Showing 1 words to 3000 words out of 10506 words

Chapter 1 - SHIMFIƊAR AURENA by Zahra Surbajo

21 Apr 2026

5

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************



🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*


*Bismillahirrahmanir rahim*

*Wannan littafi na kudi ne ki siya 500 ki karanta,,in kinsan fitarmin dashi zakiyi
to karma ki siya kibar kuɗinki.*

*daban yake da sauran se kin karanta zaki fahimci hakan*

*FREE PAGE DAGA 1-15*

*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044 Aturo shaidar biya ta nan*


*1*



"Prince ya kamata kayi wani abu akan lamarinnan,yin shurunka ne fa ke Ƙara haifar
da tarin matsaloli acikin gidan nan,me martaba kanshi in yaji bazeji daɗi ba in
baka ɗauki mataki ba"cewar Sadeeq
Wanda aka kira da prince gyara zamanshi yayi sannan ya lumshe ido,gami da taɓe
baki,alamun abun be dameshi ba.

Sadeeq bin shi yayi da kallo,baki buɗe,dama yasan baze yi magana ba dan inda sabo
ya saba da halayensa.cikin girmamawa yaci gaba da faɗin.

"Bayyanar video na tsiraicinka ranka ya daɗe abune da masarautarnan bazata iya kare
zubewar mutuncinka ba,ya kamata ka duba batunnan"sadeeq ya sake faɗi cikin damuwa.

Har yanzu idonsa a lumshe suke,bashi da niyyar buɗesu,hakanne yasa sadeeq ya
fahimci bazeyi magana ba yanzu,dole tasa sadeeq miƙewa yay masa sallama sannan ya
fice daga falon.

Ba tare da damuwar komai ba ya gyara zamansa ya ɗauko remote ya sauya tashar da
yakeson kalla,be jima ba ya miƙe cikin takun isa da ƙasaita yabar falon,yana tafiya
kamar wanda aka yiwa dole.

Ƙofar da zata sadashi da ɓangaren mahaifiyarsa ya nufa,fadawa da bayin gida se
zubewa suke ƙasa suna masa kirari,har ya shige ƙofar.

Koda ya shiga bata falon ƙasan,dan haka taka stairs yayi zuwa sama inda yasan ze
sameta,ilai kuwa yana shiga yaganta kishingiɗe,ana matsa mata ƙafa,yayin da
jakadiya ke gefenta tana bata labarai masu daɗi.

Sallama yayi ya shiga,suna ganinshi jakadiya da ɗayar matar dake matsamata ƙafar
suka zube suna miƙo gaisuwa gareshi,ganin mahaifiyarshi na gurinne yasa ya amsa a
daƙile sannan ya zube agaban mahaifiyar tashi yace"barka da hutawa mami"ya faɗi
cikin wani daddaɗan sauti.
Miƙewa zaune tayi fuskarta ɗauke da fara'a tace "Aliyu hydara na kaine da rana
haka?"

Shuru yayi bece komaiba,sema samun guri da yayi ya zauna,ita ta haifi abunta dan
haka tasan halin kayanta.dan haka dubanta takai gun jakadiyya tace"ku ɗan bamu
guri,zan gana da yarima"

Ba musu suka rusuna alamar girmamawa sannan suka fice daga falon.

Suna fita ya rarrafa ya isa gareta,ya kwantar da kanshi a cinyarta,yafara magana
kamar ƙaramin yaro cike da shagwaɓa,"mami don Allah kisa baki Abbana ya barni in
tafi Swizland ɗinnan,bada wasa nake ba na gaji da zama anan please mami"ya ƙarasa
maganar cikin magiya yana jijjiga hannunta.

"Wai Hydar so nawa kakeso a faɗa maka ne,Abban ka yace bazaka koma ba,so yake ka
fahimci shaanin mulki da kyau sabida kaine magajinsa,meyasa bazaka masa biyayya
bane Hydar?"mami tayi maganar tana shafa gashin kanshi dake kwance lub kamar na
larabawa.

Miƙewa zaune yayi ya tattaro dukkan natsuwarshi sannan yace"mami ke
mahaifiyatace,nasan dole kinason farinciki na,kuma duk wani abu daze taɓa mutuncina
bazaki so shi ba"

"wannan hakane Aliyu na"mami ta bashi amsa.

Ajiyar zuciya yayi sannan yaci gaba da faɗin"Mami wata ƙaddara ta faɗo min,ni ba
mazinaci bane mami amma se ga wani video an turomin shi ni ɗin a tsirara tare da
wata yarinya wacce ko saninta banyi ba,ana barazanar sakin videon a cikin
masarautarnan"ya ƙarasa maganar cikin yanayin dake nuna ɓacin rai.

A zabure mami tasa hannunta akan bakinshi ta toshe masa baki wasu siraran hawaye na
biyo idonta.

Rungumeta Aliyu yayi,ya saki wani kuka,wanda tunda abun ya faru be taɓa nunawa kowa
ya dameshi ba,amma sosai abun ya ɗaga hankalinshi matuƙa,gaba ɗaya kanshi a kulle
yake.se yanzu daya iso gaban mahaifiyarshi ne yasamu kukan yazo masa.

Hannunshi taja suka bar falon suka koma ɗakinta,kan gado ta zaunar dashi sannan ta
kulle ƙofar,ta zuge glasan window,ruwa ta ɗebo masa a dispenser me sanyi ta bashi
yasha,ya ɗan numfasa sannan tace cikin rauni.

"Tunda mahaifinka ya bayyana ka a matsayin mejiran gado Hydar nasan ƙalubalen
rayuwane zasui ta tunkaroka,wanda sede ƙarfin addua ne kawai ze warware duk wata
matsala,na yarda da tarbiyyar da nai maka Aliyu,ka ɗauki komai muƙaddarine daga
Allah kuma ze wuce"ta faɗi tana shafa kanshi.

"Mami inaso ne na binciko koma waye yay min hakan,shine yasa nakeson zuwa can ɗin
dan abun zefi sirri"ya faɗi yana ƙoƙarin kauda damuwarshi,dan yasan inde yashiga
damuwa mahaifiyarshi na shiga wacce tafi tashi,kasancewar shi kaɗai Allah ya bata.

"kabar komai a hannun Allah zeyi magani,kabar batun tafiyar tukuna muga me ze
faru"mami ta faɗi cikin ƙarfafa masa guiwa.

Dole ya bar batun tafiyar,ya ɗan zauna agunta ta gama yimasa nasiha da
adduoi,sannan yay mata sallama ya tafi,koda ya baro gurinta babu me cewa shine yay
kuka yanzu sabida ya dawo yarima hydar ɗinsa me cikar isa da ƙasaita.


Muje zuwa


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*DUK WACCE TABIYA BAN SATA BA PLS TAIMIN MGN NA RASA NUMBERS ƊIN KUNE*


*na kuɗine ki siya ki biya ki karanta,kar ki bari aɗauko abaki ki karanta kyauta,na
taka muhimmiyar rawa gurin kawo muku wannan littafin,daban yake da sauran,karki
bari abaki labari,akwai soyayya,abun dariya,ban haushi,tausayi,da abubuwan ban
mamaki,magunguna,da tarin adduoi ma banbanta,domin kariya daga dukkan sharri,salon
iya ba shimfiɗa hakkinta,duk acikin wannan littafi akan farashi 500 kacal,baki da
danasani,asiyansa*

*ga wanda besan marubuciyar ba,to marubuciyar littafin SURBAJO,UMMU AYMANA,KANO TO
JIDDA,DA SAURANSU CE,kowa ko yaji gangami ay yasan da labari😄*

*Zahra Muhammed Nasir 2084024749 UBA*

*Aturo shaidar biya tanan 07044600044, bana adding agroup na faɗi anƙi ji to yanzu
inayi ki turo ɗari biyar ta adding ɗin zan saki,in novel dinama kikeso tsoho ki
turo dari biyar ɗin😊*

*FREE PAGE 1-15*
*2*



Da mahaukacin gudu ta faɗo gidan,da wanke wanke taci karo da ike idonta a rufe yake
sam bata lura ba seda ta faɗa cikin kayan,jikake kwacham,ko tsayawa batayi ba ta
sake fallawa da gudu cikin ɗakin,

Kwance take kan tabarma tana sauraron shiri agidan radio taji,an taka mata ciki an
wuce da gudu,a firgice ta miƙe zaune,dan tasan ko aykin waye,ilai kuwa itan ce,dan
ta hangeta lokacin da take ƙoƙarin shigewa ƙarƙashin gadonta na ƙarfe.

Da sauri ta miƙe jin hayaniya a tsakar gidan ta fito,yara ne maza sun kai su bakwai
a tsaye suna ta haki,kowa rai aɓace.

Gyara tsayuwar ɗaurin ɗankwalinta tayi sannan tace"to me kuma ya faru naganku,tsaye
anan?"inna ta tambaya.

Ɗaya daga cikin yaranne yabata amsa da cewa"Inna Deeyanah ce muna ball tazo ta
ɗauke ta fasa mana,shine mu kuma muka biyo ta ta biyamu".

Ɓata rai inna tayi dan aduniya in akwai abinda inna ta tsana to shine ace ga laifin
Deeyanah."Deeyanar ce zata iya wani fasa muku ball sabida tsabar rashin tsoron
Allah kunbi kun addabi yarinya bata ci muku ba bata sha muku ba to wallahi kuji
tsoron Allah Deeyanah marainiyace in kuka cuceta se kun shiga wuta" ta faɗi cike da
masifa.

"Inna ƙarya suke min,ni ko ball ɗin ma ban gani ba,ina cikin tafiyata suka biyoni
da gudu"cewar Deeyanah daga can ƙasan gadon Inna.

"bari ɓata bakinki,shalele,sharri irin na mutanen garin nan wanne ne ban sani
ba,kuma wallahi zasuyi su bari"Cewar inna.
"wallahi inna ba sharri muke mata ba,ita ta fasa kuma fasasshiyar tana
hannunta,aduba mana"cewar wani yaron kamar zeyi kuka.

"dama ay kai jabiru da ganinka anga munafuki,harda in duba to ubanka zan
duba,kunsan Allah in baku fice daga gidannan ba na lahira seya fiku jin daɗi."inna
ta faɗi tana ƙoƙarin ɗauko ma doki ayko da gudu yaran suka fice daga gidan.

Ɗakin dake kusa da nata ne aka buɗe aka fito,mace ce dattijuwa kamar innar,"kinga
yaya,wallahi kibi rayuwa a hankali,wannan abun da kikeyi ba abinda ze haifar se
lalacewar tarbiyyar Deeyanah,kuma in ta lalace ke kanki bazaki so ta ba"bata ƙarasa
me takeson faɗi ba, Inna ta katseta cikin hargagi da masifa.

"Aniyarki ta biki Uwani,wallahi bakinki yasari ɗanyen kashi,wato fatan ma da kikewa
gudaliyar jikar tawa ma kenan ko,ay dama najima da sanin maƙiyan Deeyanah harda na
gida,to duk zakuyi ku bari,Deeyanah ta tauraruwa ce"cewar inna kamar zata daki
uwanin.

Deeyanah ce ta fito hannunta ɗauke da ball da ta fasawa yaran da suka biyota.
Kallonta inna tayi cike da mamaki tace"gudaliya,a ina kuma kika samo fasasshiyar
ball ɗin?"ta faɗi tana jawota jikinta.


Cikin taɓara da shagwaɓa tace"a ƙasan gadonki mana"

Cikin borin kunya inna tace"au eh anyi haka,jiya na samota nima"tayi maganar tana
satar kallon gefen da uwani take.
Uwani ko salati ta shiga yi tana tafa hannaye tace"yaya kiji tsoron Allah ball ɗin
da aka kawo ƙarar ta akan tace fa yanzu,amma sabida tsabar ɗaurin gindi data samu
shine kikace wai ke kika samo jiya"

"to na faɗi ɗin in da abinda zakiyi kiyi,muje ciki gudaliya ta"inna tafaɗi tana jan
hannun Deeyanah suka shige cikin ɗakinta.


Uwani ko tsananin mamakine yasa takasa cewa komai bare tai yunƙurin,barin
gurin.itade tasan wannan ba gata bane ake mata.

Muje zuwa.



Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*


*na kuɗine ki siya ki biya ki karanta,kar ki bari aɗauko abaki ki karanta kyauta,na
taka muhimmiyar rawa gurin kawo muku wannan littafin,daban yake da sauran,karki
bari abaki labari,akwai soyayya,abun dariya,ban haushi,tausayi,da abubuwan ban
mamaki,magunguna,da tarin adduoi ma banbanta,domin kariya daga dukkan sharri,salon
iya ba shimfiɗa hakkinta,duk acikin wannan littafi akan farashi 500 kacal,baki da
danasani,asiyansa*

*ga wanda besan marubuciyar ba,to marubuciyar littafin SURBAJO,UMMU AYMANA,KANO TO
JIDDA,DA SAURANSU CE,kowa ko yaji gangami ay yasan da labari😄*

*Zahra Muhammed Nasir 2084024749 UBA*

*Aturo shaidar biya tanan 07044600044, bana adding agroup na faɗi anƙi ji to yanzu
inayi ki turo ɗari biyar ta adding ɗin zan saki,in novel dinama kikeso tsoho ki
turo dari biyar ɗin😊*


*FREE PAGE*


*3*


Yau kasuwa,dan haka tun safe inna ke tuyar wainar rogon da Deeyanah zata kai mata
tallah kasuwar.

Farin bokiti aka cika mata da ita,sannan tayo wanka,ta sauya kaya,taci adonta,tazo
inda innar ke suyar.

"Inna gaskiya yau in na siyar miki ɗari biyu zaki bani,dan inaso in biya jimmalo
bashinta na kafi zabo da nasha mata"Deeyanah ta faɗi a tsanake kamar ba ita ba.

"ba komai gudaliya zan baki kede kidawo da wuri kawai"cewar inna tana murza mata
gammo.
Tana gama naɗa mata gammon ta ɗora mata bokitin,tai mata sallama ta fice inna ta
bita da adduar samun kasuwa.

Deeyanah na fitowa ta fara ciniki,ana siya itama tana siyan abun da yay mata daɗi
ba abinda yay mata zafi.

Yaran matane sa'anninta suka tsaida ita,tsayawa tayi tana dubansu cikin alamun
rashin gaskiya,"yauwa yau wa muka kama?"ɗaya daga cikin yaran tace,

Shuru Deeyanah tayi dan bata da mafita yau a hannunsu,

"ko ki biyani kuɗin kafi zabona ko muyi miki na jaki yanzu nan"inji jimmalo dake
ƙoƙarin cakumo Deeyanah.

Cinikin hannunta ta miƙa mata,ayki jimmalo ta amshe suka duddungure mata kai suka
wuce,suna faɗin"shegiya da ido kamar mayya".

Wani lungu Deeyanah ta shiga da bokitin tallan,tai zamanta,bokitin ta buɗe taci
taci ta ƙoshi sannan ta rufe,tana saƙa abunda zata yiwa su jimmalo wanda bazasu
taɓa mancewa da ita ba.

A taƙaice de Deeyanah seda ta cinye wainar rogon tass sannan ta kamo hanyar
gida,bayan tayi birgima acikin jar ƙasa tai futufutu,ta fasa bokitin.

Kuka take kamar ranta ze fita,haka ta shigo gida tana ɗingishi ga hijabinta duk a
yage.
Inna ta tada sallahr laasar kenan tajiyo kukanta,ko sallamewa batayiba ta fito da
gudu,haka itama uwani da hanzarinta ta fito dan ganin meke faruwa.

Inna na hangota tace"Nashiga uku na ni Fatima,na lalace,gudaliyata meyasameki
haka"ta ƙarasa maganar hawaye na biyo idonta,ta ƙarasa ta kamota,ayko sharab ta
faɗa jikin innar tana sakin wani marayan kuka.

Hankalin Inna in yayi dubu ya tashi,dan haka tun kan taji abinda ya sametan itama
take kuka,dan tasan ba ƙaramin iftila'i bane kukan Deeyanah.

Seda suka ci kukansu ma'ishi sannan Deeyanah tace cikin kukan"naje kasuwa na gama
siyar da wainata tass har wani mutumi yace inyi sauri inzo gida in ƙaro ze siya ta
ɗari uku,na taho akan hanya,shine su jimmalo da Hari ƴar gidan sabo kafinta,suka
kamani a hanya suka min dukan tsiya suka kwace kuɗin suka yagamin kaya sannan suka
fasa bakitin,jimmalo harda cewa nida kakata mayu ne"ta ƙarasa maganar tana me sake
rushewa da kuka.

Kamar guguwa haka Inna ta miƙe ta kamo hannun Deeyanahr tana faɗin"duk wanda besan
balai da masifa ba arayuwarsa to Deeyanahr Inna ce be taɓo ba,yau se naga uban daya
tsaya musu a garinnan,zasu san ko waye ubanki a ƙasar nan,ni zaa yiwa iya
shege,taso muje in gwada musu matsayinki"tayi hanyar ƙofar gidan tana surfa zagi.

Da sauri uwani ta dakatar da ita,tace"don Allah yaya kiyi haƙuri kibi komai a
sannu,wallahi ta iya yiwuwa ƙaryar Deeyanah ce,se kinje kuma azo aji kunya"

"munafuka me baƙar aniya,har Deeyanahr ce take ƙarya,to wallahi ko ƙarya takeyi yau
se sun san matsayinta,dama ay ke ba ƙaunarta kike yiba ba abinda bazaki faɗi
ba"tana kaiwa nan ta fincike tayi wucewarta riƙe da hannun gudaliyar tata.

Suna fita kai tsaye shagon Isa me saida waya suka nufa.yana ganinsu ya miƙe da
hanzari,yace"subuhanallahi,Inna me yasamu Deeyanah naganta a haka?ko mashin ne ya
buge ta?"yayi maganar yana ƙarewa Deeyanahr kallo.
"wanne mashin Isa,jimmalo ƴar gidan me gari,da yarinyarnan hari ta gurin sabo
kafinta,sune suka haɗu suka mata wannan dukan suka kwace kuɗin tallan ta,sannan
sukace nida ita duk mayune,Isa ka duba fa kagani,wallahi bazan yarda ba"inna ta
faɗi cikin tsananin masifa kamar isan ne ya mata laifin.

"to inna ande bincika ko an tabbatar da afkuwar lamarin?"isa ya tambaya a ɗan
tsorace.

"binciken uban me zan tsaya yi bayan abinda idona ya gani kuma kunne na yaji,kai ni
banson wannan maganar dan ba ita ta kawoni ba,maza ka kiramin,Habubakar a waya
yanzunnan kabani shi"ta faɗi cikin faɗa.

Ba musu Isa ya danna lambar mahaifin Deeyanah,bugu ɗaya ana biyun ya ɗaga,cikin
girmamawa isa yaɗan rusuna ya gaisheshi sannan yace"ranka ya daɗe,dama innace
zatayi magana dakai"

Inspector general of police Abubakar Adamu Kaita,shine Mahaifi ga Deeyanahr Inna.

Yana tsaka da meeting da kwamishinonin sa ne wayar isa ta shigo,yasan kiran na
Mahaifiyarsa ne,dole ya tsaida taron ya fito don amsa kiran,dan ita kaɗai yake waya
da ita a wayar shiyasa ko yaransa be ba wayar koda yaushe tana tare dashi.

Miƙawa Inna wayar isa yayi ya koma gefe.

"Habubakar ina son ganinka ne yau yau ɗinnan base gobe ba"cewar inna batare data
amsa gaisuwar da yake mata ba.

Dafe kanshi IG yayi da yay mugun sara masa,ga shugaban ƙasa yabashi wani
assigment,ga shi Inna tace yazo yau ba gobe ba,cikin biyayya yace"inna zuwan nawa
nada muhimmancine a yau,kece ba lafiya ko takwarar taki?"

"Ban sani ba nade ce kazo,in kuma bakazo yau ba wlh seka haɗu da fushina"tana kaiwa
nan ta cillawa isa wayarshi ta ja hannunta suka koma gida.

Isa be ce komaiba ya kwashe wayar a ƙasa ya koma bakin kasuwancinshi.

Ɗakin taron IG ya shigo,cikin yanayin damuwa yace "kuyi haƙuri wani uzurin gaggawa
ya sameni yanzu,sede ku kasance cikin shiri,ƙarfe goma na daren yau zamu sake
zama,zan yi ƙoƙarin dawowa akan lokaci".



Fatan alkhairi sukai masa sannan ya fice masu tsaron lafiyarsa suka mara masa
baya,kai tsaye airport suka kaishi,kamin ya ƙaraso an shirya pjet ɗin daze
kaishi,be jima sosai ba suka ɗaga zuwa katsina.


Tafiya ce ta sauri,shiyasa yana sauka a katsina yace sukaishi kaita a helicopter
kawai,ba musu akayi kamar yadda ya buƙata.



Muje zuwa.


Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*


*na kuɗine 500 kacal kibiya kisha karatu,update biyu arana insha Allahu,ze ƙayatar
daku masu karatu*

*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*a turo shaidar biya ta nan 07044600044 whatsapp*


*4*


Filin ball na garin ya sauka,kasancewar ba nisa zuwa gidan innar daga gun a ƙafarsa
ya tako,masu tsaron lafiyarsa na take masa baya.
Yayin da mutane suka taru suna kallon shi,duk inda ya wuce se ya ɗaga musu hannu
gamida sallama,har ya iso gidan na mahaifiyarsa,wanda har kwanan gobe yana baƙin
cikin zamanta acikinsa.

A tsakar gida ya samesu su duka har da Inna uwani,cikin ladabi ya tsuguna agaban
inna yace "inna barka da yammaci mun sameku lafiya?"

"Da baka same mu lafiya ba zaka ganmu ne"inna ta bashi amsa kamar zata dakeshi.

Shuru yayi ya duƙar da kanshi ƙasa,a hankali ya furta"kiyi haƙuri inna"

"ka riƙe haƙurinka,ba shi na kiraka ka ban ba,Deeyanah tace wasu yara agarinnan
suka kama suka daka,taƙamarsu bata da galihu har da cewa ni da ita mayune,to yanzi
base anjima ba inaso kasa ƴan sanda su wulaƙanta min su a gaban Deeyanah dan ranta
yayi fari"ta faɗi tana huci kamar kububuwa.

Ɗago kai yayi da sauri ya dubi mahaifiyar tashi sakamakon jin maƙasudin kiran nasa
tun daga Abuja zuwa kaita.
Dubansa ya kai gun Deeyanah,dake rakuɓe a gefen inna tana ware ido alamun rashin
gaskiya.take ya fahimci batun akwai ƙarya acikinsa.

"inna kin tsaurara bincike sosai kuwa kar azo ayi abunda zaa ji kunya,tunda de
kinfa Deeyanah ba kunya ce da ita ba,kar aje ko laifin tane"IG ya faɗi cikin
girmamawa.

"binciken uban me zanyi habubakar,wato ƙiyayyar da kakewa uwar Deeyanah kakeson
maida ta kan ɗiyarta marainiya,to wallahi kayi kaɗan kayi tsururu, kuma ay ba
shawarar ka na nema ba bare kace zaka tsaramin yadda zaayi,umarni na baka ka
aykatashi yanzu"

Miƙewa yayi jiki asanyaye yace "Deeyanah zo muje kuje da jamian tsaro akamo yaran
da kukai faɗan"ba musu ta bishi suka fice agidan.

Cikin mintunan da basufi goma ba jimmalo da hari suka bayyanah agaban Deeyanah da
inna,

Binciken abinda ya faru yayi ,Deeyanah tayi wiƙiwiƙi.
Tsananin takaicine yasa ya kasa magana,dan haka miƙewa yayi ya fice daga gidan ko
sallama beyiwa Innarba.
Muje zuwa



*Assalama alaikum*

*Ina mata ma'abota son gyara nazo muku d hadaddan maganin Gyaran breast sadidan*

*Y'r uwa maza garzayo maganinmu* *ingantaccene nono ko yakai silifas kwanciya insha
Allah kikai amfanid maganinmu zakiga aikinsa mace sai d gyara nono shine martabar*
*mace*

*Maganinmu yana ciko d breast su tashi suyi bul bul a 1week maganinmu Bashi d side
effect*

*Maganinmu masu yaye suna amfani dashi y'anmata kowa zai iya amfani dashi mata
adaure adinga gyara ki kankaro mutuncinci*

*WhatsApp 08063114606 Call08120337219*
*Location: Kano*

Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHIMFIƊAR AURENA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*


*Shawara karki soma karantawa in baki biya ba gudun ya ɗauko daɗi ba ƙarashe😄ki
siya abunki kai waye,akan kuɗi 500 kacal,babu danasani awannan littafi,kisiya muyi
tafiyar nan dake,munayin ki over surbajo,to nide banga alama ba😄tunda kinƙi siyan
littafina kina jiran na kyauta*

*Zahra Muhammed Nasir 2084024749 UBA*

*A turo shaidar biya tanan 07044600044*


*5*



Takaici da baƙin ciki ne yasa IG wucewa batare da yayiwa inna sallama ba,ace akan
shirmen banza ataso shi tun daga Abuja zuwa kaita dan kawai yaji ƙarya,kai gaskiya
inna bata masa adalci.

A nata ɓangaren inna borin kunya ta shiga yi tana faɗin"da basu dungure mata kan ba
ay da bazatace su ɗin bane,"

Uwani dake gefe tana kallon ikon Allah ajiyar zuciya tayi tace "kowa ya biye zuciya
zeyi dana sani,Allah ya kyauta"tana kaiwa nan ta miƙƙe ta shige ɗakinta.

Inna maimakon tayiwa Deeyanah faɗa,rungumota tayi jikinta,tana shafa kanta
tace"barsu gudaliyata duk zasuyi su bari,ke ɗin dashen Allah ce"

********

A can Abuja ko IG daya koma ɗage zaman dayace zeyi yayi zuwa kwana uku masu
zuwa,dan gaba ɗaya baya jin daɗin jikinshi.

Zaune yake a falon shi yana duba jaridun da aka kawo mishi kasancewar yau saturday
yana gida.

Hajiya maryam ce ta shigo falon cikin wani leshi daya gaji da haɗuwa,tayi
kwalliyarta data ƙara fito da kyanta.

Gefen mijin nata taje ta zauna ta langaɓar da kai gefe,dake nuna tana cikin damuwa.

Ɗago kai IG yayi ya dubeta,cike da kulawa ya ajiye jaridar hannunshi ya kamo
hannunta dayasha jan lalle yace "ya akayi ne gimbiyata?,menene matsalarki?"

Kwantar da kai tayi kan kafaɗarshi tace cikin muryar shagwaɓa"Abban Deeyanah,yanzu
fisabilillahi haka zaka zuba ido

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login