din ko akwai may magana na sake tambayan ku ?
Shiru nayi ina kallon wayana don hankalina ma baya a kan su ko kadan ina abinda nake da wayan nawa tun fara maganan shi damu.
Cikin firgici na dago kaina don jin ya ambaci sunana da sauri na amsa da naam yace bakiji bane nace ba magana kina ta faman kallon waya a hannun ki.
Nace a sanyaye ba komai Allah ya bamu hakkurin zama da junan mu bisa amana da gaskiya yace Amin tare da dan furzo iska daga bakin shi.
Mikewa yayi daga zaune yana fadin oyo muje na kai ki gida ko kada yamma ya kara yi muna anan din sai na dawo yace tare da fara hanya ta mike tabi bayan shi bataiwa kowa magana ba a cikin mu ta mike tabi bayan shi suka fice daga gidan duk muka bisu da kallon ikon Allah.
Akan wanan tsohuwar yake wanan rawan kafan haka wa mutane wanan aiko marigayiya ta girma balle mu don dai tana da dan karamin jiki ne kawai ba a ganewa.
Ni dai ban tanka ta ba sai ma Aisha da nake kira tazo ta kwashe cups din da suka sha ruwa dashi a falon.
Sai faman tsuki take zubawa bandai tsunka ba ina daga kwance karshe ma mikewa nayi zuwa dakina suna ta zunduma zagi ita da zulfa da ta kira a waya.
A raina nace nima haka suke zunduma min zagi na halittana yadda ransu yaso amma ni banga abin kushewa ba don shi ya gani yace yanayi ai

********* ********* *********
Duk wani rawan kafa da kika san namiji nayi idan ya kara aure shi daddy keyi abin ma zaban kunya gareshi amma shikan ko a jikin shi ma.
Baya shigowa gidan sai goma da wani abu na safe idan ya dan zauna zai mike yace ya fita sai hindatu tace zaka dai koma gun amaryan ka dai.
Ni damuwana shine inda zan bar yarana na tafi karatu don dai ba zan iya barin su gun hindatu ba gaskiya mutumin da bai iya kula da kansa ba shine zai iya kula da dan wani.
Ina kwance daki tunda na dawo ban fita ba na kunna A C yana sauko min da sanyi a jikina idanuwa suna a lumshe kamar ina barci a lokacin.
Ya shigo dakin dauke da wasu takardu a hannun shi kafa da ke mike ya dan ja yatsun su sai na bude idanuwa na na sauke su a gareshi.
Yace barcin marance kike ko mai zaune na mike ina fadin ba barci nakeyi ba na dai kwanta ne kawai.
Miko min takardun yayi na karba tare da dubawa pasphot ne na Aisha da jinior da baba da haidar a cikin ledan komai na tafiyan su an shirya masu.
Ban san sanda na sake murmushi ba a fuskana nace masha Allah daddy kamar kasan abinda ke damuna a raina duk kwanakin nan ke nan.
Yace na sani mana tunda zurfin ciki baya barin kiyi magana amma ni nasan dole ne ai ya damay ki a ranki.
Na dago kai nai mashi godiya tare da cewa su sauran a nan gida zasu zauna ko may ?
Yace na gama magana a kan su idan nan din baiyi masu ba zasu koma Kano har ki dawo wurin Zulfa ko hajiya na ina hakan yayi maki daidai.
Nace eh yai min nagode nace sai dai doctor Fati ta roke ni na bar mata Atika a gidan ta ta zauna har na dawo.
Ya dago da sauri ya kalle ni tare da cewa umm,umm don ita bani na haifeta ba za ai wanan shawaran ban sani ba ko may kada kice ki canza mata makarantan da kikayi bai damay ni ba a baya ido kawai na sa maki tunda ke baki iya fada min abinda ya faru har kika kai ga yin hakan gareta.
Don ki nuna min ke ma yanzu wuyan ki yayi kauri kina iya samun kudin da zaki dauki nauyin su batare da ni ba.
Ki dai tuna zaman yaran nan a wurin ki sai da amincewa na don in ba amince ba babu dan da zai zo ya zauna min a gida hakana na kyaleshi.
Don naga kawai suna bukatan taimako ne kema haka zaman ki dasu akwai karuwa a gareshi yasa na barki ban maki magana ba.
A sanyaye nace kayi hakuri daddy amma ni banyi haka da wata manufa ba sai gujewa bacin rai kawai don yadda yaran suka dauko yi mata zai iya haifar da fitina watarana shiyasa na canza mata makaranta din ba wani abuba.
Yace naki ke nan idan kinyi laifin anyi magana saiu kice zakiiba mutum hakkuri akai to ni babin sson mace tace zatta shige min gaba a gidana kinji na fada maki.
Shiru nayi har ya gama ya fita ban yi magana ba ya juya da bacin rai yabar min dakin na sauke ajiyan zuciya tare da binn bayan shi da kallo.
Wani sabon surfa da Amira ta tsiro shine weekend sai tace a gidan amaryan daddy zatayi ni dai banyi magana ba iyakata ido sai ta dawo tana wani jiji da kai a gidan har da kokarin sake magana.
Ba wanda yasan da zancen tafiya na sai da tafiya yazo gap ne aka sani saura sati mu bar kasan lokacin amarya takai wata daya a gidan.
Na fahinci kamar har yanzu aikin ta yana kano zuwa take tana dawowa nan Abuja din amma dai bamuji a bakin maigidan ba.
Gashi idan zata dawo sai ranan da ya dace ace nice da girki take dawowa garin sai dai naga da yamma ya shirya yace zai tafi gidan Raliya tana gari.
Abin naci min rai amma naga kwana nawa ya rage na daga na basu wuri suci kan su aa tsakaniin su don haka na danne zuciyana nai shiru.
Munje kano nai sallama da mutane muka dawo daren da zamu wuce naga tashin hankali gun hindatu ba ita kadai ba har da sauran matan daddy sai da sukai korafi wai yana kashe min kudi kamar ni kadai ce matar shi.
Nasan ba plan din kowa bane na hindatu ce ita tanemi sauran da wanan magana ban bi ta kan su ba nikan sai Nasir da yasha kuka wai ba zan barshi ba in tafi.
Daddy da kan shi yai min magana yaushe ne zan kai Atika din gidan doctor Fati ta zauna nace aii na jaye maganan yace bayan kkun kiitsa kuma ga yadda zakuyi zakice kun fasa nima naga hakan zaifi son barin ta a nan akwai matsala don haka kikirata ki sheda mata maganan yana nan.
Nai mai godiya na kirata na fada mata taita murna nace masoya na asali ke nan sai bare yai maka abin alherin da baka zata ba ma a duniya.
Na gama da wanan matsalan dake damuna na Atika yanzu banda sauran kunci a tare dani sai shiri na nakeyi na tafiya yawancin kayana duk dama na loda nakaiwa iyayyena da yan uwa na agida abu kadan na bari a dakina.
Helen ma na mayar da ita gun wacce tabani ita amma akwai wata yar wajen aikin mu data karbi yarinyar kuma a hannun su.
Washegari kukan da Nasir keyi ya sa hankalina yai mugun dagawa don zance bann taba ganin yana kuka haka ba sai naji jikina yai sanyi nace na fasa tafiyan kawai zan zauna.
Na samu daddy da magaban aiko ya hauni da masifa yace akan Nasir zakice kin fasa tafiya kin san nawa aka kashe kan wanan tafiyan naki da yanzu zaki zo min da maganan rubish.
In dai don Nasir ne ki bari nan da wata daya zan mai komai sai ya biyo ki bashi ke nan ba haka muka kama hanya ni ko sallama da abokan zama ma banyi ba don ba fuskan yin haka a garesu yadda muke.
Jirgin lagos muka shiga mun kwana daya muka daga wani abokin daddy ne yai ta dawainiya damu don da yace dashu zamuyi tafiyan amma daga baya sai cewa yayi ba zai samu zuwa ba zaizo daga baya.
Nasan matsala daga matan shi haka ban damu ba muka wuce abin mu tunda bukatana ya biya.
Mun sauka lafiya a kasan na Germany inda aka tura ni karatun don an watsa mu ne ba wuri daya aka aje mu ba da sauran kowa da inda aka kaishi.
Gida dan madaidaici aka kama muna har karatun yara sai da akai muna komai a kan shi na fara fita gun aikina na fitan da damuwan komai a raina na rungumi karatuna gadan gadan.
Aisha zamu bari a gida ita da Haidar tai aiyukan gida daya dace ni da jinior da baba kuma mu fice wuein neman ilimi da ya kawo mu kasan.
Idan mun dawo ni zan koya masu karatun addini sai wani lokaci mu watse sai kuma gobe haka rayuwan mu a can yaci gaba da gudana gwanin ban sha, awa damu.
Watan mu hudu a kasan amma babu daddy habu dalilin shi sai dai can ba a rasa ba yakan dan bugo waya yaji lafiyan mu yadan yi hira da yaran sai ya kashe.
Naso saka damuwa ga hakan amma nabawa kaina magana na mayar da hankalina ga abinda zai fishe.
Ranan na dawo ina zaune da yarana a falo muna hiran mu a cikin raha da jin dadi sai ganin an turo kofa mukayi kawai.
Gaba daya hankalin mu ya koma a kofan yana saye cikin kayan sanyi muka bishi da ido abin mamaki babu yaro ko daya da yai daukun ganin shi a lokacin balle suje su taro shi kamar an masu nasiha a hakan.
Sai Aisha ce tai mai sannu da zuwa nikan kallon kallon muke dashi don watan mu bakwai ke nan yanzu da zuwa sai gashi ya ziyarce mu yau.
Roku roku nake don cikin jikina yana ganuwan haihuwa a lokacin da kyat na iya bude bakina nai mashi sannu da zuwa.
Yace Aisha kece baki fushi dani ke nan don naga sauran duk fushi suke dani ga alama ?
Ban yi magana ba ya samu wuri ya zauna ya mika hannu baba yazo sai yaron ya noke ya nufo ni inda nake.
Yace Jinior harda kkai fushi kake da daddy yaron baiyi magana ba yai shiru nace dasu oya a gaida daddy cikin harshen turanci.
A sanyaye suka fara gaidashi sai dai basuje inda yake zaune ba komai na sha Aisha ta kawo mai sai dai ya kasa sha.
Nan ya fara magana cikin karfin hali irin na maza wai nasa yaran sunyi banza dashi in ban hura masu kunne da kalaman banza ba akan may zasuyi mai haka.
Nidai shiru nayi har ya karaci fadan shi ya mike yana tambayan Aisha dakina ta nuna mai ya shiga na mike da kyat nabi bayan shi.
Sannu da zuwa na sake mai tare da tambayan mutanen gida ya amsa min a bashe da suna lafiya kawai.
Falon nadawo wurin yaran don shi ya shiga wanka nai masu fada kan abinda sukayi ma uban nasu duk sukai min shiru.
Ya fito ya samu wuri ya zauna lokacin muna kitchen muna hada mai abincin da zaici don bamu damu da girka abinci ba don mun saba da abincin can.
Ban fito ba ina jin shi yana hira da yaran sai da muka gama komai na jera na shiga wanka lokavin sallah yayi mukai sallah.
Sai bayan mu idar ne na samu zama a falon wurin su na sake gaidashi tare da tambayan kowa a gida.
Yace duk suna lafiya haka muka zauna ba wani sakewa kowa da abinda zuciyar shi ke saka mai a lokacin.
Sai dare mun kwanta ne yake cewa wai banyi murna da ganin shi ba gashinan har na fara sawa yaran shi kiyayyan shi a ransu.
Raina yai mugun baci nace haba daddy ya kamata kai min adalci hakana please har fa nan makwabtar kasan nan kake da matar ka amma ka kasa zuwa ka ganmu don kana gudun bacin ran matarka ga yin hakan.
May kaji nace maka ina ganin sam baisan nasan sun fito honey moon ba da ita sai da yaji na fadi sai ya fara yan kamay kamay da fada irin na maza idan basu da gaskiya.
Wai dama yasan shi nakewa ni kasa nawa ya fita dani ina amarya nace nasan da hakan kuma ni hakan ba komai ba ne a guna ai.
Don bakaji nai magana ba sai yanzu da kakawo wanan magana don haka a barni naji da abinda ke gabana ni ba kishi ya damay ni ba fatana naga na rabu da cijin dake jikina lafiya.
Duk abinda mutum zaiyi ni ba ruwana don nasan akwai Allah yana ganin komai yace dana san bacin ran da zanzo na samu ke nan da banbar abinda nake nazo dubaku ba ai.
Nace aini ba don ni kazo ba kadai zo watakila don yaran ka ne ko wani harkan gaban ka tunda nan din wurin zuwan ka ne dama.
Shiru yayi bai sake magana ba muka kwana a hakan don a tunanen shi tunda yaji nai magana yasan raina ya baci sosai don shi kan shi yasa baida gaskiya.
Banyi wani dokin ganin shi ba yadda ya tsanmata don a dadafe muke zaman da yai muna kwana biyu.
Satin shi daya ya shirya zai koma sai gashi haihuwa yazo min da daren nan ana washegari ya wuce dole ya tsaya na sauka lafiya dana babba dashi na haifo mashi kamarsu dashi har ya baci sosai ga wani girma da yaron yazo dashi.
Wanan karon Aisha ce mai karban jegon ita ke mun komai daga ni har yaron bamu da matsakan komai .
Nan ya bugo waya gida yana sheda masu haihuwan nawa abu ga kishin mata sai aka juye zancen wai dama yasan lokacin haihuwa na yayi yasa ya tafi gun mu.
Dako dadi suke ji yayi banza damu don kowa yasan bai je ba tun tafiyan mu hakan na masu dadi yadda yai watsi damu can.
Duk da ba wani zaman dadi ne a tsakanin su ukun ba fitinane ko yaushe a tsakanin su ba sassauci ga komai yadda muka barsu haka ake.
Don Raliya tai masu tazara sosai ga komai sunki kwantar da hankalin su su fahinci ta fisu iya zama da namiji sosai.
Ashe bayan wucewan mu Amira can ta tare gidan ta ba dadi ko yaushe sai sun kwasa dole ya tattaro ta ya maidata kano don hindatu tace bata zama da ita tunda ta guje ta da farko.
Shiko Nasir yanzu bai zama gida sai dare zasu ganshi tun uban bai farga ba har ya gane haka gudun kada yaron ya lalace mai ya mayar dashi Kano gidan kakannin shi da zama.
Sai aka bar hindatu da yarta kawai a gidan sai masu aikin su gaba daya ya kasa hada kan gidan nashi yadda yaso komai na batun tabarbare mai.
Zulfa ta haifi da namiji itama bayan mu tsakanin mu da ita wata daya ne da kwanaki sai da yaga komai ya koma min normal ya kara sati ya shirya bayan ya radawa yaron suna da Abdulrahaman.
Ya koma gida Nigeria inda yaci gaba da harkokin shi na yau da kullun sati uku nayi na koma karatuna don ba wani hutu sai renon yaron ya koma hannun Aisha.
Munyi waya da zulfa nai mata barka itama din tai min nai mamaki da ta kirani tana min barka da haihuwa.
Na tambaye ta kowa tace suna lafiya tun wanan lokacin takan dan kira waya mu gaisa nima dana ga haka nakan kirata mu gaisa sai dai ban yarda muyi wani hira mai tsawo.
Wani rana mama laraba na kira mun gaisa take cewa dani gaskiya Rahama banji dadi da kika bar kasan nan kika bar yaron nan yana shirin lalacewa ba.
Gabana ne ya fadi nace wa tace Nasir mana nan dai take min bayanin komai a kan shi banji dadi ba ranan na rufe ido na fadawa daddy magana son raina kan watsi da iyalin shi da yake kokari yi ya tare gun mace daya kuma na roke shi da ya turo min yaron do dawowa na ba yanzu ba koda na gama zan kara jonawa ne naci gaba don dawowan ma ya fita min a rai.
Banda kewar iyayyena banda damuwa ga kowa yanzu da sannu sannu na dawo da Atika da Nasir a waje don ina samun kudi sosai yana shigo mun tunda ba komai nake dasu ba a can komai da mukeyi daddy ne yake biya a katkashin shi.
Kulawan da bamu samu daga gareshi ne kawai matsala wanan kuma haka maza suke da giyar aure idan ta rude su.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NR, , ,
88

Alhamdullahi zance komai nawa yanzu ya kammala a gare ni sai hamdala da godiya ga ubangiji a gare ni.
Naje da niyan yin shekara daya da watanni

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login