Showing 3001 words to 6000 words out of 31587 words

Chapter 2 - DUBAI PART 2 HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

20 Nov 2025

546

maqale a hannun Habeey ta cafki
wuyanta tana jijjigata tana fadin “wlh baki isa ki zama surukata ba tsinanniya matsiyataciya yar
tasha karuw..." Wani kira dayakeyi Mata tare da finciketa daga jikin Habeey dinne ya dawo da
ita hayyacinta ta saki wuyan habeey da sauri taja baya. Tana kallon yanda take fitar da numfashi a wahalce ga wata kumfa da take fitarwa a bakinta tayi
saurin juyawa zata fice governor Waziri ya kira sunanta tare da cewa “kafin ki fita kisan da
saninki indai yar mutane fa mutu sanadin taaddancinki wlh sai kinyi zaman jarun"




Wata ajiyar numfashi Habeey tayi komai nata ya daina motsawa Taheer ya dira gabanta ta
dagota yana danna qirjinta yana Kiran sunanta Dad ya miqe da sauri ya fita yaje ya taho da
likitan itakuwa Mom tayi wuqi² cikin tsoro da tashin hankali Granny kuwa mamakin lamarin Mom
ne ya hanata cewa komai sai dauke Safnah da tayi tasata a sabon gadon da ubanta ya siyo
mata.
Rufuwa likitocin sukayi akan Habeey harda Taheer sun bata sama da awanni uku sannan suka
samu numfashin ya daidaita suka fito zuwa lkcn Mom ta sace jikinta tabar asibitin ta wucce
gidan yayarta tana kuka take zayyane mata komai har auren Saudat yar qanin Dad Sahabi data
nema masa tasa Saudat ta dawo daga England kawai saboda ta hadata da Taheer amma abin
yana neman gagara.



Yanda take kuka yasa Hajiya Ummah yayarta dariya tace “kece uwa kece kike da wuqa kike da
nama fah yanzu dai shawara daya itace tunda ya kafe saiya auri yarinyar nan ki qyaleshi ya
aureta din kodan rufuwar asirinku game da wannan yar kafin fatiha din ayi auren cikin sirri ta
tare ta yanda babu Wanda zaisan ba aure aka haifeta" Girgiza kai tayi tace “aikin gama ya riga ya gama Ummah sirrin dan siyasa baya buya ni kaina
baa gurin Taheer naji haihuwar ba kirana akayi da baquwar number aka fadamin karuwar dana
ta haihu a asibiti kaza har lambar dakin aka turomin"




Shiru sukayi na wani dogon lkc sannan Ummah ta magantu da cewa “shawara ta biyu kije ki
hada baki da likitan ayiwa jaririyar allurar guba ta mutu kowa ya huta..." Da sauri Mom ta kalli
Ummah tace “kuma nayi kisa Ummah aa bazan iya ba nikam inajin tsoro na lura daga Granny
har Dad hankalinsu yana kan wannan jaririyar" Murmushin takaici Ummah tayi tace “shikenan kije zanyi tunanin mafita kafin a sallamesu daga

asibiti cikin wata biyun da kukasa na bikinsa da Saudat dole ne a mantar dashi tunanin wannan
karuwar yarinyar idan ba hakaba tabbas da matsala don zama ku iya daura masa auren ya saki
matar" miqewa Mom tayi tace “dakuwa na tsine masa ya qarasa lalacewa"





Da haka ta fice a gdan driventa yajata suka fice suka nufi government house suna tsayawa ta
fito ta shiga gdan bangaren yammatan nata ta shiga ta tarar dasu sun rufu akan Saudat sunata
rarrashinta itakuma sai kuka takeyi, salati Mom tayi ta shiga cikin dakin tana tambayarsu
menene. Kuka bai bari Saudat tayi bayani ba sai shassheqa da takeyi Bushirah tabe baki tayi ta shige
bathroom Kubrah ta dago tace “Yaya Taheer ne ya dawo ya shiga dakinsa yana neman wani
abu kawai ita kuma sai tabisa dakin munyi qoqarin hanata taqi hanuwa, bamusan me tace masa
ba kawai sai gani mukayi ya fito da ita a hannunsa ya jefar da ita a parlour yana jibgarta kamar
Allah ya aikosa yana gama dukanta ya fice ya hau motarsa yabar gdan itakuma munyi munyi da
ita ta fada mana me tace masa taqi"



Zama Mom tayi zuciyarta na tafasa tace “ke me kikace masa da yaja miki wannan dukan sa'ar
haka?" Cikin shassheqar kuka tace “wai...wai don na shiga ya fito daga wanka shine na matsi
mai zan shafa masa ya juyo ya dakamin tsawa wai na fice masa daga part shi...shine nace
karuwa ma ta samu lkcnsa balleni da zanzama matar sunnah shine ya juyo yacemin wai karna
qara cewa da uwar yarsa karuwa domin tabashi abinda a duniya babu wanda ya amince ya
bashi sai itadin kuma Koda zaa bashi to bayan wadda tabashi zasu biyo, nikuma sai nace ai ko
a shari'a shege bashida gado saboda haka matsayin dan halak yana sama qololuwa dana dan
zina, wlh Mom ban qaraba ban rageba kawai naji ya shaqeni ya hadani da bango ya gwaramin
kaina da gini ni bansan ya akayi ba kawai saiji nayi ya zubar dani a parlour yasa belt ya rinqa
dukana kamar jaka daqyar su Solomon suka qwaceni...."



Ta qarashe mgnr cikin gunjin kuka ta zame bayanta Mom tayi saurin rintse idonta saboda yanda
ya farfasa Mata jiki da belt tace “yanzu Mom haka zan rayu da Yaya Taheer babu tausayi babu
soyayya ace karuwa ma tafika matsayi a gurin mijinka, gsky Mom da sake duk da inason Taheer
Allah ya jarrabi zuciyata da qaunarsa tun bangansa a zahiri ba Mom zan iya jure kowanne
wulaqanci a gurinsa indai zai rayu dani matsayin matarsa saboda nasan yanda ciwon so yake
nasan abinda yakeji Mom amma bazan dauki duka akan karuwa ba Mom waini meye
Habeeytan nan da yake yawan ambata take dashi dani bani dashi? Meye tafini don Allah ki
fadamin meye aibina da Yaya Taheer yaqi naam da soyayyata duk da kasancewata yar uwarsa
ta jini wacce na yarda da naqasunsa da komai na aminta zan rayu dashi a haka"

Shafa kanta Mom tayi ta share mata hawayenta tace “na rasa meye yasa Taheer ya zama me
taurin kai akan yarinyar nan wlh a baya duk abinda na nuna masa bana raayinsa duk son da
yakewa abinnan ya hqr dashi amma nakasa juya zuciyarsa akan yarinyar nan wai harni Taheer
yake kallo yacemin indai ban janye auresa dake ba nabarsa ya auri Habeey ba to shakka babu
zakiyi nadamar zuwanki duniya kuma zina yanzu yafara saboda zuciyar Habeey a hannunsa
take duk yanda yayi da ita haka takebi, Saudat zanji tsananin kunyar Sahabi da Zahrah
qanwata idan har nakasa tanqwara zuciyar Taheer ya aureki bari kiji wani Abu" kunnenta ta
kama ta rada Mata wata mgn sukayi dariya tare da rungumeta tace “shiyasa nake sonki Mom
har mafarkin first night dina a gidan Yaya Taheer nakeyi yauma saida nayi mafarki ganinan a
kwance a qirjinsa yanata shafa sumata"




Rufe mata baki tayi tana dariya tace “saudat bakida dama wai yaushe Abbanki zaizo 9ja ne?"
Lumshe idonta tayi tace “yacemin tunda ya rasa “Matarsa ta fari Hajar lkcn da cikinsa watanni
uku a jikinta ya fara wannan ciwon zuciyar yakejin idan an ambaci 9ja gabansa na faduwa
yacemin kullum mafarkinsa shine yazo 9ja amma gani yake kamar idan ya dawo abinda ya faru
shekaru ashirin da daya baya shine zai qara faruwa"
Girgiza kai Mom tayi tace “har yanzu Sahabi yana mafarkin ganin wannan Dan nasa ko yarsa
don ko jiya da mukayi waya da Mamanki take cemin wai yanzu firgita yakeyi yana yawan Kiran
sunan Hajar yana ambaton Ina dansa ko yarsa? Kuma fah bayan rabuwarsu ance nemanta
akayi aka rasa wasu ma suna cewa ta mutu" Share hawayen tausayin abbanta Saudat tayi tace “nima kullum Ina addu'ar indai dan uwana ko
yar uwata tana raye tazo gareni ko yazo gareni Mom kadaici ya isheni Mom banida abokin kuka
banida na dariya banida shaqiqin da zanyi hira dashi naji dadi nasan yanzu da dan'uwana ko
yar'uwata tana kusa gareni da zata rinqa tausata da tayani addu'a akan wannan mugun son da
nake yiwa Yaya Taheer shikuma baya sona dama tun Ina qarama Yaya Taheer ya tsaneni" ta
qarashe maganar cikin kuka me narkar da zuciya.



_Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020
zuwa_ _10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan_ _rikitaccen labari me cike
da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne._
_Account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB, saiki tura evidence_ _of payment ta wannan
number 09013718241_
_Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400 ta wannan number_ _09013718241 kada ki manta
lambobin katin ake buqata ko hotonsa._

# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*


*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*UMMUH HAIRAN*


_Qarshen free page na Happy sallah_


_Please ki biya kafin ki karanta nidai bazanyi Allah ya isaba Amma ban yafeba, da masu
fitarmin da masu karantawa basu biya ba kuda Allah_



*5*



Shafa kanta tayi tana tausarta saboda tasani iyayenta basason bacin ranta shiyasa take
lallabata saboda a gudun abinda kaje yazo amma taci alwashin duk yanda Taheer zaiyi saidai
ya mutu aure tsakaninsa da Saudat babu fashi.
Yini sukayi tanata rarrashinta hardai ta samu ta ware Bushirah da Kubrah suka fito cikin
shigarsu ta alfarma suka tarar dasu a parlour Mom ta dubesu tace “Ina zakuje?" Cikin yauqi
Kubrah tace “zamuje mugano yarmu ne kada Yaya yasamu a blacklist" wata uwar harara ta
watsa musu tare da jan tsaki ita kuwa Saudat mutuwar zaune tayi saboda mamaki wai zasuje
su gano yarsu yar zinar?




Bushirah ce ta dubi Saudat tace “dama kin tashi munje kya ragewa kanki damuwar son maso
wani ko banza kyaganshi acan gurin gudaliyar yarsa da matarsa da yakejin amutu ko a rayu a
kanta"
Wasu hawaye ne suka zubo mata ta miqe ta shige daki ta fada gado ta rushe da kuka ta fahimci
a gidan daga Mom sai Dad sune suke sonta yaran gidan gabadaya yan partyn abinda Taheer
keso ne hatta da Mahfuz da baya qasar da aka kirashi aka fada masa cewa yayi kema dai Mom
shirme kikeyi kinsan dai blood bazai taba yi miki biyayya ba indai akan baben nan ne wlh Mom
ni kaina don dai blood ya rigani afkawa ne badon hakaba da tafi haka zaayi, Mom ki share
kawai irin wannan auren fah dadine dashi tasanshi yasanta awonsu daidai ne Zaki wani zo ki
hadashi da wata qyailar yarinya...."

Kalaman na dawowa Saudat tanajin bugun zuciyarta na qaruwa ta miqe zumbur ta fita ta tarar
dasu suna shirin tashin mota ta qarasa da sauri ta bude ta shiga suka kalleta sukayi dariya
Kubrah tace “iska tana wahalar dame kayan kara nifa banga abinda zaisa na rinqa bata lkc na
akan namijin da baya sona ba musamman Yaya Taheer me masifar tsaurin raayi kinaji fah a
gabanki Jabir yake fadawa Mom ita kanta Habeeytah bata tsira daga wulaqancinsa ba idan ya
tashi itama da yake iqirarin yanaso kenan balle ke yar karere"
Itadai Shiru tayi batace qala ba har suka dauki hanya suka fara tafiya sunata hirar samarinsu
Saudat dai bata cewa komai sai tsiyayyar hawaye.




Sai magrib suka isa suna zuwa sukayi parking suka fito daidai lkcn yana fitowa da waya a kare
a kunnensa yana cewa “wlh blood bakaga babyn ba kamar kai itama da Mom take kama nayi
Mata huduba da Safeenatul Najah....."
Katse maganar yayi lkcn da sukayi karo da Saudat yayi baya da sauri tare da tsartar da yawu
yace “ke wacce irin banza ce bakya ganine" cikin rawar jiki tace “ban...ban kula ba Yaya Taheer
kayi hqr" tsaki yayi ya matsa gurin yan uwansa suka rungume juna dama gaisuwarsu kenan
yace “ashe zakuzo na dauka Mom bazata barku ba" dariya Bushirah tayi tace “ai dole abu namu
maganin a kwabemu"




Dariya sukayi dukkansu banda Saudat data zubawa sarautar Allah ido ya kama hannunsu suka
shiga dakin Granny tana sallah itakuwa Habeey tana kwance kamar gawa saboda shaqar da
Mom tayi Mata ta mayar da ciwonta farko, ya saki hannunsu ya matsa ya sanya hannunsa ya
tattare Mata gashinta daya rufe Mata fuskarta yayi kissing lips dinta yace “a kowanne hali
kyaune dake Habeeytah"
Gyaran muryar Granny yasashi saurin janyewa kunya kamar ya nutse ya juyo tare da sosa
kansa ta sakar masa ranqwashi tace “kaikam kwai fitinannen namiji a jinyacen ma bazaka qyale
yar mutane ba anya kuwa Taheer ba Mata hudu zan aura maka ba?"




Murmushi yayi yace “bazasu mayemin gurbin Habeeytah ba ita kadai gayyace Granny a duk
matan duniya babu wacce zata iya dani sama da Habeeytah" wani mashine ya caki zuciyar
Saudat tayi saurin juyawa zata fita Kubrah ta riqo hannunta tace “bakiga yar taki ba don nasan

a hannunki qila zata rayu" sake hadiye wata kibiyar baqin ciki tayi ta caki qahon zuciyarta ta
nemi guri dabar ta zauna.
Shikam yama manta da an halicceta a gurin surutu kawai yakeyi yana fasaltawa Granny irin son
da yakeyiwa Habbatullah tare da zubawa Safnah ido yana murmushi yace “wlh Granny ji nakeyi
kamar na hadiye my daughter saboda nakasa fasalta irin son da nakeyi mata nifa yanzu ko ke
kikace bakison yata Allah idan muka rabu har abada bare wani banza da rayuwata batayi kama
da tasaba dan karere"




Sarai duk wanda yake gurin ya fahimci da wadda yake amma shi har cikin ransa bada itan
yakeba, Bushirah ce ta karbi Safnah ta zuba Mata ido tace “wow! Yaya wannan babyn kamar
jinin larabawa Masha Allah amma Yaya kamar ba bakwaini ba"
Granny ce “nima da aka haifeta nace ba bakwaini bace saida likitan ya aunata yace kawai dai
me girmance amma watanta bakwai da kwana daya a cikin mahaifa yanzu ma ance a daina
jagwalgwalata amma wannan dan rawar kan yaqi barinta ta huta" murmushi yayi yace “aini
dama komai zanyi ban iyaba indai a gurinki ne tsohuwa dake" A kasalance Saudat ta taso ta leqa fuskar yarinyar ta zuba mata ido tanajin faduwar gabanta na
tsananta a ranta tana raya dama itace ta haifa masa ita qila da soyayyar yarinyar zatasa yasota
itama.




Miqo hannu tayi zata karbeta yayi saurin dauke abarsa yaje ya kwantar da ita a kusa da uwarta
sai yanzu Saudat ta samu damar kallon Have dake kwance matsayin gawa tayi saurin matsawa
gabanta tana furta “lahaula wala quwwata illah billahil aliyul'azeem" hannunta takai zata taba
fuskar Habeey yayi saurin riqe hannunta cikin tsawa yace. “Idan kika kuskura kika tabamin mata wani abu ya sameta wlh sai nayi shari'a dake
gabadayanki na tsaneki Saudat...."
Rufe masa baki tayi jikinta na rawa tace “nikuma inasonka a haka Yaya kuma saina aureka
Koda kuwa zaka kasheni don qiyayya, Taheer ba takai nakeyi ba yanzu na gama dakai domin
ko kanaso ko bakaso saika aureni dole"..........


_Gareku masoya garabasa gareku saboda murnar bikin babbar sallah daga yau 3/8/2020
zuwa_ _10/8/2020 na rage kudin da ake biya domin samun wannan_ _rikitaccen labari me cike
da turka turka single Zaki biya 150 VIP 400 idan ta account ne._
_Account 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB, saiki tura evidence_ _of payment ta wannan
number 09013718241_
_Idan katine kuma Zaki biya 200 VIP 400 ta wannan number_ _09013718241 kada ki manta
lambobin katin ake buqata ko hotonsa._

# *UMMUH HAIRAN*
[8/9, 4:07 PM] OPEN EYES MULTIMEDIA: *HABEEYTAH*
*_DUBAI PART 2_*


*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*UMMUH HAIRAN*


*6*



Tsayawa tayi sake da baki yana kallon ikon lillahi wai saita aurets dole ko a Ina aka taba yiwa
namiji auren dole? Murmushin tausayinta yayi shi gabadaya ya gama raina hankalinta hakanan
yakejin amai yana taso masa idan ya kalleta.
Juyawa yayi ya fice daidai lkcn wayarsa tayi qara ya daga da sauri tare da kasheta ya mayar
aljihunsa kusan ko yaushe a tsakanin jiya da yau sai an kirashi da number qanin na habeey
Ibrahim shikuma haushin abinda Addah tayiwa Habeey akan cikinsa yasa yaji ya tsani duk wani
wanda ya rabeta basu da adalci dangin Habeey ko kadan basusan darajar dan Adam ba, basu
da damu da itaba itace ta damu dasu take sadaukar da komai domin danginta.




Da wannan tunanin ya shiga mota yana Shirin tashinta qannen nasa suka fito Bushirah ta
matso gabansa tace “sati biyar akasa aurenka da Saudat Yaya a halin da aka ciki Habeey da
Safnah sunfi kowa buqatarka don Allah kada kayi sakacin da baiwarka Allan nan zata qara
shigs gararin rayuwa Yaya Taheer jin Habeey nakeyi kamar yar uwata ta jini" Riqe hannunta yayi yace “karki damu qanwata babu Wanda ya isa yayimin auren dole auren ma
da wannan tsakuwar yarinyar haba suma su Dad wasa sukeyi wlh Idan suka suka matsa zan
iya farke shegiya ta mutu kowa ya huta"




Yana gama fadin haka ya figi motar a guje ya nufi gidan Granny ya shiga bangarensa na gidan
yayi wanka ya kwanta ya fara aikin sanar da abokansa cewa anyi masa haihuwa mamaki sukeyi
sosai yaushe yayi aure da har matarsa ta haihu.
Shikam ko a jikinsa gani yakeyi ai shima aiki yayi ya samu abarsa sabida haka ya cancanci a
tayasa murna, daya gama buge bugen wayar tasa sai ya budo hoton sahibar tasa da yar tasa
ya rinqa kallo yana murmushi har bacci ya daukesa.
Cikin sati biyun da habeey tayi a asibiti abubuwa da dama sun faru ciki harda qarfafuwar mgnr

auren Taheer da Saudat tabbas Saudat tana cikin matsananciyar damuwa saboda Wanda
takeyi dominsa din baisan tanayi ba tana kallon yanda Khamal da Sudess samarin su Kubrah
suketa rawar qafar bikin amma banda nata angon dako kallon tsiya bata samu a gurinsa balle
na arziqi.



Da taimakon Hajiya Ummah yayar Mom da Zahrah mahaifiyar Saudat aka shiga aka fita aka
cusawa Taheer jin tsanar Habeey a ransa sunyi duk me yuwuwa su cusa masa qiyayyar
Safnansa amma abin ya faskara saima kamar qara masa qaunar yarinyar da akeyi.
Cikin sati biyun jikinta ya fara kyau sosai ta fara sanin waye yake a kanta, farkon fari kullum a
asibitin yake yini amma yanzu sai ya yini sur baizoba saidai ya kira a waya yaji ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login