Showing 39001 words to 41207 words out of 41207 words

Chapter 14 - Aisha Saddiqa Part 1 by Sumayya Takori.pdf

uwa don kada abata
zumunci in ya jingine musu ‘ya’ya saboda Polo.
Ta rasa abinda zata ce da Uban kasa, a karshe ta samu bakinta yana bashi hakuri, tana fadin
ta yi wa AbdulRasheed mata, kuma anan Gombe, sannan cikakkar bafullatana diyar dattijai. In
sha Allahu data koma Lagos zata gabatar da maganar ga mahaifinsa.
Uban kasa bai ce a’a ba, duk da yafi matukar son Abdulrasheed yayi aure a cikin gidansa,
saidai ya nemi jin su waye iyayen yarinyar data ke ikirarin ta samar masa ta kuma fada masa,
yace zai yi bincike akan Malam Yunus din da sana’arsa da gaggawa.
Ba’a kwana ba, ba’a yini ba saida komai na Malam Yunus ma’aikacin hukumar Alhazai
tsohon malamin federal government na jihar Gombe ya zo kunnen Uban kasa har asalinsa, duk
wata shaidar arziki da kyakkyawar nasaba malam Yunus Hamza da maidakinsa Haj. Zainab
Hamza sun gama samun ta a unguwarsu Jeka da fari. Sunyi waya da Haj. Zainab a ranar da zata wuce Lagos bayan an sallamesu daga FMC cewa
tana tafe a hanya zuwa gidan Malam Yunus.
Yau ko fita Abba bai yi ba, yana jiran zuwan Haj. Zainab. Bakuwar da matarsa take ambata
da alkhairi kamar tafi kowa kirki da darajta dan adam a duniya.
Nenne ta iso wajejen karfe goma na safe don taredasu ma ta karya kumallo da kunun gyada
da kosai mai zafi a falon Haj. Zainab.
Aisha na daki tana ta kumburi, Ummah tace wai zata bi kawarta Lagos tayi hutu kuma taga
likita.
Tunda Aisha take a duniya bata taba barin garin Gombe ba, kai ko Azare bata taba shiga ba

banda Billiri makaranta, balle akai ga kwana da wani wuri da ba makaranta ko dakin ta ko na
Ummanta ba.
Aisha akwai makon UWA, irin yaran nan ne da gasu dai sun girma, amma kamar yaran goye
suke agaban iyayensu mata, ko kusa bata son gusawa daga jikin Ummanta.
Amma yanzu maganar zata je tayi sati biyu a Lagos ake yi. Tun jiya da taki hada kayanta
Umma da kanta ta hada mata. Tana ta lallashin ta da cewa Haj. Zainab bazata roki alfarma ta
kasa yi mata ba. Kuma dai lafiyarta ake son ingantawa.
Budar bakin Aisha sai cewa tayi (cikin alamu na karyewar zuciya da damuwar cewa yau
Umma tace zata tafi wani gari ta kwana ba tare da ita ba).
“Amma dai Umma kinsan ba yau na fara ciwona ba ko, wane irin likita ne ban gani ba?
Kuma Umma kin dai san Asthma bata da wani magani bayan inhaler ta da wadanda nake sha
yanzu ko?”
Umma ta girgiza kai itama ranta a dame da damuwar Aisha tace “babu ciwon da bashi da
magani sai tsufa sai mutuwa kinji ko Petel, shi magani dace ne, shin Siddiqah in baki koyi shiga
mutane yanzu ba sai yaushe ne?
Ko wajen yan uwana ko na Abban ki ba kya yarda ki je ki kwana, kada ki manta watarana
aure ne zai raba mu gabadaya”.
Ai kuwa Aisha ta balle da kuka tana fadin “Umma in kika sake cewa zamu rabu in nayi aure
to bazan yi auren ba har abada”.
Umma na dariya tace “to ai Ishaq din bazai yarda ya daukemu mu biyu ba, mun yi yawa a
gidan Ishaqa”.
Aisha ta hau rantsuwa, kan cewa sun dade suna kulla alkawari itada Ishaq cewa in yayi kudi
ya tashi ginin gida zai ginawa Umma daki a gidan sa, in ba haka ba bazata yi auren ba”.
Umma abin ya bata dariya sosai, da yake lallabata take don ta yarda ta bi Hajiya Sappa sai
tace toh ya isa haka ta ji, ta kuma amince ita din itace ‘yar zaman dakin Petel (Siddiqah)”.
Suna daki suna dambarwa ita da Aishah Haj. Zainab na can gaban Malam Yunus a falonsa
tana gabatar masa da uzurinta na nemawa tilon dan ta wanda a cewarta ya manyanta auren
Aisha-Siddiqah daga mahaifin ta Malam Yunusa Hamza.
Tace masa in ya amince da ta koma Lagos zata sanar da mahaifin Abdulrasheed, cewa tayi
masa matar aure a Gombe, ba jimawa iyayen Abdulrasheed maza zasu zo da komai na dukiyar
aure, basa bukatar komai, amarya kawai za’a basu su dauka.
Malam Yunus ya hau zufa nan take, sabida kwarjinin da Nenne Sappa tayi masa sai ya kasa
cewa kai tsaye bazai bayar ba, yasa habar taguwarsa yana share zufa daga goshin sa daya
tuno irin soyayya da shaquwar dake tsakanin Ishaq da Aisha, ya kauda idonsa daga kwarjinin
Nenne yana fadin “akwai wanda ke neman aurenta tun tana kankanuwa, amma ban tari
hanzarin ki ba inna tambayi cewa shi Abdulrasheed dinne ya ga Aisha yace yana so?
Ko kuwa shi Abdulrasheed ne yace a nemo masa matar aure? Ke kuma hakannan kika ga
dacewar zaba masa Aisha-Siddiqarmu?
Nenne Sappa ta saka habar mayafinta tana share hawayen da suka kawo mata a idon ta, ta
kwashe labarin su kaf ta baiwa Malam Yunus, da yawan shekarun AbdulRasheed a duniya
amma bai taba aure ba.
A karshe ta gaya masa halin tsangwamar da take fuskanta daga dangin mijinta akan rashin
auren Prince, kowa ya bude baki laifinta yake gani, sabida mijinta baya son laifinta, da yadda

take raba dare bata barci saboda damuwa da addu’ar Allah ya yanke masa, in yana da rabon
aure a rayuwarsa Allah ya nuna mata, don ita bata yarda da wai aljana ta aure shi ba, tafi yarda
in za’a ce yawan sabgogin Polo da ya saka a gabansa ne suka cire masa tunani da sha’awar
aure kwatakwata. Har mafarkin fuskar Petel data sha yi sai da ta gaya masa a duk ranar data yi istikhara,
Malam Yunus ya tausaya ma damuwar da Nenne ke ciki akan dan nata, ya kuma dan tsorata
duk da bai gaya mata ba, shima fa yanata mafarkin mutum akan doki a ‘yan kwanakinnan,
gashi tace dan nata mai hawa Doki ne. Nenne Sappa ta katse masa tunani da cewa, “na yarda Ubangiji ya aiko ni Gombe ne
wannan karon don lokacin da nake ta addu’ar zuwan sa ya zo ga AbdulRasheed, kada ka
juyawa wannan alkhairin da nake nufin mu kulla nida ku baya.
Ka yiwa Allah malam Yunus mu taru mu taimaki juna ta hanyar kulla aure mai albarka
tsakanin ‘ya’yanmu. Wanda zai mikar da zumunci na daku har illa ma sha Allahu.
Na amince daku dari bisa dari ba tun yau ba, haka na amince da Siddiqah ce kadai zata
zama surukata a cikin duk matan dake garinnan, da wadanda ke garinsu mijina (Ilorin) dama
kasar Najeriya gabadaya Siddiqah nake fata da addu’ar ta zame min suruka.
Malam Yunus ya nisa, duk da yayi na’am da komai da Haj. Sappa ke furtawa amma yace
tayi hakuri, ba zai yi gaggawar amsawa ba sai yayi shawara da na gaba da shi, kuma sai ya san
hakikanin abinda ya hana Abdulrasheed yin aure har zuwa wannan lokacin sannan zai yarda ya
bashi Aisha, shima kuma sai idan Ishaq bai tashi aure yanzu ba. Yace ya gaji da yawan maneman auren Aisha, kullum masu zuwa yau daban dana gobe,
yace gara ya aurar da ita haka ya huta, kowa ya huta, dama bai mata alkawarin samun ilmin
gaba da sakandire ba. Amma shi baya ra’ayin karatun boko mai zurfi sam a gareta.
Burinsa shine tayi aure da wuri ta haifa masa jikokin da zai kalla a matsayin ‘ya’yan da shi
Allah bai yi nasa sun zauna a raye ba, don mahaifiyarta ma iyakacin ta firamare ya aure ta.
A karshe yace ya ji bukatar ta na son tafiya da Aisha taga likitan Asthma, sai kuma yace bai
yarda ta zauna a Lagos har sai hutu ya kare ba, saboda tana zuwa Tahfiz yin haddar Al’qur’ani
a kowanne hutu anan kusa dasu a unguwar Dawaki, da ta gama ganin likitan don Allah a dawo
da ita gida ta karasa hutunta tare da su don suma sun jima basa tare da ita tun tafiyarsu aikin
Hajji.
Nenne Sappa tayi ta mamakin wannan soyayya ta iyayen Aisha ga diyarsu Aisha, ta dauka
Haj. Zainab ce kawai ke mummuken Siddiqah ahe har baban nata, ta amince da yadda Malam
Yunus ya zaba cewa Aisha zata yi sati daya a Lagos ta dawo musu da ita gida.
Malam Yunus ya bukaci sanin waye mahaifin AbdulRasheed da kuma asalin ita Nenne anan
Gombe. Nenne ta bashi damar yayi duk wani bincike da addini ya bashi dama akan Prince
AbdulRasheed dasu iyayensa.
Sun rabu akan cewa zai yi bincike zai kuma yi shawara da maidakinsa da Yayansa, sannan
zai sa Zainaba ta sanar da ita abinda suka hadu suka yanke.
An samu shawo kan Aisha da kyar da sudin ludayi ta yarda zata bi Hajiya Sappa Lagos
bayan ta ci kuka ta koshi ta gode Allah a toilet don kada Hajiya Sappa ta ga kukanta, wai sati
guda! Sati guda babu Umma yaya rayuwa zata yi dadi ga PETEL?! Sati gudan da a cikinsa
dukkkan kundin kaddarar rayuwar Aisha take, tareda dan kabilar Yarbawa. Nenne da Aisha suka kama hanyar Lagos ta jirgin sama, domin daga Gombe kai tsaye suka

tashi a jirgin Azman mai zuwa Ikko.
**** ***** ****



MURFIN LITTAFI NA DAYA
Ga dai Aisha-Siddiqah a hanyar zuwa Lagos gidansu Prince ABDULRASHEED IDRIS
(KEHINDE) AKANNI, gidan da ga dukkan alamu zai zame mata fadar rayuwar aure da
surukuntaka, ga dai Aisha da Prince (Fullatana da Bayarabe) na shirin zama mata da miji kamar
yadda manyan alamu suka nuna, alhalin Aisha ga hasashenta da alkiblarta da take-takenta
akan kabilar Yarbawa.
Mu biyo Siddiqah Petel ‘yar Ummanta, don jin cikakken labarinta, yadda zata kaya tsakanin
ta da Polo Legend na Africa da turai, wato Yariman Ilorin PRINCE ABDULRASHEED
(KEHINDE) IDREES AKANNI, mijin da kaddara ta zabar mata su fafata har su baiwa hammata
iska a fagen soyayya, wanda ya kasance dan asalin kabilar Yarbawa. Yanzu ne zamu shiga cikin gundarin labarin Aisha da Prince. Har yanzu a himfidar labarin
muke.
Abinda zamu so sani a gaba shine; Shin ko Aisha-Siddiqah zata barranta kanta daga matan
da Prince Abdulrasheed ya riga yayiwa kudin goron maha’inta, mayaudara, masu saka khairan
da sharran, sannan (gold-diggers&insatiable)?
A cewarsa dai “duk mata marassa godiya ne, da yawansu mazinata ne, marassa tsoron Allah
ne, sannan basa yin soyayya ta fisabilillah!
Ta yaya Aisha zata goge wannan perception din daya ya riga ya ginu tun kuruciya daga
kwanya da zuciyar Prince Abdulrasheed Kehinde?
Shin ko Prince zai samu irin soyayyar da yake fata, yake kwadayi, yake mafarki, yake kuma
burin samu shekara da shekaru daga Aisha? Mun ji dai sanda yace “He’s a hopeless romantic,
in search of true LOVE! Wanda ya riga ya amince babu shi a duniya”.
Shin ko Aisha-Siddiqah zata so kabilar Yarbawa tunda ga dukkan alamu kaddarar rayuwarta
na cikinsu?
Mu karasa a littafi na biyu wanda tare suke da dan uwansa.

Taku har abada
SUMAYYAH ABDULKADIR
(TAKORIN TAKORITES)
07030137870
WHATSAPP ONLY.
10/4/2024
​ (PAID BOOK)




(INA TALLATA MUKU AISHA LAME ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)

Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a
wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements
ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control?
Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA
LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da
kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa fata hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo
ku bani labari.
-Takorinku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login