Showing 36001 words to 39000 words out of 41207 words

Chapter 13 - Aisha Saddiqa Part 1 by Sumayya Takori.pdf

kyautar warawaran zinare ta yaya zata manta ta?
In ana haddace labarin mutanen kirki Malam Yunus ya dade da haddace wannan labarin na

Haj. Sappa daga bakin matarsa. Shima kuma ya yaba da kirkin nata duk da bai ganta ba.
Domin ya san matarsa sarai shishshigi gun masu kudi ko dukiya ba halinta bane, sannan ya
shaideta kan ita din ba mai kwadayi bace, kuma mai wadatar zuci ce. Allah – Allah take
Aisha-Siddiqah wadda take kira (Petel) dinta tazo hutu, ta gwada mata warawarannan da suka
fito daga hannun Haj. Sappah, Baban Petel ya tabbatar mata na danyen farin zinare ne (white
gold) kirar kasar Saudiyyah.
Ta san Patel da son warwaro, kusan kullum baka raba hannunta da awarwaro, kamar wata
ba’indiya haka zata yi ta rawa ita kadai tana juyasu tana kadasu idan tana cikin farin cikin wani
abu, an sha ‘seezing’ dinsu a makaranta amma hakan bazai hana gobe ta sake rokon Ummanta
ta sai mata wasu ta sake sakawa ba. Ranar hutun 'yan makaranta Aisha - Siddiqa Yunus, siririyar budurwa ‘yar shekaru goma sha
shidda, Aisha mai sassanyan kyau, ma’abociyar yalwar suma (gargasa) a gira da saman idonta,
wadda kaurinsu ya fallasa adadin yawan wadda zaka tarar a gashin kanta, da tsakar rana ta
dawo gidan su daga Billiri. Motar haya ta biyo yadda ta saba ta dawo gida, ba tareda anje
daukota ba.
Data shigo dakin ta wata irin mika Aisha tayi ta gajiya da farin cikin dawawo gida, tana fadin
"Oh no place like home!". Sannan ta ajiye jakar goyonta da bacconta ta fada wanka.
Bata samu Ummanta a gida ba ta shiga makwabta gidansu Umman Abdul dubiya, don haka
Aisha take ta kissima kome da me Ummanta ta sayo mata daga Saudiyyah a hajjin bana? Ta
san dai tsarabarta tafi ta kowa yawa a wurin Umma. Allah dai yasa bata manta da sakonninta
na Abaya da dogayen riguna ba. Umman Siddiqah (yadda ake kiranta a unguwar su ta Jeka da Fari) ta dawo gida gefen
la’asar daga dubiyar data shiga a makwabtansu, ta tadda Aisha-Siddiqah ta fito daga wanka
kenan har ta saka kayan sallahrta koren jilbaab ta tada sallah. Don haka ta wuce ta hada mata
abinci, sannan ta koma dakinta ta janyo jakar tsarabarta ta soma fidda tsarabar Aisha din a
gefe. Musamman (bracelet) din wajen Nenne, ta san sai Aisha tafi murna da shi fiye da duk
tarkacen abayoyin data kwaso mata.
Aisha na idar da sallah ta ma kasa tsayawa ta shafa addu’a tsabar dokin ganin Umma, sai ta
wuce dakin Umma da gudu ta fada jikinta cike da farin cikin dawowarta lafiya, rabon ta da
Umma yau wata uku kwarara tun komawarta hutun farkon zango. Lokacin visiting dinsu duk
tana Saudiyyah. Umma ta rungume ta itama tana dariya tana fadin. “Petel am miyelwi ma (Petel dina nayi kewarki)”.
Bada bata lokaci ba ta shiga fiddo warawaran na na wajen Haj. Sappa, guda shidda rus ta
shiga zurasu a hannun Aishah daya bayan daya. Kasancewar Petel ‘yar karama mai karamin
jiki kuma ‘yar siririya, komai na halittar Siddiqah karami ne, hanci ido da baki, sai suka shige
hannun nata sukuf babu gargada, kuma basa zamewa sun zauna cif-cif kamar saida ta
gwadasu tun farko.
Rashin kumari irin na Petel yana matukar damun mahaifiyarta, don sam bata da jiki kuma
bata da kauri hakanan bata da cika ido, wasu lokutan Aisha bata da kuzari idan Asma dinta ya
motsa. Tana da Asma kadan (Mild Asthma), a gida ne ko a makaranta koyaushe baka rabata da
inhaler a tare da ita. Bakin Aisha ya fadada har kunne, don murna, warawaran sun burgeta wadanda bata san ina
Ummanta ta samo su ba, ta san dai Umma ko tana da kudin sayensu bazata saye su haka

kawai ba, Petel (Siddiqah) ta kasa boye mamakinta da farin cikinta, don ta san ko guzurin
Ummanta gabadaya aka hada bazai sayi bracelet dinnan ba, in dai na danyen zinare ne kamar
yadda suke zagin idonta. (Bayeraben mutum nada son ajiye kadarar zinare, don haka shine
kadara abin ajiyewa a wurin Nenne Sappa da ‘ya’yan ta mata, Taiwo, Firdaus da Fatima). Aisha-Siddiqah tace da Umma cikin mamaki “Umma ina kika samo awarwaro mai kyau da
tsada haka?”
Nan Umma kamar jira take don har zuwa lokacin shaukin haduwarta da Hajiya Sappa da
karamcinta na makale a ranta, kullum da tunanin sake haduwa da ita take kwana take tashi,
nan ta kwashe labarin haduwarsu da Haj. Sappa a filin Muna ta labartawa Aisha, yadda ta tsinci
jakar kudinta da yadda ta maida mata, irin amincin da ya shiga tsakanin su sanadin hakan. Ta
ce ta dai lura matar Basarakiya ce ko matar Basarake. Sannan kuma bafullatanar Gombe ce
itama.
Aisha ta koyi wasu abubuwa guda biyu cikin labarinnan da Ummanta ta gama bata yanzu,
wato “gaskiya da amana su ke sawa a so mutum!” tace a ranta “na shaida Ummana mai
gaskiyace, amana da rashin kwadayi halin Umma na ne, nima daga yau zan koye su don kowa
ya so ni. A karshe hirarsu Aisha ta yarda idan ka rike gaskiya, amana da rashin kwadayi suka zama
symbol dinka watarana zasu samo maka abinda baka taba zaton samu a rayuwarka ba, da
kauna da amincewar mutanen da kake zagaye dasu”.
A yinin ranar bakidaya har dare labarin da suke yi kenan itada Umma wato na Hajiyar Lagos,
tsakanin Aisha da Ummanta aka rasa wanda yafi wani dokin son sake haduwa da Nenne
Sappa, Aisha ta ji itama tana son matar har cikin ranta duk da kuwa labarin kirkinta kawai
Umma ta bata. Kwanan Aisha-Siddiqah uku da dawowa hutu Asthma dinta ya tashi haikan, tun asali (she’s
asthmatic) wato mai fama da ciwon Asthma ce (mild asthma) da sai ta dade bata motsa ba.
Wannan karon tashin da yayi yafi karfin a kwantar dashi da (inhaler) dinta don a karshe har sai
da ta kai su ga kwanciya hajaran majaran a babban asibitin Gombe wato (FMC Gombe) ake ta
treating Aisha.
**** **** ****
Maimartaba Uban Kasar Gombe wato Yayan Nenne (Sarkin Gombe na lokacin) ya aika mata
sammacin kira yana son ganawa da ita a gida Gombe, ido da ido, ba maganar waya bace. A
ganin Uban kasa har da daurin gindinta a rashin auren da Prince Abdulrasheed ya ki yi har
shekarun kuruciya suka fice masa, domin in tayi masa umarni a matsayin ta na uwa in har yana
son albarka dole yayi ko yana so ko baya so. Ya gaji da maganganu akan Abdulrasheed, ko’ina
ka shiga sunan Abdulrasheed Idrees Akanni ne a bakin samari ‘yan bana bakwai a kasar
Najeriya, har wani lakabi suke binsa da shi “The Latest Yoruba Demon (Prince). Ita kuwa Nenne
ta fannin ta Allah ya gani bata san ya zata yi da Abdulrasheed ba kuma, tunda har hawayenta ta
zubar masa, hakan kuma bai sa ya amsa cewa ya yarda zai yi aure ba. Iyayensa maza ma
sunyi iya bakin kokarinsu duk a banza, bai amsa musu da komaiba har gobe, bazata dorawa
kanta ciwon da baida magani ba akan abinda bata da maganinsa. Duk da cewa tafi kowa
damuwa da al’amarin idan ta tuna yawan shekarun Abdulrasheed na yanzu. Watakila baida
rabon auren ne a gidan duniya, in haka ne tana masa fatan samun masu albarka a lahira, ba
kowa ke samun rabon aure a rayuwarsa ba, ta yarda da danta dari bisa dari ba lalata ce ta hana

shi aure ba. amma mafarkin data ke ta yi a ‘yan kwanakinnan fa?
Don haka Nenne ta taho Gombe ranar wata Lahadi da nufin zata yi kwana uku a gida, ta ga
‘yan uwa da dangi ta kuma gana da dan uwanta Uban kasa da ya kira ta officially, don ta jima
rabonta da Gombe, ko bai kirata ba tayi niyyar zuwa a wannan watan.
Nenne na shigowa garin Gombe tana kwance a bayan mota ‘Ford’ direba na sharara gudu da
ita, babu wanda ya fado mata a rai sai kawarta ta filin Arfah da Filin Munnah wato Haj. Zainab
Yunus.
Don haka ta yunkura tun a cikin motar kafin su isa fadar Gombe, ta dubi direban Uban Kasa
daya daukota dake ta aikin sa na tuki tace “tsaya a gefen titi!”, sannan ta ciro wayarta a jaka ta
kira layin Haj. Zainab da tayi saving da (Zaynaba mai gaskiya).
Haj. Zainab na dagawa da sallama taji muryar Haj. Sappan Lagos kamar a mafarki, tana
fadin “Zaynaba gani a Gombe, maza turomin adireshin ki, in fara tsayawa wajenku yanzu in ga
Aisha-Siddiqah kafin na isa cikin gida in kasa samun lokacin sake fitowa kuma”. Ta kara da
cewa “ina fatan na sameku lafiya cikin alkhairi keda malam Yunus da diyata Petel Siddiqah?”. Haj. Zainab cikin ‘yar damuwa take amma kuma taji dadin ji daga Nenne Sappa ta ce “barka
da zuwa Haj. Sappa, Jabbama-jabbama da Hajiyar Lagos maraba da isowa gida jewel in the
savannah (Gombe kenan) inji ‘yan boko” duk suka yi dariya.
“Sai dai kash! Bama gida, kin ganmu nan a FMC tareda Petel din babu lafiya, asthma dinta
ya tashi, tashin da ya jima bai yi irin sa ba.
Ina cikin damuwa da asmar nan tata Haj. Sappa domin Siddiqah itace ‘ya ta goma sha daya
dana samu a duniya kafin Allah ya bar min, ban sani ba ko itama a shekarun girma Allah bazai
bar min ita ba”.
“Ashsha Zaynaba, daina fadin haka, da yardarm Allah Petel zata ji sauki, kada ki girgiza
imaninki akan ciwon ’ya’ya, ciwo ba mutuwa bane kin ji? Diyata Firdausi ma tana da (brittle
asthma) haka muke ta fama. Allah zai bata lafiya da yardarSa”.
“Nagode da karfafawa Hajiya Sappa kuma ma dai yau din alhamdulillahi tana warwarewa ba
kamar jiya ba, don har ta karbi shayi ta sha sosai”.
Nenne ta ce “to bari kawai in karaso asibitin in sameku can, ai bani ita zakiyi in tafi da ita
Lagos kawai ko na sati biyu ne taga likitan Firdausi, tunda an yi hutun makaranta, Dr. Femi ya
kware sosai akan treating asthma”. Umman Siddiqah ta kwatanta mata inda zata same su a
female ward. Tana fadi aranta “ba inda zata iya bari Petel taje inba cikin dakinta ba, in ka san
soyayya ta rabin rai ta Aisha-Siddiqah da Ummanta ne”.
Mintuna ashirin ta kawo su har kofar dakin da Aisha Siddiqah take kwance, sai Nenne ta kira
Haj. Zainab ta sanar da ita suna bakin kofa.
Hajiya Zainab ta fito ta yiwa Nenne jagora zuwa cikin dakin har gaban gadon Aisha-Siddiqah.
Wanda daki ne na mutum daya (sideroom) a sashen kwanciya na bangaren mata. Nenne ta sa
kai a dakin bakita dauke da sallama.
Kallo daya Nenne Sappah ta yiwa “AISHA-SIDDIQAH YUNUS” dake kishingide a gadon
marassa lafiya da karin ruwa a hannun ta taji wani bakon yanayi a tare da ita.
Idanun Nenne basu sauka a ko’ina ba sai akan warawaran zinaren dake hannun ta wadanda
suka kawata halittar fatar hannunta fara sol. Ga yarinyar ‘yar karama da ita (mai karamin ruwa)
wato irin amsu karamin jikin nan ce siririya sosai kamar in ta sunkuya karyewa zata yi. Idanunta
kamar na kwan zabo, masu haske da kyau. Nenne tayi birki a gaban gadon Siddiqah ta kama

hannunta mara allurar a jiki tana kallonta da murmushi, Siddiqah wadda ke kishingide akan filo,
rike da dan littafin addu’o’I na hisnul muslim a hannunta ta daga fararen idanunta a hankali tana
kallon Nenne Sappa.
Umma bata lura da yanayin kallon kaunar uwa da Haj. Sappa ta fada akan Siddiqah ba, tana
ta faman lale-maraba da Hajiyar Lagos, (jabbama-jabbama), ta bata farar kujerar roba ta ‘yan
dubiya don ta zauna amma ina! Hankalin Nenne Sappa ya tafi ga wani tunani daban. Ya bar
jikin ta gabadaya. Domin dai yau ji take a jikin ta ga uwar jikokin ta, wato ga matar Prince Abdulrasheed
Kehinde Idris Akanni, yau Allah ya nuna mata da sauran numfashinta, wadda ta dade tana
ganin surarta a cikin mafarki duk ranar data yi istikhara akan sha’anin auren Prince Kehinde.
Ta dade, ta jima tana ganin wannan kyakkyawar fuskar a cikin barcin ta, bata taba sanin
alaqar yarinyar da mafarkan istikhararta ba. Taji a ranta bata iya barin Gombe ba tareda
Aisha-Siddiqah ba.
Lokacin da Aisha-Siddiqah ta bude baki tana gaida Nenne da sassanyar muryarta ta mai
jinya Nenne kasa amasawa tayi, domin Aisha da komai nata ya shiga ran Nenne farat daya
(daga gani na farko). Ji tayi kamar ta sace ta kawai ta gudu da ita Ikko, in yaso ta aurawa Prince
Abdulrasheed Kehinde. Ta san dai ko zaiki kowacce mace banda wannan kyakkyawar halittar
dake gabanta.
Da kyar ta iya amsa gaisuwar Siddiqah da wani kyakkyawan (maternal feeling) akan fuskarta.
Kafin su zauna su bude babin hirar Saudiyyah tsakanin Hajiyar Lagos da kawarta Hajiya Zainab
irinta wadanda suka aminta da juna, tabbas kawancensu hadin Allah ne kawai, domin ajin
rayuwarsu ko kusa ba daya bane. Allah shi yake hada mutum da mutum su kaunaci juna
saboda Allah.
Nenne tace da Haj. Zainab ta nema mata iznin Baban Aisha tana so ta tafi da ita Lagos taga
likitansu Firdausi, kwararre ne sosai akan lalurar huhu da numfashi, wanda shi yake duba
Princess Firdausi (itama asthmatic ce), daga nan tana so Aisha ta karasa hutun wannan zangon
a hannun ta. Hajiya Zainab tayi dan jimmm! Kafin tace “Babanta yana wajen aikinsa amma na san ba zai
ki baki Petel ba, don ba tun yau yake da labarinki ba, zan masa bayani idan ya dawo kafin ki
gama abinda ya kawo ki Gombe, kwarai nice dai zanyi kewarta, don bama raba gari tun
haihuwarta sai da ta fara makaranta a Billiri. Akwai yaron da ke rikon neman aurenta Ishaqa dan makwabtanmu, yana jami’a a Ibadan,
yanada da hakki shima a sanar dashi kafin ku tafi din”.
Nenne tace cikin jin faduwar gaban ta sameta a take “an yi musu baiko ne?” Kafin Haj.
Zainab ta bata amsa Nenne ta kira sunan Allah sau ba adadi tana neman daukinsa akan Allah
yasa Aisha rabon su ce. Wani ikon Allah sai Haj. Zaina tace “A’ah tukunna, Ishaqa dalibi ne a
jami’a, mahaifinsa yace sai ya kammala ya fara aiki koda zai masa aure, suna dai matukar
kaunar juna shi da Petel kowa ya sani, sabida shi Aisha bata sauraron kowa.
Gida biyu ne a tsakanin mu dasu, tare suka taso tun suna kanana soyayyar ba ta yau bace,
kuma dai Ishaq yana da hankali da nasaba mai kyau, ya dade yana hidima da ita don haka
dukkanmu mun yi na’am da shi tuntuni sai fatan Allah ya nuna mana lokacin”.
Aisha na jin su, kunya kamar tayi yaya! Sai ‘yan mutsu-mutsu take kamar tace kasar ta tsage
ta shige.

A karshe Haj. Zainab da Haj. Sappa sunyi sallama kan sai jibi zata zo ta gana da Baban
Aisha, in ya amince ta wuce da ita Lagos ganin kwararren likitan numfashi da huhu. Da Nenne
zata tafi ne ta matsa gaban gadon Siddiqah.
Tana murmushi tasa hannu ta shafa gashin kanta cike da damuwar ganin yadda take ta
kokawa da inhaler ita kadai, tace “get well soon my dear, Allah ya baki lafiya kinji ko Siddiqah?
Sai na dawo”.
Har bakin mota Haj. Zainab ta raka Nenne. Suka sake kafa sabuwar hira kafin suyi sallama
da kyar.
Nenne Sappa ta samu dan uwanta Uban kasar Gombe da iyalinsa lafiya, suka sha hirar
zumunci irin wadda suka dade basu sha ba. Kafin ya gaya mata maqasudin abinda yasa shi
kiran da yayi mata, wanda dama ta tsammace shi tun ma kafin ta ji shi. Maganar dai guda day
ace. Gabadaya danginta da iyayenta da dangin mahaifinsa da nasa mahaifin basu da damuwa
yanzu sai ta auren Prince.
“Ki turo AbdulRasheed ya zo ya ga ‘yar uwarsa Naziha, malaman fada sun gayamin idan har
ba auren muka yi masa da kanmu ba, a haka zai kare rayuwarsa bazai taba kawo mace yace
yana so ba don sunce aljana ta aure shi.
Sannan ance dani akwai aguminsu na maketan Yarbawa makiya Kakansa, akwai kuma sihiri
irinna magauta gidansu duk a jikin sa, bazai taba ganin mace yace yana so ya aura ba”.
Nenne tayi ajiyar zuciya cikin damuwa, bata son irin wannan false beliefs din ita sam,
gasgata malaman tsubbu da Yayanta Uban kasa ke yi a rayuwarsa yana damunta, ita tafi yarda
da cewa auren Abdulrasheed LOKACI ne bai yi ba, kuma koda yayi din, duk da za’a kira shi
‘LATE MARRIAGE’ tofa ba zai wanke masa tarihin cewa ya jima bai yi aure ba, don haka ba
kowacce mace zata yarda ya aura ba musamman cikin ‘ya’yan ‘yan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login