Showing 6001 words to 9000 words out of 81127 words
juyayyar rayuwace ta kowa da kalar halinsa da dabiarsa,
Makaranta ma tunda tagama js 3 sai karatun ya tsaya kasancewar Bata mgn gashi batada Wanda ke janta a jiki da kulawa bare tasamu qwarin gwiwar yin karatun.
*_SARKI ZAKI NEYO_* yazama riqaqqen sarkin yan daba da Babu kamarsa a yankin Dan kuwa kowa na tsoronsa da shakkarsa,
Babu ubanda yake tsoro sbd girman mulkin dayake bazawa a dabanci gashi manya sun daure masa gindi ko hukuma Bata tabasa,
Daqyar ya hada diploma wadda itama rabi zuwa rabi Rashin zuwa,
Shahararren mai kudi DIKKO DILLA dake zaune a qasar south Africa da matarsa 'daya da 'yayansa biyu mace da namiji, yadawo qasar Nigeria sbd wani boyayyan burinsa dayakeson cikawa akan wasu takardu dayafi shekaru goma Sha takwas Yana so Saidai bazai samesuba Saida jajirtaccen mara tsoro wato Zaki Wanda ya dade Yana bibiyarsa sbd labarinsa da aka kawo masa akan izzarsa da tarin mulkin dayake bazawa a troway yakuma tabbarda shine kadai zai iya samo masasu shiyasa yajaza ajiki tun dawowarsa Nigeria yazamto shine babban yaronsa Wanda duniya ta shaidar Dan kuwa yafi yarda dashi akan 'dansa dayake kusan sa'anni da zakin kokuma ma ya girmi zakin.
Zaki shine yasan dukkanin wani sirri na dikko na dukkanin gurbatacciyar sana'arsa da dukiyarsa,
Duk wani aiki dikko baya shawara da kowa sai amintaccensa Zaki Dan kuwa ba laifi Yana matuqar qaunar Zaki duk da shima wani lokacin Zaki baya ragar masa Kuma shima ba'a taba Wanda yaji Yana shakka da fargababa kamar Zaki Dan kuwa Zaki shine yaronsa Amma shine yake shakkar Zaki ba zakine yake shakkarsaba.
Hakan yasa *_AMAAN DILLA_* da mahaifiyarsa *_MRS DILLA_* tsananin kishi da tsanar zaki wanda sukaci alwashin nakasta rayuwarsa ta yanda har abada za'a manta da sunan zaki atarihi.
Zaki tun bayan rasuwar ummansa Babu Wanda yake qauna samada Nadiya saidai Bata gabansa har mantawa yakeyi da ita musamman dayaga irin rayuwar kadaici da maraicin datakeyi a cikin gidan idan bai dauke idanuwansa akansu ba zai raba dukkanin yan gidan da wasu sassa na jikinsu ne kawai shiyasa ya tattarasu ya watsar,
JABIR shine mutum na biyu da Zaki yake tsananin qauna aryuwarsa sbd tsintosa dayayi adaidai lokacinda dikko Dilla yasa aka kashe masa iyaye shima aka biyosa akashesa shine ya kubutar dashi duk da shima baisan dikkone yasa aka kashe iayayen jabir ba,
Abin yaso taba qwaqwalwar jabir sosai Dan har tabin hankali yayi tsawon lokaci Zaki na kula dashi agidan
Kosu baba dattiya da iya talatu sunci wuyar ciwonsa sbd yanda yake hauka tuburan
Haka Zaki yayita wahala dashi harya warke yazama babban yaronsa shima duk da ba wata tazarar shekarune a tsakaninsu ba,
Zakine ya gabatarwada dukkanin yaransa na kusa Dana nesa jabir amatsayin JJ baban yaronsa wato magajinsa.
JJ ayanzu duniya baida kamar Zaki Wanda yakejinsa tamkar jininsa Dan zai iya bada rayuwarsa akan zaki.,
Lurada abinda Zaki yafiso duk duniya yasa baida abin qauna kamar Nadiya,
koyaushe shine mai tattali da bawa Nadiya kulawa duk da Zaki ko ajikinsa Saidai Yana fada masa bayason kowa nashiga shaanin cikin gidan.
Dattiya da talatu kuwa tuni Zaki yazamar musu uban Dole Dan kuwa cin uban kowa yakeyi a gidan shiyasa ba'a masa ganganci,
Shikuwa dattiya Rashin danganarsa kesa Yana shiga huruminsa
Shikuwa yasa adaidata masa shi.
Zainab Sam Bata jin magana akwaita dason rayuwar qyale qyale Wanda yasa kullum take cikin kwashe kwashen qawaye da samari Wanda koda Gigi basa zuwa qofar gidan fira sbd hurumin zakine Saidai su hadu wani wajen,
Zakine kawai ko sunansa taji take shiga taitayinta sbd tsoronsa sanin baya wasa yanzu ne zai sauya mata kamanni hardai idan yaji tanayin Rashin kunya cikin gida.
Dahiru dai malamin makarantar secondary ta kwana ta maza a wata local government shiyasa Sam baya zama acan yake zaune staff quarters.
**********
Babban gurin taron na stadium yacika maqil da manyan qusoshin qasa shiyasa securities sukai yawa agurin ga yan jaridu da masu tv stations sai dauka sukeyi ana cikin haka shugaban taro dikko Dilla ya iso da babban yaronsa Zaki tareda securities nan aka dinga daukarsu hoto harsuka shigo gurin nan aka fara gabatarda taron.
Ana cikin yi Zaki yafito JJ na gefensa tareda wasu daga cikin manyan yaransa wato su nano.
Kallon mabarata da 'yan maula dake jere cikin uwar Rana yayi zai gumi suke hadawa idanuwansa suka sauka kan kawunsa dattiya da mal idi sai gumi sukeyi suna qyallin Vaseline Sam hankalinsu naga qofa suga wani babba yafito sufara shiyasa Basu lura dashiba.
ya daure fuska tareda kallon qafafuwan kawun dake nade kamar gurgu alamar yau qaryar qurgunta zaiyi.
Kallon JJ yayi masa alama da ido man take JJ yasaki murmushi suka koma ciki.
#MAMUH
[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee8_*
'Dagata yayi cak tana buge buge yakwantarda ita qasa tareda danneta Yana neman wuyar rigarta inda zai zura hannunsa.,
Sake lalubar kofin silverta tayi hankalinta a matuqar tashe ganin rabata da mutuncinta zaiyi Dan kuwa tuni ya farka rigarta dataqi Bari hannunsa yahau kan qirjinta da kyau.
Wani irin kuka takeyi mai qarfi Saidai ba sauti,
Hannunta ne ya sauka akan kofinta ta wuwuri kofin ta jefa saitin qofa da qarfi gashi qofar itama langa langa ce.
Sautin qarar sai akan kunnen Zaki sbd hakanan yau yakasa bacci Wanda JJ ma ganin hakan yakasa bacci.
Dattiya ma yaji ya miqe yataso da fitilarsa Yana fitowa tsakiyar gidan gabansa yayi mummunan faduwa jin motsi mai qarfi Yana fitowa dakin nadiyar.
Sbd tashin hankali sakin fitilarsa yayi ya banka dakin da qarfi Yana kiran sunanta hankali tashe.
ba zato yaji mugun bugu a bakinsa a gigice ya dago cikin duhun ya riqo hannun Nadiya Yana qoqarin qwaceta ban qaton ya haushi da bugu.
Tun lokacinda kawun yakira sunan Nadia ya rufe idanuwansa ahankali sbd jin jikinsa nafara rawa.
JJ ne yayi saurin miqewa daga kwance yadauki fitila da wata sharbebiyar kakkaifar Adda yafito ya nufi tsakar gidan.
Bayan fitars JJ sake rintse ido yayi wannan karon numfashinsa yaji Yana shaqewa kamar mai asthma.
JJ na isa yaga abinda ke faruwa nadiyarma kamar ta suma ga kawun yariqeta yaqi sakarwa shegen shikuwa dukan hannun kawun yakeyi Yana janta.
Cikin tsananin tashin hankali da baqin ciki jj yakaiwa kb din wani mugun naushi a fuska Saida yasaki wani razanannen ihun daya tayarda sauran mutanen gidan duk Suka fito.
Sunan Nadia da kawun yasake Kira da qarfi yasa iya talatu kallon kayanta dasuke yage tafara salati tana tsinewa kb.
Shaqosa JJ yayi a fusace ya daga hannu zai Kai masa mugun duka kb din ya daga hannu zai tare sai ganin hannun sukayi a qasa jini na wani irin tsirtawa wani guntun fitsari iya talatu tasaki zainab kuwa gabaki daya tasaki nata fitsarin sbd Basu taba ganin wannan tashin hankalin ba.
Dukkaninsu juyowa sukayi sukaga Zaki riqeda addar da JJ ya ajiye.
Atake kb yafadi Yana ihu da qarfi sbd ganin hannunsa a qasa ga Zaki ya sare,
JJ ne kawai baiji tsoron ganin jini da abinda Zaki yayiba tunda sun Saba gani aikinsu ne,
Shaqo kb din yayi Zaki ya hanasa tareda jawo kb ko gani bayayi sbd tsananin halinda yake ciki yau idan bai raba kb da duniyaba bayajin abinda yakeji zai fada masa,
Rintse ido yayi ya hangota kwance some jikin kawu kayanta dake babbarke ne suke neman haukata qwaqwalwarsa.
Wata sharbebiyar wuqa ya fizgo a jikin jj ya yaga wandon kb din da ita ya daga da qarfi zai sare masa gabansa JJ dasu nano dasuka firfito daga dakin qofar gidan Suka riqesa suna Allah ya huci zuciyarka sarki Amma karka masa wannan hukuncin,
Cikin hasala jj yace"
Neyo kabarmu dashi,
Yataba hurumin da ba'a tabawa zamuji dashi.
Wurgi yayi da wuqar Yana yamutsa kansa jin yake kamar ya cinnawa kansa wuta sbd zafin da zuciyarsa keyi,
Jiyake abinda ya tokare masa a qirji kamar zai kashesha,
Da qarfi yace"
Ku sauyamin kamanninsa yanda ko uwar data haifesa koya warke bazata ganesa ba,
Ku karya sauran dayan hannunsa daya taba suturar dake jikinta,
Ku karyamin qafafunsa,
Ku kasheminshi,
Ruwa JJ yayi saurin kawo masa yayi wurgi dasu Yana cewa"
Zuciyata zata saukane idan nagansa kwance cikin mummunan yanayi.
Aikuwa wani irin duka su JJ dasu Nanu sukai masa duk da dare ne atake gurin yacika Dole aka Kira police ganin zasu kashesa.
Koda police sukazo kb kawai Suka dauka sukai asibiti dashi tareda gundulen hannunsa a leda.
Cikin gidan kuwa ruwa zainab ta debo qafafunta da hannuwata na rawa taba baban ya kelayawa Nadia
Atake ta farfado a firgice cikin tsananin tsoro jikinta na rawa
Zainab tayi saurin rungumeta tana hawaye itama sbd kaf dinsu gidan suna tsananin son junansu Saidai halayensu ne kesa ka dauka basason junansu.
Baban kuwa miqewa yayi yace suje dakin zainab su kwanta tare.
A Daren Kam kowa bai koma bacciba musamman Zaki da dattiya daya qara gama yanke shawarar aurar da ita cikin qanqanin lokaci.
Washe gari duk wasu yaran Zaki Saida sukai baqin cikin wannan Rana sbd sarki dai ranar ko qofar gida bai fitoba ataqaice dai Saida ale dikko ya Aiko masa da babban likitansa ya dubasa sbd ko miqewa tsaye daidai ciwon kirji mai qarfi yaqi Bari yayi.
Kb Kuwa ba'a mutuba Amma anci wuya Dan kuwa gabaki daya a kumbure yake ga jini daya zubar sosai sai qara masa akeyi gashidai yanxu baida hannu daya Kuma hukuma nagani tayi biris yanajin sauki aka sallamesa yayi alwashin saiya Rama abinda sarki yayi masa shida yaransa Dan kuwa shima baya tafiya.
Bayan kwana biyu duk tasake zama wata iri da ita sbd sanyi data qarayi sosai gabaki daya rayuwarta mutum biyune rayuwarta,BABANTA da YAYA ZAKI tunda abin nan yafaru Zaki ya daukewa 'yan gidan wuta gabaki daya sai shakkarsa taqara shigarsu sai kaffa kaffa sukeyi musamman ma ita.
Baba kuwa tuni yasamu mal zailani da maganar auren da 'dansa bello yace yanaso na Nadia.
Babu wani dogon qunbiya qunbiya Suka gama maganarsu tunda kowa yasan kowa tare sukai samartakarsu.
Bayan mal zailani yayi magana da bello kan maganar shima yace a shirye yake asa Rana kawai.
Har gida mal zailani yasamu dattiya shida wani yayansa da abokinsa
Shima dattiya yakirawo mal idi
Suka sake magana akai neman aure Suka bada kudin nema dubu goma.
Washe baki dattiya yayi ganin 'yan dubu dubu Yana cewa aransa""Ankwana biyu baa haduba"
Karba sukayi aka yanke ranar aure wata biyu masu zuwa insha Allah.
Suna tafiya dattiya yasake qirga kudin Yana murmushi yaciro dubu biyu ya miqawa mal idi ya zuba saura aljihu Suka fita.
Lokacinda ya sanarda iya talatu maganar kallonsa tayi cikeda haushi tace"
Kai yanxu Dan Allah shine ka karbi kudin gaisuwar zuqeqiyar yarinya kamar Nadia a dubu goma??
Kunna radio dinsa yayi Yana kamo gidan fm yace"
Eh ko dubu biyar ne dai na bayar
Lokacinda wani shegen zai sake shigowa ya asarani kinacan kina baccin wahala ko dubu 'daya bazatayiba.
Tsuke fuska tayi tana hararar qafafunsa dasukai 'yar banzar qura tace"
To nidai karka doramin wainnan qafafun masu dau'da a tabarmar sallah ta tunda Nima koda nahada kudin gumina nasiyeta kanacan kana yawon ta zubar a gari.
A kufule ya kalleta yace"
To ko natashi ma akai gaba daya?
Talatu kin renani waike bakisan darajar miji bane koyaushe bakimin 'daa sai gasa baqaqen maganganu.
Tabe baki tayi tana cigaba da hada garin matarta data gama zubawa 'yar fulawa.
Miqewa yayi Yana masifa ya zari babbar rigarsa ya fice koba komai yau basuje sana'ar ba gwara ko ita yaje yasamo ko dubu biyu ko 'daya yamaga ana taro acan gaba.
Da harara tabi bayansa tana cewa"
Kadaiji dashi
Lokacinda jarababben mai mulkin gidannan zaiji ka karbi kudin gaisuwar nan ai lokacin ne zanbaka tabarmar jinyar kanka.
Zainab dake fitowa cikin daki tasaki dariya sbd tana jinsu sbd itama tasan daga baban har bellon na ruwa tsundum.
NADIA kuwa yitayi kamar batasan abinda ke faruwa tacigaba da sha'ainin rayuwarta.
#MAMUH.
[2/21, 3:43 PM] Ummuanwar😍: *_Mamuhgee7_*
Ana tashi taron nan maroqa Suka hau aikinsu aka dinga musu barin kudi suna godia
Kawu Dattiya ji yayi yau ranar datafi kowace Rana sa'a ce Dan kuwa tuni kudinsa Suka Kai dubu takwas ya tura aljihun wandonsa tareda qara gyara zama yayi Yana cewa"
To Ashe musakan nan sunfimu samun kudi aikuwa yau Nima cikinku zan lafe tunda qiris yarage tantirin can bai maidani musakinba.
Sake lanqwashe qafa yayi kamar musakin gaske yayi kalar tausayi.
Saida duk baqi Suka watse kafin ale dikko yafito tareda Zaki sake da Amaan 'dansa.
Kallon tarin mabaratan yayi ransa na baci shi arayuwarsa ya tsani mabaratan nan da son banza yayi musu yawa wato su sai mutum ya Nemo zuso karban banxa.
Yanayin yanda ya dauke Kai daga kallonsu yasa ran Zaki ya baci sbd duk lalacewar kawunsa Babu Wanda ya isa ya wulaqanta masashi,
Shi shikadai ne yakeda ikon masa Abu bawai Kuma Dan Baya sonsaba saidan yanasone yaji wuya ya canxa wata sana'ar.
Kallonsu yayi yakalli security yace"
A sallamesu abar musakai su kadai za'ayiwa sadaka.
Idi najin haka yayi saurin nade qafarsa shima Dan kuwa baza'ai babushiba,
Kallon baqin ciki dattiya yayi masa Yana hadiye yawun fargaba sbd yasan Dole akwai balainda yake Shirin qulla musu shine shikuma tsohon banxan nan idi ya nade baisan balain dake cikeda kallondq zaki ke musuba.
Aikuwa duk aka watse aka barsu su tara musakai nan dikko ya kalli Zaki yace"
Lion yaya hakane?
Batareda yakalli dikkon ba yace"
Ale sadaka zakayi musu ta musamman sbd banaso su manta wannan ranar.
Ba musu ale dikko yafito da maqudan kudi bunch guda na dubu 'daya 'daya
Atake Suka hau zare idanuwa kamar sunga aljanna idi har wani qaiqayi hannuwansa ke masa.
Kallon JJ Zaki yayi atake ya dauko wani buhu Dan qarami yafara walwalewa.
Zaki na kallonsu ya karbi rafar kudin ya miqawa nano yace"
Ka Raba musu ita Amma bayan munga waye musakin gaske.
JJ kuwa Yana gama warware buhun ya cillo musu abunda ke ciki.,
Wani sharbeben baqin dogon maciji ne aciki yafado tsakiyarsu..,
Wani irin juyin waina dattiya yayi tareda miqewa yayi gabas aguje rigarsa na cika da isa yana dingisa qafarsa datai tsami sbd lanqwasawa,
Idi kuwa duk abinda yasamu yayi watsi dashi yanka a guje hularsa datai masa yawa tana faduwa,
Sauranma atake Suka kwasa aguje suna tsinewa Zaki.
Mutum biyune musakan gaske Wainda aka Bari Basu iya gudu su dinma qoqarin guduwar sukeyi da Jan gindi.
Kallonsu Zaki yayi ya girgiza Kai kafin ya kalli Nanu dake dariya yace raba musu rabonsu ne sukadai.
JJ kuwa mataccen macijin ya dauka Wanda bamai cewa matacce ne sbd bada jimawaba yaransa Suka kashesa agurin taron.
Mota Suka nufa dikko na 'yar dariyar jin dadin abinda Zaki yayi musu.
Bude masa mota drivern sa yayi yashiga Suka wuce Yana jaddadawa Zaki gobe qarfe goma na safe zasuje wani guri.
Bayan tafiyarsa shima shida yaransa Suka shiga motocinsu Suka bar gurin.
Dattiya yariga idi isowa gida duk da qafarsa tuni tadau wani irin zogi musamman yanda ta kumbura tu da yashigo gida ya zauna qofar dakinsa kan shimfidar tabarma yakalli talatu dataqi tambayarsa ya akayi yadawo yau ko sauran takalmin Babu a qafarsa.
Numfashin 6acin Rai yasauke cikeda baqin ciki yace"
Wlh yau nayi baqin ciki da Dana sanin Rashin tambayar ruqayya waye uban wannan nan yaron harta rasu tabarmin ajalina.,
Sai alokacin talatu takallesa tana zubawa tsiminta ruwan magananin 'dan kanoma sbd yayi Dan bauri anfi cewa yaji magani tace"
Idan dai qashi nada tauri to kare baida aikin komai,
Bazaka kama kankaba Zaki bazai daina wahalarda rayuwarkaba.
Qwafa yayi yace"
Kinkuwa San yau Wai Ni Zaki zai jefowa baqin kumurcin maciji dabanda qafafu yau dakin shiga taqaba.,
Wlh cikin tsananin rashin Imani yasa JJ ya jefo manashi
Ni yanxuma idi nakeji idan ba akansa iftila'in yafada ba.
Sallamar idi ce ta katsesa fuskarnan murtuk Babu alamar rahama sbd shi komaima nasa ya zubar acan har 'yan dubunsa bakwai da 'dari hudu duk ya watsar wannan wace irin masifa ce,
Cikin tsananin zafin Rai da baqin ciki yace"
Allah ya tsinewa ubanda yayiwa ruqayya cikin balai.
Amin dattiya da iya talatu Suka fada atare sbd tsananin matsen dasuke da zakin.
Dattiya dake jin tsananin zugin qafarsa data fara kumburi yace"
Allah yaji qanki ruqayya ya saka Miki da duk Wanda yayi Miki wannan ta'asar Dan kuwa yaci amanar marainiya baiwar Allah ta tafi ta huta da ganin wannan balai.......
Shigowar JJ ce tasa dukkaninsu yin tsit suna matse fuska da bacin rai sbd sunsan Zaki na kusa tunda sukaga JJ.
Nadiya dake zaune gefen talatu tana mata aiki tana dago Kai Yana shigowa
Kyakkyawar fuskarnan tasa a tamke Saidai wani sirrin kwarjininsa dake Hana ayi masa kallon qwaf yasa tayi qasa da kanta kafin yaqarasa sauke takaicinsu baba akanta.
Dakinsa yashiga daidai shigowar zainab da hijabin data aro gurin anty samira amaryar baba idi sbd sanin Yaya Zaki nanan tunda taga bataliyarsa a qofar gidan.
Tashi baba idin yayi Yana sake daure fuska Yana Harare Harare ya fice Yana cewa"
Allah dai baya bacci tunda gumi akace dai mutum ya hada gurin neman halas Kuma mun hada Amma gashinan.
Kawu Dattiya najinsa yaqiyin magana sbd kar ajisu Dan shidai yagaji da wannan masifar daga yanxu zai ringa iya yinsa gurin raba hanyarsa da Zaki Dan yagama sani yanxu Kam tsaf Zaki zai iya ganin bayansa,
Shi wlh dama yasani yabari neyo ya auri ruqayya dabataje ta samo musu wannan iftila'in ba Dan kuwa gwara ta'addancin neyo so ba adadi akan na Zaki tunda gashinan sbd harta haihu ta rasu Bata daina qaunar neyoba tunda Zaki ma aliyu haidar neyo tasaka masa gashinan sunan neyon yabisa.
Tashi Nadiya tayi sum sum ta dauki bokiti ta Debi ruwa da tsintsiya ta nufi bayi tafara wankewa sanin duk yafita yashawo Rana idan yadawo Yana wanka.
Tana gama wankewa tafito kenan shikuma zai shiga baisan da itaba
Itama batasan dashiba sukai karo tayi saurin yin baya zata fadi
Da hanu daya yariqo hannunta a tsorace ta dago Saidai takasa kallon fuskarsa kafin tasake dagowa ya jehota waje tareda rufo bayin.
Dattiya da tun dazu ya miqe zuciyarsa na tsalle ganin Zaki zai shiga bayi 'yarsa na ciki Yana ganin anjehota waje yasake ajiyar zuciya sbd Rashin madafa sai kawai yahau Nadia da fadan Rashin dalili,
A zuciyarsa kuwa sauqi yakeji da duk iskancin Zaki baya ko kallon mata bare nemansu da lalata sbd 'yar Nadiarsa yake gudun a lalata tunda ita zainab uwarta ta daure mata gindi tana yawonta bai saniba ko tagama lalacewar,
Ita kuwa Nadia ko maqure masa ita akayi za'ayi lalata da ita batada muryar idon neman ceto,
Kai shidaima gwara yayi mata aure ya huta ta huta itama Dan haka zai bama 'dan gidan mal zailani dayake sana'ar gyaran su fanka dama tunda yace Yana sonta.
NADIA kyakkyawar black beauty ce Saidai ba baqa bace sosai Sam batada wani jiki sosai hakama tsawonta daidai misali Saidai kusan dukkaninta daka ganta kasan mahaifiyarta ta 'dauko Saidai 'dan duhun fatar na mahaifintane ta dauko.
Sanyin haline da ita shiyasa ayukanta Suka zama suma a sanyaye takeyinsu.
Juyi tayi kan shimfidarta tareda