🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 NA *MARYAM ISMAIL MAJIDADI* Facebook Maryam ismail majidad'in kainuwa wattpad MARYAMMAJIDADI123 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *Ya Allah na rokeka yanda ka bani ikon fara littafin nan lafiya ya Allah ka bani ikon gamashi lafiya,ya Allah na rokeka ka kawar da alkalamina a wurin rubuta sabonka,Allah ka kara mana basira ,kasa kuma sakon da muke isarwa yana zuwa inda ya dace,Allah na rokeka ka bani ikon gama littafin lafiya,littafina kirkirarran labari ne,bamyi shi dan wani ko wata ba,haka zalika salonsa na daban ne* *Fallow me on wattpad pls real fans at maryammajidadi123* page 1 ALHAJI SULAIMAN shi ne asalin sunan mai gidan matarsa d'aya HAJIYA KHADIJA yaran su biyu JAFAR DA KABIR .ALHAJI SULAIMAN katsina shine mahaifarsa cikin karamar hukumar BINDAWA ya taso yana da rufin asiri babu laifi yana sana'ar saye da sayarwa ta kayan masarufi ,babu laifi Allah yasawa sana'ar tasa albarka ,suna zaune cikin farin ciki da mutunta juna,HAJIYA KHADIJA tana da k'anwa JAMILA wacce take aure nan kusa da ita,sai dai mijin JAMILA ,MALAN SALE ba wani k'arfine da shi sosai ba,duk da haka be gaza wajen kula da iyalansa ba yarinyar su d'aya BILKISU,BILKISU babu abunda ta bari na halin mahaifiyarta watao JAMILA ,JAMILA akwai san abun duniya da hangen na wani,d'an jin da'in da yayarta ta fita KHADIJA sai ya tsone mata ido,tun daga nan ta k'ulla wani mugun kulli a zuciyarta,zaune suke cikin babban parlon mahad'ar gidan kasancewar anan d'ayan b'angaren su Malan SALE ke zaune,breakfast sukeyi akan teburin cin abinci ma daidai ci. Gyaran murya ALHAJI SULAIMAN yayi tsoho mai dattako da mutunta kowa ,tsoho na gari mai sanin darajar d'an Adam,ruwa ya kurb'a kad'an sannan yace"ya kamata a yanzu yaran nan auyi aure,kunga babu abunda suka rasa kowa yayi karatunsa daidai gwargwado ga sana'a JAFAR ya gajeni,shima KABIR Alhamdullilah tun da yana aekin company dinsa,BILKISU ma ta gama makaranta". "wannan shawara tayi kyau Alhaji,gaskiya hakan ya kamata dan bazamu zuba masu ido muna kallonsu ba"Malan SALE ya fad'a,wata uwar harara Jamila ta watsa masa duk da taji dad'in zancen mijin yayar tata,sinne kai BILKISU ta farayi dan tasan dole yanzu za'a fad'awa BABA tana tare da KABIR,gyara zama JAMILA tayi wacce suke kira da Goggo tace "to ae Baban yara zancenka yazo kan gab'a kuwa,domin Kabir da Bilkisu sun gama dai dai ta kansu,sai a tsaida rana kawai".murmushin jin dad'i ya sub'ucewa ALHAJI SULAIMAN(BABA) yace "kai Alhmdllh masha Allah,Allah abun godiya dama ina ta daukin wannan rana ,bana so Bilkisu ta fita waje sai Allah ya ansa addu'a ta,dama shi JAFAR yana tare da yarinyar aminina wato ALHAJI AMINU CHANJI sai ayi komai rana d'aya a wuce wurin".wani mugun fad'uwa gaban Goggo yayi tana maimai ta sunan ALHAJI AMINU CHANJI tasan babu wanda be sansa ba,tab lallai akwai tashin hankali kenan ya fad'a a ranta,take wani mak'ok'on bak'in ciki ya k'ara taso mata,da k'yar ta dannesa tana murmushin yak'e. KHADIJA(MAMA) kam murna tayi sosai dan tasan yarinyar Alhajin Aminun wata SHA'AWA tasanta sosai natsatsiyar yarinyace gata kyakyawa ajin farko kuma y'ar gata ce dan ita kad'ai ce mace sai yayanta d'aya BASHEER ,tayi zurfin karatu gata da tarin dukiya tun tana da k'ananun shekaru,sosai MAMA tayi murna dan yarda JAFAR baya da hayaniya baza taso ya auri wacce zata bashi wahala ba.haka suka watse daga cin abincin kowa da abunda yake cikin ransa.cikin sati biyu aka gama komai aka tsai da ranar auran nan da wata d'aya,anan cikin filin gidan BABA ya ibarwa yaransa ya gina masu ko wanne part dinsa mai kyau na zamani ,shi da kanshi ya had'a lefe komai iri d'aya ko wacce akwati shidda lokacin biki sai k'ara doso kai yakeyi,ankai lefe sosai aka samu tarbar arziki daga dangin SHA'AWA,na BILKISU kam a nan suka karb'a abinsu tunda tuwana mai na zasuyi,tun da akayi jeren SHA'AWA BILKISU ta tada hankalinta ganin tsadaddun kayan da aka zuba mata,tun daga nan hassada ta shiga tsakaninsu,duk da itama BABA yayi k'ok'ari sosai,sai dai sam idonta yana hango na sama da ita,ba wani bidi'a akayi bikin ranar juma'a dubban al'umma auka shaida auren JAFAR SULAIMAN BINDAWA DA AMARYARSA SHA'AWANATU AMINU CHANJI sai na KABIR SULAIMAN BINDAWA DA AMARYARSA BILKISU SALE BINDAWA akan sadaki naira dubu talatin,haka aka sha hidimar biki har walima cikin mutun ta juna,tun da BILKISU ta daura idonta akan SHA'AWA taji wata muguwar tsanarta danta fita komai kama daga kyau da kuma dace,dan gani takeyi JAFAR yafi KABIR samu kuma haka dinne,balle tun a wurin bikin ALHAJI AMINU yaiwa sirikin nasa kyautar milyan d'aya ya k'ara a kasuwancin sa,itama kuma SHA'AWA tana da kamfanoni da filaye da shaguna.ko kad'an SHA'AWA batajin dadin zama da BILKISU dan makirace bata barinta sakewa sai ta fakaicin idon mutane take kuntata mata,SHA'AWA kam bata da hayaniya ko kad'an shiyasa bata damuwa da BILKISUN ,sosai Goggo ta shiga bokaye ta mallake KABIR tas bayajin maganar kowa sai nata komi ya samo yana sakarwa y'arta,a haka sukayu nasarar saka masa kiyayyar d'an uwansa ,akwan a tashi babu wuya wurin Allah watansu ukku da aure sai ga SHA'AWA da ciki BILKISU ko shiru,ranar da maganar ta fito BILKISU kusan hauka tayi dan ita ko b'atan wata bata tab'a yi ba,haka taita renan cikinta da dadi da babu,duk da tanajin dadi sosai wurin mijinta da kuma iyayensa da BABA da MAMA da MALAN ba daga baya ba wurin kyawawan hali da son mutane wurin Goggo da Bilkisu kadai take samun matsala,a haka har tazo lokacin haihuwa duk da ta sha wahala amma cikin ikon Allah ta haifo yaranta kyawawa har biyu duka maxa masu matuk'ar k'ama da JAFAR,tun da BILKISU taji labari ta fad'a d'akin Goggo tana ihu tana watsi da kaya kamar sabuwar mahaukaciya,da k'yar Goggo ta lallasheta tace"ki daina wannan kukan ,kina dani banfa mutu ba bare kiyi kukan maraici,ba sai munbar yaran da rai ba sannan zatayi maki sisi ba,yadda jininki be taka gidan nan na,haka zalika babu wanda ya isa ya taka wannan gidan,dolo muga bayansu zamu shirya komai kafin a sallamesu asibiti".Sosai BILKISU taji dad'i dan tasan halin Goggon tata,BASHEER da ke tsaye bakin tagar ya sauke ajiyar zuciya yayi saurin barin wurin kada su fahimci wani yaji b'angaren k'anwarsa SHA'AWA ya shiga ya ibi kayan da zai iba yafito uabar gidan tare da neman mafita,har ya isa asibitin baya da mafita sai shawarar d'aya da zuciyarsa ke basa na ya d'auke yaro d'aya ya gudu da shi wanda ko y'ar uwarsa ba zata gane hakan ba,danshi ya dad'e da yin aure yana zaune a k'asar CANADA amma har yau matarsa ko b'ari bata tab'ayi ba,da k'yar ya shawo kan DR din daya k'arb'i haihuwar sai da sukayi rubuce rubuce kuma yayi masa rantsuwa bazai tab'a cutar da yaron ba,duk da DR din yasan yayi zalinci amma haka ya daure ya daukko yaron SHA'AWA babban yaba BASHEER ,can kuma ya saka gawar wani jaririn yace Allah yaiwa d'aya rasuwa,sunji babu dad'i sai dai sukayi hakuri akayi masa suttura aka ruhoshi,har rawar murna BILKISU ta taka tana fad'an sora d'ayan shima,tun da BASHEER ya k'arbi yaron be k'ara kwana ba ya wuce CANADA sosai matarsa ta tausaya masa,ta kuma k'arb'a ,sukayi karyar tana da ciki ,kuma zasu tafi wani aeki dan nan da wata d'aya zata haihu idan sun dawo zai kawo masu baby in Allah ya sauketa lafiya,sosai ALHAJI AMINU yayi masa fad'an ya boye matarsa tana da ciki har sai da ta kusa haihuwa zai fad'a,shikan BASHEER hakuri yayita basu.kwanansu biyu a asibiti jikin SHA'AWA yayi kyau dan hakan da dare za'a sallameta ko da mahaifinta yazo nan take ya mallakawa jaririn babban Company dinsa na sarrafa ashana ya bawa JAFAR takardun aka maida sunan jaririn wanda JAFAR yayi masa huduba da AMINU dan karamcin mutumen,sai da BILKISU ta fakaici idon kowa sannan ta share kwallah ta kuma kudiri aniyar yau zata zartar da shawarar da zuciyarta ke bata,sai da bayan isha'i sannan tace zata tafi,ganin babu kowa d'akin yasa tayiwa SHA'AWA sallama ta fito,lab'ewa tayi ko da taga ta shiga bayi aeko ta shigo da sand'a ta murd'e wuyan jaririn saboda rashin imani ,da sauri ta fice abunta,tana fita kuma SHA'AWA ta fito ganin Babyn baya motsi yasa ta saka kuka daidai haka JAFAR ya shigo an kira DR ya tabbatar murd'e masa wuya akayi amma kab aka rasa wanda yayi hakan,wannan dalilinne yasa JAFAR rokar SHA'AWA akan kada ta fitar da dalilin mutuwar yaron suyi hakuri Allah zai kuma basu wani,tayi kuka sosai na rashin yaronta,BILKISU na zuwa ta iske rasuwar harta rigata isowa ta hau murna tana fad'awa Goggo meya faru,murna fal ransu,haka SHA'AWA ta dawo da kewar yaranta,watansu bakwai ta rasuwa yayin da BILKISU ke dauke da ciki tsawon wata shidda sai cika take tana batsewa ita a dole mai ciki,tab'ara kawai takeyi da tuna isa ,a haka lokacin haihuwa yayi ta santalo yaronta namiji kyakyawa dan duk ya fisu kyau da fari,sosai kowa yayi murna har SHA'AWA da lokaci d'aya taji kaunar yaron ranar suna yaro yaci SULAIMAN zasuna kiransa da (AHAAD),sakarwa SHA'AWA shi BILKISU keyi a yunaninta wai ta zama y'ar renonta dan ko yaushe yana wurin SHA'AWA nono kawai take kaishi yasha wurin BILKISU .wani irin shakuwa da soyayya mai karfi ta shiga tsakanin SHA'AWA da AHAAD ko motsi zatayi yana mak'ale da ita hakan yasa take jinsa kamar ita ta haifesa cikin gwaranci har yake ce mata UMMU JAFAR kuma ya kirasa ABBU ,BILKISU yace MUMMY KABIR kuma yace masa DADDY,shekararsa hudu BILKISU ta muma samun ciki sai ta k'ara fita harkar AHAAD babu ruwanta dashi wai karya takura mata,yayin da ita kuwa SHA'AWA har lokacin shiru bata kara koda b'atan wata ba.lokacin haihuwa BILKISU ta k'ara haihuwar namiji ranar suna yaro yaci SALE suna kiransa (AMAAN),tunda MUMMY ta haifi AMAAN sai ta k'ara mantawa da AHAAD babu abunda take so sama da AMAAN ko motsi yayi yanzu tahau tambaya ko ina tana mak'ale dashi,wannan dalilinne ya k'ara sanya rashin sabo tsakaninta da AHAAD ,tun tashin AHAAD wani murd'ad'en yaro ya taso ko kad'an baya magana sai ta kama baya son hayaniya baya shiga harkar kowa,tun a yarinta yake matuk'ar son aekin SOJA ,ko mai nashi a natse yakeyin shi dan a lokacin yana tunaninma UMMU ce mamanshi,AMAAN kam ya taso sakakken yaro bayajin bari babu abunda ya saka gaba sai gadara da tsabar rashin ji suna da kishiyoyin halaye shi da AHAAD wannan yasa ko kad'an basa zama inuwa d'aya,shekarar AHAAD sha hudu lokacin yana SS1,dan AHAAD badai kok'ari ba a lokacin kuma saukarsa biyu,AMAAN kuma yana da shekara goma yana JS1 saboda shegen wasa kullun cikin dawo dashi baya akeyi,kuma a lokacin ne BILKISU wato MUMMY ta kuma haihuwar y'arta mace,sosai sukayi murna,duk da su MAMA rashin haihuwar SHA'AWA yana damunsu,sai dai sun mik'awa Allah buwayi gagara misali lamarinsu,ranar suna yarinya taci suna FADILA,sosai AMAAN ke matuk'ar son FADILA yana cewa shima AHAAD yaje mamanshi ta haifa masa tashi,kasancewar FADILA ita kad'ai mace sai kowa ya mik'a kulawarsa gareta,shekarar FADILA d'aya UMMU ta samu ciki,sosai sukayi farincikin da suka dad'e basuyi ba,JAFAR kam har sadaka yayi don murna,kulawa kam ba'a maganarta a ta ko wanne ba'angare,cikin ikon Allah lokacin haihuwa UMMU ta haifo yaranta masu masifar kyau kamar aljannu duka mata ,duk ko kwantonka baka isa ka iya ganesu ba,yaran har sunfi UMMU kyau ga farinsu da daukar ido,murna a wurin AHAAD ba'a magana dan rasa inda zai saka kansa yayi,ko da ALHAJI AMINU yazo nanma sai da yayiwa jariran kyautar kudad'e masu tsoka,BILKISU kam haushi kamar ya kasheta tace ita data haihu wai kad'an ya bata(kuji k'arfin hali ba ja'ma'a😂),ranar suna anyi shagali na gani na fad'a,nera tayi kuka kuwa,yara sukaci suna NAJWA da NAJMA,sai muce Allah ya raya,tun daga wannan lokacin duk wani gata da kula ya dawo kan NAJWA da NAJMA mussamman NAJMA wacce ke da fara'a da son mutane tana yarda da kowa,inko taga AHAAD har tsalle takeyi,shima yana masifar sonta dan yafi daukarta ma akan NAJWA duk da ba'a ganesu shi yana iya ganesu,watan su NAJMA 7 ,Allah yayiwa mahaifan SHA'AWA rasuwa ta dalilin hatsarin jirgin sama ta hanyarsu ta dawowa daga Canada sunje ganin jaririn BASHEER din, mutuwar data girgiza kowa a garin katsina kasancewar ALHAJI AMINU sananne ne,anyi kuka sosai d rashin ,BASHEER ma da matarsa yazo tare da jaririnsu,kafin ya tafi aka raba gado,sosai yayiwa y'ar uwarsa nasiha sannan ya kwashe iyalanshi suka tafi yana kuma begen k'anwarsa,bayan rasuwar da wata biyu shima BABA ALHAJI SULAIMAN Allah ya k'arb'i kayansa shi da JAMILA (Goggo) da SALE ,a motar MAMA kad'ai aka fidda da ranta,sosai ahalin suka girgiza dan BILKISU har d'an k'aramin hauka tayi saboda rashin Goggo,sai dai muce Allah yajikansu,tun daga wannan lokaci JAFAR ya koma LAGOS yayi masu tanfatseten gini ya kwashi MAMA da iyalansa da kuma KABIR da iyalansa suka dawo lagos da zama,NAJMA ta taso yarinya marar tsoro duk da k'ananun shekarunta idan su MUMMY sukawa UMMU abu takan dage ta rama mata,ko kadan bata da tsoro,ga son mutane da fara'a badai kaga tana fushi ba,yayin da NAJWA ta taso yarinya mai sanyin hali ko kad'an bata damuwa da abunda ke faruwa a gidan,sai dai in anyi ta bawa UMMU hak'uri,suna da shekara 10 YAA AHAAD ya samu aeki ya fito a CAPTAIN na sojojin k'asa,yasha gwagwarmayar rayuwa,yayin da ya ida zama babban saurayi kuma d'an gayu na gani na fad'a,sab'anin AMAAN take aekin zaman Office a Campany din ABBU. inga ruwan comments sai na k'arawa alk'alamina kauri.pls share Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arahe🙏 STYLISH STAR⭐ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 NA *MARYAM ISMAIL MAJIDADI* Facebook Maryam ismail majidad'in kainuwa wattpad MARYAMMAJIDADI123 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* page 2 lab'e take jikin window sai aekin turar baki gaba takeyi,ga fuska ta shagwab'e kamar zata fashe da kuka,jin k'arar bud'e gate yasa ta juya da sauri dan ganin waye ya shigo,ganin motocin AMAAN ya sakata fad'in "yauwa Allah",shikam cikin takun k'asaita da nuna zallar ya cika namiji ya k'araso wurin fuskarsa dauke da murmushi,hannunta ya kama yace"wa kuma ya tab'a satauniyar gidan nan haka?".wani far tayi da ido dukda k'ananun shekarunta saika dauka hakan kamar yanga takeyi sai dai kuma haka hallittarta take,cikin sonyin kuka tace"Yaa Amaan ba Ummu bace ba",yasan sarai wani rashin jin tayi dan NAJMA ba dai rashin ji ba,wannan dalilin yasa ya jawota jikinshi da soyayyar k'arya dansu cinma wasu nasarorin su,"rabu da Ummu kinji,ae yanzu na dawo zo muje ".be jira ansarta ba ya kama hannunta zuwa part dinsu,sai da sukazo daidai k'ofar d'akinsa sai taja ta tsaya tare da sunkuyar da kai k'asa,shima kallonta yayi yace"yadai?,shigo mu tafi mana",hud'ubar Ummu ta fad'o mata a rai kamar yanzu take maganar na cewa kada ku sake naga kuna shiga d'akin mazan gidan nan in ba ta kama dole ba,girgiza hannunta da yayi yasa ta dawo daga tunanin data tafi"no ka shiga dai zan jiraka a parlo"ta k'are maganar cikin sanyayyar murya da d'an k'aramin bakinta .isowar MUMMY wurin yasa duk suka juyo suna kallonta tace"AMAAN ina ka tsaya haka?,kuma nasan kasan yau Yayanku zai dawo ko?".yatsine fuska yayi cikin isa yace"to da me zan masa?,nifa MUMMY nace ki daina had'ani da wannan mishkilin mai daukar kansa yafi kowa,karma ya dawo ni ba abunda ya dameni dashi"Amaan ya k'are maganar cikin gadara"Allah ya baka hakuri Son ,zo muje NAJMA kafin ya kammala shirinsa"hannun NAJMA taja sukayi room dinta,siririn tsaki AMAAN yaja ya wuce d'akinshi da tunani kala kala. suna shiga bedroom din MUMMY ,NAJMA ta langwab'e fuska tana narai narai da ido wanda gashin ido gazar gazar suka cika idon saika dauka ta k'ara ne"MUMMY da gaske Yaa Ahaad zai zo yau?,naga Ummu da masu aeki sunata girki da yawa".murmushi Mummy tayi najin dad'in sunyi nasarar jan NAJMA jikinsu tace"eh mana,yana k'araso har Idi ya tafi daukoshi tare da DADDY "zaro dara daran idanuwanta tayi masha Allah na fad'a da ganin yadda idanuwanta ke da girma,ta daura hannu a kai tace"munga ta kanmu,yanzu zai hanani zaman parlo da magana a gida",shafa kanta Mummy tayi tace"karki damu zan maki maganinsa bazan bari ya tab'amun y'ar lelena ba"da sauri NAJMA ta rungume Mummy tana dariya da jin dad'i fal ranta.da sauri suka mik'e sukayo waje danjin k'arar motoci na shigowa ,mota ukku ta shigo sukayi parking,tsayawa sukayi kowa fuskarsa dauke da murmushi yana jiran fitowar gwarzon wanda ya dad'e baya k'asar,harsu Ummu sun fito,sojoji ne suka fito tare da zagaye motar tsakiya Daddy kam tuni ya fito ya k'araso wurin su Mummy,koda Emanuel ya bud'e masa motar ya dad'e be fito ba,sannan a hankali ya fara zuro k'afarsa dake sanye cikin takalmin sojoji bak'ak'e,ya dad'e kafin ya idasa fitowa baki d'aya,masha Allah sanye yake da wandon kakin soji sai bak'ar T-shirt,hannunsa daure da agogon soji wani sanyayyan k'amshi ya feso tare da iskar dake kad'awa ,kallona na mai da garesa,fuskarnan kamar kullun daure take babu alamun wasa,fari ne ga idanuwa masu daukar hankali da rikita marar gaskiya,yana da tsayi sosai ga faffad'adan k'irji,lumshe idanuwansa yayi wanda suke dauke da tarin gajiya ,duka hannuwansa ya saka cikin aljihun wandonsa ya fara takowa cikin izza da tsantsar mulki,tafiyar AHAAD kad'ai abun kalloce,cikin natsuwa ya k'araso garesu ,kai tsaye gaban Ummu yaje ya duk'a har k'asa cikin sanyin murya wanda saika natsu sosai zakaji me yake cewa yace"UMMUna sannu da gida?".cikin dauki da murmushi dake nuna tsantsar soyayya ta daura hannunta akan kafad'arsa ta dagoshi tace"yauwa Babana,barka da dawowa,ka tafi kabar mana kewa"murmushi kawai yayi,gaisuwar da NAJWA take masa ya sakashi juyawa yana kallonta,cikin murna tace"Yaa Ahaad sannu da dawowa,ya hanya?",kallo d'aya yayi mata ya gane NAJWA ce ,"Alhmdllh "kawai ya fad'a,ya wuce wurin MUMMY rungumeta yayi tare da daura kansa akan kafad'arsa yace"i miss u mom",duk da tarin haushin da takeji ya fara zuwa wurin UMMU haka ta daure ta kirkiri murmushin k'arya tace"nima nayi kewarka Son,sannu da hanya,muje ciki ka huta",cikin d'ari d'ari NAJMA tace"sannu da dawowa"beko kalleta ba,tunda yaji yanayin maganar sai kawai ya share,duka suka dunguma zuwa cikin gidan,wani haushin yakaici ya k'ule NAJMA cikin ranta tace"kambu wallahi da sakal inna k'ara kulaka kamun wannan shariyar ae"sosai ranta ya sosu dan NAJMA ta tsani wulak'anci. A parlo suka samu AMAAN yana ta faman latse latse a waya,da sauri ya sauke k'afarsa daya daura d'aya kan d'aya yace"your welcome back brother",gyad'a masa kai kawai AHAAD yayi dan harga Allah ya gaji da magana,a parlo suka zauna ,shikan necewa kowa komai ba ya wuce part dinsu dan ya samu ya watsa ruwa,Idi ne ya shigo da jikkar laptop dinsa da phones nasa har k'asa ya duka ya bawa Daddy yace"Y'allabai k'aramin Alhaji yabar jakkar sa a mota ",karb'a Daddy"yayi yace sannu da kokari Idi".kallonsa ga NAJMA ya mayar yace "tashi ki bawa Yayanku kila a iya kiransa".wani fad'uwar gaba NAJMA taji daurewa tayi ta karb'a dan Daddy kam ba zata iya masa gardama ba,mutum na gari da sanin ya kamata duk da ABBU dinsu baya zama k'asar amma baya nuna masu k'yara ko banbanci da yaran nasu,mikewa tayi ta karb'a jikinta na rawa tana tsoron had'uwa da AHAAD,a hanya sukaci karo da FADILA wani banzan kallo ta watsawa NAJMA tace"halan ke mahaukaciya ce da bakya ganin mutane in uwarkice zaki bangajeta haka."wani uban tsaki NAJMA taja tana bin FADILA da mugun kallo tace"to ae inaga yanzu kinga banbanci balle ki kira uwata a ciki,ke har wata abace da mutun zai san ta taho bare ya kauce,ina ajin balle girman gaskiya kin yaudari kanki ,wannan kuma ya zama na k'arshe in dak'ik'ancinki ya tashi da zaki saka uwata a ciki"bata jira cewar FADILA ba tayi gaba abunta fuska had'e,sake da bak'i haka FADILA ta bita da kallo cikin d'aga murya tace"kan ubancan wallahi yau sai anyi bala'i a gidan nan ,sai kin gayamun uban waye dad'ik'ik'i"da sauri AMAAN ya fizgi hannun FADILA ya toshe mata baki,dak'in MUMMY ya shiga da ita ya saka key,cikin hassala FADILA tace"nifa Yaa Amaan bansan wannan abun wallahi,yarinya ta zageni ka hanani cin ubanta a gidan nan"wata uwar harara ya b'alla mata yace "aeke bansan yaushe zakiyi hankali ba,kwata kwata bakya rabawa,bakiga meta dauko bane?,kayan Yaa Ahaad ne fa,so kikeyi ki jawo mana bala'in da duka gidan zaita cin ubanmu,kike wani kwashe baki ke ga uwar bala'i,to ki sani watan k'aryaki ne ya tsaya a gidan nan,rigima karki fasa wallahi,tsab zan tattara kayana na gudu sai ya yafi na dawo",knocking k'ofar da akayi ne ya k'ara daga hankalinsu,sosai FADILA ta tsorata ,hannu ta daura saman kai tace"shikenan na shiga ukku ni Fadi,na janyowa kaina bala'i"sai hawaye sharr,"kaini bansan tsabar iskanci ,ku bud'emun k'ofa na shigo"MUMMY ta fad'a cikin tsawa dajin haushi,jin muryar MUMMY yasa AMAAN bud'e d'akin,tana shigowa ta ja tunga ta tsaya tana rike kunkumi cikin hassala tace"wallahi ba'a isaba,be yiwuwa in haifi yaron da cikina amma kuma ya fifita wata banza a kaina,ina tsaye amma ko kallo ban isheshi ba sai da yaje ya gaishe da waccan gayyar tsiyar sannan yazo wurina,wallahi na gaji da ganin SHA'AWA a gidan nan".dafata AMAAN yayi yace"cooldown MUMMY ae dama kece kika tsaya b'ata mana lokaci,kawai ki bani dama nayiwa yarinyar nan wayau ta fad'amun komai kawai sai mu aekasu",murmushin takaici MUMMY tayi tace"tabbas lokaci yayi da zamu kawar da abunda ya tsaya amana a hanya,lokaci yayi da zamu wataya,amma sam in har NAJMA na gidan can ba zaka iya aekata komai ba,kabar ganinta da k'ananun shekaru amma akwai wata baiwa da Allah ya bata,ni zanyi maganin ta,daga baya sai kayi sauran aekin,sanan kuma ka bari sai waccan gayyar tsiyar ABBUN naku ya dawo dan shima ya kamata ya tafi ko dan mu gaje dukiya,dama ta haramce ya tara"(kujimun MUMMY da k'arfin hali fa😄😂),wata sanyayyar ajiyar zuciya FADILA ta sauke tace "wallahi gara ku hanzarta,danni zan iya shak'e waccan matsiyaciyar yarinyar wata rana,shegiya me kalar aljannu,haka akwai koma ace mune baya,kullun sune gabanmu,to gara komai ya canza na gaji da zama baya","karku damu in dai ni BALKISU diyace ga JAMILA kuma nononta na sha to zanyi maganin abun cikin ruwan sanyi ba tare da samun matsala ba,amma ya zama dole ku kawar da k'iyayyar da kukewa NAJMA dole mu jata jikinmu har zuwa lokacin da burinmu zai cika"haka sukaita k'ullawa da sak'awa,nikan nace hmm muje dai zuwa . tsaye tayi bak'in d'akin gabata na fad'uwa ta rasa me zatayi,knocking ta yi har sau ukku amma shiru ba ansa,hakan yasa tayi shahada ta tura k'ofar ta shiga,wani sanyayyan kamshin dad'i ya bigi hancinta sai da ta lumshe ido,kafin ta daura k'afarta akan lallausan carpet din dake malale tsakar d'akin,komai na d'akin blue ne sai golding kad'an babu wani yawan tarkace a dakin sai dai yayi masifar had'uwa,gani takeyi kamar yaune ta fara shigowa d'akin,zaune yake a d'aya daga cikin chairs na d'akin ya daura k'afarsa d'aya kan d'aya ya lumshe idanuwansa kamar mai barci,a hankali yake taunar pink lips dinsa wanda hakan ya zame masa jiki,wandon sojinne jikinsa sai vest kawai,shagala tayi da kallonsa,kamar daga sama taji muryarsa yace"meye?"dukda k'ananun shekarunta sai da taji daban cikin in ina tace"Daddy yace na kawo maka wannan"be ko motsa ba bare tasa ran zai mata magana,kusan minti biyar sannan ya mike ya iso gabanta ya kama hannunta ya had'e wuri d'aya,zaro idanuwa tayi harta fara hawaye tace "dan Allah Yaya kayi hakuri wallahi na daina"kallo ya k'ara binta dashi cikin hassala yace"tun yaushe na hanaki saka kaya haka"kallon jikinta tayi wando ne iya gwaiwa sai farar vest sai net data sakawa kanta,cikin kuka tace"Yaa barci na tashi ,shine kuma MUMMY ta fito dani haka"ta k'are maganar tana turo baki,k'ara had'e fuska yayi yasa hannu ya murd'e bakin da k'arfi,wani azabar zagi taji da zugi sun ziyarci ballanta ,tuni suka koma kalar ja,ihu take san yi amma ba dama,sai hawaye kawai dake zarya a kumatunta,cikin kausasshiyar murya yace"next time zan cire bakin ne,in ance ki fita haka kuma ki kara fita haka pls"ya k'arashe maganar yana ingizar da ita,k'asa ta fad'i ta bige kai da bango wani ihun azaba ta saki,ganin ya nufota yasa ta arce ana kare tana kuka,kwafa yayi ya juya sam ya tsani shigar banza,dukda ba wani girma NAJMA din tayi ba,kuma bata da kiba ko kadan,yawan masifarta da surutunta yasa ko kad'an basa zama inuwa d'aya,haushi take bashi ,shiyasa baya d'aga mata k'afa ko kad'an. Da gudu ta shige parta dinsu kai tsaye jikin UMMU ta sauka tana kara fasa k'ara,"nikau iskancin yarinyar nan yawa gareshi,yo in banda sakalci meye na haye uwarki da girmanki haka,ki wani ishi mutane da bakinki kamar na tsuntu"MAMA ta fad'a wacce ke zaune tana dama fura,wata harara NAJMA ta balla mata tace"anje anyi to","kimun iskanci wallahi insa wancan mishkilin bayahuden ya maki shegen duka,nama nasan shiya sakaki kuka yanzu"wani kukan NAJMA ta kuma sakawa,dariya NAJWA ta saka aeko fad'an ya juye kanta,da k'yar UMMU ta rabasu ta zauna rungume da NAJMA tana aekin lallashi dan NAJMA badai bak'ar zuciya ba,abu kad'an zai hassalata. *yanzu aka fara,salon na dabanne kudai ku bani comments nima na dage da faranta maku rai,kamar yadda na fada labari ne na daban salonsa daban da ko wanne,pls share* Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe. STYLISH STAR⭐ Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 NA *MARYAM ISMAIL MAJIDADI* Facebook Maryam ismail majidad'in kainuwa wattpad MARYAMMAJIDADI123 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* page 3-5 "kinga ki daina wannan kukan kinji Yarinyata,kuma ABBU dinki zai dawo anjima fa"UMMU ta fad'a a cikin kunnen NAJMA,saurin d'ago idanuwanta tayi tace"la da gaske Ummu?"ta k'arashe tambayar cike da yarinta."da gaske mana,amma in kika b'ata fuskanki ae kinsan bazaiji dad'i ba",rungume UMMU NAJMA tayi tana wani dariyan farin ciki da gudu tabar cinyar UMMU tayo main parlo na gidan gaba d'aya.tsayawa tayi tana k'arewa HAJIYA SADIYA kallo wacce keta kwad'a sallama,wani haushi ya ziyarci NAJMA ita bata san me wannan matar ta mata ba,ko kad'an jininsu bai had'uba,ganin ISLAM a bayanta yasa ta k'are had'e fuska tamkar an aeko mata da mutuwa,remote ta dauka ta zauna tare da fara canza tasha"ikon Allah ke baki ganin manyanki ,anata sallama kinyi wani shiru,wannan aeba tarbiyavbaceba,ita SHA'AWAN haka ta koya maki?"ta k'are maganar tana wani yatsina fuska,ita ga babbar HAJIYA,wani irin banzan kallo NAJMA ta jefa mata tace"karki kuskura,abun naki ya tsaya iya kaina,dan wallahi yanzu zan tata rashin kunya ga tsohuwa ahto"da sauri MUMMY ta fito dan taji maganar NAJMA kuma tasan k'aramin aekinta ne tayi abunda yafi wannan ma,"dan Allah AMINIYA kiyi hakuri,kinsan halin yaran yanzu,yanzu dai zo muje daga ciki ma tattauna"kallon mamaki HAJIYA SADIYA tabi MUMMY dashi cikin ranta tace anya lafiyar BILKISU kuwa qlau bari dai naje naji,jan hannun ISLAM tayi wanda tun d'azu take cika tana batsewa tana hararar NAJMA ,tana samu su MUMMY sukayi gaba aeko ta maza ta gayyato FADILA tare da fad'a mata abunda ya faru,jikinsu har rawa yakeyi su fito sai dai parlon wayam hakan yasa suka nufi wurin sha'k'atawar gidan sunsan iyakar yawanta kenan,aeko anan suka sameta ,harda gudu suka had'a suna zuwa FADILA ta dag'a hannu zata kaiwa NAJMA mari,da sauri ta duk'e ta mari iska tana d'agowa tace"kan ubancan,yo wallahi da kin mareni yau gidannan da kinga tashin hankalin da baki tab'a gamo dashi ba,ko uwata bata tab'a tamarina ba sai ke kutt",carab ISLAM tace"ae uwarki daban mu dabankuma da kinsan darajan uwar taki da bakiyiwa ta wasu wulak'anci ba"ji kake tas tas tas NAJMA ta dauke ISLAM da mari har ukku ta nunata da yatsa tace"yarinya ki kiyayi bakinki,uwata tafi gaban shiga irin wannan k'azamin bakin naki in kuma wani dukan kikeso to ki maimaita banza kawai"kuka ISLAM ta fashe dashi tace"wallahi Allah saina rama"tuni dambe ya kacame a tsakaninsu NAJMA ta yarda ISLAM k'asa tahau jibga kamar Allah ya aeko ta,ita kam FADILA sai faman janye NAJMA takeyi tanaso itama ta daketa,duk su biyun sun rasa yadda zasuyi da ita,da gudu NAJWA ta k'araso wurin tana cewa"innalillahi dan Allah kuyi hakuri ,ku daina mana"kuka ta sanya tana k'ok'arin rabasu. Zaune yake daga gefansu idonshi lumshe kamar mai bacci ,sanye yake da 3quater ja sai farar t-shirt,cup din lemun dake hannunsa ya ajiye ya d'ago idanuwansa yana kallonsu gaba d'aya hayaniyarsu ta dameshi tun da suka fara fad'an duk yana jin me sukeyi,tabbas yasan basu lura dashi ba da basuyi gigin wannan fad'an ba,yunk'urawa yayi ya mike ,takalmansa farare y'an soke ya sanya tare da zura duka hannayensa a aljihu,cikin takun izza da cikarsa na namiji ya k'araso wurin wata tsawa ya daka masu,tuni suka saki juna kowa ta kama kanta,da sauri NAJWA ta had'iye kukan da takeyi,kallonsu kawai yayi cikin sanyi murya yace"ku sameni d'aki"yana zuwa nan ya juya ya wuce,wani saban kukan NAJWA ta saki tace"shi kenan kun janyo mana,wayyo Allah dama banzo nan ba","dallah malama ki rufe mana baki,to da waya gayyatoki matsoraciya kawai,ni in kinga ina fad'ana ki daina wani zomun rabo tunda zuwanki baya da amfani"NAJMA ta fad'a tana bin hanyar d'akin AHAAD dukda a tsorace take sosai sai dai bata san raini ,bata so su ISLAM su fahimci halin da take ciki na tsoronsa,sukam duk hawaye sukeyi a haka suka shiga d'akin,zaune suka sameshi a chair yayi d'aya kan d'aya,rage tsawansu sukayi d'an nesa dashi ,a hankali FADILA tace "Yaa AHAAD gamu","idan na sake jin bakinki sai kin raina kanki"ya fad'a amma ko motsi beyi ba,bazaka tab'a cewa shi yayi maganan ba,can kusan minti biyar ya d'ago yana k'are masu kallo duksun jikgata da rage tsawon,NAJMA ce kawai ta daure amma shi yaga gajiyanta sai dai sanin halinta da yayi na nuna jarumta ga abu,"NAJWA tashi ki tafi"sai da gaban NAJMA ya fad'i dukda kanta k'asa yake tasa ita zai kira,aeko har had'a step takeyi garin barin d'akin,cikin kausasshiyar murya yace"meyasa bakwajin magana?"cikin san kuka ISLAM da FADILA sukace "Yaa AHAAD dan Allah kayi hakuri,wallahi itace da tsokana tun farko"wani wawan kallo ya bisu dashi sora kad'an su saki fitsari yace"na tambaya ne",har lokacin kuma NAJMA bata d'agoba ko ta motsa ba,saboda tsabar zuciya"magana ta k'arshe wannan ya zama fad'a na karshe da zan kamaku kunayi,wallahi idan kuma kuka dab'a kunsan sauran,kuna manya amma rashin kunya baya barinku zama lafiya a gida,ku tashi kuje ke kuma NAJMA ki tsaya"wani zuciyanne ya k'ara ciwota,tana jin gudu gudun su FADILA suka wuce a d'akin,k'arasowa yayi gabanta ,ji tayi zuciyarta na neman fad'owa saboda azabar tsoro,amma ta dake still bata d'ago ba,"a gidan nan ina kuma kika sabo tarbiyar yiwa manya fitsara?"ya fad'a murya a tsawace, bakinta na rawa tace"ba ko ina","owk raini ne ?"shiru bata ansa ba sai fashewa da tayi da wani irin azabban kuka,zama kawai tayi ta had'e kanta da gwaiwa taci gaba da rairo kuka,cikin haushi ya mangare mata kai yace"na maki wani abunne sarkin jan sheri",bata kulasa ba taci gaba da kukanta a hankali tace"wallahi duk shegiyar data kuma sakamun Uwa a shirmenta saina illata..."wani wawan bugu ya kaima bakinta da sauri ta had'e maganar ta fad'a jikinshi ta rungumeshi kwarai tana cewa"Yaa kayi hakuri wallahi na daina","inafa zaki daina sai ranar dana cire wannan bakin dake zagi da rashin kunya sakarya kawai",jin kamar zai k'ara dukanta yasa ta kuma nak'aleshi,wani irin yanayi yaji yana shigarshi lokaci d'aya ,boyayyen ajiyar zuciya ya sauke yace"tashi ki barmun d'aki kin wani cikani da ihu kafin ni na karyaki kin"aeko kamar jira takeyi ta runtuma a guje,wani b'oyeyyen murmushi ya saki mai mai wuyar gani a fuskarshi yace"y'ar k'aramar yarinya sai jaraba",sometimes har mamakin jarabar NAJMA yakeyi har tsoro take bashi,bata da hakuri ko kad'an ga bak'ar zuciya,ko ina ta samota oho,dan UMMU da ABBU badai hakuri ba,ko magana ma basu cika yiba. tana fita ta k'ofar baya ta bi,d'akinsu ta shiga ta kwanta a bed tana rabsar kuka har bacci yayi awan gaba da ita a hakan.tana shan baccinta ABBU ya dawo,sai da ya shigo har d'aki ya ganta sannan ya wuce nasu d'akin danya kimtsa,ko da ya tambaya meya sakata kuka,NAJWA ta fad'a masa murmushi kawai yayi yace"kai MAMANA akwai rigima wallahi",dariya MAMA tayi tace"ni dai bata gadoni ba,dan bani nace a saka mata KHADIJA ba,jarabar yarinyar can tayi yawa wallahi,kamar jira takeyi a tab'ata tahu bala'i can dai tayo gadonta kai wannan yarinyar jarabar JAMILA(GOGGO) ,babu abunda ta baro itace ta tashi da masifa haka"duka dariya suka saka sannan ya wuce abunshi. B'angaren su MUMMY kam suna shiga d'aki HAJIYA SADIYA tace"AMINIYA me nake gani haka?wace irin tab'ewace ta sameki har kike gogan bayan y'ar SHA'AWA?",dariya MUMMY tayi tace "haba kwantar da hankalinki kinsan bani abu sai da dalili ae,wani abun nake nema a yarinyar kinsan itace garkuwar iyayen nata ae,dana sayeta zata bamu labarin komai kafin mu aeka dasu"dariya HAJIYA SADIYA tasa wacce yara ke kira da AUNTY tace"yauwa AMINIYATA ni dai nasan angulu ce ke bakya jewar banza,ni yanzu ga maganin nan na ansa maki,kiyi kok'ari yaci wallahi yana ci ya gama aeki,zai dawo hannunki duk wannan zafin kan na KABIR{DADDY} wallahi tafiya zaiyi sai yadda kika juya abunki,dama ga takarar SENATOR dinnan da ABBAN ISLAM ke kok'arin ya fito tun da shi na mutane ne tuni zasu tada jam'iyyah mu zama mu ke da gwamnati,ba za'ace suita siyasa ba amma cikinsu a rasa me fitowa takara ba"wani murmushin jin dadi MUMMY tayi sannan ta karbi maganin,sosai suka sha fira kafin HAJIYA SADIYA ta wuce akan cewa kome kenan sai sun sake had'uwa. *inji ruwan comments reader's dan ALLAH ,danshi zan karanun kwarin gwaiwar suburbudo maku labarin,har yanzu bamu shiga sarkakiyar labarin ba ,kudai ku kasance dani majidadi zanjin ya zata kaya* Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe STYLISH STAR⭐ Jorderh majidadi *RUHIN FANSA* PAGE 6_10 Mummy da kanta tayi girki a ranar,alkubus tayi da miyar agushi tasha busasshen kifi,fa kaitar idon masu aeki tayi ta zuba maganin daidai inda tasan zata bawa Daddy,saurin juyowa tayi danjin sallamar Abbu bata san zai dawo a lokacin nan ba,fuska ta saki tace "tace a'a barka da dawowa Abbu ashe ana tafe?"tayi tambayar fuskarta sake,shima murmushin yayi yace"wallahi fa ina hanya Mummyn yara,ya hidima da gida kuma?,fatan na sameku lafiya?","lafiya qlau Alhmdllh"ta fad'a da gudu Fadila ta fito tana masa oyoyo fad'awa tayi jikinshi,wani uwar harara Ahaad ya jefa mata yace"sai kin karya mana shi ko","a'a Babana barta ae tayi kewan babanta da yawa ne ,ko Fadilana"ya karashe maganar yaba kallonta,kai ta d'aga alamun eh,fitowar Najwa da Ummu da Mama ya mai da hankalinsu kansu,sai harara Fadila ke zabgawa Najwa ,ko kulata batayi ba saboda bata da rigima kwatakwata,cikin girmamawa Abbu ya duk'a har k'asa yace"ina wuni Mama ,mun sameku lafiya?","lafiya qlau Jafar ,sannu da dawowa","yauwa Mama"rungumesa Najwa tayi tana jin kaunar Baban nata,shima tsam ya riketa a jikinshi,"kaji mun tab'ara in banda tsoron Allah ke Najwa shine zaki mak'alemun y'a in banda daukar alhaki".dariya suka saka banda Ahaad da yake mik'awa Fadila jikkar Abbu yace"zan wuce sama","kaga gantalalle,balcecen banza me halin yahudawa,kai kullun fuska a tamke kuma ba sakewa da y'an uwa,nikan ba haka mariganyi na yake ba gaskiya,daba sani dana hana wannan suna gaskiya",kwafa Ahaad yayi bece komai ba,sai tamke fuska daya kumayi ya wuce part dinsu kai tsaye,kowa b'angarensa ya wuce dan su shirya su dawo dining,suna shiga b'angarensa suka zauna yace"Ummu ina Daughter na ,tunda na taho idanuwana suke mararin ganinta,hankalina yayi kanta,daurewa kawai nayi da ban ganta a parlo ba",murmushi Ummu tayi tana Mika masa cup din ruwa tace"Abban Najwa kana yawan nuna soyayyar Najma,baka tunanin hakan zai iya shafar zumuncin yaranmu?,son yayi yawa ",cup din ruwan yakai bakinsa yasa sannan ya ajiye ya maido da hankalinsa kan Ummu yace"amma Ummu ae kinsan ina b'oyewa ,kuma Ina kwatanta adalci,duk abunda zan mallakawa Najma kinsan ina k'ok'arin mallakashi ga y'an uwanta,saboda haka kici gaba da addu'a kawai",wanka yayi ya shirya kafin suka fito dining din,fitowar Najma kenan daga d'aki sai cika takeyi tana batsewa tsabar masifa kawai ke cinta ,fuskarnan kamar an sauko mata da mutuwa,d'agowa tayi danjin kamshin turaren Abbu aeko da gudu ta ruga ta rungumesa ,shima rik'eta yayi sosai a jikinsa a kunnenta ya rad'a mata"Ina kika b'oye Lilly na",turo baki tayi tanawa Ahaad kallon k'asa Wanda bema nuna yasan da shigowarta ba a shag'wab'e tace"Yaya ne",murmushi kawai Abbu yayi yaja hannunta suka k'arasa dining,a fakaice Mummy ta zabga masu harara tana magana da zuciyarta,duka suka hallara dining ,Daddy yana gaishe da Abbu ba yabo babu fallasa,Mummy da kanta ta zubawa kowa kafin suka zauna suka fara ci a nutse,banda Ahaad dake ta faman latsa waya,Abbu ne ya kashe shirun da fad'in" nikan ina Amaan ne?tun da na shigo gidan nan banji ko motsinshi ba","Ina fa zakaji motsinshi yana can yana fama da shashanci sai faman shegen yawo"Mama ta fad'a tana tab'e baki tare da kai loma a baki(honi Mama tamu ta mutunci bata bar kowa ba🤣😂),shigowa parlon yayi yace"dama ke kullun saka ido kika saka a gaba)cewar Amaan dake shigowa parlon,sosai ya daure zuciyarsa ya samu ya saisaita kanshi ya duk'a dan harga Allah yana matuk'ar kiyayyar Abbu a gidan ganin yafi Daddynshi komai,kanshi a k'asa yace"Abbu barka da dawowa",cike da sakin fuska Abbu yace"lafiya qlau Amaan,sannu ya kok'ari?","lafiya qlau"ya fad'a yana Jan kujera kusa da Najma yana zama,kamo hannunta yayi cike da kulawa yace"sweet sis,barka da hutawa",wani irin bugawa gaban Ahaad yayi,yana maimaita sunan da Amaan ya Kira Najma dashi,ga hannunsu da yake gani rik'e da juna,ta k'asan table ya saka k'afarsa dake cikin b'ak'aken takalmanshi ya danne k'afarta da k'arfi harda murzawa yakeyi,wani irin k'ara Najma ta saki tana kallon k'asa,hankalin kowa ya dawo kanta,kowa yana tambayarta lafiya,shikam ko motsawa beyi ba bare kasa ran shi yayi muguntar,wani irin bakin ciki da kishi ya turnike Fadila tana jin tsanar Najma Wanda ta zarta da komai a rayuwa,saurin had'e kukanta tayi tace"ji nayi kamar wani abu yana bina fa"ta k'are maganar a shag'wab'e,"shine kuma dan iskanci zaki wa mutane ihu,wallahi Najma saina sab'a maki a gidan nan"Ummu ta fad'a,"ni dai wallahi da ba'a hannuna aka haifi yarinyar nan ba da sai ince canzota akayi,duk wani iyar shege yana wurin falwayar yarinyar nan uwar tsawo ,ko kad'an bata da hankali".harara Najma ta zubawa Mama,sai dai ta kasa cewa komai tasan tsab zata sha fad'a wuin Abbu komai zatayi yana dauka amma banda takurawa Mama,a k'a'idar Ahaad komai zaici sai yasha tea,kallon tea din dake kusa dashi Najma tayi sai tiririn zafi yakeyi,a hankali ta dunga matsar da hannunta har ta tankad'o cup din ya zub'e a hannunsa da yake latsa waya dashi,da sauri ya d'ago jin azabar zafin dake ratsa shi,sai dai ko motsi beyi ba,tana kallon idonshi wani irin tsoro ya ziyarceta tayi saurin duk'ar da kai,"innalillahi Najma anya kina da hankali kuwa"gani Ummu ta yunk'ura yasa tabar wurin da gudun tsiya,bowl me ruwan sanyi Ummu ta dauko tana saka hannun Ahaad ciki,sai jera masa sannu takeyi,kowa ya mai da hankalinsa a kansa,rike hannun Ummu yayi bayabo ba fallasa yace"Ummu am owk,zanje jirginmu ya kusa tashi",sai lokacin suka San zai tafi,bankwana yayi masu ya wuce part dinshi,jikkar labtop dinsa da phones ya dauka yabi ta k'ofar baya ,ta window ya hangota tana lek'enshi,yi yayi kamar be ganta ba,da sauri Ema ya rugo ya k'arb'i jakkarsa yaransa sai saluting nashi sukeyi,hannu kawai ya d'aga masu ya shige mota,kamar ko yaushe mota ukku suka cika suka nufi airport,"mutun sai shegen mishkilanci da gadara"Najma ta fad'a tana turo baki. "Mummy just kawai ki bari nayi me nayi niyyah"Amaan ya fad'a yana fita waje,kai tsaye wurin Najma ya nufa tana zaune tana ta faman rubuce rubuce,dafata yayi yace"lil sannu da aeki",ba tare data dagoba tace yauwa Yaya",tattara books din tayi ta maido hankalinta a kanshi ,a hankali yace"waini sis har ina Abbu yake b'oyon takardunku na filaye da campanies dinku,na dai San k'anwar tawa babbar yarinyace akwai tarin dukiya"washe baki Najma tayi tace"wallahi ko Yaya ,kaga Campany dina ukku sai filaye da tarin kudad'e,kullun Abbu cikin saka mana kud'i a accounts dinmu yake,gana Ummu data raba mana kudad'enta ni da sister,ga Wanda Grandpa ya bamu akace tun haihuwarmu"."ah ah kice dai da Hajiya nake zaune ban sani ba,ranki ya dad'e,uwar gidana"ya k'are maganar yana risinawa,dariya Najma keyi harda k'yalk'alawa tace"wallahi fa duka Documents din suna d'akinshi a k'asan gado cikin wani akwatin k'arfe yace sai mun gama scul zai bamu".wani irin sanyin dad'i ya ratsa Amaan dajin yasan inda kayan suke,haka yaita janta da fira har lokaci ya tafi. Wani irin k'ara Najma ta saki tare da isawa inda Najwa ke kwance malemale cikin jini duk an soketa da wuk'a,ga k'asanta na zubar jini anyi mata faca faca almar fad'e ,saurin riketa tayi tana kuka dukta gigice tace"wa yayi maki haka,wallahi bazan barshi ba".cikin wahalar numfashi Najwa take magana a hankali tace"yanzu ba wannan lokacin bane ba,duka dukiyata na baki,na tura duk wani kudina a account dinki,kowa yayi wannan akan dukiya yayi shi,ki zama jaruma ,ki dauki fansa akan koma waye,kada kiyi kuka kada ki karaya"wata magana ta k'ara gaya mata a kunne a hankali tace"kiyi komai ta sirri"takardu ta mika mata a wata jakka ,take komai nata ya saki,rai yayi hakinsa,cikin ihu Najma tayi d'akin su Ummu tana kwalla masu Kira,abun da ta ganine yasa komai nata tsayawa dukda k'ananun shekarunta hakan sai da ya girgizata,Abbu ne kwance cikin jini,sai Ummu dake kwance itama jikinta duk jini,jin motsin mutane a gaban part din ya sakata lekawa da sauri,dukansu fuskarsu a rufe da bakin abu,ganin suna zubawa ko ina fetir yasa tayi d'akinsu da sauri,jikkar da Najwa ta bata ta dauka bata jira komai ba tayo part din su Ummu,a bakin mamaki a lokacin gawar Abbu kawai ta iske,kuma babu alamun an fita dan babu sawun jini,ji tayi an fizgota da k'arfi zuwa waje,juyawa tayi ta boye jakkar saboda kashedin da Najwa tayi mata,sauri takeyi taga masu zuba fetir din kafin a kunna wutan,baya tayo da sauri ganin part din ya kama da wuta bal bal,wani irin ihu ta saki tana kiran sunan su Abbu,da sauri Amaan ya k'araso ya janye ta ,kallonshi tayi kamar mesan gano abu sai kuma ta k'ank'amesa tana kuma sakin kuka mai k'unar zuciya,nunfashinta ne ya dauke gaba d'aya ta sume a jikinshi,shafa bayanta yayi ga fuskarsa dauke da murmushi mai wuyar fassaruwa,daukarta yayi ya shiga part dinsu da ita,kuka riris Mama keyi tayi zaune a k'asa tana fad'an innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,wannan gobara ta cutar damu"kuka sosai Mummy da Fadila keyi kamar ransu zai fita,Daddy kam ya rasa ta cewa ya goya hannuwa a baya ga masu kashe wuta sunzo ,a kujera Amaan ya ajiye Najma kanta Mama tayi tana girgizata"Allahu akbar,ashe Najma tana raye ita,rashin jinki yayi amfani nasan fita kikayi har wutar ta kama baki ciki"sai kuma ta fashe da kuka,ruwa Mummy ta shafawa Najma ,wani irin yunk'urowa tayi da sauri sai dai idonta kyam hawaye kawai ke zarya a kan fuskarta,bata ida daskarewa ba sai da taji ana sanarwa Daddy sai dai suyi hak'uri ga tokar su Abbu nan da Ummu an kwaso harda ta Najwa,girgiza kai Najma tayi dan tabbas tasan lokacin da wutar ta kama Ummu hata d'akin,sai dai bata ce komai ba,dafe kanta tayi dake barazanar tarwatsewa tabbas ita kanta tasan shekarunta sunyi k'anana da daukar wannan tashin hankalin.kuka ya koma sabo gida ya kuma rud'ewa tuni ko ina ya dauka da rasuwar Alhaji Jafar Sulaiman Bindawa da iyalansa. Bayan sati biyu *Yanzu muka shiga labarin,ku dai ku bani ruwan comments nikan n saki alkalamina* *Kuyi hak'uri da jina shiru kwana biyu wayana ne ya lalace,amma yanzu na canza zaku rika jina* Stylish star 🌟 Jorderh majidadi *RUHIN FANSA* page 11-15 Abubuwa sun faru dana dad'i da akasin haka,gaba d'aya yanayin gidan ya canza yanzu,kullun cikin farin ciki suke da jin dad'i kasancewar yanzu suna da yak'inin babu Wanda zai iya tarar masu gaba,Mama kam komai sukeyi tana saka ido dan lamarin Bilkisu sai dai addu' hakan yasa bata kula ta ko kad'an kullun tana part dinta,ba k'aramin abu bane ke fiddota ba. Kwance take tana bacci sai zufa takeyi kamar wacce wani abu ke faruwa da ita a cikin bacci,a wani irin firgice ta farka bakinta dauke da addu'a,hawaye suka zubo a idanunta da gudu tayi waje ga ganin gabanta batayi,babu kowa a bakin gate hakan yasa ta fice abunta,dukda hanata fita da Mama keyi,kiyy kiyyy motar ta bada k'ara tare da tsayawa ,Driver din motar ya fito a hassale yace"ke wacce irin dabbar yarinya ce?,baki ganin gabanki salan ki jawa mutane sheri ko?".fitowar mai asalin motar yasa yayi saurin had'iye sauran maganarsa mussamman da yaga irin kallon da take binsa dashi matace da ba zata gazawa shekaru 40 ba kyakyawa da ita ta sha wankanta na alfarma,cikin dad'in murya da mutunta dan adam tace"Bala meye haka,so nawa nake gaya maka ka daina irin wannan halin?","kiyi hak'uri Hajiya naga da yanzu ta janyo mana wani tashin hankalin ".wani banzan kallo Najma ta bisa dashi kafin ta maido hankalinta ga Hajiya Maryam dake tambayarta "yarinya lafiya kuwa?,me kike so?".hawaye wasu na korar wasu da k'arfi tace"adalci nake buk'ata zaku bani?,i want justice"ganin kamar bata cikin hayyacinta yasa Aiban dake bayan Hajiya Maryam fitowa ,kyakyawan namiji ajin farko San kowa kin wanda ya rasa Aiban ba fari bane ba sai dai yana da haske mai kyau Wanda kallo d'aya zaka masa kasan hutu ya ratsa shi,dogo ne me faffad'an kirji gashin kanshi mai sheki irin me gazar gazar dinnan,kallonta yayi cikin dad'in murya yace"ayyah Mr kyakyawa ki daina b'ata fuskanki haka da kuka please,me akayi maki?",takai tsawan minti biyu tana kallonsa ,tana k'arewa halittar Allah kallo,manyan idanuwanta da suka fara canza cala ta lumshe tare da taune lips kawai sai ta juya tana share hawayen dake k'ok'arin zubo mata,har Aiban ya d'aga k'afa zai bita Hajiya Maryam (Ammi) ta rik'e hannunsa suka koma mota. A hankali take tafiya harta iso gidan kai tsaye baya ta wuce ,dan bata buk'atar hayaniya ko wani magana yanzu,tunda abun nan ya faru Najma tayi wani irin sanyi bata magana ko kad'an ,zakayi abunka kaci ka tsire ko kallo baka isheta ba,magana ta zama abu mafi tsada a wurinta,ga rashin san hayaniya ,gaba d'aya ta canza wani irin mishkilanci ya shigeta. Cikin tak'un k'asaita yake fitowa daga mota dawowarsa k'asar kenan tun bayar tafiyarsa,sauri kawai yakeyi yaje yaga Ummu ya tambayeta meyasa kullun wayarsu ita da Abbu a kashe,in ya tambayi y'an gida kuma suita masa b'oyeb'oye wanda sarai yasan dole akwai abunda ake b'oye masa,wannan dalilin yasa ya dawo k'asarma badan ya gama abunda yakeyi ba(Allah sarki Ahaad besan meke faruwa ba😭).sanye yake cikin kak'in uniform na soji yayi wani masifar kyau sosai kayan suka masa kyau ga wani sihirtaccen kamshi da yake fitarwa,so yakeyi sai ya fara yin wanka kafin ya shiga cikin gidan,kayansa ya karb'a a hannun Ema ya wuce ta k'ofar baya,tun daga nesa take jiyo k'amshin turarensa ga wani irin fad'uwar gaba amma ko motsawa batayi ba,kallon bayanta yakeyi harya iso kusa da ita,hakan yayi daidai da iskar me dad'in gaske na yanayin damana yake kad'awa tare da k'amshin k'asa gashin kanta dukya tashi,hannu tasa da niyar mayar da gashin bayan kunnenta taji an sakar mata wani azababben rank'washi,mai makon yaga ta juyo da masifa kamar yarda ta saba balle batasan waye ba sai yaga ta taune lips dinta kamar zata huda tare da yamutse fuska a hankali ta juyo kallo d'aya tayi masa ta kauda kanta,wani irin fad'uwa gabansa yayi ganin halin da take ciki,daure fuska ya kuma yi yace"wuce ki rufe kanki",bata ce komai ba ta Mike ta nufi cikin gida,tsaye kawai yayi yana kallon wani irin sauyin da be tab'a zato ba,anya wannan Najma ce kuwa,sosai abun ya bashi mamaki,d'age kafad'a yayi alamun ina ruwansa yayi ciki abunsa,yana shiga d'aki tun a parlo ya fara cire kayansa,duk da baya nan d'akin ba laifi and'an gara amma kallo d'aya yayi mashi ya gane wannan ba gyaran Ummu bane ba kuma bana Najwa bane ba ko Najma dan yasan suma takan sakasu gyaran d'akinshi, toilet ya shiga yayi wanka daure da towel ya fito ga k'arami yana goge sumar kanshi,phone dinshi ya dauka ya Kira waya banji meye fad'a ba sai naga ya ci gaba da abunda yakeyi kuma. "Najma nace ki gayamun haka zakici gaba da rayuwa bacin abinci ba walwala ,Najma magana ma gagararki takeyi,dan Allah kiyi hak'uri mu dauki kaddara kinsan ko wanne bawa da tashi kaddara nasan abun dole ya tab'aki amma banyi tunanin zaikai haka ba,ace gobara ta cinye naka tas ba Wanda ta rage ae akwai tashin hankali wallahi".hular dake hannunta ta net ta saka tare da cukuicuye tulin gashin kanta Wanda yake safkowa har tsakiyar baya,ta sakashi cikin net din cikin sanyin murya Wanda muryarta ta dad'e da komawa haka tace"dan Allah Mama kibar hayaniya haka,ni ba abunda ke damuna,kawai dai nasan yanzu babu zafin da bazan iya jurewa ba,zuciyata ta daskare bana k'arayin kuka dan ciwon cin amanar da akamun kuma zan iya jure komai yanzu,kuma....."saurin rufe bakinta tayi gudun kada Mama ta gane inda ta dosa,yasa ta juya zata kwanta,shigowa Fadila tayi tace"Yaa Ahaad yace kizo Najma"."lailahaillah yauni Dije naga abunda ya isheni,waini Fadila yaushe zakiyi hankali haka kawai yarin haihuwa bana haihuwa bad'i ki ringa shigomun wurin ba sallama kamar tsohuwar b'arauniya?".turo haki Fadila tayi tace"bayan wacce nayi baki ansa ba"ta juya ta fice abunta.bin bayanta Najma tayi ta wuce part din Ahaad duk surutun da Fadila keyi ko kad'an bata kulata ba,tana zuwa bakin k'ofa ta d'an tsaya kafin ta kwankwasa k'ofar,sai da tayi kusan sau ukku sannan can cikin mak'oshi yace "shigo"tunda ta shigo ya kafeta da ido har tazo gabansa ta d'uk'a amma batace komai ba,kusan minti ukku suna haka sannan yace"zaki gyaramun d'akin nan ne",kai kawai ta gyad'a ta mik'e cikin sanyi,d'akin baya buk'atar wani gyara amma haka ta dage tana gyara ko ina kamar yadda Ummu ke koya masu,ji takeyi kamar ta saka ihu ko zataji sauki a hankali take tuna ranakun da suke taya Ummu aeki,saurin had'iye hawayenta tayi,ta k'arasa mopping din ta wanke toilet tuni d'akin ya dau k'amshi ba kamar yadda akayi gayaran d'azu sama sama ba,duk abunda takeyi yana kallonta,mamakin canzawarta yakeyi sai dai ya hango tsantsar damuwa da tashin hankali a tattare da ita,kallon inda ta tsurawa ido yayi akan bedside drawer dinsa pictures dinsa ne da Ummu da Abbu,sai wani d'aya da yake cikin kak'i,fad'uwa gabansa yayi daurews yayi ya janyo hannunta,wani irin yarr yaji amma ya dake a hankali yana lumshe ido yace"Ina Ummu?"kallon mamaki ta bisa dashi sai dai ta kasa cewa komai,girgiza hannunta yayi da k'arfi yace"please kice wani abu"hawayen data kasa tsaidawa ne suka gangaro akan fuskarta a hankali tace"duka sun rasu",wani irin zaro ido yayi yana mata wani mugun kallo yace"na lura bakya da hankali har yanzu amma ae me 11yrs ya isa ace yana da hankali"silifas dinsa ya zura yayo waje a matuk'ar rikice,a parlo ya samu duka y'an gidan suna kwasar dariya,a k'ufule yace"Mummy me kuke tunanin kunyi?,ace ba Wanda zai iya gayamun abunda ke faruwa a gida?".sai yanzu Mama ta fito tace"saboda basa so hankalinka ya tashi shiyasa har gobara ta cinye wan ubanka da matarsa data reneka da kuma kanwarka Najwa,Najma kadai Allah yasa bata cikin part din"tuni idanuwansa sun canza cala,wani irin harbawa zuciyarsa keyi da k'arfi,dafe kansa yayi dake barazanar tarwatsewa,tuni ya fara k'yarma,cikin tsantsar b'acin rai yace"yanzu idan iyayena suka mutu baza'a gayamun ba,sai su danba haihuwata sukayi ba,wallahi bana kallonku da banbanci hasalima yadda na shaku da Ummu ko kwatan hakan banyi da Mummy ba"ji yayi jiri na neman kwace masa da sauri Daddy ya kamasa ya zaunar da shi,ruwan sanyi Najma ta miko Daddy ya bashi yasha ,a hankali yake sauke ajiyar zuciya,kallon mutanan parlon kawai yakeyi"a wanne station kukayi reporting ?",maganarsa ta dawo da Mummy cikin hayyacinta kallon tsab yake mata yana ganin yadda ta rasa abun fad'a,mikewa kawai yayi yabar parlon be sake cewa komai ba.boyeyen ajiyar zuciya Mummy ta sauke duk da tasan bawai yabar case din bane ba,amma tana tunanin kafin yayi wani yunkurin zata iya gyara kokai. Shigowar Nani Fammah yasa Najma sakin murmushin da batayi niyyah ba,aeko da gudu taje ta rungumeta tace"Nayi kewarki Nani".Nani babbar macace zata iya kaiwa shekara 36 amma tana da kyan jiki duk da ta kasance ba musulma ba ,ba zaka iya gane shekarunta ba,ita take taya Ummu rainon su Najma har suka girma kuma ita ke kula da komai nasu har yanzu,tayi tafiya zuwa garinsu ne sati biyu daya wuce duk da bata nan komai ya faru,amma ta San komai a waya,shiyasa ta dawo danta kula da Najma,Nani Fammah itace amintacciyar mai aekin Ummu. *Gaskiya bana jin dadin yadda bakwa comments yarda ya dace ba kamar da farko ba,idan har naga ba comments alamun bakwajin dad'in lavarin kenan to zan daina rubutawa kuwa in ba'a gyara ba* Allah ka gafartawa iyayenmu kasa muyi kyakyawan karshe. Stylish star ☀️ Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 16_20 Cikin dishewar murya Najma tace"nayi kewarki sosai Nani"kanta take shafa cike da tausayinta dan tanajin kamar ita ta haifi Najma,"nima nayi kewarki y'ata"."Ina ga tunda kin dawo zaifi ku koma part din su Ummu da aka gama gyara jiya,komai kuke buk'ata saiku nema"cewar Mummy ta k'arashe maganar tana hayewa sama,gaisa da mutan gidan Nani tayi kafin taja hannun Najma suka tafi part din,babu laifi an gyara,kuma an zuzzuba y'an abubuwan buk'ata sai dai ba masu tsad'a ba.gyara ko ina sukayi tsab kafin Najma ta shiga wanka,da gudu tayo waje daure da towel tana nuna hanyar toilet cikin firgici,kamata Nani tayi tana girgizata tace"kina lafiya?,meye a ciki?,me kika gani?"ta jero mata wad'an nan tambayoyin.hannunta na k'yarma take nuna toilet din tana cewa"Nani Najwa ce,na ganta a ciki".lek'a toilet din Nani tayi amma babu komai,juyowa tayi tace "inaga kin tsorata ne babu komai a ciki".ajiyar zuciya Najma ta sauke tace"wallahi Nani na ganta a ciki,kuma ba k'arya nayi ba","ok naji kin ganta yanzu kije ki shirya, Driver zai kaiku duba exams dinku na JSCE ,Yayanku nasan Monday ku koka SS 1".turo d'an k'aramin bakinta tayi,addu'a tayi sannan ta shiga toilet din. Alhmdllh jarabawa tayi kyau,har sun gama komai Monday zasu koma SS1,sosai Najma tayi kuka ganin number din Najwa kuma itama taci,wani tuk'uk'un haushi ya isheta a hankali tace"zama ba nawa bane ba,dole RUHIna ya zama me cike da buri da zummar San daukar FANSA,na yi alkawari sai sun biya abunda suka yimun nan da bada jimawa ba"ta k'are maganar tana share hawayen idonta. Tunda ta shigo ta hango shi zaune yayi crossing legs dinsa idanuwansa a lumshe da ganinsa kasan ya zurma duniyar tunani,harta wuce ko motsawa beyi ba,sai da ya dad'e a haka kafin ya mik'e ya shiga parlon,maganar da Mummy ta masa yasa ya tsaya cak yana sauraranta,sai da ta gama sannan ya juyo yace"ni na ce suke su dibo,itama ae ya kamata ta koma scul din"juyawa yayi yaci gaba da tafiyarsa.k'wafa Mummy tayi tana aeyana ranta yadda zatayi maganin Ahaad. Shirin bacci tayi ta kwanta a d'akinta,lumshe idanuwanta tayi kamar meson yin bacci amma kuma hakan ya gagara,ji tayi kamar motsi a gefanta,a hankali ta soma bude kyawawan idanuwanta,sosai ta zarosu tare da mikewa tana fad'an "kece ,kece da gaske?" "Kada ki tsorata banzo danna cutar da y'ar uwata kuma jini na ba,mafi soyuwa a gareni ba,a'a sai kawai dan taimako, RUHINA bazai tab'a kwanciya ba ,inhar ba mun dauki fansa ba,fad'an yafi k'arfinki,sai dai ni ina cike da burin daukar FANSA,dole su sadaukar dole su ruhin d'ayansu ya zama RUHIN FANSA ga abunda suka aekata mana. Luuuu Najma tayi tana shirin somewa,da sauri Nani ta shigo tana kiran sunanta,ganin zata fad'i yasa tayi k'ok'arin tarota sai dai kafin ta tareta taga ta mik'e lafiya qlau kamar ba ita wani abun ya sama ba,sai dai idonta kawai daya canza ya zama ja."Nani kije ki kwanta ina lafiya ni"."y'ata ki kuka da kanki naji komai Ruhin y'ar uwarki ya fad'a haka ki zama a ankare,duk da yanzu na tabbatar Ruhin Najwa yana jikinki",kai kawai ta gyad'a mata sannan ta kwanta,tun daga wannan ranar Najma bata kuma jin d'uriyar Ruhin Najwa ba. 3years later Abubuwa da yawa sun faru na dad'i da marar dad'i,naci gaba da kuma fad'uwa dama rayuwa haka take dole akwai k'alubale akwai kuma nasara duk bawan dayayi imani da Allah to dole a jarabashi,hakan ta faru ga wannan family mai cike da abubuwan al'ajabi,ciki harda kammala secondary school dasu Najma sukayi.yanzu suna gida basa zuwa ko ina. Zaune take tsakiyar parlon,ta k'ara girma sosai duk da ko kad'an Najma bata da alamar k'iba a jikinta ,sai dai ba kuma zaka kirata wacce bata da shape ba,komai alamun girma sun bayyana a jikinta,daka ganta kaga cikakkiyar mace mai aji daji da kanta da kuma isa da mulki.kanta duk'e k'asa ta harde hannuwanta tana murd'a kamar tana wasa dasu,wani daddan k'amshin turare ya doshi hancinta sai dai ko k'an bata motsa ba bare ta d'ago sallama yayi amma shiru sai da ya k'ara sannan ta d'ago manyan adanuwanta ta zubasu garesa cikin dad'in murya da sai ka natsu zakaji me tace ta ansa sallamar,wani irin fad'uwa gabansa yayi yasan ko shekara d'ari zaiyi bazai tab'a manta me wannan fuskar ba,yana tare da ita,fuskar da kullun sai idanuwansa sun tariyo masa ita,ya makance akan nemanta,tsawan shekara hud'u be k'ara ganinta ba sai yau.maganar Mummy ce ta dawo dashi hayyacinshi tace"a'a Aiban ka k'araso kenan,sannu shigo mana kamar ba d'an gida ba zaka wani toge bak'in k'ofa"murmushi Aiban yayi tare da shigowa cikin tank'ameman parlon,amma idonsa k'yar akan Najma wacce tayi kamarma bata San wani ya shigo ba dan tunda ta mayar da kanta bata kuma d'agowa ba,"kije ki kawo masa abunsha kafin inzo"Mummy ta fad'a tana kallon Najma,ta d'an jima kamar ba zata tashi ba sai kuma ta mik'e ta nufi hanyar kitchen,kayan jikinta yabi da kallo sanye take cikin wando iya gwaywa fari sai t-shirt ash colour kanta yana cikin net,sai silifas ga wata agogo bak'a mai shegen kyau daure a tsintsiyar hannunta,har ta b'acewa ganinsa idonshi na kanta,ruwa da lemu ta dauro a k'aramin tray ta dauko,a ransa yace bata da k'iba sai dai akwai shape ba laifi komai ya dace da jikinta,a rayuwar Najma ta tsani kallo hakan yasa ta b'allawa Aiban harara tare da ajiye tray din,jin da tayi an fizgota ta mik'e tsaye yasa ta juyo a masifance taga wanne isasshen ne,Fadila ce ,cikin tsawa take fad'in"uban meye had'inki da Wanda zan aura?,wallahi Najma bazan tab'a barinki kiyi hasara a kaina ba wannan karon,kin jibge a gida babu mai so shine abun har yakai kin fara bin mazan mu".kamanta na k'arshe ji Najma tayi kamar ta watsa mata ruwan zafi ,da k'yar ta had'a harrufan bakinta tace"sake ni"y'an gidan har kowa ya fito wata irin yanayin murya Najma tace"sake ni"ba shiri Fadila ta saketa.tuni idanuwanta sun canza cala cikin kausasshiyar murya tace"ya zama na k'arshe da zaki shake yin wannan shashancin a kaina,in ba haka ba"k'wafa kawai tayi ta nemi hanyar fita,bin bayanta Amaan yayi yana bata hak'uri dan awai abunda yake buk'ata wurinta,cikin gajiya da ganinsa a tare da ita tace"please wai lafiya?",daurewa yayi yace"dama zan tambayeki ne,wai dan Allah ko kinsan ina Abbu ya ajiye wata agogo tashi?"ji Najma tayi kamar ta shak'esa sai kuma ta daure tace"ban sani ba"tayi gaba abunta,kwantaccen gashin sajenshi ya shafa yace"zakizo hannu ne,ni na wuce ajinki balle ki rik'a wani shan murr,lokacin dana saninki yazo ne" Kuka Fadila tasa tace"wallahi Mummy bazan tab'a barin Najma tayi nasarar kwacemun Aiban ba,ya kamata kiyi wani abu inba haka ba tabbas akwai gagarumin tashin hankalin dake doso gidan nan,Dan itama zan aeka da ita"saurin rufe mata baki Mummy tayi tace"ke baki da hankali kike irin wannan maganar idan wani yaji fa,kamar dai bani na haifeki ba,zanyi maganin komai kima fara daukar kanki a matsayin matar Aiban kawai"dariyar jin dad'i Fadila tayi ta mik'e tace"da kinmun haka kin gamamun komai"sannan ta fita,kallon Amaan takeyi hannunsa rik'e da Karan sigari yana busawa,"har yanzu dai baka rabu da sigari ba ko Amaan?,baka San lafiyarka?,to aeko ya zama dole ka barta yanzu.murmushin takaici yayi yace"babu kuma Wanda ya isa ya hani sha,idan kuma kina musu to ki kwatanta hanani,ni yanzu bana zaman kowa,so kisan akan me zamu rik'ayin magana". Inji ruwan comments pls share Stylish star Jorderh majidadi Page 21-25 "Nani inaji a jikina mamana tana raye,bata mutu ha"."meye haka kike fad'a anya Najma bakin fara zaucewa kwana biyun nan ba?".dafe kai Najma tayi cikin k'osawa da magana tace"ba wani zaucewa feelings din da nakeji yanzu ya banbanta dana ko yaushe".gyad'a kai Nani Fammah tayi tace"to ina rok'on hakan ya zama gaskiya ,da zanfi kowa farin ciki idan y'ata ta kuma kasancewa da Mamanta na asali"ta k'are maganar tana shafa fuskar Najma,murmushi sukayi tare da rungumar juna,saurin kallon agogon hannunta tayi Wanda a b'oye tasa aka canzawa cala ta danna tana k'are mata kallo,da sauri tace"Nani zanje baya",bata jira cewar Nani ba ta fice ta k'ofar baya kai tsaye bayan window din Amaan ta lab'e tana hango me akeyi a ciki,"Barrister ka fad'amun gaskiya kawai ".murmushi Bar Abbas yayi yace"Alhaji yabar wasiyyah da kada a bawa kowa dukiyarsa sai yaransa to kuma sun rasu da d'aya,yanzu bana da ikon fiddo kudin harsai ta cika wannan shekarun daya iba,amma kada ka damu lokacin nayi zan mallaka maku komai".murmushin jin dad'i Mummy tayi tace"inko harka rik'e amana ka zama daga cikinmu ta tabbas zaka samu kaso me tsoka,kuma ba zaka samu matsala ba kaga mijina shine Governor na katsina ,kaga ka samu y'anci"dariya yayi sosai ,sannan suka dauki cups da lemu a ciki suka sha cike da farin ciki. Ganin Bar Abbas zai fito yasa tayi baya da sauri ,ganin babu kowa a bayansa yasa ta fito ,da ido ya mata signal sannan ya jefa mata takarda , gyad'a kanta tayi ta dauki paper din ta tura a cikin rigarta,gabanta ne yayi mugun fad'uwa ganin sun had'a ido da Amaan tana zatan koya ganta, murmushin mugunta yayi yace"a'a yanzu kika zo ko kin dad'e a nan?",kawar da tsoron tayi tace"yanzu nazo"bata jira cewarsa ba tayi gaba abunta zuwa part din Mama,nuna ta da hannu yayi ta baya alamun ya gama da ita sannan ya koma d'aki,safa da marwa yaci gaba da yi kafin ya kalli Mummy yace"ya kamata Najma ta mutu".zaro ido Hajiya sadiya tayi tace"meyasa zata mutu,meye wannan yarinyar ta sani balle kuma a ce za'a kasheta?"kalllonsa ya maido garesu zama yayi ya daura k'afa d'aya kan d'aya yace"tsinken daka raina shi yake tsone maka ido,yanzu na ganta a wurin nan kuma ina da yak'inin taji komai amma sai ta wayance,yarinyar na lura tana da masifar wayau da fahimta,kuma dai kunsan tana da ilimi dukda mun hanata damar wucewa gaba karatu"."amma Amaan mace face,ina taga jarumtar daukar Fansa?,mace ba zata tab'a yin abunda namiji yayi ba,sai dai kuma bank'i shawararka ba,amma ina son abi hanyar da waccan mayatacciyar tsohuwar ba zata zargi komai ba,kun dai sai komai nata yanzu ya ta'allaka ne akan Najma".shiru duka sukayi alamar tunani can Amaan yace"zamu samu Dr ne d'an hannu ya bamu magani mu bata ta fara ciwo,idan kuma ta kwanta sai yayi mata allurar da zata kasheta ta ruwan sanyi"."yes hakan yayi ,shawara mai kyau sai dai waye likitan da zai mana wannan aekin?"Hajiya Sadiya ta fad'a,"Aiban,Aiban shi ya kamata ya mana wannan aekin saboda shine na jikinmu"Mummy ta fad'a,zaro ido Hajiya sadiya tayi tace"na shiga ukku ni sadiya,anya Bilkisu kina da hankali kuwa?,gaskiya kina buk'atar aekin k'walwa Aiban din zaiyi wannan aekin?,ko da wasa karku tab'a barin Aiban ya gane abunda mukeyi inko haka ta faru to ina tabbatar maku koni dana haifesa bazan tsira ba,saboda halina nak'in talakka Aiban be cika San zama Nigeria ba yafi zama can Canada wurin Auntynshi Maryam,dama dai ace Islam ce a matsayinshi da bana haufi,dan da tasha nono na bata zub'ar ba"."shikenan ku barmun aekin zan samu Wanda zaiyi mun komai"Amaan ya fad'a a haka suka baro part din kowa da tunanin dake ransa. Tana shiga d'akin Mama Fadila ta gani kwance tana ta faman danne danne a waya hankalinta kwance,k'afa ta saka mata tayi taga taga zata fad'i,amma tayi k'ok'arin dafa bango ta juyo tana kallonta kallon tuhuma,mikewa Fadila tayi tace"ae wallahi baki ba zaman jin dad'i a gidan nan,banza me kwacen saurayi kawai,ke ba namiji ba amma bakya da shiga sai k'ananun kaya da wando sai kace d'iyar kafurai?,a hakan zai soki,to ina fad'a maki sama tayiwa yaro nisa sai dai ya tada kai yai kallo,yadda kika baro cikin uwarki kisa a ranki haka ba zaki tab'a samun Aiban ba,banza karuwar gid...."had'iye sauran maganarta tayi danjin wasu irin zafafan maruka daga ko wanne kuncinta wani ihu ta saki hakan yasa Mama fitowa da gudu tana cewa"shikenan tashin duniyar yazo,kowa yayi ta kansa masu bak'in hali karsu rab'oni"turus ta tsaya tana kallon su Najma tace"ku kuma daga ina?,wannan wanne irin iskanci ne zaku cikamun kunne da ihu".a kausashe Najma ta muna Fadila da yatsa tace"wannan ya zama na k'arshe da zaki kuma ambaton iyayena a shirmenki,kuma ina so ki sani zan iya daukar komai daga gareki amma banda ki kirani karuwa ,waye kuma wani Aiban wai da mutun ne?,sai faman shishigi kikeyi amma baki k'arb'u ba ,shi Aiban din yaa nuna yana sanki ne bake kika kai kanki ba,to bari kiji ni ba soyayya zanyi da Aiban ba amma zan jawoshi jikina na kwaceshi daga gareki tunda haka kikeso,kuka inga duk fad'in gidan nan Wanda ya isa ya hanani abunda nayi niyyah","wallahi baki isaba ke k'aramar y'ar iska ce,zan nuna maki baki kaaiba,ni ni kadai ce wacce ta isa ta kula Aiban,ke har kin kai matsayin da kika mareni ,yau akwai tashin hankali a gidan nan wallahi"Fadila ta fad'a,"ke bansan iskancin banza da wofi,k'atuwar banza ki isheni da ihu a d'aki ni ku hita can waje ku k'araci iskancin naku,Dan kunga labcecen bayahude baya nan shine zaku tada hankalin kowa a gidan".uwar harara Fadila ta aekawa Mama tayi kan Najma dake shirin fita,da sauri ta damk'o gashin kan Najma dake cikin net ta janyo da k'arfi,had'e fuska Najma tayi tana jin zafin tab'a gashin na ratsa ta,a hassale ta juyo ta ingiza Fadila ta fad'a k'asa kanta ya bugu da table na tsakar d'akin ,wani uban dukan ta kuma yi mata a baki kan kace me dambe ya kaure a tsakaninsu,ihu Mama keyi tana neman ceto ta koma can bakin k'ofar d'aki tana cewa"wayyo jama'a na annabi Bilkisu kuzo kada suyi kisan kai,wayyo Sale(kana ina)na shiga ukku sun haifamun jaraba"sai kuma ta sake fashewa da kuka,shak'e Fadila Najma tayi kafin kace me ta canza mata kamanni dan sukanta takeyi kamar Allah ya aekota ko ganin gabanta bata yi,jin ihun Mama yasa duka sukayo part dinta harda Nani dake nufo wurin ga y'an aeki duksun fito,duk k'arfi Amaan kasa k'wace Fadila yayi,dan ba k'aramin shak'a Najma tayi mata ba,har idanuwanta sun zazzago ta fara hango mutuwa tana wani kuka,Mummy da Nani kam kuka suka saka,shigowarsa kenan daga wani aeki daya fita yau kwanansa biyu baya gidan a matuk'ar gajiye yake sai faman lumshe ido yakeyi,da gudu Mama data fito neman taimako tayo kansa tace"ka duba girman Allah Sule kaje kayi ceton rai,tunda uwata ta haifi ban tab'a ganin Najma a wannan yanayin ba kace karta kashe y'ar uwarta ita ta kashe kanta sai surutai takeyi mararsa kan gado"kamar bazai jeba kuma sai ya fara takawa cikin jarumta yayi part din,yana shiga yaga abunda ke faruwa ae da sauri ya k'arasa yana k'ok'arin k'watar Fadila dake dab da kabari(🤣😂honi Najma),ganin Najma tak'i saketa hakan ya tilasta masa saka duka k'arfinsa ya ingijeta tayi taga taga zata fad'i yayi saurin rik'o hannunta ,fizge fizge ta farayi tana kiran"wallahi yau saina yi maganinki duk wani iskanci da kikemun kawai saka maki ido nakeyi,banza jahila"Fadila kam jikin Mummy ta fad'a fuska duk jini sai neman sik'ewa takeyi."ki natsu mana,meye haka?"cikin sanyin murya yake maganar ganin bata sauraransa yasa ya zabga mata mari cikin tsawa yace"nace kima mutane shiru,bana san hayaniyar nan"sai lokacin Najma ta samu damar kuka wani irin zafi takeji a zuciyarta ji takeyi kamar anan watsa mata garwashin wuta,murya bata fita ta fashe da kuka,kafin Nani ta kamata yai saurin janyota yabar d'akin da ita,ranga ranga Amaan ya dauki Fadila suka nufi part din Mummy a gado ya ajiyeta tare da Kira likita,Mummy kam ta cika tayi fal sai sauke ajiyar zuciya takeyi da k'arfi tace"kai ina wallahi Sam bazai yiwu ba ba'a haifi yarinyar ba,ta maidamun jini na haka,wallahi sai yanzu na tabbatar da lokacin mutuwarki yayi shegiya mai siffar aljannu"."ohni Allah ya ceceni ba'a kashe kowa ba anan,yanzu da Kabiru saiya k'ullaceni ,Allah ya tsareni labcece yazo kan lokaci"sai kuma ta kwashe xa dariya tace"maganin y'ar banza kenan,nasan ita ta tsokaneta gobema ta k'ara in wahala bata isheta ba"haka Mama keta faman surutu ita kad'ai. A chair ya zauna yana kallon yadda take huci kamar taci babu,tabbas sai yau ya tabbatar tana nan a matsayinta na Najma sauyi ne kawai ta samu saboda halina rayuwa,girziga hannunta yayi amma Sam taki d'agowa saima hawaye dake bin kuncinta ga idanuwanta da suka rik'ide zuwa ja,ruwa mai sanyin gaske ya zuba a Mug bece komai ba ya kai a bakinta,bata ce komai ba ta fara shan ruwan dan dama tana buk'a ba zata iya magana bane ba,sai da ta shanye tas sannan ta koma tana ajiyar zuciya ,ta dad'e a haka kafin ya d'ago kanta gani yayi ta lanhwab'e a jikinsa alamun bacci yayi awan gaba da ita sai sauke numfashi takeyi tare da ajiyar zuciya,murmushi yayi yaja lips dinta a hankali yace"sarkin rigima kawai",a bed ya mai data yaja mata duvet kafin ya wuce d'ayan d'akin dan yayi wanka ya samu ya huta.soi da likita yabawa Fadila allurai sannan ta samu sukunin ciwan da jikinta yake mata tea tasha mai zafi sannan tasha magani daga nan bacci yayi awan gaba da ita. "Naji bayanan ku amma ina baku shawara ku bari wannan satin ya fita kudun kada a zargi Fadila,indai zaku biyani ba abunda zai hanani yi maku aekinku"murmushi Amaan yayi yace"kada ka damu ko nawa ne zan baka ae shiyasa na nemoka dan nasan zaka iya"sosai Dr Jameelu yayi dariya yace"zan wuce sai ka jini"misabaha sukayi kafin ya tafi.datiyar jin dad'i Mummy tayi tace"komai yazo k'arshe Najma". Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe,pls share. Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *MARYAM ISMAIL MAJIDADI* ______________________ __________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* *RUHIN FANSA Fans yau page din naku ne,ina jin dad'in yadda kuke nuna k'auna a novel din nan kuma kuke comments yadda ya kamata,I luv u guy,son so fisabilillah* Page 26-30 Tsaye yake yana kallon yadda ta jik'e da zufa sai jujjuya kanta takeyi alamun firgici da tsoro,wani ihu ta saki ta mik'e tana neman guduwa,cikin zafin nama ya rungumota zuwa jikinshi bubbuga bayanta yakeyi ,a hankali yake tofa mata addu'a,k'ank'amesa tayi kamar za'a k'wace mata shi,sun dad'e a haka kafin ta nutsu,d'agowa tayi a hankali tana kallonsa,wata uwar harara ya jefa mata yace"dallah malama barmun d'aki,kuma kici gaba da wasa da addu'a kinji ko?"ya k'are maganar yana tureta,tsare shi tayi da ido kamar mai tunanin abu sai kawai ta had'e fuskarta kamar an mata mutuwa ta kawar da kanta ta mik'e tabar d'akin,kai tsaye part dinsu ta nufa ,da sauri Nani ta rungumeta tace"kin tsorata ni y'ata ,meyasa kika yi haka?,na damu a kanki bana son wani abu ya sameki"ta k'are maganar tana hawaye tare da shafa fuskar.hannuwan Nani ta rik'e tace"karki damu dani ina lafiya ae,yanzu ba lokacin tsoro bane ba,lokaci ne yayi da nima zan nuna ina da daraja"bata jira cewar Nani ba tayi d'akinta Toilet ta shiga tayi wanka,tea tasha a tsai tsaye ta fito babban parlo na gidan Wanda rabon data zauna harta manta,zama tayi tare da d'aura d'aya kan d'aya ga Mug din lemu a hannunta,TV ta kunna ta mai da hankalinta gaba d'aya a kallon. Tsaye Mummy tayi daga stairs sai cika takeyi tana batsewa a hassale tace"kan uban nan,wallahi y'ar cikina bata isa ta juya gidan nan ba"da sassarfa ta k'araso parlon remote ta dauka ta kashe TV din tana k'arewa Najma kallo ,sanye take da purple siket yad'an wuce gwaywa mai tsaga a baya sai farar T-shirt anyi rubutu da Purple colour,gashin kanta ta saki tare da dauresa da rivom shima purple,sosai tayi kyau duk da ba wani tarkace a fuskarta,da hannu take nunata sama da k'asa tace"dube ki,kalleki saboda Allah kuma kullun kina Kiran kanki a matsayin musulma ,shigarki bata da banbanci data kafirai,ko wanne namiji haka yake kallonki "wani murmushin mai rikitarwa Najma tayi cikin kwantar da kai tace"Mummy ae a shiga kawai na tsaya,wannan kuma tsakanina da ubangijina ne ke baki da hurumin yanke hukunci akan shigata,and kuma ae Allah da abunda ke zuciya yake amfani bakya ganin in aka tona zuciya wasu ba zasu fito ba balle suyi yawo?,ki saka wannan a rai dama can yanayin shigata kenan kuma zanci gaba da yinta har lokacin da Allah yayi zan daina,kuma zanyi abunda ko wanne Namiji zai iya aekatawa ,zamana mace bazai tab'a zama gazawa ba".kallonta ta maida ga Iro sarkin mota daya shigo tace"iro a fiddo mun motar Abbu ina so zan fita"jiki na rawa ya ansa da "to ranki ya dad'e ,wannen Driver ne zai kaiki?"sai da ta d'an nisa sannan tace"ba bak'ata"da sauri ya gyad'a kai ya fita dan cika umarnin Hajiyar tasa,itakam d'aki ta koma hills ta sanyo masu masifar kyau da tsini sai handbang duka cakarsu white colour eyeglasses ta daura bak'i tayi kyau sosai mukulin hannun Iro ta k'arb'a tayi waje tana taku dai dai,Mummy kam tsaye tayi kamar statue ko motsi ta kasa yi,ta kasa yarda wai Najma ce ta zama haka lallai sun sakar mata da yawa,da sauri ta k'arasa ta window tana lek'enta,Najma kam wata dalleliyar Ranz rover ta shiga ba'a y'ar yayi ta fice gidan da gudu.hannu Mummy ta daura saman kai tana cike da matuk'ar mamaki yaushe ma Najma ta iya mota?da sauri tayi hanyar d'akin Amaan. Tuk'i takeyi hankali kwance sai lokacin nasan Najma dana phone ,wayarta ta fiddo Samsung Galaxy S7 ta turawa wata number sak'o ,kai tsaye wani pack ta nufa na y'ay'an manya ,parking tayi ta dad'e bata fitoba kafin ta zuro kyakyawan k'arta ,cikin Jan hankali take tafiyan babu Wanda ya damu da shigarta kasancewar lagos ba daga baya ba wurin k'abilu sai dai kyan da tayi yasa maza da yawa raja'a garin kallonta.a can private wuri ta zauna tana duba agogon hannunta ,abun sha aka kawo mata ,kad'an ta kurb'a lemu,zare glass din idonta tayi cike da k'osawa tace"Barrister ka dad'e fa",zama Barrister Abbas yayi yace "sorry ranki ya dad'e na tsaya duba wasu muhimman files dinne"ya k'are maganar yana ajiyesu a gabanta.d'auka tayi ta fara duddubawa ta d'an jima kafin ta saki murmushi tace"thank u,na gode kwarai da gaske ".cike da tausayinta yace"kada ki damu,munyi zaman amana da mahaifinki ya zama dole garemu mu rik'e amanarsa,duk kud'ad'en daya kamata su shiga account din ki sabo an tura,ga ATM nan da duk abunda ya dace".murmushi tayi ta k'ara godiya ta k'arb'a y'ar jakkar daya mik'o mata,sallama sukayi sannan ta juyo da niyar wucewa,ji tayi ta bige da mutun da sauri tayi baya ta d'ago dan taga wanene, murmushi dauke fuskar Aiban yace"malama Najma ashe ana ganinku a irin wannan wurin?",murmushin ta mayar masa tace"mezai hana idan mutun yana da wani uziri"kai ya jinjina yace"haka ne,ya kike?"a takaice ta ansa"da lafiya zan wuce"saurin Shan gabanta yayi ,gani tayi yayi mata wani irin k'warjini ga kyau sosai da batayi zaton yana dashi ba sai yau data k'are masa kallo,katse mata tunani yayi da fad'in"kamar kina jira nazo sai kice zaki tafi?,ya kamata ko a matsayin aboki a bani matsugunni please".juya manya manyan idanuwanta tayi,Wanda Sora kad'an ya shid'e saboda yadda suka dauki hankalinshi ,ji tayi ba zata iya musu dashi ba a sanyaye tace"tohm barka da zuwa aboki"bata jira cewarsa ba tayi gaba abunta.juyawa yayi yana k'are mata kallo yadda tayi masifar kyau ko kad'an Najma bata da k'iba sai dai tana da hips ba laifi ,gemunsa ya shafa a hankali ya furta"Masha Allah bata da banbancin da indiyawan usul"kanshi ya d'an buga sannan yayi gaba.cikin natsuwa take driving harta iso gida,gabanta ne yayi mumunar fad'uwa ganin Ahaad ya tare k'ofar shiga parts din gidan gaba d'aya ya zuba hannuwansa cikin aljihu,daurewa tayi ta fito tana tafiya cikin natsuwa,ganin irin mugun kallon da yake mata yasa ta tsaya gabansa ba tare da tace komai ba"ke wacce irin dabbar yarinya ce?,harkin isa just look at ur dressing"ya k'are maganar cikin tsantsar b'acin rai.sosai ta tsorata da yanayinsa tace"ni banga me shigana yayi ba ae"marin daya dauketa da shine ya sakata suma na y'an mintuna yace"har kina da wannan bakin?,ki fad'amun daga gidan ubanwa kike kafin na karyaki a nan".dafe kunci tayi tabi ta gefensa zata wuce fizgota yayi harta kusa fad'uwa ,"na gaji na gaji,me kake nema wurina Yaa Ahaad in baka iya ganina haka toka tafi,ka dai San bazan tab'a aekata abunda zai zubarmun da mutunci na ba a matsayina na wacce bata da kowa sai Nani d'ina,wannan shigar wani abunne daban tsakanina da ubangijina ina da abubuwan daya kamata na nuna zan iya,dan Allah na rok'eka ka barni na zauna lafiya naji da maraicina,na kumayi abunda zan iya,is barni na cika burina and kuma ina so ka sani I want to be a Soldier"ta k'are maganar tare da had'a hannuwa biyu alamar rok'o,File dinta da suka zube taga an mik'o mata ,k'arb'a tayi tare da kallon Wanda ya mik'o mata wani irin mumunar fad'uwa gabansu yayi su duka biyun,kauda hakan tayi ta k'arb'i files din ta shiga parlon,a table ta ajiye abunda ta shigo dashi cikin d'aga murya tace"Yaa Amaan,Yaa Amaan"cike da firgici Amaan ,Mummy da Fadila suka fito Wanda fuskarta ke a kumbure,kallo d'aya ta masu ta kauda kai tace"ka k'araso mana",murmushi kawai yayi ya k'araso yana kallonta."ina lissafin kayan da aka shigo dasu wancan satin?"wani kallon raini yayi mata yace "na rik'esu akai ae,me zakiyi dasu"."ka natsu nan a matsayin shugabarka ta aeki nake ,ba a matsayin k'anwarka ba,Dan haka ka fad'amun meye lissafin?",wani irin firgici da tsoro ya bayyana garesu,murmushi Ahaad yayi da suke shigowa da Muslim ya tsaya kallon ikon Allah,"a Campanyn ashana an siyar da kaya na million 25,sai na kayan masarufi na million 30"ya k'are maganar yana kallonta,murmushi tayi cikin haushi tace"lissafi yafi haka,a Campanyn ashana an sayar da kaya na million 30 ne,na kayan masarufi kuma na million 50 ne,dan haka duk inda million 30 yake to kaje ka nemosa nan da sati d'aya,kafin nazo akan sauran,ina mai sanar da kai daga gobe zan fara fita aeki kuma a matsayin shugabar ko wanne company da yake mallakin Babana,ka kula"kayanta ta kwashe tabar wurin tana tafiya cikin izza da k'asaita ,Mummy kallo takeyi tsab kamar Abbu ne ya dawo saboda har yanayin tafiyarsu iri d'aya,da kuma yadda yake harkokinsa "ragab ta fad'a a chair tana mai da numfashi hankali a yashe tace"shi kenan bansan meye abunyi ba kuma".gyad'a kai Ahaad yayi yaja hannun Muslim sukayi part dinsa,ruwan sanyi Amaan yasha yace"mun kashe maciji amma bamu sare kansa ba". Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe. Stylish star Jorderh majidadi *RUHIN FANSA* *MARYAM ISMAIL MAJIDADI* *_________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* *inawa masoyana fatan alkhairi,na dawo zamuci gaba da gashi,na sadaukar da page din kyauta gareku na gode da soyayyarku ,masu Kira da masu text a chart ko a phone na gode kwarai Wanda ban samu amsamawa ba yayi hakuri kunsan abubuwan da yawa majidadinku na nan cikin koshin lafiya Kuma ta dawo dan faranta making* PAGE 31-35 Dafe kai Amaan yayi yace"tab wallahi akwai babbar matsala dole musan abunyi","kwarai kuwa karka damu zan shirya wani abun,yo me akai akayi Najma Allah na tuba yarinyar da aka haifa akan tafin hannuna"Mummy ta fad'a tana mik'ewa tare da wucewa d'akinta,Najma Kam tana shiga part dinsu taga babu kowa Kai tsaye d'akinta ta shiga ta adana files din da tazo dasu,sannan ta saka kayan training ta fito,bayan gidan ta zagaya kallon k'ofar tayi an dad'e ba'a bud'e wurin ba da sunan a shiga sai dai duk week masu aeki sukan shiga su gyara wurin,bud'ewa tayi ta shiga ko ina fes abubuwa da yawa suke dawo mata akan wurin ,gani takeyi kamar zataga Abbu ya fito dan motsa jiki duk safiya,goge guntun hawayen dake idonta tayi ta soma motsa jikinta kamar zata shid'e training kala kala takeyi tana Kuma koyon abubuwa da dama,tuni tayi zufa sharkab ,fitowa tayi babban filin wurin Wanda yake k'awace da filawowi da Kuma glasses masu matukar k'yau filin an tana deshi ne saboda buk'atar gudu,gudu ta fara tana zagaye filin.Muslim dake kallonta ta window ya juyo ya kalli Ahaad yace"wacece waccan yarinyar?),shiru kamar beji saba sai Kuma yaje"Najma".da sauri Muslim ya juyo yace"what Najma kana nufin itace ta zama haka?,Amma nayi mamaki meye Kuma tsakaninta da Ahaad?".d'ago daradaran idanuwansa yayi a lokacin da yake k'arasowa gaban window din kallonsa yakai gareta,yaga yadda duka halittar jikinta ke motsawa wani irin kishi yaji ya turnik'eshi,janyo hannun Muslim yayi suka zauna amma be kuma cewa komai ba.a matuk'ar gajiye ta zauna a chairs din wurin da sauri cikin masu kula da wurin ta kawo mata glass cup dauke da ruwan sanyi,hannu tasa tare da janye gashin kanta daya rufe mata ido,sannan ta k'arbi ruwan tana tana mai da numfashi a hankali a hankali,sai da ta huta sosai sannan ta dauki k'aramin towel tana Kuma goge fuskarta tayo hanyar fitowa,ji tayi ta buge da mutun tayi baya zata fad'i,hannunta ya riko yana kallonta Sora kad'an takai k'asa Kuma yaki d'agota ya Kuma ki barinta ta k'arasa k'asa ,turo d'an k'aramin bakinta tayi tace"ae dama da gangan zaka tureni,ni ka sakeni"waro ido Ahaad yayi yace"what"sakinta yayi ta fad'a akan stairs din wurin ta bige k'ugu rintse ido tayi da k'arfi zata saki k'ara yace"shihhhhh a hakan zaki zama sojan?",had'e fuska tayi ta shanye hawayenta ta mik'e tana murgud'a masa baki tabi ta gefan sa ta wuce tana rike k'ugu murmushi yayi ya juya"wallahi har yanzu baka bar mugunta ba mugun banza "Muslim ya fad'a yana tangare k'eyar Ahaad,be dai ce komai ba har suka bar gidan. Bayan wani lokaci Tun daga lokacin da Najma ta koma office komai yayi daidai ga ma'aikatanta ,tana matuk'ar k'ok'ari tanayin duk abunda ya dace sai dai ta zama busy bata da lokacin kanta balle na wani,dukiya Kam Alhmdllh sai habbaka takeyi sai dai Sam ba haka Amaan da Mummy suka so ba dan ta tare masu ko ina ,duk da suna cutarta ta k'asan k'asa amma sam sai ta nuna bata damuba,b'angaren Fadila Kam tunda sukayi fad'a da Najma har yanzu takeyi ciwo tsaitsaye har yakai ga ya kwantar da ita dukta bi ta k'are sai wahala takeyi tsabar taurin kai ya hanata zuwa asibiti a dubata Kuma taki yarda ko wanne likita ya dubata.Zaune suke kowa ya zurfafa cikin tunani "yes yes"Amaan ya fad'a yace ku kwantar da hankalinku komai yazo k'arshe,kubarmun komai nan da kwana kad'an zakuga sakamako."to Alhmdllh hakan yayi kyau dama sanyarka ce ta saka muke shan wahala ya kamata ayi komai da tsari gaskiya"Hajiya Sadiya ta fad'a.fad'ad'a murmushi Mummy tayi tace"karki damu,Amaan mun baka wuk'a da nama in dai nina haifeka yarinyar nan karta kuma sati biyu a duniya koma meye kayi,sai dai kayi a hankali dan yayanku yau zai shigo gari"."Baku da matsala Mummy zanyi komai yadda ya dace".fitowarta kenan daga meeting tayi matuk'ar gajiya sanye take da suit bak'a sai rigar cikin fara tasha zanzaro daura suit din saman tayi a k'ugunta kanta sanye cikin wata k'aramar farar himar ta idonta sanye cikin farin eye glasses ,shoe dinta bak'ak'e hill dasu tayi matuk'ar kyau sosai sai zuba kamshi takeyi duba tsadaddiyar agogon hannunta tayi kafin taja siririn tsaki ta nufi office dinta,tsaye tayi ganin Aiban zaune yana zama jiranta , mataimakiyar ta taso da sauri ta k'arfi files din hannunta tayi cikin office din dasu ,zama Najma tayi akan bench din da yake zaune sai dai d'an nesa dashi tace "ae ban san ka k'araso ba".murmushi me kyan kallo ya mata yace "ya za'ae ki sani bayan gimbiyar tawa tana can tana fama da harkar kasuwanci".y'ar dariya tayi tace"wannan suna yana mun nauyi ina laifin k'anwa ko kuma k'awa"."zaki gane nan gaba dukkin wuce wannan matsayin a tare dani"d'agowar da sukayi sukayi ido hudu da Fadila wanda shigowarta kenan tayi kyau cikin shigar bak'in dogin riga saidai tayi rama ba laifi ga wani haske da tayi,fuskarnan tata murtuke kamar an aeko mata da mutuwa tayo kansu tace"kutumar uba,yanzu Aiban cin amanar da kakeyimun kenan?,to wallahi bazan tab'a y'arda ba Kuma wannan zai zama na k'arshe,ganin tayo kan Najma yasa ya Mike da sauri ya shiga tsakaninsu yace"Fadila meye haka?,sai kin tara mana mutane?,karki kuskura kiyi k'ok'arin kaiwa gareta".wasu hawayen bak'in ciki suka zubowa Fadila tace"lallai Namiji ,Namiji ba d'an goyo ba ,akan wancan sakaryar kake wani tareni karna tab'ata ?,ina hankalinka yaje ?ko ka manya ita din k'anwatace shine cin amanar ya wuce kan kowa sai k'anwata zakaso ?,wallahi wallahi indai ina numfashi hakan bazai tab'a faruwa ba"tureshi tayi cikin huci da zafin zuciya ta nuna Najma da d'an yatsa tace"ke Kuma butulu maciyiya amana,macijiya wacce bata ramin kanta wallahi saina saka kinyi kukan wuya,wallahi saina zama Dana sani a rayuwarki bazan tab'a raga maki ba,Kuma ina gargad'inki ki rabu da Aiban,stay away from him"jikkarta ta dauka data fad'i k'asa ta fasa k'arasawa ciki ta fita da gudu tana kuka Kai tsaye inda tasan zata samu Islam ta nufa. Najma Kam har yanzu bata motsa daga inda takeba sai da ya juyo yace"madam dan Allah kiyi hakuri"hannu ta d'aga masa tace"karka damu kasan nasan komai,Amma aeni ina tare da Kaine a matsayin aboki kuma Yaya bawai bawani abun ba,itace take kasa fahimta nasan tana sanka ae tasan bazan tab'a sanka da aure ba ,sai dai muyi rayuwa mu mutunta juna,ni zan wuce gida"bata jira cewarsa ba ta shiga office dinta hand bag da key din motarta da jikkar laptop dinta ta dauko ta fito,bata samesa a wurinba dama tayi zaton hakan,mota ta shiga tayi hanyar gidan zuciyarta da tunani kalakala harta k'arasa gidan zuciyarta bata samu sukuni ba,me gadi ya bud'e mata gate ta shiga ta dad'e a ciki kafin ta kwaso kayanta ta fito zuwa cikin gidan,a parlo ta yada zango zama tayi tare da fad'in washh,ta soma rage aninayen gaban rigarta tana k'ok'arin zare rigarne ta d'ago idonta sukayi ido hudu da Ahaad da Mama dake zaune parlon, saurin mayar da rigar tayi,"rasa kunya aeda kin k'arasa cire rigan,ni wallahi Hadiza na gaji da halinki yarinya kin koma d'iyar arna,innalillahi,yanzu Sule ka jimun yarinyar nan wai y'ar musulmi kullun yana zarya kan titi da fita k'asashe ,ae duk laifinka ne,hakkinka ne itadin amana ce a wurinka ka Kuma sani,amma kayi burus da hakan"had'e fuska Najma tayi tace"zaki fara ko?,ae nasan me kikeyiwa nifa aure yanzu baya gabana bare kice zan rasa mijin aure,Kuma ae ina da hankali bazanyi abunda zai cutar dani ba,to kisa ido ki kallo"."ka gani ko ka gani da idonka tsab yarinyar nan ta canza"d'agowa tayi da niyar magana karab suka had'a ido da Ahaad had'e maganar tayi ya duka tare da zare shoe dinta ta kwashi kayanta zata wuce,wani kallon tsana Fadila kebinta dashi wanda shigowarta kenan ,kauda Kai Najma tayi yabar parlon gaba d'aya,da murna Nani ta tareta tare da rungumeta tace"sannu da dawowa y'ata,bari na baki ruwa"kafin tayi magana Nani tasa mata Cup a baki ruwan tasha sannan tace "na gode Nani ,ya zaman gidan?"dariya Nani tayi tace a'a komai lafiya lau gaki yanzu kin dawo gidan yamun haske sosai "dariya sukayi duka kafin Nani ta Kuma cewa"kije kiyi wanka ki huta kafin kizo kici abinci"ta k'are maganar tana shafa mata Kai,rike hannun Nani tayi cike da tsantsar Sonta da kularta tace"Nani ina sanki sosai,ke din ta dabance".dariya itama tayi tace"ina sanki y'ata sosai"kayanta ta dauka tayi d'akinta. "Ina fad'a maku idan kuka kuskura aka samu matsala to kunsan sauran,ayi komai yadda ya dace"Islam ta fad'a tana kallon Maza su hud'u dake gabanta."warning na k'arshe ne wannan kuyi duk yadda za'ayi kuyi komai yadda ya dace"Fadila ta fad'a.dariya babban cikinsu yayi cikin murya marar dadin sauti yace "an gama baku da matsala ,bayau na fara irin haka ba,kudai da komai yayi daidai ku biya kudi kawai"rafar kud'i Islam ta mik'a masa tace"inkun gama zan baku sauran"basuce komai ba suka wuce. "Zaman me kikeyi anan wurin?,ya naga baki da k'arfin jiki Kuma?"rike hannun Nani tayi tace"inajin zazzafi da ciwan Kai ne Nani"subhanallah tun yaushe?,Kuma kike zaune da ciwo baki fad'awa kowa ba?"Amaan ya fad'a yana k'arasa shigowa d'akin."ah karka damu ba wani case bane ba"."a'a bazai yiwuba zama da ciwo K'aramin alhaji dole zamu kaita asibiti yanzu"."Nani Zan Kira likita ya dubata a gida kawai"ya fad'a yana zaro waya a aljihu Dr Jamilu ya kira yace yazo gida zai duba Najma,bayan ya kashe wayar yace masu"zanje na dawo kafin ya iso"be jira cewarsuba ya kuma fita yana turawa Dr Jamilu text akan maganar da sukayi kwanaki. Tofa akwai turka turka kudai ku biyo majidadi danjin ya zata Kaya. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi Mana kyakyawan k'arshe Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *MARYAM ISMAIL MAJIDADI* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 36-40 Jinginar da kanta tayi tare da lumshe ido alamun ciwan kan yana matuk'ar damunta,sannu kawai Nani ke jera mata. B'angaren su Amaan kuwa ba dadewa Dr Jamil yazo kai tsaye part din Mummy ya wuce ya shiga bakinsa dauke da sallama,babu kowa a parlon sai Daddy yana karatun jarida idanuwansa sanye da siririn farin glass cikin sakin fuska yace"a'a Dr Jamil yau a gidan namu?,to k'araso ciki kake tsayawa kamar wani bak'o".Shima fuskarsa sake ya k'araso ya zauna gefen Daddy tare da cewa "Alhaji barka da hutawa,na sameku lafiya?"."lafiya qlau Alhmdllh ,waye baya lafiya a gidan Kuma?"kafin ya bada ansa Mummy da fitowarta kenan ta karb'e da fadin"Najma ce ta dawo aeki babu lafiya,shine Amaan ya kirasa ya dubata".kamar Daddy zai tuna wani abu sai kuma ya kasa dan a tsawan lokacin nan mantawa yakeyi da wata Najma balle yasan halin da take ciki kasa fadan komai yayi yaci gaba da duba jaridan sa,alama Mummy tayiwa Dr Jamil daya biyota,suka fice kai tsaye d'akin Amaan suka wuce,tsaye suka samesa Shima yana jiran k'arasowarsu,ajiyar zuciya ya sauke yace"tun d'azu nake lek'en zuwanku ae"baki Mummy ta tab'e tace "ae dole ka jiramu Daddynku ya fara samu a parlo ,na dauka zai iya yin wata magana a Kai amma sai naji shiru"."ae kema kinsan bazai iya magana ba,dan malamin nan Hajiya Sadiya tace aekinsa ba daga baya ba,yanzu dai muyi abunda ya kawo mu,Dr Jamil muna sauraranka".numfasa yayi yace "kamar yadda kuka buk'ata an shirya komai ,sai dai alluran zai dauki tsawon sati d'aya a jikinta kafin ya kasheta lokaci d'aya,in har bata samu lucky na sake rayuwa ba,dan ba kowa ke iya hayewa alluran ba"."what maganan banza mu da ke buk'atar in da hali ta mutu yau,amma zaka kawo wani maganar sati d'aya"Mummy ta fad'a yare da mik'ewa tsaye,"cool down Mummy meye na saurin,ni mun riga mun gama magana dashi,kinsan ni na Kira likita ya dubata me kike tunani idan wani abun ya sameta kuma?kada ki manta Yaa Ahaad yana gida fa,kawai kibar aeki a hannu na zanyi komai dan in k'arbo maki martabarki da dukiyar da kike buk'ata Mummyna wannan alk'awarina ne"Amaan ya fad'a tare da dafa kafad'un Mummy.murmushi ta sakar masa tace"am proud of you son,Allah yayi maka albarka"ta k'are maganar tana shafa kansa dajin wani irin tsananin soyayyar d'an nata a ranta.part dinta ta koma yayin da Dr da Amaan suka wuce part din Najma. Da sand'a ta shiga parlon juye juye ta farayi da sauri ta bud'e firij din d'akin tare da kwashe lemun data tabbatar Najma bata shan ko wanne inba shi ba,ta canza da wani da ta shigo,jin tafiya yasa tayi saurin juyowa tana sakin murmushi,Amaan da Dr Jamil ta gani cikin wayencewa Fadila tace"a'a Yaya sannunku,harkun k'araso?".Amaan be wani damuba da ganin Fadila d'akin yace"eh,na tsaya tahowa da Dr ne zai dubata"bedroom suka wuce ,cikin sauri Fadila ta shigo ta dafa kan Najma tace"Ayyah sannu sister yanzu Mummy ke fad'amun bakiji dad'i ba,ni yau nazo da shirin muyi fad'a sai in iske baki lafiya,dan Allah ki warke da wuri kinji y'ar uwata"murmushi Najma tayi tace"soon kuwa,k'awar fad'a"da yake kowa yasan yadda suke zaune sai ba wanda ya damu da Fadilan,kallon lemun Hannun Fadila Najma tayi tace"pls help me with that".kallon kwalban Fadila tayi tace"owk owk bara na kawo cup saina zuba maki,kafin nan Dr ya gama dubaki"waje tayi da lemun ,sannu Dr Jamil ya mata ta ansa sannan ya tambayeta meke damunta,"kaina sai kuma d'an zazzab'i"."owk sannu Allah ya baki lafiya yanzu zanyi maki allura da magunguna insha Allah zakiji sauki Kuma ki samu ki d'anyi bacci"Kai kawai ta gyad'a masa a galabaice,magunguna ya fiddo ya nunawa Nani yadda zata bata,sannan ya had'a allura kala biyu ya juyo yace masu "excuse us"fita sukayi,ita kuma ta juya ba tare da tace komai ba,har ya gama alluran duka biyu ko motsi bata yi ba,dukda zafin dake ratsata,"to an gama yanzu ki samu Kisha ko tea sai kisha maganin".thank u kawai ta fad'a tare da gyara kwanciya fitowa yayi ya kalli Amaan yace"am done,zamu iya tafiya,Allah ya bata lafiya","ameen mun gode kwarai Dr"Nani ta fad'a,dakin suka shiga ita da Fadila tallafota Fadila tayi ta bata tea din data had'a mata tun kafin ace tayi kad'an tasha tea din sanan tasha drugs din,lemun da Fadila ta kawo ta dauka tasha kad'an sannan ta kwanta alamun tana buk'atar hutawa,"ki kwanta ki huta sosai y'ata zanje d'akin Mama yanzu ta aeko kirana Zan mata amala, ba jimawa zan dawo"Kai kawai ta gyad'a Fadila ma ta mata sai da safe sannan suka fita a tare . A gajiye ya shigo d'akinsa burinsa kawai yasha ruwa me d'an sanyi ko ya huce gajiyar daya dauko ganin firij din yayi empty dafe Kai yayi be tuna komai ba ya fad'a toilet ya sakarwa kansa shower a gaggauce yayi wankan danjin ana niyar tada sallah boxer da jallabiya ya saka tare da fesa turare silifas masu taushi ya saka ya fito yana tafiya kamar bayason taka k'asa Kuma a haka wai sauri yakeyi,ji yayi bazai iya fitaba ba tare da yasha ruwa ba,ganin part din Najma shine mafi kusa dashi yasa ya shiga kawai babu kowa parlon sai TV dake aekinta kai tsaye firij ya nufa ya bud'e babu ruwa sai lemu kawai,kallon lemunan ciki yayi can ya hango irin wanda yafi so yasan duk gidan shi kadai sai Najma keshan bakin lemu dan haka ya dauka ya kafa baki ya shanye tas,ji yayi wani sanyin dad'i na ratsa shi,ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido,Kai tsaye bedroom din Najma ya d'an tura yace"kina ciki kuwa?"lumshe idonta tayi kamar ba zata ansa ba sai Kuma tace"me kake buk'ata?"kallonta yayi k'udundune a bargo yace"are u sick?"Kai kawai ta gyad'a masa,bud'e baki yayi da niyar yin magana sai kuma yayi shiru ya runtse ido da k'arfi danjin wani irin juyawa da maransa yayi ga wani irin yanayi daya tsinci kanshi a ciki,juyowa yayi da niyar barin d'akin da gudu Fadila ta fice wacce take lab'e tun d'azu a hankali tace"yes yes yes,wannan ma wani nasara ne,nasan hakan zaifi ciwo".Ahaad Kam yana janyo k'ofar d'akin ya dafe bango,zubewa yayi a k'asa ya dafe mara yanajin kamar zata tsage biyu dan azaba.Najma Kam wani wahallan barci tayi awan gaba da ita sanadiyar allurar barcin da Dr Jamil ya mata saita rinjayi abunda tasha a lemu.waya Fadila ta dauko ta dannawa yaran data bawa aeki kira bugu d'aya ya dauka cikin isa tace"basai kunzo ba ,wani plan din yayi aeki,amma duk da haka anjima zan turo maku sauran kudin aekinku"bata jira cewarsa ba ta katse wayar,rawar murna ta fara takawa ,sannan da gudu tayi part din Mama danta k'ara daukewa Nani hankali. A yanzu Kam Ahaad ya gama jigatuwa ya fita hayyacinsa kwakwaran motsi baya iyawa ji yakeyi kamar yaci babu bankad'a k'ofar d'akin yayi ya koma harya fara ganin dishi dishi yaye bargo dake rufe a jikin Najma yayi ,itakam ko motsawa batayi ba.fad'awa yayi a kanta ya fara romancing dinta da k'arfi k'arfi baya kojin Kira kafin kace me ya k'arasa rikicewa ya kasa controlling kanshi.bayan wasu mintuna shigowa tayi d'akin tana jujjuyawa wani irin dariya ta kwashe dashi harda tafa hannuwa,hannu tasa da niyar bud'e duvet din da suke ciki sai kawai tace"bankai nan ba,kallon tsiraicinku haramun"wata dariyar ta saka tafi tayi nan wasu maza biyu suka shigo tace "ku daukesa ku Mai dasa part dinsa karkuyi wani kuskure balle ku janyo ya farka in haka ta faru to kusan mutuwarku tazo".Kai suka d'aga mata wani zanin ta janyo ta rufawa Najma sannan ta janye na k'asanta yadda zasu samu damar dauke Ahaad,haka suka daukesa zuwa part dinsa data nuna masu a bed suka ajiyeshi suka ajiye kayansa da suka kwaso sannan suka fice tare da rufe kofar,hannu ta jinjina masu kafin itama tabar wurin gaba d'aya .ranta fari k'al kamar ta zuba ruwa k'asa ta sha. Wani irin zaro ido Nani tayi gabanta ya buga da k'arfi ,ta saki plat din dake hannunta ya tarwatse abunda ke ciki ya zube,shigowarta kenan hannu ta daura akai tana shirin k'wallah ihu,sai tayi saurin toshe bakinta hawaye na gangarowa akan idonta da sauri ta k'araso gareta ganin zanin gadon duk jini ga yadda aka mata faca faca yasa ta tabbatar da abunda take zargi,rasa me zatayi tayi ,ta shiga tsananin firgici da tashin hankali da sauri tayi k'ok'arin janyeta ta gyara wurin ,bata fatan ta farka balle ta gane hakan dukda tasan ba iya boye mata zatayi ba,cikin k'ank'anin lokaci ta gyara wurin sannan ta goggoge mata jikinta ta saka mata wasu kayan duk a sand'a take wannan gudun karta farka ,rufe ta ta kumayi da duvet sannan ta fita tare da janyo d'akin,bakin k'ofar ta sulale sai lokacin kukanta ya samu damar fitowa tana kiran" na shiga ukku ni Fammah,waye yayi wannan aekin?waye zai wulak'antamun marainiyar y'ata,rayuwata bata da amfani tunda na kasa kareki Najma,ki yafe mun Najma ,bansan meye zai biyo baya ba bayan wannan"haka taketa rusa kuka cikin tsananin tashin hankali da firgici. *Tofa wasa farin girki,ana wata ga wata,wata wutar kuma ta sake b'allowa,ku dai ku biyo Majidadin danjin ya zata Kaya,inji ruwan comment kuga ruwan typing,sanso fisabilillah masoyana* Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arshe. Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Telegram Maryam majidadi *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 41-45 A hankali ya soma bud'e idanuwansa da yakejin sun masa nauyi sosai ga gefen kansa dake matuk'ar sara masa,sake lumshe idon yayi lokacin daya d'aga duvet din da yake rufe yaga ba Kaya a jikinsa,zumbur ya mik'e yana kallon d'akin da yake,son tunu abunda ya faru yakeyi amma ya kasa tunda cikinsa ya fara masa ciwo daga nan bazai iya k'ara tuna komai ba,zaro ido yayi da yaga duvet din d'akin Najma a jikinsa ga Kuma kayansa a gefe"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ya Allah kasa ba abunda nake tunani bane"ji yayi ya fara rawar sanyi wani mugun zazzab'i ya rufeshi saurin Kuma lullubewa yayi hankalinsa a matuk'ar tashe,karanto ko wacce addu'a tazo gabansa kawai yakeyi. "Ina fatan ya mata alluran dai?"Mummy ta tambaya."kwarai kuwa komai ya tafi yarda mukeso,yanzu sora muga result kawai"Amaan ya fad'a yana dariyar farin ciki,sannan yaci gaba da cewa "dole Kuma a yanzu mu zama kusa da ita,mu nuna mata soyayya ko dan ta dawo mana da files din data d'iba kafin lokacin wucewarta"shiru Mummy tayi alamun tunani tace"aeba wanda zaiyi wannan aekin sai Mama da Ahaad,duk da y'ar tsamar dake tare da Ahaad da Najma na tabbatar ta yarda da gaskiyarsa,ka barmun wannan aekin a hannuna kawai"haka sukaita tattauna suna neman hanyar bulliwa lamarin nasu. A hankali ta soma bud'e idanuwanta ,ji takeyi barcinma be isheta ba ,yunk'urawa tayi zata tashi da sauri ta koma ta kwanta tare da sakin wata razananniyar k'ara sakamakon wani irin zafi da zugi da taji a k'asan,dafe kai tayi tana neman kurma wani ihun saurin rufe mata baki Nani Fammah tayi tana girgiza mata Kai alamun tayi shiru,kallon tuhuma takeyiwa Nani cikin muryar kuka tace"Nani Nani meya sameni?,waya tab'ani,ki gayamun shin kedin kin dawo kin samu wani a tare dani ne?"shirun da Nani tayi yasa Najma yunk'urawa da k'arfi duk sai taji zafin da takeji ta dainaji ,ji takeyi kamar ana watsa mata wuta a zuciyarta kamar ta bud'e kirjinta ta ciro zuciyar tayar kota samu sukuni,saurin riketa Nani tayi itama ta fashe da kuka tace"ban sani ba nima,bansan waye ba,ki gafarceni ina b'angaren Mama sai na dawo na sameki a haka"zama dab'as Najma tayi a k'asan tiyil wasu irin zafafan hawayen takaici nabin kuncinta a hankali sautin kukan nata ke fita tace"shikenan an gama dani,an daukemun abu mafi daraja a rayuwata,wannan tabbas shiri ne,an wulak'antani wulak'anci mafi muni,da nasan zanga wannan rana dana rok'i mutuwata tun tuni,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un". rungumeta Nani tayi suka soma kuka,cikin muryar kuka Nani ke fadin"ki daina fadan haka y'ata,ba kanki aka fara haka ba,komai zai wuce ki maida hankalinki ki nutsu ki tarbi komai yazo maki ki shirya da ko wanne irin k'alubale a rayuwa,wannan baya nufin fad'uwarki y'ata kedin jarumace kuma jajirtacciya,yanzu nake son ganin jarumtarki,babu wanda yasan hakan ta faru da ke,to zamu b'oye hakan har ki gano wanda ya aekata mana haka,dan Allah karkicemun a'a".wani kukan Najma ta Kuma saki ta rungume Nani ,da k'yar Nani ta lallasheta ta gyara mata jikinta zuwa lokacin Zazzab'i ya gama rufeta,magani ta bata da tea sannan ta lallabata tayi barci,zama tayi tana shafa tulun sumar gashin kanta tana matuk'ar jin tausayin yarinyar a ranta. Turo d'akin Mama tayi tace"haba Fammah yanzu kika baro d'akina Kuma baki gayamun Najma ba lafiya ba,yanzu kin kyauta kenan jikar tawa".kirkiro murmushi Fammah tayi tace"kiyi hakuri Hajiya naga dare yayi ne,bana so ki tashi hankalin ki shiyasa ban fad'a maki ba,Kuma naga taji sauki yanzu haka tana barci ma"."uhm ni dai bazance komai ba,banda zaman amana da ba yafe maki zanyi ba,wannan ae zamba cikin aminci ne,banda Allah yasa Bilkisu tayi hankali aeda ba sanin zanyi ba,Najma kadai nake kallo naji dadi itadin jinin Jafar ce,da wani abu ya sameta sai kun biyani jikata wallahi Allah ko kuma hukuma ta rabani da ke da kika b'oyemun"Mama ta k'are maganar tana k'arasa tana kallon fuskar Najma da ke barci,kallo d'aya zaka mata ka gane barcin na dole ne,Kuma bajin dadinshi takeyi ba."Allah ya baki lafiya kinji jikata,Kuma data farka ki kawota bangarena saita warke zata dawo wurinki",da to Nani ta ansa dan ta saba da rigimar Mama ko damuwa batayi ma,bayau suka saba irin wannan ba.fita Mama tayi tana sababi. Najma Kam ba ita ta farka ba sai Kiran farko na asuba,k'ara bud'e ido tayi ganin Nani rike da hannunta tana barci akan plastic chair ta daura kanta gefen bed din ,a haka ta kwana,hawayene suka zubowa Najma ta daura d'ayan hannunta akan na Nani a hankali tace"insha Allah nazan safaukarba Nani ,zanyi domin ke kuma zanyi domin neman wa iyayena da y'ar uwata adalci,na koyi abubuwa da dama a wurinki Kuma bazan taba bari hakan ya tafi ba,ina sanki Nani",zare hannunta tayi ba laifi yanzu tana d'an iya tafiya wanka tayi ta gasa jikinta sosai sanna ta dauro alwala ta fito bayan ta gama sallah ta shirya ta dauko al-qur'ani ta fara karatu k'asa k'asa. 10:00am Fadila ta shigo d'akin da shigarta na fita bakinta dauke da sallama ,mamaki ne ya kamata k'arara ganin Najma zaune tana aeki a laptop ,b'oye mamakin tayi tace"Kai Alhmdllh sis kinji sauki sosai ma,har an fara aeki?,gaskiya kina da kokari sosai".d'agowa Najma tayi fuskarta dauke da k'ayataccen murmushi me kashe zuciyar mak'iyi tace"kwarai kuwa sis,ae Zazzab'in ba wani bane dama,Alhmdllh ina jina ras,kasalane kawai zai hanani zuwa Office yau"a fakaice Fadila ta banka mata harara tace"ae haka akeso,Allah ya kara lafiya,dama zan fita ne nace bara na dubaki"."Allah ya tsare,nikan na warke sosai"da Ameen Fadila ta ansa ta fita zuciyarta cike da tunanuka iri iri,ba haka taso ba,taso kowa ya gane anyiwa Najma fyad'e har Mama ta koreta daga gidan,amma sai taga sab'anin hakan,lallai akwai sauran aeki a gabanta. Haka Mama tazo duba Najma da jiki Amaan ma hakan,yadda suka sake mata ne yake bata mamaki,amma saita wayance ta shige cikinsu dason gano wani abu amma tabbas tasan suna da wani Shirin a kanta."keni tashi ga kunu nayo maki Kisha ko kinji dadin jikinki"Mama ta fad'a tana zama kusa da Najma.maganar Mama ce ta katse mata tunani ta mik'e a hankali tace"Hajiya Kakata barka da safiya".tsuke baki Mama tayi tace"bazan ansa ba,ae kullun saikin dawo daga gantallen aekinki kike zuwa ki gaisheni to bana so yanzu kuma"y'ar dariya Najma tayi tace"kajimun Mama ina lokacin da nake fita baki tashi ba,so kike inzo tashinki ki hauni da fad'a har misa nayi latti ko?"."ke dai kika sani tashi kisha"karb'ar cup din Najma tayi kunun gyad'a ne da yaji madara sai fatan dankalin hausa da yasha kayan kamshi da y'an ciki,girki yayi Dadi sosai Najma taci abincin tace"ah y'ar tsohuwa ashe har yanzu hannu na nan zam zam dai"."kwarai kuwa dan idan nayi girki baki iya irinsa ku dama ba abunda Kuka iya sai rikon biro da farar paper ayi aure aje aeta fad'a da miji,yaran gidan nan yanzu aeya kamata kowa yasan inda ya nufa na gaji da ganinku haka"turo baki Najma tayi tace"be zaki fara ko,ae sai kiyiwa sauran auren nikam ba yanzu ba dama Kuma nice auta a gidan"dariya kaka tayi tace"autar da ta riga kowa yin aure ko?"zaro ido Najma tayi tace"Mama ban gane ba"shiru tayi mata ta tattara kayanta tayi gaba tana tuno abubuwa da yawa a baya.itama Najma sharewa tayi dan tsab tasan halin Mama da tsokana ga tsufa Kuma. 4days later Eh yanzu Najma ta warke ras,har ciwon da takeji a k'asanta ta daina ji,ta koma office saidai wani lokacin ta rik'ajin jikinta kamar ba nata ba,kamar wani ciwan nasan kamata ne.a kasalance ta fito daga office sanye take da suit kamar kullun amma yau blue colour ta nannade gashin kanta,dogayen takalma e a k'afarta tana tafiya tana nishi idanuwanta har rufewa suke kokarin yi,"lafiya kuwa?,meke damunki?"Aiban ya fad'a wanda shigowarsa wurinta kenan.juya idanuwanta tayi ba tare da tace komai ba,ta mik'a masa key din motarta,karb'a yayi yasa cikin masu aekin wurin suka taimaka mata zuwa mota,shi yaja motar zuwa gida,wani irin fad'uwar gaba ta samu Ahaad lokacin da yaga Aiban rike da hannun Najma yana k'ok'arin fitowa da ita a mota,matse glass cup din hannunsa yayi ya fashe har ya yanke masa tafin hannu,tsura masu ido yayi yanajin kamar ya tashi ya shak'e Aiban,mik'ewa Muslim yayi yace"brother lafiya?,me yake samunta ne"zaro ido Aiban yayi yace"Muslim yaushe ka shigo gari ne?,ko Hajiya bata sani ba bare ni"dariya Muslim yayi yace"ba jimawa na shigo zamuyi wani aekine da Captain,bata da lafiya ne".kallonsa Najma tayi tace"lafiya ta qlau kawai inajin jiri ne,Kuma yanzu kamai yayi daidaima"dariya Muslim yayi yace"bata ko dai kina tsoron allura ne?"murmushi kawai tayi ta juyo tace"na gode friend Allah yabar tare zaka iya tafiya"da Ameen ya ansa sannan suka k'arasa wurin Ahaad ,hannu Aiban ya bashi ,hannu Shima ya mik'a masa sukayi musabaha Aiban yace"barka dai Captain Ashe Kaine abokin Brother din nawa"Gyad'a Kai kawai Ahaad yayi .kallonsa Muslim yayi yace"wannan shine Aiban yaron Yayar Ummana da nake gaya maka muna da y'an uwa a nan garin"murmushi Ahaad ya k'ak'aro yace"nice to meet u bro"."zanje gida yanzu anjima zamu had'u"Muslim ya fada yana bin bayan Aiban ,a motar Muslim suka tafi dan Aiban yabar tasa a company. "Wallahi Mama Kinga yanzu Najma ba lafiya ya isheta ba,ya kamata ta bawa y'an uwanta wata dama su taimaka mata akan wannan company din ,balle ga Ahaad yazo gida Kuma zai jima dan wani aeki yazoyi"Mummy ta fad'a."Nima nayi tunanin hakan tunda yanzu jikin sai a hankali Kuma ta kafe taki bari likita ya dubata,zan mata magana idan ta warke inma so takeyi saita koma wani kawai "wani sanyin dad'i ya ziyarci Mummy.shigowar Najma d'akin yasa ta hadiye sauran maganarta,zama tayi a chair bata tankawa kowa ba taumshe ido hannunta rike a kanta. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arshe Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Telegram Maryam majidadi *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 46-50 "Wai ke me yake damunki ne?,tarbiyar da aka baki kenan?,yaushe kike k'ok'arin ki zama haka?"Ahaad yayi tambayar a hassale."yau naga abunda ya isheni Sule meyake faruwane ka shigo kana wani bubbudemun hanci kana jaraba Kai da ubanwa Kuma?"Mama ta fad'a tana mik'ewa tsaye,wata uwar harara ya banka mata yace"ae wacce nake da ita ta San kanta"sai lokacin Najma ta bud'e lumsassun idanuwanta ta budesu a kanshi ta tsura masa ido"ki janye mun wannan idon naki kwalakwala Mai kama dana mayu".murmushi Najma tayi sannan tace"wani abun ya faru ne?",da k'arfi ya fizgota daga zaunen da take ya murd'e mata hannu zuwa baya cikin haushi yace"wannan ya zama last warning da zan ganki wani yayi k'ok'arin tab'a jikinki,idan Kuma hakan ta sake faruwa to kinsan me zan iyayi ae",a galabaice take danba k'aramin riko yayi mata ba, numfashi taja itama cikin muryar rad'a tace"toka saurara kaji,ni ba budurwarka bace so baka da damar yin kishi a kain..."jin ya Kuma murd'a hannun yasa ta saki y'ar k'ara tare da hadiye sauran maganarta,bankad'ata yayi ta fad'a a k'asa,"la'ilahaillah Bilki kin haifo annoba a gidannan,kina zaune yana k'ok'arin kashe y'ar uwarsa amma kin kasa katab'us,Allah ya isanta mugu,Allah ya saka mata,mugu labcecen banza bayahude"k'wafa yayi yabar d'akin rainshi a matuk'ar jagule,sai lokacin Mummy ta kamata ta tayata ta zauna tace"sannu Najma kinsan halin Yayan naku ku rik'a kiyayewa muma ba d'aga mana yayi ba,sannu bara na baki ruwa"gyad'awa Mummy Kai kawai tayi karb'ar Mug din ruwan tayi tasha ta mik'e zata fita,da sauri Mama tace"ina zakije inaso muyi magana dake",wayar hannunta ta duba tace"zamuyi magana anjima yanzu anmun Kiran gaggawa"bata jira cewar Mama ba ta d'aga wayar ta fita,gama sauraran sakatariyar tata tayi sanan tace"owk I will be on my way back"part dinsu ta shiga ,cikin sauri ta shirya cikin dogon riga mai rover kalarta ja bakin dogon takalmi ta saka ,tubke kashin kanta tayi sannan ta dauki siririn bakin gyale ta daure kanta,hand bag ta dauka da key din mota,sosai tayi kyau sai azabar kamshi takeyi rumgumar Nani tayi ,kiss ta mata a kumatu tace"Nani ina dawowa yanzu"da Fadila ta had'u tana k'ok'arin fita daga gate din gidan,cikin takun Isa ta k'araso gareta tace"Najma fita zakiyi ne?",ba tare data kalleta ba ta d'aga mata Kai,"to ki ajiyeni gidansu Islam motana tana wurin wanki kuma har yanzu wannan d'an rainin hankalin Idi bai dawo da ita ba",da sauri Najma ta d'ago ta kalleta tace"Baba idi dinne kike fad'awa haka?".tsuka Fadila taja tace"aekin banza to shidin ubanki ne?,ko Kuma kalar dangin naki har takai gareshi,ni wallahi shiyasa ba ko wacce magana nakeso nayi a gabanki ba"ko kulata Najma batayi ba ta shige mota,ganin bata da niyar shigowa yasa ta fara k'ok'arin tayar da motar da sauri ta zaga ta bud'e motar,murmushi kawai Najma tayi taja motar.Ahaad Kam kallonsu kawai yakeyi ta window ya rasa meke masa dadi,yanzu baya da makama ya zai b'ullowa Najma d wannan rayuwar data dauka bazai yiwu ya zuba mata ido ba tayi shigar da take so ba ta Kuma fita lokacin da take so ba,duk da bawai zarginta yakeyi ba,sai dai yana ganin hakan Sam be kamata ba,balle yadda take yarinya mai k'ananun shekaru irin haka,dole yasan abunyi kafin lokacin komawarsa.kai tsaye k'ofar gidansu Islam tayi parking ,kallonta Fadila tayi tace"Najma ya kamata ki shiga kinsan yau Islam ta had'a paty ne na dawowar y'ar uwarta k'asarnan da Kuma k'anwar mamanta"Najma kallon tsadaddiyar agogon hannunta tayi tace"Fadi ina da meeting ,Kuma lokaci na neman k'ure mani","aeba saikin zauna ba pls ,dan Allah"bud'e motar kawai Najma tayi ta fito Dan babu amfanin musun wani lokacinne zata kuma cinyewa,murmushin mugunta Fadila tayi tace"naga da k'afar da zakije meeting din,keda dogon takalmin naki k'asa zaku tsinci kanku,shegiya kawai".a tare suka shiga gidan kamar abun arziki, decorations ta gani ta ko ina,gidan yayi kyau sosai ciki suka k'arasa can bayan lambun gidan aka shirya dan gabatar da patyn,tunda ta shigo wurin mazan wurin da matan wurin suke kallonta kowa da abunda yake ayyana a ransa,ji tayi dukta tsargu ta rasa sukuni dan ita ba ma'abociyar zuwa irin wad'annan wuraren bane,bata son yawan hayaniya yanzu kam,Jan hannunta Fadila tayi zuwa inda taga Islam,tab'ota tayi cikin jin dadi Islam ta juyo tare da rungumar Fadila tace"gaskiya nayi fushi daga bari naje na dawo shine sai yanzu kike dawowa,Kuma abun harda gayyar sodi?"dariya suka saka tare da tafawa sannan Fadila tace"gaskiya ba haka ya kamata ta samu tarba ba,itace ta kawoni motata na wurin wanki"far da ido Islam tayi sannan ta mikawa Najma hannu alamun su gaisa,basarwa Najma tayi ta bata hannu itama,kallonsu tayi tace"na tayaki murnar dawowar y'ar uwarki sai dai ina rok'on Allah yasa hali ba d'aya ba,magiya da taimako ya kawoni nan dan taron naga baikai armashin ace kamata Billionaire nazo wurin ba,fatan alkhairi"sakin hannun Islam tayi ta juya zata tafi,"kan uban can,wannan ae gaba d'ayanmu ta had'a ta wulak'ance,lallai wallahi zanyi maganinki"Islam ta fad'a a fusace bin bayan Najma tayi da sauri Fadila ta rikota tace "come down ,zakiga mezai faru yanzu"bata k'arasa magana ba sukaga santsi ya ibeta ta tafi zata sulale runtse idonta tayi da k'arfi ta sadakas ta jita a k'asa,dama gashi ba k'arfin jiki takeji ba dauriyace kawai,ji tayi ta fad'a akan jikin mutun ya rungumota da k'arfi zuwa faffad'an kirjinshi,hakan yayi daidai da sakin sanyayyar wak'ar soyayyah mai dadin gaske ,a hankali ta soma bud'e idonta ta saukesu akan kyakyawar fuskarshi sanye yake cikin T-SHIRT red colour wai wando jeans bak'i,gashin kan nan yasha gyara sai salki yakeyi ga wani shu'umin k'amshin turaren da takeyi,gira d'aya ya d'aga mata tare da kanne ido yace"kallon fa y'an mata?"lumshe idonta tayi ta sake waresu a kanshi tace"Yaa Ahaad mezan kallah a nan?"ta k'are maganar tana turo d'an k'aramin bakinta,hannu yasa ya murd'e baki saida ta saki k'ara sannan ya saki yace"kinamun rashin kunya saina cire bakin,Kuma na sakeki ki fad'i a nan".mik'ewa yayi tare da sakinta,dafe Kai Fadila tayi tace"wallahi Yaa Ahaad be tab'a b'atamun rai irin yau ba,wai wama ya gayyato shi"."ae kinfi kowa sani,Yaa Muslim fa Shima yazo ba dole ki gansa ba"Islam ta k'are maganar tana Jan siririn tsaki,"amma wallahi ya bada mu"Fadila ta fad'a cikin haushi.ido suka had'a da Aiban murmushi kawai yayi mata ya juya zai bar wurin,yunkurin binsa tayi Ahaad ya rike hannunta ya matse sosai yace"karki kuskura,inba so kikeyi na b'allaki a wajen nan ba"sahagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka,cikin shiga ta alfarma ta k'araso wurin duk abunda akeyi akan idonta ,kallon tuhuma takebin Ahaad dashi ,idanuwansu na haduwa gaban Shuhada yayi mugun fad'uwa,kallonta takeyi tana son tasan ina ta taba ganin me kama da ita amma ta kasa tunowa,cikin sanyayyar murya tace"Yaa Ahaad wacece wannan?"sai lokacin yasan da isowar Shuhada a wurin,yi yayi kamar ya share sai Kuma yaga rashin dacewar hakan yace"Najma"sake fuska Shuhada tayi tace"wow kace lil sis dinmu,sai yau Allah yayi zanga Najma ,ina samun labarinki a wurin Yaa Ahaad"harara ya watsa mata ,da sauri Shuhada tayi shiru tare da sunkuyar da Kai,balle sai da tasha matuk'ar wahala kafin ya yarda yazo wurin,wayen cewa Najma tayi tace"sannu Auntyn mu,ashe ina da rabon ganinki a yau"ta k'arashe maganar tana k'unshe dariyar dake cinta tana kallon yadda Ahaad ya had'e fuska.riko hannnunta Shuhada tayi tace"nayi farin ciki da ganinki ,ina fatan kema patyn yazomun da ke?",k'ara sakewa Najma tayi saboda lokaci d'aya taji tana matuk'ar son Shuhada tace"a'a Auntyna hanyace ta biyo dani,ina da meeting,amma insha Allah zan maki zuwan kanki,sai dai ko sunan Auntyn ban sani ba"murmushi Shuhada tayi tace"haba yanzu aeke k'awata ce,tunda Kinga zamuyi sa'annin juna kinga mun zama k'awaye kenan sunana Shuhada"."wow nice name,amma zan wuce yanzu kada inyi latti"har Najma ta juya zata wuce Shuhada ta riketa ,wani irin bugawa gabansu yayi su duka biyun suka d'ago a tare,basarwa Shuhada tayi tace"kimun alk'awari zaki dawo",gyad'a kai Najma tayi tare da murmushi,matsawa tayi kusa da Ahaad a hankali tace"ba laifi akwai kyau sosai,sai dai k'aramar yarinyace kamarmu,Kai da baka son kowa sai babbar mace?",dungure mata Kai yayi ta wuce tana dariya abunta. Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe. Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Telegram Maryam majidadi *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* *Godiya gareku masoyana marar adadi,hakika kuna sakani farin ciki marar misaltuwa,ku d'in na dabanne son so fisabilillah,ina jin dad'in comments dinku,haka zalika masu Kira ma na gode* *Wannan page din sadaukarwa ne ga* Shugabata *Aunty Fauza y'ar amana* *Yayata Momyn Ahlan* *Sai sister Ummu Nasmah* Page 51-55 Kai tsaye Najma motarta ta shiga,wasu hawayene suka zubo mata,duk'ar da kanta tayi tana jin sautin bugun zuciyarta na tsananta,tabbas tasan tana cikin garari da mugun tashin hankali,wai yau itace ba a matsayin cikakkiyar budurwa ba,abun takaici shine bata ma san waye ya k'arb'i budurcin nata ba,"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,nasan na gama rayuwa me dad'i waye zai aureni haka a wulak'ance?,waye zai yarda dani?lallai dole na daina shagala nayi abunda ya kamata,tunda nake ban tab'a ganin y'an uwa irin nawa ba"ta k'are maganar cikij muryar kuka,tada motar tayi tabar wurin Kai tsaye inda zasuyi meeting taje,shiga tayi tare da basu hak'uri akan makaran da tayi,Mai gabatarwa gabatar sannan aka fara taron ,cikin manyan jami'anta d'aya ya mik'e yace"ranki ya dad'e babban abunda ya taramu shine mun mik'o kokenmu akan ayyukan da kika sabayi na alkhairi,duk sabbin islamiyyun da masalatan da kikace a gina y'allab'ai Amaan ya hana k'arass ginin ya rufe duk wani account da muke cirar kud'i dan gabatar da aekin,Kuma be bamu wata sahihiyar hujja akai ba"jinjina kai tayi cike da tunanuka iri iri sannan ta mik'e tsaye tazo tsakiyar wurin tayiwa kowa sallama da fatan alkhairi sannan tace"naji k'orafinku,ina so ku sani babu abunda za'a fasa,inaso gobe ayyukan suci gaba ,sannan ga kud'in gidajen marayu da kudin sauran magunguna na NNJ special Hospital,da kudin da ake rabawa nakasasassu"kallonta ta mayar ga ma'ajin dake kula da wannan harkokin tace "zan tura maka kudi yanzu"wayarta ta dauka ta tura masa million 20 ,sannan taci gaba da cewa"ku fara da wannan in ana buk'atar k'ari k'ofa a bud'e take".haka sukaita saka mata albarka taron ya tashi cikin kwanciyar hankali kowa fuskarsa da fara'a, a hankali take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ji takeyi tamkar ana yankar naman jikinta wani irin zafi da ciwo yake mata,dafe Kai tayi tanajin zufa na keto mata a wahalce tace"ya Allah,nikam na rasa wannan wanne irin ciwo ne"Driving ta fara ba shiri ta tsaida motar ta fito da sauri dan bazata iya tukinba Kuma ga wani fitinanniyan ciwon da takeji,ganin mutane sunata kallonta yasa dukta fara tsarguwa da kanta daga nesa taji wasu suna cewa"kuji waccen ba itace y'ar gidan marigayi Alhaji Jafar mai K'wal ba,ae babu Wanda nesan Family dinba,amma kuma ae ta mutu tare da iyayenta"."ke Hanna me kike fad'a haka,ancefa y'an biyu ne,wannan ae batayi kama da wacce ta mutu ba,wallahi dukiya rahma ce"Jamila ta fad'a.girgiza Kai Najma tayi ta saki murmushi Mai k'una tace"dukiya babban tashin hankali ne,inama ni Allah ya bari kamarku da nayi rayuwar farin ciki dajin Dadi"ji tayi tana buk'atar ruwa,duka motarta ta duba babu ruwa,Kuma babu shago a ciki,k'arasa tayi wurinsu Hanna tayi masu sallama.washe baki sukayi tare da ansa sallamar ,cikin cool voice tace"Dan Allah ko zaku sayarmun da ruwa nasha?"haba Aunty ae ba'a sayar da ruwan nan,zamu baki kisha dai"."la la,jama'a kuzo kuga y'ar indiya ko ince y'ar indiya,irin wad'an nan da muke gani a film,wallahi itace cikin Wanda muka kalla a TV jiya"k'aramar yarinya y'ar shekara 7 ke fad'a"dariya ta kama Najma ,sosai takeyin dariyar nan ma suka k'ara shagala da kallonta sosai dariyan yayi mats kyau,k'arb'ar ruwan da Jamila ke bata tayi ,Bismillah tayi tare da kai ruwan baki,yana hawa kan harshenta ta maidoshi da sauri,tambayarta suka shigayi amma batace komai,duk yarda taso tasha ruwan kasawa tayi ,wani irin tausayinsu ya kamata tayi alk'awarin taimaka masu ,kafin tabar wurin ta saba da mutane sosai dukda dauriya kawai takeyi saboda tsabar ciwan dake cinta.a haka ta tuk'a motarta zuwa gida,ko da ta shiga bata kula kowa ba,da gudu Fadila ta fad'o jikinta tare da sakin kuka,tace"sister na rok'eki da girman Allah ki taimaka mun,wallahi in gaskiya ta fito Yaa Ahaad zai kashe ni"cikin rashin fahimta Najma ta bita da kallo sannan tace"ki natsu mana ,me yake damunki?,ni ban gane komai bafa".ganin duk Fadila ta rikice yasa ta kama hannunta d'akin Fadilan suka shiga tare da zama gefen bed,wani banzan kallo Islam ta bita dashi wacce ke kwance daga ita sai y'ar k'aramar riga mai hannun vest tana taunar gum,tsaki Islam taja tace"haba Fadila wannan wanne irin iskanci ne zaki sakamu gaba kina rusa ihu daga dawowarmu,kefa kika janyoni Kuma kinsan a buk'ace nake in baki bani abunda nakeso toni zan tashi na nemi wata bazan iya ba"wani irin zaro ido Najma tayi tana k'ok'arin tattaro kalaman Islam ta had'asu akan ma'aunin fahimta girgiza Kai tayi bata San yarda da abunda zuciyarta ke fad'a mata,maganar Fadila ta dawo da ita daga tunanin da ta jefa kanta da taji tana cewa"haba Islam ki tausayamun mana,kefa kinsan komai,kinsan Kuma in hakan ya fito dukanmu mun gama yawo wallahi","a'a kedai kin gama yawo Kam,kinsan ba zaki iyaba kika fara?,kiyi da ita nikan ta fita ta bamu wuri,ko Kuma ni nayi a gabanta dan har ita na soma k'wad'ayinta kam"wani banzan kallo Najma takebin Islam dashi da kuma tsantsar tsana da k'yamar halinsu indai abunda take tunani ne,"sister dan Allah ke kad'ai zaki iyamun wannan taimakon ,kullun inata Zazzab'in dare shine Mummy ta gayawa Yaa Ahaad tace masa Kuma naki zuwa Hospital ,shine ya Kira Dr yace ya dubani,Kinga abunda ya bani yana son yimun awan masu ciki,Kuma ni ina zargin ina dashi "ture Fadila Najma tayi daga jikinta tace"meye kike son fad'a mani?,garin yaya kika bari hakan ta faru,Fadila kinsan girman zunubin da kika aekata kuwa?,wanne mugun ne kika zauna ya rabaki da abu mafi daraja a rayuwarki?"lumshe ido Fadila tayi yace"yanzu ba wannan lokacin bane,ki duba girman Allah ki taimaki y'ar uwarki daga baya mayi magana akan wannan".rok'on Najma tai tayi sannan ta k'arb'a roban taje tayi fitsari ta kawowa Fadila suka fita tare,ita ta wuce part din Mama ita Kuma ta wuce part din Ahaad,kamar wacce ruwa yaci haka Fadila ta shiga tare da mik'a roban,wani mugun kallo Ahaad yayi mata yace"now get out, idiot gal kawai"da gudu tayo waje tana jin zuciyarta kamar zatayi tsalle ta fito. Da wani irin mamaki Najma ke kallon Mama saidai ta kasa furta koda kalma d'aya,"kinajin mena fad'a maki ko Hadiza?,kinyi shiru baki ko kallona kefa macace,mace mai rauni ce bazaki tab'ayin abinda Namiji zaiyi ba".wani k'ululun bakin ciki ya tsayawa Najma a rai murmushi tayi tace"ba komai Mama za'ayi hakan indai hakan zai zama farin cikinki",mik'ewa tayi zata fita taci karo da Daddy kallonsa ta tsayayi saboda ba zata iya tuna rabon data ganshi ba,duk'awa tayi tace"Daddy barka da wuni".gy'ada kansa yayi yace" yauwa barka sannu"ya karkata ta gefenta ya wuce ciki wurin Mama,wasu hawayen ne masu d'umin gaske suka samu damar gangarowa daga idonta,lumshe zara zaran girar idonta tayi Wanda saika rantse da Allah sakasu tayi ,sannan ta ware ta goge idonta tayi cikin part dinsu abunta."Dr ina son result nan da anjima pls do ur best bana so ya dauki lokaci"Ahaad ya fad'a .gyad'a Kai Dr yayi yace"insha Allah kafin lokacinma zan kawo ranka ya d'ad'e"sannan sukayi sallama ya fita. Bayan awa d'aya Cikin wani irin firgici Ahaad yake kallon saka makon yace"wannan bamai yiwuwa bane,ka koyi aekinka da kyau?,yarinyar nan bata da aure fa,a iya sani na ba Kuma yawo taneyi ba"."wannan aekin ni nayishi da kaina,Kuma abunda ya bada kenan kaje ka binciketa zata fad'a maka gaskiya".harda d'an gudu gudu ya had'a zuwa main parlo na gidan,ganin bazai iya k'ara wani takun ba yasa ya tsaya cikin d'aga murya yace"Fadila ,Fadila"wani irin fad'uwa gaban Fadila yayi ta daura hannu a Kai tace"na shiga ukku ni Fadila yanzu Kuma me nayi?".tsaki Islam taja ta tashi ta dauki after dress ta daura akan k'aramar rigarta tace"muje muga meye ".a tare suka fito nan suka iske Mama,Mummy ,Daddy da Amaan kowa yayi tsaye kamar ruwa yaci shi.wani wawan maruka ya zubawa Fadila Wanda ya haddasa mata daukewar wuta na tsawan mintuna kafin razananniyar tsawarshi ta dawo da ita cikin hayyacinsa yace"Dan uwarki waye yayi maki ciki?"tambayarsa ta girgiza kowa a wurin a matuk'ar mamaki Mummy tace"Ahaad bansan iskanci ya zaks rik'a had'a y'ata da wannan alkaba'in?"."to ko result zai mata karyane"ya fad'a tare da bawa Mummy takardar.kuka Fadila ta saka,wani kukan kura yayi ya damk'ota yahau jibga kamar zai cire mata rai,kanta ne ya bugu da table ta saki wani muguwan k'ara,da gudu Najma da Nani suka fito.ganin yana k'ok'arin takata yasa Najma saurin duk'awa gabansa ta rike k'afar tace"Yaya dan Allah kayi hakuri karka kasheta",lumshe idonsa yayi sannan ya bud'e da sauri Najma ta sakeshi tayi baya saboda yadda ta razana da ganin kwayar idonshi yau Sulaiman Ahaad dinshi yake sak,cikin kakkausar murya yace"koki fad'amun waye ko Kuma yau banga me rabani dake ba wallahi,y'ar iska kawai"ganin da gaske Ahaad hallakata zaiyi cikin kuka tace"wallahi Yaya ba result dina bane,na Najma ne,itace tayi fitsarin bani ba"zaro ido yayi ya maido kallonsa ga Najma yace"da gaske take?,I mean kece akayiwa awo da sunanta"shiru Najma tayi ta kasa fahimtar komai,cikin tsawa wacce ta haddasa mata juyawar ciki yace"answer me".bata iya magana ba Kai kawai take gyad'awa alamar eh,wani irin sanyi jikinsa yayi kan chair ya fad'a tare da dafe kansa dake barazanar tarwatsewa,"cikin shege a jikinki Najma"Mummy ta fad'a da k'arfi.a matuk'ar firgice Najma ta d'aga tana bin Mummy da kallon tambaya juyowar da zatayi sukayi ido biyu da Aiban,ji tayi ta k'ara shiga firgici da k'yar ta harhad'o kalmar"ciki...ku..ma,Mummy ni" Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arshe. For comments ko shawara 07033636337 Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Telegram Maryam majidadi *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 56-60 "To ko baki yarda da me takardan ya k'unsa bane?,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,haba Najma ina ganinki me hankali ashe abun kunyar da zaki ibo mana kenan,kaf zuri'armu babu mai cikin shege sai ke"Mommy ta k'are maganar tana sharar hawayen k'arya.d'ago Najma tayi cikin rud'ewa tace"haba Mummy ya zaki rik'a had'ani da irin wannan ?,ni banyi zina ba,ni banyi komai "ta fad'a da k'arfi.cikin zafin zuciya Ahaad ya taso yayo kanta wata irin shak'a yayi mata tare da zuba mata kyawawan maruka har guda biyu,jibgarta ya shigayi ta ko ina bayaji baya gani,Najma kam banda ihu babu abunda takeyi,da gudu Nani ta iso gareshi ta rike masa hannuwa duk biyu tace"ka barta haka,y'allabai kayi hakuri komai ya faru bada saninta b....."had'iye sauran maganarta tayi lokacin daya ingijeta ta fad'a k'asa.cikin wani irin zafin zuciya Najma da maganarta ke fita da k'yar tace"karka Kuma wannan kuskuren a rayuwarka,zan iyayin komai akan Nani na,ita ta zame min uwa madadin mahaifiyata duk abunda uwa kewa yaranta ita keyimun,shin tsawon lokutan nan kasan ta yarda na rayu?,ni ako yaushe ina girmama mahaifiyarka,babu dadi ka wulak'anta wacce take matsayin uwa a gareni tayimun abunda dukanku jinina kuka kasa yimun"k'ara sha'areta yayi da k'arfi,wani ihu Mama ta saka tace"na shiga ukku abun naka bana hankali bane,labcecen banza,wallahi ka bigi Bilki gata nan tsaye a gabanka munafiki,komai ya faru ae laifinka ne,yarinya ta kai minzalin aure aeya kamata ka kula da ita amma saboda bak'in hali irin naka kaki saurarena wallahi ka sakarmun jika kafin hukuma ta shiga tsakanina da kai da wannan uwar taka me lak'awa jikata cikin shege"ganin ko sauraren Mama bayayi yasa Aiban shigowa da sauri shida Shuhada ,cikin zafin rai Aiban yace"haba Ahaad kayi hauka ne?,tashin hankali baya warware tashin hankali,in rai ya b'aci hankali yabar gushewa,tana da juna biyu saika janyo wata matsalar kuma?,ka saketa yanzu",dafa Ahaad Shuhada tayi tace"Dan girman ubangijinmu Allah kayi hak'uri ka sassautawa zuciyarka ka saki Najma,karka kasheta "kuka ta fashe dashi,wani irin muguwan harara ya wurga mata da rinannun idanuwansa Wanda yasa Shuhada matsawa baya da sauri tana silalewa k'asa,Ahaad kam sakin Najma yayi ya dafe kanshi yanajin zuciyarsa na barazanar tarwatsewa a kausashiyar murya yace tare da nunata da yatsa"kin bani mamaki,ashe dama zaki iya aekata mumunan abu irin haka?,b'allagaza dabba,ko a cikin dabbobi babbancin naki dabanne,sai ki gaya mana karuwanci kike fitayi ba aeki ba,dama can wannan aekin ba kwanta mun yayi a raiba,ke abun kyamace Najma ke fasik'ace,mazinaciya mazinaciya,da igiyar aurenki amma kije ki aekata zina?,na tsaneki na tsaneki,na tsaneki bana kosan sake ganin wannan k'azamar fuskar taki a rayuwata,bazan tab'a yafe maki abunda kika aekata mun ba"ya k'are maganar hawaye na fitowa daga idanuwansa,numfashin kowa tsayawa yayi bama na Najma ba, a matuk'ar firgice Mummy tazo ta dafashi tace"son me naji kana fad'a Najma tana da aure?"cikin k'unar zuciya yace"kwarai kuwa Mummy Najma tana da igiyoyin aurena a kanta,kuma aure na yarda addinin musulunci ya tanada,na biya sadakinta da abu mafi daraja kafin aka daura aurena da ita tun tana y'ar shekara d'aya"fad'awa yayi jikin Mummy ya rungumota sosai yace"Mummy ta cuceni ta yaudareni,matata ta Sunnah da aekata zina,na tsaneta dan Allah kice ta tafi tabar nan wurin",juya ido kawai Najma takeyi gaba d'aya ta rasa meke mata dad'i ta kasa gane duniya take ko lahira yau itace a matsayin matar Ahaad na tsawon shekaru ba tare data sani ba,wata uwar k'ara ta saki ta sulale k'asa sumammiya,kuka Mama ta saki gab'a d'aya wurin ya k'arasa rud'ewa Daddy kam ya kasa aewatar da komai illah zama da yayi tare dayin k'asa da kanshi.babu zama dirshen Shuhada tayi tabbas sai yau tasan kuka rahama ne,wai yau Ahaad ne da aure?,Wanda duk duniya babu Wanda takeso sama dashi,zata iya hak'ura da kamai amma banda zama da kishiya ,sai dai Kuma yarda yakejin son Ahaad a ranta batajin zata iya hak'ura tabar ma wata shi.Aiban kam da sauri yayi kan Najma yana girgizata tare da kiran sunanta,wata uwar tsawa Ahaad ya daka mashi yace"ka saketa ,dama ae Kaine kwaraton nata ba kowa ba,babu Wanda take kulawa a sanina sai kai,ina so in fad'a maka inhar kana da saka hannu akan wannan wallahi Allah anzan tab'a d'aga maka ba,da duk Wanda na gano yana da saka hannu a wannan".ware ido Fadila tayi dukta raina kanta dukda tana cike da matsanancin tsoro haka ta daure tare da wayincewa,ruwa Nani ta mikowa Aiban da yak'i sauraren kowa ,ya k'arb'a tare da zubawa Najma,wata irin ajiyar zuciya ta saki ta mik'e da k'arfi tare da sakin kuka mai cin rai cikin dakiyar murya tace"bazai tab'a yiwuwa ba,bazan tab'a k'arb'ar wannan auren ba,nafi tsanarka fiye da yacce ka tsaneni,kayi gaskiya inhar da gaske kake ni dabbace Kuma karuwa naji dukna k'arb'a wannan aeba kaina farau ba,ka sakeni bazan tab'a iya zama inuwa d'aya da kai ba"takowa yayi har zuwa gabanta ya Kuma daure fuska ya fito a aenahin Ahaad dinshi yace"dama illar karuwanci kenan,ae kinsan inda kika kai mutuncin naki dole ki k'arb'a,Kuma kedin kin kasance me fuska biyu,Kuma baki da maraba da jahila ilimi beyi amfani ba,da iyayenmu na nan da wannan abun kunyar zai k'arasa mana su amma sai yau nake godewa Allah da suka mutu bs tare dasun riski wannan abun kunyar ba".murmushi Amaan yayi yace"wai meye na tashin hankalin yarinyar da bayau ta fara bin maza ba,so nawa na ganta kawai rufa mata asiri nakeyi,amma babu kalar namijin da batabi".lumshe ido Najma tayi tanajin kalaman Amaan kamar yana watsa mata garwashin wuta,hawayene sukaci gaba da zarya akan kumatunta bakinta ya soma rawa ta rasa kalmar furtawa illah innalillahi wa'inna ilaihir raju'un da taketa fad'a a zuciyarta dake barazanar tarwatsewa,matsowa Aiban yayi gabanta hannu yasa ya share mata hawayen yace"ki daina wannan kukan Najma ganin hawayenki yana tab'amun zuciya,ki daure ki k'arb'i kaddararki,sannan ki daure ki sanar mana da mahaifin yaran nan,nayi maki alk'awari kina haihuwa zan aureki,ba karuwa suke kiranki ba koda a gidan karuwai kike zan tabbatar na cika alk'awarina a kanki,bazan tab'a k'asa a guiwa ba,balle har yanzu ni ban zargeki ba,na dauki hakan a matsayin tsautsayi,indai har zaki soni to tabbas zan aureki a haka Kuma na rike abunda Allah ya baki tamkar nawa,ba zasu tab'a kukan maraici ba ,kuma zasu k'arb'a sunan Aiban a matsayin mahaifi"wani wawan duka Ahaad ya kaiwa Aiban a baki take jini ya b'alle bakinsa ya fashe ,dafe wurin yayi da sauri Mummy ta shiga tsakaninsu tace"Sulaiman kayi hauka ne?,akan karuwa zaka daki d'an aminiyata,ae babu batun aure yanzu basai anjima ba zaka datse igiyar dake tsakaninku sannan ka gayamun a yaushe akayimun wannan cin amanar da bak'in zalincin ba tare Dana sani ba".cikin dakiyar murya Najma tace"ko baki fad'a ba bazan k'ara awa d'aya a matsayin matar d'anki ba,never no way,dole ka sakeni yanzu".ji yayi k'afafuwansa na neman gaza daukarsa ,cikin kuka Mama tace"shege munafiki ka sakarmun jika yanzu basai anjima ba,kaga ta samu d'an mutuncu zai aureta ba irinku ba gadon Bilki"ihu Fadila ta saka tace"wallahi bazai yiwuba indai ina da rai Aiban baya da wata matar data wuce ni,wannan ae zalinci ne,jikanki yace neso shine za'a lik'awa mijina wallahi Aiban bazai auri jaruwaba wacce ta bayar da mutuncinta ga k'artan banza"runtse ido Najma tayi da k'arfi Amma ta kasa cewa komai,"tsaiwar uban meye kakeyi ka saketa yanzun nan,ko in tsine maka ba zan tab'a iya had'a jini da Sha'awa ba"cikin k'arfin dauriya ya furta "ni Ahaad Kabir Bindawa na saki matata Najma Jafar Bindawa saki d'aya"."uban meye yaci sauran biyun?"Mummy ta fad'a,girgiza kai ya shigayi yayi saurin ficewa daga d'akin yana goge guntun hawayen da yake k'ok'arin fitowa a idonshi.wani murmushin takaici Najma ta saki da k'yar take had'a yawu tana jin jiri na nemen kwasarta bango ta dafe tare da fara karanto duk addu'ar da tazo kanta.da gudu Fadila tayi hanyar fita tana sambatu tana kiran "yau k'arshen komai zaizo,yau zakiga abunda Ni Fadila zan it's aekatawa wallahi saina ajiye maki tabon da yafi wannan muni a rayuwarki,bazan tab'a barin kiyi nasara a kaina ba".Nani ta kama Najma sukayi part dinsu kuka tashin hankalinsu a lokacin ba'a misaltashi,jikin Nani Najma ta fad'a ta fara rusa kuka Wanda bata San dalilinsa ba.Aiban kam da k'yar ya lallab'a Shuhada ya tafi da ita gida,Wanda Shima ya gama fita hayyacinsa dauriya kawai yakeyi. *Tofa kunji yarda tashin hankali ya b'arke a wannan ahalin shin koya zata kaya ?kudai ku biyoni danjin k'arashen labarin* Allah ka gafartawa iyayenmu kayi Mana kyakyawan k'arshe Stylish star Jorderh majidadi 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RUHIN FANSA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 Na *Maryam ismail Majidadi* Telegram Maryam majidadi *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *_________________________________* Page 61-70 *End of part one* Zaune kawai Najma amma ta rasa gane duniya take ko lahira,gani takeyi kamar mafarki takeyi,rungume k'aton hotonta da Ummu da Abbi da Najwa tayi,wani irin marayan kuka ta saki mai ban tausayi,shafa pic din takeyi a hankali ta furta"nayi kewarku,a tunanina na saba da zama babu ku,amma gashi yanzu ne lokaci mafi mahimmanci da nake buk'atarku,ina buk'atar mai taimakona ,meyasa kuka tafi kuka barni?"shafa cikinta takeyi tayi zumbur ta mik'e tace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,nice da cikin da ba'a san ubanshi ba,ni Kaina bazan iya nuna waye ubansu ba,Allahumma ajirni fi musibati wa'akilibni khairan minha,ya Allah ka bani mafita"dafe kanta tayi tanajin yana barazanar tarwatsewa gashi lokaci d'aya ta soma jin jiri na ibarta,Nani kam kuka takeyi tana kuma lallashin Najma amma abun yaci tura. Mama ta buga uban tagumi sai hawaye takeyi,kiris take jira ta fashe sallamar Daddy yasa ta saki kukan da take nemanyi cikin masifa tace"Haba Kabiru yanzu a gabanka akai wannan d'ayan aeki,kanaji kana gani wancan bayahuden banzar ya sakarmun jika ba laifin tsaye bana zaune,kai ace iyalenka sunfi k'arfinka?,kaine babba a gidan nan fa,Kaine zaka iya daidaita komai daya lalace,amma ka zama hoto Bilki ta gama shanyeka,duk da tana y'ar y'ar'uwata amma ko kad'an basu da halin kirki,ya zama dole a gareka ka had'a taro na gaggawa ta warware abunda ke faruwa,ya zama dole kowa yasan dalilin aure Najma da Ahaad tunda magana ta fito fili,ka duba girman Allah ka zama namiji haba Kabiru"sai da ya tabbatar Mama ta gama sannan yace "kiyi hak'uri ki daina kuka insha Allah zansan abunyi,ni Kaina bana jin dadin abunda yake faruwa sai dai kuma bana so na yanke hukuncin da bai dace ba,ban sanin me yake zuwa kaina Mama amma aeta addu'a insha Allah komai zaiyi daidai"sallama yayiwa Mama ya fita yanajin wani nauyi a zuciyarsa sai dai besan kuma me zai iya aekatawa ba.Daddy yana zuwa ya iske Mummy da Amaan tsaye suna jiran shigowarsa"basai ka zauna bafa dama shigowarka nake jira,yau saika gayamun wanne macucinne ya had'a auren d'ana da waccen karuwar?,wallahi bazai yiwuba sam wannan ae munafirci ne"Mummy ta fad'a,kafin Daddy ya bada ansa sukaji muryar Mama tace"munenan muka munafirceki ae,a kanmu ya dace ki huce marar kunya"k'asa Mummy tayi da kai tace kowa ya sameni a parlo yanzu,juyawa tayi ta fita,uwar harara Mummy ta b'allawa Daddy sannan taja hannun Amaan suka fito parlo ,zaune suka samu Mama a kujera ga Ahaad zaune k'asa kusa da ita ya daura kanshi akan cinyarta idanuwansa a lumshe kamar meyin barci,duka jijiyoyin kanshi sun tashi radau radau kamar zanasu akayi.yatsina fuska Mummy tayi sannan suka zauna,Daddy ma ya zauan.a hankali take takowa zuwa wurin Nani na rik'e da hannunta danji takeyi kamar zata fad'i k'afuwanta basa daukarta,bakinta kam ya bushe yayi fari ko miyo da zata had'a babu saboda tsananin tashin hankali,can gefe suka zauna ita da Nani kamar marayu,Mamace ta bud'e taro da addu'a sannan tace tambaya ta farko anan shine "Hadiza ki fad'a mana wa yayi maki ciki?,waye uban d'an dake cikinki?".wani fad'uwar gaba ya dirarwa Najma ta lashi busassun lab'anta ta sunkuyar da kanta k'asa hawaye suna bin kuncinta cikin dishewar murya tace"ki tambayi Fadila ita tasan abunda ni ban sani ba"."wannan wanne irin sakarcu ne?Fadila ita keda ciki ko ke?,kiyi magana da kikasan kowa zai kama a matsayin ansa mana"Mummy ta fad'a .daure fuska Najma tayi tamau kamar an mata mutuwa tace"ban sani ba,nice uwa Kuma nice uba"gyad'a kai Mama tayi tace "dalilin taraku anan badan komai bane sai don mu samu mafita ga matsalar da ta kunno ga ahalin nan mai dunbin tarihi,yanzu idan muka yarda magana ta fita cikin minti kad'an zata zage duniya,musassaman gareki zaifi illah Najma keta mutane ce,Kuma mai taimakonsu ce Kuma y'a ga Jafar to tabbas cikin mintoci abun zai bazu,sannan abu na biyu shine sanin dalilin auren Najma da Ahaad"."Mama kiyi magana kai tsaye ki bada dalilin aurensu amma magana kam ae ta fita ta gama,tunda ciki dole ya fito,Kuma ae fita takeyi Kuma bazata iya hak'ura da zuwa wurin kwartonta ba"Amaan ya fad'a duk abunnan sai yanzu Ahaad ya d'ago yana aekawa Amaan da wata muguwar kallo mai cike da ka shiga taitayinka,ji yayi da Amaan na maganar kamar ana yankar naman jikinsa da addane zuciyarsa kam suya kawai takeyi kamar ana soyen gy'ada,kallo d'aya zakawa Ahaad ka kawar da fuska saboda yanda ya canza kammanci saboda tsabar b'acin rai,ya koma sojan nashi na asali babu alamun Wasa tare dashi,da sauri Amaan yayi shiru ganin irin badak'alar dake dososhi idan harya kuskura yaci gaba da magana,nisa Mama tayi tace a shekarun baya lokacin Najma tana da shekara d'aya a duniya ita da y'ar uwarta Najwa Kuma cikin shekararne kakanku wato mijina ya rasu saidai kafin ya rasu yayi abunda ya dace ,abun ya fara ne daga lokacin da kika dauki hassada da Karan tsana kika daurawa Sha'awa,Kuma a lokacin kina zarginta da janye hankalin d'anki Ahaad wanda bakiga d'awainiyar da tasha dashi ba,haihuwar Ahaad kawai kikayi amma ke kanki kinsan ita ta masa wahala ta uwa kuma Ahaad tarbiyar Sha'awa ne shiyasa ya banbanta da wannan shashashun yaran naki"wani Kallo Amaan yabi Mama dashi,dakuwa tayi masa tace"ungo wannan ja'irin yaro,kai meka sani ,ita uwar taka ae tasan komai,Kuma batayi la'akari da cewa Allah shike azirta bayinsa ba,dan Sha'awa ta fita komai bashi ke nufin ta fita wurin Allah ba,wannan jin zafin shiya kawo rarrabuwa tsakanin iyalinmu,Wanda hakan ba k'aramin d'aga mana hankali yayi ba,babu jituwa tsakanin Kabir da Jafar Wanda a da ba haka suke ba,sune mafi soyuwar y'an uwa Wanda na gani Wanda d'ayansu zai iya sadaukar da rayuwarsa danya ceci ta d'an uwansa wanda nayi kukan hakan ,nayi bak'in cikin rarrabuwa kan Yarana,Kuma har Allah ya k'arb'i ran d'an uwansa basu dawo kamar da ba,wannan dalilin ne yasa Alhaji Sulaiman kakanku ya yanke shawarar had'a yaransu aure tun suna k'anana Wanda muna ganin hakan zai kawo mana mafita,lokacin daya kawomun maganar banyi tantama ba na amince amma ya zomun da niyar had'a aure Amaan da Najwa ne"."tabdi lallai da anyi babban kuskure kuwa,ni za'a aurawa wad'annan jinin karuwan?".kallon rainin wayau Najma tayiwa Amaan cikin hassala da dasasshiyar murya da bata fita sosai tace"da ita zata fi kowa bak'in ciki saboda ta auri dangin bunch of murders,gaba dayanku haka kuke makisa ,azzalumai kawai"wani wawan mari taji an dauketa dashi ba tare da tayi aune ba,Ahaad ne ya mareta ya nuna ta da yatsa amma ya kasa furta komai,cikin sanyin murya tace"kayi komai kaso,amma wannan ya zama rana ta k'arshe da zakayi k'ok'arin daura hannunka akan jikina,dan bazan tab'a iya jurewa ba,karka yarda sauran girman da nake ganinka dashi ya idasa zubewa kamar nasu"."ya isa haka kada na k'ara jin wannan shashancin a tattare daku,ba kamar ke da yake Ahaad wanki ne to kome yayi maki dole ki girmamashi"Mama ta fad'a sannan taci gaba da cewa ana zuwa wurin daurin auren a parlon Baban Sha'awa wato Alhaji Aminu ,Ahaad ya shigo rike da hannun Najma zama yayi yanajin me ake fad'a a lokacin yana shekara goma sha biyu,kallonsu Alhaji Aminu yayi yace"wannan aure akan Ahaad da Najma ya dace ba Amaan da Najwa ba,dalilina shine Najma tun tana k'arama kuna ganin yarda take shiga wurinsu Kuma kome zasu mata zatayi kuka anjima ta koma saboda yarda ta shak'u da Ahaad,kuma shima ku lura yana yawan fad'a da kowa a kanta,Najwa kam ko yarda dasu batayi data gansu da ta soma kuka wannan shawara ce".da wad'annan bayanan kowa ya gamsu Jafar ya duba jikin Ahaad dan ganin meye zai bada a matsayin sadaki,agogon hannunsa ya kallah wacce ak'allah a wannan lokacin zatayi dubu d'ari biyu ya dafashi yace " "Babana ka bada sadakin k'anwarka,zamuyi maku aure yanzu"kasancewar Ahaad yarone me wayau da basira da saurin fahimtar abu Kuma ya gane kome suke nufi yasa ya warwaro agogon hannunshi da kanshi yace"Abbuna wannan zaiyi?"murmushi dukansu sukayi suka k'arb'a tare da saka masa albarka sannan aka daura auren wannan shine dalilin auren Ahaad da Najma".turo baki Mummy tayi tare da sakin shewa tace"to Alhmdllh Allah ya rabamu da bakin iri,ada ae Ahaad a mallake hake amma yanzu da matsafiyar ta mutu ae gashi ya dawo gareni"murmushi mai kuna Najma tayi sannan ta mik'e tsaye tace"waya gaya maku Mamana ta mutu?,ko da yake dama ae pretending aekinku ne,ina so ku sani ina nan zuwa gareku,zaku biya kome kuka aekata"wata irin zuface ta kuma karyowa Amaan da Mummy suka kalli juna,cikin zuciya Mummy tace badai yarinyar nan ta gano sirrinmu ba,dole musan abunyi,Amaan kam suman zaune yayi yana tunanin meye hujjarta ta kirasu Makasa Kuma yanzu tace Mamanta na da rai Kuma zasu biya,dawowa hayyacinsa yayi sanadiyar tafin da Najma tayi a saitin fuskarsa ta sakar masa murmushi,sannan ta juya ta fice.mikewa Ahaad yayi yabar masu parlon yana zuwa d'akinshi ya Kuma dafe kanshi akwati ya dauko ya soma zuba duk kayan daya shiga gabansa ,dan ko gani sosai bayayi,abubuwanshi ya kwasa ya fito parlon ,tararsa Najma tayi kowa yana kallonta tace"badai wannan shike had'a rigimar ba?,badai su suka sanya kowa namu cikin tashin hankali ba?meye dukiyar gado?wanda kunsan ba naku bane ba amma kuka saka San zuciya a kai ba?"ta k'are maganar tana d'aga files din ,duka wani dunbin dukiyarsu yana wurin sannan taci gaba da cewa zan tafi nabar maku har gidan bazan Kuma ci daga wannan dukiyar ko sha ba,bazan k'aru da komai da ita ba dukda hakkina ne"hannun Ahaad ta kama ta saka files din ,sannan tayi waya banji me aka ce mata ba naji tace"shikenan ka shigo kawai".cire sims dinta tayi ta karya ta ajiye masu wayar taja hannun Nani tayi hanyar fita.kuka Mama ta saki tana kiranta amma Najma ko waiwayowa batayi ba,Mummy da Amaan murmushi kawai sukeyi,a hankali Amaan yace"Mummy yanzu zata fad'i,Dr Jamil ya gayamun allurar yauce ranarta ta k'arshe a jikinta"wani irin sanyi ne ya ratsa Mummy dajin batun Amaan.tana fitowa cikin gate din sukayi karo da Fadila,wani murmushi Fadila ta saki tace"Najma Jafar Bindawa my beloved sis,am going to miss u,zanga yarda zaku kasance tare zanga abunda zai kallah harya birgesa kyau shine abunda kike tak'ama dashi da dukiya kuma,yanzu ba dukiyar kyan ma zaki rasashi,da sauri Najma ta tura Nani gefe hakan yayi daidai da shigowar Aiban kuma,dariya Fadila ta kwashe dashi kafin Najma tayi magana ta fito da kwalbar Acid din dake bayanta ta watsashi a fuskar Najma a gefen dama,wata irin gigitacciyar k'ara Najma ta saki,Nani ma ihun ta saki ,Fadila kam ta saki kwalbar a k'asa ta shek'a a guje Islam ta dauketa a mota,da wani irin gudu Aiban ya k'araso Najma ta fad'o a hannunsa,k'ok'arin saka hannu takeyi ta shafa fuskar amma ya rike hannayenta hawaye nabin kuncinshi.jin ihu yayi yawa yasa y'an cikin gidan suka fito da gudu saidai har Aiban ya fice daga gate din Nani na biye dashi,wani irin nishi Najma tayi ta fara zubar da bakin abu kawai jikinta ya sake duk wata abu da zata nuna tana da rai ya daina aeki,"no no no it's can't be possible,Najma karki tafi ki barmu,da gudu Ahaad da Amaan suka fito gate din,amma sai dai sukaga k'urar tashin mota."waye yazo ya fita yanzu"Amaan ya tambayi me gadi,share k'wallah yayi yace "bansanshi ba,amma ya fita yana kuka Hajiya Najma ta rasu"wani irin bugawa gaban Ahaad yayi take jinsa da ganinsa suka dauke ya fad'i a wurin sumamme.kuka Mummy da Mama suka saka Daddy kam rasa ina zai saka kanshi yayi .daukar Ahaad sukayi zuwa cikin gida sannan suka fara Kiran Dr.kafin kace me cikin y'an mintoci labari ya bazu an zubawa Najma Acid ,sannan an kasheta kuma an gudu da gawarta,wannan labarin ya fita ne ta hanyar Islam ,tuni gani ya karad'e kowa da abunda yake fad'a ,masu muka nayi masu addu'a nayi abun takaicin shine Kuma ba'asan wa yayi mata wannan abun ba.a labarai Shuhada ta gani wata irin k'ara ta k'wallah tayo waje ba mayafi tana rusa kuka dan harga Allah tanajin soyayyar Najma kamar y'ar uwarta ta jini.ba shiri Hajiya Sadiya ta riketa amma taki natsuwa har sai da suka tafi gidan .da k'yar suka samu hanyar shiga gidan,ko ina y'an sanda ne zagaye da wurin sai sojoji yaran Ahaad sun hana y'an jarida shiga gidan. *Tofa ya wannan abun zai kasance,lallai akwai rudarwa da sarkakiya kudai ku biyoni a part 2 danjin ya wannan labarin zai kasance,shin Najma zatayi nasara kuwa?ina Fadila ta tafi?me yake damun Ahaad?ina Aiban zai kai gawar Najma da Nani?ina makomar Mummy da Dr Jamil da Kuma Amaan?ya Shuhada zata kasance,meye rawar da Hajiya Sadiya zata Kuma takawa?ina labarin Barrister Abbas mai kula da harkokin Abbi?,shin da gaske Ummu bata mutu ba?wannan tambayoyin dukku nemi ansoshinku a part 2* *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan k'arshe* Stylish star Jorderh majidadi 07033636337 for shawara or comments