Showing 3001 words to 6000 words out of 10506 words

Chapter 2 - SHIMFIƊAR AURENA by Zahra Surbajo

21 Apr 2026

4

kabar Deeyanah a hannun Inna ba makaranta,ba
ilimin addini bare na zamani,sede tallah da yawon banza tana ɗauko magana
tarbiyarta na daɗa lalacewa?"

Runtse ido IG yayi dan matar tashi ta soso inda ke masa ƙaiƙayi,kullum da wannan
baƙin cikin yake kwana yake tashi,cikin damuwa yace.

"a har kullum maryamu ban taɓa danasanin zama dake ba,kina sona kina son duk wani
abu nawa,sede mahaifiyata ita bata sonki da duk wani abu daya shafeki,tunda Aisha
ta mutu gun haihuwa,inna ta alaƙanta hakan dake,ko kaɗan bata ƙaunar ta bamu
Deeyanah,na rasa yazanyi in amshi yarinyar nan in inganta rayuwarta,gaba ɗaya
yarinyar yanzu in kika ganta wlh irin yaran nan ne marasa kunya ga ƙarya da haɗa
sharri,kuma ita inna bata ganin hakan a matsayin laifi,ita har kullum son Deeyanar
ne baa yi shiyasa ake mata hakan".

"Duk wannan Alhaji ni be dameniba,kawai tsorona ranar lahira Allah ze tuhumeka kan
tarbiyar Deeyanah,yakamata de kayi wani abu akai"

Shuru ce ta biyo baya,kowa na saƙa da warwara azuciyarshi domin neman mafita.

Yinin Ranar IG yayi shi gun tunanin yadda zebi inna ta bashi ƴarshi cikin ruwan
sanyi batare da sun samu matsala ba.


Bayan kwana biyu ya yanke shawarar zuwa kaita ya tuntuɓi inna akan maganar.

Da azahar ya isa garin,cikin rakiyar jami'an tsaro ko ina ya kaure da jiniya.

Yau ta gama suyar wainar rogonta kenan ya shigo gidan,dan haka arziƙin gurin zama
ma be samuba se uwani ce ta shimfiɗa masa tabarma ya zauna.

"Deeyanah kiyi sauri kizo ki wuce rana tayi,kisamu ki shishshigar da ita kamin
la'asar"cewar inna tana naɗa mata gammo.

Da saurinta ta fito,taci adonta tana gyara mayafinta,tace "inna yau in na siyar zan
siyo rinbom acikin kuɗin"cewar Deeyanah wacce ko kallo mahaifin nata be isheta
ba,sabida inna tace mata shi da matarshi ne suka kashe mata mahaifiyarta,Allah ne
ma ya tsare da har da ita zasu haɗa.

Ɗora mata wainar tayi,tabita har soro tana mata fatan samun kasuwa,sannan ta dawo
cikin gidan tayi kamar batasan dashi a gurin ba.

Wasu hawayene masu zafi suka gangaro daga idon IG ganin shi da yaba Milliyan dubu
baya,gashi ƴarshi ta ɗauki tallan dabe wuce na dubu ɗaya ba zataje tayi gogayya da
maza.share hawayen yayi sannan ya ƙarasa kusa da innar.
Tsugunawa yayi yace "inna barka da rana mun sameku lafiya?"

Seda tagama shan ƙamshi sannan tace"lafiya"

Shuru yayi na ɗan lokaci sannan yace"inna dama nazo ne neman alfarma agunki,kiban
Deeyanah mutafi Abuja asata a makaranta,zamanta a haka beda amfani in kikayi
laakari da cewa...."tass inna ta ɗaukeshi da mari,wanda yasashi yin shuru badan ya
shirya yin hakan ba,lalle inna kin kai ƙwaruwa the whole IG guda.

Rintse idonshi yayi,ya dafe gurin,cikin tsantsan mamakin mahaifiyar tashi,da ta
maida marin fuskarshi kamar abun wasa.

"a sata a makaranta ko kuma ku ida nufinku akanta nason ganin bayanta,to bazan baka
ba,kai daga yau kakuma zuwamin da magana makamanciyar wannan wallahi seka gane
kuranka,ɓacemin da gani,sullutu bawan mace".cewar inna bakinta har kumfa yakeyi.


Bece komai ba ya miƙe ya fice dag Gidan jamian tsaronshi dake waje suna jiransa
suka mara masa baya.

Suna cikin tafiya,ya hangi Deeyanar gurin wasu leburori ta ajiye tallan tana ta
rawa atsakiyarsu suna mata tafi,wani har jan hijab ɗinta yake.

Runtse ido IG yayi yana karanto duk adduar data zo bakinshi, umarni yabada a ɗauko
masa ita.

Ba musu jami'i ɗaya ya fice a motar ya isa inda take bece komai ba ya
sunkutota,tana ihu yasa ta a motar kusa da mahaifinta,direba yaja suka bar garin da
hanzari.


Muje zuwa



Surbajo for life
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*na kuɗine 500 kacal,ki biya ayi tafiyar dake,akwai tarin ilimi acikinsa,da
nishaɗantarwa uwa uba soyayya me tsayawa a zuciyar me karatu,ki turo naki mu jera
dake😄*

*Zahra muhammed Nasir 2084024749 UBA*

*07044600044 Aturo shaidar biyan tanan,whatsapp*

*ta acct kawai ake biyan kuɗin littafin,in baki da acct akwai pos so in son siya
kike se ki turo ta pos ɗin,nagode*

*6*
Tunda ta waigo taganta zaune kusa da mahaifin nata setaja bakinta ta tsuke,ta dena
kukan dan tasan inde inna nada rai ba wanda ya isa yay mata tilas.

Koda suka isa katsina airport aka kaisu,lokacin da jirgin ze tashi ne Deeyanah ta
fara ihu tana faɗin"wayyo Allah na innata zasu kaini saman jannati,wayyo kayan
cikina duk sun kwashe su,wallahi amai zanyi ku saukeni"da ike a ɗaure take da seat
bell ba wanda yabi takanta.


Suna isa Abuja kai tsaye gidanshi aka kaishi shi da Deeyanah.

Hajiya Maryam na zaune a falo taga mijin nata yashigo ya taso ƙeyar Deeyanar agaba
tana turo baki gaba.

Cike da farin ciki hajiya ta miƙe ta kamo Deeyanar tana faɗin "Alhmdllh,ƴata ta
dawo gareni,Allah na gode maka"

Da sauri Deeyanah ta kwace hannunta ta matsa gefe tace cike da tsiwa da rashin
kunya "ƴarki ko de ƴar kishiyarki da kika kashe,ay wallahi nima nice ajalinki"ta
faɗi ba tare da tsoron kowa ba.

A fusace IG ya ɗauketa da wani gigitaccen mari,wanda nan take ta saki futsari ta
fashe da kuka.

Da sauri hajiya ta shiga tsakaninsu tace"haba alhaji taya zaka daka ta tata,ay
yarinyace abi komai a sannu,in kace da zafi zaka bi komai baze haifar da ɗa me ido
ba"ta ƙarasa maganar cikin sigar rarrashi.

Guri IG ya nema ya zauna,yana huci dan gaba ɗaya haushin Deeyanar yake ji kamar yay
ta dukanta se ta dena motsi.

Jan hannunta hajiya tayi,da bazata bita ba amma tuno zafin hannun IG bata san
lokacin data bi tan ba tana kuka.

Sashin yaran gidan takaita,dawowarsu daga makaranta kenan,suna ganin hajiyar kowa
ya duƙa yana gaisheta,amsawa tayi cikin walwala,tacewa ƴar babbar wacce zasuyi
saanni da Deeyanah "Munauwara ga sister ku nan ta gurin innarku ta kaita,maza ki sa
tayi wanka ta kimtsa,taci abinci kamin in dawo".

Bata jira amsar su ba ta saki hannunta ta koma gun mijinta dan ta kwantar mai da
hankali,dan ta fahimci acikin zafin rai yake.

Ruwa ta ɗebo masa me sanyi ta bashi yasha sannan tajashi zuwa ɗakinsa,ta taimaka
masa ya rage kayan jikinsa,sannan taje toilet ta haɗa masa ruwan wanka ya shiga.

Kamin ya fito ta fito masa da kayan dazesa marasa nauyi,sannan ta kwaso abincinsa
ta kawo ɗakin,yana fitowa taimaka masa tayi ya kimtsa,sannan ta zuba masa abincin
yaci yasha ruwa ta kwashe kayan,sannan ta dawo.

Jikinshi taje ta kwanta,tace cikin taushin murya"Abban Deeyanah ina fatan de da
yarda da amincewar inna kuka taho,dan naga tafiyar kamar ba shiri kuka yo ta?"ta
ƙarasa maganar tana wasa da hannunsa.

Murmushin takaici yayi,sannan yace"maryamu bada izinin inna na taho da deeyana
ba,"daga haka ya kwashe duk abinda ya wakana ya shaida mata.

Sosai tausayin mijin nata ya kamata wasu siraran hawaye suka shiga zubo mata cikin
kuka tace "shekara da shekaru Abban deeyanah rashin jituwa kaida mahaifiyarka duk
dan saboda ni,"da sauri ya rungumota jikinshi ya fara rarrashinta da kalamai masu
daɗi.

Dena kukan tayi sannan tace"ayi gaggawar saka deeyanah makaranta,dan akwai duhu na
jahilci a tattare da ita,sabida a samu ta natsu,duk wani sakarci dena shi zatayi in
Allah ya yarda,"

"hajiya kiyi haƙuri da halayenta,ko kaɗan deeyanah bata da kunya,don Allah ki zama
me juriya watarana ze zama labari"IG ya faɗi cikin sigar rarrashi.
Murmushi tayi sannan tace "uwace fa ni Alhaji,kadama wannan ya dameka insha Allahu
zan jure har zuwa lokacin da zata fahimci gaskiya"cewar hajiya tana murmushi.

A can kaita kuwa,da Inna taga har laasar bata ga Deeyanah ba mayafinta ta ɗauka ta
tafi neman ta hankali a tashe.

.Muje zuwa


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*


*free pages sun kusa ƙarewa,hanzarta ki mallaki naki 500 ne kacal ba tsada,domin ki
shigo cikin tafiyar ayi dake,shimfiɗar aurena yasha bam bam da saura,shi ɗin na
musamman ne*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*A turo shaidar biyan tanan 07044600044 ta acct kawai banda recharge card*

*9*

A zabure dukansu suka miƙe suna kallonta,dan sosai suka tsorata da ganin nata.
Baki na rawa hajiya maryam tace"sannu da zuwa inna"

Ay kamar jira inna take ta fara da cewa"munafuka baƙar daga me fasa taro,tauraruwa
me wutsiya ganin ki ba alkhairi ba,kin tarwatsamin farincikina dana ahalina,"

IG ne ya matso kusa da Hajiya maryam yace mata cikin sigar rarrashi "go
inside,please kiyi haƙuri"hawaye ke bin idonta amma seda tayi masa murmushin
ƙarfafa guiwa sannan ta juya ta bar gurin.

"bariki alalen gero,wato habubakar ni ka maida ƴar iska sabida matarka,to wallahi
ku da kwanciyar hankali se kun miƙomin jikata gareni,baku isa ba wallahi kunyi
tsararo"

Tsugunawa yayi gabanta cikin damuwa da tsantsar takaici yace"inna kullum burinki
shine kiga ina miki biyayya,sabida haihuwata da kikayi,amma ni fafur ƴata kin hana
taga mutuncina ma bare har ayi tunanin zata soni wata rana,kinsa ta tsaneni bata
ganin girmana,inna me nai miki ne da zafi har haka dayasa bakyason kwanciyar
hankalina,nine fa Abubakar ɗinki ɗanki ɗaya tak a duniya,ba ƙya gudun ciwon damuwa
ya kamani nima ki rasa ni shikenan kin huta"yayi maganar hawaye na biyo idonsa.
Sosai jikin Inna yayi matuƙar yin sanyi,jin kalamin na IG tabbas in ya mutu ko ta
shiga uku,dan bata da sauran ɗan da zata nuna a mazaunin nata baya ga shi ɗin.

Hannunta IG ya kama ganin ta ɗanyi sanyin ya kaita kan kujera ta zauna batare da
musun komai ba,ruwa ya kawo mata me sanyi,sannan ya je dinning ya haɗo mata abinci
da zafinsa yasha kayan lambu da naman kaza yazo ya durƙusa agabanta,yasa cokalin ya
ɗebo abincin ya nufi bakinta dashi,seda ta doka masa harara sannan ta amshi
abincin,to dama in banda fitinar Inna ta ɗebo yunwa,dan haka sosai taci abincin da
IG ya zubo matan,ruwa tasha tayi hamdala sannan tace "ina gudaliyata?"tayi tambayar
kadaran kada han.

"inna deeyanah na lagos can na kaita karatu,kuma insha Allahu sun kusa samun
hutu,da zaran ta dawo zaa kawo miki ita tai miki hutun acan"cewar IG cikin dabur
dabur.

"lagos fa kace habubakar?kai ko wacce irin tsana ce kaiwa yarinyar nan daze sa ka
kaita lagos makaranta?"inna ta faɗi cikin faɗa.

"kiyi haƙuri inna,ilimin can yafi nanan shiyasa na kaita ba ƙiyayya tsakani na da
deeyanah har abada sabida ƴata ce kuma ina sonta,bazan taɓa yin abinda ze cutar da
ita ba"cewar IG cikin biyayya.

"habubakar nifa ba kai ne bana so ba,matarka ce bana so ƙiriƙiri ta kashe Aisha
amma ido da addini ka kasa miƙata ga mahukunta su kasheta itama, taya kake tunanin
zan iya ganin farinta har in yarda jikata ta zauna agunta,to wallahi da sake"cewar
inna cikin ɓacin rai.


"inna kinfi kowa sanin maryam ba ta kashe Aisha ba,hasalima taimakonta taje
yi,tsautsayi da ƙarar kwana yasa Aisha ta rasu,to akan wanne dalili kikeso ki manna
alhakin mutuwar Aisha akan maryam,inna kifa tuna zamu mutu muje ga Allah duk abinda
muka tabbatar da bamu da yaƙini akansa abu mafi sauƙi mu watsar dashi dan wucewa
lami lafiya"

Be ida me yakeson faɗiba yaji ta rushe masa da kuka,tana faɗin"habubakar nice
nakewa matarka ƙarya da sharri ko,ni kasa agaba kana wulaƙantawa har haka,ba komai
Habubakar na barwa maryam ɗin kai duniya da lahira tunda ta fini agurinka"

Cikin tsananin tashin hankali,ya zube a gabanta yana magiya kan ta janye furucinta
na cewa ta barwa maryam shi,da ƙyar yashawo kanta ta haƙura ta janye.

Ɗakin saukar baƙi ya kaita da kanshi ya gyara mata gado da duk abinda zata buƙata
sannan ya fito yajawo mata ƙofar.

Gaba ɗaya ya rasa meke masa daɗi,komai ya kulle masa yarasa ta ina ze fara. wannan
wacce irin rayuwace.


*********;

Wata guda inna ta kwashe a Abuja zaman jiran dawowar deeyanah,ba irin
wulaƙanci,ƙasƙanci da cin mutuncin dasu IG basu gani ba agun inna azaman nata a
gidansu.

Ta hanasu saƙat acikin gida sede ko yaushe suna ɗaki,in ba gurin aykiba.dan motsin
kirki sukayi agabanta se tace zaginta sukeyi,ko tace munafuncinta sukeyi.


Ana wannan bidirin ne Deeyanah ta iso daga lagos sakamakon hutun da aka musu.cike
da mummunar manufa ta iso gidan na mahaifinta.

Ga mamakin inna rawar ƙafar da take tunanin deeyanah zatayi in ta ganta setaga
batayiba,dan har wani shan ƙamshi takewa innar.
Hmmmm

Muje de zuwa



Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*To jiya na kammala littafin TAYI MIN ƘANƘANTA,yanzu ga SHIMFIƊAR AURENA na kuɗine
daban yake da sauran,kibiya 500 kisamu damar karantashi har ƙarshe,karki fara baki
samu ƙarashen ba ki soni kiso littafina ki siya ki biya shine soyayya😄*

*Zahra muhammed Nasir 2084024749 UBA*

*07044600044 a turo shaidar biyan ta nan,ta acct kawai banda kati*


*7*


Inna yawo take lungu da saƙo na garin neman Deeyanah tun tana sa ran ganinta har ta
soma fidda rai,zuwa yanzu kuka take wiwi,

Ta shawo kwanar lungun gidansu ta haɗu da Audu ɗaya daga cikin leburorin da aka
ɗauki deeyanah agun su.ganin tana kuka ne yasa yace"Innar Deeyanah lafiya kike
kuwa?"
Cikin kuka tace"Deeyanah ce tunda ta fita da tallah banganta ba,na nemeta har na
gaji"ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka.

"Deeyanah ay tun ɗazu wasu ƴansanda suka ɗauketa takai tallah gurinmu,sun tafi da
ita a motocinsu masu jiniya"cewar Audu cikin yanayi na tausayawa.

Ay Inna bata jira yagama bayaninba ta juya da gudu ta nufi gun isa me waya tana
faɗin"Shikenan gudaliyata Habubakar yakai min ke inda zaa kasheki kamar yadda aka
kashe mahaifiyarki,wayyo ni fatima ina zansa rayuwata ba marainiyar Allah"a haka ta
ƙaraso gun isan,jamaa se kallonta akeyi.

Isa na ganinta ya taso da saurinsa,yana faɗin "inna lafiya kuwa?"bata bashi amsa
ba se cewa da tayi"ka kiramin yaron nan mara mutunci,nace ka kiramin habubakar
yanzun nan"tace cikin ƙaraji.

Jikin Isa har rawa yake ya danna lambar baban Deeyanah.

IG na zaune a falo yaji ƙarar wayar daya ware domin inna,dama yasan zaayi hakan,dan
haka cikin dauriya ya ɗaga wayar.
Isa na jin an ɗaga ya miƙa mata,ay yana bata ta fara da cewa.

"yau na tabbatar da cewa habubakar kai ba jini na bane,wato na hanaka tafiya da
deeyanah shine kasaceta ka kaimin ita inda zaa kashe to wlh cikin daren nan ka
kawomin ƴata"
"Inna kiyi haƙuri amma batu na gaskiya Deeyanah bazata dawo gunki ba sabida tsarin
da kika ɗorata akai,in muka koma ga Allah ni zaa tuhuma game da amanarta da Allah
ya bani,inna ina miki biyayya sede wannan karon Deeyanah ta dawo kenan kiyi haƙuri
ki kwantar da hankalinki"yana kaiwa nan ya kashe wayar gaba ɗaya ya kwantar da
kanshi jikin kujera yana tunanin mafita game da matsalar inna.

Inna ko jin ya kashe ne yasa ta shiga surfa masa zagi tana birgima agurin ita ala
lalle dole se isa ya kaita Abuja.

da ƙyar isa ya rarrasheta yakaita gida,ranar kwana tayi tana kuka,inna uwani tayi
rarrashin har ta gaji.

IG na kashe wayar miƙewa yayi ya nufi ɓangaren yaranshi,ayko suna ganinshi kowa ya
taso yazo ya rungumeshi suna masa sannu da zuwa banda Deeyanah wacce tunda ya shigo
take doka masa harara,gami da taɓe bakinta.

Zama yayi cikinsu yana sauraron kowa da damuwarsa,Abulkhairi ne yace "daddy waccan
auntyn bata da kirki tun ɗazu take ta dukanmu"ya faɗi yana nuna deeyanah.

Ɗago ido IG yayi ya dubi Deeyanar data cika tana jiran ko ta kwana,murmushi yayi
sannan yace "laifi kukai mata,shiyasa ta dokekun"
Taɓe baki tayi ta kauda kanta gefe.

Kallonta kawai IG yake,cikin nuna kulawa yace mata "mamanah ya baƙunci?"ya faɗi
lokacin daya kamo hannunta.

Ƙoƙarin kwace hannun takeyi amma ta kasa,dan haka shuru tayi tana kallonshi,batare
data amsa masa ba.

murmushi yayi yace"cikin satin nan zaki makaranta,ki samu ilimi dan ki koma gun
innarki ki kula da ita"se alokacin tayi magana jin ya ambaci inna,"ni amaidani
gunta banason makarantar,ay sabida rashin makarantar ne yasa ka tsani mamana har
kuka kasheta dan ita bata da ilimin boko,to nima bana son makarantar"

Sosai batun ya taɓa zuciyarshi amma yasan deeyanah bata da laifi me laifin inna ce
dan duk itace ta cusa mata ƙiyayyarshi a zuciyarta.

Be ce komai ba ya saki hannunta yabaro ɗakin yana saƙe saƙe a zuciyarshi.

Muje zuwa
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*na kuɗine ki biya kan ki karanta,dan samun damar karance shi gaba ɗaya 500 ne
kacal*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*A turo shaidar biyan tanan 07044600044*

*10*

Deeyanah wanka tayi taci abinci sannan ta dawo falo ta zauna tana girgiza ƙafa,tana
cika da batsewa.

Inna ce ta shigo jikinta har ɓari yake taje kusa da ita ta zauna fuskarta ɗauke da
murmushi,ta kamo hannun deeyanah tace"gudaliya ta kinga yadda kika ƙara yin kyau
kuwa?"

Yatsina fuska deeyanah tayi sannan tace"ko?"

"Kwarai gudaliya shiyasa nakeso gobe muyi asubancin tafiya kaita,sabida nasan muna
zuwa samari se sunyi kamar su cinyeki"inna ta faɗi tana washe baki.

"ku tafi ina,?ke da wa kuma?"deeyanah tayi tambayar tana ware ido.

"mu tafi kaita mana,ni da ke"inna ta faɗi tana dariya.

Wata shewa deeyanah tayi sannan ta miƙe ta fara juyawa agaban inna tana faɗin"haba
inna yanzu ke ko dole aka miki kan ki tafi dani kaita kya fara,?kuma samari ay nafi
ƙarfin na can sede na nan"ta faɗi tana wani kakkarya jiki.

Baki inna ta saki tana kallonta,da ƙyar ta iya cewa"nufinki ke bazaki koma can ba?"

"yauwa tunda kin fahimta,eh ni nazo kenan bazan koma ba,"deeyanah ta faɗi batare da
damuwar komai ba.

Hawayene ke biyo idon inna,cikin kuka tace"yanzu ni zaki watsawa ƙasa a
ido,deeyana,bafa irin rashin mutuncin da banyiwa mahaifinki ba kan tahowa dake
bada izinina ba"

"kinga inna ina cikin nishaɗi yanzu karki ɓatamin rai,nace bazan koma ba,kibarni
mana,akwai burika da nakeso in cika anan,in natafi taya zanyi hakan,"deeyanah ta
faɗi cikin sigar nuna ƙosawa.

"nima ba inda zani inde ba zaki bini ba"cewar inna tana share hawayenta.

"better"cewar deeyanah lokacin data miƙe tabar falon.

bin bayanta inna tayi da kallo,a ranta ta ce "yaro man kaza"

Deeyanah,ko tana barin gurin,kitchen ta shiga,morning fresh ta ɗauko,tazo ƙofar
ɗakin mummy ta juye shi a ƙasa kan tiles.

Tana gamawa ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin,tana ƙwanƙwasawa ta koma gefe da gudu,ta
ɓoye,Hajiya maryam zuciyarta guda ta buɗe ƙofar,ganin bataga kowa bane,yasa tayi
yunƙurin leƙawa falo taga ko me ƙwanƙwasa ƙofar can ya koma.

Ay tana saka ƙafarta se kan morning fresh ɗin,ayko santsi ya kwasheta,suuuuu ji
kake tim ta daku da ƙasa,ay deeyanah na ganin ta faɗin ta fito daga inda ta ɓoye ta
fara cashewa agabanta tana dariya tana faɗin"faɗuwar guzuma,sede kaji tim tim,"tana
faɗi tana zagaye hajiya maryam wacce ta kasa motsawa bare ta tashi sabida buguwa da
hannunta da ƙugunta sukayi, tana rawa da waƙa.

Wasu hawayene masu zafi suka shiga ambaliya a idon hajiya maryam ɗin.ganin yadda
deeyanah ke mata,akan laifin da na nata ba.

Muje zuwa

Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*


*masu maida novels ɗina Audio kuyi hattara,wahala nake na rubuta,ku kwashe a
bati,ku je kuna neman kuɗi dasu,to kusani duk wanda ya maida littafina audio ya
nemi kuɗi dashi alhalin ni ba siya yayi aguna ba,wallahi bazan barshi ba,zanyi duk
me yiwuwa wajen ganin na bi kadin hakkina,in so kake ka ɗora akwai numbata a book
dina kadauka muyi ciniki kaje kayi neman kuɗinka,wanda akayi a baya wannan ya wuce
amma wlh yanzu ba sani ba sabo*

*Free page daga 1 zuwa 15 ƙoƙarta ki mallaki naki,500 ne kacal,karki bari abaki
labari SHIMFIƊAR AURENA shi daban yake da sauran*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044 A turo shaidar biyan tanan.ta acct kawai banda kati*

*8*


Wasa farin girki,tun inna nasa ran ganin andawo da deeyana har ta fara cire
rai,hakan ne yasa ta fara shirin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login