Showing 51001 words to 54000 words out of 58684 words
akalar idanunta kan wanda ke mgnr cikin yanayi na rashin
madafa ta zubansa idanu tanason tuno inda ta sanshi shi ta kasa tunawa ganin yana nufota
yasata janye injin idanunta daga kansa ta zubawa selling idanu, hakan ya bashi damar
matsowa har inda take ya zubanta idanu a hankali yace “inane yanzun keyi Miki ciwo?" Shiru tayi masa brain nata na tariyo mata dalilin faɗawarta wannan halin ta yunƙura zata tashi
da sauri mutumin ya riƙe ta tare da ƙwalawa wata nurse kira suka taimaka mata ta tashi zaune
ta dubesu cikin rashin hayyaci tace “kwanana nawa anan?" Kallon juna sukayi namijin yace
“biyu" cikin tashin hankali tace “Na shiga uku ɗana Hudais ina yake a wanne hali yake yanzun?"
Babu me amsar wannan tambaya tata domin basusan komai game da itaba har gara ma Dr
Amin shi yanayiwa yanayinta kallon sani amma ya rasa gane inda yasanta, kalmar ta ɗaya ta
sanyashi jin wata faɗuwar gaba ta ɗarsar masa.
Hawaye ne ya rinƙa zubo mata wani na bin wani ta ɗago cikin kuka mara sauti tace “Don Allah
ku taimaka min ku faɗamin halin da Hudais yake ciki inajin tsoron kada wani abu ya sameshi
gashi mahaifinsa baya gari...."
Dafa gefen gadon Dr Amin yayi yace “Kiyi hƙr kinga yanzu bakida lfy ƙafarki akwai ciwo
sakamakon accident ɗin da kika samu kuma abinda ke cikinki yana samun barazanar zubewa
idan kika cika takurawa da tunani komai zai iya faruwa" batace masa komai ba kuma bata daina
kukan da takeyi ba ta kwantar da kanta a cikin cinyarta can ta ɗago tace “Wai nan ɗin wanne
gari ne?" Nurse Zainab ce tace “Kina ne Abuja ko kinsan wani anan?" Da mugun sauri ta dago
tace meye ya kawoni Abuja....." Maganar ce ta shaƙeta saboda irin kallon da Dr Amin yake yi
mata ta kawar da kai ta fara ƙosawa da wannan mugun kallon nashi da ta rasa dalilinsa.
Kwanciyarta Nurse Zainab ta taimaka mata ta gyara Dr ya fita yana cewa Zainab a bata kulawa
zanje gda na ɗan huta idan na dawo za'a kwance wannan bandejin aci gaba da treatment din
ƙafar a kula sosai" jinjina masa tayi ya dubi Beebah yace “Madam ko kina bukatar a taho Miki
da wani abu?" Baisamu arzikin ko daga hannu ba hakan ya tabbatar masa wannan duk inda ta
fito miskilar gaske ce bai takura kansa da son sai yaji daga gareta ba ya juya ya fice yanajin
wani irin yanayi me nauyi game da ita a zuciyarsa saidai shi da kansa gargaɗin kansa yake yi
domin yanayi ya nuna itan matar wani ce ko kuma sakin wani ce. Da wannan mutuwar jikin ya isa gdansa ya buɗe ya shiga yayi parking ya fito ya nufi kofar da
zata sadashi da asalin cikin parlourn gidan ya buɗe ya shiga babu kowa a parlourn don haka kai
tsaye ya nufi sama acan ya jiyo hayaniyar yaran ya isa ya bude dakin nasu sunata wasansu
suna ganinsa sukayo kansa suna “Oyoyo Dad" kama hannunsu yayi yana musu yar gajerar
dariya yace “Ina Mom ɗinku?" Ƙaramin ne ya karyar dakai yace “Yau Mom hutu takeji tace kada
mu dameta" yasan ƙiriniyarsu shiyasa ya saki hannunsu yace “Ok kuje kuyi alwala bari nayi
wanka nazo muyi jam'in sallar Azahar" shigewa ciki yaran maza guda biyu sukayi da gudu yayi
murmushi ya nufi ɗakin uwargidan nasa ya buɗe tana kwance a gado tana latsa waya tana
ganinsa ta tashi tanayi masa murmushi ta tarosa tayi hugging nasa tare da kissing ƙirjinsa tace
“your are welcome my jannati" shafa kanta yayi yace “Welcome sweeter ya fama da ƙiriniyar
yara?"
Rausayar dakai tayi tace “Sun dameni habeebty shiyasa nace suje suyi playing games su barni
na huta" Safeenah kenan macen gaske ta samu lambar yabo wajen iya kula da miji matsalarta
ɗaya baƙin kishi ko kaɗan bata ƙaunar taga wata mace ta raɓi mijinta wannan yasa bata ƙaunar
duk wani abu da zaisa mijinta yaji a ransa ta cancanci yayi mata kishiya, ta gwammace ko
zatasha wahala itadai tasha indai zata rayu da Dr Amin ɗin ta ita kaɗai, wannan kenan.
Jansa tayi har bathroom sukayi wanka suka fito yaje sukayi sallah su da yaransu sannan suka
zauna cin abinci sunacin abincin zuciyarsa na gurin petiant ɗinsa yarinyar ta tsaye masa a rai,
yanason jin dalilin barowarta gda shikam yanayinta yana nuna masa duk inda ta fito babban
gidane batayi masa kama da matar yara ba. To yau ɗin ma bai iya bawa Safeenah labarin petiant din tasa da baisan sunanta ba sai ita ce
tace “Nikam Sweeter ya labarin yarinyar da kace tsautsayi yasa ka bigeta a Kano Amma ka
kawota asibitinka saboda ka bata kulawa?" Numfashi ya sauke yace “har yanzu babu wani
labari game da itan saidai yanayi yana nuna itaɗin matar wani ce Inma mutuwar aure tasa ta
baro gidanta ko kuma wata babbar damuwa to koma dai menene inason ta kara samun sauƙi
sai muyi magana a nutse"
Jinjina kai tayi tare da cewa “To Allah yasa muji alkhairi" amsawa yayi da Amin ya miƙe yace
“inajin bacci zanje na ɗan kwanta hudu ki tasheni" itama miƙewa tayi suka tafi ɗakin tare suka
kwanta suna ƴar hirarsu ta ma'aurata har bacci ya ɗauke su.
***********
Kwanan Habeeb ɗaya a Lagos hankalinsa ya dawo gida saboda yinin da yayi yana kiran wayar
Beebah tana ring amma ba'a ɗagawa, gashi duk wani wanda zai samu bayani ta gurinsa ya kira
wanda ya ɗaga ne zaice masa kawai ya dawo gida babu lafiya wasu kuwa basa ɗagawa, lkcn
da Najeeb da Hajiya Kilishi suka sanar dashi gidan babu lafiya dare yayi nisa don a kallah
lokacin sha biyu ta wucce. Dole tasa ya kwanan zaune sai wajen asuba ya samu bacci barawo ya ɗauke shi aikam babu
shiri ya tashi saboda ko a mafarkin baiga alkhairi ba karfe takwas jirginsa ya daga sai Birnin
Dutse yayi saa kuwa Najeeb na jiransa kai tsaye gdansa ya nufa dashi cike da tausayin halin da
aminin nasa zai zama a ciki, shidai ya hakikance duk wannan abun da akace ya faru koda
Habeeb kamawa yayi da idanunsa yanda yakeson yarinyar nan bazai taɓa yanke hukuncin da
Mai Martaba ya yanke wa auren su ba.
Tun daga babban parlourn ya fara fuskantar tabbas gidan ba lafiya lau yake ba domin kuwa
babu wata alama da take nuna an gyara shi yau, haka ya kutsa sashin Beebah yana ƙwala
mata kira amma shiru yanda yaga ɗakin a hargitse kayanta duk a baje a kasa yasa gabansa
faɗuwa ya juya ga Najeeb yace “Batada lafiya ne?"
Sunkuyar dakai Najeeb yayi ya riƙe kafaɗarsa da ƙarfi ya jijjigashi yace “Ka sanar dani meye ya
faru da Wyf bayan tafiyata?" Janyewa yayi yace “kazo muje cikin gida zakaji komai" to dake
neman bayani yakeyi baiyi musu ba yace “nasan ma bazai wucce suna can ba" da wannan
suka fita suka nufi gidan sarautar suna zuwa ya fita a motar ko parking Najeeb bai gama yi ba
ya shige ciki yana ƙwalawa Kilishi kira, tana ɗakinta tanaba Hudais madara taji kiran nasa
gabanta ya yanke ya faɗi tasan yau hauka ne a gidan harsai anyi kamar ayi masa turu.
Miƙewa tayi ta fita yana ganin Hudais a hannunta yace “Ina Wyf ɗin take Kilishi jikin nata ne ya
matsa ne?" Sunkuyar dakai tayi hawaye ya zubo mata tace “Tabbas Habeebu Wlh tallahi
Habeebatullah bata cikin mutane masu dauɗa da zunubin zina amma kash abin tur da Allah
wadarai anyi amfani da wani saurayi da kuma shaidar da maigadin gdanka ya bayar an kitsawa
Mai Martaba ƙarya da gaskiya akan cewa tun lkcn daka tafi London Beebah ke kawo maza
gidanka sai jiya asirinta ya tonu Habeeb Mai Martaba yayima Beebah korar kare tare da aron
bakinka ya datse igiyoyin auren dake tsakaninku, bayan haka kuma ya karɓe Ibrahim daga
gareta, wlh tun jiyan da abin ya faru na baza mutane su lalubomin ita don na hakikance wannan
ƙazafi ne ƙage ne..........
[5/19, 7:59 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 45-46*_
_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number
09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_
_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba_
Tunda Kilishi ta fara mgnr jikin Habeeb ya ɗauki wata rawa ya miƙe tsaye da nufin ya fice jiri ya
fara ɗaukarsa dole ya koma ya zauna yana tare da dafe kansa dake sara masa da ƙarfi jikinsa
na ƙara ɗaukar tsuma ya furta “Innanillahi wa inna ilaihirraji'un Allahumma ajirni fih musibati
wa'akalifni khairin minha" yayi wannan furuci yafi sau ashirin kafin ya aro juriya ya dago
idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur ya zubasu akan Kilishi yace “Yanzu ina ta tafi?" Cikin
sarewar murya Kilishi tace “Inda nasan inda ta tafi da bazakaji meye ma ya faru ba Habeeb"
Sake dafe kansa yayi yana ayyana abubuwa da yawa tabbas ya tabbata wannan tsabar
sharrine da makirci aka ƙullawa Habeebah ko kaɗan baiga laifinta ba domin Hausawa sunce in
wani yaƙika da yini wani da shekara yake neman ka kuma ƙasar Allah me yalwa ce in aka
ƙyamace ka anan idan kayi gaba murna za'ayi dakai, Amma shima Yakamata kafin ta tafi ta
dubashi meye ma yasa bata kirashi ba ya nema masu mafita domin ya haƙiƙance ko Shari'a
bata isa rabashi da matarsa ba matuƙar yana numfashi a doran duniya bare kuma ma akan
karya da son zuciya.
Miƙewa yayi ya nufi ƙofar fita yana haɗa hanya kamar ɗan ƙwaya sukaci karo da Mai Martaba a
hanya ko kallonsa baiyi ba yayi gaba abinsa Najeeb yace “Habeeb Mai Martaba na magana"
batare daya juyo ba yace “Me zanyi masa to son rayuwata yakeyi da zaimin magana ya barni
na mutu ma mana tunda burinsa kenan. Yana faɗin haka yana shiga Mota dake Najeeb bai cire key ɗin ba ya kunna ta da mugun gudu
ya fice daga gidan sarautar yanda yake tuƙin ya tsorata kowa don tabbas ba cikin hayyaci yake
ba.
Shikuwa kamar yanda zuciyarsa ke gudu wajen ganin ya isa inda zaiga Beebah haka yake keta
mugun gudu a hanyar ya nufi ƙauyen su Beebah karo na biyu tun bayan aurensu da yazo
ƙauyen ya tsaya yana ƙare wa gdansu Beebah kallo yasha gyara kamar baa ƙauye ba yananan
tsaye Baba Jimo ya fito ya tsaya turus ganin Habeeb ɗin a tsaye jikin mota. Cikin hassalar bala'i ya nufoshi yana nunashi da yatsa yace “Wato kai kunnen ƙashi ne
dakai ko nace karka ƙara takowa gareni shine ka sake dawowa halan ajali ne ke ɗawainiya
dakai....."
Cikin karayar zuciya Habeeb yayi ƙasa hawaye ya zubo masa yace “Wlh Baba ba laifina bane
ko a mafarki bantaɓa jin a raina akwai ranar da zan iya rabuwa da Beebah ba Bana Beebah
rayuwata ce ka taimakeni ka bani matata......
Kallon bakada hankali ya rinƙa bin Habeeb dashi can yace “Kai yaro fice cikin ƙwayar
idanuna kaga nayi kala da wasanka? Zakazo kana cewa na baka matarka wacce matar ke
gareka a gurina?" Miƙewa Habeeb yayi cikin nunkuwar tashin hankali yace “Wai Beebah banan
tazo ba Baba?" Duk da Baba Jimo yana cikin halin tsananin fushi Saida gabansa ya faɗi yace
“batazo ba ina tayi cemaka tayi zatazo nan?"
Hannu Habeeb ya zuba a kansa yace “Na shiga uku Ni Habibu Habeebah ina kike....."
Cakumarsa Baba Jimo yayi yace “Na rantse da abar dogarona kamar yanda ka ɓatar min da
Bibo kaima labarinka saiya shafe saina ɓatar dakai...." Shi baima damu da riƙon da yayi masa
ba hawaye kawai yake shara yana cewa “Mai Martaba ka cuceni ka wargatsamin gda ka tafi da
farin cikina, yanzu ina Beebah tashiga ita ba cikakkiyar lafiya ba?" Fir Baba Jimo yaƙi sakin Habeeb kawai sai huci yakeyi yau ga ranar yayansa Uda gashi
mutuwa tayi gaggawa, daƙyar mutane suka raba hannun Baba Jimo da kwalar rigar Habeeb
rigima ta sarƙe shi Habeeb na roƙonsa ya bashi matarsa idan yasan tazo shi kuma yana
rantsuwar saiya fito masa da yarsa rigima har gidan Dagaci koda Dagaci yaji abinda ke faruwa
a bakin Habeeb hankalinsa yayi mugun tashi shima tabbas abin akwai tashin hankali gashi
babbar damuwar baasan inda za'a nemi Beebah ba.
Duk yanda Dagaci yaso Baba Jimo yabar Habeeb ya tafi yaji da damuwarsa hanawa yayi Saida
Dagacin yasa aka kira irin bokayensu na tsubbu suka tabbatarwa da Jimo Habeebah tananan
cikin aminci kuma zata dawo saidai basusan inda take ba, to sannan ne fah hankalinsa ya
kwanta yabar Habeeb ya tafi amma da sharaɗin duk inda Habeebah take ya nemo masa ita
tunda ubansa bayason zamansa da ita to ta gama aurensa har abada.
Shidai bai bawa mgnrsu muhimmanci ba burinsa kawai sanin inda Beebah take, hakanan ya
ɗauki hanyar Dutse ikon Allah ne kawai ya kaisa gida kai tsaye ɓangaren Khausar ya shiga ya
tarar da ita taci wanka sai faman taunar cingam takeyi kamar karuwa.
Babu furuci ba komai ya ajiye mata takarda a cinyarta ya fice daga ɗakin da sauri ya nufi ɗakin
Beebah ya faɗa gadonta yaja rigarta ya rungume a ƙirjinsa numfashinsa na ɗaukewa yana
janyoshi da ƙyar yanda zuciyarsa ke masa zafi a yanzu
Haka baya buƙatar kowa a tare dashi ji yake yi ma kamar ya tashi yabar garin, zuciyace ta
bashi shawarar dole ma ya bar garin da daren ya tattare komansa washegari daga masallaci ya
ɗauki mota sai Abuja Saida ya shiga cikin garin Abuja ya kira babban amininsa da sukayi karatu
dashi a Oxford cikin murna engineer Wali yazo ya taroshi daga yanayi ya fahimci Habeeb na
cikin damuwa haka dai suka ƙarasa gdansa zama Habeeb yayi ya dafe kansa da yakeyi masa
wani mugun ciwo, dafashi Wali yayi yace “Nayi mamakin ziyararka ta bazata haka duk da dai
yanayinka ya nunamin baka cikin nutsuwa shin ko zan iya sanin meye ke faruwa?"
Iska ya furzar ya miƙe ya nufi wani ɗaki ya buɗe ya shiga bathroom ya watsa ruwa yana fitowa
ya kwanta zazzaɓi na sauko masa me zafi.
Shigowar Wali ce ta sashi sake jan bargo Wali ya janye yace “wai meye yake faruwa ne Habeeb
ina matanka ko wani abu ya faru ne?"
Numfashi ya sauke me huci yace “Ka kiramin likita" baiyi masa jayayya ba ya dauki wayarsa ya
latsa wayar cousins dinsa Dr Al'Amin yayi masa bayani yace masa ok yanzun yanakan wata
petiant ne amma yana gamawa zaizo. Haka sukayi sallama ya aje wayar sukaci gaba da zaman
kurame Wali ya gaji yace “Don Allah ka faɗamin meke faruwa ina Hudais da mamansa?"
Zubawa Wali ido yayi can yace “Bansan inda Habeebah take ba tafiyar da nace maka nayi
zuwa Lagos wasu abubuwa suka faru har yasanya Mai Martaba yanke hukuncin sakarmin mata
da bakinsa bada nawa ba kuma ya ƙwace mata ɗanta ɗaya data ɗauki so ƙauna da burin
duniya ta ɗora masa ɗan da takejin zata iya rabuwa da komai dominsa Zubair Habeebah na
sona amma na tabbatar da a yanda take da haƙuri da kawaici kuma a lkc guda idan hƙrnta ya
kare take da kafiya Wallahi ba zata nemeni ba koda kuwa sona zai zama silar yankewar
numfashinta, meye yasa Mai Martaba zai rabani da zuciyata Zubairu Habeebah rayuwata ce
inajin yanda zuciyata take zafi da zugin ciwo tsaf zata iya daina aiki indai babu Wyf a kusa dani
Wanne taimako zaka bani ta dawo gareni Zubair don Allah Please help me....."
[5/20, 9:07 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 47-48*_
_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number
09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_
_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba_
Jinjina kai da girman lamarin Engineer Wali yaci gaba da yi can Habeeb yace “kasa na faɗa
maka damuwata kuma kayimin shiru Shikenan tunda bakada abin faɗa kaje kaima kubarni na
mutun in hankalinku zai kwanta...." Katseshi Wali yayi yace “Not ka gane Friend ina tunanin
rayuwa irin taku ta gidan sarauta meyesa bakuson bare a cikinku ne meye yasa kuke yanke
hukunci da son rai Wallahi duk da cewa bantaɓa ganin Maman Hudais ba amma zuciyata bata
amince zata aikata wannan abinda akace ta aikata ba haba shi Mai Martaba hankalinsa ne ya
gushe ko kuwa rufa ido akayi masa yarinyar da batasan kowa ba sai kai da Ahlinka yarinyar da
kai da kanka Saida kukasha ƙwarbai kafin ta amince dakai har ku fara gudanar da Sunnah da
ita yarinyar da kowa ya sani ko ƙawa bata taɓayi ba sannan batada fitina kullum cikin nutsattsen
yanayi take Habeeb wato kayi gaggawa daka datse igiyar aurenka dake kan ƙanwarka Khausar
inada yaƙinin ita tasan komai kuma bazai wucce shiri da tuggunsu ba"
Numfashi ya sauke yaci gaba da cewa “Kai akaso a dasawa kokwanto tsana da ƙyamar Maman
Hudais sai aka ga wannan bazai yiwu ba domin bakai ka dasawa kanka yarda da soyayyarta ba
shine aka juya lamarin kan Mai Martaba ta yanda zaka tabbatar da abin shiri ne
Meye ya kawo Mai Martaba gidanka a wannan lokacin kuma meye yasa ba'a bari anji abinda ita
Beeban zatace ba sannan meye yasa ba'a kiraka ba domin sanar dakai a daidai lokacin? To
duk waɗannan abubuwan abin dubawa ne amma bamu da lokacin dubasu kawai ta ina kake
tunanin zamu fara neman yarinyar nan?" Taɓa ƙofar akayi hakan ya dakatar da hirar tasu Engineer Wali ya tashi ya buɗewa Dr Al'Amin
ya shigo yana duban Habeeb sukayi musabaha ya dubi Wali