Showing 3001 words to 6000 words out of 81127 words
da buta ya nufi dakin Yana isa qofar yajita gam alamar iya talatu ta rufe Dan dama tasan wlh Zaki bazai bar babanba.
Ganin bingo yayo gurinsa aguje ya nufi qofar fita yatararda an qargameta Yana juyowa bingo na yowar tsalle zan afko masa shima tsallen ya daga yayi gefe yakama katanga zai hau Amma kasancewar dattijanci yasa yakasa Amma Kuma bai fasaba Yana kama katangar yanaji hannunsa ya gwafce Amma bai tsayaba ba wata wata ya dire waje sai cikin kwatar gidan mal idi atake ya miqe Yana dingisawa ya fada gidan mal idi Yana rafka gigitacciyar sallama.
Kallonsa mal idi yayi Yana haskasa da fitila yace"
Lfy mal dattiya?
'dingisawa yayi Yana gyara tsayuwarsa sbd qugunsa daya riqe yace"
Haba mal idi yaza'ayi kabar kwata qofar gida haka ba'a ragewa gashi yanxu naje wucewa na fada
Yanxu Dan Allah idan banibane wani yaji ciwofa?""ya qarasa zancen Yana matse ido cikin duhu sbd tsananin zugi da qafarsa da hannunsa suke masa.
Cikin jimami mal idi yace"
Naji zan gyara kwatar kaje kajida kanka dai yanxu.
Cikin masifa yace"
Au hakama zakace??
To mal datti yanxu kakeson nagyara da daddaren kokuwa?nace zan gyara da safe.
Waiwayen qofa yayi Yana hararar idin cikin duhu Dan so yayi yace zai gyara yanxu saiya tayasa har bingo yabar gidan ga qafarsa da hannunsa sai shegen zugi suke masa,,,kaiii Allah ya tsinewa ubanda yayiwa ruqayya cikin Zaki dandai shikam Zaki yazame masa masifa da balai yanzu dabai guduba yanaji Yana gani bingo zai yayyage masa Kaya da mazaunansa ta yanda saiyafi wata baije yawon maularsaba..
MAMUH.
[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee3_*
Jan qafarsa data riqe yayi Yana 'dingisawa a duduqe ya nufi qofar gidan nasa Yana tura qyauren yaji yabude yasaki wata irin qwafa yana cewa"
Nibansan menayiwa ruqayya ba zataimin wannan sakayyar ta ha'do zuri'a da dangin marasa Imani gashinan 'danta zai kasheni kwanana Basu qareba.
Tunda yaji qofar abude yasan sunkama bingo dinsu shiyasa yashigo Kai tsaye
Itama iya talatu tsabar Rashin 'da'a ga miji sai yanxu daya gama hasarewa zata bude qofar dakinta.
Tsuke fuska yayi ya kwadawa Nadiya Kira tafito tana sunkuyar dakai sbd sanin dazu Bata fitoba daya kirata.
Ciki ciki yayi da qananun idanuwansa yafara zuba mata fadan Rashin arziki kafin yasata ta debo masa ruwa ya wanke jikinsa da duk yabaci da kwata ya dudduqa ya qarasa 'daki Yana sakarwa talatu nata fadan a kaikaice itadai Bata kulasaba sbd gabaki daya ranta har lokacin abace yake.
Haka Suka kwana kowa na hararar Dan uwansa.
Qarfe 6 na safe ta Dora ruwan kunu a babbar tukunya tahau aikin sharar gidan kafin ta bude dakin kaji da akuyoyin iya talatu Suka fito Suka hau walwalarsu a tsakar gidan tana cikin wanke wanke yashigo gidan wuyansa rataye da towel milk da brush tareda Colgate toothpaste.
Kallo daya tayi masa taci gaba da aikinta sbd batada muryar ko gaisuwa shiyasa iyakacinta da kowa ido.
Ruwa yadiba a qaramin plastic bucket yakoma dakinsa ya zura heater ya kunna ya fito qofar gidan inda yake cikeda yaransa wasu na karyawa wasu na wasa makamansu sbd taron yau.
Wata kujerar busashen katakoce dake kafe acikin qasar gurin alamar tariga tashiga qasa bazata taba daukuwaba ga sulbi sbd alamar dadewarta da qarkonta
JJ yayi saurin dauke wuqar daya Dora gurin Zaki ya zauna ya karbar wuqar Yana bin bakin kaifinta da ido yace"
JJ wannan qwamar taka yau cikin takalmina zan sata akwai Wanda dikko keson nayiwa zanen yorbawa agurin taron.
Dariya JJ yayi shida Nanu..
Nanu yace"
Sarki kowaye wannan za'ayiwa na yorbawa tasa taqare tunda sarkine dakansa zai masa aiki.
Wani irin murmushin gayya yayi Wanda ya lotsarda kumatunsa ya 'daga wuqar Yana kallo yace"
Yau uwarsa bacci zatayi tana sauke ajiyar zuciyar kukan dazata yini tanayi.
Dukkaninsu dariya Suka sheqe da ita suna"""Allah ya tarwatsa maqiyanka sarki.
Ruwa Nanu yakawo masa yafara brush dinsa daganan zaune sukuwa nan wasu Suka cigaba da gyara makamansu.
Kallon JJ daya qura masa ido yayi yasaki wani slow murmushi Yana jingina da bayan kujerar yace"
Yaya akayine magajin Zaki.
Cikeda jin dadi jj yashafo tarin sumar kansa da akayiwa kitson cuku bayan anyi dying dinta zuwa baqi da brown yace"
Neyo yau kwarjinin naka bazai Barima ko alh dikko yafika cikawa mutane idoba.
Murmushi yasakeyi Yana shafo gemunsa na tsantsar ta'addancinsa dayake tarawa ya miqe tsaye tareda nufar qofar gida zai shige yace"
Magajin Zaki Kaine kadai kakewa Zaki kwarjini bayan Kai Babu ubanda bazan ketawa rigar mutunci ba ciki kuwa harda tsohon najadun gidan nan.
Shigewa yayi jj yabi bayansa da kallo Yana girmama girman qauna da matsayinda neyo yakedashi arayuwarsa sbd shine yamaidasa mutum yacirosa daga basifa da balain dayafi ta'addanci,
Yazame masa uwa uba tareda cike duk wani gurbi na Dan uwa dayake buqata aduniya shi
yasa zai iya sadaukarwa da neyo rayuwarsa.
Wanka yayo yafito daga bayin tsakar gidan sanyeda threequater wando da qaramin tawul rataye a wuyansa.
Kallo daya Nadiya tayiwa qaqqarfan jikinsa dake bayyanarda qarfinsa,
Wani dogon tabone da sarar Adda yake zane a qirjinsa har zuwa gefen qugunsa Wanda aka ta6a yimasa lokacin daya fara haduwa da JJ sadai Wanda yayi masa sarar yananan yarasa qafafuwansa har abada Dan kuwa Saran rage yaran neyon sukaiwa qafafuwansa Allah yasa yanada kwana agaba.
Wannan tabo shine tabo 'daya dake jikin neyo sbd tsananin tsaron dake taredashi na yaransa Wainda Suka sadaukarda rayukansu akan sarkinsu.
Cikin wani tsinannan army three quarter da baqar riga Mara hannu data bayyanarda qwandarsa dake bawa baba tsoro yafito fuskarnan sanyeda baqin goggles yafito inda qofar gidan take cike dam da duk wani 'dan daba dake qarqashin ikonsa agarin kowane da kalar mugun makaminda ke soke ajikinsa atake guri yadau ihu da kirarin sai sarki.....
Wuqarda JJ ke miqo masa ya karba Yana sokewa cikin takalminsa Yana qarasawa jikin motocinda alh dikko ya Basu Dan hidima
Yana shiga JJ yashiga nan kowa yasamu Suka shiga atake Suka cike golf guda da bus biyu tareda Hilux 'daya Suka wuce cikin wani matsiyacin gudu dayasa mutane kakkaucewa da gudu suna matsarda kayan sana'arsu.
Baba ma Yana tashi yau din yaji qafarsa taqara tsami radadi take masa sosai ya dingisa ya fito tsakar gidan iya talatu dake zaune suna lissafin kudin kunu da Nadiya ta kallesa a dage tana dakatawa daga lissafin tace"
Wannan Kuma wane irin sabon salone kake mana gurgunta?
Qin tankata yayi yakalli Nadiya data sauke Kai Yana hada 'yan biyar biyar guri 'daya yace"
Ke tashi kaimin ruwa bayi nayi wanka inada gurin zuwa.
Tashi tayi ta nufi bokiti
Iya talatu tasake kallonsa tace"
Magana fa nayi kanaji kayi uwar shegiya Dani.
Tsuke fuska yayi Yana sake dingisawa yace"
Talatu wlh wata Rana Saidai kijiki cikin takaba tsundum matuqar ba rabuwa mukayi da Zaki ba,
Wannan masifa tayi yawa
Gabaki daya tsufa neman damqata yakeyi sbd masifar gidan nan,
Ga naki gana 'yayanki gana wannan sarkin dababu rawani sai neman gigita rayuwata yakeyi.
Kallonsa talatun tayi tana girgiza Kai tace"
Ai wlh kwadayinkane da zalamarka ta abin duniya takaimu ga haka,
Qiri qiri katura ruqayya aikatau qasar inyamurai gashinan takawo Mana abinda yaci uwar uban kwadayinmu ta mutu ta barmu da jidalin qaqa nikayi
Gashi kaikuma Allah bai samaka danganar tsayawa inda kakeba shiyasa muke azabtuwa muda tattalin arzikinmu konace tattalin arzikina tunda Kai bayan matacciyar tsohuwar rigar ba abinda ka aje.
Sake tsuke fuska yayi yace"
Wannan tattalin arzikin naki na hainci gwara na mutu da tsohuwar rigar tawa danayi irinta.
Yanxu dai naji wannan Ina kake cewa zakaje da gurguwar qafar?
'dan sake fuska yayi Yana cewa"
Yau wani gagarumin taro za'ayi daya hada kaf dukkanin qusoshin qasa dasukaci Suka tada wuya musamman sbd taron na alh dikko Dilla ne
Dan haka dole naje Dan kuwa yau 'yan maula ma kasuwarsuce
Bazan zauna acinye duniya badaniba koba komai da 'dingisarnan zan qara lankwashewa nafi kowa samu.
Baka daddara ba kenan""tafada tana hararar gefensa.
Yana kama hanyar bayi yace"
Daka mutu gwara kazama biri.
Bayin yashege Bata sake kulasaba Suka cigaba da lissafi sbd kullum ita arayuwarta a lissafi ta qare.
Cikin wani yadin 'dan Madina kalar baqi da siminti yafito da babbar rigarsa ta kullum ya sanyo hularsa datai mugun masa yawa wadda itama gurin maular yasamota.
Wani irin zaku'do kafada yakeyi Yana gyara babbar rigarsa da hularsa qafafunsa da fuskarsa kuwa tsaf sukaji Vaseline sai maiqo sukeyi ya kalli Nadiya dake gefen talatu tana gyaran shinkafa yace Ina takalmin Zaki na jiya daya zuciya ya wurgo?
Kallonsa sukayi atare itada iya talatu Saidai Kuma basuyi mamakiba saboda sanin waye baban.
Miqewa tayi ta nufi inda ta ajiyesu kusada dakinsa ta dauko takawowa baban ya karba Yana cewa"
Wannan dinkin dakikayi bai tsukuba Amma hakan zaiyi maleji.
Sakawa yayi batareda yakalli talatu ba ya baza rigarsa ya wuce sbd ganin baqin ciki talatun ke yimasa.
#MAMUH
[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee9_*
Bayan sati biyu da magana ranar jumaa da yamma Bello yazo qofar gidan tareda abokinsa nuhu dukkaninsu sunyi adonsu cikin yadin wagambari na leda sai qyalli yakeyi na gugar dayaji,
Dattiya dake tareda idi a bakin masallacin layin suna magana Yana hangosu ya washe baki cikin jin dadi sbd yanzu yagama adduar Allah yakawo masa hanyar samun ko dubu 'dayace.
Atareda mal idin Suka fito sarari dansu hangosu aikuwa suna hangosu gurinsu Suka nufo har qasa Suka durqusa Suka gaidasu
Dattiya sai saka musu albarka yakeyi Yana washe baki kafin yayi gaba Yana cewa"
Bismillah ku qaraso ciki aikaima Bello yanzu kazama 'dan gida tunda zaka auri NADIYA.
Wasu ruwa da JJ yasaka abaki Suka mugun dawo masa da qarfi sbd jin maganar qarshe da kawun yafada,
Tari yafara mai qarfi sbd sosai ruwan Suka sarqesa,
Kallon qofar dakin sarki yayi sbd yabarsa Yana bacci yakumasan qila yatashi.
Saurin juyawa yayi yashiga dakin yagansa Yana motsin tashi Kuma ya tabbatarda baijiba.
Juyowa yayi yafito zuciyarsa na jujjuya zancen to kodai shine baiji daidai ba Amma Kuma su bellon yanda suke wani sassauke Kai yatabbarda akwai wani abin.
Kasa zama yayi yakoma dakin yaga yatashi Yana zaune bakin katifa Yana waya cikin basarwa yagane da ale dikko ne yake wayar,
Sake juyawa yayi ya fice duk hankalinsa ba'a kwance ba sbd bayason sarkin ya fito.
Bai gama tunaniba yagansa ya fito fresh skin dinsa mai haske Yana zufa alamar zafine yafito dashi koba komai lokacin wankan maraicensa ne.
Bai kalli qofar gidanba idan su JJ da sauran yaransa suke yayi cikin gida Dan yin wanka da threequater dinsa da armless riga dama sai tawul rataye a wuyansa fuskarnan tamke kamar ko yaushe.
Zainab ce tafara hangosa ta miqe tareda daukar wayarta dake gefenta tareda takalmanta data gama wankewa ta nufi dakinsu tana cewa"
To Bello sai anjima nizan shiga na Dan yi waya.
Cikeda jin dadi bellon yace"
Yauwa zainab to nagode.
Cikin 'daga murya iya talatu tace"
Ke Nadiya bazakiyi sauri kifito bane kinbarsu sun gaji da tsugunawar qafafuwansu harsun fara rawa.
Batareda dattiya yasan da zuwansa ba yace"
Shashanci me kika tsayayi haka za'ayi auren kije kina masa sanyin jiki?
Baice musu qala sai ita daya kalla lokacinda tafito sanyeda sabon hijabi zainab ta sanyo mata Hoda harda janbaki maroon dayayi mata kyau sosai kasancewar Bata taba saka janbaki mai kalaba iyakacinta Vaseline abaki.
Wani mugun kallo ya watsa mata atake ta rikice tana neman juyawa cikin muryarsa mai saka shiga taitayinta yace"
Bani ruwan wanka.
Da sauri nuhu abokin Bello ya miqe Yana cewa"
Sarki Bari na debo maka da kaina ma...
Wani kallo sarkin yayi masa dayashi saurin sakin bokitin...
Gyaran murya dattiya yayi tareda hararar gefen zakin yasaki yaqen Dole yace"
Nuhu Aida kabarshi ta Diba tabashi saiku koma daga soron gidan zaima fi muku nutsuwa can din.
Aikuwa kamar jira suke Suka miqe Suka koma soron gidan Dan dama dukkaninsu a tsarge suke da ganin Zaki na gida sun dauka bayanan.
Aikuwa tana Kai masa ruwan tadawo ta nufi soron gidan tanajin ba dadi cikin ranta sbd ganin wani kallo dayayi mata lokacinda ta aje masa ruwan.
Suna ganinta Bello yahau washe baki sai alokacin Suka saki jiki Suka fara gaisawa itadai tana rakube a gefe.
Nuhu ne ya zaqe yanata jawo musu fira sbd yafi bellon rawar Kai da iyayi shikuwa bellon sai kallonta yake Yana murmushi Dan kuwa shi harya farajin sati biyar dinda Suka rage sun masa nisa.
Qamshin sabulun wankansa na imperial L da ita kadai tasani yasata sake rabewa tareda sunkuyar dakanta
Bello kuwa harda qara Ware idanuwansa da kyau Yana sake mata kallon qurulla
Ga nuhu sai kawo musu zancen soyayya da yanda Bello kesonta yakeyi Yana qarawa.
Tsaf fararen idonsa Suka shiga cikin nata atake jikinta yadau rawa taji hawaye na ciko idanuwanta.
Yana shigowa soron JJ yataso daga qofar gida yashigo
Kallo daya yayiwa Zaki yaga ba fuskar masa magana harya shige dakinsa shikuma yajuyo gurinsu Bello fuska a hade yace"
Kai ku Ware daga nan bamason hayaniya,
Wuqa ya fitar mai shegen kaifi da qyalli ya Dora saitin wandon Bello da jikinsa yafara mazari yace"
Duk Randa nasake ganinka gidan nan saina maka zanen gobirawa anan""yaqarasa fada Yana zungurin wandon da wuqar.
Nuhu tuni yayi muryar sanyi yace"
Zamu kikyaye oga JJ.
Qofa ya nuna musu tuni Suka wuce da sauri wani na tunkudar wani musamman sauran yaran neyon dake cikeda qofar gida duk sun mimmiqe.
Kamar Bello zai fashe da kuka haka ya isa gida ya tube yasaka riga da wandonsa na aiki ya nufi shago Yana fushi Dan kuwa wlh JJ yacucesa daya korosu Dan kuwa so yayi yau ya dasa soyayyarsa a zuciyar nadiyarsa.
JJ kuwa bayan fitarsu mayarda wuqarsa yayi ya juyo gurinta fuskarsa a sake sosai Dan dama dashi kadaine take dadewa Yana Mana fira.
Fira yadinga mata wani lokacin har murmushi takeyi tana rufe fuska sbd rabi duk tsokanarta ne yakeyi da maganar soyayya.
Ahaka har kusan magriba kafin yabarta tashiga gida tana murmushi shikuma yayi waje Dan kuwa yasan sarki baison kusancin kowa ayanxu.
Dattiya dake jiran shigowarta ya qurawa hannunta dake cikin hijabi ido
Cikin sanyi take qarasowa tana murmushinda itama Bata saniba
Ahasale dattiya yace"
Wai meyene haka kike tafiya kamar Mara ruwan jiki???bazaki cire hannunki daga hijabin bane saikace matar alaramma.
Fitarda hannuwanta tayi yaga Babu komai a hannun ya tsuke fuska yace"
Ruwan alwala kikazo dibar musu???
Girgiza Kai tayi tareda masa alamar sun wuce.
Cikin yayi da qananun idanuwansa tareda miqewa ya dauki buta baisake cewa kowa qala ba yashige bayi tun acan ma yayo alwalarsa Yana fitowa butar kawai ya aje ya fice.
A masallaci ma koda yaje kusada Zaki da JJ yasamu sahu nan yasake tsuke fuska musamman dayaga JJ namasa wani ladabi yasan cutarsa zasuyi Saidai ganin fuskar JJ a tamke tam Babu Wasa yasa yasake tsuke tasa shima Dan ko gaisuwa baiso.
Ana gama sallah yafito JJ yabiyo bayansa suna fitowa yaja ya tsaya yace"
Lafiya zaka bini?
Murmushi JJ yayi Yana Sosa Kai cikin 'dan ladabi zaiyi magana kawun ya katsesa da cewa"
Wannan ladabun mai amsheka ba sam,
Kafitomin a zallar yanda kake kamun magana idan ma itace kakeda ita.
To kawu dama inson Nadiya ne shine nakeson sanarda Kai Kuma Nima aurenta nakeson yi......
Wani kallon takaici kawun yamasa kafin cikin bacin Rai yace"
'yar tawa zanbawa magajin dake jiran gado a dabanci,ta'addanci,da Sara Suka?
Wato gani dattiyan mahaukata tunda kaga Ina sake muku fus....
Ido hudu yayida Zaki dake bayansu saiya qarasa maganarsa da cewa"
Kaga jabiru kabarni da wannan maganar nariga nabawasu Bello saura sati biyar bikin ma.
Juyawa JJ yayi sbd jin yanda kawun yayi magana cikin lalama sabanin farko daya fara masa Rashin arziki
saiyaga Zaki yasaki murmushi kenan ganinsa yasa kawun sassauta harshensa.
Ahankali yaqaraso yau kyawunsa duk yasake bayyana sbd jallabiyace yasako ash data fito da farin fatarsa ta asalin Igbo.
Kallon kawu yayi yace"
Muje gida kawu.
niba gida zani ba inada abinyi.
Juyawa sukayi Suka barsa
Sanin akwai abinda ke Shirin faruwa yasa yabiyo bayansu Yana zuba masifarsa suna jinsa sukai banxa dashi.
Har tsakar gida Suka shiga Zaki ya kalli kawun yace"
JJ nason auren waccan yarinyar
Meyasa baza'a bashiba?????
Kallon JJ kawu yayi yace'
Sbd Ni ubanta namata miji.
Kallonsa Zaki yayi yace"
Shikenan????
Eh"kawun yada Kai tsaye sbd shima yau Rashin arzikin yakeji.
Juyawa yayi ya wuce JJ yabi bayansa suka fita.
#MAMUH.
[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee6_*
Sanin Babu Wanda ke ragarwa mahaifiyarsa a gidan yasa Babu Wanda yake ganin girmansa acikinsu saima dai idan Yana gida Babu mai iya yanka mata Rashin arziki sbd tsoron Rashin mutuncinsa Dan kuwa Duk da yake bamai shekaru sosaiba yanada matuqar kwarjini dakuma farin jini saidaifa baida sauqi ko kadan idan katabasa.
Sosai dahiru yamayarda hankali kan karatu Amma Zaki Sam yaqi mayarda hankali ga manyanci yafara kama umman tasa yanzu Bata iya cewa kullum saitaje makaranta taga idan yaje,
Yau zuwa gobe Rashin zuwa ahaka dai yagama primary yashiga js 1
A wannan lokacin ne dattiya ya auro amaryarsa daga wani qauye dasukaje maula gurin wani mai kudin qauyen,
Amaryar tasa yarinyace 'yar kimanin shekara goma Sha Tara shiyasa abin yafi baqantawa iya talatu yarasa wadda zai aura sai yarinyar daya kusa haihuwa.
Tun zahra'u najin wuyar rayuwar gidan harta Saba da taimakon ruqayya Dan kuwa tun satin farko dattiya ya daina siyo mata abinci yace tashiga Sanaa Dan kuwa gidan kowa sanaa yakeyi yaciyar dakansa dukda idan yayo samu yakan siyo mata tsire da nono sushige dakinta su cinye yace ta goge bakinta.
Ahaka shekaru Suka ja harta samu ciki
Lokacin ruqayya ke kulada ita sosai sbd cikin yazo mata da matsaloli gashi na farin tuni ta kumbure tako ina
Sosai ruqayya kejin tausayinta.
Dattiya ma tuni hankalinsa yatashi sbd har cikin ransa yanason zahra'u sbd biyayyarta da yanda ta iya zama acikinsu ta koyi hakuri da duk halayensu.
Zaki madai duk gidan itace abokiyar shirinsa anty zahra'unsa abinda take fada mata ko ummansa baya fada mata sbd karta masa fada ita kuwa anty zahra'u Saidai tayi masa nasiha.
talatu tahaifi mace da sati biyu
Zahra'u ta haihu Saidai tana haihuwa atake Allah yakarbi ranta yabar 'yar jaririyar data Haifa wadda taci suna *_NADIA_* 'yar talatu kuwa aka saka mata suna ZAINAB.
umman Zaki itace taci gaba da rainon Nadiya wadda ta taso cikin maraicin uwa da uba Dan kuwa dattiya tunda zahra'u ta rasu kamar Wanda aka zarewa notin Kai 'daya ya qara zaburewa Sam baya ragawa uban kowa yanzu ga shegen son kudinsa daya qaru
Danma wani lokacin Zaki na shige masa gaba sbd ta'addancin daya fara qarfafa acikinsa.
Nadiya tunda tafara girma umma ruqayya tagano Bata iya magana suka fara yawon asibiti Saidai koyaushe kudine ake tsago musu Wainda Batasan Ina zata samosuba shiyasa suka dangana,
Zaki da Nadiya Sam Babu wata jituwa sbd Sam bayason iskanci da raini bare wata banzar shagwaba wadda umman ke shagwabata duk da haka alqawrine ya dauka da yardar Allah shine zai nemowa nadiyar lafiya kowace irin qasace tunda ummansa naso.
Ahankali shekaru suka shude Nadiya nada shekara goma Sha biyu ummansu ta rasu tabarta cikin maraici Dan kuwa tuni rayuwar gidan tafara mata tsanani duk da ba duka ba zagi Saidai fa rayuwar gidan wata