Showing 27001 words to 30000 words out of 43214 words
Chapter 10 - YAKANAH! BOOK COMPLETED BY TAKORI KABARA .pdf
a ba Jibril ya sha mai". Ya
sake zaro wasu, "Wannan kuma sai a rabawa su Ruma, karshen watan nan zan zo insha Allah
in abin da nake jira ya fito".
Ta ce, "Meye abin da kake jira?"
Ya yi murmushi kadan,
"Sai na zo din dai Inna".
Bayan fitar sa ta shiga dakin Fati, ta tarar da ita ta yi wanka ta sauya kaya, cikin doguwar riga
kirar Omman ruwan makuba, ta makala dan kankanin hijabi fari iya wuyanta, fuskarta sumul
babu ko tabon pimples ko daya, sannan babu wani make-up amma ta yi kyau sosai.
Akwai wata boyayyar kauna da Inna Halima ke yiwa Fati, wadda ta dasu a ranta tun daga
lokacin da ta fara zama da ita daki daya, ta fahimce ta, ta fahimci akidar ta.
A wancan lokacin ta ce a ranta, ina ma ina da wani babban da in aura mishi Fati ko ya samu
tabarrakin da ke tattare da ita, Khalid bai isa aure ba. To ashe dukkan su rabon Sulaiman ne,
haka Allah ya tsara.
Ta zamo daga gadon ta russuna tana gai da Inna, ta kama hannun ta suka zauna a gefen
gadon tare, ta ce,
"Mun kwana lafiya Fatima?" Ta ce, "Lafiya kalau Inna, ya ya gajiyar ku?" Ta ce, "Gajiya ta bi
lafiya Fatima, mu za mu wuce Bakori, sai kuma Allah ya hada mu cikin alherin sa".
Idanun ta suka yi rau-rau kamar za ta yi kuka, Inna ta ce, "A'a, kada mu yi haka da ke, mun yi
waya da Alti tana nan dawowa karshen wannan satin, ba za ki zauna cikin kadaici ba. Sannan
ungo wannan".Ta mika mata kwalin karamar waya kirar Nokia, ta ce "A hade take da caji da
komai har layi an sanya, jiya na aika Jibril mijin Ruma ya siyo, duk wata matsalar ki kada ki
nemi kowa ki neme ni. Sannan kada ki ji shayin gaya min komai wai don ina uwar Sulaiman,
dukkanin ku 'ya’yana ne, baki da wata damuwa?"
Cikin nishin kukan da ke son ya balle ta ce,
"Dama........dama ina so a karbo min Nana ne".
Inna ta yi shiru kamar tana tunanin wani abu, can kuma ta ce, "Ki dai yi hakuri zuwa rana ‘i ta
yau din, ko kin manta ke AMARYA ce?
Ki huta kwana bakwai, ki kula da mijin ki. Rana ita yau za a kawo miki 'ya'yan ki dukkan su.
Allah ya yi muku albarka kan biyayyar da ku kai mana, kuma ya sa 'ya'yan ku su yi muku fiye da
ita.
Kada ki yi wasa da GIRKI Fati, domin shi ne mafi saukin hanyar isa ga zuciyar miji. Na barku
lafiya".
"AMARYA! AMARYA!!"
Fati ta maimaita kalmar Inna. Bayan fitar Innar. Sannan ta koma ta kwanta rub da ciki a kan
katifar ta “I'm not a bride Inna (ni ba amarya ba ce Inna).
Ita amarya cikin farin ciki take, cikin sa take kwana, cikin sa take wayar gari, cike da soyayyar
mijinta. Amma ni yaya na kwana?
Kwana na yi cikin suyar zuciya da tunanin 'yar uwata abar sona, wadda take min soyayyar da
babu mai yi min ita a duniya, in ka cire iyayena.
Bana kin sa shi yake kina, a kan laifin da ban sani ba. Ban san so ba balle in ce bana son sa.
Amma ni meye laifina a kan auren da nima ba so nake ba?
"Kulawar MATA yake nema…..".
Ta tuno furucin karshe na Hadizah. To ga ni na zama matar tasa Yaya Hadiza, wace irin kulawa
kike nufi in ba shi? He is old enough ya kula da kansa, wanka zan mishi ko pampers zan cire
masa? Goyon shi zan yi ko feader zan ba shi? Ban san wacce irin kulawa kike nufi ba.
Ta kai bayan hannu ta shafe hawayen ta, banda GIRKI kamar yadda Inna ta ce, in za a kashe ta
ba ta san wata extra kulawa ta daban da mace ke yiwa miji ba. Sannan ba ta iya shisshigi da
cusa kai a inda ba za ta yi kwarjini ba.
Bayan tafiyar su Inna gidan sai ya yi shiru, babu sauran wani mahaluki in ka dauke Malam Ilu
dake can bakin ‘gate’ yana gadi, an bar ta daga ita sai halinta. Ji ta yi kamar an kawo ta kabarin
ta, ta yi kuka ta yi kuka har ta gode Allah. A karshe ta tattara komi ta mikawa Allah, ta jawo kular
da Inna ta ajiye mata ta debi abinci tana ci. Ai ba ta tashi jin tsoro ba, sai da karfe tara na dare ya yi, Fati ba ta taba kwana a gidan da babu
mutane ba, ta tabbatar ita kadai za ta kwana a wannan katon gida, don tuni ta san Dr. Sulaiman
ya saba aikin kwana.
Jikinta ya soma mazari kamar ana kada mata gangi, ta daddage ta takure a can karshen katifa
ta kudundune cikin bargo tana dakacen ina ma ita ce ta tafi, Hadiza ta zauna, ko babu komai
Hadiza ta fita bukatar rayuwar.
Na farko tana aikin lada, ta hanyar ceton rayuwar mata ‘yan uwanta. Na biyu tana da 'ya'ya
tana kula da tarbiyyar su da rayuwar su, na uku tana da mijin da ke son ta suke rayuwa cikin so
da kaunar juna.
To amma ita fa? Babu sidi babu sadada. Ba ta kai karshen tunanin ta ba ta ji karar fashewar
tangaran a kitchen, wannan ya tabbatar mata ba ita kadai ce a gidan ba, to wane ne? Ta san
dai ba maigidan bane, don shi in ya dawo karfe shida ba ya kara fita sai takwas, ba kuma zai
dawo ba sai past ten sai dai in yana da aikin kwana. Ta ji dan tsoron ya ragu, ko ba komi tana da confidence na cewa akwai mutum cikin gidan ba ita
kadai ba ce. Ta mike ta fito ta nufi kitchen, wanda ba ta zata ba shi din ta gani, ya tara hannu
cikin famfon sink yana wanke jinin da ke bulbula daga hannun sa, ga kuma kwai yana ta kauri a
kan cooker. Ta karasa da sauri ta sauke, ta kashe gass din. Ta dauki tsintsiyar laushi ta soma tattare
fasashshen tangaran din, kafin ta farga ya fice a kitchen din yana ta disar da jini a kan tiles.
A take ta hada wani kwan ta soya masa, ta juye a farantin tangaran ta debi ‘cake’ samosa da
spring roll cikin firji ta dumama a microwave , ta tafasa ruwa nan da nan ta juye a karamin tea
flask ta kwasa ta yo falo don ta bashi.
Ya tada kai da karamin filo yana kwance a tsakiyar kilishi, sanye da fararen riga da wando na
barci marasa nauyi, har yanzu dan yatsansa bulbular da jinni yake, amma bai damu ba, kamar
ba jikinsa ba, ta zo gaban shi ta russuna ta aje mishi, sannan ta sanyaya murya ta ce,
"I'm sorry!".
Bai kalle ta ba, haka bai amsa ba kamar bai san Allah ya yi ruwan tsirar ta a gun ba. Kai
bangaren data ke ma bai kalla ba. Ta mike za ta koma daki cike da tunanin hannun shi da ke ta
kwararar da jini, amma matsayin shi na likita bai yi wani kokari ba ko yaya ne don dakatar da
gudun jinin ba. Ta san da Hadiza tana nan Allah kadai ya san irin gigicewar da za ta yi, sannan za ta sa mishi
magani ne ta daure, sannan ta yi ta jinyar ciwon har sai ya warke.
Hakan ya taba faruwa da ya sharce babban dan yatsan sa garin ferar tuffaha, irin wannan
kulawar kenan Hadiza ke nufi ta yiwa mijinta? Da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa.
Aka ce wargi ma wuri shika samu; ko fuska babu, ba ta son tuno yadda ya yi da fuska kaman
an aiko mishi da manzon mutuwa lokacin da ta shiga kitchen din.
Ba ta kai ga shiga daki ba ya yi mata wata irin tsawa wadda ta gigita ta, ya ce,
"Ke!"
Ta juyo da sauri. Ya ce,
"Zo ki batar min da wannan shirgin naki a nan, na ce da ke ina bukatar taimako ne?"
Jiki na rawa ta dawo ta russuna za ta dauke, ya kama fatar kunnuwan ta da riko mai karfi, ta sa
kuka don azaba. Ya ce,
"Daga yau sai yau kada ki kara shiga shirgina, ko me za ki ji na yi kada ki zo inda nake, tunda
ban neme ki ba. Na yi kama da saurayin ki ne? Be careful ni Yayanki ne, mijin Yayarki, Hadiza.
Idan kin manta in tuna miki. Tun da kin yarda a kawo ki ki yi zaman 'ya'ya ki lalata kuruciyar ki a
banza, to ki yi ta yi. Ranar da kika gaji, ki gaya min in maida ke gida, kina ji na?' Cikin kuka ta daga mishi kai, ya saki kunnen ta ya ce, "To kwashe su a nan tun ban yi ball dasu
ba, kema in babballaki". (Yana nuna wa da hannayen shi irin yadda zai babballa ta din).
Jikinta na kyarma ta kwashe ta yi kitchen dasu, ya ja tsaki "Tsuu…." A ranshi ya ce,
"Kai! Inna da Malam sun takaice ni wallahi, me zan diba a jikin wannan fingi-fingin?" Ya yi ball
da filon da yake kwance ya mike ya nufi (exercise area) din sa.
Fati bata daddara ba, washegari tunda ta tashi da asuba ba ta koma ba, kitchen ta shiga ta
shirya kalacin funkason alkama da miyar agushi. Wanda ta kwaba tun daren jiya. Ta kara da
Quaker oat da plantain soyayya ta aza a ‘master dining’ din shi kamar yadda ta ga Hadiza na yi.
Da gudu ta koma daki ta kulle, yana fitowa zai fita rike da ‘brief case’ ya yi tozali da sabbin
warmers, sai kamshi ke tashi bisa dining din shi. Da gaske yunwa ta gallabe shi, hanjin cikinsa
har rawa yake. Sai dai yana ganin idan ya ci ya zama sakarai tunda ga abin da ya ce da ita jiya,
kuma raini zai gitta. Don haka ya hadiye azababbiyar yunwar shi ya fice. yana shiga AKTH ya nufi gun cin abincin
manyan likitoci na asibitin, can ya yi kalacin sa. Sai dai a bakinsa babu dandano, don Hadiza ta
riga ta sangarta shi da cimar Fati mai dadin da ba ya misaltuwa, ya kuma fi na Goggo Alti
wadda a da yake ganin babu wadda ta kaita iya sarrafa abinci, musamman na Hausawa wanda
ya fi kama mishi ciki kasancewar shi ma'abocin tara yunwa kafin ya yi quenching din ta.
Da ta tabbatar ya fita, ta fito ta bude ma’adanan abincin, babu abin da aka taba. Bata ji haushi
ba, ta tattara ta mikawa Malam Ilu bayan ta dibi iya wanda take ganin za ta iya ci, ta koma daki
ta yi wanka sannan ta zauna cin abinci.
Tana kammalawa wayarta da ta sa a caji ta yi kara, ta amsa cikin kamilalliyar muryar ta, Inna ce.
Suka gaisa, sannan ta mikawa Malam Sulaiman shima suka gaisa.
Ya yi mata addu’a sosai, ya kara da cewa, ta jure duk wani rashin jin dadi da za ta fuskanta
daga mai sunan shi, nature (halittar shi) kenan, fara nuna kiyayya ga abu kamin ya so shi. Da
yardar Allah watarana za ta tashi da riba.
Ranta ya yi fari, zuciyarta ta yi haske, a kalla ta san ta samu surukai na gari da ke son ta. Ta
kara jin karfin gwiwar son ci gaba da kyautatawa Sulaiman, ba don ya yabe ta ko ya so ta ba.
Ita ma ba son na shi take yi ba, sai dai ba za ta iya yin watsi da al’amarin shi kamar yadda ya
bukata ba, saboda alkawarin da ta daukar wa Hadiza, ta tabbata sakayyar ta na wurin Allah. Don haka ta mike ta nufi dakin shi don ganin ko akwai gyararrakin da za ta iya, cikin sa’a rufe
kofar kawai ya yi amma bai sa key ba.
Ta murda ta shiga cikin sallama duk da babu kowa, wannan tarbiyya ce mai kyau sabida
mala’ikun rahma. Dakin babu kintsi, ko ina takardu baja-baja, gado a yamutse, kayan wanki a
toilet fal cikin kwando.
A jikin bed side ta yi tozali da ‘yar uwarta tana murmushi. Ta karasa ta dauki ‘frame’ din hoton
tana shafawa a hankali tana murmushi itama, hawaye fal idanun ta.
Ta maida shi mazaunin shi ta nade hannun riga ta soma gyara komai neatly, ta cire bed sheet
ta canza wani. Ta kunna A.C don dakin ya yi sanyi.
Ta koma toilet ta hau wankin da ya dauke ta har zuwa azahar, ta fito da kayan inda suke
shanya ta shanya, ta wanke bandakin sosai da parazone, sai daukar ido yake, ta jawo kofofin ta
fito ta soma aikin falo wanda babu datti sosai don su Inna sun tsaftace ko ina kamin su tafi.
Zuwa la’asar kayan sun bushe, sai tashin kamshin Dr. Sulaiman suke kamar yanzu aka fesa
turaren gidan (Chris Adams) ba’a sanya su a omo ba.
Ta yi shimfida a falo ta soma goge su da dutsen guga, ta kammala cikin dan lokaci, ta je ta jera
mishi a wardrove ta kunna burner ta turare dakin da bandakin da touch me, sannan ta fita ta
koma dakinta ta yi wanka ta kwanta tana hutawa.
Bai dawo gidan ba sai goma na dare, nan ya soma shakar daddadan kamshin amarcin da gidan
ke yi, ya kara cin karo da sakon Fati a kan dining cikin wasu flasks din asu zabar kyau ba na
dazu ba.
“Wato yarinyar nan ba ta jin magana”.
Ya fadi a zuci.
Ya danna kai dakin shi, kamar ya sume don daddadan kamshin da dakin ke yi, da wata ni’ima ta
musamman dake fita, wanda ya gauraye da rabar split mai sanyaya zuciya da kasalantar da
gangar jiki.
Ya bude wardrove don ya sauya kaya, nan ma ya cimma sakon Fatima Ja’afar Mai-Yadi. Ya
girgiza kai ya ce,
“Na san maganin ki tunda baki da zuciya”.
Washegari ma Fati ta kara yin kalacin kunun tsamiya dan leda, da poncake ta aza dining. Yau
ma da ya gani wucewa yayi yana girgiza kai, cikin ransa yake fadin.
“Lafiya ce ta yi miki yawa kike losing energy din ki a banza!”.
‘Surely’ yana bukatar abincin, amma girman sa da yake tattali a idanun ta ya hana shi. In ya ci
girkin ta ashe tana da amfani cikin gidan kenan, shi kuma so yake ya nuna mata da ita da babu
duk daya. Babu wani amfani da mace za ta yi masa tunda ya rasa wadda yake so, ya jure
rashin Hadiza ma balle rashin cin abincin da yake so? Haka suke ta gangarawa har tsayin sati guda. Ranar lahadi yana gida, Mukhtar ya yi sallama ta
hanyar danna kararrawa.
Ya tashi daga kan computer ya je ya bude, Mukhtar Ja’afar ne rungume da Baby Nanah, Munib
da Muniba na biye da shi, suka rangada da gudu suka rungume mahaifin su.
Shi ma ya rungume su yana bin kowannen su da sumba, idon shi a lumshe. Suka karasa cikin
falon shi da Mukhtar, Mukhtar ya mika mishi Nana, ya karbe ta ya rungume yana sunsunar ta.
Sannan ya tsaya yana kallon ta, kamannin shi da ita har sun yi yawa.
Suka yi musabiha da Mukhtar, yake gaya mishi Inna ce ta yi waya ta ce a kawo su wajen babar
su. “Ina Fatin ne? Ko barci take?”
Cikin dauriya ya ce, “Bari in duba”.
Ta fito daga wanka ke nan tana rufe kofar bandaki, karamin towell ne ta daura daga kirji zuwa
cinyoyin ta, kanta cikin hular wanka, tana jona hand dryer don busar da gashin kanta da ya jike.
Ya turo kofar ya shigo, idanun shi suka yi kyakkyawan gani, shi kadai ya san abin da ya tsirga
daga yatsar kafa zuwa zuciya da kwakwalwar sa, ashe model yarinya ce a cikin HIJABI?
Kallon second biyu ya yi mata ya dauke kansa, sannan ya juya da sauri cikin kakkausar murya
ya ce,
“Mukhtar ke kiran ki”.
Ta zubo doguwar rigar shadda ‘dark-bluesenegalese’ ta dora da matsakaicin hijabi, ta tadda su
a falon.
Ai kuwa su Munib suka yo tsalle suka yo kanta, har suna kokarin kada ita. Itama ta rungume su,
suka soma jero mata tambayoyi.
“Anti Fati, Mummy ba ta dawo ba har yanzu? Ina kika tafi muka daina ganin ki? Nana tana ta
kuka idan bakya nan, don Allah kar ki kara tafiya ki barmu…..”.
Ta ce, “Ba zan kara ba”. Ta kamo hannun Muniba, “Ba inda zan je muna tare kun ji my kids?”
Suka yi murmushi sannan ta karasa ta russuna ta gai da Yayanta, wanda suke ta hirar su shi da
Sulaiman, ta nufi firjin kitchen ta kawo mishi lemon (Donsimon) da gorar ruwan (Eva) mai
rangwamen sanyi.
Mukhtar bai dade ba ya yi musu sallama ya tafi. Bayan ya karbi lambar Fati. Tana so ta karbi
Nana amma tana bisa cinyoyin sa, ta fara kuka don ta dade ba ta sha madara ba.
Dole ya mika mata ita, hannuwan su suka saka kara gogewa dana juna. Wasu irin hannuwa
gareta masu bala’in taushi kamar auduga, wadanda suka tada tsigogin jikinsa. Ita kuma suka
haifar mata da kasala irin wadda ta ji a ranar da hannun ta ya fara shafar nasa.
A hanzarce ya mike, “Oya kids! Muje mu sha (Ice-cream)”.
Suka yi tsalle suka dane kafadun shi, Munib ya ce,
“Amma har da Anti Fati za mu je?”
Ya yi kamar bai ji shi ba, ita dai jakar kayan su ta dauka ta yi ciki da Nana a hannun ta. Ya
sunkuci yaran shi duka biyun a kowanne hannu daya du girmansu, suka yi waje.
Dama tana da tafasasshen ruwa cikin filas a kitchen, nan da nan ta dama madara ta soma
baiwa Nana bayan ta sha iska.
****Kayan cefanen su sun kare, ba ta san ya za tai ta gaya mishi ba, saboda irin yadda yake bi
ya daure