Showing 42001 words to 43214 words out of 43214 words

Chapter 15 - YAKANAH! BOOK COMPLETED BY TAKORI KABARA .pdf


makarantar Islamiyya ta yara maza da mata a nan Abuja, da aka sanyawa suna NANA
HADIZAH ISLAMIYYAH. Haddar Alkur’ani mai girma ake yi tsantsa, sai sauran littattafan addini
irin su Ishmawi, Bulugul Maram, Sirah, Hadith, Al-Akhdari, Fikh da koyar da harshen larabci.
Ana zuwa daga karfe biyu na rana zuwa shida na yamma.
Ba ta da abin da za ta ce da Dr. kuma Minista, Sulaiman dan Sulaiman, sai godiya da addu’ar
alheri, domin ya gama cika mata burinta na son yada ilimin Alkur’ani da hadisi, kamar yadda ta
ke buri.
Ya lullube ta da duk wasu alhairori na rayuwa, ya lullube ta da so da kauna. Gaskiyar Babanta
ne; Alqur’anin ta ba zai bari ta tozarta ba!!!

Ta san Sulaiman ba ya son ta ya aure ta, kuma ba zai taba son wata diya mace kamar yadda ya
so Hadiza ba, amma tana tantama a halin yanzu, idan son da yake mata baiyi kunnen doki da
wanda ya yi wa Yayarta Dr. Hadiza ba.

A alfarma ta soyayyah, ta san ba ta cancanci Dr. Sulaiman ya so ta a wancan lokacin ba, amma

ya so ta saboda hakuri, juriyar ta da YAKANAR ta. Ya so ta sabida kyawawan halayenta.
“Mene ne YAKANAH?”
Nayi tattaki har gidan Dr. BAKORI na tambayi Malamarmu, Dr. Fatima Ja’afar Mai-Yadi.
Ta yi murmushin ta mai motsa zuciya tace.
“Takori ba ki san Yakanah ba?”
Na ce, “Ina zan sani Fati? Sai ku malaman addini”.
Ta yi murmushi ta ce,
“Nima daliba ce SUMAYYAH! Sai dai in sanar da ke dan abin da na sani a dalibtaka ta”.
Na ce, “daure ki sanar dani Aunty Fati, komi kankantar sa. Domin al’umma zasu so su san me
ita wannan kalma ta YAKANAH take nufi?”.
Faty ta yi murmushi tana dubana ;

MECE CE YAKANAH???

Ita YAKANAH ba kasaifai ake ganin ta a wajen yawancin mutane ba, YAKANAH ita ce take
daukaka darajar mai yin Ibadah, ta kai shi wani matsayi na daukaka a wajen Allah. YAKANAH
ita ce tushen dukkanin aiyuka na gari, wato daukacin ayyukan kirki suna fitowa ne daga cikin ta.
Mutum mai YAKANAH shi ne mai yin babban jihadi ko gwagwarmaya da kansa wajen watsi da
abubuwan da rai da zuciya ke so, saboda neman yardar Ubangiji, da neman dadin falalar sa,
tare da nuna biyayya a gare shi.
An ambaci irin wadannan mutane a cikin Alkur’ani mai girma, kamar cikin suratul Al-Imran
(3:17) Al-Nisa’i (4:25, 127-128), Fussilati (41:34) da sauran su.
Irin wannan babban jihadi da kai ana yin sa ne tsakanin mutum da zuciyar sa (Nafs
Al-Ammara), domin sauya ta ya zuwa (Nafs Al-Lawwama), sannan ya zuwa zuciya
madaukakiya (Nafs Al-Mutma’innah).
Saboda haka madallah da ita wannan baiwa ta YAKANAH, domin tana kai masu yin Ibadah
zuwa ga matakin shiga cikin rukunin salihai wadanda a koyaushe suna masu yin godiya a kan
dukkanin abin da ya zo musu daga Allah.
YAKANAH it ce kololiyar taqwa wato tsoron Allah. Takwah kuma ita ce mai kore tsoron haduwa
da Allah (wanda ba ya jin kunyar ubangijinsa kuma mai sabon sa, shi ne mai zama cikin
fargabar haduwa da Allah).
Daya daga cikin ma’anar YAKANAH ita ce, ka dinga kallon kanka a matsayin kai ba kowa bane
a cikin jama’a, kuma kowa ya fi ka, saboda haka YAKANAH tana nuni da rashin kasancewar
mutum cikin halin GIRMAN KAI!
Misalai: Idan ka kasance mutum ne kai mai YAKANAH ta gaske, a duk lokacin da ka gamu da
wani mutum wanda baka san shi ba, komi lalacewar sa, sai ka ce da kanka a cikin zuciyar ka.
“Watakila matsayin wannan mutum a wajen Allah ya fi nawa”.
Idan kuwa ka gamu da yaro kankani, sai ka cewa kanka, “Ka ga wanda ba ya sabon Allah, ni
kuwa ina yi”.
Idan kuwa ka gamu da wanda ya girme ka, sai ka ce, “Ka ga wanda ya jima yana bautar
Ubangiji tuntuni kafin ni”.
Idan kuwa ka yi kicibus da mutum mai dimbin ilimi, sai ka ce, “Ga wanda aka yiwa baiwa da
abin da ni bani da shi, domin ya fi ni ilimi, kuma yana aiki da ilimin sa, amma ni ko ya ya dai?”

Idan kuwa ka yi karo da jahili, sai ka ce, “Dubi wani yana sabon Allah cikin rashin sani, ni kuma
ina yi cikin sani. Ga shi kuma ban san yanda karshen sa zai kasance ba, kuma ban san nawa
karshen ba. Ko me zai zama a nan gaba? Allah shi ya fi kowa sani”.
Idan kuwa ka gamu da kafiri, sai ka ce da kanka, “Wa ya sani? Watakila nan gaba ya musulunta
kafin ya mutu, kuma wa ya sani ko ni kuma in mutu a kafirce?”
Ire-iren wadannan maganganun gaba daya suna nuni da halin mutumin da YAKANAH da
tawali’u suka baibaye shi, yake kuma cikin hali na binciken kansa a koyaushe.
Dalilin irin wannan tunani a zuciyar wannan bawan Allah shi ne, yana cikin yanayi na rashin
yarda da kansa. Tare da rashin tabbas game da abin da zai abku wajen haduwar sa da Allah.
Ire-iren wadannan tunani kuwa suna nuna karfin imani ne da dogaro da Allah madaukakin sarki
wanda shi ne tushen kaskantar da kai.
A kowanne lokaci idan bawa ya kaskantar da kansa, Allah zai kare shi daga masifu, kuma ya ba
shi sirrin “Ikhlasi” Wato nacewa da son bin hakikar gaskiya a dukkannin al’amuransa na yau da
kullum. Daga wannan mataki ne mutum zai kasance cikin mutane ‘yan kadan wadanda suka
samu yardar Allah tare da kusanci da shi. YAKANAH ita ce kofar da ake bi ta cikinta zuwa wurin da baiwar Allah da rahamar sa suke
muhimmancin YAKANAH ga musulmi kamar kwatankwacin bargo ne a cikin kashi.
YAKANAH tana a matsayin bargo na Ibadah, kuma sauran ayyuka suna a matsayi na kashi.
Bayin Allah wadanda ake kira ‘zahideen’ masu cike da da’a da tsantsenin duniya, tare da
‘nasiqeen’ masu sadaukar da rayuwar su domin bautar Ubangiji, dukkannin su suna ji da
wannan baiwa ta YAKANAH. Bayin Allah masu YAKANAH basa yin maganganu barkatai, basa yin tsegumi ko wata muguwar
magana a game da wani a bayan idanun sa, su kan fadi abin alheri ne a game da shi. Ba sa
shiga sharo ba shanu, kuma zuciyar su fes take. Ta kuma nisanta da miyagun dabi’u, kamar
hargowa da JI DA KAI. Wato kirjin irin wadannan bayin Allah garau yake. Duk maganar da irin wadannan bayin Allah masu YAKANAH suka fadi, ta dace dai-dai da abin
da suka yi, suka kuma yi imani da shi.
Basu da wani abu da za su boye a zuciyar su domin kada wani ya sani, wato basu da wani
mummunan abu a tare dasu.
Bayin Allah ne masu zallar gaskiya da rikon ta, wanda duk ya yi hulda da irin su zai ga cewa
basa fafutukar neman kuskure a kan wani, maimakon haka, a shirye suke wajen neman
kuskure daga wajen su, wato a kan kansu.
Basa yarda su zauna tare da (marada) (masu kawo tsegumi). Don haka ‘yan uwa musulmi mu
yi damara da kokarin kasancewa cikin bayi masu YAKANAH, mu rike addininmu, mu kama
Alqur’anin mu, mu suturce jikinmu, mu tsayar da sallah domin samun dacewa a duniya da
lahira. Kamar jarumar wannan littafi, Allah ya bamu iko amin summa amin. Takori..

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login