Showing 39001 words to 42000 words out of 43214 words
Chapter 14 - YAKANAH! BOOK COMPLETED BY TAKORI KABARA .pdf
wata makociyar Inna Goggo mai gyada. Ba ta shigo gidan ba sai bayan azahar, lokacin
shi da Malam suna kofar gida suna sallah da mutane. Ta zaga ta bayan su ta shiga gidan ta
shige uwar dakin Inna. Ya dawo dakin Inna suna hira, shiru-shiru bai ga Fati ba. Ya ce,
“Wai yarinyar nan Inna gudu na take yi?’
Ta ce, “Ni ina na sanar muku, ai kun fi kusa”.
Ya ce, “Tana ina ne?”
Ta nuna mishi uwar dakin ta da dan alinta, ita kuma ta fita don ta dora sanwar dare.
Tana jin shi zai shigo ta yi linkim a gadon Inna, ita a dole barci take. Ya karaso ya zauna a saitin
kanta yana kallon kyakkyawar fuskarta ta dan hasken tagar Inna da ya ratso, babu wadatar
haske a dakin don haka ya fiddo wayar shi yana haskata sosai.
Ta soma rikide mashi tana komawa Hadiza! Kanshi ya dinga zagayawa jiri ya soma diban shi, a
lokacin da ya soma romancing din ta da fuskar Hadizahh……...
Ta yi wani irin juyi ita a dole barci take, kamin wani dan lokaci al’amura suka rikice musu, tun
tana pretending har al’amarin yafi karfin kawaicinta da juriyar ta. Jin maganar Inna a falo ya sa
ta daddage ta kwaci kanta, jikinta babu inda ba ya rawa saboda firgici da sabon al’amarin da ba
ta taba tsintar kanta a ciki ba. Idanun shi a galabaice ya ce, “Haba Hadizah! Don Allah Hadizahh.....!!”
Wani haushi ya kama Fati, karona farko a rayuwarta da kishin Hadiza ya darsu a ranta, wato ma
da sunan Hadiza yake alakanta ta, sannan ne zai iya auratayya da ita?
Za ta fita ya cafke hannun ta, ta wani irin juyo tana hararar sa. Wai an ce aikin banza, harara a
duhu. Don kuwa bai gani ba.
Shi ma ya juyo kukan Nana da maganar Inna, don haka ya yi saurin sakin hannun ta, ta fita
amma shi bai fito a lokacin ba, sai da ya daidaita kansa tukunna. Sai dai fa shaddar Ghanilla
baka wul duk ta yamutse.
Yana tsaye a falon Alti ta shigo suka gaisa, ya ce,
“Goggo Alti sai ku shirya tafiya zamu yi”.
Ta ce, “To ranka ya dade”.
Fati ta kwakkwabe fuska ta ce,
“Nifa Inna sai gobe zan tafi”.
Inna ta ce, “A’a, ga mijin ki ya zo tun daga wata uwa duniya ai wurin ki ya zo, yana bukatar
kulawar ki, tashi ku tafi idan ya koma sai ku dawo, mu kullum muna maraba daku”.
Ba da son ranta ba ta tattara kayan su suka tafi. Wannan karon ma a baya ta zauna ita da Alti,
duk yaran har Nana suna gaba.
A ranshi ya ce,
“Tunda na rasa Hadiza ai ba abin da ba zan gani ba, ga shi na zama direban Fati ina ji ina
gani…..”.
Har suka isa gida babu wanda ya ce da dan uwansa uffan, don babu fuska a wurin Fati, fushi
take sosai kan biris din da ya yi da ita tsayin shekara guda da doriya.
Sai shi da Munib suke ta hirar su, Alti na mamakin wadannan ma’aurata da ba ta san yaushe za
su saduda su san Annabi ya faku ba. Ba ta san kuma laifin na wane ne a tsakanin su ba.
Suna zuwa gida ta dauko makullin dakin sa ta shiga ta soma gyara, duk da dama a gyare yake,
domin duk bayan sati biyu take shiga ta share ta gyara ta wanke toilet.
Shi kuma da ya ajiye su fita ya yi, bai dawo ba sai karfe goma na dare. Ya yi wanka ya yi
excercise ya zuba pajamas da turaren shi na kullum, amma a yau sai ya samu kansa da karawa
da ‘Boss-Intense’, ya cakuda da ‘far away’. Sannan ya kara da ‘Gio-Gio Armani….’ Ango sosai.
Mai ji da koshin lafiya da kuruciya, wanda Allah yayiwa duk wata ni’ima ta rayuwa. Ya tadda Fati a dakinta, ita ma lokacin ta yi wanka tana busar da gashin ta da hand dryer, cikin
wasu tausasan nighties, masu shara-shara, ya kashe dirayar ya ajiye a gefe, cikin kunnuwan ta
yake rada mata.
“…..Ki yi hakuri mana Fati…..don Allah ba don ni ba”.
Ta ce, “Da aka yi me fa?”
Ya ce, “Rashin kiran ki a waya, ba haka kawai bane ina da hujjoji na”.
Cikin raunin murya ta ce,
“Kana da hujja sosai, hujjar baka damu dani ba, kana kiran kowa ban da ni, ba sai ka yi haka
zan san cewa baka so na ba, lika maka ni aka yi. Tuni na kwana da sanin wannan......” Hawaye
suka balle mata.
Ya juyo ta da sauri suka fuskanci juna, sanyin numfashin su na dukan fuskar kowannen su. Ya
ce,
“Ni na ce da ke bana son ki?”
“Baka fada ba amma ka nuna mini, ka nunawa zuciyata. Tunda har ka iya ka yi shekara baka
nemi jin lafiya ta ba, saboda ni kadai ka tsana a duniya, a kan laifin da ban sani ba”.
Ya yi murmushi sosai ya ce, “Dole sai ta bakin ki zan ji lafiyar ki? Ina ji a bakunan da ba za su yi
min karya ba.
Maganar lika min ke aka yi, sai in ce MADALLAH da wadanda suka lika min ke, yaa ke
ma’abociyar YAKANAH!.
Domin na hadu da alhairori da yawa a tare da auren ki. Ki yi min afuwa Fatima kamar kullum,
ban san ki da kullaci ba, saboda ke na jingine komi dake gabana na zo, kada ki sagar min da
gwiwa, saboda in gyara zaman mu, in gyara kurakurai na.
Na tabbata Hadiza ta tafi;
She is my past…... and you are my present.....!!!”
Haka ya ci gaba da kalallame ta da kalami masu dadi, har ya samu ya karbi abin nan mai
matukar daraja daga gare ta. Ya rungume ta tsantsan yana fadi a ranshi,
“Yaya, (Sa’adatu) ta haifi ‘ya’yan baiwa”.
Albarka da addu’a, hadi da godiya mara iyaka Fati ta samu daga Dr. Saiman har ta gode Allah.
A bisa yanayin daya risketa. Idan aka ce mata wani abu mai kama da MAFARKI to
wannan ranar ce. Ranar da bata taba mafarkin gani cikin mafarkanta ba. It’s a dream that
comes true. Bata jin akwai wani sauran buri da ya rage mata a rayuwa bayan na cikawa da
imani da dorewar wannan ‘indescribable moment’ har karshen rayuwarta.
****
Kwanaki biyar din nan da yayi bai zuwa ko’ina sai barzar amarci, har Fati ta saba, duk da tana
matukar cin kwakwa, tana galabaita matuka da wannan sabuwar rayuwa data samu kanta. To
abin ne an tara shi fal, tsawon shekaru biyu ba kadan.
Albarka kam tana shan ta, ya soma tunanin yadda zai iya komawa ya bar Fati, saboda yadda ta
zamo wani bangare na gangar jikinsa, zuciyar sa da ruhin sa gabadaya, ga shi suna tsaka da
karatu balle ya yi mata visa in ya so yaran a kai su wajen Yaya.
A gobe ne zai tashi zuwa Lagos, daga nan ya bi jirgi mai zuwa Chicago. Fati tana hada mishi
kaya, duk jikinta ya yi sanyi saboda mugun sabon da suka yi cikin kwanaki shidda kacal,
sannan ga wata iri kewa na cin zuciyarta mai wuyar bayyanawa.
Ya fito daga wanka yana tsane kanshi da karamin tawul, jin kansa yake wani sabo, fresh, kamar
yanzu aka bare shi a leda. Tunda ya samu ya sauke al’amuran da suka takurawa zuciyar shi da
lafiyar shi. Inda zai iya maida Fati ciki, da watakila ya yi hakan ya sanya ta cikin ya gudu da ita.
Abin alfahari ce ga duk namijin da Allah ya baiwa, ya gode Allah da bai bi son zuciyar shi ya
bijirewa iyayen shi ba. Ya tabbata da tuni yazo yana nadama. Nadama mara amfani kuwa.
Ta mika mishi wasu kayan barci ‘yan Indonesia marassa nauyi, ta ci gaba da hada sauran. Ashe
hawaye take zubarwa shi bai sani ba, ya sanya kayan barcin, ya zauna a gabanta ya janye
jakar kayan da ta ke hadawa, ya kamo dukkan hannuwanta biyu ya rike cikin nashi.
“Haba Fati! Ai sai ki karya min gwiwa, ku yi shiri ke da Nana ku raka ni har Lagos, sai in sanyo
ku a jirgi ku dawo. In kin yi kuka ke da kike da ababen debe kewa (‘ya’ya) ni kuma in yi ya ya?
Kamar yau ne za ki ga na je na dawo, mai da hawayen nan maza-maza bana son ganin su”.
Ta ja shessheka tana kokarin mai da hawayen, daga nan kuma aka koma aikin lada, mai
gigitarwa.
Karo na farko da Fati ta taka matattakalar jirgi a rayuwarta. A Lagos sun jima suna tsimayen
lokacin tashin jirgi me zuwa Chicago, yana ta tausar ta da kalami masu dadi kamar ba Dr.
Sulaiman ba, da cewa; ta kula da kanta, karatunta, da ‘ya’yanta. Suna daga mishi hannu ita da
Nana ya bi matattakalar jirgin da sauri, ba tareda waiwaye ba, ya tabbata zai yi kewar su.
Karfe biyu na rana nasu jirgin (Bell-View) ya dawo dasu gida (Kano). Malam Habu ya debe su a
Airport.
Tun tana damuwa da rashin Sulaiman har ta saba, ta sanyawa ranta salama, musamman kuma
da yake duk dare suna tare a waya, ta maida hankali kan karatun ta da rainon ‘ya’yan ta.
Shekara kwana ga mai yawan rai, Dr. Sulaiman-Sulaiman Bakori, ya gama course din shi cikin
nasara da shi da sauran likitoci ‘yan uwansa. Aka yi mishi sauyin aiki da karin girma zuwa
babban asibitin koyarwa na Abuja, a lokacin Fati na mataki na uku a jami’a, dauke da tsohon
ciki na haihuwa yau ko gobe.
Zuwa wannan lokacin Fati ta gama mallake komi na Sulaiman, da da’arta, halayen ta da addinin
ta. Ita ce matar shi mafi kusanci da shi, sannan kawar shi abokiyar shawarar shi. A gefe abin so
da kaunar shi.
Iyayen na matukar alfahari da wannan aure da suka hada a bayan ran marigayiya Hadiza,
wadda har gobe, jibi, har gata basu daina yi mata addu’a ba. Kuma tunaninta bai taba gushewa
daga zuciyar kowannensu ba.
Dr. Sulaiman yana Abuja, sai week end yake zuwa musu, sai ko in duk sun samu hutu suma su
ke bin shi Abujan.
Ranar wata litinin kwana daya da tafiyar Sulaiman nakuda ta kama Fati, suka nufi asibiti ita da
Alti, yaran duk suna Karkasara.
Kafin magariba ta haifi sankacecen danta mai kama da Baban shi har farcen kafa. Sai waya Dr.
Surayyah ta yi mishi cewa baby ya iso. Sai ga shi a washegari kamar an jefo shi, ya tadda Fati
da baby a ‘aminity’, sai dai dakin cike yake da ‘yan uwanta. Sai daga nesa yake jifanta da
murmushin
‘bani da abin da zan gode miki’.
Ita ma murmushin take masa da su kadai suka san ma’anar abin su.
Ba da son ranshi ba Yaya ta wuce da ita gida inda za ta yi wanka, don Alti an aiko mata rasuwar
danta a kauyen su Kukawa, don haka za ta tafi a washegari.
Dakin ta na da Yaya ta gyara mata suke wankan, Munib dan kankanba ya kasa sukuni saboda
ya yi kani namiji dan uwan sa. Bini-bini zai ce a ba shi ya dauke shi, ita kuma Fati ba ta gajiya
da mika mishi shi.
Kawarta Fa’iza ta zo mata barka wadda ita ma an yi auren ta tuni, suka wuni sur suna hirar
bayan rabo, don Fati ta zamewa Fa’iza abin sha’awa ganin yadda ta yi kyau ta kara girma,
yanda duk wanda ya dube ta duba daya zai tabbatar tana da kwanciyar hankali a gidanta.
Sabanin ita da kishiya ta sa ta gaba, ta hana ta zaman lafiya. Fati na tausar ta tare da ba ta
shawarwari na gari.
Ranar suna yaro ya ci sunan Malam, wato Ja’afar. Malam ya roke su kar su boye mashi suna su
kira shi da Jafarun shi.
Juma’a yamma lis, Dr. Sulaiman ya iso Kano daga Abuja, kai tsaye gidan surukan sa ya fara
dosa. Bayan motar shi dankare da himilin tsaraba, Yaya ta yi mishi shimfida da sabuwar
tabarma, ta sunto baby da ke bayan ta ta mika mishi.
A lokacin Fati ta fito daga bandaki, ta yi daurin kirji ta rufu da tawul, ta sha dukan ganye, jikin
nan ya kara zama fresh, fatar nan ta kara zama mai taushin gani a ido.
Ta kasan ido ya dube ta, sai ya ga duk ta canza mishi, ta kara zama yarinya danya sharaf. Da
alama ba ta da damuwa, sun barshi da kadaici, sai fama yake da biro da takarda.
Yaya ta shige kitchen ta barsu, ai kamar jira yake ta tashi ya yi ma dakin Fati tsinke. Tana tsane
gashin kanta da tawul ya bude mata dukkan hannuwan sa bayan ya aje babyn a cikin katifar sa.
Ta rufe ido tana dariya, shima ya san bazata iya ba, har a gobe halayenta na kawaici da
alkunya basa canzawa, sai shi ne ya karaso ya rungume ta tsantsan a hankali, yana fada mata
kalaman da suka zama sirri ne a tsakanin su tana ta sakin murmushi. Cikin ranta addu’a take
Allah ya barta da SULAYMAN dinta, ya dorar da rayuwarsu cikin daukaka da soyayya, kamar
yadda ta faro, har zuwa ranar da suka daina numfashi.
*** ***
SHEKARU GOMA SHA BIYAR A GABA!
Taron rantsar da sabbin ministoci da mai girma shugaban kasa President Umaru Musa ‘Yar
Aduwa zai gabatar a yau a hotel din NICON NOGA, har da babban likitan zuciya da kasarmu
Najeriya ke tanka how
da shi, wato Dr. Sulaiman Sulaiman Bakori, wanda aka rantsar a matsayin Ministan Lafiya na
kasa baki daya. Ranar Litinin, ashirin da shida ga watan Maris, na wannan shekarar.
Dr. Fatima Ja’afar, H.O.D Islamic, a jami’ar Abuja, cikakkiyar mace ‘yar kimanin shekaru talatin
da bakwai da haihuwa, uwar ‘ya’ya biyar a halin yanzu, in ka hada da manyan ‘ya’yan ta Munib,
Muniba da Nana Khadija sun zama su takwas kenan.
Tana sanye da bakar abaya kirar Bahrain da mayafinta, hannunsu sakale dana juna suka isa ga
mazaunin su, daukacin Ministocin da ake shirin rantsar wa suna tare da matansu da rakiyar
‘ya’yansu, to haka suma, Muniba, Nana Khadija, da Ja’afar. Ya yin da suka baro Mufida, Mufid
da Ibrahim da dan autan su Abdulhak a gida, cikin kulawaar tsohuwa Alti.
Bayan mai girma shugaban kasa ya rantsar da Ministocinsa, aka zarce da gagarumar walima.
Ba su baro dakin taron ba sai dare, suna kan hanyar isowa gida wayar Munib ta shigo, wanda
ke can kasar ‘Srilanka’ yana karatun harhada magunguna.
Munib Ya ce,
“Daddy kun manta dani, ko waya an fi sati ba wanda ya yi min.
Yanzu nake jin abin alheri a BBC, congratulations Daddy!”
Ya ce, “Kwantar da hankalin ka Munib, zirga-zirga ta hana mu neman ka. Ina mai yi maka
albishir da cewa, muna tafe dukkanin mu cikin satin nan, sai ka tanadar mana better”.
Ya yi ihu ya ce, “Allah Daddy da gaske?”
Fati ta amshe wayar ta ce,
“Amma sai in point din ka na wannan semester ya kai CGPA 4.00, if not, babu wanda zai zo”.
Ya ce, “Wallahi 4.60 ma na samu Mummy”.
Ta ce, “Ah, lallai Babban Yaya ka gama min komai, zuwan kowa ya zama dole, tunda duk muna
cikin hutu”.
Ja’afar ya amshe wayar ya ci gaba da ba shi labarin duk shagulgulan da ake yi a yau. Munib ya
ciji yatsa ya ce,
“Ayya! Na yi missing….”.
Daga nan sai Muniba, ita kuwa Nana ta ce, ba za ta yi magana da shi ba tunda baya yi mata
waya sai budurwar sa kawarta Naina.
Daddy ya harare ta ya ce,
“Bana son sakarci, shi ba shi da wata budurwa dan makaranta ne”.
Ta ce, “Amma yake yi mata waya yake yo mata tsaraba in zai zo?”.
Ya ce, “Ba kanwar shi ba ce? Ke ba ya yi miki?”
Ta ce, “Wallahi Daddy nata ya fi yawa, har da kati an rubuta I LUV YOU”.
Fati ta tintsire da dariya, shi kuma Dr. Sulaiman sai ya rasa ta cewa, yaran zamani sai a barsu,
da wayonsu ake haifar su.
Ya dubi Fati da wani irin sassanyan kallo, “Momin yara, wai da gaske ne Munib yana da
budurwa?”
Ta rausayar da kai ta ce, “Shirmen Nana ne, Naina Bunza, tana da shiga ran kowa sosai ba
Munib kadai ba, suna shiri da Munib sosai sabida kokarinta.”. (Diyar Dr. Surayyah).
Ya ce, “Ba zan yi mamaki ba in son nata yake, ai jin kanshi yake matured (balagagge) kamar
kowa”.
Dariya ta kama Fati, sai da ta murmusa sosai.
Sun isa gida yara kowanne ya kama harkar gabansa, ya cacumi Fati su kai sama ana biyan
bashin soyayya, wadda hidimar kwana biyu ba ta bari ba. Suka ci gaba da amsa sakonnin taya
murna da fatan alheri daga ‘yan uwa da abokan arziki, har tsayin sati daya.
Ranar juma’a jirgin MEA International ya tashi dasu zuwa Srilanka, har filin jirgi Munib yaje ya
taro su, ya dauki Abdulhaq ya rungume suka karasa zuwa makarantar su bayan sun yi booking
din hotel din da za su sauka.
Farin cikin Munib ba sai an fada ba, ya rasa inda zai sa iyayen shi da ‘yan uwan shi. Dr.
Sulaiman ya yi bincike sosai kan karatun shi, ya yaba sosai da hazakar da yaron ke nunawa.
Kwanan su uku suka wuce Saudiyyah suka yi Umarah, sannan suka dawo gida.
Da albashinta da ta ke tari, da kuma taimakon Dr. Sulaiman, Dr. Fatima Ja’afar, ta bude