Showing 21001 words to 24000 words out of 41207 words
Chapter 8 - Aisha Saddiqa Part 1 by Sumayya Takori.pdf
fara ‘match’ din.
‘Umpire’ (mai bada umarni/alkalin wasa) ya duba lokaci a agogonsa, yaga lallai lokacin da
aka saka domin farawa ya cika, karfe hudu na yamma ta cika daidai (agogon kasar Argentina).
Sai kawai ya kada kararrawa… and the match begins marvellously (wasan ya fara da
matukar ban sha’awa, da burge idanun dubban masu kallo matuka gaya), masu gani physically
cikin ‘yan kallo da masu gani virtually.
Abin takaici Dokin kowa ya tafi, amma nasa Dokin bai ko motsa ba, sai ya tsaya yana kartar
kasa cikin ‘yan mutsu-mutsu da alamu na kin son tafiya, babu gaira babu dalili kuma, hasali ma
dai Doki Saheeb bai taba yin irin haka ga ubangidansa ba tunda ya mallakeshi.
Wanda hakan ya bashi mamaki, at the same time ya kuma fusata shi matuka. Da kakkausar
muryarsa ta ‘yan Polo, wadda ta fito very harsh and unpleasant (raspy voice) yace da dokin
nasa;
“SAHEEB!!!”
Saheeb din yayi haniniya cikin amsawa, amma bai tafi ba. Ya kara cewa da sauti mai karfi
fiyeda na farko “SAHEEB, Go!”. Wanda hakan ya zama fusataccen umarni na biyu ga Dokin da
aka kira da suna “SAHEEB” abinda bai taba faruwa ga Dokin ba (ubangidansa yayi masa
umarni sau biyu). Shi kansa dokin sai ya rikice. (Thoroughbred Horse) ne wato haihuwar
Argentina kuma acan aka raine shi har ya girma, mamallakin nasa ya kwashe shekaru yana
kiwata shi cikin gata da kula da lafiyarsa da tsaftar jikinsa da akaifarsa, kasancewarsa (favourite
horse) dinsa cikin duka Dawakan da ya mallaka a (stable) din dake Ranch House dinsa (wajen
kiwon Dawakai a jere cikin gidan gona).
Ba Saheeb ne kadai Dokinsa ba, Dawakan hawansa sun kai shida, amma shine na gaban
goshinsa, babu mai ganin soyayya da gatan da Saheeb ke samu.
A ka’ida duk bayan shekaru biyu sai ya sake lafiyayyen Doki, amma shi wannan da ya kira
“Saheeb” abokinsa ne da bai taba sake shi ba, kula yake da shi kamar dan cikinsa, kasacewar
ya fito daga hannun daraja, wato hannun Kakansa da yake matukar so (dattijo mai ran karfe),
tun lokacin da Kakan nasa yayi masa kyautar sa har kawo yau yake son Dokin sosai. Kakansa ya saya masa Dokin ne a wani zuwa da yayi musamman har kasar Argentina da
kansa, don ganewa idonsa yadda babban jikan nasa yake gudanar da wasan nasa na Polo, a
lokacin gasar ‘World Polo Championship’, wanda shima an gudanar dashi ne anan kasar
Argentina. Haka yake bata lokacinsa da aljihunsa wajen kula dashi da lafiyarsa, kamar yadda
yake kula da tasa lafiyar.
Abincin da ake masa cusa dashi daban dana sauran Dawakai ‘yan uwansa, haka yanada
kwararren Vetrenary Doctor dinsa (likitan dabbobi), wurin kwanan Saheeb na musamman ne
cikin duka Dawakansa.
Saheeb yana kwana ne a cikin korran ciyayi masu taushi (pitch grass) dake cikin (stable)
dinsa.
Mai kula da taje gashinsa da rage shi da gyara shi da yankan kumbarsa zaman Dokin yake a
gidansa dindindin, ma’aikaci ne specialist akan raino da kula da Dawakai yake zaman albashi
domin kula da Doki “SAHEEB” a (ranch house) din mamallakinsa shine Pareto.
Albashi na musamman Pareto yake lamushewa daga aljihun maigidansa don kula da
hamshakin Dokin nan nasa (Saheeb).
Shi wannan saurayin Ba’ajantine (Pareto) wani kwararren ‘Horse Breeder’ ne, wanda yayi
karatunsa da kwarewa musamman akan kiwon Dawakai da kula dasu.
**** **** ****
Umarni na biyu wanda ya fito cikin matukar fusata daga Ubangidansa, da dukan da yayi
masa da sandar Polon dake hannunsa (polo mallet), shi ya sanya Doki SAHEEB yin fitar kibiya
don bin umarnin ubangidansa, ya daddage ya taka a guje, yabi bayan sauran Dawakan har nan
da nan kamar kiftawar ido ya cimmasu. Daganan mahayan suka saki ragamar Dawakan a guje, da wani irin gudu mai gigitarwa.
‘Helmet’ din dake kan kowannensu, wadda ta rufe rabin fuskokinsu ta bar rabi a waje, shi zai sa
ka gane cewa Abdulrasheed (Kehinde) shikadai ne bakar fata dan Africa a cikin su, kuma dan
kasarmu ta “Najeriya” mai wakiltar hadakar kasashen Africa ta yamma a ‘tournament’ din. Baka jin komai na tashi daga bangaren ‘yan kallo (sashen ‘yan Africa) sai ‘applause’ na kiran
sunansa da fito da usur, cikin ambaton “…. PRINCE!!! PRINCE! PRINCE!” Suna masu daga
masa hannu cikin tarin kauna da bada karfin guiwa…. As he started to lead the match now….
wato ya zamo shine akan gaba, dokinsa ya yiwa sauran fintinkau, duk da kasancewar dokinsa
yayi jinkiri da farko, amma daga bisani dokin gudu yake baya ko sassautawa kamar ma ya fita a
hayyacinsa sabida sabo da yayi jinkiri, gudu kawai SAHEEB yake zubawa kamar zai tashi sama
dashi, har shi da kansa ya sha jinin jikinsa cewa gudun da Saheeb yake yi yau ya zarta kima.
Gab da zasu isa ‘goal’ ne mummunan tsautsayin mara dadin ji da gani mai muni sosai ya
afku.
Taki kadan kafin isar su ga ‘goal’, PRINCE ya fado kasa daga dokinsa ji kake timmm!
Sakamakon faduwar bazata da dokin nasa Saheeb yayi, alhalin yana gab da isa ‘goal’.
Nan da nan hankula suka tashi, ‘yan kallo suka mike tsaye cikin alhini, Alkalan gasa ma haka
suka dakata, aka kawo gado nan da nan aka dauke shi daga wajen zuwa asibiti, bayan an fara
bashi duk wani taimakon gaggawa tun a hanya kafin a isa asibitin dashi.
Karo na sau ba adadi da faduwarsa a Doki, a duka tarihin hawa dokinsa tun na kuruciya, bai
taba faduwa yaji rauni irin na wannan karon ba, Saheeb ya raunata shi sosai, bayan kwashe
kusan shekaru masa dan dama yana wasan Polo dashi a wurare daban daban cikin kasar
Argentina. Duk da bashi kadai yake hawa ba, wato wani zubin yana hawa wasu Dawakan bayan
Saheeb kuma lafiyayyu kamarsa, amma ya camfa cewa yafi jin kaimi da sakewa da nishadi idan
ya hau shi don yin wasan Polo, kuma yafi samu nasara idan Saheeb ya hau. Ko babu komai ya
fito ne daga hannu mai albarka, hannun Kakansa Sarki AbdulRasheed Akanni. Playing Polo has been the hobby of his life. Ya sha cin kofin zinare a wasan ‘polo’ a ciki da
waje, a garuruwa daban-daban na kasashen duniya.
Don haka wannan faduwar bazata da ta faru yau da Prince, ba ‘yan Africa kadai masoya
Prince ta dagawa hankali ba, har dasu Turawan na Ajantina, wato (host country) na wasan da
ake gudanarwa, da mahukunta gasar na kasar ta Argentina.
Wani hamshakin asibiti mai zaman kansa aka kai Prince AbdulRasheed yake zaman jinya a
can ba nisa da gidansa.
Zaka yi mamaki in kaji cewa, duka raununnukan nan da yaji a jikin sa, har da karaya a kafa
da hannu, sabida ba karamin faduwa yayi ba, domin Dokinnan sai da ya wulwula shi a sama
sannan ya tika shi da kasa, amma raunukan nan basu dame shi ba, haka zugin ciwon su bai
dami Prince Abdulrasheed ba, kamar subucewar kofin gasar nan, na ‘champion’ din duniya a
POLO daga hannunsa.….
Wanda da wannan tsautsayin bai faru ba, ya saka ran zai kai shi ga attaining 10+ goal polo
handicap (highest rank of the world’s polo player).
**** **** ****
BANANA ISLAND, LAGOS
P
rincess Fatima, ta shigo da dan saurinta tana cewa da mahaifiyarsu Hajiya Sappa.
“Ni me ya faru da kunnen Nenne na ne? Anata kiran ki a waya tun dazu kina kallonta ido
hudu amma dagawa ta gagara, halan baki ji kiraye-kirayen bama Nenne?
Tun daga falo nake jiyo ringing din wayarki ba kakkautawa. Nenne meke damunki haka yau?
Tun safe nake ganinki haka sukuku (moody) cikin tagumi da damuwarnan, duk kin birkice”.
Princess Fatima, ta karasa shigowa dakin na mahaifiyar su cikin shiga ta alfarma ta ‘ya’yan
manyan sarakuna, ta fadawa mahaifiyarta Nenne Sappa kalaman cikin taushin murya, Nenne
dake gyangyadi akan dardumar data yi sallahr walha ta dago tana duban Fatima fuskarta fal
damuwa. A hankali ta bude ido sosai daga lumshewar data yi musu ta dubi doguwar diyarta
Gimbiya Fatima, kyakkyawa ta karshe, wadda ke tsaye a kanta da wayar Nenne din a hannunta
data sunkuya ta dauka a gabanta, har zuwa lokacin anata kira ba'a daina ba.
Da sauri Nenne tace “Miko min wayar, Allah yasa shine, bana cikin nutsuwa Fatima,
saboda yau kwana biyu bai kira ni ba, gyangyadinnan da kika ga nake yi mafarkinsa nakeyi a
cikinsa, wai bashi da lafiya, dadin dadawa tun shekaranjiya rabon da ya kira ni, abinda bai taba
yi ba, jinkirta kira na a duk yanayin da yake ciki (koda kuwa ace yana kan Doki ne)”. Fatima ta mika mata wayar, sannan ta zauna a gefe tana bata labarai. “Nenne jiya ne
‘Championship Tournament’ din su Hammah fa, a can Argentina, bashi da lokacin kansa kin
sani. Na so inje kallo physically Dade (Baba) ya hanani, tun dazu kuma na kunna ‘PoloLine.TV’
ba’a nuno gasar ba. “I am worried too”. Ta karasa fada da harshen yarbanci. Wato itama cikin damuwar take
kwatankwacin ta mahaifiyarsu.
Ba tareda ta amsawa Fatima maganarta ba Nenne ta amsa wayar da ake tayi mata ba
kakkautawa da sallama cikakkiya irin tata ta nutsuwa, ta hanyar nemawa wanda ya kirata
amincin Ubangiji ba tare da ta san cewa katon Bayahude bane ke kiranta ba musulmi bane ba
kuma Dan nata ba, duk kuwa da cewa da lambarsa aka kira ta. A wayar aka shiga yiwa Nenne bayani da harshen da ba ganewa take yi ba, wato yaren
“Araucano” na Argentina.
“Sunana Pareto Danny, ina magana daga wayar ubangidana, ya samu tsautsayi ne… muna
asibiti, inason magana da Mother dinsa…”.
Don haka sai kawai ta mikawa Princess Fatima wayar cikin yamutsa fuska tace “ungo nan
Fatima, kiji me wannan yake fadi haka?”.
Ba don ma taga lambar ta Ajantina bace da bazata amsa kiran ba, a ka’idarta Nenne Sappa
bata amsa bakuwar lamba, amma kasancewar ta san cewa AbdulRasheed yana can, kuma yau
kwanaki biyu kenan tana alhinin rashin kiran wayarsa da bata samu ba kamar kullum, domin
duk halin da yake ciki baya kasa kiranta kona minti uku ne, shine yasa ta amsa wannan kiran da
gaggawa don jikinta ya bata ya shafe shi.
Maganar mintuna kusan uku Princess Fatima tayi da Pareto a wayar, ta fahimci me yake
kokarin sanar dasu, wato Prince ya fado daga Doki, ya jikkata fiyeda koyaushe, yana asibiti a
kwance da karaya a hannunsa, don haka Fatima sarkin raki sai kawai ta saki wayar a kasa ta
dora hannuwa aka ta sakawa Nenne kuka.
Kasancewar Fatima mai tsananin so ga Yayan nata kuma mai saurin kuka. Suna son
junansu suna kula da juna shigowar bare cikinsu ne dai karbarsa sai a hankali. Nenne nata
tambayarta ta gaya mata me aka ce mata?
Da kyar, kafin Fatima tace cikin hawaye “Nenne Hammanmu wai, ya fado daga Doki yaji
raunuka a jikinsa, yana asibiti can a kwance, an kira Dade a gaya masa ba’a sameshi ba shine
aka kira ki”.
“Subhanallah!”
Inji Nenne, cikin kidimewa da mikewa tsaye, tana cewa “wannan DOKI!” Nan dai ta nemi
fulatancin da take gwadawa akan AbdulRasheed sau tari yau ta rasa, Nenne bata jure rashin
lafiyarsa ko kadan, duk da yana jimawa bai fadi a doki ba amma ko ya fadi baya jin wani ciwo
na azo a gani, yaushe rabon ace yana kwance a asibiti ma ta manta koda ya fado daga Doki bai
taba kwanciya asibiti ba sai dai ya sha maganin ciwon jiki yakwanat zuwa wayewar gari ya
shiga harkokinsa, bait aba samun mummunan wani rauni ba.
Cikin damuwa ta ce da Fatima tayi mata ‘booking flight’ mafi kusa, tace da kanta zata tafi har
can ta yi jinyarsa, tunda dama duk suna da Visa na shiga Argentina sun saba zuwar masa
koyaushe suke so.
Kasancewar a kasar Argentina Prince AlbdulRasheed ya mallaki gidan kansa (Ranch
House) mai ‘field’ na ‘Polo’ a cikinsa.
Iyayensa, Taiwo da danta na fari Hakeem (kafin a haifi Kiki) da kannensa mata ‘yan biyu
Firdausi da Fatima, na yawan kai masa ziyara gidan, kafin ya samu aiki a Qatar refinery y araba
rayuwarsa gida biyu tsakanin Qatar da Argentina. A Qatar Penthouse gareshi wanda bai kai
girman gidansa na Argentina ba kuma babu Dawakansa acan. Sai Princess Fatima tace itama don Allah zata bi Nenne gun Hamma suyi jinyar tasa tare,
tace bazata iya zama a gida ba, alhalin bata san halin da Hamma ke ciki ba, damuwa zata
isheta, don haka suka fara shirin tafiya itada Nenne.
Princess Firdausi kadai da masu aikinsu aka bari a gidan, don ta jira dawowar Dade ta kuma
kula da gida wato ta jira mahaifinsu da zai dawo a satin, kada ya dawo gidan babu kowa kuma
agidansa kawai yake cin abinci, wanda shima ya tafi nasa ‘medical check up’ din ne na lalurar
sugar dinsa a Egypt. Wani abun burgewa da wannan gidan nasu Prince Abdulrasheed shine tringualism dinsu;
Babu irin yaren da bazaka ji anayi a gidan su AbdulRasheed ba cikin manyan yarukan nan uku
su da iyayensu biyu da kannensa mata, tsakanin Hausa, Fulatanci da ‘native language’ na
Babansu wato Yoruba, duk babu wanda basa ji, kuma babu wanda basa yi, wato babu wanda
basa yarawa a junansu.
**** **** ****
THE PRINCE
N
enne Sappa da Princess Fatima sun sauka lafiya a kasar Argentina a wani marece na tsakiyar
winter season, ana tsaka da tsuga yayyafin kankara. Nenne Sappa sanye da Hijab dinta ruwan
kasa-kasa daga samanta har kasa, yayinda Princess Fatima ke sanye cikin wasu ‘Blue Royal
Outfits’ masu kauri.
Kamar yadda aka riga aka tsara hakan ce ta kasance; yaronsa Pareto shi yazo ya daukesu
da wata kankanuwar motar Abdulrasheed din (Alfa Romeo), daga filin jirgi zuwa asibitin da
yake, Pareto yayi musu jagora har dakin da Prince yake a kwance yana jinya a asibitin kashi.
Sanda suka shiga dakin barci yake yi sadidan, don zugin hadewar kashi ya ishe shi,
hakan yasa aka yi masa allurar barci don ya samu sa’ida ya kuma huta azabar.
Nenne da Princess Fatima, suka taka suka isa gareshi suka tsaya a kansa suka kura masa
ido, suna kallon kyakkyawar fuskarsa (with great affection) da alhini cikin idanunsu, daga bisani
duk suka aje mayafansu akan kujera don yin alwallah su sauke sallolin da suka riskesu a
hanya. Har suka yi sallah suka idar duk AbdulRasheed yana barci na karfin allura baima san da
zuwan nasu ba.
Pareto wanda shi yake kula dashi a asibitin kafin isowar ‘yan gidansu, shi ya kawo musu
abinci na alfarma daga ‘restaurant’ din asibitin, daga cikin provisions din da aka yiwa Engnr.
AbdulRasheed, duk irin abincin da yake so shi asibitin zai bashi, haka wadanda ke tare dashi
don kula dashi. Sai magriba ya farka, yana bude ido a hankali, ya yi tozali da Nenne a gefensa tana
sallah, Nennensa, daidai lokacin data sallame sallahr, wani kyakkyawan murmushi Prince ya
saki yana fadin,
“welcome my Nenne, saukar yaushe haka babu zato? What a surprise!”
Sannan ya yunkura ya tashi zaune da kyar, ta mike daga kan dardumar ta gyara masa filo a
bayansa yadda zaiji dadin jingina sannan taja kujera daidai kansa ta zauna, shikuma ya
gaisheta cikin harshen Yoruba. Ita kuma sai ta mayar masa cikin fulatanci, haka sukeyi daman,
in sun yi mata tana ji amma bata mayarwa, don har gobe Nenne jefi-jefi take yin yaren mijinta
da ‘ya’yanta, tafi rike nata da kyau. Bata son yadda yaranta suka fi yin na Babansu suke kin yin
nata, ba kuma don basu iya ba saidon sun fi girmama nasu.
Nenne ta koma kujerar daidai kanshi ta zauna, ta dubi yadda ya sha daurin bandeji
waje-waje, hannu da kafa duk karaya, tayi kwafa cikin damuwa da takaici ta ce.
“Isn’t this enough Hammansu? Ni na tabbata yadda ka