Showing 27001 words to 30000 words out of 41207 words

Chapter 10 - Aisha Saddiqa Part 1 by Sumayya Takori.pdf

a Tokyo, shine cinta
shine shanta, shine sutturarta da duk wani shopping dinta duk don ya katangeta daga neman
wani abu ta rasa a rayuwarta duk da shima a lokacin ya dogara ne da abinda Kakanshi ke turo
masa duk wata, da na mahaifinsa, a matsayinsa na dalibin postgraduate, soyayya ta gaskiya ba
irin wadda bai yi mata ba, har da ta kauce hanya, domin ta saka shi ya danyi deviating daga
tarbiyyar da Nennensa ta bashi, duk don ya faranta ma fiancée dinsa Hasinah ya kuma
katangeta daga sha’war wasu mazan ba don yana so ba.
A dalilin ganewa da yayi cewa ta soma wayewa da irin wannan rayuwar da tazo ta tarar
‘yammata da samari kamarta nayi a jami’a, lokacin da ya fahimci ita din mai son wannan
rayuwar ce sai ya biye mata, bisa dalilai guda biyu; na farko son da yake mata, na biyu tsoron
shi na kada ta kwadaici wani, idan shi din yaki biye mata. Da wannan Hasinah ta dulmiyar dashi a baya cikin rayuwar soyayyar shan minti, kazamar
rayuwar da ’yammata irinta ke yi a turai, rayuwa ta rashin tarbiyya da baya ko son tunawa yayi
da Hasinah yanzu.
Duk da haka a kullum yana godewa Allah da bai taba sanin Haseenah diya mace ba (as in
having sex) bai taba ba. Sai abinda ba’a rasa ba bisa jagorancinta.
Amma duk da soyayyar shan mintin da ya biye mata suka soma ba don yana jin dadin
afkuwar hakan ba, saboda a irin son da yake ma Hasinah yafi so ko meye zai shiga tsakanin su
sai ya mallaketa ta hanyar aure, amma ta nuna ita bazata iya jira har zuwa wannan lokacin da
Nenne zata amince da maganarta ba, dole ya biye mata suke kananan abubuwan da har ransa
baya so. Don kuwa mace duk inda take komai kankantarta shaidaniya ce, balle shaidancin
Hasinah mai license ne tunda ‘yar kwararo ce, amma duk da hakan biyemata din domin ya
katangeta bai sa ya iya ya rike sha’awarta da hangenta da kwadayinta na abinda shi har lokacin
ya kasa yi mata ba, saboda addu’ar Uwa ta dare da rana dake tasiri a kansa, ya kasa rike
sha’awar Hasinah daga sauran mazan da basu kaishi komai ba.
Amma a bukatun rayuwarta kam na yau da gobe baya jin ya gaza, sai dai don ta kasance
mai son bushasha da sha’awar rayuwar kere sa’a.
By Allah! Yayi duk wata bajinta da namiji kamarsa mai gata da asali da nasaba tsarkakakkiya
ta sarauta da ilmi mai zurfi da malanta bazai yi akan matar da ya tsinto a kwararon gidan
marayu ba!
Bayan duk wannan wane irin sakamako ya samu a mahaukacin son nan kuma gurbatacce
da yayiwa Hasinah???
Prince ya runtse ido da karfi, yana tuna Hasinah a ranar, da kazantaccen yanayin da yazo ya

samesu ba zato, mantuwa yayi ya dawo, abin mamaki tareda kaninsa Adetokumbo Abdulfatahi
Akanni, the worst part dinma kuma a dakinsa sannan a kan gadonsa.
Saboda kawai Abdulfatahi ya fishi kudi, ya fishi iya shege ya fishi rashin tsoron Allah, uwa
uba yanada ra’ayin yin bushashar arzikinsa ga matan banzan duk da zasu bashi jikinsu, don a
lokacin shi Abdulfatahi wani babban Automobile Business Mogul ne, kasancewar a tsakanin
Japan da Spain yake harkar shigo da motocinsa, to duk sanda ya shigo Tokyo a wajen dan
uwansa Prince Abdulrasheed yake sauka, baya sauka a hotel, kuma ta haka ne ya san Hasinah
a matsayin fiancée din dan uwansa, har suka saba shi da ita suna tsokanar juna irin dai wasan
nan na kanin miji da wadda Yayansa zai aura.
Yaya akayi-yaya akayi suka sarke a bayan idonsa kuma bai taba gane komai a tsakaninsu ba
banda sani da yayi tun fila azal Hasinah mai dogon buri ce, mai kwadayi ce, mai son
kyale-kyalen mata na fita tsara ce wato (Hasinah is a designer baby) sannan yana ankare da
cewa tana son wannan harkar, a hakan kuma yana iya bakin kokarinsa akanta, don ganin bata
rasa komai take bukata ba, kusan duk abinda iyayensa ke aiko masa a matsayinsa na dalibi a
lokacin akan bukatun Hasinah masu dan Karen tsada yake karar dasu da kwalliyarta na sittiru
tsadaddu, da kayan kawa da khyale-khyale ba tareda Nenne ta sani ba. Ko dama ita Nenne
from day one, Hasinan bata kwanta mata ba tunda aka ce a gidan marayu aka daukota, tun a
lokacin Nenne tace “NASABA” wato tsatso, wani abu ce mai girma da muhimmanci a neman
aure to amma Hasinah fa?
Suwa zata bugi kirji ta kira Kakannin jikokinta na wajen uwa na jikin Abdulrasheed Kehinde?
Shikuma har a lokacin lallaba Nenne yake yi akan ta yarda ta karbi Hasinah a matsayin
surukarta, ita kadai zuciyarsa keso, ita yake yiwa kauna ta saboda Allah ba zai iya auren
kowacce mace in ba itaba.
Shi ya bata surname da Bello Ambursa lokacin da zai shigar da ita makaranta, sunan
abokinsa Bello da ya rasu.
Sakamakon da ya samu a duk wannan sadaukarwar da yayiwa Hasinah shine Hasinah ta
bige da cin amanarsa, itada dan uwansa mafi kusanci dashi, mafi kazantar cin amana har a
gadon barcinsa kuma a gidansa. A cire maganar girman zina wadda lahani ce mai girma ga
martabar diya mace. Abin ya kara dawo masa sabo. Kamar yanzu-yanzu ya faru. Shekaru goma sha hudu kenan
da faruwar al’amarin a can baya, amma kullum sabo scene din yake koma masa a idanu da
zuciyarsa, in ya tuna ko aka yi masa fadan yin aure ko ya kamata ya zabi matar aure a family
dinshi. Nan da nan jikin sa ya hau tsuma, zazzabi mai zafi ya rufe shi, makwallatonsa na kaiwa
da komowa, zuciyarsa kamar ta hudo kirjinsa ta fito sabida yadda take hawa da sauka don
bacin rai…..
Ya dade bai shiga bacin rai irin na yau ba sakamakon wannan dogon tunanin da yayi. Ita da
kanta Nenne ta lura da halin canjin mood da kalamanta suka jefa dan ta Prince AbdulRasheed,
sai taji wani irin babu dadi a zuciyarta da kasan ranta.
Ita ta san Abdulrashid dinta is always bold and smart fiyeda Taiwo, kasancewarta mace
tanada saurin nuna rauni (sai karambani da rawar kai da shiga sharo ba shanu), but today he
looks pale har fiyeda Taiwo uwar kankanba idan ta raunana.
A ganinsa tunda har uwar data haifeshi ma ta fara yarda da zargin da duniya ke masa na
cewa wai (he is gay), don kawai yana rayuwa a cikin turawan yamma, kuma yana practicing

wasansu na tseren Doki a matsayin sha’awar ransa kuma sana’a mai girma, hujjar kowa ta
makala masa wannan zargin shine kawai don ya ki yarda yayi aure ko kawo mace gidansa da
sunan matarsa?
Zargi wani abu ne mai girma da muni a musulunci balle zargi irin wanda duniya ke masa.
Auren ai Sunnah ne ba farillah ba tunda Alhamdulillah yana iya rike kansa ta hanyoyin da addini
ya koyar.
Kusan kullum baka Abdulrasheed da azumin litinin da alhamis a bakinsa, baya kallon
haramun, balle kai kansa inda ake aikatata, he is always busy planning and scheduling his Polo
time-tables across the globe da tsara ayyukansa na Consultation a matatar man fetur a (Qatar
refinery). Zina ai sai mutum ya bata kafa take shigowa rayuwarsa. Ga kuma addu’ar tsayayyyar Uwa irin Nenne Sappa a kansa kullum wadda zamu iya cewa
itace babban makamin dake katange Abdulrasheed ga ayyukan sabo in akayi la’akari da
yanayin rayuwar ‘yan Polo.
Duk da cewa Nenne ta yi dana sanin furta masa damuwarta, amma kuma hakan ya
taimakawa zuciyarta, yanayin da ya shiga kadai yasa ta rage tasirin zargin na mutane daga
ranta akan dan nata, ko daga irin halin rudu da damuwar da ya shiga akan maganar kadai ta
gane ba haka bane, zargi ne mai muni ake masa da shaci-fadin mutane da basu da gadon ka
sai gadon magana akan ka.
Ita kawai tayi la’akari ne da fadar nan ta hausawa dake cewa “ka haifi Da, amma baka haifi
halinshi ba” kuma akace wai “ba’a shaidar ‘ya’yan yau”, da kuma yadda kana tufka a
matsayinka na uwa; modern society da influence na ilmin zamani na warware maka tufkar ta
baya, musamman shi AbdulRasheed da in akayi la’akari da irin ‘life-style’ dinsa, wato yanayin
rayuwarsa da yadda yake gudanar da ita gabadaya kome aka ce akansa al’umma bazata musa
ba.
​ “To me ya hanaka aure har yau Kehinde? Na roke ka da girman Allah yau ka gayamin.
Ni mahaifiyarka ce da baka da wanda ya fini ba kuma wadda zata rufa asirinka a duniya irina.
Shin idan baka sanar dani hakikanin matsalarka ba, wa zaka sanarwa a duniyarnan?”
​ Zuwa lokacin ya soma dawowa cikin hayyacinsa, amma maimakon ya baiwa Nenne
amsar data dace da tambayar data yi masa, wato menene hakikanin abinda yasa ko zancen
aure baya kaunar a yi masa? Sai ya bige da maida zancen wani kala daban, don Nenne ta bar
zancen, don har gobe babu wanda ya san abinda Adetokumbo yayi masa kaf cikin zuri’ar su,
daga shi sai shi Tokumbon, sai kuma Taiwo, sai ita shaidaniyar HASINAH! Da bai san a wace
duniyar take yanzu ba. Sai kuma Allah da ya haliccesu.
Zai kuma cigaba da barin wannan zancen a ransa yana haunting dinsa shikadai ba tareda ya
gayawa wani a danginsu ko iyayensu ba bayan Taiwo, albarkacin zumuncin Akanni’s da hadin
kan gidansu.
Yau ace wani cikin zuri’ar Emir Abdulrasheed Akanni yana zina da macen da ba tasa bama
abu ne da zai taba mutuncin su bakidaya, abun kunya ne ba karami ba, ga zuri’ar sarki
Abdulrasheed Abdullateef Akanni a idon talakawansu dake ganin martabarsu da girman
nasabarsu, wanda zai iya lalata hadin kan gidansu gabadaya wanda gida ne ko kuwa zuri’a ce
data zamo abun buga misali a ciki da wajen jihar Ilorin.
​ Sai ya maida abun zolaya ga Nenne, bayan ya maida murmushi mai sanyi akan
fuskarsa, Prince ya soma magana cikin lallashin mahaifiyarsa.

“To yanzu Nenne, ki gayamin saboda Allah, duk fadin Najeriya wacece kike ganin zata aureni
da tsillin furfura kamar yadda Fatima tace, umh?
Ta kuma kaunace ni da furfurar nikadai ba tare data hada soyayyata data wani na ba? Ba
kuma don abin duniya da reputation dina (shaharata) a kan wasan Polo ba, soyayya pure nake
nufi tsarkakakkiya ta saboda Allah! A dai yawan shekaru irin nawa, wadanda babu sauran
kuruciya a cikinsu yanzu? Believe me Nenne, duk matan zamanin nan, ina fade ina karawa kullum (are nothing but
gold-diggers) sannan karnukane babu daraja a tare dasu.
Daga kan HASINAH AMBURSA… na gama rufe babin mata Nenne, (they just want money
over pure LOVE), don haka basa gabana gabadayansu Nenne, har abada babu ni babu ‘ya’ya
mata”.
Nenne sai ta bishi da ido zuruuu! Ta kasa gane inda zantukansa suka dosa. Me Hasinan da
ta san yanaso kamar ya cire ransa ya bata tayi masa da ya karya zuciyarsa haka?
Ashe a kanta ne yake gudun mata tun zamanin samartakarsa?
Ta dade bata kara jin komai game da Hasinah din ba. Ko daga bakin aminiyarta uwar dakinta
(Taiwo) bata kara jin zancenta ba. Wacce a baya kullum suka hadu bata da aiki sai lallashin
Nenne ta barshi ya auri Haseenah.
A lokacin AbdulRasheed ya koma ya jingina da filo a jikin gadon jinyarsa, ya runtse idonsa a
hankali yana motsa hannunsa na dama kadan da aka kwance daga daurin karaya. A can kasan
zuciyarsa magana yake shikadai wadda baisan tana fita a fatar bakinsa ba, tana shiga kunnen
mahaifiyarsa. “I am now a hopeless romantic. I want an idealist (true love)”.
Wanda ya riga yayi amanna da cewa babu shi sam-sam a zamanin yanzu. Babu irin soyayyar
da yake burin samu!
Domin y agama yardarwa kansa a wannan qarnin da muke ciki, wani qarni ne da mafi yawan
mata suka daina soyayya irin wadda yake buri ta domin Allah, ba don komai ba sai don
zukatansu sun zarme da kwadayi da son rayuwar duniya da ta wuce kima, hakan yasa suka
zama insatiable ga mazan da Allah ya basu masu yi musu kauna ta gaskiya, suka maida
kawunansu sex slaves to rich men (sun zamar da kansu bayin biyan bukatar gangar jikin maza
masu kudi ko mulki, soyayya ta hakika ta gushe a zukatan mata.
Engnr. Abdurasheed ya kara kishingida sosai yana cigaba da cewa da kansa da kansa.
“I am a hopeless romantic. I want true love!”.
(Karin haske). “Prince AbdulRasheed (Kehinde) Idrees Akanni, yana nufin ya riga ya
yardarwa kansa cewa babu soyayya ta gaskiya, true love is hard to find, or does not exist at all,
matan yanzu duka are incapable of that...!”.
**** **** ****
Ba jimawa saboda irin kulawar da yake samu ya karasa warwarewa, aka sallamesu. Suka
koma gidansa.
A wannan dan zaman jinyar da Nenne Sappa tayi na dan ta Prince AbdulRasheed Kehinde, a
kasar Argentina, ya basu damar samun shakuwa da wani irin kusanci da juna na uwa da data
wada y agama mallakar hnkalinsa amma still yana bukatar kulawar Nenne da zamanta a
gefensa, shekaru da yawa basu samu damar zama tare na lokaci mai tsaho irin haka ba,
saboda yawace-yawacensa na Polo a duniya.

Nenne ce ke dafa masa duk abinda zaya ci da kanta kullum, wanda shi da kansa yake zabar
abinda zata dafa masa, haka take saka shi a gaba sai ya ci sosai, sannan ta tabbatar da ya sha
magungunansa akan kari, wanda take barowa da hannunta akan farin tafin hannunta ta zuba
ruwa a tambulan mai garai-garai ta bashi ya hadiya akan idonta don Abdurasheed baya son
kwayar magani sai akan idon Nenne don baya son abinda zai bata mata rai tun yana yaro.
Saida AbulRashid ya warke ragas har ya fara shirin komawa wajen aikinsa a Qatar sannan
sukayi sallama shi da Nenne da ‘yar uwarsa Fatima, Taiwo ta tabbatar masa zata sameshi a
Qatar in ta samu leave ta ga jikin nasa. Sun kwana hira shi da Nenne yau, zancen da baya so
ko kankani a yi masa wato zancen aure itama tana avoiding dinsa yanzu, don bata son ganin
yanayin tashin hankalin da yake fadawa a duk lokacin da tayi subutar bakin yi masa zancen
aure.
Su Nenne zasu koma Lagos a washegari, don lokacin tafiyar Nenne aikin Hajj na wannan
shekarar ya kusa.
Sun tashi zuwa Lagos da kwanaki biyu, shikuma ya tashi zuwa Qatar inda ya koma bakin
aikinsa cikin koshin lafiya.
**** **** ****
FGC BILLIRI, GOMBE

Yarbawa masu kwalo-kwalo, da Duwawu kuke tukin tuwo!!!”.
Bisola ta kauda kai bata kula ta ba, ta ci gaba da tukin Teba da take yi da ludayin karfe a cikin
robar cin abincinta mai fadi. Wannan duk bai ishi siririyar yarinyar ba mai siririn hanci da
manyan idanu masu walainiya, hakoranta yiri-yiri farare kal kamar kankara, ta sake leka fuskar
Bisola cikin matukar tsokana da iblisanci irin na ‘yammata ‘yan makarantar kwana da aka fi sani
da teenagers.
​ “Nace ko ba ku bane? Yarbawa masu kashi a kwano?!”
Jikake kyal-kyal-kyal. Yaran dakin da duka ‘yammata ne masu tashen balaga wadanda a
shekaru basu fice shekaru 15 zuwa 16 ba, in sun yi da yawa 17, dukkansu sun kara
kyalkyalewa da dariyar shakiyanci da shegantaka (mockery).
Karo na sau ba adadi da AISHATU-SIDDIQAH YUNUS tasa Bisola Akanbi kuka, sanadin
wannan wakar da irin wannan cin zarafin da take mata a gaban sauran yara tsararrakinsu da
suke kwana daki daya. Ko a aji ko a filin wasa ko a hostel kai har a masallaci in taga Bisola sai
ta mata irin wannan tsokanar. Sauran daliban kuma, wadanda suke gang din Aisha duk sanda
Aisha ta fara yima Bisola wannan wakar ta shakiyanci wadda take yi tana juya siririn
kwankwasonta (irin dai na yadda yarbawa ke juya mazaunansu) wanda baya wani motsawa
sabida sirantarta sai sun daddage sun barke da dariya.
Ba Bisola ce take basu dariya ba, karewa ma tausayi take basu, sabida yadda Aisha ta
matsa mata, ita Aishar ce take basu dariya yadda take daddagewa tana juya kwankwaso da
‘yan mazaunanta da sunan kwaikwayon tukin tuwo ko Tebar Yarbawa, alhalin kwankwason nata
duka bai fi girman a hada tafin hannu biyu ba. Farin jininta a wurin tsararrakinta kuwa sabida
kiriniyarta da kyawunta da kaifin bakinta, ga wauta da gwalangwaso abin ba’a magana.
Bisola Akanbi kullum Aisha ta fara mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login