Showing 120001 words to 123000 words out of 141755 words
Chapter 41 - NIDA PATIENT DINA Majinyacina, Ƙaddarata by MRS ISHAM
batace mishi komai ba , kuma bata tashi mishi akai ba ganin hakane yasa yatashi akan kujeran dayake ya koma wani yaci gaba da abinda yake yi sake tsayawa tayi akanshi , kallonta kawai yayi bece komai ba yadauki wayarshi yabar falon yahaura upstairs kamar daga sama yaganta agabanshi ja da baya yayi ɗan yadan tsorata saboda yasan afalo yabarta maida kallonshi yayi fallon yaga tana nan a inda yabarta sannan yakalli wacce take gabanshi addu'a yafarayi acikin zuciyarshi kafin ya ce " meye kike bukata awajena ? Meya kawoki wannan gida?" Murmushi tayi mishi kafin ta ce " abinda nake buƙata awajanka shine ranka , abinda yakawo gidan nan kuma shine kashe duk wani wanda yake cikin wannan ahalin " duk adan tsorace hafiz yake amma afusace ya ce " Allah baze taba baki nasara ba , kuma nima bazan bar hakan yafaru ba sede koke koni! Koki kasheni ko ni in kasheki" dariyar bosawa tayi harda rike ciki ganin yanda yake da karfin hali kyasta yatsunta tayi nan take kayan jikinta da ita kanta ta sauya, fara ce sol tana sanye da bakaken kaya ,matsetsen riga da wando baƙi jikin riga da wandon akwai chains , ga uban hills shima baƙi , gashin kanta brown color ne curly bakinta yasha baƙin janbaki , shiganta da komai nata na yan America ne , ja baya yakeyi tana biye dashi ta ce " zamu gani yau kaiɗin jarumine ko kuma ragone " juyawa hafiz yayi yana neman abinda ze buga mata mopper ya hango yadauko ya buga mata akanta nan take mopper ya karye sake ja da baya hafiz yayi ya ce " to ke din wacece ? meye mugun nufin ki akan mu?" Hannunta ta mika nan take yayi tsayi tashaƙo wuyar hafiz ta dagashi sama kafin ta ce" okay tunda abinda kake so ka ji kafin ka mutu , sunana Jessica kelvin " tana fadar haka ta kara shaƙe mishi wuya sannan taje can saman upstairs tana shirin wurgoshi ƙasa, kallon ƙasa hafiz yayi yaga irin mugun nisa dayake dashi da ƙasa yasan tabbas ta wurgoshi mutuwa zeyi hakan yasa muryarshi da baya fita sosai saboda shaƙeshin datayi ya ce " hairahhhhhhhhhh" dariya tayi ta ce " itakuma wacece haka shin kana ganin zata ceceka ne ?" .
Suna zaune suna hira lokacin su Abba da baba ma sun dawo suna cikin dakin , zuruf sukaga hairah ta mike jikinta ne yadau rawa , ko wannensu da al ajabi akan fuskokinsu suke kallonta, zubewa tayi aƙasa jikinta na ci gaba da rawa mikewa dukkansu sukayi suna tambayarta meya faruwa amma ba ta basu amsa ba ya Usman yasa hannu yadagota yazaunar da ita akan gadon fanan yana mata magana " hairah meyake damunki ?" hawaye takeyi jikinta na tsuma , fanan ce ta ce" kowa yanda yi shuru na wasu lokuta " mikawa hairah hannunta tayi duka biyu , daura hannayen hairah tayi da nata hannun lokaci daya jikinta yadena rawan dakyar ta iya cewa " yayana ! Zata kashemin yayana " fanan ta ce "ki fadamin meye kike kallo " ta ce " na naganta itadin makira ce kuma mara imani " sake matse hannun fanan tayi ta cigaba da magana " ta shaƙe yaya hafiz zata wurgoshi ƙasa daga upstairs" jin abinda tafada ya tsorata su de yanzu suka tuna da babu kowa agidan dasauri fanan ta ce " su waye agidan bayan hafiz din sannan akan waye kike magana?" Hairah ta ce " babu kowa agidan securites ne dasuke cikin compound babu wanda yasan abinda yake faruwa , yayana kuma ita da shine acikin falo yanzu haka tana gab da wurgoshi ƙasa" tana gama fadin haka Abba dasauri yazaro wayarshi yakira number securites din gidan nan take suka daga yasanar dasu abinda yake faruwa , kusan su ashirin suka shiga cikin falon lokacin da Jessica ta gansu dariyar mugunta tayi sannan ta ajiye hafiz a ƙasa shafa wuyanshi yayi yana tari ganin tana gangarawa downstairs ne yasa yafara rarrafawa yasulale yashiga part din Mr azaad daga nan ya bullo ta garden sannan yafito compound baba me gadi ne kaɗai se driver suka rage acikin gidan dakyar ya iya kwalawa driver kira suka shiga motar yace mishi yakaishi gun ummi da gudu driver yafisgi motar .
Gangarowa ƙasa Jessica tayi ta tsaya a tsakiyarsu wani daga cikinsu ne yafara tunkaronta duka daya ta mishi yazube aƙasa yasuma , dukansu takeyi baji ba gani kaff dinsu kaff seda ta sumar dasu da muguwar duka , sannan ta fito compound tunda baba me gadi yaganta yaji tabashi tsoro tunkafin ta ce yabude mata kofa yabude .
fita tayi tana kallon titin daya kasu gida uku nan take tagano hanyar da su hafiz sukafi ,gudu tafarayi tana ɓacewa kamar walkiya tana bin bayansu .
Hairah dake rike da hannun fanan tana kallon duk abinda ke faruwa a falon ta ce " dukkansu tamusu duka sannan ta sumar dasu , yayana kuma yanzu haka yashigo asibitin nan tana binshi abaya " tana karishe maganar da takeyi tasake hannun fanan, ta mike tsaye , tana magana da hafiz dake gudun ceton ranshi domin har cikin asibitin ta biyoshi mutane se kallonta sukeyi kamar sun samu tv , yana gudu itakuma tana tafiya cikin kwanciyar hankali.
Gudu yakeyi yana hakki yana jin kwantaccen da hairah takeyi mishi can yace " hairah naga wasu kofofi gudu biyu wanne zanshiga wanne ne kuke ciki ga ta nan abayana" tsayawa hairah tayi abakin kofa ta ce " na farko zaka shigo yaya " sude al'amarin ya matuƙar girgizasu tunani suka farayi suna tambayar kansu shin hafiz da hairah sudin su waye ?.
Da karfin gaske ya turo kofar yarungume hairah dake tsaye abakin kofa, fashewa tayi da kuka tana " yayana " suna a haka Jessica tashigo dakin ja da baya sukayi dagudu hairah taje ta buya abayan mama shikuma hafiz ya boye a bayan Mr azaad harde hannunta tayi akirjinta tana kallonsu kamar yanda suma ita suke kallo seyanzu suka gane ashe Maryam din da Abba yatsinto ce innalillahi wainna ilaijiraji unnn lallai duniya babu yadda aciki se ka taimaki mutum yazo ya cuceka shisaka yanzu taimako yayi karanci , zuciyar Abba se kuna yakeyi yana kallon Maryam yama kasa magana amma har cikin ranshi beyi danasanin taimaka mata da yayi ba domin shi tsakani da Allah yataimaka mata , kallon Mr azaad tayi ta ce " ka turo yaron bayanka ko kuma ta sanadiyyar shi kowa na dakin nan ya rasa rayuwarshi , mugun kallo fanan da Mr azaad suke watsa mata, ganin beze miko mata shi bane yasa taje gaban Mr azaad din tasa hannu zata jawoshi Mr azaad yakai mata damka a wuya sannan ya dagata sama ya hade kanta da jikin bangon dakin ta zube aƙasa, daman haushinta yakeji domin yanzu yasake tabbatarwa Ita ce nan ummul aba isin abinda yafaru da fanan tana kokarin mikewa daga bugun datasha Mr azaad ya taka ruwan cikinta so yakeyi kawai yaga ta mutu ko hakan ze rage mishi raradin abinda yakeji , sa hannu yayi ya sake damko gashin kanta , ɓacewa tayi ta dawo bayanshi ta ce " kana tunanin zaka gwada min kai jarumine hahaaa" tafada tana dariya nuna anty shayida ta yi da hairah da hafiz ta ce " dake , dake dakuma kai duk sena kasheku ayau din nan " a tsorace anty shayida ta je taboye akusa da Abba . Baba ne ya ce " baiwar Allah menene hadinki damu ? wani laifin mukayi miki ne ?" Abba ya kalli baba yace " ni ne nan nakawota gida da niyar taimaka mata ashe annoba nadauko bansaniba" Maida kallonta kan baba tayi ta ce " babu abinda kukayi mini nidin yar saƙoce nazo gudanar da abinda aka aiko nine " ummi ta ce " to waye ya aiko ki wajen mu " fanan da ranta yayi matuƙar ɓaci ne ta ce " yi shuru ummina kar wanda yasake ce mata ƙala yanzu zatayi da nasanin zuwa aikan da aka mata " tana magana tana zuro ƙafafuwan ta kasa mikewa tayi tsaye tana bin Jessica da kallo dama tun farkon ganin da ta mata taji tsanarta lokaci daya ashe akwai dalilin haka, tunkaro fanan tayi tana kallonta daga sama har kasa cikin shakiyanci ta ce" oho nagane wato ke ce sarauniya? Amma yanaga bakiyi kama da sarauniyar da kowa yake shakka ba yanda ake labarin ki se naga ba haka kike ba , kinmin kama da matsoraciya sede balaifi kinada kyau kam, dukda bake nazo kashewa ba wancar me cikin nazo kashewa sekuma kema kina da ciki sekiyi kokarin taimaka mata ta hanyar zuwa a madadin ta , hakanma ba laifi tunda kema kinada cikin " tayi magana tana kallon anty shayida dake bayan Abba ,murmushi fanan tayi ta ce" kwantar da hankali, ai gane asali ba daga fuska take ba se angwada ake ganewa . shin kinason ganin asalina? amma fa kisani in kika gani ba lallai ba kici gaba da rayuwa ba " cewar fanan da idonta yakoma kalar fari tayi magana tana damkar wuyan Jessica kokarin kwatar kanta Jessica tafara tana fisge_fisge amma takasa kwatar kanta a hannun fanan, matso da fuskanta fanan tayi daff dana Jessica,sannan ta zaro idonta da suka koma fari tass babu digon baƙi aciki , hasken cikin idonta ne yafara shiga cikin idon Jessica nan take tafara konewa ta ciki ihu tafarayi . Fanan ta ce" nasan zaki bawa wa'yanda suka aiko ki labari inkun hadu a lahira " tana gama fadin haka tasake Jessica ta fadi ƙasa nan take jikinta yafara karkarwa kamar wacce aka jonawa shocking jikinta nafitar da hayaƙi me tururi haka tadingayi har ta koma kwarangwal daga nan kuma takoma toka tabace.
Dukkansu ajiyar zuciya suka sauke ganin sun rabu da ita , jinjina mata zeenat dake ɓoye abayan mama tayi ta ce " aikin ki na kyau anty fanan" hararanta fanan tayi ta ce " kema naki nakyau saboda kin iya ɓuya kam " dariya sukayi .
Kallon hafiz fanan tayi ta ce " lallai hafiz kaiɗin jarumine kayi na mijin kokari " hafiz da se yanzu hankalin shi yakwanta ganin fanan ta gabama da Jessica yayi murmushi kawai yaje bayan mama yariko hannun hairah suka zauna akusa da ya usman ya ce" fatan babu abinda yake damunki " kai ta gyada mishi sannan ta kwantar da kanta akan kafadarshi , sude yanzu tunda sun samu sun rabu da Jessica damuwar su susan su hairah sudin menene suke dauke dashi koɗe karya sukayi musu adangane da asalinsu.
Babane ya ce " hafiz shin ya akayi kuke iya magana da junanku batare da waya ba kuma hairah take iya ganinka aduk inda kake ? " Ajiyar zuciya hairah da hafiz suka sauke atare domin sun san dama dole sesunyi zargin wani abu , hafiz ya ce " mahaifinmu yakasance babban wanzami ne dake taimako sosai kuma yana bada magani , yana aiki da aljanu to tun muna yara wata rana yadawo gida da daddare muna bacci yasa mamanmu ta tashemu , zama mukayi agabanshi ya ce " hafiz ga hairah kanwarka ce ko bayan ranmu nasan zaka iya kula da ita " sannan ya yafito da wasu abubuwa acikin leda wanda nida hairah bamu san meye aciki ba, sunce ledar yayi nan take mukaga wasu abubuwa guda uku biyu masu zubi da kunne daya kuma kamar ido , miƙa min kunnen yayi yace in rike shi da karfi sannan yabawa hairah ido da hannu ya ce itama tarike, bamufi mintuna 30 da rikewa ba muka nemi abubuwan mukarasa domin ji mukayi babu su ahannun namu ashe cikin jikinmu yashige , se babanmu yace mana wannan abinda yabamu shine zezama garkuwa garemu duk nisar duniyar damuke zamu iya magana da junanmu sannan hairah zata na kallona inde wani mugun abu ze faru ne kaɗai hakan ze kasance, tundaga wannan lokacin in waninmu yana cikin hatsari mukan iya jiyowa har musamu wa'yanda zasu taimaka , wannan shine " shuru sukayi suna jinjina wannan lamarin ta wani bangaren za'a iya cewa hakan ze taimakawa yaran amma ta tawani bangaren hakan tsubbu ne tunda bawai dashi aka haife su ba rana tsaka yasaka musu shi ajikinsu , abba ne ya ce" Allah yajikansu da rahama " suka amsa da ameen.
Washe gari doctors din ganin jikin fanan da sauki sosai yasa ya rubuta mata sallama , sungama kimtsawa mazan suke jira su shigo su tafi wa'yanda suka kwana da fanan ummi ce se anty shayida , su mama tun jiya bayan mangrib suka koma gida zeenat kuma Abba ne yacewa Mr azaad da fawwaz su maida su gida , Mr azaad da yaseer suka shigo cikin asibitin ga securites suna binsu abayana rike da manyan kwalaye yaɗuwa yayi da doctor din yabashi result din fanan, shiga cikin resting room din sukayi suka bar securites din suna rabawa majinyata da kuma nurses din asibitin kudi kamar yanda Mr azaad ya sanar da su , duk wani wanda yake cikin asibitin seda yasamu dubu dari dari , haka suka dinga kwararowa Mr azaad da family shi adduo'i , saboda awannan lokacin kafi karfin abinda zakaci arana daya ma ka godewa Allah gashi yau sun samu wani bawan Allah yaraba musu kyautar dubu ɗari _ɗari babu abinda zasu gode masa dashi sama da addu'a.
Tana zaune akan gadon ta sanya doguwar rigar atamfa kanta ba dankwali saboda bandejin dake kanta ummi ce tahaɗe mata gashin tadaure mata da ribbon zama yayi akusa da ita yasa hannu yana ɗan taba kan nata kaɗan gaisheshi tayi shida yaseer, amsawa yaseer yayi sannan yamata yajiki , Mr azaad be amsa mata gaisuwar da ta mishi ba ya ce " wifey ya jikin naki " kallon ummi tayi taga hankalinta ba'a kansu yake ba tana magana ne da yaseer, ta ce " jiki alhamdulillah" tashi sukayi da niyyar tafiya rike hannunta yayi ya mikar da ita tsaye sannan yadau gyalen da ya gani akan gadon ya rufe mata ajikinta, gaba su ummi sukayi shikuma yana rike da ita suna baya , duk inda suka wuce se jama'ar asibitin sun mishi godiya tare da sa mishi albarka haka suka shiga motoci suka dau hanyar gida , bayan sun isa ne , duk afalo suka samu su zeenat suna zaune suna zaman jiransu tashi sunayiwa fanan ya jiki ta amsa musu fuska asake wucewa da ita Mr azaad yayi zuwa part dinshi basu tsaya a ko ina ba se a bedroom dinshi zaunar da ita yayi akan gadon ya zauna akusa da kwantar da kanta tayi akan kirjinshi tana shaƙar kamshin turarensa , " habiby inasanka sosai" kallonta yayi da sexy eyes dinshi yace " wifey! inasanki bantaba tunanin aduniyar nan akwai macen da zanso har inyi rayuwar aure da ita ba se akanki Allah yadoramin sanki banajin zan iya rayuwa batare dake ba, inasonki sosai da ke dakuma unborn baby mu " dagowa tayi dasauri ta kalleshi da alamar tambaya ta ce" habiby bangane abin kake son fadamin ba ! what do you mean by our unborn baby?" daura hannunshi yayi akan shamulallen cikinta da babu alamun akwai ɗa aciki ya ce" yes up course baby kina dauke da ciki , kinadauke da jinina acikin ki munkusa zama parents, bazan iya misalta irin farin ciki da nake ciki ba " hawaye ne yafara wanke mata fuska da mamaki yake kallonta ganin daga fada mata tana dauke da ciki tafara hawaye gabanshi ne yafadi tsoronshi daya kar fanan ta ce batason cikin dake jikinta, riko hannayen ta yayi suna fuskantar juna ya ce" baby why are you crying?" rungumeshi tayi gam cikin muryan kuka ta ce" habiby kukan farin ciki nakeyi , nima yau ina dauke da baby acikina alhamdulillah zanji abinda iyaye sukeji insuna da juna biyu. habiby babban farin cikina shine zantafi in bar muku abinda zaku kalla kuji sanyi aranku , ko bayan raina nasan nabar iri aɗoron ƙasa " shi yanzu babu abinda ya tsana sama da yadinga jin maganar tafiyanta hakan daga mishi hankali yakeyi se yaji kamar shima yabita kome ze faru ya faru shafa bayanta yakeyi ya ce" kidena fadar haka ko so kike kidinga dagamin hankaline , yanzu lokacin farin ciki ne ba lokacin bakin ciki ba Please ki bari " raba jikinta da nashi tayi ta aro murmushi ta yaɓa wa fuskanta ta ce" am sorry my love bazan sake ba , yanzu fadamin wata nawa ne babyn ?" fito da result din da doctor yabashi yayi ya bude duk sun nutsu shida ita suna karantawa sosai sukayi mamaki ganin cikin wata hudu ne dede, su duk tunanin su karamin cikine da be wuce one month ba ganin yanda cikin nata yake a shamule babu alamar akwai ɗa acikinsa " laah habiby cikin wai wata hudu amma kalli cikina " tafada tana daukan hannunshi ta daura cikinta shafa cikin yayi yaduƙo da kanshi dede cikin ya mannawa cikin nata kiss shafa kanshi tayi tana murmushi ta ce " father to be " yar dariya yayi ya ce " yes yakamata ko da yaushe mahaifi yadinga jin lafiyar ɗan sa " cike da so da kaunar juna suke ta hira .
Bayan kwana biyar da sallamota anty amina ta kawo me gyaran amaren part din mommy da ba kowa aciki aka gyara aka fitar da kayan tsafinta aka konasu, aka bar musu part din anan zasuyi komai dinsu aciki zeenat ce ta fara dawuwa aka fara mata ta , anty amina tace fanan ma itama amaryace harda ita tare aka fara musu ita da zeenat.
Suhaima tadawo gombe saboda baba ne ze aurar da ita , anty amina ce tazo har gidan ta roƙi alfarma awajen mama akan ta bata aron suhaima da hairah tadauko me gyaran da zata yiwa du ka amaren gyara , dakyar mama tayarda ita gani takeyi za'a daura musu dawainiya ahaka anty amina ta lallabata ta ɗauki suhaima da hairah daga nan bayan sun fito tashiga gidansu Amira ta taroki hajiyar